Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gimbiyar....”
Baikai aya ba suka sinkayo muryar Hafiz yana fad’in “Baza’a shawo kan nata ba bak’in munafuki....”
Gaba d’aya suka juyo suna duban Hafiz wanda keta faman hure huren hanci yana cika....
Gaban Zulfa’u ya yanke ya fad’i yayinda Yusuf yace “Kaikuma waye....?”
Hafiz yai wata k’asaitacciyar murmushi kana ya dubi Zulfah da gaba d’aya tashin hankaline ya nuna a fuskarta kana yace “Au dama baki fad’a masu kinada miji ba, basusan cewa ke d’in matar aure bace....?”
Yusuf ya d’an murmusa don ya gane Hafiz tsaf tsohon mijin Zulfah ne kuma sun had’u kwanaki a gidansu Zulfa’un sanda sukaje mata gaisuwar rasuwa....
Takowa Yusuf yayi kusansa kad’an yana k’are masa duba daga sama zuwa k’asa, dab fuskar Hafiz ya matso da tasa fuskar kafin ya rage murya yace “Tsohon miji zakace, a halin yanzu Zulfa’u ta mai rabo ce....” Ai baikai aya ba Hafiz dake tururi yakai masa shak’a a wuya yana mai furta “K’arya kake wllhi tawace har abada...!”
Zulfah da Atika suka zaro idanu waje cikeda tashin hankali ta k’arasa tana fad’in “Ya Hafiz dan Allah ka sake shi, kar kaji masa ciwo....”
“Rufemun baki munafukar banza munafukar wofi wacce batasan komai ba sai cin amana, kin had’e kai da wannan Kawaliyar k’anwar uwar taki kuna cin amanata....”
Tinda Zulfa’u take Hafiz bai tab’a k’ona mata rai irinta yau ba, Aunty Bara’atu yake kira Kawaliya.... Batasan sanda hawaye suka soma gangaro mata ba, ta kasa katab’us yayinda Atika tai saurin rik’ota....
Akram ya d’ankai dubansa gareta yaga hawaye na zubo mata, duban Atika yai kana yace “Ki shiga da ita ciki...” Babu musu Atika ta jinjina masa kai kana ta janyo Zulfah tamkar rak’umi da akala suka shige cikin gida....
Maidoda dubansa ga Hafiz Akram yai kafin ya tako har gabansa yasa hannu ya cire hannayensa daga wuyar abokinsa kana yaceda Yusuf “Ba girmanka bane fad’a da mahaukaci, lets go....”
Hafiz ya saki Yusuf yana k’ok’arin rik’o Akram saidai hannu guda Akram yai amfani dashi wajen damk’e hannun Hafiz d’in da ko motsata ya kasa.... Murya a dake yake furta “Komai nada iyaka... Yanada kyau kasan madakatarka a rayuwa.....!” Daga haka jifa da hannun Hafiz d’in yai suka shige mota... Akabar Hafiz da sosa hannunsa yanda Akram ya murd’e masa... Yana ganin yanda suka kwashi mota suke shige suka bar masa k’ura....
Suna tafe Akram na sak’e sak’e cikin zuciyarsa, hukuncinda ya yanke yayi daidai, yafi kyau shid’in ya nemi auren Zulfa’u don baijin zai bari His Excellency yayi takara da wannan lunatic d’in....

A b’angaren Hafiz kuwa wajajen k’arfe taran dare ya shigo gidan mahaifinsa, wata sabuwa Baba Alhaji ya bijiro masa da zancen maida matarsa Sawwama d’akinta... Hafiz yana kumbure kumbure yake duban Hajiya kana yace “Amma dai Baba ka mance nima na kusan mutuwa kan munafukar yarinyar nan, Baba wllhi ba sona take ba, nayi imani kasheni kawai takeson yi... Haba haba saikace neman kai dani kuke... Kuda zakuyi yak’in dawo mun da farin cikina Zulfa’u kunje kuna yunk’urin dawo min da ajalina... Nidai wllhi gaskiya Baba...”
Dakatar dashi Baba Alhaji yai da fad’in “Kai rufemin baki... Shikenan kai duk wacce ka aura saika rabu da ita, so kake da k’anan shekarunka a soma k’irga maka aure... Ni nace zan dawo maka da Zulfa’u ince....?”
Hafiz ya d’ago da sauri yana washe baki yace “Allah da gaske Baba....?”
Baba Alhaji ya jinjina kai kana yace “K’warai kuwa nai maka alk’awarin dawo maka da matarka Zulfa’u gareka amma da sharad’i....”
Cikin zumud’i da k’osawa yace “Mecece sharad’in Baba...?”
Baba Alhaji ya murmusa kana yace “Alhamdulillah abinda nakeson ji kenan.... Sharad’in itace zaka maida matarka Sawwama d’akinta, ka mance komai ka maidata....”
Saida ya zabura da jin batun mahaifin nasa...
D’an girgiza kai ya soma yana fad’in “Haba Baba Dan Allah... Wllhi ni yanzu ko a k’afa aka d’auramin Sawwama zan kwance na gudu...”
Baba Alhaji ya jinjina kai yace “Idan kanason Zulfa’u zaka maido Sawwama gobe gobe d’akinta... Na gama magana...” Daga haka mik’ewa yayi ya shige d’aki yabar Hafiz zaune wajen yana sak’e sak’e da zullumi...

Hajiya kaw salallami kawai tana salati tana furta zama bai ganta ba
***

Washe gari Khalid yai shirinsa ya nufi Kaduna dukda sanin cewa zasu kwashi ‘yan kallo musamman da mahaifiyarsa, gashi sam sun kasa samunsa a waya, fitowarsa kenan dashike gidan Sameer ya sauk’a a nan unguwar ya hangeta tafe ta nufi babban kwalta da alama makaranta ta nufa..... Saida ya sak’i sassanyar murmushi don dama yana tunani idan ta riga ta tafi makaranta ba lallai su samu suyi sallama ba....
Ya gefenta ya rab’o had’ida rage glass d’in motar yana sakar mata sassanyar murmushinsa yake furta sallama...
Murmushin itama ta sakar masa wannan karon had’ida amsa masa...
Khalid yaji dad’in murmushin da ya gani saman fuskarta kana yace “Is a good thing I found you here, da ban fito da wuri ba maybe da ko sallama bazamu samu muyi ba....”
Ta d’an dubesa da alaman tambaya... Jinjina mata kai yai kana yace “Kan hayata nake zan koma Kaduna yanzu....”
Nabilah ta d’an sadda kanta k’asa kana tace “Toh Allah shi kiyaye hanya ya kaika lafiya....”
Khalid ya amsada Ameen kana ya k’arada “Shiga muje na ajiyeki a school d’in....” Yayi maganar yana bud’e security lock....
D’an dubansa tai kana tace “Karka damu yanzu zan sami adaidaita, kaje kawai kar kayi rana kasan yanayin yanda hanya suka koma yanzu....”
Yana murmushi yake furta “Tsoro kike kar a sace miki ni....?”
Ta d’an fito da idanunta waje had’ida murmusawa kana tace “Nidai bance ba...”
“Toh idanba tsoro kike ba ki shigo nai dropping d’inki....”
Zata kuma magana yace “No more excuse shige muje....”Ya k’arashe yana mai bud’e mata frontseat
Saida ta d’an juya idnunta kafin ta k’arasa ta shige.... Wani sassanyar k’amshine da ya gaurayu da sanyin AC sukai mata sallama cikin motar tasa, wani ikon Allah tin jiya dataji Yayanta Ma’aruf da Mamy suna tattaunawa kan batunsu da Khalid d’in sai ta tsinci kanta tana mai tsananin jin nauyinsa, gaba d’aya saiji tai ta kasa sakewa cikin motar ma.... Shi kansa Khalid d’in ya kula da canjin nata, wannan kallon rainin da take masa sam yau batai masa ba saima avoiding k’wayar idanunsa da takeyi.... tsakiyar motar ta hangi had’edd’en cappuccino cikin disposable cup da blueberry cookies da alama breakfast d’insa kenan.... Bai bari ta d’aga idanunta ba yace “Bismillah...”
D’an tab’e baki tai kana tace “Aaa wannan ai saiku, ni ina wannan zai k’osheni, nasan iyakacin karin kumallon naka kenan...”
Khalid ya murmusa yana karyan kwana yake furta “Seems like kin fara sanin mijinki tun yanzu....”
Ai baikai aya ba ta kuwa watso masa muguwar kallon mai firgitasa... Ya kuma sakin murmushi yana mai ayynawa cikin ransa ai saidai ba Nabila ba... Khalid yaci gaba da fad’in “Bakida labarin Sameer da Mamy harmada Mamani sun bani...?”
Wannan karon kauda kai tai daga barin duban nasa had’ida tab’e baki kana tace “Ai basukeda alhakin badani ba, Abbah na ne kawai zai haka, kuma a iyakacin sanina aurenka da Yesmin ya kusa....”
Bai kuma cewa komai ba jin ta ambato Yesmin har saida ta d’an kaikaito da fuska ta dubesa, sai yau ta k’are masa kallo, ashe kullum kallon tsoro take masa.... Khalid yakai mak’ura wajen had’uwa, ba laifin Yesmin bane data nace masa, irin mutanen nan ne da duba d’aya zaka masu kaji sun shige ranka.... Kaman yasan dubansa take aiko yana juyowa suka had’a idanu, tai saurin d’auke idanunta daga barin dubansa, babu wanda ya kuma cewa komai cikinsu har suka iso cikin babban jami’ar....
Yusrah da dandatson ‘yan ajinsu ana cike k’ofar lecture hall ko ba’ace ba isowar malami ake jira hamshak’iyar BMW d’in nasa tai parking, kowa sai santin motar yake ga kalan ja dama da d’aukan idanu....
Ta kama handle zata fice kenan tajiyo muryarsa yana fad’in “teddy bear zan tafi yak’in neman aurenmu kimin addu’a.....”
Juyowa tai tana dubansa sai kuma ta sadda idanunta k’asa sakamakon yanayin data hangi fuskar nasa ciki....
Kasa cewa komai tai har saida Khalid yace “Bakida abinda zakicemin ne...?”
A hankali ta furta “Toh ni mai zance....?”
K’uri ya mata gaba d’aya ta daburce kana yace “You pray for me, for us....”
Ta d’an dubesa harda wani jinjina mata kai alamun tabbatarwa....
Duban dandatson ‘yan ajinsu tai kana ta hango k’awarta Yusra daga can gefe tana duban motar tana murmushi kana tace “Em... Allah kaika lafiya, drive safe....” Ta kama marfin motar zata bud’e taji tak’i bud’uwa..... Juyowa tai tanai masa duban tuhuma...
Ya d’an d’aga giransa kana yace “What..?”
Shaye da mamaki take dubansa kana tace “Ka bud’e min na fice kafin malaminmu ya k’araso....”
Sai sannan ya saki murmushi kana yace “Oh Aw sorry na mance k’ofar nan ta sami matsala bata bud’ewa ta ciki saita waje... Wait barin bud’e miki....”
Nabilah ta bisa da kallo sanda ya fice ya zagayo bud’e mata marfin motar itada sam bataso ya fito ba balle a ganshi yana bud’e mata k’ofar mota....
Aiko mai motar har sai yafi kashe dandatson mutanen fiyeda motar kanta....
Kunya ya cika Nabilah sanda Khalid ya bud’e mata marfin mota, a d’arare ta fito don ko ba’a ce tasan illahirin mutanen dake wajen su suke kallo, Khalid ya rank’wafo saitin kunnenta kana yace “You take care, and kar na sake ganinki da wad’ancan yara mazan....”
Harara ta galla masa kana ta d’an saita kanta tace a hankali itama “Thanks for the ride, and safe trip...” Daga haka tasa kai ta shige kaman zata kifa don ji taima kaman k’afafunta hard’ewa suke.... Khalid ya bita da kallo har ta shige kafin ya koma motarsa ya wuce shima...
Aiko Nabila na k’arasowa Yussy ta janyo hannunta suka shige tana fad’in kalan burgewar da sukai itada Khalid....

***


Wajajen shabiyun rana ya masa a Kaduna, yana isowa gidan kai tsaye sashensa ya wuce kafin wanima yasan ya dawo gidan, Aiko Kubura ta hango giftawansa, ta saki bokatin da take shanya kana ta nufi sashen Ammi a guje tana rangad’a mata kira.... Siyama da tashinta kenan daga bacci ta sauk’o k’asa tana neman abin kari taci karoda Kubura tamkar wacce aka jefota....
“Ke ke meye haka.. Lafiya?” Siyama ta dakatar da Kubura....
Kubura na haki take nunida waje....
Siyama da takaici ya cikata tsaki tai kana tace “Mutanen nakine suka motsa kokuwa....?”
Kubura taci gaba da haki tamkar wacce abin gudu ya biyota kana tace “Aunty Siyama ya dawo....”
Siyama ta yatsina fuska kana tace “Shi wane....?”
Kubura tace “Saifu mana Aunty Siyama... amma fah shi kad’ai babu abokiyar tafiyarsa babyn dank’on da aka lik’a masa....”

Harara Siyama ta galla mata kana tace “Ke banson sakarcin banza....”
Kubura tace “Wllhi gaskiya nake fad‘I maki Aunty gayacan ya shige sashensa.....”
Siyama ta jinjina kai kana tace “Maza haura sama ki fad’iwa Ammi....”
Daga haka ta fice sashen Khalid kaman zata tashi sama...

Khalid yana k’ok’arin kwab’e riga da niyyan shiga watsa ruwa Siyama ta banko k’ofar d’akin ta shigo....
Fasa cire rigar yayi sai tsaki dayaja a hankali lokaci guda yake furta “The next time you coming into my room, would you bother to knock... Dear Sis...” Ya k’arashe yana mai k’arasowa gabanta....
Siyama na huci furta “Kai yanzu abinda kayi ya maka daidai Khalid.... Rashin mutuncin da kayi ka kyauta kenan...?”
D’aga mata hannu yayi kana yace “Wait wait, hold your lectures Siyama, as you can see I just got home... Fice min a d’aki.....” Ya k’arashe yana nuna mata k’ofa...
Muryar Ammi ne daki dodon kunnuwarsa “Bazata fice ba, ka mareta kawai sai nasan ka cika....”Hannayensa dafe da kunkumi ya d’an kauda kai gefe yana k’ok’arin calming kansa.... Juyowa ya d’anyi kana yace “Ammi ina yini....”
Dakatarshi tai ta hanyar d’aga masa hannu kana tace “Bazan amsa ba... Cikakke, aidai kaji dad’i ka aikata abinda kakeso ka watsaman k’asa a idanu... Sai ka sanar dani da baka kai Yesmin d’in Abujan ba gidan uwar wa ka tafi....”
Karaf Siyama tace “Har sai kin tambaya Ammi, wajen watsetsiyar can ya tafi ya gama watsewa...”
Izuwa lokacin zuciyar Khalid ta gama tafarfasa, shi kad’ai sai murza hannunsa dake k’ok’arin kaima Siyama mari yake... Badon Allah ya kiyaye ba tabbas data kwashi tsaraban maruka....
“You watch your mouth....” Ya fad’i idanunsa akan Siyama wanda suka gama komawa jazir....
Ammi ta shiga tafe hannaye tana fad’in “Lallai na yarda basu barka haka ba.... Shin uwar mai suka jik’a suka baka Khalid.... Ka fad’a min... !!!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya

Baisan sanda shima a harzuk’e jijyoyinsa sunyi sama yake furta “Abinda suka jik’a suka baiwa Siyama ta kasa rabuwa da Sameer nima shi suka jik’a suka bani.... Cos yarinyar da kuka tsana kuke jifarta da sharri turned out to be Siyama’s sister in-law... Nabilah ba kowa bace face k’anwar Sameer wanda suke uwa d’aya uba d’aya..!!!” Yayi maganan yana mai takowa dab gaban Siyama


Ba Siyama datayi mutuwar tsaye ba harta Ammi neman yawun bakinta tai ta rasa balle tai tunanin kalamai ka iya zuwa kan harshen ta....



SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_







*73*





Girgiza kai Siyama take cikin rashin yarda da abinda kunnuwanta ke jiyo mata, lokaci guda ta kamo hannayen Khalid tana mai furta “Khalid tell me this isn’t true.... Wasa kakemin koh, babu abinda ya had’a Sameer da wad’annan mutanen.... Tell me you’re just joking...”
Fincikar hannayensa yai kana yace “Since when muka soma wannan wasar dake abinda kikaji gaskiya ne Nabilah k’anwar mijinki ne....!”

“What was that...?” Muryar Daddy ya katsesu..... Lokaci guda Ammi dake faman girgiza kai itama cikin rashin yarda ta shiga furta “Karka sauraresa, shak’iyancin Khalid ne kawai ya motsa don an hanasa auran yarinyar shine bari ya dangantata da Sameer, yo ina Sameer ina zuri’ar yarinyar can dangin mayu.... Kai ko a halitta Sameer yayi kama da wad’ancan mutanen ne.... Wllhi k’arya yake tsantsan Daddyn Siyaaam kar ka yarda dashi.....”
Siyama dake tsananin kuka kuma janyo hannayen Khalid tai tana jijjigawa da iyakan k’arfinta take fad’in “Khalid tell me is isn’t true... Ka fad’a min k’arya kake...!!!!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya....
Daddy ne ya k’araso ya janye hannayen Siyama daga na Khalid yana mai k’ok’arin kwantarwa Siyamar hankali....
Cikin kuka Siyama ke furta “Daddy Wllhi k’arya ne, of all people those people can’t be my husband’s family.... Daddy not my Sameer....” Ta k’arashe cikin shesshek’ar kuka....
Duban Khalid dake faman watsama Siyama muguwar kallo Daddy yai kana yace “Khalid..!”
D’ago kai Khalid yai ya dube mahaifin nasa had’ida furta “Na’am Daddy..” lokaci guda yaci gaba da furta “Ka sameni a parlor na...”
Babu musu Khalid ya jinjina kai kana yabi bayan Daddyn yana mai watsawa Siyama da Ammi ke tausanta harara....

Daga can gefen k’afan mahaifin nasa ya zauna had’ida risinawa kana yace “Daddy barkada gida, ina yini....”
Amsa masa mahaifin nasa yai kana yai gyaran murya ya soma fad’in “Khalid maike faruwa...? Shin abinda naji kana fad’i gaskiya ne cewa yarinyar can k’anwar mijin Siyama ne....?”

Jinjina masa kai Khalid yai had’ida gyara zamansa kana yace “Daddy abinda kaji gaskiya ne, Nabila k’anwar Sameer ne, recently Sameer ya sami biological parents d’insa, and it happens to be Nabilah k’anwarsa ce Daddy... Wato Daddy akwai abubuwa da dama da suke faruwa a gidan nan wanda sam basa dacewa tin daga kan yanda ake gudanar da al’amran gidan nan... Daddy ba wai ina fad’in gazawarku bane a matsayinku na wad’anda hakkin kula da tarbiyan gidan nan ya rataya a wuyarsu bane most especially you Daddy... Amma maganar gaskiya fah Daddy kuskuren tin daga sama ne, ya samo asali ne daga wajenka, ka baiwa Ammi wani irin power a gidan nan wanda sai abinda taga dama akeyi, Daddy I’m not saying baiwa matarka dama da freedom kuskure bane, but Daddy everything has a limit, ina ganin a matsayinka na shugaba a gida ya kamata ka zama kaikeda final say matuk’ar bai kaucewa Shari’a ba, Daddy karfa ka mance Allah da kansa ya gargade masu imani cewa su tsare kawunansu da iyalansu daga shiga wuta, shin Daddy mecece makomar gidan nan...? Yanzu ga Siyama a gida itama bata d’auki auren da daraja ba balle mijinta sabida abinda ta taso taga akeyi kenan a gidansu, turbar da mahaifiyarta ta d’aurata bisa kenan... Sam Ammi da Siyama basu d’auki d’an adam da wata daraja ba idanba wanda suke so bane... After what she’s done a gidansu Sameer bansan da wasu idanu zata dubesu matsayin sirakanta ba, Daddy mai ya haifar da haka...? Rashin samun wadataccen tarbiya ne tin daga fari shi ya haifar da haka.... Opinion d’in kowa a gidan nan baida daraja idandai ba daga Siyama ya fito ba, Ammi bata d’aukan maganan kowa ko shawarin kowa saina Siyama, and Daddy kaikuma duk abinda Ammi ta fad’i a gidan nan shikenan daidaine kayi na’am dashi without overlooking it... Daddy please ya kamata a daina irin wannan rayuwar a gidan nan, a duba lamarin Daddy.....” Ya k’arashe cikin tsananin k’ank’an da kai da kuma murya....

Shiru ya gifta tsakaninsu tamkar mahaifin nasa bazaice komai ba, saima d’aura hab’arsa da yayi saman hannayensa guda biyu da ya dunk’ule waje guda....
Muryar Ammi ce ya katse shirun da ya ratsa cikin parlorn...
“Toh wllhi ba k’anwar Sameer ba, yau idan uwar Sameer ce wannan yarinyar babu abinda ya shalleni, wllhi bazaka aureta ba muddin ina numfashi, yo sai mai... Allah ya kiyayeni na had’a jini da matsiyata, kuma shima Sameer d’in sai ya sakar min d’iyata, wllhi bazata zauna dashi ba, naji dad’i da rabo bai tsaga tsakaninsu ba, rabuwa ya zama dole, gwara da Allah ya bayyana mana....” Bata ida maganar nata ba Siyama ta shigo tana kuka tana fad’in “Ammi wllhi bazan rabu da mijina ba.... Gaskiya ni bazan iya rabuwa da Sameer ba don wllhi ina sonshi ina k’aunarshi har kwanan gobe, Sameer is nothing like his family, tsautsayi ne da k’addara yasa suka zama danginsa, kuma ma ai su Mummy ne iyayensa shida wad’ancan mayun jini ne kawai ya had’su, but his real family are here.... So Ammi don’t think of separating us... Nida Sameer are magnets babu wanda ya isa ya rabamu not even his so called new family, yanzu zan tafi ba sai anjima ba, yanzu zan koma to win my husband back don ya zama dole na rabasa da wad’ancan annoban....!” Tana ida fad’in haka ta fice fuuuu Ammi na k’walla mata kira ko saurarenta bata tsayayi ba...
Ammi ta maidoda dubantaga Daddy tana fad’in “Daddyn Siyaam kaga fah tafiya zatayi, kayiwa Allah ka dakatar da ita kartaje su lashe min ita kaman yanda suka lashe Khalid...” Ganin bai amsata ba ya sanyata janyo Khalid tana fad’in “Tashi tashi wuce maza ka k’wato min car keys d’inta...” Khalid na tirjewa Ammi na turasa, fad’i yake “Ammi kinsan Siyama idan tayi niyyan abu no one can stop her....”
“Ka shige nace kafin na maka baki...”
Duban mahaifiyar tasa kurum yai had’ida girgiza kai kana ya fice yabi bayan Siyama...
Ya maido da dubantaga mijinta wanda ta koma masa tamkar TV kana tace “One of these days d’aya daga cikin yaranka zasu sakamin hawan jini, wani irin musifa ne wannan ace yara duk sun haukace kan dangin mayu, da ina tunanin Khalid ne kawai iftila’in ya auka masa ashe harda Siyamar kanta, yo na Siyama ma ai shine babban tashin hankali tinda an riga anyi aure, Toh wllhi ko ina mutuwa ina tashuwa ne bazan bari Khalid ya auri yarinyar can ba, kuma Siyamar ma ko kotun k’oli zamu tafi wllhi sai Sameer ya sakar min d’iyata don bazan tab’a had’a iri da dangin tsiya ba ehe....”
Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice fuuuu tana k’walla kiran yaran nata....

Birki tai a d’ari sakamakon hango Siyama da tai cikin mota Khalid na tsaye gaban motar tana fad’in ko ya kauce mata a hanya ko tabi takansa.....
Ammi ta isa jikin motar a guje tana fad’in “Nafa fad’a maki babu ke babu tsinannen yaron nan ki fito a motar nan Siyama....”
Siyama fad’i take “Ammi idan sama da k’asa zasu had’e Wllhi baki isa ki rabani da Partner ba, kuma wllhi yanzu ba sai anjima ba zan tafi na soma yak’in raba mijina da wad’ancan jarababbun.....”
Khalid fad’i yake “Siyama calm down, ki bari abi komai a sannu, ki sauk’o ayi magana ta nutsuwa babu wanda zai rabaki da mijinki amma hanyar da kika d’auko ba mai b’ullewa bace just calm down first....”
Bai rufe baki ba Siyama ta kuma baiwa mota wuta alamun batada niyan fasa abinda tai niyya... Gani zatabi kan Ammi yasa Khalid saurin janyo mahaifiyarsu gefe dake kururwa Siyama kaw taja mota ta fice a guje k’iris ya rage bata had’ada security mai bud’e mata gate d’inba
Ammi hannu aka take furta “Na shiga uku na lalace ni Farida mi nayima yaran nan suka zab’i wasu tsinannu kwashesu sama da mahaifiyarsu.....” Ta shiga rera kuka bataji bata gani, da k’yar Khalid ya iya janyota ya shigar da ita cikin gida....

***

Akram na risine gabansa ya ida amsa wayar da yake, saida ya d’an b’ata lokaci yana duba abu cikin wayar kana yace “Ina saurarenka...”

D’an gyara zamansa Akram yai kana yace “Mun gana da ita yarinyar jiya, kuma na sanar da ita abinda ke tafe damu, and daga dukkan alamun mun samu goyon bayan K’anwar mahaifiyar tata wacce take zaune gabanta, amma your Excellency wani hanzari ba gudu ba....”
Engr ya gyara zamansa kana yace “Umhum go ahead ina saurarenka...”
Akram ya kuma d’an turowa daga cikin kujeran kansa a k’asa kana yaci gaba da fad’in “Sir, ina ganin zaifi kyau idan baka bayyana mata kanka a halin yanzu ba, ma’ana naci gaba da isar mata sak’onka zuwa nan da d’an wani lokaci sabida tsohon mijinta yanada matsalan tab’in k’wak’walwa kuma Sir a matsayin da kake idan kowa yasan cewa kai kake nemanta wannan tsohon mijin nata can cause a biggest scandal for us, ni kuma hakkinane na kare reputation d’inka and your career in politics kasan abokan hamayya k’iris suke jira Rankashi dad’e...”

Shiru yai yana nazarin maganganun Akram d’in kana yace “Haka ne Akram.... Kayi daidai, hakan yayi... Bansan da mai zan biyaka ba bayan duk abubuwan da kake min.... Hak’ika ka cika d’anuwa na k’warai....”

Murmushi kwance saman fuskar Akram yace “Ka wuce haka a wajena your Excellency, ban biyaka rabin abubuwan da kake min ba dama family na gaba d’aya, you made me who I am... Bama ni kad’ai ba d’imbin mutanen da suka zama abinda suka zama yau ta dalilinka bazasu k’irgu ba, Allah ne kawai zai biyaka, muna kuma fatan Allah ya k’ara mana irinku cikin al’umma....”
Daidai nan Muhibbah ta shigo d’aukeda farantin fruits ta zuba gayu cikin riga da skirt English wears wanda suka zauna a jikinta sosai ga k’amshin turaren humra dake tashi a jikin nata wanda duk d’ah namijin data giftasa dole tsikar jikinsa ya tsargar masa....
Akram yai saurin mik’ewa kana ya risina yaceda ubagidan nasa “Sir ni zan wuce...”
Engr ya jinjina kai yace “Alright Akram, ka samu Sufi ya baka list d’in k’ungiyoyin masu neman taimakon nan sai asan abinda za’a fara taimaka masu dashi koh....”
Ya jinjina kai yana mai furta “Alright your Excellency right away...”
Ko kallon yanda Muhibbah take baiyi ba ya fice cikin sauri duka irin shu’umin kallon da take aika masa....
Akram na ficewa ta kuma matsowa jikin mijin nata tana mai fad’in “Excellency na ga fruits na kawo maka, nasan idan na biye naka bazakaci komai ba har sai ka jira yaran nan sun dawo daga islamiya....” Ta k’arashe tana mai d’auko yankakkiyar kankana da cokalin fork.....
Girgiza kai ya d’anyi had’ida kauda kai gefe kana yace “Shin wai wane irin kunnen k’ashi ne dake Muhibbah, sau nawa zance maki idan ina tare da bak’i a parlorn nan kar ki shigo, kin fito babu ko mayafi cikin wannan shiga kin wuce duk tarin ma’aikatan dake cikin gidan nan a haka kin nufo har parlorn nan... Kanki d’aya Muhibbah....”
Murmusawa tai jin Wai yau Engr ke damuwa da ita har haka, ashe dai har yanzu yana k’aunarta tinda gashi yana kishinta.... Aje plate d’in ta d’anyi kana tace “Toh Banda abinka Excellency na gani nai daga kai sai Akram ne ai...”
“Akram d’in muharammin ki ne shi...?” Ya jefo mata tambayar...
Gyara zama ta kumayi kana tace “Toh ai gani nai Akram ya riga ya zama d’an gida a gidan nan kuma ai.....”
Dakatar da ita yai ta hanyar d’aga mata hannu kana yace “That doesn’t justify your actions, kinyi kuskure karki sake nan gaba...”
A hankali cikin yanayi na shagwab’a da turo baki gaba tace “Bazan sake ba in sha Allah... kuma ai gani nayi yanzu baka wani kulawa dani a gidan nan dukda k’ok’arin da nake wajen ganin ka janye k’udirinka akaina, Ma’aruf dan Allah ka yafemin haka nan mu koma tamkar yanda muke da, I promise to be a good housewife kaji please.... Ko dai neman aure

Please Login or Register in order to submit comment