Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace “Aunty Zulfah abinda suka maki naji zafi, kiyi hak’uri dan Allah, wllhi banji dad’i ba gashi nima sun hanani gaisheki wai ni munafuka ce, kiyi hak’uri Dan Allah...” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya....

Murmushi Zulfah tayi kana ta shiga share hawayen dake kwaranya idanun Raihana kana tace “Raihanah ki daina saka damuwa ma ranki kinji koh, nidake irin tamu k’addarar kenan da Allah yaso jarabtanmu da ita, Allah ya bamu ikon ci... INDA RAI wataran duk wad’annan abubuwan zasu gushe mana su zamto labari kinji koh, kar ki mance duk tsanani yana tareda sauk’i kinji koh... Maza koma gida kafin Hajiya ta fahimci kin fito waje....”

Cikin sauri Raihanah ta jinjina kanta kana sukayi sallama da ‘yar uwarta Zulfah ta koma cikin gida a sace taci gaba da aikinta...

Raihanah marainiyace wacce tun tasowarta take shan azaba da uk’uba wajen kishiyar mahaifiyarta wato Hajiya Asabe, duk wani aikatau na cikin gida Raihanah ta iyashi tun kafin takai yanda take a yanzu, sam Hajiya Asabe bata d’aga mata k’afa dukda cewa mahaifinsu nada rufin asiri dai dai gwargwado yanda zai d’auka masu ma’aikata na cikin gida son ransu, da k’arfin gaske Hajiya kan koresu musamman yanzu da Raihanah ta kuma zama ‘yan mata, ko wadataccen lokacin karatu bata samu kaman yanda sauran ‘yan uwanta ke samu, idan ta dawo daga boko aiki na jiranta haka idan ta dawo daga islamiyya aiki na jiranta, badon mahaifinta na raye ba tabbas da ko makarntar Hajiya bazata bari tayi ba. Duk matan da Baffah Ado kan aura basa jimawa a gidan Hajiya kanyi sanadin tafiyarsu, mahaifiyar Raihanah ce ma ta d’anyi k’argo a gidan ba’a koreta ba dashike Allah yasa akwai rabon Raihanah a tsakani saidai haihuwarta da kad’an mahaifiyarta tace ga garinku, da yawan mutane sunfi danganta mutuwar mahaifiyar Raihanah da saka hannun Hajiya Asabe domin kuwa k’iri k’iri Hajiya ke nuna nata nata ne na wani kuwa ba nata bane haka nan mutanen unguwa ke mata lak’abi da Ramin Kura ‘ya’yanta kawai take so, gaba d’aya gidan tarbiya bai wadacesu ba duk goyon Hajiya garesu, Raiha ita ta fita zakka don harta mijin Zulfah ma shaye shaye yake wai anyi masa auren ne ko zai daina ga hangen ‘yanmata duk budurwar da ya k’yalla idanu kanta sai yace yana so, da anyi magana Hajiya tace sharri akewa d’anta anga shine babban jika na miji a gidan. Mahaifiyar Zulfah da danginta sam basuso auren Zulfah da Hafiz ba amma babu yanda suka iya tuni Baffah Alk’ali mahaifinta ya bada aurentawa Hafiz d’an d’anuwansa, koda mahaifin Zulfah yazo mata da batun batayi musu ba sannan take ta amincewa mahaifinta dukda cewa ga irin halin da Hafiz ke dashi uwa uba ga yarinta da yake fama dashi a lokacin da sukayi auren don dudu bai wuce ratan shekaru uku zuwa hud’u ne tsakaninsu ba., Haka nan Zulfah tayita fama da rashin hankalin Hafiz da sunan biyayyawa mahaifi, tabbas ta sakama zuciyarta Allah bazai tozartata ba tinda yaga niyyanta ta kumayi alk’awarin taka muhimmiyar rawa wajen saita rayuwar Hafiz ya inganta don shine abokin rayuwarta a halin yanzu uwa uba sun soma aje zuri’a.....

Tana tsaye bakin kwalta tana neman abin hawa idanunta sunyi luhu luhu, kalaman Mamani dana Hajiya basu daina zarya a zuciyarta da kwanyarta ba, wad’annan mata guda biyu su sukayiwa rayuwarta karar tsaye mahaifiyar mahaifinta da kuma mahaifiyar mijinta, tabbas ta had’u da k’alubale babba a rayuwarta.... Sam bataji k’aran horn d’in mota daketa faman tashi a bayanta ba, tamkar wacce aka zabura haka ta dawo daga duniyar tunani tana mai k’ok’arin juyawa taga mai wannan horn d’in yawa zai d’agata...

Lokaci guda ta saki murmushi kana ta k’arasa ta bud’e marfin motar b’angaren mai zaman banza....

“Aunty B ina yini...? Allah sa dai gida kika nufa ki ragen hanya....” Duk maganganun da take bata bari sun had’a idanu da matar data kira da Aunty B ba, sai faman sunkuyar da kai take bataso Aunty B taga idanunta da suka kumbura ta fahimci kuka tayi....

“Zulfah....!” Aunty B ta ambaci sunanta cikeda kulawa kana tace “D’ago ki kalleni...”

Kasa d’agowa tayi saima k’ok’arin dad’a kauda fuskar da tayi...

Aunty B bata kuma tsayawa bin takanta ba ta shiga janyo fuskar nata tana ganin yanda idanunta sukayi jazir sukayi luhu luhu abinka da farar mace...

Baki sake Aunty B tace “Gidan Hajiya Asabe kika fito koh, ta maki rashin mutuncin data saba koh...?” Aunty B ta k’arashe tana faman huci...

K’ok’arin girgiza kai tayi had’ida k’ak’aro murmushi kana tace “A’a Aunty, sauri nake zan k’arasa gida na samu na d’aura dinner....”

Aunty B ta tsareta da idanun tausayin d’iyar ‘yar uwar nata na kuma cika zuciyarta lokaci guda tanaji ta shiga gidan Alhaji Ado tayiwa Asabe d’add’aya don gwara su sani Zulfah nada dangin mahaifiya masu k’aunarta....

Lokaci guda Aunty B ta kashe motar kana ta fice tana mai furta “Jirani ina zuwa.....”

Ganin yanayin da Aunty B ta fice a motar gashi ta nufi kwanar gidan Baffah Ado yasa gaban Zulfah yankewa ya fad’i, a d’ari ta sauk’a ta takewa Aunty B baya tana rok’onta tayi hak’uri tazo su tafi, ai idan gyalen Aunty B ya amsa itama zata amsa sai faman watsa sauri take yawa wacce ake tinzirata....

Hajiya dasu Sahariyya sun saka Raihanah a gaba suna tambayarta gidan uwar wa ta fita gulma, Hajiya ta dubi Naja’atu dake tsaye bakin famfo ta rik’e kunkumi tana jira mahaifiyarsu ta basu izini su lakkad’i Raihanah kana tace “Najah jeki d’auko min dorinar nan don ubanta tinda bazata fad’a ba....”

Cikin muryar kuka Raihanah ke fad’in “Hajiya wllhi Allah babu yanda naje dan Allah kiyi hak’uri....”

“Bazanyi ba munafuka, badai kin rainani bane har zan sakaki aiki ki tsallake ki fice, yi sauri Najah.....” Ta k’arashe tana janyo wuyar Raihanah a dai dai sanda Aunty B ta banko k’ofar tsakar gidan ta shigo....

Jifa da Raihanah Hajiya tayi kana ta maido da dubanta ga Aunty...

Huci kurum Aunty B keyi kana tace “Hajiya Asabe kiji tsoron Allah ki tuna abinda kayiwa d’an wani za’ayiwa naka, kuma ‘ya’ya mata gareki gidan aure zasu tafi kuma bakisan wasu irin sirkai zasuyi arba dasu a gidan aurensu ba, bama wannan ba gameda Zulfa’u ki sani Zulfah ‘yar dangice bazamu zuba ido kicigaba da muzantata kina wulak’antata ba, aike abin ki gode mata ne don idan ba itaba babu mai auren wannan d’an naki... Kodashike ba laifinki bane Uwar mijinki ta bud’e maki k’ofa kiyiwa Zulfah haka amma ki sani idan a baya mun zuba maku ido yanzu bazamu zuba miki ido ki ci gaba da cin zarafinta ba, d’anki yayi kema kiyi wad’annan marassa ta idon yaran naki suyi....”

Tinda ta soma magana Hajiya ke k’yarma tana dubanta, yaran suka hayyayok’o Najah ta janyo bokatin wanke wanke Sahariyya ta finciki bulalar hannun Hajiya da sunan zasu daki Aunty B...

Murmushi kurum ta sakar masu tana mai gyara tsayuwarta tace “I dare you to try it, k’anan marassa kunya,... Na rantse da Allah maras kunyar data fasa cikinku, daga yau kun gama rashin kunya...”

Sahariyya tayi saurin sauk’e hannunta sanin mijin Aunty B Soja ne, Najah ce tayi kanta gadan gadan Hajiya tayi saurin raba tsakaninsu tana fad’in “K’yaleta k’yaleta Auta...” Ta maida dubanta ga Aunty B kana tace “Bara’atu kinyi kad’an ki shigo har cikin gidana kimin rashin mutunci, amma tinda haka kika zab’a mu zuba nidake....”

Tsaki Aunty tayi kana tace “Abinda kuka iya kenan, nidai na fad’a miki ki sakar ma Zulfah mara a mutunce, da da yanzu ba d’aya bane....” Daga haka sa kai tayi ta fice daga gidan had’ida buga masu k’ofa.....

Najah sai faman fincika take tana fad’in “Haba Hajiya haba meyasa baki barni na cirewa matar nan rashin kunyarta ba, sai me don mijinta Soja wllhi Allah Hajiya da baki barni na gurji hak’waranta ba baki birgeni ba....” Ta k’arashe tana mai jifa da bulalar hannunta had’ida wucewa d’aki fuuu....

Hajiya ta kama farar kujera dake ijiye tsakar gidan ta zauna da k’yar zuciyarta naci gaba da tafarfasa...

Sahariyya ta zauna gefenta tana tausarta, ita kuwa Raihanah ma iya cewa Allah ne ya ceceta, cikin sand’a ta wuce d’aki....

***

Har suka iso layin unguwarta bata daina tunani da fargaban abinda Aunty B ta aikata a gidan Hajiya ba, dubanta Aunty B tayi bayan ta ida parking kana ta dafata

“Zulfa’u...!”

D’ago idanu Zulfah tayi tana dubanta, Aunty B taci gaba da fad’in “ki kwantar da hankalinki komai zai wuce ya zamto labari kinji koh, zuciyarki mai kyaune nayi imani bazaki dawwama cikin k’unci ba da yardar Allah....”

Jinjina kai Zulfah tayi a hankali kana tace “Na gode Aunty....”

Aunty B ta kuma murmusawa kana tace “Always remember that we’re here for you kinji koh....”

A hankali ta jinjina kai had’ida k’ak’aro murmushi kana suka kuma yin sallama sannan Zulfah ta wuce gida....

***

*Kaduna*


Yauma kaman kullum shiryawa sukayi cikin pajamas d’insu mai launi guda, saman gadon ta hauro yanda yake zaune yana aiki bisa computer d’insa...

Kiss ta manna masa a chick kana ta mak’ale cikin jikinsa bowl d’in crackers rungume a hannunta tana ci, ganin ya bada hankalinsa sosai ga aikin da yake ya sanyata sakin murmushi kafin ta d’au cracker guda ta shiga tura masa a baki tana fad’in “C’mon Partner open up, have som.... eat....”

Kaucewa yake yana fad’in “Oh no no Partner I don’t wan to, stop... I said stop...!”

Ina kaman cewa yake ta k’ara sai tsalle take akansa tana tura masa bakinsa....

Mirgino da ita yayi ya shiga mata cakulkuli ta ko ina su duka biyu suna dariya cikeda so da k’aunar juna....

Saida sukayi laushi gaba d’aya kafin ya janyota jikinsa suka kishingid’a, yatsunsu cikin na juna Sameer ke fad’in “You know Partner, I think Khalid was right.... Bai kamata idan mun samu matsala kad’an ki tafi gida ba, if we have problems kamata yayi mu solving matsololinmu just the 2 of us ba sai an samu third party ba ballantana yajega iyayenmu kinji koh, I want this to be first and last... Can you promise me Partner...”

Cikin sanyin jiki ta jinjina kai kana tace “I promise Partner, insha Allah hakan bazai sake faruwa ba... I’m sorry...”

Murmushi yayi kana ya manna mata light kiss a labb’anta kafin ya janyo laptop d’insa yana mai ci gaba da aikinsa...

Hannunsa ta kuma janyowa kana ta kishingid’a a jikinsa, idanu a lumshe take furta “Hey Partner, guess how much I love you...?”

Murmushi yayi had’ida kuma kwantar da kanta cikin k’irjinsa yana mai shafa kwantattun sumarta had’ida lumshe idanu...

“Must I guess...?” Ya tambaya still idanunsa a rufe...

Murmushi take tana duban kyakkyawar fuskarsa kana ta shiga janyo hannunsa tana fad’in “No no no don’t guess, come I wanna show you something...”

Sauk’owa sukayi daga saman gadon Siyama tayi d’igyalgyal ta rufe masa idanunsa da tafukan hannayenta, saida suka iso bakin window kana ta bud’e tapka tapkan labulaye da aka k’awata manyan windows d’in dasu, sliding glass d’in tayi fresh air ya bugi fuskokinsu duk da cewa akwai sanyin Air-conditioner a d’akin....

Kallon taurari dake baje iya ganinka a sararin samaniya tayi kana ta saki murmushi ta cire hannayenta daga fuskarsa, tsayuwa tayi gefensa suna fuskantar window su duka biyu kana ta sakalo hannunsa cikin nata...

Saitin kunnensa cikin sigan rad’a take fad’in “Open your eyes Partner...” Ta fad’i murmushi bai gushe saman kyakkyawar fuskarta ba...

A hankali ya bud’e idanunsa had’ida sauk’esu ga sararin samaniya yana mai shak’an dadd’an iska, Muryar Siyama ya katse masa wasu tunani da sukazo zuciyarsa lokaci guda...

Ta bayansa ta zagayo had’ida rungumarsa bata daina duban taurarin ba take fad’in “Ina sonka Partner iyaka yawan taurarin dake sararin samaniya....”

Murmushi Sameer yayi kana ya kaikaito suna fuskantar juna, yatsa yasa yana gyara mata kitsonta guda da ya sauk’o fuskarta, lokaci guda yake furta “And I love you without a limit Partner, much more than all those stars shining in the Sky.... I love you more than love itself, I love you more than my own life Siyaam...”

Tinda ya soma magana Siyama ta kasa daina kallonsa, batasan wani irin so Sameer ke mata ba, take taji k’walla na neman ciko idanunta, lokaci guda ta rungumesa tsam cikin jikinta tamkar mai tsoron kada wani ya k’wace mata shi...

Murya na rawa take furta “Partner I don’t know what I do without you... I love you....”

Rungumeta shima yayi cikeda sonta da k’aunarta.... A haka har bacci yayi gaba dasu....

***


Wajajen k’arfe 11pm ya shigo gidan yana faman huci, cikin bacci ta sinkayo muryarsa na faman doka mata kira...

A firgice Zulfah ta mik’e zaune zuciyarta na faman yankewa....

“Zulfa’u..!!!”

Ya fad’i a karo na hud’u, tsaki ya buga kafin ya nufi uwar d’akin....

K’iris ya rage bai bangajeta ba yanda ya turo k’ofar, matsawa gefe tayi fuska a tamke...

“Wani rashin kunyar kikaje kikayi a gidan Hajiya, sannan abin naki har yakai ki dinga d’ebo k’annen mahaifiyarki suna zuwa suciwa Hajiyata mutunci... How dare you Zulfah...?”

Tak’aitaccen murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo kana tayi saurin gimtsewa, dubansa da kyau tayi kafin taci gaba da fad’in “First of all, kar ka saka k’annen mahaifiyata ciki, sannan meyasa baka tambayi Hajiya da k’annenka mai yakai Aunty B gidan ba... Kai kanka sanin kanka ne hak’uri nake da mahaifiyarka da k’annenka don haka kada ka kaini bango....” Tana ida fad’in haka tasa kai zata shige...

Shaye da tsananin mamaki Hafiz ke kallonta, shine Zulfa’u ke gaya masa magana haka, bai bari ta shigeba ya fincikota ta dawo da baya.....


*SameenaAleeyou📚*
[25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_................DA RABO_




*04*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*


*Dedicated to my Trio ♥*

Cikin karaji Hafiz ke ci gaba da fad’in “Ni kike cema kina hak’uri da mahaifiyata.... Ni nake aurenki ko ke kike aurena... Idan kin mance bari na tuna miki Zulfah... Duk duniyar nan idan akwai mai k’arshen hak’uri toh kuwa shakka babu nine tinda kowa gudunki yake yana k’inki amma ni nayi hak’uri na amince da aurenki, na maki sutura, na baki matsuguni sannan nake ciyar dake.... Idan baki baki mance ba you’re nothing but a Curse to our family..... Shin bayan gata da na miki har kinada bakin magana...?!”

Tunda ya soma magana take zuban hawaye zuciyarta naci gaba da k’una da tafarfasa.... Muryan Hafiz ya kuma dakan dodon kunnuwanta sanda yaci gaba da fad’in “Daga ranar da aka haifoki a zuri’armu farin ciki suka gushe, mahaifanmu suka rasa wani sashe na kasuwancinsu, al’umman gari kowa ya yarda kece silan komai, tsiyane ke bibiyarki duk yanda kika saka k’afa, gashi nan babban misali akaina tunda kika aureni na kasa mallakar kasuwancin kaina da kaina, har yanzu mahaifina ke d’awainiya dani dake...”

Baikai aya ba cikin zuban hawaye ta katsesa da fad’in “Hafiz idan ka gaji da zama dani ka sallameni gaba d’aya, ka daina k’untata min kana cemin jeki gida kawai, ka bani shaidar tafiya gida mai tushe wanda idan na tafi babu mai dawo dani.... Ka bud’e baki kace na sakeki Zulfa’u.....” Ta k’arashe muryarta har na sark’ewa sabida tsananin kuka.....

Banda kallon banza baya watsa mata komai, saida ya d’auki wasu dak’ik’ai yana watsa mata kallon banza kafin ya buga tsaki ya shige yana fad’in “Aikin banza abinda kika iya kenan.....” Har yakai k’ofa ya dawo da baya yana mai nunata da ‘yar yatsa yake fad’in “And let me warn you for the last time... Wllhi wllhi kinji na rantse duk randa kika sake tattaran wata dangin mahaifiyarki kukaje kukaci mutuncin Hajiyata ranar ne zakiga kalana da baki tab’a gani ba....!”

Daga haka wucewa yayi ya shige uwar d’aki had’ida banko k’ofar da k’arfin gaske....

Zamewa tayi had’ida zama cikin kujera k’irjinta na mata zafin gaske.....”

Ita kuma kalan tata k’addarar kenan, wannan shine rayuwarta... A hankali ta zame cikin kujeran hawaye basu daina gangaro mata ba, a nan yanda take kwance bacci yayi gaba da ita....

Cikin dare take jiyo muryarsa a tsakar kanta yana doka mata kira, babu wani lank’wasa murya balle kalaman soyayya yake sanar da ita buk’atarsa, sannan da zai biya buk’atar nasa haka nan zai tsallaketa tamkar kuyanga aka ijiye masa... Wannan shine rayuwar gidan auren Zulfa’u, sam batasan akwai wata soyayya tsakanin miji da mata ba saidaima wani abu da yafi kama da k’iyayya....

***
Safiyar Washe gari...

Babu walwala a fuskarsa ya shigo parlorn, Marliya da Nabila zaune parlor Marliya na kallo yayinda Nabila ke karatu sabida jarabawarsu na k’arshen zangon karatu da suke fuskanta,...

A tare suka gaida mahaifin nasu saidai babu wani walwala ya amsa masu...

Da mamaki Abbah ke dubansu kana yace “Mai ya hanaku tafiya karatu....?”

Nabila tace “Abbah lecture free week muke sabida satin sama zamu fara exams....”

Jinjina kai yayi kana ya maido da dubansa ga Marliya yana jiran nata amsan...

“Abbah midterm break muke....”

Nan ma ya jinjina kai kafin ya k’arada “Ina Mamyn taku....?” A tak’aice....

A tare suka basa amsa da “Tana ciki Abbah....”

Gyad’a kai kurum yayi kafin yasa kai ya nufi uwar d’akin Mamy.....

Nabila da Marliya suka kalli juna don koda basu sani ba Mamani ce ta tinziro Abbah don ta had’asu fad’a da Mamy....

Nabila ta yab’e baki tace “Nifa wai sai naji mutane suna son Grannies d’insu suna wani jidasu ni kuwa wllhi Allah ya gani addu’a nake nawa ta mutu ko zamu samu peace cikin gidan nan....”

“Umm Mamani case....” Marliya tace sanda take kishingid’a cikin kujera had’ida rungume throw pillow....

Aiko daga yanda suke zaune suka soma jiyo muryar Abbah ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba duk akan maganganun da Mamani ta kitsa masa gameda Mamy da Zulfah....

Nabila tayi jifa da handouts d’inta ta k’arasa jikin k’ofar sosai tana sauraren maganganun Abbah....

Marliya dai girgiza kai kurum tayi had’ida ficewa daga parlorn don batama fatan taji wani abinda zai d’aga mata hankali....

A bakin farandar Mamy Marliya suka kusan yin karo da Aunty Lami, ganin yanayin Marliyan ya tabbatar mata wani abin na faruwa...

“Lafiya Marliya ina zaki haka cikin fushi....?” Aunty ta tambaya....

“Abbah ke fad’awa Mamy nah kuma shirin gari ya waye nake kalla amma bazan iya ci gaba da kallo ina jiyo sautin fad’arsawa Mamy ba....” Ta fad’i kaman zatayi kuka...

Aunty ta janyota cikeda tausayawa kana tace “Kiyi hak’uri kinji Marliya kar kiyi kuka maza jeki parlor na kiyi kallonki, ki kalli tashan da kike so....”

Marliya ta jinjina kai kafin ta nufi parlorn Aunty....

Murmushi Aunty tayi kafin tayi saurin kimtsa kanta ta nufi parlorn Mamy....

Mamakine ya cikata ganin Nabila mak’ale jikin k’ofa ta manna kunnenta...

Girgiza kai Aunty tayi kafin ta k’arasa tana ambaton sunan Nabila cikin kakkausar murya...

Nabila ta d’ago a zabure tana subanta, lokaci guda ta tab’e fuska ba tareda tace da ita komai ba, Aunty taci gaba da fad’in “Ki wuce a wajen banson sakarci da rashin kunya, mai zaiki jin tattaunawar iyayenki, rashin hankali ko mai....?”

K’unk’uni Nabila keyi fuska a turb’une ta wuce Aunty tana mai ci gaba da k’unk’uninta cewa ita dai ba maras kunya bace.... Aunty ta bita da kallo yawa ta kikkifeta da mari sam tasu batazo d’aya da Nabila ba a cewarta yarinyar ita kad’ai ta fita zakka a gidan, sam Nabila batada ta ido, girman yarinyar akwai aiki inji Aunty....

Waje ta nema ta zauna a parlorn had’ida rapka uban tagumi tana jiran fitowar Abbah....

A b’angaren Nabila kuwa tana ficewa sashen Mamani ta nufa....

Sakina d’iyar Baffah Wali ta tarar parlorn tana kallo don babu a sashensu sai sunzo sashen Mamani suke kalla koda zata masu wulak’anci da masifa amma haka suke shanyewa sabida tsabagen son abin duniya...

Kallon arziki basuyima juna ba Nabila ta shige uwar d’akin....

Bata sameta a d’akin ba amma taji k’aran zuban ruwa daga bayi hakan ya tabbatar mata tana band’akin....

Bakin gado ta samu ta hakince harda d’ora k’afa d’aya bisa d’aya tana jiran fitowar Mamani daga bayi.....

***

“Sahariyya ki tashi ki dafawa yarinyar indomie tintine kin zaune sai aikin danna wayar banza kike....”

Hajiya da Khausar ke zaune bisa cnyarta ta fad’i

Tsuka Sahariyya tayi a hankali kana tace “Haba Hajiya nifah wllhi bacci ma nakeji wannan fitinanniyar yarinyar sam bata barmu munyi wani baccin kirki ba sai kuka take tana ambaton mamanta, ni wllhi Hajiya ki maidata gidan iyayenta don bazan masu bautar ‘yarsu ba nidai....” Tana k’arashe fad’in haka ta janyo earpiece d’inta ta manna a kunnenta....

Hajiya ta gyad’a kai had’ida furta yayi daidai, Najah dake faman mulka powder a fuskarta dukda cewa kayan makaranta ne jikinta kai kace biki zata yanda ta zauna tana zuba kwalliya a fuska, idanunta naga madubi take fad’in “Nidai kin gani shirin makaranta nake....” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye cikin matsattsun kayan makarantar nata....

Da mamaki Hajiya ke dubanta kana tace “Ke Najah ba Raiha tace an baku hutun kwana biyu ba, wani makarantar kuma zaki....”

Tsuka naja tayi had’ida turo baki kana tace “Wllhi Hajiya k’aryan Raiha da Marliya ne, hala dai ‘yan ajinsune aka basu mudai ba’a bamu ba...” Ta k’arashe tana zira jakkan makarantar ta.....

Hajiya ta maido da dubanta ga Sahariyya kana taci gaba da fad’in “Ke k’atuwar banza da ba makarantar kike zuwa ba ke ya kamata ki dafa mata, ace sau biyar kina zana jarabawar aji shida amma kin kasa ci gaba, dubi Zulfa’u dai da kad’an ta girmeki gashi har tana bautan k’asa, ga yarinyar can Nabilah tayi nisa ke kuwa haka nan baga karatun ba baga aurenba.....”

A hasale Sahariyya ta katseta da fad’in “Nidai karma ki had’ani da wad’ancan matsiyatan Hajiya ehe, kuma da kike maganarki ince Yaya Hafiz ma tunda aka koresa yayi satan amsa bai koma ba aidai gwarani farawa ne banyi ba, gaskiya ni Hajiya babu ruwanki da maganar makarantata balle aurena....” Tana ida fad’in haka ta buge skirt d’inta ta shige parlor tana maimaita wak’ar dake tashi cikin earpiece d’inta...

Najah ce ta dubi mahaifiyar tasu kana ta murmusa tace “Hajiya toh me amfanin Raiha tinda tace suna hutu ai sai ta dafa mata ta kula da ita kokuwa....”

“Raiha wanke wanke take kuma tana gamawa zata gyara kayan miyan abincin rana yau za’a kaiwa Alhaji can Kasuwa.....”

Najah ta jinjina kai tana mai darawa kana tace “Toh ai Hajiya sai ki mik’e ki shiga kitchen, ni na tafi sai na dawo....”

“Toh a dawo lafiya....” Hajiya ta fad’i sanda take mik’ewa tsaye, parlor ta nufa ta dangwalawa Sahariyya Khausar tana fad’in “Saiki rik’eta naje kitchen d’in.....”

Aiko ana ajiye Yarinyar ta fashe da kukan gaske sabida har ta gane Sahariyya irin tsawa da masifa data dinga mata a daren jiya don kawai tana kukan mahaifiyarta, yarinyar da duka bata wuce shekaru biyu da watanni bakwai zuwa takwas ba... Aiko Sahariyya ta bud’e murya ta daka mata tsawa wanda ya kuma birkitata harda d’auko wayar earpiece d’inta tana nuna mata zata zaneta....

Daga yanda Raihanah ke wanke wanke tana jiyo sautin kukan Khausar tausayin yarinyar ya cikata, cikin sauri ta tsame hannayenta ta nufi parlorn yanda Sahariyya da Khausar ke zaune...

Cikin sauri ta k’arasa ta d’auketa ganin yarinyar ta dungura tana kuka.....

Sahariyya ta daka mata tsawa, “Ke uban wa ya baki izinin d’aukarta....”

Cikin sanyin murya tace “Addah Sahariyya kuka fah take...”

“Toh anji kuka take saiki wuce ki ficemin da ita daga nan kafin na had’eku na daka.... Uwar kilibibi kawai....”

Cikin sauri Raihanah ta fice tana jijjiga yarinyar da tuni tayi lamo cikin jikinta, d’akinta ta nufa ta d’auko zanin goyo ta goyata a baya kana ta koma bakin aikinta, tanayi tana jijjiga Khausar har bacci yayi gaba da ita.....


***

Shaye da mamaki Mamani ta tsaya tana duban Nabilah dake zaune saman gadonta tana jijjiga k’afafu....

K’arasowa tayi cikin tafiyarta mai yanayi da d’ingishi sabida girma kana tace “Ke Halimatu lafiyarki kika shigo min har uwar d’aki ba tareda izinina ba kina faman kad’a k’afa... Hanshak’iya Mandiya...!” Ta k’arashe tana d’aura hannayenta bisa kunkuminta...

Mik’ewa Nabila tayi kana tace “Mamani ina kwana.....”

“Da ban kwanaba kya ganni maras kunya kawai....”

Nabilah ta kad’a kai kana tace “Allah ya gani na gaisheki na fita.... Dama zuwa nayi na fad’a maki na jaddada maki wllhi duk randa mahaifiyarmu ta gaji da zaman gidan nan tace zata tafi toh ki sani tare zamu tafi don wllhi Allah kinji na rantse Mamy tana sa k’afa da sunan barin gidan nan muma saidai a nememu a rasa, daga ke har Abban sai ku zauna a gidanku cikin kwanciyar hankali kiji da sauran jikokin naki amma dai kam ba ‘ya’yan Abbah ba don wllhi tafiya zamuyi....” Tana gama fad’in haka ta fice abinta ba tareda ta kuma bin takan Mamani dake daskare wajen ba...

Haba nan fah Mamani ta soma sbabi tana fad’in “Eh lallai yarinyar nan kin rik’a, laifin uban naku da ya k’yaleki kina boko yak’i aurar dake, dolema ki fand’are mana, ohni Halima bansan miyasa aka sakawa wannan maras kunyar yarinyar sunana ba, bakiyi

Please Login or Register in order to submit comment