Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k’yar Mamani ta tsaya bisa k’afafunta tana kanne idanu take duban Sawwama... “Daga duniyarmu kike kokuwa akasinta...?” Ta k’arashe tana zagaye Sawwama datasha matsu cikin ‘yar fingilan riga da wando wanda za’a iya kiransa da 3quater....
Mamani taci gaba da zagayeta tana kallo take fad’in “Ikon Allah gashi dai hausa ce bakinki ba yaren arna ba balle nace babbar kahurace ked’in.... Toh kodai b’atan hanya ne nayi ba nan bane gidan Hafizun....? Ga katarorin naki dai kaman curin sakwara, shi kaw sharab’an gashi dai kaman na masu wasan dambe tsala tsala haka nan, iko sai Allah.... Ke kaw baiwar Allah sanyi bai damunki...?”

Tinda ta soma magana Sawwama ke dubanta baki sake, lallai tsohuwar ta iya cin fuska, tazo har gidanta tana yab’a mata maganganu wanda babu wanda ya tab’a yab’a matasu....

“Ke tsohuwar ashana ki saurareni nan, nafiki iya bariki barin fad’a miki, tun kafin banyi k’asa k’asa dake ba ki fice ki barmin gida bana cikeda k’anan....”

Turo k’ofa da akaine ya sanyasu gaba d’aya maida hankalinsu ga k’ofar... Hafiz ne ya shigo rik’eda ledar kaza hannunsa sai buga sauri yake...
Mamani ta saki baki tana kallon ikon Allah tabbas ba b’atan hanya tayi ba, nan ne dai gidan jikanta Hafiz... Toh ina Zulfa’u..? Sannan wannan mai k’iran arnan kan dutsen mai take cikin gidan...
Tana kallo Sawwama ta k’arasa ta rungume Hafiz had’ida d’alewa jikinsa tanai masa oyoyo cikin salo.... K’iris ya rage Mamani bata saki sandarta ta dogarawa ba tana buga sallallami...

“Laaa ha’ila ha illahu Muhammadarrasulillahi.... Na shiga uku ni Halimah mai zan gani.....?” Ta k’arashe tana neman wajen jinginuwa da zai mata waiji domin kaw tuni Sawwama dai ta tallabo bakin Hafiz ya shiga sumbata... Mamani ta rintse idanunta da k’arfin gaske tana karanto duk lazimin da yazo bakinta....

Shiko Hafiz da dabara ya k’waci kansa hannun Sawwama ya k’araso wajen Mamani cikin sauri yana fad’in “Mamani mai kikeyi a nan... Yaushe kikazo...?”

Har lokacin ta kasa bud’e idanunta balle ta basa amsa sai salati take dokawa tana fad’in abinda da ake fad’I zai faru k’arshen zamani gashi Allah ya kawosu....
Jin zata fara kuka da kururuwa yasa Hafiz kamo hannayenta ya nufi tsakar gidan da ita har wannan lokaci idanun Mamani a rintse suke tana fad’in “Hafizu wacece wannan ince dai ba matan kwararo ka soma kawowa cikin gidan ba... Ohni Jikar mutum hud’u ita Zulfa’un na ina....?”

Sawwama da takaicin tsohuwar ya kuma kamata tare Hafiz tai da fad’in “Ina kuma zaka shigar min ita.... Wllhi karma kayi tunanin kaita parlor na... Wace itama tukuna....?”

Wani irin duba ya aika mata kana ya janyo kujera a nan tsakar gidan ya zaunar da Mamani...
Cikin k’asa da murya yake fad’iwa Mamani... “Matatace Mamani ba karuwa bace, dan Allah kada ki sake dangantata da wannan kalma kinji koh...”
Mamani ta kasa amsashi sai kallon dataci gaba da binshi dashi gaba d’aya kaman ba Hafizunta ba...Tanaji tana gani ya kuma mik’ewa ya nufi Sawwama dake faman cika tana batsewa...
“Kakata ce....” Ya fad’i yana k’asa k’asa da idanu ganin irin muguwar kallon da take aika masa....
Tsuka ta buga kana ta mik’a hannu tana fad’in “Bani nan....” Don tuni hancinta ya jiyo k’amshin kaza....

Kai a k’asa ya mik’a mata ledar ta kuwa wafce kaman jira take...

Mamani ta zuba masu idanu kaman ta samu Tv....

Sawwama ta galla mata harara tana mai ci gaba da fad’in “Kai nake jira kazo ka d’auko min paranti....” Ta k’arashe tana mai zama daga can bakin k’ofar d’akinta ta baje saman tabarma tayi d’ai d’ai ta kuwa bud’e ledar kajin k’anshi sai dakan hancin Mamani yake....

Mamani naji na gani Hafiz ya mik’e babu musu ya nufi kitchen ya d’aukowa Sawwama paranti... Zai mik’e tace “Zauna...”

Ya koma ya zauna... “Bani a baki.....” Nan ma babu musu ya shiga d’auka yana kaiwa bakinta...

Mamani da abin ya koma mata tamkar a shirin wasan kwaikwayo tagumi ta rapka tana kallon ikon Allah, duk wani umarni da Sawwama zata baiwa Hafiz cikin rawar jiki yakeyi...
Tinda take a rayuwarta bata tab’a cin karo da abinda ya sanyar mata da jiki ba irin lamarin Hafizu da sabuwar matarsa, abin mamaki saiga k’walla na neman cikowa idanun Mamani tsananin tausayin jikanta da ya dirar mata, take ta soma tunanin toh ina Zulfa’u ake wannan bidirin a gidan...

“Hafizu...” Ta ambaci sunanshi daga yanda take zaune....
Ya juyo yana dubanta, take yaji jikinsa yayo sanyi sosai ganin irin yanayin da Mamani ta shiga ciki...

“Ina Zulfa’u...?” Ta tambaya tana dubanshi...

Kafin ya sami zarafin bata amsa Sawwama dake taunar nama ta kwashe da dariya tace “Zulfa’u kike nema....? Toh jikarki bata gidan nan don tuni an jima da sakinta, kinga d’akinta can ya zama kango.....” Ta k’arashe tana kuma sakin shewa..

Mamani dataji abin kaman diran aradu kallo tabi Hafiz dashi wanda kansa ke k’asa tsawon wani lokaci...
“Hafizu da gaske ka saki Zulfa’u...?” Ta tambaya tana dubansa...

Saurin girgiza kai ya shigayi yana fad’in “A’a.... Ta tafiya tayi Mamani amma zata dawo...”

Sawwama ta kuma sakin shewa kana tace”Ashe dai bakuda labari, tun wuri ku bazama duniya neman d’iyarku don rabonta da gidan nan watanni hud’u kenan tun kafin a auroni....”

“Hafizu...!” Mamani ta fad’i tana dafe k’irji.... Lokaci guda taci gaba da jero salati tana tana tafe hannaye....Kaman wacce aka sakata mata batir nan ta soma kuka wiwiwi tana fad’in ahalil kitabi ta shanye mata jika...

Haba nan fah Sawwama ta kuma tinzira tana balbala masifawa Hafiz cewa saidai ya fice mata da wannan tsohuwar a gida don idan bata daina zaginta ba tsaf ramawa zatai...
Hafiz yasan Sawwama zata aika abinda tace tuni ya kamo Mamani suka fice daga gidan ko cinyar kazar nan ba’a gutsura mata ba dukda ranta ya biya...
Da kanshi ya tarar mata adaidaita ya sakata ya sanarwa mai adaidaitan yanda zai kaita..
Haka Mamani ta tallabo bakin mayafi tanaci gaba da kuka tana fad’in shikenan Zulfa’u bata lashe Hafizu ba ga Ahalil kitabi ta shanyesa....


SameenaAleeyou📚



*INDA RAI*
_................DA RABO_



*39*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




A daidai k’ofar gidan Baba Alhaji Mamani ta umarci mai keken da ya ijeta...
Ta lalumo kud’i a lalitanta ta biya mai adaidaitan, kai tsaye ta nufi gidan bata daina koke koke tana fad’in shikenan an shanye mata jika ba...
A farfajiyan gidan ta hangi Hajiya Haule sai jibgan Rihanah take tana fad’in sai ta fito mata da kud’inta data d’auke, Kausar na zaune gefe tana kuka fuskarta dama dama da kunu yayinda Sahariyya da Najah ke murnan tsalle suna fad’iwa Hajuyarsu ta daki kud’inta da kyau, sam ko sauraro Mamani basuyi ba...
Ganin za’a kashe mata jika ya sanyata k’ara sauri sai gani sukai Mamani ta tare dukan tana fad’iwa Hajiya ta had’e da ita ta daka...

Gaba d’aya sukabi Mamani da kallon mamaki abinda bata tab’ayi ba shine ta nuna kulawa ko damuwarta kan jikokinta mata sai gashi yau ta tarewa Raiha duka har tana cewa a had’e da ita...
Hajiya dake faman huci tana muzurai sai aikawa Mamani muguwar kallo a kwance take itako Sahariyya datafi kowa shara cewa tayi “Mamani ki kauce ki bada filiwa Hajiya tarbiyawa d’iyarta take, yo da kike cewa a had’e dake mai za’a daka a nan salon a k’arasaki ki janyowa mutane jangwamgwam....!” Batakai aya ba taji sauk’ar sandar Mamani a kafad’arta ta kaw rik’e wajen tana ihu...
Mamani taci gaba da fad’in “Ke ki kiyayeni kinsha rashin kunya a nono koh... Toh billahillazi ki bar ganina haka nan ina dogara sanda tsaf zan murk’usheki wajen nan... Ja’ira maras ta ido...”

Hajiya ta cafi zancen da fad’in “A’a nidai Mamani gaskiya ki daina aibanta min d’iya, idanma tayi rashin ta idon ai kinsan yanda ta samo....” Ta k’arashe tana danna mata harara...

Tsananin mamakin rashin tarbiyan Hajiya da yaranta ya sanya Raihanah girgiza kai tana sosa wajen da aka jibgeta hawaye na kwaranyo mata...

Jinjina kai Mamani tai kana tace “Yayi... Yayi Haule, ai bansan rashin ta idon naki ya kawo nan ba, amma ki jira kiga yanda duniya zatai dake, na tabbata ke kika tilastawa Hafizu sakin Zulfa’u, kin sabautar min da jika ta shige duniya yanzu kin kama wannan ‘yar marainiyar kina neman illatata.... Kiji tsoron gamuwarki da Allah....”

Hajiya ta saki shewa tana tafe hannaye had’ida rangad’a gud’a kana tace “Yau akeyinta... Yanzu ke Mamani bakiji kunya ba, har da kike cewa an sabautar miki da jika, har yaushe kika soma son Zulfa’u a matsayin jikarki, wani irin tsana da muzantawa ne baki mata ba yanzu don Hafizu ya saketa ba abin kimin godiya bane, Toh barikiji na fad’a miki banson kinibibi da bak’in iyayi maza ki kwashi k’afafunki ki ficemin a gida....!” Ta k’arashe cikin d’aga murya tana mai mata nuni da k’ofa...

Mamani da zuciyarta ke mata k’una a hasale ta shiga nuna Hajiya Haule da sandarta tana fad’in “Ke Haule ki kiyayeni idan kin shanye Sarki (Hakan Mamani ke kiran Baba Alhaji a matsayinsa na babban d’anta) baya ganin laifinki toh kul kada ki kuskura ki gwada rashin kunyarki akaina...”

Hajiya bata bari takai aya ba tace “Shanye Sarki saidai kar a kuma, kinga nan....” Tai nuni da tafin hannunta kana tace “D’anki na nan sai yanda na juyasa, ko kasheki zanyi bazai tab’a ganin laifina ba saidai ma ya min godiya....” Suka saki shewa itada yaranta...

Mamani da tuni hawaye sun soma zubo mata murmushi tai a hankali kana tace “Dama ita duniya abinda ka shuka shi zaka girba, ko kad’an banji zafin shanye naki d’an da Alahalil kitabi tayi ba... Hakan shine daidai, na kumaji dad’i da Zulfa’u ta rabu da auren wahala in sha Allahu alkhairi na gaba da ita....” Ta juya ta dubi Raihanah da Kausar dake rakub’e gefe guda tace “Ku taso mu tafi kun gama zaman gidan wannan azzalumar....”

Raihanah ta mik’e a tsorace tana rungume da Kausar...
Ai tuni Hajiya ta finciki Kausar tana watsa masu harara take fad’in “Koda wasa idan zaki d’auki jikar naki bisimillah amma wannan jikata ce yanda kikeji Raiha d’iyar d’anki ne haka nakeji Kausar d’iyar Danah ne don haka babu yanda Kausar zata tafi a nan gidan zata zauna...”
Ta maida dubanta ga Raihanah kana taci gaba da fad’in “Ke kuma ki bita idan kinga dama amma ki sani ubanki na dawowa zansa ya d’aukoki, munafukar banza munafukar wofi....” Ta k’arashe tana janyo mata jakan kayanta had’ida jifanta dashi... Taci gaba da fad’in “Idan dai wannan tsohuwar kakar takuce sai kinyi d’andakinsani komawa gabanta domin kaw ba k’aunarku take ba...”

Mamani bata amsata ba don gaba d’aya jikinta a sanyaye yake Sawwama ta gama kashe mata jiki ta nemi fad’a da masifan nata ma ta rasa, kamo hannun Raiha tai suka fice daga gidan, dukda cewa Raihanah bata saba da Mamani ba sannan ta sani Mamani bata son jikokinta ‘yanmata amma har cikin ranta takeji ya fiye mata zaman gidan mahaifinta gaban Hajiya...

A haka suka isa gida Raihana na gane masu hanya....

***

Bayan ficewarsu Sahariyya ta koma gefe ta zauna ta had’e rai sosai donma kar Hajiya tayi tunanin sakata wani aiki tinda Raiha ta tafi, ga wanke wanken da bata ida ba... Tab aiko billahillazi bata isa ta sakata aikin wanke wanke ba saidai tayi da kanta, k’arashe ma mik’ewa tayi ta kad’e bujenta ta shige d’aki....

***

Yesmin tsaye gaban dressing mirror tana kuma shafa yanda Nabilah ta shata mari masu kyau har guda biyu... K’wafa ta kumayi a karo na babu adadi kana tace “Wllhi sai na shayar da ita mamaki, badai a unguwar nan take ba, yazo gidan sauk’i sai tasan ta tari fad’an da yafi k’arfinta... Shegiya d’iyar matsiyata...”

Siyama dake zaune bakin gado tana duban Yesmin d’in sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “yanzu ta ina zamu b’ullo mata....”

Yesmin ta juyo da dubanta gareta kana tace “Ni nasan ta yanda zamu b’ullo mata, badai tace ita maras kunya ba, zamu nuna mata munfita iya bariki da rashin kunya, k’aramace ita a wannan makarantar....”

Siyama ta murmusa kana tace “Ni da police nake tunanin mu kawo mata...”

Girgiza kai Yesmin tai kana tace “A’a ai bata nan zamu b’ullo mata, ta yuyu wannan ta saba kwanan station tinda kikaga haka, tuggu da makirci shine kawai zai rabamu da tsinanniya...”

Siyama ta dara a hankali kana tace “Kinga zo muje kitchen ki sama mana abinda zamuci tinda kinzo na huta order...”
A tare suka fice suka nufi kitchen d’in....

***

Mamani ta lura da yanda Raiha ke d’ari d’ari da ita, tausayin yarinyar ya cika mata zuciya...
“Raihanatu sunanki koh....?”
Raihanah ta jinjina kai a hankali alamun eh....
“Kodai kece Halimatu takwaran tawa..?” Nanma a hankali ta jinjina kai alamun eh kana ta k’arada ni ce...
A fili Mamani ta furta “Alhamdulillah da ya kasance ba’a cikin wad’ancan watsattsun d’iyoyin Haulen aka sanyamin takwara ba... Ki saki jikinki kinji koh, nan gidanku ne... Da Manu da Sarki duka ‘ya’yana ne don haka nan ma gidan Babanki ne kinji koh...”

Raihana ta k’ak’aro murmushi a hankali tace “Toh Mamani....”

“Yauwa Raihantu... Kinci abinci kuwa...?”

Shiru bata amsata ba, Mamani ta fahimci bataci abincin bane, flask d’in dake gefe wanda aka kawo daga wajen Baffah Wada ta janyo ta mik’a mata tace maza taci mai isanta, shinkafa da wake ne da mai da yaji....

Mamani ta mik’e ta nufi d’aki abubuwan data aikata a baya sai dawo mata suke, yanzu idan ba’a sami Zulfa’u ba itama tamada kamisho tunda tana d’aya daga cikin masu aibantata da muzantata da k’untatawa rayuwarta... Allah dai ya bayyanar masu da Zulfa’u ta nemi yafiyar yarinyar nan don bazataso ta mutu da hakkin Zulfa’u akanta ba.... Da wannan tunani ta zauna jiran dawowan d’anta Abbah... A haka bacci yayi gaba da ita...

Raihanah kuwa tuni ta shiga tattarewa Mamani d’aki, ta gyare mata ko ina yayi tas tas gwanin ban sha’awa, tai wanke wanke ta goge ko ina, harta dangin kayan kallo su tv stand saida Raiha ta goge ko ina ta saka roomfresh waje ya d’auki k’amshi kaman ba d’akin tsohuwa ba, kiraye kirayen Sallahn azahar ya tada Mamani, mamaki ya cikata ganin ko ina a gyare bacin tasan yaran Baffah Wada da k’yar akeyi dasu suzo su gyara dama Marliya ce mai shigowa tai mata idan batada karatu....

Nan fah Mamani taga aikin Raiha ya zarce duk wanda ake mata, ita kad’ai sai murmushi take tana fad’in “A’a ikon Allah.. kaji yarinya d’iyar albarka... Oh ashe dai d’iyoyi mata rana ne dasu...” Tai maganar a hankali kana ta lek’a d’aya d’akin ta hangi Raiha na sallah cikinta nan ma tas tas kaman bashi ba...
Ta kuma sakin murmushi cikeda jin dad’i kana ta nufo waje don gabatar da alwalan azahar sai shan mamaki take don harta taakar gidan tas ta share ta gyare...

Mamani ta hangi kujeran zamanta nayin alwala a goge tsaf harda buta a gabanta, ta isa ga kujeran ta dafa ta zauna tana mamakin ina aka samo mata sabon buta... Saida ta d’aga tace “Au ikon Allah ashe dai butarce dai tawa...” K’al Raihanah ta wanke butar ta cika mata ruwa mai d’an d’umi bamai sanyi k’au ba...
Mamani sai mamaki take tana ayyana hankalin yarinyar cikin zuciyarta....

***

Wajajen k’arfe biyar ya fito daga office, tafe akan hanyarsa ta komawa gida ya hangi motar Abbah na k’ok’arin shiga gida, bazai iya shigewa ba tareda ya tsaya sun gaisa da Abbah ba, daga can yayi parking ya sauk’o ya nufi motar Abbah wanda shima tuni yayi parking d’in sakamakon hango Sameer d’in da yayi....

Cikeda risinawa yake gaida Abbahn, Abbah ya amsa masa kaman ko yaushe, fuska fal fari’a...
“Malam Sameer an taso aiki kenan...?” Abbah ya tambaya murmushi kwance saman fuskarsa...
Sameer da shima murmushin ne kwance saman fuskarsa yace “Eh Abbah an taso, ya kasuwa...?”

“Alhamdulillah... Mun gode Allah, ya wajen aikin naka... Anata fama da jama’a koh...?”

Sameer ya d’an shafa kai yace “Alhamdulillah... Toh Abbah zan wuce a huta gajjiya...”

Abbah da duk had’uwansu da Sameer bai fatan abinda zai rabasu cikin sauri ya tari Sameer d’in da tuni ya nufi motarsa da fad’in “Amm Dr nace ba ko zamu shiga kaci abinci.... Akwai fura mai kyau ma sai a dama maka...”
Sameer baison ce masa a’a sabida tsananin nauyin mutumin da yakeji d’an k’ak’aro murmushi yai yace “Ai Abbah ban jima da cin abinci a wajen aikina ba...”

Annurin fuskan Abbah ya d’an ragu, kaman zaice shikenan ka huta gajjiya sai kuma yace “Ko furan kasha Dr, tanada kyau sosai musamman nasa a dinga kawo mani...”

Sameer ya d’an kuma shafar k’eyarsa babu yanda ya iya bazai iya jada Abbah ba sabida tsananin ganin girmansa da yake....
Cikeda risinawa ya amsada “Toh..To Abbah...”

Cikin jin dad’i Abbah yace “Yauwa ko kaifah maza shigo da motar taka cikin gareji...”

Babu musu Sameer yayi yanda Abban yace, suka nufo cikin gidan tare...

Aunty Lami da fitowarta kenan daga sashen Abban don ita keda girki ta gama jere abinci kenan, nan ta hangosu sun jero suna tahowa Sameer rik’eda ‘yar jakkan Abbah....
Gabanta ya yanke ya fad’i, shikenan kullum kusancinsu k’aruwa yake, cikinta ya murd’a lokaci guda....
A daburce ta nufi sashenta tana tunanin abinyi, Aminiyar Sirri zata kira ko kuwa Haule...
Gadai Ma’aruf har cikin gida yauma, ga kuma dama ta samesu domin kaw itace da girki...
Hannunta rik’eda wayar salula ta rasa wace zata kira cikinsu, shawarin wa zata d’auka cikinsu...
Lokaci guda ta yanke shawarin kiran ko wacce cikinsu don jin yanda zasuyi da Ma’aruf...
Hajiya ta soma kira ta sanar da ita abindake wakana...
Ai babu wata wata Hajiya tace tasan yanda za’ai tai amfani da wannan dama ta zuba masa guba yaci su huta, itakaw Aminiyar Sirri cewa tayi “Yanzu ke banda abinki Lami kika saka masa guba yaci kindai san babu wacce za’a kama saike, ita Haule da take tinziraki kiyi hakan ai tasan ba kamata za’ai ba tinda ba ita ta bashi abincin ba... Nidai shawari ki bari abi komai a sannu...”

Lami ta amsada “Kumafah hakane gaskiyarce Aminiyar Sirri... Zanyi yanda kikace d’ain...” Daga haka sallama sukai tana mai ci gaba da kaikomo cikin d’aki...

Nabilah dake lab’e bakin k’ofa bata jiyo komai ba sai AMINIYAR SIRRI... Nanata ta dingayi cikin zuciyarta, Aminiyar Sirri....
Cikin sauri ta fice daga sashen ta koma can k’uryar d’aki ta shiga neman layin Aunty B...
Bugu biyu a na uku Aunty B ta d’aga...
Cikeda damuwa Nabilah ke sanar da ita sabon sunan da ta jiyo daga bakin Aunty Lami Aminiyar Sirri...

Shiru Aunty B tai kaman mai nazari kana tace “Aminiyar Sirri...? Toh mai hakan yake nufi...?”

Nabilah tace “Abinda naji kenan Aunty, and ga dukkan alamu matar da take waya da ita itace Aminiyar Sirrin... Aunty could it be possible Aminiyar Sirri itace ta taimakawa Aunty Lami wajen ganin bayan d’an uwana Ma’aruf...?”

Nanma shiru Aunty B batace komai ba, saida ta d’an d’ibi wasu dak’ik’ai kana tace “Watak’ila hakan ne Nabilah...”

“Toh wacece wannan aminiyar sirrin...? I need to find out who she’s...” Ta fad’i tana mai jaddada kalamanta...

Aunty B tace “Kodai itace wacce kike ganinsu tare ma’ana Hajiyar Hafiz....”

Girgiza kai Nabilah tai tamkar Aunty B d’in na ganinta kana tace “A’a Aunty banjin itace domin kaw ita da Hajiya takan kirata nafi kyautata zaton watace daban sannan duk yanda akai su ukun sunyi tarayya wajen ganin bayan Yayana Ma’aruf.... Amma whoever she is sai na bincikota....”

Aunty ta fuzar da iska tana mai ci gaba da fad’in “Don’t forget you’ve my support, You can always count on my support... Zan taimaka maki wajen binciko Aminiyar Sirri...”

Nabilah tai mata godiya kana sukai sallama Aunty B tana mai gargad’inta kada tayi mahaifiyarta taji wannan batu domin ko shakka babu d’aga mata hankali zaiyi ya d’ago mata tsohon mik’in dake cikin zuciyarta...


*SameenaAleeyou(Mrs💖)📚



*INDA RAI*
_................DA RABO_




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




*40*





Abbah da Sameer zaune a parlorn suna cin abinci saman darduma, sosai Abbah yake kula da d’abi’unsa wanda suke matuk’ar kama da nashi musamman a lokacin da yake matashi kaman Sameer d’in, yana son tambayar Sameer wasu abubuwan amma saidai baisan ta yanda zai soma ba, baisan ta yaya zai soma jefo masa tambayoyinsa masu wuyan fasaltuwa ba, a b’angaren Sameer ma sosai yake jin abubuwa da dama gameda mutumin saidai shima baisan ta ina zai soma ba, Mummy ita kad’ai zata warware masa sark’ak’iyar da ya tsinci kansa ciki... Idan suka had’a idanu da Abbah saidai kaga ya sakar masa murmushi mai sanyin gaske a yayinda shi Sameer d’in sai ya sami kansa yana mai sadda idanu k’asa...

Sallaman da akai ne ya sanyasu maida hankulansu zuwaga k’ofar bakunansu na mai amsa sallaman ba kowa bane illa Baba Alhaji Yayan Abbah...
Abbah ya fad’ad’a murmushinsa yana mai fad’in “A’ah Yaya kaine tafe, shigo k’araso mana, bisimillah...”
Ya k’arashe yana mai nuna masa wajen zama....

Yanayin fuskar Yayan nasa ya tabbatar masa akwai wani abin a k’asa don gaba d’aya babu walwala tattareda Baba Alhaji...

Sameer ya risina ya gaidashi ya amsa sama sama, Abbah na mik’a masa hannu alamun suyi masabaha Baba Alhaji yace “Usman ina Raihanah....?”

Shiru Abbah yayi yana tunanin wacece ma Raihanah tinda ba wai Hajiya na barinta ta fita bane...
Shiko Sameer sunan sounds familiar to him, yanata tunanin ina yasan sunan...

“Tambayarka nake ina d’iyata Raihanah..? Na dawo gida Haule ta sanar dani Mamani ta d’aukota ta taho da ita nan... Ce maka akai na gaza rik’onta ne ko mai..? Mahaifiyar tamu ma da kakeji kaike rik’eda ita sabida dai tafi nuna maka soyayya ne shiyasa take zaune gidanka, ka yankawa k’annenmu filaye cikin gidanka ka kashe masu zukata duk don ace kaiga gwani a dangi koh... Toh bada d’iyata ba ni zan iya rik’on kayana sam bazan yarda kaga gazawata ba...”

Tinda ya soma magana kan Abbah ke k’asa shiko Sameer jiki a sanyaye ya mik’e yana neman had’o kalmomin da zai masu sallama dasu tinda ya lura sauraren conversations d’insu sam ba huruminsa bane....
Kaman wani munafuki haka ya fice yana k’ok’arin saita takalmansa, saidai fitowarsa kenan sukai caraf Mamani rik’eda hannu Raiha sai balbala masifa take sun nufo sashen Abbah...
Gaban Raihanah ya yanke ya fad’i ganin fuskar mutumin da bazata tab’a mance taimakonsa a gareta ba nan gabanta, shima d’in cak ya tsaya yana dubanta domin kuwa tsaf ya ganeta, dama tanada relation da Abbah, toh kodai wancan mutumin shine mahaifinta, idan bai mance ba har k’ok’arin neman mahaifinta yayi don ya sanar dashi kalan wahala da d’iyarsa ke sha hannun matarsa, idan kaw Raihanah ta dawo nan gidan k’anin mahaifinta ne hakan sai yafi masa dad’i... Ya saki murmushi shi kad’ai kafin ta sami zarafin gaishesa fit ya b’ace a wajen... Tai wani sororo da ita don Mamani kam ma ko kulada mutum batai ba, abinka da idanun girma ga uwar masifa da take faman juyewa...

“Ke shige muje nace ayita a rubuce cewa bazaki koma gaban Haule ba...” Ta k’arashe tana zungurin Raihanah da sandar hannunta, Rihanah data dawo daga duniyar tunani tai wuf ta shiga bin bayan Mamani...

Sameer na fitowa suka had’uda Mamy wacce ta fito kitchen, a karo na biyu da ya kuma had’uwa da matar wacce yakejin wani babban al’amari gameda ita, kasa d’auke idanunta daga barin dubansa tai murmushi bai gushe saman fuskarta ba, Sameer ne yai k’ok’arin saita kansa ya soma gaidata...
Mamy tai saurin katseshi da fad’in “A’a daga waje kuma k’araso ciki mana....”
Ba abin yace mata a’a ba don sosai yake tsintar kansa da jin nauyin matar...
Yana d’an sosa k’eya yake fad’in “Toh Hajiya na gode....”
Dad’i kaman yakar Mamy ta shiga doka kirawa Nabilah da Marliya...
Duk wannan abu a idanun Aunty Lami dake lab’e akayisu, cikinta ya bada wani irin k’ara kaman mai shirin sakin zawo...
Ta dafe hannaye biyu a k’irji tana fad’in “Oh na shige na shiga uku ni Lami kullum k’ara kusanci suke.....” Jiki har na rawa ta koma sashenta ta rarumi mayafi ta fice fuuu...
Nabilah dake lab’e tana duban Aunty Lami yanda take lek’en Mamy da wannan mutumi sosai abin ya bata mamaki, toh wannan d’in wayene sannan meyasa Aunty Lami ke lek’ensa.... Kiranda Mamy ke mata ya sanya batabi Aunty Lami d’in ba don ganin k’anda ta nufa daga ganin wannan mutumi da kwanaki ta ganshi parlorn Abbah, tanason sanin alak’arsa da gidansu....

***
Baba Alhaji na hango Raiha ya mik’e yana sab’a babbar riga yake fad’in “Ke shige mu tafi gida....”
Bai kai aya ba Mamani da ta k’arashe dogorowa da sandarta tace “Bazata tafi ba, nace bazata bika ba.... Ai bansan ka zama shanyayye har haka ba, bansan Haule har haka ta shanyeka ba, auho ta bika ku tafi ku sabautar da ita kaman yanda kuka sabautar da Zulfa’u koh....?”

Gaban Abbah ya yanke ya fad’i jin an ambato d’iyarsa Zulfa’u...
Saurin d’ago kai yai yana duban Mamani da Baba Alhaji kana yace “Mamani mai kike nufi... Ina Zulfa’u... Shin ba auren Hafiz take ba....?”

Lokaci guda Mamani ta saki kuka tana tattaro bakin zani take fad’in “Manu ka yafeni, ka yafeni tsanar Zulfa’u

Please Login or Register in order to submit comment