Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa, d’ago murtuk’ekk’en fuskar da babu alamun annuri cikinta yayi kana yace “Ubanwa yace ki amsa min waya....?!”

Bata amsa shi ba haka nan bata d’ago idanu ta dubeshi ba.,,,

Ya kuma daka mata tsawa “Nace da izinin ubanwa kika d’aga min waya...? Yaushema kika soma tab’a min wayata a gidan nan...?”

Shiru bata bashi amsa ba...

“Ba magana nake miki ba..!!” Ya kuma daka mata tsawa...

Saida tasa tafukan hannayenta ta share hawaye suka sauk’o fuskarta kana tayi k’ok’arin saita kanta tace “Kayi hak’uri....” A tak’aice....

Huci kawai yake yana dubanta kana yayi k’wafa yaci gaba da fad’in “Sai kinyi abu kicewa mutum yayi hak’uri bayan ni hak’urin zama dake nake, an lik’amin ke ana tausana ana bani hak’urin ci gaba da zama dake matar da babu wani alkhairi a tattaredake face sharri.. Wllhi kinji na rantse zan maki kashedi na k’arshe duk ranar da aka kuma kirata kika d’aga sai na karyaki kafin na maidake gidan iyayenki su baki tarbiya da kyau, duk kuma abinda kikaji daga wayata ke kika jiyowa kanki don babu ubanda ya aikeki d’agawa... Jaka mai farar k’afa....”

Yana gama yab’a mata munan kalamai yayi shirinsa abinsa ya fice yana neman layin Sawwama da tak’i d’aga kiransa....

Can k’uryar d’aki Zulfah ta rakub’e idnunta na mata wani irin barkono don kukan ma nemansa tayi ta rasa, wannan shine mijin da mahaifinta ya zab’ar mata zama dashi har yake ikirarin idan tayi abunda aka sakota babu ita babu shi sannan kada ta dawo masa gida ta nemi wani uban ba shi ba, ita kuma kalan tata k’addarar kenan, haka Allah yaso ya jarabceta, inama ace Hafiz ya tsaya a zagi da wulak’anci kawai, inama ace aure ya k’ara ba bin matan titi ba, shin wannan shine wanda iyayenta suka zab’ar mata tayi rayuwar sunnah dashi..? Wannan shine uban ‘ya’yanta da zasu tashi suyi alfahari dashi su nunashi suce ga mahaifinsu...? Shin idan iyayenta sun zab’ar mata wannan mutumin ita tayi adalci wa ‘ya’yan da zata haifa kenan....? Take wasu hawaye masu tsananin rad’ad’i taji suna gangaro mata... Ta jima tak’ure a wajen tanayin mai isarta kafin ta mik’e ta nufi band’aki ta d’auro alwala ta shiga mik’a kukanta ga Ubangiji wanda batada gatan da yafi Shi.....

***

Tun bayan shigowarta office d’in tayi amai ak’alla sau uku kenan, harta coffee d’in da sakatariyarta ta kawo mata hamamin kawai saida ya sata k’waza amai, gaba d’aya ta zama pale and weak, batajin kuzari sam a tattareda ita ga tashin zuciya da ya addabeta, a halin yanzu bata buk’atan komai face hutu saidai zamanta a office d’in ya fiye mata don bataso Ammy ta fahimci halin da take ciki idan har abinda take zargi ya tabbata....

Wani aman ne yazo mata ta mik’e a guje ta kuma fad’awa bathroom tana kumayi... Tamkar zata amayar harda ‘yan hanjinta haka take nishi....

Da k’yar da dafe bango ta fito daga bathroom d’in yanda ta tadda aminiyarta k’wara d’aya tak a duniya zaune saman kujera mai kallon nata damuwa kwance saman fuskarta alamun taji yanda take k’waza aman....

Kallo guda Siyama tayiwa Laila ta d’auke kai kafin ta isa k’aramar fridge d’in dake a cikin office d’in ta d’auko chocolate tana afawa a bakinta ko zata sami sauk’in tashin zuciyar da ya addabeta....

Zama tayi saman kujerarta ta d’an kishingid’a had’ida lumshe idanu tana mai maida numfashi a hankali....

Kaman daga sama ta tsinkayo muryar Laila tana fad’in “Siyama wai bazakije asibiti ba kina zaune da ciwo, ki duba ki gani yau d’aya yanda kika lalace....

Gyara zamanta ta d’anyi kana tace “Laila bazaki gane ba, ni na rigada nasan abinda ke damuna amma saidai idan shid’in ne I’m not ready yet, Wllhi ban shirya zama uwa ba, ban shirya d’aukan responsibilities ba Laila not now....”

K’uri Laila ta mata kana tace “Tirk’ashi, toh amma kema kinyi kuskure da kika bari kika d’auki ciki baki shirya ba...”

Siyama ta jinjina kai tace “I know Laila, wllhi na sani shiyasa ma na kiraki don bansan yaya zanyi ba sauk’ina d’aya Sameer baya nan balle ya fahimci wani abu...”

Laila ta tab’e baki kad’an kana tace “Toh yanzu da kika riga kika d’auki cikin me kike so ayi, nidai a nawa ganin kawai ki hak’uri ki haife abinki tinda dai dama bamu isa muce komai sai mun shirya ma zuwansa ba, just take the risks ki haifa kawai....”

Banda harara Siyama bata aika mata komai, gajeren tsaki tayi kana tace “You’re not helping... Idan na haihu yanzu komai na rayuwata canzawa zatayi, harta d’anda na haifah can come between us nida Partner, maybe ma yafi son d’an sama dani sannan zan iya rasa attention d’in mijina gaba d’aya... Bama wannan ba kawai I’m not ready to become a mother......”

Laila ta jinjina kai kana tace “Tun farko you shouldn’t be so careless, da ace kina taking precautions da ba’azo nan ba... Amma yanzu shawari d’aya ce idan har bakison haife cikin nan muje ayi flushing d’insa and start taking precautions kin fahimta...”

Siyama ta jinjina kai a hankali kana tace “Then it has to be today, like right now don banso na koma gida a halinda nake ciki....”

Laila ta jinina kai kafin Siyama ta mik’e ta rufe office d’in sukayi ficewarsu...

Suna tafe a mota take ganin sak’on shi na shigowa, a hankali ta saki murmushi kana ta furta “I’m sorry Partner.... I love you too...”

Da gefen ido Laila ke dubanta had’da tab’e baki, a haka suka karyi kwanan asibitin.....

Siyama na hawaye ga k’irjinta dake bugawa haka ta shiga d’akin operation d’in nan fuskar Sameer na mata gizo cikin zuciyarta da k’wayan idanunta...

***

Nabilah da Aunty B sukayi jigum jigum suna duban Zulfah da tun zuwansu a haka take ta kuma kasa sanar dasu meke damunta...

Nabila ta yab’e baki tace “Aunty wllhi karma ki tambaya wannan mijin nata da danginsa sun k’unsa mata wani abin ne....”

Zulfah ta aikawa Nabila harara kana ta dubi Aunty B dake dubanta a yagalgale kana tace “Aunty karki biye na wannan yarinyar ni wllhi babu komai kewar Kausar ne kawai ya addabeni...”

Aunty B ta jinjina kai tace “Ehhh naga alama ai, kewar d’iyarki shiyasa fuskarki duk ta kumbura, idan kewar d’iyarkice karki damu don yau zata dawo gareki... Nabilah tashi muje...” Aunty B ta k’arashe tana sab’a mayafi...

Nabila kaman akan k’aya take tuni ta mik’e tanaji tamkar sallah...

Zulfah tayi saurin shan gabansu tana fad’in “Aunty don Allah ku barta kawai ai idan ta gama hutun za’a dawo da ita...”

Idan gyalen Aunty B ya amsa itama zata amsa ko kula Zulfa’u batayi ba ta fizgo hannun Nabila suka fice Nabilar na kuma ingizata....


Dafe kai kurum Zulfah tayi tana ambaton Allah don tasan yau sai yanda ta kaya tsakanin su Nabilah da Hajiya da yaranta...



SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_




*13*






Cikin sauri Zulfah ta koma d’aki ta zura hijab ta fice bakin layi sauri sauri tana neman adaidaita.....

***

Raihana suka tadda tsakar gidan goyeda Kausar tana dakar d’anyar kub’iyar miyan dare ga k’amshi daddawa dake faman tashi alamun ta d’aura sanwa tuni....

Baki har kunne ta k’araso ta rungume Nabilah tana masu sannu da zuwa don ba barinta ake taje gidajen Baffahnin nata ba balle taga ‘yan uwan nata....

Nabilah sai faman binta da kallo take yanda duk ta zagwanye ta wani lalace ba kaman yanda ta ganta kwanan baya ba kafin a masu hutun makaranta don makaranta d’aya Raihana da Marliya autar Mamy suke hasalima ajinsu guda ga islamiya ma anyi hutu duk kad’aici ya isheta, Kausar ce mai d’ibe mata kewa don d’an zaman da yarinyar tayi a gidan har sun saba....

“Addah Nabilah Ina Marliya wato tinda akayi hutu ko lek’owa ta dainayi....”

Nabilah dai dubanta kawai take cikeda mamakin wai dama Raihana ke abincin gidan Baba Alhaji lallai Hajiya ta cika azzaluma...

“Raiha kece mai abincin...?”

Nabilah ta tambaya tana dafe da Raihanar...

Murmushin yak’e Raihana tayi kana ta jinjina kai lokaci guda tana mai jijjiga Kausar dake bayanta...

“Toh ina sauran gardayen gidan kike girki ke kad’ai...?”

Raihanah ta d’an juya a tsorace ta hangi k’ofar parlorn Hajiya kana tace “Aunty Sahariyya tana d’aki tana bacci Najah kuma sun fita ina tsammanin ta raka Hajiya unguwa ne.... Amma ai na saba Addah Nabilah kullum ni nakeyi...” Tayi maganar tana mai murmushi mai cikeda ban tausayi...

Dafata Aunty B tayi kana tace “Karki damu yarinya idan sunyi tunanin cutarki suke k’wararki suke sunyi kuskure domin kuwa kece dai kikaci ribar zama dasu duk yanda kikaje a rayuwa babu yanda bazaki iya zama ba don haka kece kikaci ribar zamada Hajiya kinji koh...”

A hankali Raihanah ke jinjina kai tana shafa hannayenta da tuni sunyi kanta sabida tsananin tuk’a tuwo mai tarin yawa da ake aikawa kasuwa da sauran aikace aikace da suka girmi shekarunta....

Nabilah ta dubi Aunty suna jinjina mugunta irinta Hajiyar Hafiz kana tace “Aunty sauk’i abin Raiha na nan kuma na tabbata tana kulada Kausar amma da wa yasan yanda zasu ballagazantar da yarinyar nan don bawai imani ne dasu ba...”

Aunty tace “Sauk’ota mu ganta...”

Babu musu Raihana ta soma kiciniyar sauk’e Kausar take ta soma rusa kuka alamun baccin tsoro tayi....

Sahariyya da ta sinkayo kukan nata tamkar a mafarki uban tsuka ta buga kana ta yaye labulen window tana fad’in “Ke Raiha kukan uban mai kuma yarinyar nan keyi....?”

Cak ta tsaya da kalaman nata tana kuma k’anne idanunta masu cikeda bacci tana hango fuskokin Nabila da Aunty B dake faman danna mata mummunar kallo....

“Ke Raiha su waye wad’annan tsaye sunama mutane kallon raini...?”

Kafin Raihana ta bata amsa ta sinkayo muryar Aunty B mai cikeda charisma tana fad’in “Uwarki ne... Tambad’edd’iya marar kunya...”

Kambala’in chan.... Sahariyya ta ambata cikin zuciyarta, lallai zata shayar da matar nan mamaki don ta lura kan matar hayak’i....

A fujajan ta gyara d’aurin k’irjinta ta nufo waje don dama d’abi’arta kenan zama da d’aurin k’irji musamman lokacin zafi....


“Wllhi wllhi babu matar da ta isa ta shigo har cikin gidan ubana ta zagi uwata... Wllhi kinyi kad’an fitsararrun yaranki ma sunyi kad’an...!!”

Kafin Sahariyya takai aya Nabilah ta katsetsada fad’in “Fitsara har ya wuce wacce aka baku ita a matsayin tarbiya ai ya b’aci.... Wllhi kikayi gigin zagin Aunty gabana zan shayar dake mamakin da baki tab’a shansa ba rayuwarki gaba d’aya....!”

Sahariyya ta daka tsalle tana tafe hannaye had’ida kururuwa tana mai gyara d’aurin k’irjinta, lokaci guda take furta “Lallai Nabilah kin rik’a ni kike zagi kanki tsaye don ubanki tamkar wata sa’arki ce ni...”

“Badai ubana ba wllhi yafi k’arfin ki zagesa dukda kuskuren da ta tafka ya d’auki d’iya mai daraja sukutum ya baiwa wannan lusarin Yayan naku....”

Haba nan fah Sahariyya tayo kan Nabilah tana huci tuni Aunty B ta tsare tsakaninsu suna gogan k’irji itada Sahariyya take fad’in “Kika kuskura kika tab’a d’iyata zakiyi kwanan guardroom billahillazi.... Bari kiji na fad’a miki ba wajenki nazo ba don ke ba sa’ar yita bace wajen uwarki nazo idan kuma ban sameta ba zan baki sak’o ki bata kuma ki tabbata sak’ona ya isa gareta k’aramar marar kunya....” Ta k’arashe tana mai hankad’e Sahariyya da tuni ta zube k’asa....

Tsoro da firgici suka cika Raihana tuni ta rungume Kausar suka rakub’e gefe guda....

Yunk’urin da Sahariyya tayo zata tashi sallama da karauniyar su Hajiya ya gauraye gidan, shigowarsu da kad’an Zulfah ma ta shigo a birkice....

Haba nan fah Sahariyya ta shiga runtuma kururuwa tana fad’in “Wayyo Hajiya wayyo Hajiyata taron dangi sukamin, wayyo k’ashin bayana wayyo k’afata....”

Haba ai kankace mai Hajiya tayi jifa da k’ullin k’auri data samo a unguwa tayo kan Aunty B gadan gadan Najah kuwa tayi kan ‘yar uwarta Sahariyya tana taimaka mata, tuni Zulfah da Nabilah suka tare Auntyn su dukan da Hajiya ta kawo ya sauk’a kan Zulfah...

Kausar da taga an kaiwa mahaifiyarta jibga da saida ya kusan aikata k’asa wani irin kuka ta cilla mai tsananin k’aran gaske... A tamanin Raihanah ta fice da ita daga gidan a guje sam batasan sun iso bakin kwalta ba...


Gaba d’aya hankalinsa naga wayarsa ko zata kira, driving yake yana duban wayar alamun yana jiran kiranta amma shiru, k’iris ya rage baibi kan budurwar dake rungume da k’aramar yarinya ba... Wani irin birki Sameer ya danna lokaci guda had’ida kifa kansa yana mai ambato Allah....

Cikeda fargaban abinda ka iya faruwa ya d’ago fuskansa yana duban gaban motar nasa, ganin bai gansu ba yasa shi saurin bud’e marfin motar ya fito yana lek’en ina suka shige wani lungun suka shige.... Komai ya faru in a flash, tabbas yasan ya kusan buge mutane guda biyu amma ga tsananin mamakinsa bai gansu ba kuma baiga wani gidan suka shige ba bai kumaga wani lungun suka shige ba....

Tsananin horn da ake masa daga bayansa ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi....

Cikin tsananin huci Hafiz ke d’ago hannu yana fad’in “Dallah Malam ka wani zo ka tare hanya mutane zasu wuce... Sai kuzo da manyan motocinku na k’arya kuna k’ababawa mutane a kwalta....”

Tunda ya soma magan Sameer ke dubansa yanajin wani abin na tsargar masa, bai iya amsa shi ba sai bud’e mota da yayi ya shige had’ida tada motar ya kaucewa Hafiz ya shige bai daina bambami yana fad’in titi bana uban kowa bane....

Kwanan da Hafiz ya shige Sameer ya dinga kallo yanajin kwanyarsa da zuciyarsa suna yunk’urin tuno masa wani abin.... A hankali ya dafe goshinsa yana ambaton Allah kafin yaja motar ya wuce gida....

***

Duk k’ok’arin Zulfah taga tayi k’ok’arin raba wannan fad’a abu yaci tura a haka Hafiz ya shigo ya taddasu, aiko Hajiya na ganinsa ta zube k’asa tana kururuwa tana fad’in zasu kasheta Zulfa’u da danginta zasu karta....



SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_



*14*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



Abu kaman had’in baki nan fah yaran Hajiya gaba d’aya suka cafe suna rantse rantse da kururuwan cewa kashe masu uwa za’ayi....

Tsananin mamaki ya hana Aunty B da Nabilah furta komai sun zubawa sarautar Allah idanu suna ganin makirci irin wacce basu tab’a gani ba wajen Hajiya da d’iyoyinta...

Hajiya taci gaba da fad’in “Wllhi tallahi saika saketa, wllhi ka gama zama aure da wannan matsiyaciyar....”

Hafiz da k’irjinsa ya bada wani irin sauti ba tareda sanin dalili ba saurin k’arasawa ga Hajiya yayi kana yace “Amma dai Hajiya kinsan Alhaji ba bari zaiyi na saketa ba koh, kuma ai biyayya nake masa...”

Bai kai aya ba Hajiya ta katsesa da fad’in “Biyayya..? Toh biyayyar taci uwarta, wllhi saika saketa wannan wataran ba saidai azo a samu gawata ba donma dai Allah ya kiyaye su Sahariyya na nan da wayasan abinda zasumin, kana gani dai ga ‘yar uwarka Shariyya tsaban bugu saida suka kwab’e mata riga suka kuma targad’ata a hannu... Wllhi Hafiz saika saketa idanma ubanta bazai karb’eta tabi bola ko tabi titi don na tabbata wannan tsiyar babu mai kuma kwasanta.....”

Aunty B ce ta kece da dariya had’ida rangad’a gud’a kana tace “Ai idan baki mance ba ba bola ko titi kika d’aukota ba, a mutunce aka dank’a mata ku don babu tsiya a tattareda ita, sannan da wannan watsettsen auren shika sai yafi komai dad’i wajenmu barikiji na fad’a miki, idan har d’anki ya cika d’an halak yau Zulfa’u ta gama zaman aurensa, idan har ya haifu ya bata takardan sakinta kaman yanda kike ikirari....”

Hajiya banda tsuma bata komai sai faman bin Bara’atu da kallo kurum take, takai dubantaga Hafiz da yayi tsuru gefe yana duban Aunty B ta yanda take shiga bata nan take fita ba kana tace “Ka daiji da kunnuwarka koh, toh ka sakar masu tsiyarsu idanba so kake nai maka baki ba, wllhi saika saki Zulfa’u....”

Zulfah kuwa cikin kuka ta rik’e hannun Aunty B tana fad’in “Aunty don Allah kiyi hak’uri kada ki bari ya sakeni, Hajiya kuyi hak’uri don Allah wllhi hakan bazata sake faruwa ba In sha Allah....”

“Ke dalla can rufe min baki, shegen rashin zuciya yawa kare ya tand’e.. Toh ya sakekin mana sai mai, kin wani b’are bakiwa mutane kina kuka wllhi sai ya sakeki ya gani idan bakida gata....”

Hajiya zatai magana Hafiz yayi saurin katseta da fad’in “Inace matatace kuma nike zaman hak’urin nan da ita, kuma ai iyayenmu suka had’a wannan aure don haka gaskiya ni bazan saketa yanzu ba, ba yanzu nayi niyyan rabuwa da ita ba......”

Baikai aya ba Hajiya ta fashe da kuka had’ida kamo bakin zani tana fad’in Zulfa’u da danginta sun shanye mata d’a, tuni yasa kai zai fice Sahariyya da Nabilah sukayi saurin shan gabansa a guje, Sahariyya na fad’in “Haba Yaya haba kan wannan abar zaka bari tsinuwar Hajiya ya kamaka ga mata bila adadi a gari wllhi ka sakar masu d’iyarsu ka huta....”

Nabilah ta cafe da fad’in “Ahtoh nima dai hakan na gani Ya Hafiz duda dai ba shiri muke ba amma banso tsinuwar Hajiya ta kamaka ai dai gwara ka saki Addah Zulfah kowama ya huta....”

Batakai aya ba ya soma kwab’e takalman k’afafunsa alamun zai kai masu bugu gaba d’aya, a d’ari suka arce kowa tayi bayan ‘yan uwanta.....

Kasa fita yayi daga gidan don tuni Hajiya ta rufe k’ofa tana fad’in “Babu yanda zaije bai saki Zulfah ba, k’wafa kurum Hafiz yayi ya koma parlorn Hajiya yayi zamansa sai faman tsuma yake....

Hajiya zata bisa parlorn Zulfah tayi saurin fincikan hannunta daga rik’onda Aunty B ta mata ta tafi ta sha gaban Hajiya had’ida durk’usawa ya hawaye dake bin k’uncinta take fad’in “Hajiya don Allah kiyi hak’uri, wllhi idan Ya Hafiz ya sakeni Abbah tsinemin zaiyi, Hajiya kiyi hak’uri ki yafeni don Allah, idan dai Kausar ce na bar miki ita duniya da lahira amma dan Allah kada ki rabani da mijina, na rok’i arzikinki....”

Tsananin takaicin Zulfah da ya rufe Aunty B da Nabila tamkar film haka suke duban lamarin suna mamakin wane irin rashin zuciyane wannan....

Itako Hajiya shewa ta buga tana k’arema Zulfah duba daga yanda take duk’e tana hawaye kana tace “Wllhi idan ni na haifi Hafiz Zulfa’u, idan ni na shayar dashi na tsawon watanni ashirin wllhi sai ya baki takardan saki yanzu basai anjima ba idan yaso Abban naki ya tsine miki kibi ‘ya’yan kaji dama yaya balle kin sami tsinuwar mahaifi ai saidai ki soma bin bola, cikani dalla dangin tsiya mai farin sawu....” Ta k’arashe tana fizgan bakin zaninta daga rik’onda Zulfah ta mata....

Juyowa Zulfah tayi cikin hawaye tana duban Aunty B dake tsaye tamkar gunki tana dubanta tama rasa takaici ko tausayin Zulfah takeji....

Jiki a sanyaye Aunty B ta isa ta kamo Zulfah ta mik’ar da ita tsaye had’ida rungumarta take kuwa wani sabon kukan ya kufcewa Zulfah, Rihanah dake tsaye gefe can rungumeda Kausar sai hawayene ke gangaro mata....

Nabilah kuwa tab’e baki tai tana duban kowa da idanu...

Basukaiga barin gidan ba saiga Hajiya da mik’akk’iyar takarda hannunta tana faman washe baki had’ida tafiya irinta tak’ama...

Dungurin Zulfah tai da takardan kana tace “Alhamdulillahi d’ana ya rabu da alk’ak’ai yanzu kasuwancinsa zai bunk’asa yanzu zaiga cigaba a rayuwarsa yanzu al’amra zasu soma tafiya masa yanda yake so... Maza a k’ara gaba akai farin sawu wani wajen...” Ta k’arashe tana dank’a mata takardan...

Take Zulfah taji hawayenta sun k’ame, ta kuma juya takardan hannunta na tsananin rawa, takai dubantaga Hajiya da yaranta dake faman shewa Sahariyya da Naja’atu kana ta maido da dubanta ga Aunty B da Nabila....

“Aunty Ya Hafiz bai sakeni ba ki bari na shiga na tambayeshi naji daga bakinshi Dan Allah....”

Girgiza mata kai Aunty B tayi kana ta amshi takardan ta rik’ota tace “Muje, muje Zulfa’u....”

Zulfah na hawaye take fad’in “Aunty Kausar.....”

Juyawa Aunty B tai ta hangi Kausar dake rungume hannun Raihana kana ta tafi zata amsota... Ai kan ta isa Hajiya ta isa ta fizge yarinyar tana fad’in “Wa aje da ita ina bayan ga ubanta mahaifinta nan a raye, yo ai ko mutuwa yayi ba k’arewan aure ba babu yanda zataje nan shine gidansu.... Ku dai ku tattara tsamin k’afafunku ku fice tinda anyi maku abinda kukeso....”

Duk bala’i irin na Aunty B saida taji jikinta ya mata sanyi tausayin Zulfah da Kausar ya kuma kamata, sai tanaji sam bata kyauta ba donji take tamkar ita ta kashe ma Zulfa’u aure don koda Nabilah zatai magana Auntyn ita ta kwab’eta suka rungume ‘yar uwarsu suka fice....

***

Dubansa Shamsu ya kuma a karo na biyu yanda ko tab’a abincin dake bisa dinning table d’in baiyi ba har ya sauk’o daga sama wajen Mama, tasowa yayi daga parlorn ya dawo dining area d’in had’ida jan kujeran gefen Sameer ya zauna....

Dafasa Shamsu yayi kana yace “Still thinking about her, kodai zamuje Kaduna gobe ne, karka damu I’ll drive...”

Girgiza kai Sameer yayi had’ida fuzar da iska kana yace “I don’t know I don’t know Shamsu,so many things on my mind.... can k’asan zuciyana inaji Partner is not ok, inajin kaman wani abin ya sameta, sannan a nan kuma Ina ganin abubuwa wanda suke min tamkar na sansu wani wajen, I don’t know bansan meke faruwa ba Shamsu....”

Zuru Shamsu ya masa kana ya d’an sauk’e ajiyan zuciya yace “Toh ko dai bakason zaman unguwar ne...?”

Cikin sauri ya girgiza kai had’ida fad’in “No no no, in fact this is the best.... Har ina tunanin randa Mama zata gaji da zamana a nan....”

Shamsu ya d’an dara kana yace “Kasan Mama bazata tab’a damuwa ba In fact hakan sai yafi mata dad’i.... Kasan mai za’ayi tashi mu d’an fita...”

Babu musu Sameer ya mik’e suka fice ko zai refreshing....

***

Ko k’afafunta ta kasa motsawa sai faman tamke idanu take ga tsananin jiwa dake shirin kada ita... Dole Laila ce tai driving d’insu zuwa gida....

Siyama ta kasa fitowa daga mota nan ma saida Laila ta taimaka mata, a bakin k’ofar parlor suka lab’e kana Siyama ta umarci Laila ta lek’a mata idan Ammi da magulmatan ma’aikatanta basa downstairs sai su wuce cikin sauri gudun kada Ammi ta d’ago komai.....

Hakan kuwa akayi, Laila na na rik’eda ita har suka haura sama d’akin Siyama...

Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Siyama tai kana ta fad’a toilet don kuma kimtsa kanta....

Tsayuwa tai gaban madubi dake barhroom d’in tana duban kanta, b’angare na zuiyarta ta tambayarta _Siyama kin tabbata abinda kikai kinyi dadidai...?_

Take d’aya b’angaren ya shiga raya mata hakan shine daidai Siyama domin kuwa haihuwa yana nufin canza rayuwarki ne gaba d’aya, komai naki zai canza kama daga suffar jikinki zuwa hidiman kulada yara, ke kuwa baki shiryama wannan ba hasalima shi kanshi mijin naki haihuwa bata damesa ba domin kuwa ko a d’an irin tad’i da kuke na soyayya bai tab’a sako miki batun haihuwa ciki ba baima tab’a hasashoki da juna biyu ba balle yara, kin yanke hukunci mai kyau....

Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tai sanda ta jiyo Laila na k’wank’wansa mata k’ofar bayin tana fad’in me takene haka a bathroom tai sauri ta fito ta sha maganinta kafin lokaci ya wuce...

Cikin wahalcecciyar murya tace “I’m coming,...”

B’alle magingunan Laila taci gaba dayi tana aje matasu su zama ready... Tamkar wacce aka jefota saiga Ammi a d’akin ta shigo....

Gaban Laila ya yanke ya fad’i don bata mance gamuwarsu da Ammi ba sanda tai k’ok’arin raba k’awancensu da Siyama, don a cewar Ammi sam hankalinta bai kwanta da Laila ba gashi ita kuwa Siyama duniya batada k’awa sai Laila....

Gaisar da Ammi tai ta amsa a tak’aice kana tace “Ina Siyamar....?”

Laila tace “Tana bayi...”

Ammi ta jinjina kai kana ba tareda ta amsa ba.... Duban d’akin taci gaba da yi tanason gano wani abin....

Duban Laila ta kumayi a kaikaice kana tace “Idan ta fito kice Ina nemanta....”

Babu musu Laila ta jinjina mata kai tana ficewa ta kwaikwayi maganarta had’ida buga tsuka....

***

Koda suka tafi can gidan Zulfan suka d’ebo ‘yan wasu kayayyakin sakawanta ba gida suka wuce ba kai tsaye gidan Aunty B suka wuce don Aunty B d’in tafiso da safe ta kaita wajen mahaifan nata tayi bayanin komai.....

Koda Nabilah zata tafi na saida Aunty B ta kwab’eta cewa kada tacema Mamy komai tukuna...

Haka Zulfa’u tai kusan kwana tana hawaye, abubuwa da dama sun cika mata kwanyarta da zuciyarta, uwa uba mutuwan aurenta, ga musiban da zataje can gida ta tarar wajen Abbah, wajen Mamy ma tasan bazata samu da sauk’i ba, ga d’iyarta can hannun Hajiya da d’iyoyinta wanda tasan sai abinda sukaga dama zasu mata tunda dai tasan tsanar da suka mata ya shafi d’iyarta.....

A hankali ta rintse idanunta hawaye masu d’umi suka gangaro mata, cikin tsananin sanyi jiki ta mik’e ta nufi bathroom d’auro alwala.....

***

Tinda ya isa gidan yaji gidan ya masa sarari da yawa, yakai dubansa ga kujeran da kullum idan ya dawo a wajen yake hangota kodai tana bacci ko kallo ko kuwa karatu... Ya jima sosai yana duban wajen kafin ya d’an tab’e baki ya k’araso ya zauna cikin kujera had’ida dafe kansa kad’an, kana ganin sa zaka

Please Login or Register in order to submit comment