Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Ma’aruf.... Shin dama Dumba tana k’asar nan tsawon shekarun nan...?”

Take wannan suna DUMBA tai ranking a k’wak’walwan Sameer, tabbas ya tab’ajin wannan suna, idan bai mance ba DUMBA itace matar da Mummynsa tace ta basu shi.... Toh wacece DUMBA.... How’s she connected to all this...?!!”

(Idan mai karatu bai mance ba dai DUMBA itace matar data bada rik’on Ma’aruf (Sameer) hannun Hajiya Fatahiyya).



SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_




*90*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






A hankali Sameer Ke takawa har ya isa gaban Mamy... “Mamy wacece Dumba...? Mecece alak’arku....? Ya akai Dumba ta mik’a rik’ona hannun Hajiya Fatahiyya Mummy na....? Idan ban mance ba according to Mummy ta bani labarin cewa ita wannan Dumbar itace matarsa ta bata rik’ona, sannan aikatau takewa Mummy na... Koda Mummy na ta tambayeta cewa daga ina ta samoni sai ta sanar da ita cewa Aminai uku suna yunk’urin hallak’ani shisa ta yanke shawarin turani wani waje mai nisan zango na tafi almajiranci har Allah ya nufa ta mik’a rik’ona hannun Mummy Fatahiyya.... Shin Mamy ita wannan Dumban wacece ita dan koda na tambayi Mummy ina zan sami Dumba a lokacinda nake neman iyayensa na asali Mummy ta sanar dani cewa ita kanta batasan yanda Dumba take rayuwa ba a halin yanzu.... Yanzu na samu wasu k’arin haske na sanadiyar b’acewata na kumaji wad’anda sukeda alhakin hakan... Tambaya guda da zan maki Mamy shin ita wannan Dumbar wacece... And how are you related...??”

Waje yai tsit da jin zancen Sameer da tambayoyinsa ga mahaifiyarsa, kowa so yake yaji wad’annan amsoshi... Mamy ta d’ago kai tana dubansa kana tace “Ma’aruf... Hak’ik’a Dumba ‘yar uwata ce da muka taso tare... Dumba d’iyace ga Yayar mahaifiyarmu, sanda ta rasa iyayenta rik’onta ya koma hannun mahaifiyarmu... Kaman yanda na baka labari cewa mud’in ‘yan asalin garin Jada ne ta jihar Adamawa, mahaifinmu haifeffen garin Jada ne, mahaifiyarmu kuwa asalinta ‘yar k’asar Mali ce, bafulatanar K’asar Mali ce, yak’i ya tarwatsa iyayensu a wancan shekarun, shi kuma mahaifinmu a lokacin Soja ne, lokacinda aka turasu yak’i da ‘yanta’adda acan k’asar Mali lokacin ya had’u da mahaifiyarmu har ya aureta kasancewar zasu jima sosai a k’asar Mali suna yak’i da ‘yan ta’adda hakan yasa yai aurensa a can... Sun kwashe shekaru da dama suna zaune a Mali suna yak’an ta’addanci har Allah ya albarkacesu da yara ‘yanmata guda biyu, ni da kuma babbar Yayarmu Abidah.... Toh a wannan shekarun ne lokacin Ina k’arama mahaifinmu ya yanke shawarin dawowa damu k’asarsa ta haihuwa Nigeria sabida gaba d’aya yak’i ya cinye yankinsu mahaifiyata a k’asar Mali, kusan danginta gaba d’aya saiko d’aid’aiku yak’i ya had’edasu ciki harda mahaifan Dumba.. Sanadiyar da yasa rik’on Dumba ya koma hannun mahaifiyarmu kenan.... “ Numfasawa tai kana tace “Barin dakata a nan kar labarin ya shiga cikin wani labari a tak’aice dai kaji alak’ar dake tsakanina da Dumba....”

Sameer ya numfasa kad’an kana yace “Toh ya akai Dumba ta zama wacce alhakin b’acewana Ke hannunta....?”

Wannan karon su Lami da Haule ta kalla kana tace “Wannan ne nima ban sani ba Ma’aruf, Inaga su ya kamata su sanar damu yanda suka had’e kai da Dumba wajen yunk’urin salwantar da rayuwarka... Domin kaw a iyaka sanina rana tsaka Dumba ta matsa min da cewa zata tafi ta nemi danginta a Mali idan mu mahaifinmu d’an Nigeria ne ita bazata tab’a mance cewa asalinta Mali bane.... Dama tin da jimawa Dumba tanada wannan buri shiyasa ko aure tak’i tayi a Nigeria tace har sai ta koma k’asarta ta haihuwa.... Tambayar a nan bansan ya akai ta zamto aminiya gasu Haule ba har suka had’e kai wajen salwantar dakai....”
Kaman daga sama suka sinkayo muryar Haule tana fad’in “Ko a wancan lokacin bama jituwa da Dumba, kuma tabbas Dumba tayi gaskiya da tace Aminai uku suna yunk’urin halak’a rayuwar Ma’aruf.... AMINIYAR SIRRI ba Dumba bace kaman yanda kika d’auka, Aminiyar Sirri tafi Dumba kusanci dake...”
Ta k’arashe maganar tana duban Bara’atu da kanta Ke kife tana hawaye... Dum! Dum!!Dum!!! Sautin bugun k’irjin Mamy.... Gaba d’aya kallo ya komaga Aunty Bara’atu....
Girgiza kai Mamy ta shiga yi cikin rashin yarda da abinda take gani, lokaci guda bakinta na tsanani rawa take furta “A’a... A’a Haule, hakan ba mai yuwa bane.... Haule hakan bazai tab’a kasancewa gaskiya ba....!!!”

Haule ta shek’e da wani irin dariya kana tace “Gata nan gabanki ta musa idan ba itace AMINIYAR SIRRI BA, ta musa idan ba itace ta jagoranci ragamar salwantar da d’anki ba... Gata nan gabanki....”

Innnalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Allahumma ajirni fi musibati wa aklifli khairan minha.... Kalaman da zuciyar Mamy Ke iya nanatawa kenan, k’ololuwar tashin hankain data tsinci kanta ciki bazai misaltu ba, ta ya za’ace ‘yaruwarta ta jini zata mata haka... Ta ya za’ace ‘yaruwarta da ta aminta da ita zata mata wannan babban butulci... Kai gaba d’aya jama’an dake wajen kansu ya k’ulle... Harta su Abbah dasu Mamani saida tashin hankali ya nuna sosai a tattaredasu, tashin hankalin da zasu iya cewa tun bayan b’acewar Ma’aruf basu sake fuskantar irinta ba.... Wato Aminai uku da sukai yunk’urin Salwantar da Ma’aruf kaman yanda Dumba ta fad’i Haule ce da Lami had’ida Bara’atu... Kai wannan irin butulci da mai yai kama, Ke duniya mecece cikin ki bacin tarin maciya amana da azzalumai....
Dik yanda Engr yaso ya fice a wajen ya basu privacy tinda yaga rikici ne na family amma ya kasa, ji yake bazai iya tafiya ba har sai yaga k’arshen al’amarin nan, ji yake can k’asar zuciyarsa tamkar ya tab’a rayuwa a wata duniya irin tasu....Tausayin mahaifiyar Sameer ya cika zuciyarsa, ga wani shauk’i da yakeji tinda yaji an ambaci Sameer da suna Ma’aruf, wani ikon Allah ashe sunansu d’aya gashi labarinsu yaso yayi shige tinda shima Sameer ba a gaban iyayensa ya girma ba shima rabasa da nasa iyayen akai... Tabbas labarin rayuwarsu yaso yai shige....

Kasa furta komai Mamy tai, ta kasa tab’uka komai, saiko tsayuwa sororo da tai gaban Aunty Bara’atu... Sameer yasa duka hannayensa biyu ya tallafi mahaifiyarsa ganin tayi rauni sosai, shin waye ma bazai rauni ba da jin irin wannan labari mai tsananin tashin hankli....
Girgiza kai Mamy taci gaba da yi tana duban Aunty B sa kanta ke kife k’asa, tabbas da ace k’asa zai gsaga ta shige ciki da hakan ya fiye mata sauk’i... Ta ya zata iya d’ago idanu ta dubi ‘yar uwarta...? Ta yaya, bayan wannan babban al’amari dake faruwa dasu....

Murya a matuk’ar sanyaye Mamy Ke fad’in “Bara’atu d’ago fuskarki ki k’aryatasu... Nasan hakan sam ba mai yuwu bane... D’ago kice min K’arya suke ‘yar uwata... Kinji, Dan Allah d’ago ki k’aryata wannan mummunar sharri da suke jifanki da ita... Bara’atu kice min k’arya suke ba kece Aminiyar Sirri ba... Kinji ‘yar uwata...!!” Ta k’arashe tana mai jijjiga Aunty Bara’atu da har lokacin fuskarta Ke kife k’asa....Haule da Lami suka dubi juna suna masu aikama juna makiran murmushi....
A haka Mamy taci gaba da jijjiga Aunty B da iayaka k’arfinta, wannan karon zaka iya hango tsananin tafasa da zuciyarta keyi sabida yanda fuskarta ta rine zuwa jajazir haka nan k’wayan idanunta... Fad’i take “Bara’atu ki k’aruatasu nace... Ki k’aryatasu ‘yaruwata, bazaki tab’a min haka ba ni na sani... A lokacinda na rasa Ma’aruf kina taredani.... Baki tab’a k’yaleni ba daidai da dak’ik’a guda... Dik kalan tashin hankalinda na shiga, taredake nai overcoming d’insu, a lokacinda kowa ya juya min baya ked’in kina taredani ‘yaruwata... Abinda suke fad’i bazai tab’a yuwa ba.... Ki cemin k’arya suke Bara’atu..!!!”
Aunty B da itama kanta ahesshek’ar kuka take, a zuciye ta fincika ta d’ago tana duban Mamy lokaci guda take furta “Eh... Eh Ya Mariya ni ce Aminiyarsu ta Sirri.... Taredani suka shirya komai... Na taimaka masu sun cika burinsu na kawarda Ma’aruf gaban iyayensa.... Kuma ni ce nan na mik’a shi hannun Dumba...”
Innalillahi wa Inn’ilaihi Raji’un.... Kalman da zuciyoyi sukaci gaba da nanatawa kenan.... Aunty B na kuka sosai take duban Mamy da tai mutuwar tsaye a wajen tana dubanta cikin rashin yarda da abubuwan dake faruwa....
Lokaci guda Aunty Bara’atu taci gaba da fad’in “Mamy inaso ki tuna mai ya faru a ranar da Ma’aruf zai b’ace....”
Mamy da hawayen dake idanunta suka k’afe a hankali ta soma furta “Babu abinda ya b’ace a kaina gameda wannan rana da abu biyu suka auku dani... Muhimman abubuwa guda biyu, RASHI da kuma SAMU.... Ranar da na rasa d’ahna Ma’aruf, kuma ranan da na haifi d’iyata Zulfa’u.....
Wata ranace ta Alhamis mai cikeda tsananin zafin rana...

_WAIWAYE_

Shekaru ashirin da Shida da suka Shud’e......

Zaune suke saman tabarma itada d’an nata da bazai haura shekaru uku ba, wata matashiyar budurwa tai sallama ta shigo... Da alama budurwar a gajjiye ta shigo hakan yasa ko gaisarda matar data tadda zaune saman tabarmar batai ba saima fad’i da take “Auchh! Gaskiya ana rana Mamy... Kinji waje kuwa... Wllhi badon jarabawa da muke ba da gobe bazanje poly ba ni wllhi na gaji...” Ta k’arashe tana matashi da jakkanta had’ida d’an kishingid’a gefe...

Matar data kirada Mamy murmusawa tai had’ida d’an muskutawa kad’an sabida bayanta da yai mata tsami sakamon zungureren cikin dake jikinta, haihuwa ko yanzu ko anjima

“Banda abinki Bara’atu mai kukai a karatu, yanzu fah kuka fara...Shekararki ta farko fah kenan, kuma ki godewa Allah cikinmu uku kin sami damar tafiya gaba da sakandare kagi da k’anan shekarunki tinda har yanzu baki kai ashirin ba, dan haka koda wasa kada kiyi sake da damarki kinji koh....”
Murmusawa Bara’atu tai kana ta mik’e ta rungume Mamy tana fad’in “Yah Mariya mai zanyi a rayuwar nan idan babu ke... Ina k’aunarki sosai ‘yaruwata shisa sam bazan iya zaman gidan Ya Abidah ba na zab’i na zauna dake....”
Murmusawa Mamy tai had’ida d’an dungurinta kana tace “Amma ai Yaya Abidar ita ta fara rik’onki kafin nima nai auren koh... Ita d’in uwace a garemu dukanmu dikda abinda ya faru....”
Cikin sauri Bara’atu ta janyo hannayen Mamy tana fad’in “Dan Allah kada ki soma tuno abinda ya faru baya kinsan likita ya hanaki shiga damuwa ko dan lafiyar abinda Ke cikinki sannan idan Abbah yazo ya taddaki cikin damuwa fad’a zaiyi shima...”
Mamy ta murmusa a hankali kana tace “Tabbas Usman shi ya dawo min da Farin cikin da na rasa a baya... Amma Bara’atu har yau na kasa cire alhakin mutuwar Fatima da Ma’aruf a wuyana.... Shin ta yaya zan bar yaro d’an shekaru shida da jaririya sabuwar baihuwa cikin tsumman goyo....?”
Aunty Bara’atu ta kuma kamo hannayenta tace “Babu laifinki Mamy, hakan Allah ya k’addara kuma kema kinyi iyaka naki k’ok’arin ganin kin kub’utar dasu amma Allah bai nufa sud’in masu rayuwa bane... Ina fata Yaya zata fahimci haka watarana, ta daina d’aura alhakin b’acewar d’anta Ma’aruf da kuma ‘yar autarmu Fatima a wuyarki....” Numfasawa Mamy tai had’ida da kai dubantaga Ma’aruf daketa wasan sa hankali kwance... Bara’atu ma kai dubantaga Ma’aruf d’in tai kana tace “Da Ma’aruf Babba yana raye k’ila da yakai shekaru goma sha da ya soma zama saurayi.... Nasan yanda kike k’aunar Ma’aruf Babba Mamy, kuma wannan suna Mamy shi ya saka miki har yabi bakinmu gaba d’aya....”

Mamy ta kuma murmusawa had’ida goge hawayen da suka gangaro mata kana tace “Ma’aruf d’ah na... Haihuwarsa kawai Yaya tayi amma inajin har k’asan zuciyata tamkar na fita k’aunarsa... Kuma ban cire rai ba INDA RAI DA RABON wata rana Allah ya kuma had’amu....”
D’an murmusawa Bara’atu tai kana tace “Mamy Ma’aruf ya tafi kuma Allah ya bamu wani Ma’aruf d’in... Dik irin k’aunar da kikewa Ma’aruf Babba ki had’asu kan Ma’aruf k’arami tinda dama shi d’an Gata ne wajen Kakarsa da iyayensa....”

Mamy ta kuma murmusawa tana mai duban d’an nata yanda yaketa wasan sa hankali kwance...
Muryar Bara’atu ne ya dawo da ita daga duniyar tinanin da ta tafi tana mai furta “Ma’aruf... Zo yaro na...!”
Dubanta yai sai ya mak’e kafad’a ...
“Aw bazakazo ba sarkin ‘yan k’iwa...”
Nanma mak’e kafad’a yai kana ya fad’a jikin mahaifiyarsa yana mai furta “O’o nidai Mammy.....” Cikin muryarsa da yake gwari gwari irinta yara....

Aunty Bara’atu tace “Toh ai shikenan dama na sayo maka motar wasa kuma bazan baka ba....”
Ambato mota da tai yasa yaron zuwa gareta a guje yana fad’in sai ta basa mota,
“Laaa Kaga yaro zai tara min jama’a Nifa wasa nake maka....”
Mamy tace “Ah toh aiko sai ki bashi tinda kin iya zolaya....”

Abu kaman wasa yaro ya dinga kuka sai an sai mai jiyin jiyin.... Baiji bai gani kuka yake....
Mamy ta dubeta tace “Kinsan mahaifinsa baya nan balle ya fita ya sai masa, kuma Kakarsa data k’wallafa rai akansa tanajin kukansa zaki ganta a nan tana sababi, ni kuma ga halinda nake ciki wllhi sam bansan tashin hankali, da kukan Ma’aruf zanji ko kuwa da fad’an Mamani zanji, ki tashi tun wuri tin dare bai maki ba kije ki nemo mota....”

Bara’atu ta mik’e tace “Aiko bara na tafi bakin kasuwa na sayo mai....” A haka ta zira mayafinta ta nufi k’of, yayinda Mamy taci gaba da rarrashin Ma’aruf da kaman an saka masa batir sai kuka yake....
Jim kad’an Bara’atu da dawo a firgice...
Mamy tace “A’a lafiya Bara’atu...? Har kin dawo....”
A d’an daburce tace “Mamy Dumba ce tazo daga gidan Yaya tace tana nemana kuma ba lafiya take ba...”

Mamy da damuwa ya nuna itama a fuskarta tace “Wai DUMBA bata wuce ba...? Inji tin shekaran jiya tace zata bar garin nan...?”
Bara’atu tace “Inaga sabida jikin Yayan ne yasa Ya Dumba bata tafi tin shekaran jiyan ba... Amma tace min yanzu haka akan hanyarta take shisa tazo kirana naje na zauna da Yaya Abida....”
Mamy ta numfasa tace “Toh Bara’atu ko zamuje tare ne....?”

Girgiza kai Bara’atu tai kana tace “Mamy sanin kanki ne Yaya ta miki iyaka da gidanta... Ga kuma halinda kike ciki... Dan Allah kada kije Yaya ta miki wani abinda zai d’aga miki hankali yai affecting d’an cikinki... Ki barni ni zanje kinji koh... Zan kula da ita....”

Jinjina kai Mamy tai jiki a sanyaye dikda cewa har lokacin Ma’aruf kuka yake “Toh shikenan Bara’atu, kije Allah ya tsare kinji koh... Allah kuma shi miki albarka....”

A hankali Bara’atu ta jinjina kai kana ta fice cikin sauri....
Juyowa Mamy tai tana duban Ma’aruf da har lokacin yak’i yin shiru sai kukan a sai masa mota yake.... A hankali ta dafasa tace “Ma’aruf... Mota kake so...?”
Ya jinjina mata kai cikin sauri....
D’an fuzar da iska tai a hankali dikda bayanta da takeji kaman abu na mintsilinta, bata fatan Mamani ta shigo ta taddasu hakan tasan abun bazai kyau ba, dan idan Mamani tai mata tatas Bara’atu ba shiru zatai ba sabida fad’a irin nata itama, ita kuma bata fatan abinda zai d’aga hankalinta dana mijinta tinda mahaifiyarsa ce, idan kaji Mamy ta samu sab’ani da mijinta toh fah ka tabbata akan mahaifiyarsa ce kuma kan an tab’a tilon jikanta Ma’aruf ne... Hakan yasa Mamy ya zaro mayafi tace “Muje bakin kasuwan na sai maka....”
Tiryan tiryan suka d’au hanyar kasuwa tana rik’eda hannun d’anta ga zungureren ciki da ya sauk’a k’asa sosai... Sun isa kasuwa ana cikin mota abu kaman wasa ta soma jin ciwo na k’aruwa, sam bata kawo haihuwa zatai ba, aiko ashe dai haihuwarce tazo, azaba yasa ta saki hannun Ma’aruf tana kame mararta da cikinta... Kan kace me matan da suke kasuwar sun rufu akanta ana k’ok’arin bata d’auki na gaggawa... Tana iya jiyo sautin kukan Ma’aruf yana ambato sunanta “Mamy! Mamy!! Mamy!!!....”
Itama d’in ambato sunansa take “D’ah na, ku agazamin akwai d’ahna a wajen nan... Ma’aruf!!!” Inaaa tuni sarkin kasuwa ya iso da mota matan nan sun saka Mamy ciki an nufi asibitin general da iya dan babu wanda ya saurari cewa da take d’anta d’anta duk a zatonsu d’an cikinta take nufi....
Mamy ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Daga wannan lokaci ban sake jin d’uriyan d’ah na Ma’aruf ba.... Farkawa nai na ganni kwance a gadon asibiti ga kuma jinjira a gabana nad’e cikin showel, abinda na fara fad’iwa nurses d’in shine “Ina D’ah nah... Ina Ma’aruf...? !!”
Nurse ta kusa dani ta d’auko jinjirar da na haifa ta mik’a min tana mai fad’in “Ba yaro kika haifa ba yarinya ce Gata nan....”
Cikin wane irin k’ara nake furta tare nake da d’ah na su bani d’ah na... Nurses sukace su basuga wani yaro ba ni kad’ai aka kawo ni.... Haka na dinga kuka ina fad’in su bani d’ah na, har saida suka min alluran bacci sannan dan ko jinjirar da na haifa na kasa d’auka....
Ko bayan dana dawo hayyacina na tadda labarin haihuwata ya isa ga ‘yanuwan mijina, Haka Mamani tamin chaaa a asibiti tace bataji ba bata gani ba sai na nemo mata jikanta Ma’aruf da ganganci na d’aukesa na tafi dashi kasuwa na salwantar dashi, wannan dalili yasa k’iyayyata data d’iyata Zulfa’u yai tasiri a zuciyar Mamani a cewarta ganganci na ne yasa na tafi dashi dikda ansan tsautsayi sannan ita kuma Zulfa’u itace mai farar k’afa yasa ranan da zatazo duniya d’an uwanta ya b’ace... A b’angaren mijina ma ban sami wani sauk’i ba domin kaw shima da hukuncin mahaifiyarsa yake aiki.... Bara’atu......” Birki ta d’anja sanda ta ambaci sunan Bara’atu kana ta d’ago kod’add’un idanunta a hankali tana dubanta....
Mamy ta sa hannayenta biyu ta share fuskarta kana taci gaba da fad’in “Bara’atu ‘yar uwata ita kad’ai ce bata gujeni ba... Kuma bata juya min baya ba... Tana nan taredani tsawon shakarun nan... Dan harta aure data tashi yi saida naita bata baki nace bazai yuwu ta k’are rayuwarta a kula dani da kuma yarana ba... Bara’atu ta sadaukarda lokutanta dukiyarta soyayyarta da duk wani abinda ta mallaka a gareni da ahalina... Dikda cewa mijinta ba mazauni bane, bata zab’i ta bishi ba, ta zab’i ta zauna dani a nan ta kula dani da kuma ahalina.... Bara’atu itace komai nawa tsawon shekarun nan wacce nake gani naji sanyi, wacce take d’ebe min kewa da soyayyarta mai tsafta, wacce take nuna min hanya a lokacinda na tassama b’acewa, K’anwa data zamto tamkar uwa a gareni... Shin ta yaya matar da muka aminta da ita nida ahalina zata mana haka..? Shin ta yaya zuciyata zata aminta da hakan ....’”” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata...

Aunty B da kukanta ya tsananta durk’usawa tai gaban Mamy hannayenta biyu had’e waje guda lokaci guda take furta “Ki yafeni Mamy... Ki yafeni ‘yar uwata....!!” Ta kasa ci gaba da magana sai kuka.... Wajen yai tsit sai sautin kuka kawai da kakeji...
Haule ta tako tazo tsakiyarsu tana mai sakin shewa kana tace “Toh Mariya kin daiji wacece Aminiyar Sirri kuma tsawon shekarun nan har bayan bayyanar d’anki Ma’aruf bamu daina Aminci da AMINIYAR SIRRI ba..... Ba mijina bane kawai maci amanan d’an uwansa k’anwarki itace gasunk’umar maciyiya amana... Hasalima mu taimakon Ma’aruf muka tasamma yi wannan munafukar k’anwar taki itace tazo da shawarin a salwantar dashi... Itace AMINIYAR SIRRI...”

Wata Murya sukaji daga bayansu tana fad’in “Idan kunyi tunanin Bara’atu itace AMINIYAR SIRRI kunyi babban kuskure... AMINIYAR SIRRI ta rayu ne a tsakaninku cikin jikin Bara’atu..... A yau d’in zaku bud’e bakunan ku da kanku ku fad’i duk irin bak’in aikin da kuka aikata......”

Gabaki d’aya suka juya suna duban k’ofa.. Matar da babu wanda ya tsammaci ganinta a waje irin wannan.....

“Ni ce nan AMINIYAR SIRRI... Sirrikan zasu ci gaba da hak’o kansu... Wasu sirrika ne da wasu mutane suka jima da binnewa... Wasu sirrika ne da aka jima da aza masu k’asa... Kyawawan ayyuka sukan tafiyar da munana... Saidai wasu sirrikan basu yarda su b’oye kansu... Sukan bayyana kansu domin hakan ya zamto izna ga al’umman da zasuzo a baya....!” Ta k’arashe tana isa gaban Mamani da tai mutuwar zaune tana jin kalaman nata.... Yayinda gwaggwanayen Kazaure suka mik’e zumbur, Mamy da Aunty Bara’atu sukai mutuwar zaune suna kallonta....
Wani irin bugu k’irjin Engr yai saida ya dafe garundake gefensa sakamakon ganin fuskar wannan mata da yai.... Take k’wak’walwarsa ta shiga tina wasu abubuwa da suka faru shekaru masu tsawo... Haka ya dinga hango hotunan abin cikin k’wayar idanunsa tin sanda Mamy ta soma kwararo bayananta bugu da k’ari bayyanar wannan matar cikin k’wayan idanunsa... Dikda girma da ya kamata fuska ne da ya jima yana masa gizo a kwanyarsa da k’wayan idanunsa......


SameenaAleeyou📚





*INDA RAI*
_................DA RABO_




*91*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Wannan ya kalli wannan wancan ya kalli wancan, hakance ta kasance... Wata sabuwa ana wata ga wata... Sameer da kansa gabaki d’aya ya k’ulle bud’e baki yai yace “Wai meke faruwa ne a nan... Wacece ke kuma...?!”
Matar ta maida dubantaga Sameer kana tace “Ni ce Aminiyar Sirri.. Nima kuma nayi tarayya ne da wata Aminiyar ta Sirri a yayinda na tura wata Aminiyar ta Sirri ta wakilceni tsakaninsu.....!!”
Haule da Lami harma da Baba Alhaji da mugun mamaki suke kallon matar nan... Wato ita Lami bama tasan mijin Haule nada babban kaso cikin zunubin da sukai tarayya ba sai yanzu.... Ita dik a nata zaton su uku suka k’ulla wannan sharri... Daga ita sai Haule saiko Aminiyarsu ta Sirri... Toh yanzu ga wasu batu suna fitowa daga baya... Lami kanta abin ya soma bata tsoro... Take ta tina jawabin Malaminsu na taubbu da ya tab’a sanar dasu muddin basuyi aikin da kyau ba Toh fah bazasu tab’a fahimtar komai ba, Abu a duhu ne zaita bayyana masu... Eh lallai ta yarda da batun Malam na cewa Abu a duhu... Ta yarda aikin had’aka akai wajen kawar da Ma’aruf tinda ga wasu fuskoki da batasan dasu ba cikin aikin suna kan bayyana...

Yanzu kam kan kowa ya kwance.... Wane irin al’amari ne wannan...??
Take Sameer ya shiga girgiza kai yana huci lokaci guda yake furta “Aminiyar Sirri Aminiyar Sirri..! Aminiyar Sirri....!!Shin Wai menene wannan Kalmar...? Maiyasa har yanzu magana k’wakk’wara ya kasa bayyana...? Maiyasa har yanzu gaskiya guda d’aya ta kasa fitowa... What’s all this..??”
Abbah ne ya nufi Sameer yana furta “Mu fice a nan d’ahnah, muje ka huta...”
Girgiza kai Sameer yake cikeda rud’ani yana furta “No Abbah I need to know everything, every single thing....I need to get to the bottom of this...!”
Baikai aya ba Ya Abida ta katsesa da fad’in “Babu wanda zai bar wajen nan sai an gama warware komai...!” Usman akwai abinda ya kamata kaima ka sani....!!”
Abbah da k’irjinsa ya buga kuma dubanta yai kana ya d’an girgiza kai yace “Ya Abidah kin jima kina shan magani na cutar damuwa (depression) inaga har yanzu baki ida warkewa ba... Ya kamata duk mu watse, duk wanda ya zalinci wani mu fawwala ma Allah komai, a b’angarena nida iyalina na tabbata bamuda matsalar yafiya....”
Matar da ya kirada Ya Abidah ta katsesa da fad’in “Usman ni d’in na jimada warkewa... Sannan akwai wasu sirrika da basu tab’a yardane su binne kansu... Ko Mamani...??”
Mamani da tuni idanunta sun kad’a girgiza kai ta soma tana k’ok’arin mik’ewa take fad’in “Kinga Abidah.... Maza ki fice mana a gida, magana ya riga ya k’are... Yanzu dai ga Ma’aruf Allah ya bayyana mana shi kuma in sha Allah dik muguntar mugu da k’ullin mai k’ulli bazai sake kama jikana ba... Jeki ki tafi can da k’uncin rayuwarki ki....”
Batakai aya ba Ya Abidah ta katseta da fad’in “Dama muguntarsu bai tab’a tasiri akan Ma’aruf ba ko sau d’aya ne kaman yanda sukai tunanin yayi... Kaman yanda sukai tunanin ya tafi tafiya ta har abada da bazai kuma dawowa ba.... Sannan sirrin da kikeso ki ci gaba da b’oyewa d’anki Usman bazai tab’a b’oyuwa ba muddin za’a warware wannan al’amari....”
Mamaki ya cika illahirin jama’an dake wajen idan ka d’auke Engr da har yanzu bai dawo daga duniyar tinanin da yai nisa ciki ba, memory d’insa ne kawai take flashing back... Hotunan abubuwa sunata dawowa kwanyarsa...

Mamani ta dubi Abbah tace “Alk’ali kada ka saurari matar nan... Na rok’i arzikinka kaji d’ahna....!” Ta k’arashe tana k’ok’arin kamo hannayensa....
Girgiza kai Abbah yake cikeda d’imauta lokaci guda yake furta “A’a Mamani.... Inaso naji abinda matar nan zatace....”
Juyowa yai yana duban Ya Abidah lokaci guda yake furta muna saurarenki....”
Ya Abidah ta jinjina kai kana taci gaba da fad’in “Banso kukaji wannan daga bakina ba, amma ku sani dole ce tasa zan amoda wannan Sirri da ya jima a rufe...”
K’irajai sukaci gaba da bugu.... A yayinda Ya Abidah taci gaba da fad’in “Kaman yanda kuka sani nida ‘yar uwata Mariya bama ga maciji, na mata iyaka da kaina, na kumayi iyaka ma kaina da ita da yanda take rayuwa dama duk wani wanda ya jib’inceta.... Saidai hakan baisa na kasa cika alk’awarinda na d’aukawa mahaifiyarmu ba cewa nid’in zan kula da ahalinmu bayan babu

Please Login or Register in order to submit comment