Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idanu kana tace “Hajiya rainonsa aka kawo min...”
Na dubeta sosai kana nace anya Dumba ki sanar dani gaskiya ina mahaifiyar yaron nan yake kuka irin haka... Idan bakiso na kira miki ‘yansanda tun wuri gwara ki sanar dani gaskiyar lamarin.... Dumba ta shiga rarraba idanu ganin da gaske nike saita sanar dani yanda ta samo yaro ta duk’a har k’asa tana bani hak’uri tana fad’in zan sanar dake gaskiya Hajiya...
Yaron nan rayuwarsa cikin had’ari take, yanzu haka aminai uku sun zaci ya jima a barzahu Hajiya ni kuma bazan iya kashe rai ba....
Naci gaba da dubanta da tsananin mamaki kana nace Dumba ban gane ba... So kike kicemin ked’in kwangilar kisa aka baki...?
Kan Dumba na k’asa hawaye na d’igo mata tace k’warai kuwa Hajiya amma wllhi bazan iya ba don ban tab’a kashe koda k’aramar dabba ba ballanta d’an mutum k’aramin yaro kaman wannan wanda bashida hakkin kowa, na zab’i na barshi a raye ba kaman yanda sukai zato ba... Saidai bansan yaya zanyi dashi ba bansan ina zan b’oyeshi ba nayi tunanin idan ya k’ara girma kad’an na turashi almajiranci ta chan k’asashen Chadi yanda zai b’ace daga duniyarsu har abada....
Tinda Dumba ta soma magana hawaye ke zubo min had’ida tsananin tausayinka....” Mummy ta sauk’e ajiyan zuciya kana taci gaba da fad’in “Sameer ni na buk’aci Dumba ta barmin rik’onka a hannuna, aka kuwayi sa’a da maigidana ya dawo ya taddaka taredani gwanin ban sha’awa yanda ka sake dani kana amsan abincin daga hannuna, yayita mamakin ina na samo yaro nan na zayyane masa komai, shid’inma tausayinka ne tsantsan ya kamashi amma sai yace bazamu bi maganar Dumba haka kurum ba gwara mubi diddigi muji ina ta samo yaron nan don kardai ma sato shi tayi mutum a yau abin tsoro ne, watak’ila dangin yaron nan iyayensa nata nemansa wata k’ila ‘yansanda ke neman Dumba ta shirya wannan labari, nabi shawarin mijina washe gari muka tafi gidan wacce ta samo mana Dumba matsayin ‘yar aiki saidai bamu sami labari mai dad’i ba domin kuwa ita kanta dillanci masu aiki take sannan ta sanar damu ita kanta batasan ina zata samu Dumba ba, nan na soma yarda da maganganun mijina, wata k’ila Dumba mugun nufi ne tattare da ita, neman duniya munyi bamu sami Dumba ba gashi batako sanar damu sunanka ba, nida mijina muka yanke shawarin kiranka da suna Sameer, da fari Dad d’inka yaso a damk’a ka hannun hukuma ko cibiyar kulada marayu amma fir nak’i hakan nace nidai Allah ne ya bani d’ah daga sama, a dole ya amince da buk’atata muka rik’eka matsayin d’anmu, a wannan lokacin Dad d’inka ya sami aiki a jami’ar Amurka muka d’unguma muka nufi gida Gombe donyi masu sallama sunyita mamakin ganin mu da yaro kasancewar mun d’au shekaru ba tareda sunsan yanda muke ba hakan yasa sukai zaton ko haihuwa nayi wasu sukai ta cewa k’ila da ciki na tafi kenan, masu mana murna suka mana masu nuna bak’in cikinsu sukai, nan dai muka sanar masu sallama mukazo yi masu zamu koma k’asar Amurka da zama na wasu lokuta, duk duniyar nan bayan Dumba da bamusan yanda zamu sameta ba saiko aminiyata Farida su kad’aine sukasan cewa bamu ne muka haifeka ba.....!” Mummy ta k’arashe tana matse k’walla da bakin zaninta...
Yayinda Sameer kansa ke k’asa hawaye naci gaba da gangaro masa tambayoyi da dama suna neman tarwatsa masa kwanya...

A hankali ya d’ago ya dubi Mummy dake d’igan hawaye wani irin tausayinta da k’aunarta ya lullub’esa.... Jiki a sanyaye ya mik’e ya isa ga Mummy ya durk’usa had’ida d’ora kansa saman cinyarta yana kuka sosai, itama d’in kukan take sosai...
Cikin muryar kuka yake fad’in “I’m sorry Mummy, Mummy I’m sorry... Dan Allah ki yafemin, hak’ika banida gatan data wuceki a fad’in duniyar nan, da ace baki amsheni ba k’ila da yanzu an kasheni kokuma an turani wani k’asar almajiranci kaman yanda wancar matar tace... Mummy banida abinda zan biyaku keda Daddy.... Allah shi kad’ai zai iya maku sakayya.....”
Rik’o fuskar Sameer mai zuban hawaye tai itama tana hawayen take fad’in “Sameer ka daina mana godiya, har gobe kai d’ah ne a garemu koda ka sami asalin iyayenka ka sani har abada zakaci gaba da kasancewa d’ah a gareni... Sameer ka kawo haske da farin ciki ma rayuwata wanda na rasa a baya... Har abada kai d’anah ne koda ace ban haifeka ba amma a zuciyata you’re my only son.....!” Gaba d’aya suka kuma fashewa da kuka had’ida rungume juna...
Idan ka gansu sai sun baka tausayi, cikin zuciyarsa yake maimaita AMINAI UKU, Ya sha alwashin INDA RAI sai ya binciko su waye Aminai uku su waye suka rabashi da iyayensa da danginsa, su waye sukai farautar rayuwarsa shekaru talatin baya........!”

***

K’arfe biyu daidai ya sauk’a a garin Kano ko sallama baiyiwa Ammi ba ya fice abinsa, bai zarce ko ina ba sai gidan Mamani, aiko taji dad’in ziyarar tasa sai haba haba dashi take tana fad’in “Lale Haladu d’an gayu....” Tuni ta umarci Raihana data kawo masa abinci da abin sha... Tana ida kawo masa taceda Mamani zata sashen su Marliya lokacin kai abinci asibiti yayi zasu kai abincin Abbah...
Mamani ta jinjina mata kai kana tace su kula da hanya itama tana nan tafe idan rana yayi sanyi.....
Raiha ta amsa mata cikeda ladabi kana ta fice...

Duban Mamani yai kana yace “Mamani waye babu lafiya...?”
Mamani tace “Abbansu ne ke asibiti yau kwana biyu kenan...”
Khalid ya d’anyi shiru kaman mai nazari har Raiha ta kusan k’ofar fita daga sashen Mamani yaceda Mamani su tsaya zai kaisu asibitin...
Mamani tace “Kai Haladu da d’awainiya haka...”
Khalid ya kurb’i ruwan gabanshi yace “A’a haba dai ai babu komai Mamani....”

“Ayya Haladu yaron arziki....” Ta d’an bud’e murya ta kira Raiha tace “Maza kicewa ‘yan uwan naki za’a kaiku koh, ku jirashi yana nan fitowa...”
Raiha ta amsa had’ida jinjina kai kana ta nufi sashensu Nabila...

Mamani ta dubi Khalid dake k’ok’arin mik’ewa nan ta hangi rama da ya d’anyi shima..
Turus tai tana dubansa kana tace “Haladu lafiya kake kuwa... Jibi yanda ka rame ba kaman wancan lokacin da na ganka ba sannan d’an walwalan da kake yanzu du babu lafiya dai koh...?”
K’ak’aro murmushi yai yana ciro car keys d’insa daga aljihu yace “Babu komai Mamani kawai dai gajjiyan hanyace, barinje mu duba Abban...”
Mamani ta jinjina kai ba wai don ta yarda dashi ba tace “Toh abincin fah....?”
Nan ma cewa yayi sai sun dawo yaci, Mamani dai dubansa take gaba d’aya kaman wani abin na damunsa, fatan alheri da adawo lafiya tai masu kana ya fice...

Nabila ta dubi Raiha kana tace “Bak’on Mamanin ne yace zai kaimu....?”
Raiha ta jinjina kai tace “Eh Addah Naby inagama ya fice tuntuni mu yake jira....”
Daidai nan Marliya ta fito da basket na abinci tace “Mujenku koh...”
Itadai Nabilah dubansu kurum take kafin ta zira takalmanta ta biyo bayansu don tuni Marliya da Raiha sun fice...
Suka gaidashi ya amsa masu da sakin fuska kana ya bud’e masu backseat suka shige...
Yaja ya tsaya yana jiran fitowarta...
Tana tafe tana gyara zaman wuyan hijab d’inta kaman wacce akace ta d’ago idanu nan sukai ido hud’u yana tsaye ya hard’e hannaye fuskar nan tamau babu alamun walwala yana jifanta da firgitaccen kallo... Take ta d’aure fuska itama sai sakin huci tana tuna cin zarafin dasu Yesmin suka mata akanshi.....


SameenaAleeyou 📚



*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*45*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Kaman zata sa kai ta juya sai ta jiyo muryar Marliya tana fad’i mata ta k’araso su tafi....
Ta d’an d’auki wasu dak’ik’ai tana tsaye kaman bazata motsa ba sai kuma ta dawo da baya, Khalid yana ganin haka ya bud’e mota ya shige...
Itako Nabila tana k’arasowa ta nufi back seat saidai taji marfin motar a kulle, da shike glass d’an a zuge yake hakan ya bata daman danna masa harara daga cikin mirror shid’inma ita yake duba fuska babu walwala, bai tankata ba sai bud’e mata front seat da yai....
Marliya na dubansu tana karantarsu tabbas ko ba’ace ba wannan shine saurayin da Nabila ke ambatonsa, ikon Allah ashe ba Abbah kawai ba harta Mamani ya sani, Marliya tace cikin zuciyarta...
Idanunsa a kanne yake dubanta, bataso ‘yan uwan nata su fahimci wani abu, hakan yasa ta nufi frontseat tana tab’awa kuwa ta jita a bud’e, fuska a tamke babu walwala ta shige....
Kaman wanda yake jira tana shigewa yaja motar ya soma tafiya... Bakajin komai sai sautin music dake tashi a hankali cikin motar.... Marliya ce kurum da Raihana ke magana jifa jifa a b’angaren Khalid da Nabilah kuwa kowa da abinda yake sak’awa cikin zuciyarsa...
Tafiyar da bata wuce ta mintoci ashirin zuwa ashirin da ashirin da biyar ba ta kaisu asibitin....
Marliya da Raiha suka masa godiya suka sauk’a suka nufi cikin asibitin da kwandon abincin... Kafin Nabilah tai wani katab’us da niyyan fita saiji tai ya saka motar lock...
Ta kuma jan handle d’in taji tabbas a kulle ne.... Tsananin takaici ya kuma cikata...
Fuska a tamke ta juyo tanai masa wani irin duba.... Cikin tsantsan kufula take dubansa... Ba tareda ya dubeta ba yace “Tell me is it true....?”
Da tsananin mamaki ta kuma dubansa zuciyarta na kuma tafasa...
Cikin tsananin fushi take fad’in “Kaga malam ka bud’e mun k’ofa na fi....” Batakai aya ba ya katseta cikin tsananin fushi da d’aga murya lokaci guda ya juyo da fuskarsa yana dubanta...
“I’m asking you to tell me the meaning of this...!!” Ya k’arashe yana nuna mata hoton video d’in dasu Siyama suka mata yara na mata wak’an karuwace....
Zuciyarta taci gaba da sosuwa tamkar zata fito waje, take taji k’walla na neman ciko idanunta...
Banda watsa mata muguwar kallo Khalid baya komai, jin tayi shiru ya sanyashi jinjina kai had’i da sakin gajeren murmushi kana yace “So it is true.... Da gaske ne kenan... Why Teddy Bear....? Meyasa... Meyasa...? Why did you choose to break my heart.... Tell me why..!!!?” Ya k’arashe tamkar wanda zai shak’o wuyanta...
Cikin tsananin tafasan zuciya idanunta na zubar da k’walla take fad’in “This is all your fault, da ace baka shigo cikin rayuwata ba da babu wanda zaimin wannan cin zarafin, meyasa baka tambayai wad’anda suka tura maka ba idan gaskiyace ko akasinta... Why do you even care...? Meye had’ina dakai meyasa bazaka k’yaleni ba ka fice a rayuwata ba... Ni Nabilah ban tab’a giving up ma fad’a ba sai akanka.... Why just can’t you stay away, why is it so hard for you...!?” Batakai aya ba ya katseta da fad’in “Because I Love you.... I love you so much, abinda kike tambaya ba mai yuwa bane... Ina Sonki Nabeelah....” Ya k’arashe cikin tsananin huci yana mai kallon k’wayan idanunta mai zuban hawaye....
A hankali tasa bayan hannunta tana goge hawayen kana tace “Please ka bud’e min na fice...” Tai maganar cikin tsananin sanyin murya...
Ya d’auki wasu dak’ikai yana duban yanda jikinta yai sanyi sosai kafin yasa hannunsa akan security lock d’in ya bud’e...
Har ta shige cikin asibitin tana matsan k’walla kalaman ina sonki da Khalid ya fad’i mata basu daina yawo a kwanyarta ba....
Da k’yar ta iya saita kanta kana ta nufi ward d’in da Abbah yake don sam bataso iyayen nata su gano wani abu....
Da sallama saman bakinta ta shigo d’akin, saidai tsananin sanyi jikinta yai ganin gaba d’ayansu idanunsu akanta ne... Nabilah tasha jinin jikinta domin kuwa tasan dole Mamy ta tambayi ina ta tsaya ga ‘yan uwanta tuni sun shigo, duba d’aya zakaiwa Mamy ka fahimci magana ne sosai a bakinta, su Marliya ma duk sunsha jinin jikinsu don har tunanin shigowar Nabilar suke....
Fitowar Abbah daga bayi ne ya ceceta Mamy ta had’iye tambayar da tai niyyan jefo mata ta k’arasa domin taimakawa mijinta....
Gaba d’aya suka rusuna suna gaida Abban sai amsa masu yake da sakin fuska yana fad’in su k’araso kusansa sosai su gaisa don ya shirya gina wata shak’uwa ta musamman da yaransa....

Abbah yace Mamy ta huta yaransa suyi serving nasa, jiki har rawa yake Nabilah ta mik’e tana k’ok’arin serving Abbah cikedajin dad’in yanda Babansu ya canza, tanayi tana satan kallon Mamy da har lokacin muguwar kallo kurum take aika mata....
Abbah sai jan yaran nasa da fira yake yana tambayansu abubuwa sosai gameda rayuwarsu musamman gameda karatunsu, gwanin ban sha’awa....
Knocking da akai a k’ofa ya d’an katse masu firan nasu, Mamy ta bada izinin shigowa, ya shigo sallama saman bakinsa wasu samari guda biyu suka biyo bayanshi da carton d’in ruwa da nau’in lemu har kashi uku....
Suka gaidasu suka fice...
Khalid ya k’arasa shigowa Mamy tanai masa nuni da farar kujeran dake gefe, k’irjin Nabila sai faman lugude yake, Abbah yaso ganesa bayan sun gaisa nan Khalid d’in ke sanar dashi abokin Sameer ne da suka tab’a kai masa ziyara tare a gida... Nan fah aka soma sabon gaisuwa musamma da Abbah yaji cewa abokin Sameer ne....
Marliya ta k’arada fad’in shinema ya kawosu... Nabilah ta jefa mata kallo aiko itama kallon tuhumar Mamy ke mata.... Gaba d’aya ta kasa sakewa alla alla take ya tashi ya tafi, batasan uwar gulmar daya shigo dashi gaida Abbah ba da alama saida ya tsallaka kanti tsallake yayo sayayyan sannan ya shigo, wani irin muguwar haushinsa ke d’awainya da ita.....
Mamy dai bata wani sake da Khalid d’in ba kaman yanda Abbah ya sake dashi, bai wani jima sosai ba ya masu sallama had’ida fatan samun sauk’iwa Abbah...

Har suka k’araci zamansu Mamy bata sakewa Nabilah ba ita kanta tasan had’uwarsu da Mamy bazasu wanye lafiya ba she had a lot to explain to her...

Daga nan ne suka tambayi Mamyn cewa zasu biya gidan Baba Alhaji su duba Kausar hakan yayi mata don dama suna k’ok’arin shirya randa zasu d’auko yarinyar itada Zulfa’u saidai sabida ciwon Abbah suka dakata sai ya sami sauk’i kar a kuma k’ara masa damuwa kan wata damuwa tinda tasan zai wuya Hajiyar Hafiz ta basu yarinyar cikin sauk’i....

***


Sun k’ule itada Lami a uwar d’aki suna tattauna lamarin, su k’ulla wannan su sak’a wancan kaman daga sama suka jiyo hayaniyar Sahariyya tana faman bambami, Hajiya da Aunty Lami suka dubi juna a tare, a tamanin Hajiya ta mik’e tana gyara d’aurin zani ta nufo waje Aunty Lami na take mata baya...
Sahariyya ta kasa ta tsare tana d’aga k’irji sama tana ci gaba da tafe hannaye tana fad’in “Billahillazi baki isa ba ba’a haifeki ba Kausar ta fiki gadara da gidan Ubanta, tinda ko yaushe yaga dama zai iya sallamarki kaman yanda ya sallami uwar yarinyar....!”

Sawwama tai tak’aitaccen murmushi kana takai dubantaga yanda su Hajiya ke tsaye, lokaci guda ta gyara tsayuwarta had’ida tallabo Kausar dake rik’e a hannunta, cikin yatsina fuska had’ida kuma turo kallabinta gaban goshi tai nuniga Hajiya da ‘yar yatsa kana ta kuma duban Sahariyya tace “Kinga ko wancan ma haka tai ta bari, ki tambayeta kiji idan ta isa ta saka Hafiz ya sakeni.... Balle ke k’aramar ‘yar iska k’aramar marar kunya wacce ko ajin farko baki ida ba...!” Ba Sahariyya data saki baki tana duban ikon Allah ba harta Aunty Lami da Hajiyar Hafiz d’in tsaye sukai tamkar gumaka suna duban Sawwama wacce ta zame masu tamkar dodanniya....
Cikin taku na k’asaita ta k’araso gaban Hajiya kana ta dangwala mata Kausar tana mai fad’in “Gata nan.... Ai dama na fad’i maki kada kiyi gigin barinta gidana domin batada muhalli cikinsa sannan ba raino aka auroni nayi ba rainon d’anki da nake idan baki gode min bazaki k’aromin ba... Gata idan kunga dama ku jefarta waje amma wllhi wllhi kunji na rantse ba cikin gidana ba....!”

Tasa kai tana k’ok’arin juyawa, banda huci da tafasa Sahariyya bata komai, duban Hajiya kawai take tana jira taga matakin da zata d’auka bataga alamun Hajiya zata motsa ba...
A d’ari Sahariyya ta sunkumo Kausar tana fad’in “Wllhi billahillazi kinyi kad’an ki shigo har cikin gidan mahaifina kiciwa mahaifiyata kashi aka k’aramar karuwa, wllhi k’aryar iskanci kike Kausar bata gida sai gidan mahaifinta....!”
Dariyar rainin hankali Sawwama ta d’anyi a tak’aice tana mai watsawa Sahariyya muguwar harara lokaci guda ta d’aga hannu ta d’auke Sahariyya da wata shu’umar mari wanda saida yasa tai kusan sakin Kausar a k’asa...
A daidai lokacinda su Nabila su Raiha suka shigo gidan da sallama....
Tukunyar tafasheshen ruwan d’anwake dake gefe sai faman tafasa yake Sahariyya tai kan Sawwama tana k’ok’arin cakumota had’ida jifa da Kausar da batamasan ina take k’ok’arin jefata ba... Cikin wani irin zabura Raihanah ta saki k’ara ta nufi Kausar da tuni tayi ambaliya cikin ruwan d’anwaken nan, tukunyar ta hantsilo ta zubewa Raihanah a b’angaren jikinta a yayinda take k’ok’arin ceto rayuwar Kausar... Wani irin k’ara Raihanah ta saki sanda ta rungume Kausar da tuni kukanta ya d’auke cak....
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un....
Nabila da Marliya daskarewa sukai cikin tsananin tashin hankali yayindasu Hajiya suka d’imauce lokaci guda, harta Sahariyya da Sawwama saida suka tsaya cak da fad’an da suke suna duban Raihana da Kausar da tuni sunyi wanka da tafashesshen ruwan d’anwake....

Zulfah dake k’ok’arin saka k’afafunta cikin ward d’in Abbah wani irin bugawa k’irjinta yai jiri ya kusan aikata k’asa ba tareda sanin dalili ba, da dafe ta ida shigowa cikin ward d’in.....


SameenaAleeyou 📚



*INDA RAI*
_................DA RABO_



*46*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Aunty Lami ce tai kazar kazar aka kwashesu zuwa asibitin masu fama da matsalar k’unan wuta.... Gaba d’aya su Nabilah Hajiya da Marliya harmada Sahariyya suka d’unguma suka take masu baya...
Suna isa asibiti aka wuce dasu emergency.... Dr Awwab abokin aikin Sameer a nan asibitin Kanon shi ya amshi case d’in nasu, saidai gaba d’aya shi kansa lamarin ya shige masa duhu musmman Kausar wacce ta k’one sosai domin kuwa idan ba sa’a ba k’unan ka iya tab’a zuciyarta kuma idan har hakan ne ta kasance yasan abu ne mai matuk’ar wahala ta tashi saidai wani ikon Allah musamman duba da k’aranci na shekarunta da tsananin taushi da fatarta kedashi, a sani hakan yasa dole ya nemi taimakon Sameer domin kaw babu kaman shi a asibitin wajen sanin fata da gyaranta....
Sameer yana gab da shigowa garin Kano akai masa waya daga asibiti cewa akwai emergency.... Bai wata wata ba ya wuce asibitin domin ceton rayukan bayin Allah da suka sami had’arin wuta....

A b’angarensu Nabilah kuwa suna reception kowa da addu’an dake bakinsa dukda cewa babu wanda ya iya tsagaita hawayensa, Aunty Lami ce mai k’arfin hali tana dnnanrsu don harta Hajiya dirshan tai a reception d’in tana matsan k’walla da bakin mayafi tana fad’in ta shiga uku ta lalace sun kashewa Hafiz d’iya.... Kukan nata banda k’ona ran Nabila baya komai ji take tamkar taje ta rufe Hajiya da duka don takaici...
Aunty Lami ce tai k’arfin halin kiran Mamy ta sanar da ita halin da ake ciki da kuma asibitin da suke... Banda salati da ambaton Allah Mamy bata komai, sauk’in abin Abbah yana bacci baisan abindake faruwa ba, Mamy na cikin yanayin ne Zulfah ta turo k’ofa ta shigo da alama daga wajen aiki take, kallo guda taiwa Mamy ta kuma jin gabanta ya mugun fad’uwa.... A b’angaren Mamy ma duban Zulfa’un da tai si taji zuciyarta ta kuma yankewa, ta kasa jurewa domin kaw idanunta sun gaza b’oye hakan....
Cikin tsananin sanyin jiki Zulfah tace “Mamy lafiya ya na ganki haka kodai jikin Abbah ne....?”

Mamy ta kasa jurewa sai k’walla da suka ciko idanunta, cikin sauri ta janyo hannun Zulfah suka fice daga d’akin gudun kada Abbah ya tashi....
Saida tai k’ok’arin kwantarwa Zulfa’u hankali kafin ta sanar da ita halin da ake ciki....
Tuni k’walla sun ciko idanunta, ta kuma duban Mamy tana mai k’ok’arin goge hawayen dake zubo mata take fad’in “Mamy duk laifina ne meyasa na bar masu d’iyata, meyasa na barta babu kula....!” Kuka yaci k’arfinta...
Rik’eta Mamy tai ta zaunarta saman kujera dake gefe, cikin sigan lallashi da lallama take fad’in “Kar kice haka Zulfa’u, komai muk’addari ne daga Allah... Tuni Allah ya hukunta hakan, yau koda Kausar na taredake bazata wuce abinda Allah ya k’addara mata ba, kiyi hak’uri muyi masu addu’a Allah Ubangiji ya basu lafiya, yanzu ki tashi na kira Bara’atu zata taho ku tafi ku duba jikin nasu kinga ni bazai yuwu na tafi na bar Abbanku ba... Zulfa’u ki kwantar da hankalinki kinji koh don Allah kada ki d’aga hankalinki...”
Banda jinjina kai Zulfah bata komai sai matsan hawaye da take...
Jim kad’an Aunty B ta iso a fujajan suka wuce asibiti....

***

Kasancewar Kausar tafi jin jiki domin kaw gaba d’ayanta ta fad’a cikin tafashesshen ruwan danwaken sannan dashike k’aramar yarinyace sosai fatarta akwai taushi sosai hakan yasa k’unar yafi mata illa, Sameer na isowa ita suka soma attending, take aka preparing surgery aka shige da ita....
Sosai k’unar ya shiga jikin yarinyar domin kuwa ya riga da ya tab’a heart d’inta, sanda Sameer ya fuskanci k’unar ya shiga sosai take jikinsa yai sanyi domin yasan zai wuya yarinyar takai labari, Allahu Akbar ai kuwa basu jima da soma aikin ba zuciyar Kausar ta daina bugawa... Baisan dalili ba amma har ransa yaji mutuwar yarinyar, jikinsa yai matuk’ar yin sanyi, ya saba da irin hakan tinda ba yau bane ya soma aikin likitanci amma mutuwar wannan yarinyar a hannunsa yayi bala’ain d’aga masa hankali....
A hankali ya zame hannayensa yana mai k’urama na’urar dake nuna tsayuwan bugun zuciyar idanu...
Dr Awwab ya girgiza masa kai alamun babu ta riga ta rasu....
Sameer ya lumshe idanunsa a hankali kana suka nufo waje shida Awwab sauran nurses na k’ok’arin shirya Kausar...

A bakin theatre room d’in suka tsaya bayan sun kwab’e mask d’in dake bisa hancinsu da bakinsu suna tattauna lamarin yanda Awwab ke sanar dashi family d’in suna reception...
Sameer ya jinjina kai yace “Kace su biyu ne masu case d’in...?”
Awwab ya jinjina kai yace “Yes su biyu ne babbar tana ward nata bai shiga deep kaman na ita wannan k’aramar ba....”

Sameer ya d’an jinjina kai a hankali kana yace “Ok ka sanar da nurses d’in they should get the second patient ready zan k’arasa nai magana da family d’insu....”

Awwab ya jinjina kai yace “Ok sai ka iso....”
Jinjina masa kai kurum Sameer yai kafin ya nufi reception...

Zulfa’u da Aunty B suna isowa Su Marliya da Nabilah suka k’arasa a guje suka rungume Addarsu suna kuka... Aunty B kuwa banda jifa da kallo tskaninta dasu Hajiya bata komai, jira kawai take taji silan k’unan taji su waye sukai sanadi..
Zulfah ta kuma karaya ganin ‘yan uwanta sun rungumeta suna kuka, cikin tsananin rawar murya take furta “Nabilah ku fad’a min ina Kausar da Raiha...? Dan Allah ku fad’a min d’akin da suke naje na gansu....”

Wani irin bugu Sameer yaji k’irjinsa nayi sanda ya danno reception yai tozali da mutanen da bai jima da sanin cewa ‘yan uwansa bane... Zulfa’u Nabilah da Marliya yake duba da raunannun idanunsa yanda suka rungume juna suna kuka.... Yana jiyo sanda Zulfah ke fad’in ina d’iyarta...? Zuciyarsa ta kuma karyewa... Kenan yarinyar ‘yar uwarshi ce ta rasu a hannunsa... Ta yaya zai soma sanar da ita cewa d’iyarta ta rasu... Shin wannan shine farkon abinda zai soma had’asa da ‘yan uwansa... Mummunar labari irin wannan, ta yaya zai iya jurewa ya tink’ari ‘yan uwansa da wannan batu...? Tsananin tausayinsu gaba d’aya shida ‘yan uwan nasa ya rufe masa zuciya.... A hankali ya soma takawa har ya isa garesu yai tsaye ba tareda sunsan cewa wani na tsaye kansu ba.... Aunty B kuwa nata aikin lallashinsu tana fad’in addu’a zasuyi ba kuka ba In sha Allah Kausar da Raihanah zasu sami lafiya....

Su Hajiya suna hango shi yayi tsaye suka nufi kansa suna tambayarsa Hajiya na fad’in “Likita ina jikata...? Ka fad’a mini ina tak...?” Muryar Hajiya ya sark’e sanda tai idanu hud’u da mutumin da ya bayyana gabanta matsayin likita, zuciyarta ta shiga harbawa da sauri, tsoro da firgici suka bayyana mata.... Ta soma tunanin kodai Ma’aruf gizo yake mata... Tsananin tashin hankali ya wanzu a tattareda Hajiya... Idanu hud’u sukai itada Aunty Lami wacce itama hakance ta kasance da ita, ko shakka babu su biyun suna buk’atar keb’ewa su tattauna lamarin Ma’aruf wanda ke barazanar tarwatsa masu rayuwa...


Maganganun Hajiya ya dawo da hankulansu, gaba d’aya kallon sani suke masa... Sahariyya kaw tuni jikinta ya d’au rawa har ta mance mai ya kawosu asibitin ta shiga bin Sameer da mayen kallo tana yank’are baki had’ida komad’a ita kad’ai... Tabbas ba gizo yake mata ba wannan na nuni da alamun cewa shid’in nata ne da sannu zai zama rabonta tinda gashi Allah ya kuma had’asu, ita kad’ai sai sakin murmushi take tamkar tab’ebb’iya...
Zulfa’u tai k’arfin halin maimaita tambayarta “Dr how’s my daughter.... How’s she doing.... Ina take dan Allah.. Shin zamu iya ganinsu...?”

D’an jim Sameer yayi ba tareda ya iya furta koda

Please Login or Register in order to submit comment