Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata harara kana tace “Keda kika amso sai kisan yanda zakiyi da jakkar don nikam bazan d’auka ba.. Gwarama kisan yanda zaki samo shi ki bashi abunshi...”Ta k’arashe tana k’ok’arin tattare books d’inta..
Yusrah ta d’an harereta tace “Wllhi sai na bud’e...”
Ta k’arashe tana bud’e jakkar...
Da tsananin mamaki ta tsaya tana duban abindake ciki, tai saurin tab’a Nabilah tana fad’in “Ke kalli abinda ke ciki...”
Nabilah tai pause tana duban Teddy Bear fara k’al mai kyau harda ‘yar crown akanta, dariya ya kusa kufce mata, lallai wannan yama gama rainata, itace zai kawowa abin wasa... Tai k’wafa kana ta finciki Teddy bear d’in hannu Yusrah kafin ta sami zarafin magana taci murya na tashi cikin teddy d’in _I’m sorry_... Suka dubi juna itada Yusrah cikeda mamaki suna kuma duban Teddy d’in...
Nabilah ta sake motsa Teddy d’in domin tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiyo mata nan kuma sukaji Teddy d’in ya sake fad’in _I love You_ Ai a d’ari ta saki Teddy d’in ya fad’i k’asa ta saki k’ara cikin firgita...
‘Yan aji suka juyo suna dubansu, Yusrah tai saurin d’auko Teddy d’in tana dariya had’ida furta “Lallai nashi salon daban ne wayyo Allah na... Wato dai bazai bud’i baki ya sanar dake ba saidai ya turo d’an aike da sak’o...Gaskiya k’awata na miki murna...” Ta k’arashe tana rungume teddy d’in cikeda nuna farin ciki...
Nabilah da gaba d’aya jikinta ya mutu kasa furta komai tayi sai k’urama teddy d’in idanu da tai, can k’asar zuciyarta wani irin annashuwa takeji wanda batasan dalili ba, gaba d’aya sai ta koma wata sukuku da ita haka nan...
Koda sukazo tafiya gida Yusrah ta damk’a mata jakan teddy d’inta tana fad’in “Matar Bear ki adanashi da kyau kuma don Allah ki amince ki zama baby bear d’inshi don wllhi kun bala’in dacewa...”

Harara Nabilah ta galla mata kana tace “Allah ya sawak’e min, ina zuwa gida zan kirashi yazo ya amshi abunshi ko na jefar...”

Yusrah ta dara tana fad’in “Ahab na yaushe k’wayar idanunki sun nuna kin kamu da son bear babe....” Nabilah ta kai mata duka Yusrah ta zille ta shige adaidaita tana dariya tana fad’in idan bear ya kira a gaisheshi...

Nabilah ta rakata da harara tana fad’in zasu had’u gobe ne...
Tinda ta shiga adaidaita itama kalaman take kan nanatawa cikin zuciyarta _I’m Sorry.... I Love you_ A hankali ta saki murmushin da batasan daga ina ya taso mata ba, har ta isa gida tinani take cikin adaidaitan....

***

Ya jima sosai a masallacin yana lazimi da kai kukansa ga mahaliccinsa situation d’in da yake ciki Allah ya kawo masa mafita...
Ya mik’e ya maida Alkur’an ma’ajiyanshi... D’ago idanun da zai ya hangi Abbah daga can gefe wanda shima nashi kukan ya kawo wajen mahallicin shi, Abbah yana d’ago idanu sukai ido hud’u da Sameer wanda ya hangi rama da ya d’anyi... Su duka biyun suka k’urama juna idanu tamkar masu tunanin wani abun....

Sameer yai k’ok’arin k’ak’aro murmushi ya sakarwa Abbah kana ya nufo yanda yake a zaune....
Saidai yana k’arasowane ya hangi damshin hawaye a idanun Dattijo Abbah.. Jikin Sameer ya kuma yin sanyi sakamakon hango hawaye da yayi cikin idanun Dattijon....
A hankali ya duk’a yayi zama irinta rak’umi a gaban Abbah...



SameenaAleeyou📚
[08/02, 13:34] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_...............DA RABO_



*33*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Shamsu bai ida rufe baki ba Siyama ta shigo kanta a k’asa tana satan kallon Sameer wanda ya koma tamkar bai tab’a murmushi ba tsawon rayuwarsa...
Shamsu ya mik’e ya basu waje ya fice gaba d’aya ko d’an zolayar data zamar masa d’abi’a bai tsaya yinta ba don ya fahimci abokin nasa da matarsa suna buk’atar ganawa mai mahimmanci...

Daga can kujerar gefenshi ta zauna tana mai kuma shan jinin jikinta, a hankali ta furta “Partner...!”

Wani duban da yai mata ya sanyata had’iye maganar nata...
“What brings you here...? Wait da izininwa ma kika taho har garin nan...? Kodayake bai kamata na tsaya tambayarki batun neman izini ba tinda kinyi abinda yafi wannan.... Ki tashi ki koma yanda kika fito bana buk’atarki a nan...”

Tai saurin d’agowa tana dubansa k’irjinta na bugawa da sauri, anya wannan Sameer d’inta ne kokuwa dai canza shi akai....
Ya kuma darara mata tsawa “Nace ki tashi ki koma yanda kika fito...!”

Tai saurin zabura k’walla na k’ok’arin ciko idanunta, cikin muryar kuka take furta “Partner wllhi babu yanda zan koma sai ka saurareni, haba Sameer does it has to be like this... Can’t you see I’m suffering.... Sameer just pills ka gani fah... Kuma at least sai ka bani dama nai bayani, meyasa kake punishing soyayyarmu haka... Sameer we both know that we love each other so much, Please mana Partner...”

Da tsananin mamaki da takaici ya d’ago yana dubanta kana ya girgiza kai yace “Did you just say love...? Siyama kinsan abinda ake kira so kuwa....?” Yayi maganar yana mata wani irin duba da rinannun idanunsa...

A hankali ta sauk’ar da nata idanun k’asa...
Sameer ya girgiza kai a hankali kana yaci gaba da fad’in “Da ace kinsan matsayin abinda kike fad’i da baki aikata abinda kika aikata ba.... Mutumin da yake sonka bazai tab’a k’yamatar abinda zai fito daga jikinka ba.... Shiyasa nakeson jin dalilin amincewa aurena da kikayi idan har bakison had’a zuri’a dani....”

Tai saurin d’ago idanunta mai zuban hawaye tana dubansa, lokaci guda ta shiga girgiza kai tana furta “Ba haka bane Partner...”

“Toh yaya ne..!!?” Ya tambaya cikin d’aga murya da ware idanu wanda daga gani zuciyarsa zafi take masa...

Cikin muryar kuka taci gaba da fad’in “Partner I don’t want to share your love with anyone else, I want you to love me, just me and only me... Even your parents don babu yanda na iya ne shiyasa nake tsoron idan ka haifi yara zaka daina sona...” Ta k’arashe tana goge hawayen da suka wanke mata fuska....

A yayinda Sameer ya mata k’uri yana dubanta.... Siyama ta gangaro daga kujeran da take zaune hawaye naci gaba da kwaranya mata ta durk’usa gabanshi, cikin muryar kuka taci gaba da fad’in “Partner I’m sorry... I really I am... I I I’m only human, and I thought I was doing what’s best for the both of us.... please forgive me.... I didn’t mean to hurt you...”

Tuni zuciyarsa ta karaya, sam bai k’aunar yaga mutum na kuka balle ace mace macenma matarshi ta sunnah... A hankali yasa hannuwansa duka biyu ya tallafo Siyama dukda cewa abinda ta masa abu ne mai wuyan yafewa....
Tuni ta shige cikin jikinsa tana sakin wani sabon kuka...
Murya can k’asa yake furta “Is ok... Ya isa haka ki daina kuka, abinda ban gane ba shine meyasa zaki aikata such a horrible thing like that... Bakiso ki haihu dani ne... Kina gudun abin kunya ne sabida kar ace uban ‘ya’yanki baida asali... Wannan shine dalilinki...?”

D’agowa tai tana dubansa da watery eyes d’inta, lokaci guda ta shiga girgiza kai tana mai furta “What... Asali....? I don’t get you....”

Gyara mata zama yayi kana yace “Don’t play a dumb here Siyama, wannan shine dalilinki ba wancan silly excuse d’in da kika bani ba.... C’mon sweetheart, idan har da gaske kina sona don’t lie to me anymore... Please... So tell is there anything you’re not telling me....” Ya k’arashe yana rik’e da ‘yan yatsunta...

Saida ta had’iyi wani miyau sanda ta tuna kalaman Ammi cewa taci da shan maganin hana d’aukan ciki kana ta girgiza kai tace “I don’t anything please believe me Partner... Wai meke faruwa ne...?”

K’uri ya mata da rinannun idanunsa domin kuwa har k’asan zuciyarsa yakeji akwai abubuwa da Siyama ke b’oye masa tin bayan abinda ya faru tsakaninsu...Cikin wane irin yanayi ya furta “It turns out mutanen da tun tasowata na sansu a matsayin mahaifa na basune suka haifeni ba...”

A firgice Siyama ta mik’e zaune daga jikinshi tana dubanshi...
Girgiza kai ta shigayi tana furta “But... how... How comes...?”

Jinjina mata kai ya kumayi kana yace “Yes, Momy and Dad aren’t my real parents....”

Cikeda shock Siyama tace “If they aren’t your parents, then where are your real parents...?”

“I don’t know... Ban sani ba nima, bansan ya akai na k’are a hannunsu ba, dukda cewa basu tab’a nunamin wani abu ba basu tab’a muzguna min ba tsawon rayuwata dasu I think I deserve to know who my real parents are... Sannan na cancanci nasan dalilin da yasa na koma hannunsu, shin iyayena mutuwa sukayi kokuwa suna raye, idan har suna raye inaso na gansu na masu tambayoyi da dama idan kuwa sun mutu mai matsayin mutanen da na girma a hannunsu... I’ve a lot of questions....”

Hannayensa Siyama ta rik’e fuskarta d’aukeda tsananin damuwa kana tace “I’m sorry Partner, this must be hard for you... Wannan lokaci ne da ya kamata na zamto ina gefenka, kayi hak’uri Partner...”

K’ak’aro murmushi yai ya sakar mata kana yace “Now that you know... Shin kinaso kici gaba da zama dani a haka....Zaki iya ci gaba da k’aunata after learning all this...?” Ya mata k’uri yana dubanta...

Murmushi ta sakar masa kana ta matso cikin jikinshi ta kwanta....
“I’ll always love and accept you for you are... remember, kaid’in nakeso just you...”

A hankali ya jinjina kai gajeren murmushi saman fuskarsa kana yace “Are you sure..?”

D’agowa tai tana dubansa kana tace “Wait.. Are you doubting me again...?”

K’uri ya mata yana nazarinta kafin ya sakar mata murmushi ya janyota jikinsa ya rungume... Lokaci guda yayima waje guda k’uri yana nazarin abubuwa.....

***

Nabila taima wayarta k’uri tana kuma juya Teddy d’in da Khalid ya bata, ita kad’ai take sakin murmushi tana mamakin salonshi, ko ba’a fad’a ba da alama kiranshi take jira.... Marliya ce ta shigo ta taddata a haka... Kallo ta bita dashi tana mamakin mai ya had’ata da teddy...
Marliya tai saurin k’arasawa saman gadon had’ida fincikan teddy d’in tana fad’in “Addah Naby ina kika samo wannan...? Dan Allah ki bani....”

Nabilah data d’an firgita fauce teddy din tai tana fad’in “Ke da Allah bani nan god’e god’e dake mai zakiyi dashi...”

Marliya ta d’an b’ata fuska tace “Toh ke mai yakeyi wajenki...?”

Nabilah ta d’an daburce lokaci guda ta shiga inda inda tana furta “Ni.. ni wa yace miki nawa ne na Kausar ne gobe zan kai mata...” Ta k’arashe tana tura Teddy d’in cikin drawer...

Marliya dai k’uri ta mata ganin yanda ‘yar uwar tata ta zama nervous all of a sudden, gaba d’aya Nabilah canzawa take a ‘yan kwanakin... D’an gyaran murya tai kana tai mata seda safe ta wuce wajen kwanciyarta....
Nabilah dai kwanciya kawai tai amma zuciyarta fal tunani Khalid ne ciki, ta janyo drawer d’in data jefa teddy din ciki tana duba murmushi kwance saman fuskarta, Marliya dake k’yallare da idanu guda tamkar mai bacci sai karantar ta take...
Vibration d’in da wayarta tai ne ta d’an razaneta...
Tai saurin zabura k’irjinta na bugawa da sauri, shid’in ne mai kira...
Ta lumshe idanunta a hankali had’ida sakin deep breath, saida wayar tai ringing kaman zata yanke sannan Nabilah tai k’arfin halin d’agawa....
Shiru kaman ba mai niyyan magana cikinsu....
Kaman daga sama don har ta cire rai bazai magana ba sai kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Are you still there....?”

Ta rasa mai zatace kaman tai hanging up sai kuma tai k’ok’arin saita kanta don bataso ya fahimci halin da take ciki, da d’an fad’a take furta “Kaga Malam kazo ka amshi kyautarka babu abinda zanyi dashi ko nai maka kama da mai wasan yara ne...?”

Ya murmusa a hankali daga yanda yake kishingid’e kana yace “Like right now... Can I come over...?”

Juya idanu tai kana tace “Kaga Malam karma kai tunanin zuwa gidanmu don Abbah baya tolerating kowa ya tsaya masa a k’ofar gida...”

“Idan ban mance ba gani na biyu da kikamin a gidanku a parlorn Abbah ne, so idan zanzo wajenki ba waje zan tsaya ba saidai a parlor... And I didn’t call to receive goodnight scolds.... And don’t sleep late because you’ve class tomorrow....Take care....” Daga haka katse kiran yai yana sakin murmushi ba tareda ya jira cewarta ba...

Tabi wayar da kallo tana mamakin hali irin na Khalid.... Murmushi ta saki ita kad’ai had’ida girgiza kai kana ta aje wayar ta kwanta tana sakin murmushi tana maimaita kalmarsa ta k’arashe cikin zuciyarta....

Marliya dake mak’ale da idanu tana dubanta dad’i ya rufe ta ganin Addar tata is finally giving herself a chance to be in a relationship, ba kaman yanda idan an mata maganan saurayi a baya ba tayita fad’a da masifa kenan tana fad’in ita bazata tab’a yin aure ba don bazata d’auki wani disappointment ba ganin yanda Addarta Zulfa’u tasha wahala gidan aure... Lallai dole Mamy taji wannan batu....

***

Washe gari da rana su biyu suke zaune gaban Malaminsu suna kora masa bayani....
Wata laya ya aje saman k’asa da aka zana da yatsu cikin babban tray, ya aje cazbaha saman layar kana ya dubi Lami da Haule....

Haule da ta gama zak’uwa tace “Malam mai ka gani....?”

Jinjina kai Malam yayi kana yace “Tabbas Ma’aruf na raye hasalima yana tsakankaninku kuma yana gab da dawowa cikin danginsa....”

Aunty Lami ta shiga sallallami tana furta sun shiga uku sun lalace Aminiyar Sirri ta cucesu datasa suka amince ta kashe Ma’aruf..
Haule ta shiga mintsilinta tana fad’in tai shiru sunzo wajen mai share masu kukansu...

Malam yace “Mai kukeso ayi...?”

Cikin sauri Haule tace “Malam kafin ya bayyana cikin dangi munaso a gama dashi ma’ana a kasheshi...”
Lami ta kalleta a firgice tana girgiza kai kana tace “A’a Malam a kuma badd’ashi a nisantashi da danginshi na har abada....”

Malam yace “Naji ra’ayoyinku..... Yanzu abinda za’ai ko wacce a cikinku zata d’au ‘ya’yan calbin guda d’ai d’ai...”

***

Hafiz na zube a parlor ya d’an sami baccin rana musamman da ya samu jarabebbiyar matarsa bata nan har wani hamdala saida yayi ya zube saman kujera bacci yai gaba dashi, nan cikin baccin nasa ya soma jiyo kururwa ana ihun b’arawo.... Ya mik’e zunbur ya fice a guje tamkar zararre ya nufi k’ofar gidan....

Cincirindon mutane ya taddata ana jajanta satar Babur da akai, sai lokacin ya tuna ashe a waje ya aje babur d’insa koda ya dawo daga kasuwa....



SameenaAleeyou📚
[09/02, 10:19] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_................DA RABO_




*32*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*





Sam Abbah baiso Sameer ya fahimci halin da yake ciki don haka bai kuma d’ago kai sun had’a idanu ba, idanun nasa naga cazbaha da yake ja a hankali, Sameer ya d’an bud’e murya kad’an ya gaidashi...
Abbah ya amsa cikin raunanniyar murya yana mai k’ok’arin had’iye damuwarshi....
Shiru na wasu ‘yan lokuta suka gifta....
Sameer yana son tambayar Dattijon wanda bai nuna komai a gareshi ba sai karamci tun had’uwarsu amma saidai baisan ta yanda zai soma tambayarsa damuwarshi ba, baisan mai zaice ba amma kam har cikin zuciyarsa yakejin zogin ganin bawan Allahn haka cikin damuwa.... Muryar Abban ne ya katse masa tunaninsa sanda yake fad’in “Rayuwa takanzo ma bawa da abubuwa da dama wanda bai tab’a zato ba balle tsammani, rayuwar duniya gaba d’ayanta jarabawace.... Ta fannuka daban daban Allah yakan jarabci bayinsa, idan bawa ya yarda da k’addara kyakkyawa da akasinta tabbas shi yaci ribar rayuwar duniya... Da yawan mutane sukan halaka sakamakon fad’uwa jarabawar da Allah yaso jarabtarsu da ita....”

Tunda ya soma magana Sameer ke dubansa yanaji tamkar nasiha yake mashi tamkar ya shiga zuciyarshi yaga halin da yake ciki, Abbah yaci gaba da fad’in “Maiyasa tsawon rayuwata na danganta jarabawar da Ubangijina ya min da cewa laifin matata ne...? Mai yasa na biyewa mahaifiyata muka taru muka d’aurawa baiwar Allah laifi tsawon shekaru talatin....? Maiyasa rayuwata ta sauya tun daga wannan lokacin....?” Hawaye suka soma kwararo mashi sanda yaci gaba da fad’in “Shin da gaske banyi tawakkali da rashin Ma’aruf ba.... Mai yasa na kasa amincewa zuciyata Ma’aruf ya tafi tafiya ta har abada kuma bazai dawo gareni ba....” Babban mutum kaman Abbah ya kifa kanshi yana kuka sosai wanda ya karya zuciyar Sameer matuk’a, tsananin tausayin dattijon ya rufe shi... Kodaji zaka fahimci abubuwan da Abbah ke fad’i sun jima suna damunsa cikin zuciyarsa saidai bai samu wanda zai sharing dashi ba....
A hankali Sameer ya kai hannu ya dafa kafad’an Abbah guda...
Abbah ya d’ago k’wayar idanunsu ta had’e waje guda su duka biyu zuban hawaye suke mai tsananin ban tausayi da tab’a zuciya...
A hankali Sameer yake furta “Rayuwa haka takanzo mana da abubuwa masu tsananin ban mamaki... amma babu yanda muka iya dole mu amshi wad’annan k’addarori a bisa yanda sukazo mana....”

Abbah ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Wad’annan sune k’addarorin da na kasa bud’e ido na gani tuntuni.... Idanuna sun rufe wajen d’aura laifin ga mahaifiyarshi wacce itama na tabbata rayuwarta ya kasance cikin tsananin na tsawon shekarun talatin, maimakon na zamto mai bata k’arfin gwiwa sai na kasance mai cuzguna mata da k’ara mata bak’in ciki, matata wacce nafiso wacce idanuna suka rufe na rasa farin cikina a tattareda ita, farin cikin da muka gina tun farkon had’uwarmu.....”
Sameer ya masa k’uri cikeda son jin asalin labarin wad’annan bayin Allah.....

D’an gyara zamansa yayi kana yace “Baba don Allah ka sanar dani labarinka.....”

Abbah ya d’ago idanu yana duban Sameer wani irin duba mai cikeda shauk’i kana ya shiga girgiza kai lokaci guda yake furta “Labarina ya canza ne shekaru talatin baya...” Lokaci guda kuma yaci gaba da girgiza kai yana furta “A’a Sameer, banso na saka ma raina cewa Ma’aruf na raye, sabida na jirashi tsawon shekaru talatin ko zai dawo amma bai dawo ba....”

Sameer da k’irjinsa ke tsananin bugu a hankali ya furta “Baba... Wanene Ma’aruf...?”

Abbah yai shiru na wasu dak’ik’ai kana yace “Ma’aruf d’anah ne wanda na rasashi tun yana shekaru uku a duniya....”
Gyara zama Sameer ya kumayi kana yace “Mutuwa yayi ko kuwa b’acewa yayi...?”

Abbah ya d’ago ya kuma dubansa kana yace “Duka.... Ya b’ace sannan ya mutu....”

“Ya akai kasan ya mutu....?”
Sameer ya jefo mishi tambayar

Murmushin k’arfin hali Abbah yai kana yace “Da ace yana raye da ya dawo garemu... Mun nemeshi a duk yanda ya dace mu sameshi amma bamu sameshi ba... Ma’aruf ya jima da mutuwa....” Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa tsaye saidai jiri ya kusan dawo dashi k’asa...
Sameer yai saurin tallafo shi yana fad’in “Sannu Baba, are you alright...? Muje barin kaika gida...”

Abbah ya girgiza kai yace “A’a kar ka damu zan iya tafiya....”

Girgiza masa kai Sameer ma yayi kana yace “A’a muje na kaika....” Ya k’arashe yana rik’edashi...
Murmushi Abbah yayi kana yace “Na gode...” Cikin zuciyarsa yana ayyana farin ciki da iyayen Sameer suke kasancewa ciki samun nagartaccen d’ah tamkar Sameer....
A haka suka fito har haraban masallacin, Sameer ya gyarawa Abbah takalmansa ya saka suna tafe yana tambayar Abbah ko yana shan maganin hawan jininshi da kyau abinka da likita.....

A haka suka k’araso gida hannun Sameer rungume da kafad’un Abbah yana taimaka mashi, Aunty Lami dake tacan baya wajen famfo tana tattare wasu kaya a igiyan shanya ta hangi Abbah da wannan matashi wanda ta masa suna da Ma’aruf suna tafe rungumeda juna tamkar asalin d’ah da mahaifi....
K’irjinta yayi wani irin bugawa tamkar an ijiye mata guduma akai, jikinta ya d’auki karkarwa batasan sanda tai watsi da kayan dake hannunta ba, tabisu da kallo har suka b’acewa ganinta....
A fujajan ta koma d’aki ta shiga zagayawa gumi na karyo mata, shikenan ta faru ta k’are, kar dai wad’annan bayin Allah sun fahimci junansu ne....? Kardai hasashensu ya zamto gaskiya ne....? A kullum k’ara kusanci suke da juna, tabbas idan basuyi wani hobb’asa ba sunaji suna gani da gaske Ma’aruf zai dawo cikin rayuwarsu...
Lami ta had’i wata miyau mai d’ankaren azaba kana ta shiga neman layin Haule jikinta har wani k’yarma yake sabida tsananin tsoro....

A kusan k’ofan sashen Abbah suka had’u da Marliya zata shige, nan ta tsaya tana gaidasu had’ida shiga damuwa ganin mahaifinta an tallafo shi...
A d’an daburce tace “Abbah lafiya... Maike damunka...?”

Sameer ne yace “Karki damu ba wani abu bane, da zaran ya kwanta ya sami hutu zai warware...”
Abbah ya k’arada “Kiramin mahaifiyarki...”

Cikin sauri fuska d’aukeda damuwa Marliya tace “Toh Abbah...” Nan take ta nufi sashen Mamy..
A yanda Mamy ta ganta ta tabbata babu lafiya....
Mamy tai saurin aje ludayin damun fura dake hannunta don tinda Aunty Lami ta bata shawrin ta sassautawa kanta da tunanin cewa Ma’aruf ka iya dawowa take k’ok’arin d’aukar shawarin dukda cewa can k’asar zuciyarta tanajin bazata iya ba domin kaw abune mai matuk’ar wahala... Matsar da langar tai kana tace “Marliya lafiya na ganki haka...?”

Marliya ta d’an share k’wallan da suka ciko idanunta tace “Mamy Abbah ne...”
Mamy ta mik’e zumbur cikeda tashin hankali take furta “Mai ya sami Abbanki...?”

“Mamy Abbah baida lafiya, yana sashen shi... Yace kije...”

Marliya bata ida fad’i ba Mamy ta fice a fujajan ta nufi sashen mijinta....

Sameer na k’ok’arin zaunar da Abbah had’ida jingina mashi bayanshi jikin cushion Mamy ta sako kai parlorn.....
Take k’irjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri...
Ta kasa ci gaba da tafiya ta tsaya cak tana kallon ikon Allah...
K’wayan idanunta suka sauya lokaci guda sanda ta tsinci kanta tana mai ci gaba da takawa a hankali har ta isa garesu....
A dai-dai lokacinda Sameer ya d’ago k’wayar idanunsu suka sark’e waje guda....
Wani irin yanayi maras fasaltuwa suka tsinci kawunansu ciki.... Su duka biyu sunaima juna wani irin duba mai cikeda shauk’e, abubuwa da dama suke iya hangowa cikin idanun junansu...
Abbah dake daga kishingid’e ya kafesu da idanu yana kallon duban da sukema juna zuciyarsa na harbawa....
Abbah ne ya katse shirun da fad’in “Na gode likita....”
Sameer yai saurin dawowa cikin hankalinsa yai k’ok’arin k’ak’aro murmushi yace “Babu komai Baba...” Lokaci guda ya shiga gaisheda matar da bayyanarta gabanshi yai tsananin jefasa cikin wani yanayi maras fasaltuwa....

A b’angaren Mamy ma k’arfin hali tai kana tai k’ok’arin saita kanta ta amsa masa da sakin fuska bata daina mashi wani irin duba mai nuni da wani babban al’amari ba...
Abbah ya fahimci halin da Mamy ta tsinci kanta ciki, domin kuwa yanayi ne wanda ya tsinci kanshi ciki a lokacinda ya soma had’uwada Sameer, baiso taci gaba da wahala tana sakama ranta Ma’aruf zai dawo garesu tunda Sameer ya tabbatar mashi yanada nashi iyayen hasalima aiki ya kawo shi nan sannan babu ta yanda za’ai Sameer ya kasance d’ansu Ma’aruf wanda ya jima da b’acewa, watak’ila dai yanayi da kamanni ne yakedashi irinta Ma’aruf d’insu, a halin yanzu bai k’aunar matarshi uwar ‘ya’ayanshi ta kuma kasancewa cikin k’unci, zai k’ok’arin kawar mata da duk wasu k’unci data kasance ciki a baya wannan shine kawai hanyar da zaibi ya mayewa matarsa gurbin tarin bak’in cikin da ya jefata ciki a baya....

Mamy ce ta katse shirun da fad’in “Abbah meke faruwa, Marliya tace min bakada lafiya....” Ta k’arashe tana matsowa kusanshi...

Abbah ya sakar mata murmushi mai taushin gaske kana yace “Kar ki d’aga hankalinki Mariya, is a good thing wannan yaro Sameer yana wajen, bugu da k’ari k’wararren likita ne....”

Mamy ta jinjina kai fuska fal fari’a tana mai furta “Allah sarki... Sannu bawan Allah...”

Sameer ya d’ago ya dubeta fuskarsa d’aukeda murmushi yace “Babu komai Hajiya.... Ammm ni zan wuce, sai a kula da shan maganin BP d’inshi sannan ya rage yawan tunani...” Ya d’an juyo ya dubi Abbah kana yace “Baba a kula...”

Abbah ya jinjina kai yace “In sha Allah Sameer... Na gode k’warai...”

“A’a Baba ka daina godiya a gareni dan Allah an riga an zama d’aya....”
Abbah ya jinjina kai cikeda jin dad’i daga shi har Mamy duban Sameer suke tamkar yaci gaba da zama haka a gabansu suna dubansa suna murmushi....
Ganin da gaske tafiya yakeda niyyanyi yasa Mamy saurin mik’ewa tana fad’in “A’a ka tsaya a kawo maka abinci...”

Sameer yace “A’a Mama na gode...”
Mamy tabisa da kallo jin ya kiratada Mama...
Ta d’an murmusa tace “A’a zakaci wani abu dan Allah... Koda fura ne ka tsaya ka sha yanzu na damata ban jima da had’ata ba...”

Take murmushin Sameer ya fad’ad’a ya koma ya zauna yana mai furta “Aiko inason damun fura sosai tun tasowata...”

Gaban Mamy ya kuma fad’uwa, jikinta ya kuma yin sanyi tana mai duban Sameer d’in... A hankali ta mik’e ta nufi sashenta jiki a sanyaye ta had’o masa damun fura da kindirmo...
Sameer kaw gyara zama sosai saman darduma yana sha yana santi don dama rabonsa da abinci mai k’wari tun daren shekaran jiya....
Abbah da Mamy sukai masa k’uri suna dubansa zukatansu nai masu wani irin dad’i, su duka biyun Ma’aruf suke hanga zaune wajen...

Aunty Lami dake lab’e jikin k’ofa zuciyarta sai faman harbawa take musamman da taga yanda wannan matashi ke shan kindirmon, jikinta ya kuma tabbatar mata cewa lallai wannan Ma’aruf ne, dole su b’adda wannan mutumi a doron k’asa kafin ya dawo cikin rayuwarsu dumu dumu... Farin cikin da Mariya ta rasa shekaru talatin baya bazai kuma dawo mata ba...
Tai k’wafa a hankali

Please Login or Register in order to submit comment