Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi daga kitchen, mik’ewa tayi saman sofa ta d’an kishingid’a had’ida lumshe idanunta, tanajin sanda Malam Sallau ya shigo da suitcase d’inta ya ajiye daga bayan parlorn yana mai fad’in “Hajiya ga jakar a nan...”

Ko zarafin amsashi Siyama bata samu ba har lokacin idanunta a lumshe suke, wasu irin tunani marassa kangado masu tada hankali su suka addabeta, yanzu idan Partner ya kasa jure rashinta kusanshi fah? Idan ya fad’a wata rayuwar fah..? Ko kuma idan yace zai k’ara aure fah... Shin waima da wasu irin mutane zaike huld’a....?” Ire iren tunanin dake zuwa zuciyarta kenan har Kubura mai aikin Ammi ta shigo parlorn Siyama bataji shigowarta ba...

Turus Kuburan tayi tana duban Siyama dake kwance saman sofa idanu a lumshe ko takalmin k’afarta bata samu zarafin cirewa ba dashike d’aure yake da belt...

Kubura ta kuma juyawa ta kalli akwati a gefe... D’an k’arasowa ta shigayi cikeda risinawa tana kiran Siyama...

“Aunty..! Aunty..!!!..” Shiru Siyama bata amsa ba...

Saida Kubura ta d’an buga kujeran kad’an tana k’ara fad’in “Aunty....”

Sai sannan Siyama ta bud’e idanunta had’ida d’an yamutsa fuska...

“Aunty lafiya kuwa...?” Kubura ta tambaya...

A kaikaice Siyama ta dubeta fuska babu walwala kana tace “Banson gulmarku ta masu aiki d’auki jakata ki haura min da ita sama d’akina...”

Kubura ta jinjina kai tana fad’in “A’a wai Aunty gani nayi kaman bakida lafiya shiyasa na tambaya....”

Gajeren tsaki Siyama tayi don ta tsani shiga sharo babu shanu irinta ma’aikatan gidan Ammi musamman Kubura, kallon data watsa mata yasa bata kuma cewa komai ba ta ciccib’i jakan tana washe hak’wara don ko babu komai zatake samun na kashewa don Siyama akwai sake hannu shiyasa duk ma’aikatan gidan ke bata girma kama daga masu gadi har ma’aikatan cikin gidan itadai barta da basarwa wanda usulin d’abi’artace miskilace ta gaske ba kasafai take shiga hark’an mutane ba shiyasa ko k’awaye basufi a k’irga ba wanda takedasu, tanada zafin rai abu k’ank’ani ke b’ata mata rai hakan yasa duk wanda yasanta yake shan maganin zama da ita... Da yawan mutane sukan d’auketa mace mai gadara da isa da ji da kai wasu kuwa kan d’auki hakan da cewa goyon data samu ne na sangarci daga gidansu... Idan kaji hayaniyar Siyama toh fah ka tabbata Khalid ne ya tab’ata shiyasa mahaifinta ya d’auki muk’ami mai girma a kampaninsa ya damk’a mata....


Ammy dake zarya cikin makeken d’akinta tana waya nan ta hangi Kubura da jaka nik’inik’i tana haurowa zata shige d’akin Siyama... A’a mamaki ya kama Ammy cikin sauri ta katse wayar da take kana ta tsare Kubura da fad’in “Ke ke yaya wannan fah...? Daga ina....?”

Kubura na haki take fad’in “Ammy Aunty Siyama ce tazo tana parlorn k’asa tana kwance, Ammy inaji dai babu lafiya ne don baki ganta ba gaskiya.....”

“Ke ya isheni bani hanya na wuce....” Ammy ta katseta sanda take sauk’owa daga bene cikin tsananin tashin hankali....

Kwance ta hangi Siyama har lokacin.... Cikin sauri Ammy ta k’arasa gareta.....


****

Kallon juna sukayi a karo na biyu kafin suka kuma tafe hannaye suna shewa irinta aminan asali, Hajiya taci gaba da juya super wax d’in dake hannunta kana tace “Ke Lami bakida kyau kin rantse sai kin mallaki tsohuwar nan...”

Aunty Lami ta kuma juya idanu kana tace “Ai idan sunsan wata basu san wata ba, nid’in nan dai da a baya aka ambata da juya mujiya merere wanere sai an dawo ana bina tako ina... Sai na zamto almiski duk yanda na shiga na bar k’amshina....”

Hajiya rik’e da hab’a take duban Aunty Lami kana suka kuma saka shewa, Hajiyar Hafiz tace ya labarin aminyar sirri....?”

A tare suka kwashe da dariya kana Aunty Lami tace “Zancen kike nema bara kiga na tashi na tafi kafin Abbah ya dawo daga kasuwa don yau zai komo d’akina gwara naje na masa shiri tinda ita wancan bataga kwanciyar hankalin ba ma ballanta ta tsaya kulada miji....” Ta k’arashe maganar tana tura zanin cikin bak’ar leda....

Hajiya ta mik’e tana gyara d’aurin zani take fad’in “Ai ni babban abinda kemin dad’i shine yanda Mamani ke matuk’ar k’aunar Hafiz sam bata ganin laifinsa idan kuwa baki mance ba a baya itace dai tak’i jinin d’ana ta d’auki son duniya ta d’aura kan Ma’aruf yaronda sam ashe ba mai zama bane k’ashinsa ya jima da daddagewa cikin k’asa....”

Aunty Lami tace “Hafiz kam ai d’an albarka ne tinda ya zage yake cimin uban yarinyar nan da kyau yanzu babu wacce ta tsayamin a wuya kaman wancan yarinya figeggiya marar ta idon nan...”

“Nabilah koh...?” Inji Hajiya dake yamutsa fuska...

“Keda kika sani, shegiyar yarinya gaba d’aya ta tsayamin a wuya tamin k’ebebe na rasa ta yanda zan b’ullo ma lamarinta.....”

Hajiya tayi k’wafa kana tace “Kar ki damu k’awata itama haka zamu samo hanyar da zamu sabautar da rayuwarta, idan Mariya taga yaranta gaba d’aya suna wahala a gidan aure itama hankalinta sam bazai kwanta ba tinda dai dama itama ba dad’in takeji ba...”

Aunty Lami ta jinjina kai kana tace “Shikenan ni zan wuce sai kinji wayata yanda muka kaya da sirkarki...”

Suka kuma tafe hannaye had’ida shewa kafin Lami ta fice....


***


Ammi na k’arasowa yanda take wayar Siyamar ta d’au ruri, tamkar wacce aka zabura haka ta mik’e ta d’au wayar tana dubawa, hannayenta har rawa suke, hotonsa da ya bayyana da sunan Partner ya sanyatayin k’urima wayar, tun jiya take neman layinsa baya shiga tun bayan da ta kira taji isarsa, ta kira Sultan ma don taji ko lafiya saidai Sultan d’in ya sanar da ita sun rabu tun da rana don shi Abuja ya wuce...

A hankali ta saita kanta kafin ta d’aga wayar....

“Partner....” Ya fad’i daga d’aya b’angaren cikin sassanyar muryarsa...

Maimakon tayi magana sai kukan da ta sake masa....

Sameer yasan hakan ka iya faruwa, cikin kwantar da hankali ya soma fad’in “Siyama what’s wrong, meke faruwa...?”

Cikin kuka take fad’in “Really Partner..? Are you seriously asking me that question...? Kasan sau nawa nayi trying layinka baya shiga, I was so worried about you, amma kai da alama baka damu kasan halin da ka barni ciki ba....” Ta k’arashe cikin tsananin b’acin rai...

A hankali ya shafi sumarsa had’ida fuzar da iska kana yace “I’m sorry... Ki daina kuka kinji, I’m at work right now, we talk later kinji... I love you....” Daga haka bai jira cewarta ba ya katse wayar...

Da tsananin mamaki take duban wayar.... Bata daina duban wayar ba take fad’in “He hangup on me....” Tayi saurin juyowa ta dubi Ammi dake zaune gefenta ta mata k’uri kana tace “Ammi Sameer ya bar sona, kin gani fah kashe wayar yayi, aikinsa yafi mahimmanci a wajensa fiyedani....”

Rungumota Ammi tayi kana tace “Siyama don Allah ki kwantar da hankalinki ni irin wannan soyayya da kikewa Sameer har tsoro yake bani, shifa namiji ba’a nuna masa soyayya irin haka sabida b’acin rana, nasha fad’a miki ki koyi son abu baya baya irin wannan ne randa ya bijiro miki da halinsu na maza sai ki shiga damuwa koma ki jawa kanki wani cutan...”

Shiru tayi tana duban Ammi zuciyarta na gaya mata wani abu, kardai maganganun Ammi su tabbata watarana Sameer ya rabu da ita.... Take taji gabanta yayi mugun fad’uwa lallai kuwa zata iya rasa rayuwarta idan irin wannan ranar tazo....

Duban Ammi ta kumayi kana tace “Ammi kina ganin Sameer zai iya rabuwa dani...?”

Ammi ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Bance zai rabu dake ba Siyama amma ki sani ita rayuwar nan komai ka iya faruwa, ba lallaine rayuwarmu ta tafi yanda muka tsara muke kuma so ba, wasu lokutan dole a samu sauyin lamari, kuma dole musa a ranmu komai ka iya faruwa ballanta namiji da sam baida tabbas, kina ganin abinda Babanku ya min yaje yayi aurensa a can wata k’asar ba tareda sanina ba, ba don zuwan social media ba k’ilada har yanzu bamusan nada wata matar ba... Kuma yanzu da haihuwa ta shiga tsakaninsu haka zaku tashi bakusan kunada wasu ‘yan uwa ba... Ke ya kamata kifi kowa d’aukan darasi tinda kece mutum ta farko da kika gano Daddynku has another wife....”

Tsoro da fargaba suka kuma kama Siyama, wannan dalili dama shiyasa ta zamto very paranoid, duk yanda mijinta yake tsoro da damuwar abunda ka iya zuwa yazo shike damunta, damuwarta kar Mijinta ya mata irin abinda mahaifinta yayiwa mahaifiyarta, so tari takan yarda Sameer na tsananin k’aunarta amma idan ta tuna yanda suka taso suka tadda iyayensu cikeda k’aunar juna sam bazakayi tunanin Daddy zai iya k’ara aure ba tareda sanin Ammi ba, wannan dalili yasa wani sa’ain take samun shakku dukda irin kula da soyayya da Sameer ke nuna mata, don bazata mance ba lokacin data gano Daddy nada wata matar ta hanyar facebook har saida tafi mahaifiyarta shiga tashin hankali, da k’yar ta yafewa magaifin nata don da ta d’au alwashin barin gidansa ne na har abada, shi kuwa a duniya yaransa sune rayuwarsa....

Da wannan tunani da maganganun Ammi yasa jikin Siyama yin matuk’ar sanyi, k’ok’arin danne zuciyarta tayi had’ida kashe wayar gaba d’aya don karma ta kasa jurewa ta kuma neman layin Sameer....


****


Tun daga waje yayi sallamada muk’arabban nasa don ba k’aramin gajjiya yayi ba burinsa ya shiga gida ya huta, yinin yau ranar sunyisa ne suna yawon campaign k’auyuka k’auyuka....

Baiyi mamakin ganinsu zube a parlor ba ko wacce ta rungume teddy bear d’inta tana bacci, k’aramar mai kimanin shekaru uku kwance cinyar ‘yar matashiyar mai kimanin shekaru shida su duka suna bacci, shi kuwa babban mai kimanin shekaru goma yana can gefe da alama shima gajjiya da buga game d’in yayi har bacci yayi awon gaba dashi....

A hankali yasoma takowa cikin parlorn had’ida k’urawa yaran nasa idanu cikeda tsananin tausayi da b’acin rai, har abada baijin Muhibbah zata samu lokacinsa dana yaransu, a baya yakan sakama ransa cewa INDA RAI da rabon ta daina a gaba amma ya lura hakan abune mai matuk’ar wahala, wannan shine rayuwar da Muhibbah ta girma akai ta kuma saba, so tari a baya sukan shirya tafiya k’asashe da ‘yan uwanta da iyayenta ba tareda saninsa ba wasu lokutan ma saidai yaga ana processing visa da sunan zasuyi tafiya Dad ya shirya tafiya zuwa k’asa kaza da yaransa gaba d’aya, bai isa kuma ya nuna k’in amincewarsa ba ko rashin yardarsa sai nasa mahaifin yayi fushi dashi, dashike Muhimma d’iyace ga aminin mahaifinsa, tun a lokutan baya kenan kafin mahaifinsa ya rasu, sannan lokacin da mahaifinsa ya kusa rasuwa saida ya kuma masa kashedi akan ya rik’e Muhibba ko mai zata masa idan har yana son gamawa da duniya lafiya wannan dalili yasa duk wani abunda Muhibbah zatayi yake k’ok’arin kawarda kai, yakai ya kawo yanzu bada ‘yan uwanta take yawon k’asashen dataga dama ba da k’awayenta gogaggun ‘yan bariki take, dama sam zaman gidan kam batayi rayuwar yaran da komai Nannies ke masu, a baya kafin commitments su masa yawa shi da kansa yake kulada yaransa idan ta tafi gantalinta....

K’aramar ya soma d’agawa da niyyar kaisu makwancinsu nan ko ya hangi busassun hawaye kwance a fuskarta, ta kuwa yi saurin k’ank’ameshi tana ambaton Daddy alamun da kukan tayi bacci, tsam ya rungumeta had’ida kwantar da ita saman kafad’unsa yana jijjjigata yana lallashi alamun yanaso ta koma baccin kaman daga sama yaji k’aran takalminta mai tsini waya manne a kunne tana aikin waya da k’awaye kaman yanda ta saba, suna kuma zuzutata da haukatata da sunan First Lady.....



SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_





*11*




Yana jin yanda ta nufi upstairs tana rangad’a kirawa ma’aikatan gidan, sam batayi tsammanin samunshi a sashenta ba dukda cewa taga motocinsa waje ga securities da suka k’aru hakan ya tabbatar mata yana gida....

Ta cikin k’ofar glass da ya raba staircase da cikin parlorn ta hango bayansa rungume da k’aramar ‘yarta mai suna Najma, saida ta juya idanunta kafin ta soma takowa ta shigo cikin parlorn tana fad’in “Ya akayi Murja ta barsu sukayi bacci a parlor, Gosh! I really don’t know what’s wrong with her, saida na fad’a mata ta tabbata ta kaisu d’akunansu don mai zata barsu zube a nan...?”

Tunda ta soma magana k’ala bai ce mata ba har Murja ta k’araso a guje cikeda d’imauta ganin irin muguwar kallo da uwar gijiyar tata ke aika mata....

Aiko kafin ta samu zarafin magana tun daga nesa Muhibbah ta tsareta da fad’in “Murja what’s meaning of all this, me nace miki kafin na fita... Ta yaya zaki bar min yara zube a nan kaman sun rasa gatansu, kinacan kin sake bakida hanci kina shegen kallon nan naki koh...?”

Cikin sark’ewar murya take fad’in “Haj... Hajiya kiyi hak’uri dama Irfaan ne yace zaiyi game bazai kwanta ba shine k’annen ke kuka saidai su zauna dashi shiyasa.....”

Bata kai aya ba Muhibbah ta kuma darara mata tsawa...

“Ni dallah rufe min baki before I lose my patience completely...”

Cikin kid’ima ta kuma nufo mahaifin yaran zata karb’i k’aramar jiki na rawa....

Girgiza mata kai yayi kana yace “Jeki abunki...” Ya fad’i a tak’aice

Cikin risinawa ta kuma basu hak’uri da alk’awarin hakan bazai kuma faruwa ba kana ta fice....

Kafesa da idanu Muhibbah tayi ganin kota kanta baibi ba ya nufi upstairs da d’iyarsa....

Cak ya tsaya da tafiyar nasa sanda ya sinkayo muryarta tana fad’in “Meye ma’anar abunda kayi kenan... Yaya zan baiwa mai aikina umarni kace ta barshi...? Kuma dai kasan ba iya d’aukan yaran nan zanyi ba, don babu wanda zan iya d’agawa cikinsu...”! Ta k’arashe tana jifa da jakkanta saman kujera.....

Baice komai ba haka nan bai juyo ya dubeta ba yaci gaba da tafiyarsa... Haka ya dinga sintirin kai yaran d’akunan baccinsu had’ida tofa masu azkar na bacci kana ya sauk’o don tafiya sashensa, har lokacin Muhibbah na make saman kujera tana faman ci gaba da waya...

Baice mata ci kanki ba ya sunkuya ya d’auki agogonsa da links dinsa saman center table....

Tab’e baki tayi sanda ya fice kana ta mik’e ta nufi d’akinta don shirin bacci....

Kaman ko yaushe saida tayi wanka ta shafa mayukan k’amshinta masu tafiya da hankalin mijinta duk kalan fushin da yake ciki, tayi wasu ‘yan kimtse kimtsen da take kafin bacci kana ta nufi sashen mijin nata....

Bata sameshi cikin d’akin ba hakan ya tabbatar mata cewa band’aki yake don tana iya jiyo zuban ruwa daga yanda take kwance saman gadonsa....

Sam bai kula da ita ba don hankalinsa naga warware hannun jallabiyar dake jikinsa da alama alwala ya d’auro...

Kallo d’aya ya mata yaji zuciyarsa na masa tsananin k’una, wato Muhibbah tasan lagonsa tasan shi wane iri mutum ne, tunda ba wata matar yakedashi ba babu yanda za’ayi ya iya k’aurace mata shiyasa take abunda taga dama don tasan duk fushin da zaiyi zai dawo gareta...

Bata ankaraba taji dakakkiyar muryarsa na fad’in “Tashi ki ficemin a d’aki, kuma kar na kuma ganinki cikin d’akin nan kinajina koh....”

Da tsananin mamaki take dubansa kana tace “Ban gane ba, ni kake kora....?”

“Do I need to repeat myself... Ki tashi ki fice nace..!!” Wannan karon cikin tsananin daka tsawa yayi maganar wanda saida ya figita Muhibbah ta mik’e babu shiri....

“MA’ARUF ni kake kora daga d’akinka, ka mance abinda Baba yace maka akaina...?”

A zuciye yayo kanta yana k’ok’arin kai maita mari sabida tuno tarin kuncin rayuwar data jefasa ciki dukda kyakkyawan alak’arsa da jama’a, bai marenta ba sai sauk’e hannunsa da yayi tamkar ya tuna wani abun kana yace “Get out....”

Kallo ta bisa dashi don bata tab’a ganinsa cikin tsananin b’acin rai irinta yau ba...

Sa kai tayi zata shige tana fad’in “Fine zan fice maka a d’aki amma ka sani nima duk randa ka kwaso buk’atarka ka kawo gareni zan rama, kuma idan akan yara ne ai sunada Nanny mai kuladasu sannan yawan fita da nake ai gani nayi campaign nake maka....”

Bata kai aya ba taji ya damk’ota ya dawo da ita cikin d’akin yana mai ci gaba da huci....

Idanuwansa sun kad’a sunyi jazir yake fad’in “Idan kina tunanin ni Ma’aruf zan nemi wani abu you’re very much mistaken, albarkacin Abbah kike zaune a gidan nan, sannan daga rana mai kaman ta yau ki sani bani buk’atar komai daga gareki, idan kinga dama yawonki ya kaiki har birnin sin babu matsalata ballantana damuwata, gameda campaign kuma I did not ask for your help nor your support, in fact I don’t need any of these from you.... Now, get out.... Get out I said....!”

Ya k’arashe yana nuna mata tangamemen k’ofar d’akin dake bud’e...

Da tsananin mamaki take dubansa kafin tasa kai ta fice zuciyarta na tsananin mata zogi, tana tafe tana mamakin itace yau Ma’aruf Mutallab zai wulak’anta, harda cewa baya buk’atar komai daga gareta...? Tabbas badon tsananin soyayyar da take masa ba da tuni tayi tafiyarta ta bar masa gidansa taji dad’in yawonta da kyau ba tareda fargaba ko tunanin miji ba, tana jin yanda Ma’aruf ya rufe k’ofar d’akin da k’arfin gaske...

Tana isa sashenta ta fad’a d’aki ta d’au waya had’ida kiran aminiyarta Shamzy tana sanar da ita yanda sukayi da Ma’aruf....

***


Har wajajen k’arfe shad’ayan dare baiyi bacci ba, yana nan zaune a parlor yana ci gaba da dialing layinta amma baya shiga...

Shamsu dake tasye jikin k’aramar fridge dake gefen parlorn kallo yabisa dashi jin yanata faman nanata abu guda....

“Com’n Partner.... Pick up your phone....”

K’arasowa Shamsu yayi had’ida zama gefensa ya d’auki remote ya canza daga tashan labaru zuwa na movie kana ya maido da dubansa ga abokin nasa yace “Doc are you sure you’re alright...?”

Fuzar da iska Sameer yayi kana yace “Bazaka ganeba abokina, Siyama has that nasty temper you know, abu k’ank’ani zai b’ata mata rai sannan sam bazatayiwa mutum uzuri ba.... Na tabbata fushi tayi, She is not answering any of my calls... And I miss her... so terribly....”

Murmushi Shamsu yayi kana yace “Then give her space, ka barta ta huce idan Allah ya kaimu gobe you call her again..”

Jinjina kai Sameer yayi kana yace “Wai yaushe zakayi aure ne...?”

Tak’aitaccen murmushi Shamsu yayi kana ya kurb’i ruwa yace “Lokaci muke jira Sameer, May be k’arshen shekara....”

Sameer ya jinjina kai kana yace “Toh Allah sa gaskiyar kenan wannan karon...”

Shamsu ya kuma darawa had’ida mik’ewa yana fad’in “Zancen kakeso Doctor....”

Sameer ya jefa masa pillow yana fad’in “A daina yaudaran yaran mutane haka nan ayi k’ok’ari a nutsu waje guda, first thing tomorrow morning kafin na fice Surgery zan samu Mama da batun, zaka sani ne mayaudarin banza kawai...”

Banda dariya Shamsu baya komai har ya shige d’aki, jimawa kad’an Sameer ya mik’e shima ya kashe kayan kallon ya nufi d’akin da aka masa masauk’i gefe da na abokinsa Shamsuddeen.....

Misalin k’arfe 8:am suka fito a tare daga sashen Mama zasu wuce aiki, Sameer sai dariyar sille Shamsu da Mama tayi yake, dole ne itama taso taga tilon d’anta ya ajiye Iyali amma sam aure baya gaban Shamsu... A haka har suka shige motocinsu Shamsu na shak’e da Sameer ganin yanda ya biyewa Mama suka masa tas...

Kallo ya dinga bin ginin unguwar dashi yanajin wani sanyi cikin zuciyarsa, baisan dalilin jin hakan ba amma can k’asan zuciyarsa ji yake tamkar ya tab’a zuwa wajen, ko wucewa ko wani abu mai kama da haka, gashi dai unguwar mai yawan jama’a ne da hayaniya ba kaman unguwannin da ya taso cikinsu ba tsawon rayuwarsa, dukda hayaniya da yawan jama’a dake cikeda wannan unguwa sai yaji dad’in unguwar da kwanciyar hankali fiyeda tunaninsa, da k’yar ya karb’i tayin Shamsu ya sauk’a gidansu da niyyan yin kwana biyu kafin ya samu nasa apartment d’in don da hotel ya nufa amma Shamsu fir ya hanasa a dole yazo gidansu ya sauk’a...

Shamsu abokin Sameer ne wanda sukayi makaranta tare a can k’asar India, a lokacin baida amini sai Shamsu harta gidan da suka kama GIDA GUDA ne, iyayen Shamsu sunsan Sameer haka iyayen Sameer sunsan Shamsu, hasalima Shamsu idan ya tafi Kaduna gidansu Sameer yake sauk’a shiyasa wannan karon Shamsun ma ya dage sai Sameer d’in ya sauk’a nasu gidan....

Haka Sameer yayita bin unguwar da kallo murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarsa yanajin natsuwa sosai cikin zuciyarsa.....

***

Tana zaune gefensa yana karyawa cikin shirinsa na tafiya kasuwa sai faman zuba santi yake tana jin dad’i da sanyi har cikin zuciyarta, gradually burinta suna kan cika.... Sai faman murmusawa take tana kwarkwasa...

Abbah ya kuma tand’e hannunsa kana yace “Zuba min kunun rabin kofi, Aunty Lami tayi yanda yace Abbah ya shiga kurb’an kununsa yana lumshe idanu...

Kaman daga sama suka jiyo sallaman Mamani rungume da turmin zanin da Aunty Lami ta kawo mata daren jiya, sai faman wage baki take tana ci gaba da k’waza sallama dukda cewa sun amsa mata sallaman nata....

Tuni Aunty Lami ta shiga murmusawa tana kuma sadda kai k’asa had’ida gaida Mamani...

Cikin sakewar fuska Mamani ke amsata tana fad’in “Lafiya lou sirkar arziki, nazo nuna ma d’ana abin arzikin da akewa uwarsa ya shaida...”

Aunty Lami ta kuma murmusawa tana fad’in “Haba Mamani wannan ai ba komai bane ni uwa na d’aukeki.....”

Mamani tana amsa gaisuwar Abbah take fad’in “Kaji koh, kaji d’iyar albarka abinda take fad’i, uwa ta d’aukeni....”

Abbah da tun bayan b’acewar d’ansa Ma’aruf da k’yar ake ganin murmushinsa sai gashi nan yana murmusawa a hankali kana yace “Lami kawo mata abincin...”

Kafin Aunty Lami ta basa amsa Mamani ta katse sa da fad’in “Wa ai nikam ‘yar gata ce don ina tunanin kafin naka ya iso gareka nawa ya riga isa gareni...”

Aunty Lami ta kuma sakin murmushi tana fad’in “Dole mu kula dake sosai Mamani ko don mu samu albarka rayuwarmu tayi kyau....”

Haba nan fah Mamani ta kuma washe baki cikeda jin dad’i....

Mamy dake tsaye jikin k’ofar kasa shigowa tayi sabida tsananin sanyi da gwiwoyinta suka mata, take taji hawaye na neman ciko idanunta, a hankali tasa kai ta juya had’ida komawa d’akinta don ji tayi sam bazata iya shiga ba, tausayin kanta ne ya kamata sanda ta zauna saman gado had’ida rapka uban tagumi da duka hannayenta biyu hawaye na gangarowa saman k’uncinta.....



SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*12*







Tsaye take tana linke kayan wanki da bata jimada shigowa dasu ba, sam duba wayar mijinta ba d’abi’arta bace, hasalima sai wayar ta k’araci ringing d’inta koda baya kusa bazata d’aga ba sannan bazata duba ba har sai yazo da kansa ya d’aga ko kuma ya samu missed calls, wannan d’abi’ace da mahaifiyarta ta horasda ita domin samun zaman lafiya mai d’aurewa a gidan aurenta....

Sau biyu kenan ana kira batakai dubanta ga wayar ba har ta k’araci ringing d’inta dukda cewa wayar a gefen kayan da take linkewa yake, jin ana sake kira yasata kai dubanta ga k’ofar band’akin ko zai fito amma shiru saima k’aran zuban shower da take iya jiyowa ga uban sauti da ya k’ure a d’aya wayar tasa domin d’abi’arsa ce tun yana matashi idan zai shiga band’aki sai ya k’ure sautin wak’a har yayi aure bai daina, tayi tayi ta hanasa wannan d’abi’a amma abu yaci tura k’arashe ta yanke shawarin tayasa da addu’a...

Tunaninta guda kodai Hajiya ce mai kira, k’ilama zatace azo a d’auki Kausar ce, take taji farin ciki ya mamaye zuciyarta annashuwa da annuri sun cika fuskarta sakamakon tuno d’iyarta da tayi....

Cikin sauri tayi jifa da rigar da take linkewa ta suri wayar tana duban screen d’in, dukda lamba ce kawai babu suna hakan bai hanata tunanin k’ila d’iyarta bace, jiki har na rawa Zulfah ta d’aga wayar ta k’ara a kunnenta ba tareda tace komai ba ga k’irjinta dake faman lugude...

Daga d’aya b’angaren cikin tsananin fad’a Sawwama ke fad’in “Dole kaki d’aga wayata munafukin Allah ta’ala, shine zakace min babu komai tsakaninka da Zabba’u toh yau k’wai ya fashe har hoton d’akin da kuke watsewa a hotel an nuna min, wllhi wllhi Hafiz idan kana tunanin zaka iya fooling wannan shashashar matar taka toh ni baka isa ba wllhi sai na danna maku rashin mutunci daga kai har Zabba’un zaka zo ne ka sameni....”

Daga haka katse wayar tayi cikin tsananin b’acin rai da huci...

Zulfah dake rik’eda wayar tamkar gunki ko motsawa ta kasayi, maganganun Sawwama ke ci gaba da yawo cikin kwanyarta, ta kasa motsawa haka nan ta kasa ijiye wayar har lokacin wayar na mak’ale a kunnenta...

A haka Hafiz ya fito daga bayi ya hangeta rik’eda wayarsa tamkar wacce aka dasa, take zuciyarsa ta shiga masa zafi domin idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa shine a d’aga masa wayarsa....

Tsawa ya daka mata daga yanda take tsaye amma ko gizau batayi ba saima dubansa da takeyi da idanunta da suka kad’a sukayi jazir har lokacin tana nan tsaye, da k’arfin gaske ya fuzge wayarsa a dai dai lokacinda hawaye mai d’umi ya sauk’a saman k’uncinta....

Bai daina huci ba ya shiga duba kiranda ta

Please Login or Register in order to submit comment