Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaro maras jin magana har yake fifita Siyama sama dashi, ya kasance yafi yarda da Siyama sama dashi, ashe dai k’iriniyace kawai irinta yarinta amma a zahirin gaskiya d’an nasa mutumin kirki ne wanda kuma yasan yakamata dikda k’arancin shekarunsa.... Hannun Khalid guda Daddy ya kamo kana yace “Do you want us to go out... Any place you’ve in mind....”
Wannan murmushi mai bayyana hak’wara Khalid yai kana yace “A’a Daddy babu yanda zamuje, muna nan a nan tareda family d’inmu... I want to meet my sisters....” Ya k’arashe murmushi kwance saman fuskarsa....
Daddy yaji dad’i harda d’an bubbuga kafad’ar Khalid kana yace “K’annen ka sun dawo daga islamiya, nayi mamaki da bakaji k’iriniyarsu ba, koda yake you really are preoccupied shiyasa bazakaji hayanaiyarsu ba...”
Ya d’an murmusa kad’an shima ba tareda yace komai ba...
A tare suka nufo parlorn shida mahaifinsa... Yaran gaba d’aya suna saman dining table don already lokacin dinner ne... Mahaifiyarsu sai fama dasu take da gani yaran akwai k’iriniya babu laifi.... Hango wani mutumi da sukai tareda mahaifinsu ya sanyasu zuba masa ido ga kuma kamanni da yakeyi da Daddynsu... Ijlaal tace “Mummy who’s he...?”
Mahaifiyar tasu ta d’an rank’wafo kad’an saitin fuskan yaran, cikin murya k’asa k’asa take furta “Girls go and say hello to your brother...”
Gaba d’aya kallon mamaki suka bita dashi kafin Humy ta ije fork d’in hannunta kafin tai magana mahaifiyar tasu ta kuma masu alamu da idanu kan suje su gaida Khalid...
A tare suka fito daga cikin kujeran suka nufo Khalid da ya kasa janye idanunsa daga barin dubansu... Saida suka k’araso gabansa Humy ta d’an ja baya kad’an tace “Wait how comes bamu sanka ba...? Da gaske kai Yayanmu ne... And ina kake all these while... Mummy ce mamarka kaima...?” Khalid yai tsaye yana duban yarinyar da jinjina wayonta... Daddy ne ya d’anyi gyaran murya ganin Khalid yai tsaye sakare kana yace “Kids ku k’yale Yayanku ya huta yai tafiya ya gaji... Muje koh....” Ya k’arashe yana mai kamo hannayensu, Ijaal ta saki hannun Daddy ‘yar k’aramar ta k’arasa da gudu ta rungume Khalid tana mai furta “Welcome Yaya... Kar ka sake tafiya ka barmu kaji, dama a sch su Nazira suna cewa sunada brother... Nima nace masu yanzu inada brother..?” Tai maganar tana mai langab’e kai...
Samun kansa yai da sakin murmushi kana ya durk’usa ya rage tsawon sa gabanta, hannayenta ya kamo kana yace “Of course you can...” Annuri ya cika fuskokin illahirin mutanen parlorn... Khalid ya dafa fuskarta kad’an kana yace “And you are...?”
Humaira tai saurin cewa “She’s Ijlaal and I’m Humaira but you can call me Humy...” Khalid ya murmusa yana jin son yaran na shiga cikin ransa a hankali
Ijlaal tace “Zance masu my brother is handsome and he has muscles duk wanda ya bullying d’ina a sch zai rama min....” Wannan karon dariya suka d’anyi gaba d’aya kana Khalid yace “Of course I won’t allow them to bully such a beautiful princess like you....”
Ijaal na Washe hak’wara tace “Da gaske Yaya nafi Addah Humy kyau...?”
Juyawa yai ya kalli Humaira da mood d’inta ya d’an canza kana ya saki murmushi ya mik’a mata d’aya hannun yana mai furta “Come here...” Da sauri ta k’arasa Daddy dai table ya shige wajen matarsa suna kallon draman yaran nasu cikeda jin dad’i....
Khalid ya dafa kansu su duka biyu kana yace “I know you must’ve watched that cartoon... What’s its name again...?” Ya d’anyi shiru kaman mai tinani kana yace “Frozen..” Harda tsallensu sukace “Yes Elsa and Ana....”
Khalid ya jinajina kai murmushi bai bar saman fuskarsa ba kana yace “Good, just like Elsa and Ana you both are beautiful princesses...” Yaran suka rungumesa gaba d’aya suna fad’in “We love you brother..” Rungumarsu yai wani irin sanyi na ziyartar zuciyarsa.... A b’angaren Daddy ma dad’i ne ya mamaye zuciyarsa, hukuncin da ya yanke na zuwa da Khalid baiyi kuskure ba, kafin washe gari yaran sun sake sun saba sosai da Khalid gwanin nan sha’awa...

A d’aki Daddy yake labartawa Daula halinda ake ciki na maganan auren Khalid d’in da draman da ake da mahaifiyarsa... Tausayin Khalid ya cika zuciyarta, Khalid yanada zuciya mai kyau he deserves to be happy, zataso ya auri macen da yake so... Ta d’an muskuta kana tace “Toh yanzu shikenan kuma sai ka zuba ido a aura masa macen da bai so, haba Abu Humaira ta ya zakai ma d’anka haka...?”

Sauk’e ajiyan zuciya Daddy yai kana yace “For secondo ban tab’a goyon bayan Khalid ya auri Yesmin ba cikin zuciyata, nadai nunawa mahaifiyarsa hakan ne don mu rabu lafiya, kinsan banason hayaniya...”
Mood d’inta ya d’an canza, shin har yaushene mijinta zai daina tsoron matarsa ya soma gudanar da al’amransa tamkar maigida a gidansa... Ganin tayi shiru tamkar wacce tai nisa a tunani yasa Daddy rik’o hannunta kad’an kana yace “Nasan mai kike tunani, Daula wllhi duk yanda naso na takawa Farida birki bana iyawa... Inada zafi a waje wa mutane amma when it comes to Farida nafi k’ank’ara sanyi, duk decision d’in data yanke ji nake yayi... Kimin addu’a please....” Ya k’arashe kaman wani k’aramin yaro... Tausayin mijin nata ya cika zuciyarta, da ciwo Kaga babban mutum haka ya koma tamkar wani lusari.... Rungumo kansa cikin k’irjinta tai kana tace “Kar ka damu Abu Humaira, jarabawace Allah ya baka ikon ci, wataran komai zai zama labari da izinin Allah, bazan gushe ba ina mai maka addu’a da samun sauk’i cikin lamuranka....Amma ga shawari gameda auren Khalid...”
Wannan karon d’agowa Daddy yai yana dubanta sosai....

***

KANO

Ya Abida ta kuma duban k’anwar tata a karo na biyu kana ta girgiza kai tace “Wai shin har yanzu baki daina zuwa min da wannan zancen ba...? Sanin kanki ne abinda kike nema bazai tab’a yuwa ba... A sanadiyarta Iyayenmu suka mutu da bak’in cikina... A sanadiyarta na rasa d’ah na mafi soyuwa a gareni, a sanadiyarta na rasa mijina... A sanadiyarta na rasa duk wani farin ciki da na kasance cikinsa a baya.. Duba duba kiga girman gidan nan babu kowa cikinta, dagani sai tarin dukiya... Babu Magaji... Babu kowa sai halittun tsuntsaye... Tin daga ranan da na rasa Ma’aruf na saka ma raina nima na zama macecciya.... Nake zama cikin gidan nan bana fita ko ina bana sauraren tv ko radio bana rayuwa tareda kowa.... Jira nake nima tawa ta sameni... Na rasa komai, na rasa komai Bara’atu sai tarin dukiyar da Abbas ya mutu ya barmin wanda shima nayi imani da bak’in cikina ya mutu koda bai fad’a min ba... Wacece sila...? Duk wannan abubuwan da suka faru k’anwatace sila..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka..... Da sauri Aunty B ta rungumeta tana mai furta “Shiyasa nace miki lokaci yayi da zaki ci gaba da rayuwa kaman kowa Yaya, lokaci yayi da zaki mance komai, ki rungumi k’addara wala’alla Ma’aruf d’inki na raye kaman yanda Ma’aruf d’in Ya Mariya yake raye, kar ki mance bayan tulin shekarun nan Ya Mariya ta cire Rai daga samun Ma’aruf d’inta sai gashi ta sameshi, Yaya wala’alla naki Ma’aruf d’in ma yana raye... Daga shi har Fatima bamu sake jin d’uriyarsu ba bayan wad’annan shekarun.... Jikina yana bani basu mutu ba, zamu samesu zamu sake had’uwa dasu kaman yanda muka had’uda Ma’aruf k’arami... Lokaci yayi da zaki fita daga wannan rami da kika binne kanki ciki.... You’ve to live again dan Allah Yaya....” Ta k’arashe cikin tsananin raunin murya mai cikeda kuka....
Ya Abida ta kifa kanta tana tunin d’anta mutanen data rasa a rayuwarta a shekarun baya.....

Har Aunty B ta koma gida bata daina kuka ba, tashin hankalin da ita kanta batada cikakken wayo sanda abubuwan suka faru ya dawo mata Sabo, wani al’amari ne da k’addara ta riga fata aukuwa.... Su kuma kalan tasu k’addaran kenan... Shin shi musulmi ba’a sanshi da hak’uri da d’aukar k’addara bane a duk yanda tazo masa...? Shin maiyasa tasu k’addaran tazo a haka...? Shin maiyasa ‘yaruwarta bazata zama mai yafiya da d’aukan k’addara ba....? Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suna masu gangaro mata... Wannan itace k’addararsu..... A haka Zulfa’u ta shigo ta taddata.... Zama tai gefenta zuciyarta nai mata rauni, da matuk’ar wuya kaga hawaye a fuskar Aunt din nata sai abu yakai mak’ura, hannu ta mik’a kana ta rik’o na Aunty B tace “Aunty meke damunki dan Allah... Ki sanar dani....”
Murmushin k’arfin hali Aunty B tai kana tace “Zulfa’u wata rana zuri’armu zata cika, mutanen da muka rasa a baya zasu dawo garemu... Shin Zulfa’u ana mutuwa a dawo...?”
Mamaki ya cika Zulfa jin irin maganganun da Aunty take marassa kan gado....
Dafe hannayen nata tai kana tace “Aunty bansan meke damunki ba, amma ki sani you can always count on me, sabida kema ko Yaushe kina tsaya mana dagani har ‘yan uwana cikin jin dad’i ko akasinsa, Aunty kema bazan barki ba a lokacin da kike buk’atan wani....”
Rungumeta Aunty B tai sosai Hawaye naci gaba da kwaranyo mata..... Cikin zuciyarta take addu’an Allah ya kawo masu wata rana da ahalinsu zasu zama k’ark’ashin inuwa guda kuma su yafi juna....

***

A ‘yan kwanaki biyun da Khalid yai dasu Aunty Daula kaman yanda yake kiran matar Baban nashi sosai suka saba, daga ita har yaran nata sosai Khalid yaji dad’in zama dasu suma kuma sunji dad’in zama dashi har saida Aunty Daula da yaranta suka buk’aci Khalid ya k’ara masu kwanaki, abu kaman wasa sai gashi har sun doshi sati, wani irin rayuwa mai dad’i da babu hayaniya ko tashin hankali cikinta yake experiencing, rayuwar da sam bai samu da mahaifiyarsa da ‘yaruwarsa ba wanda su a kullum son kansu suke ba kaman Aunty Daula da yaranta ba wanda soyayyan ‘yan uwa ya cika zukatansu.... Ji yayi ya sake sosai dasu har bayaso ya baro su, inama zasu had’u gaba d’aya harda Siyama da Ammi suyi irin wannan rayuwa mai ban sha’awa da tarin memories masu d’ad’in tunawa.... Da k’yar su Humaira da Ijlaal sukai sallama da Khalid saida Aunty Daula da Daddy sukaita fama dasu Khalid d’inma ya masu alk’awarin sake visiting d’insu soon sauk’in abin ma su Irfaan cousins d’insu sunzo sai suka d’ebe masu kewan Yayan nasu.... Wasa wasa satityikw sun shud’e, a ko wane b’angare shirye shirye suke gudanarwa, can Kano gidan Abbah shirye shiryen Bikin Sahariyya da Sameer suke dikda cewa a b’angaren ango ba haka take ba, gaba d’aya shi ya yama mance da wani shirin biki da ake yafi bada muhimmanci ga aikinsa Wanda yake ceton rayukan al’umma ne, har yau ko saka amaryar tasa a ido baiyi ba, kaman yanda ba hakan ta kasance ga b’angaren amaryar ba, dikda cewa bata ida warkewa sosai ba hakan bai hanata gudanar da shirye shiryenta ba, daga ita har Haule basu sama basu k’asa, dik wannan buduri da suke Najah dai kallonsu kawai take da matuk’ar sanyin jiki... Anya idan ta bari burin iyayenta na aurawa Ya Ma’aruf Addarta Sahariyya tayi daidai, Ta tina binda taji iyayen nata suna tattaunawa kwanaki a asibiti lokacin kwanciyar Hajiya, tagumi ta rafka tana neman mafita, fad’in gaskiya na daidai da tonuwar asirin iyayenta ne, Toh amma idan tai shiru kuma abin sai yafi muni, ta basu dama suci gaba da b’arna a doron k’asa ne... A hankali ta rintse idanunta tana rok’on Allah ya kawo mata mafita....
A b’angaren Akram ma yanzu kam sun sansanta sosai da Zulfa’u har yana maganan turo magabata dikda cewa itace mai d’an taka masa birki, ga Hafiz ma da har yanzu ya kasa ya tsare sai matarsa ta koma garesa yayinda a can b’angaren Daddy kuma a nan Kaduna ya k’udiri niyyan farantawa d’ansa Khalid koda hakan zai haifar da tashin hankali tsakaninsa da matarsa, duk yanda Siyama taso ta shawo kan Sameer su shirya abu ya gagara, Ammi da Laila kaw sosai suka sa azamar raba Sameer da Siyama rabuwa ta har abada, wannan ya baiwa Laila da Sultan daman cika burinsu (Idan baku mance ba Sultan abokin Sameer ne wanda suka taso a nan Kaduna tare kuma yake cin dunduniyarsa sabida wata manufa tasa)... Wasa wasa har takai Laila ta soma k’ulla wata dangantaka tsakanin Siyama da Sultan dikda cewa sun kwana da sanin tsakanin Sultan d’in da Sameer....
Yauma suna zaune a wani waje na shak’atawa su ukun, sai k’ok’arin cheering Siyama suke wacce gaba d’aya da ganinta kasan hankalinta bai jikinta, mik’ewa Sultan yai kana yace yana zuwa... Laila ta masa wani duba Kafin ya shige.... Dafa hannayenta dake zube saman table Laila tai kana tace “K’awata Wai meye ne haka, dan Allah ki saki ranki baki ganin we’re here to make you feel better, Sultan zaiji babu dad’i idan yaga duk efforts d’insa kina basarwa...”
Da mamaki Siyama ke duban Laila kana tace “Laila kin San abinda kike fad’i kuwa...? Nifa ban gane wannan kyautatawa da Sultan ke min ba bayan duk abinda nayima abokinsa... Ni bansan wayace ki gayyato mana shi ba ma....”
Murmushi Laila tai kana tace “Aw ke yanzu baki gane nufin Sultan akanki ba...? Toh idan baki gane ba ki bud’e idanunki sosai ki fahimcesa... Sultan is trying to give you what Sameer refuses to give you... Sultan zai iya maye gurbin Sameer a wajenki idan kin basa dama kuma ya baki duk wata kulawa da soyayya da Sameer ya kasa baki....”
Wannan karon tsaye Siyama ta mik’e cikin tsananin b’acin Rai take duban Lailar... Lokaci guda take furta “Kin faran shan k’waya ne Laila ban sani ba, da auren Sameer akaina kike cewa na baiwa wani chance waninma of all people abokinsa... you must be insane Laila...”
Kamo hannunta Laila tai ta zaunarta, saida ta gyara zama kafin taci gaba da fad’in “Haba Siyama ya kike neman ki badani, saikace wata ba wayeyyiba, ki dubeki son kowa kin wanda ya rasa, gaki kyakkyawa gaki da karatunki gaki d’iyar masu kud’i... Duk wad’annan qualities d’in kin had’a sannan ki bari wani namiji yake baki wahala, haba Siyama karfa ki mance ke kin juyawa mahaifiyarki baya a sabida shi sannan shi ya kasa defending d’inki gaban family d’insa, think about it Sameer ba sonki yake ba, da ace yana sonki da bai miki haka ba... Da duk wad’annan features d’in da kikeda ki tsaya namiji k’wara yana baki wahala, tell me meye Sameer yafi Sultan dashi, profession d’insu guda idanma kasancewarsa likita ne ya rufe miki idanu kika kasa gameda shi.. Saidai kuma idan kyaun hakittarsa ne ke rud’inki...”
Wani duba Siyama ta watsawa Laila kana tace “Laila sanin kanki ne ban tab’a son wani d’a namiji ba sai Sameer kinsan hakan tin muna high school, banjima kuma akwai wani d’ah namiji da zan mallaka masa gurbin da Sameer ya mallaka cikin zuciyata... I cannot...”
Tab’e baki Laila tai tana dubanta kafin ta mik’e a fusace tana fad’in “Toh gaskiya ni idan bazaki bud’e idanunki kiga abindake faruwa a gabanki ba zan barki da iyawarki, kiyita wulak’anta kanki kan wanda bai d’aukeki da wata daraja ba, Kinga tafiyata.!””” Daga haka Laila tasa hannu ta d’auki jakarta ta wuce fuuu tamkar mai shirin tashi sama... Siyama ta bita da kallo tana kiran sunanta inaa Laila ko juyowa batai ba... Daidai nan Sultan ya k’araso hannunsa rik’eda cup d’in ice cream guda biyu.... Murmushi ya sakar mata kana yace “Ina k’awar taki..?”
Murmushin yak’e Siyamar tai kana tace “Ta ta wuce I guess....”
Sultan ya zauna yana mai aje mata kofin ice cream guda yake fad’in “Too bad gashi na kawo maku ice cream din nan da nake baku labari duk garin nan babu mai dad’insa kuyi tasting da kanku kuji...” Yayi maganar da siga ta barkwanci...
Tak’aitaccen dariya Siyamar ma tai...

Daga yanda Laila ke tsaye shu’umin murmushi tai kana ta ciro wayarta cikin jaka ta shiga kashe masu hotuna lokaci guda take furta “Saini Laila amaryar Sameer... Bani sa abu a gaba naga kasawa, na sami shaidu k’warara da zanyi amfani dasu wajen datse aurenki da Sameer, na farko shaidar zubar masa da ciki da kikayi na biyu cin amanansa da abokinsa...” Ta kuma tintsirewa da dariya had’ida jefa wayarta cikin jaka kana ta bar wajen....

SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_





*78*



Gaba d’aya Hajiya Haule da Baba Alhaji sun hura wuta sosai kan maganar auren Sameer da Sahariyya, babu yanda Abbah baiyi ba su d’an k’ara lokaci amma inaa sun azalzala ayi ayi auren, ko Sahariyyar dake matuk’ar d’aukin auren bata rawar k’afar da iyayenta keyi gashi har rana mai kaman ta yau basuga idon ango ba, Hajiya Haule ta tasa Baba Alhaji gaba da cewa yaje ya sami k’aninsa da batun, don gaba d’aya basu san wanne Sameer ke ciki ba....
Hafiz dake gefe ya cika yayi fam sai hura hanci yake yana aikama iyayen nasa kallon wulak’anci....
Hajiya takai dubansa garesa yanda ya cika yai fam kana tace “Kai kuma fah....?”
K’wafa yai a hankali “Amma Hajiya gaskiya ni baku kyauta min, nayi abinda Baba Alhaji keso na maida tsinanniyar can d’akinta maiyasa ni baza’a cika min nawa burinba, maiyasa za’a min alk’awarin dawo min da matata kuma ak’i cikawa... Idan duniya da gaskiya idan ba wani al’amarin kuke b’oyewa gameda aurawa Sameer Sahariyya ba ai nima sai ku hura wuta a had’a auren da nawa...”
Hajiya ta tab’e baki kad’an tana duban Baba Alhaji kana tace “A’ah toh, ai ga Baban naka... Babu yanda banyi ba yayi maganar dawoda Zulfa’u amma yayi k’ememe yayi banza dani, bansan wata kalar muguwar asiri Magajiya da d’iyarta suka hura masa ba... Gashi nan tambayesa kaji daga bakinsa....”

Baba Alhaji dake muzurai cikeda fad’a ya soma fad’in “Ni ba wai nak’i Zulfa’u ta koma gidan Hafiz bane, ince shika uku ya mata, a ina kuka tab’a jin anyi shika uku an gyara aure... Kuma banda abinka me ita wannan yarinya Sawwama ta rageka dashi...”
Baikai aya ba Hafiz ya mik’e cikin hura hanci da d’aga kafad’u sama yake fad’in “Nifah Baba Alhaji saki d’aya tak naiwa matata don haka babu wanda ya isa yace bazan iya maidata ba, kuma idan bazaka sa baki ba a had’a aurenmu da Sahariyya wllhi wllhi kaji na maka rantsuwa zan tono ko mene shirinku kuma zan fallasaku a bainar jama’a, sannan bayan haka zan rabuda Sawwama ta hanyar da bakai zato ba...” Ya k’arashe tamkar zaikaiwa mahaifin nasa bugu, sai faman hura hanci da d’aga kafad’a da wuya yake....
Hajiya da ‘yan hanjinta suka kad’a don tasan tsaf Hafiz zai aika abinda yace, idan yaso tsaf zai binciko sirrinsu, murmusawa tai kana tace “Sha kuruminka d’ah na idan dai Zulfa’u ce ta koma gidanka an gama babu shegen da ya isa ya datse aurenku, ince nice nan sanadin rabuwarku, toh ka kwantar da hankalinka aurenku ya koma an gama... Ka kwantar da hankalinka kaji d’ah na Zulfa’u ta dawo gareka an gama...”

Murmushi da gefen baki Hafiz yai yana wani jijjiga shi kad’ai kana yace “Ku tabbata zaku cika alk’awarinku, don idan ba haka ba....” Ya kuma yin wata murmushi kana yace “Wllhi tallahi billahi zan mance ku iyayena ne, zan kuma iya zama barazanaga rayuwarku....” Daga haka sa kai yai ya fice daga gidan gaba d’aya....
Hajiya Haule da tashin hankali ya nuna k’arara ta fuskarta ta dubi mijinta “Kanaji abinda yake fad’i koh.... Toh wllhi tun wuri kasan yanda zakaida yaron nan don ko shakka banayi Hafiz zai aika dik abinda yace... Uban da yace kasashi maido da wancan hatsabibiyar yarinyar, sanin kanka ne idan yaso sai ya bankad’o duk wasu sirrika da muka jima muna aza masa k’asa...” Daga haka ficewa tai fuuu bata tsaya sauraren mijin nata ba...
Tashin hankali ne sosai ya wanzu saman fuskar Baba Alhaji... Tirk’ashi, aiko bazaiso Hafiz yasan cewa nada wani bak’in k’ulli a zuciyarshi ba, kama daga ‘ya’yansa har zuwa ‘yanuwansa kai harta jama’an gari sai sun k’yamacesa shida baida burin ya zamto mutumin da al’umma zatai alfahari dashi dukda hakan ya kasa samuwa a gareshi, wannan d’aukaka ta d’anuwansa da yake burin ya zamto shikeda ita sam bai samu ba, yanzu asirinsa ya tonu kuma ai shikenan babu mai kuma masa kallon yanada wani kima.... Yarfe zufan daya tsartsafo goshinsa yai kana ya mik’e ya shiga aza babbar rigarsa bai zarce ko ina ba sai gidan Abbah...

Abbah ya jinjina kai a hankali “Ban tari numfashinka ba Yaya, amma gameda Zulfa’u bazan canza zancena ba, zan kirawota muji daga bakinta, karka mance Shari’a ta bata damar zab’awa kanta miji, zab’an mijinta ba a hannunmu yake ba, iyakaci namu mu gudanar da bincike mu kuma bata shawari, amma banda maganar tilastawa...”
Kad’a ‘yar yatsarsa kurum yake yana duban d’anuwan nasa, baisan wace irin shegiyar taurin zuciya Usman kedashi ba, tin suna yara haka nan yakeda kafiya akan kalamansa, idan yayi magana toh ita kenan guda d’aya, sanin kansa ne wasu abin d’aga masa k’afa yake matsayinsa na wandake gaba dashi...
Baba Alhaji ya kuma gyara zamansa had’ida fitowa kad’an daga cikin kujeran ba tareda ya janye idanunsa daga duban Abban yake fad’in “Ina ita Zulfa’un take....?”

“Tana can Gwammaja gidan k’anwar mahaifiyarta Bara’atu...” Cewan Abbah dake k’ok’arin danna remote d’in tv sakamakon wutan nepa da aka kawo...
Shiru Baba Alhaji yai tamkar mai nazari kana yace “Lallai lallai ta tattara ta dawo gida, idan yaso gobe idan Allah ya kaimu sai mu zauna gaba d’aya mu tuntub’eta muji idan akwai wanda take so ne, idan kuma babu bazamu zuba mata ido ta tare gidan Bara’atu da ita kanta tarbiya bawai ya isheta bane, ni sam ban yarda da tarbiyarta ba balle har a bata rik’on yarinya.... Sannan shi kuma Sameer d’in idan ya shigo sai ka sanar dashi lallai lallai ina nemanshi...” Daga ida fad’in haka mik’ewa yai yana sab’a babbar riga ya nufi k’ofa...
Jinjina kai kurum Abbah yake yana mai fad’in “A sauk’a lafiya Yaya....” Ko amsashi bai sami zarafin yi ba ya fice cikin sauri tamkar wanda ake ingizasa...

Daga nan bai zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Magajiya, yau zuwansa na uku kenan saidai tarban da ya samu yau yasha bambam da zuwan da yai sai biyu a baya.... Ta fito parlorn cikin kwalliya na kece raini kaman kullum, sai watsa k’amshi take dikda k’aurin hayak’in wuwi da sigari da hancinka ka iya shak’o maka, don k’amshin tiraren daban yake tashi haka ma warin k’ayan mayen, koda Baba Alhaji ya tambayeta sai ce masa tai yaran mak’otanta ne marassa jin magana saitin windows d’inta suke zuwa su hura hayak’insu.... Ta marairaice fuska sosai kana tace “Alhajina shin wai baka yarda dani bane...?”
Baba Alhaji ya murmusa “Na yarda dake mana Magajiya, ni abinda ban gane ba yau d’in naga sai b’ata fuska kike ko wani ne ya tab’a min ke....?”
Rausayar da idanu tai cikeda kisisina da salo na kashe murya take fad’in “Toh ba d’anka Hafiz bane yake gurza ma tilon d’iyata wulak’anci ba, har yau zaman doya da manja suke sam yak’i aminta da ita bacin duk magiya da kwantar da kai da take masa.... Ni tsoro nake kar yace zai kuma rabuwa da ita a karo na biyu...” Ta k’arashe tana wani rau rau da idanu tamkar budurwa mai tashen k’uruciya....

Baba Alhaji ya murmusa ya kurb’i lemu mai sanyi da aka kawo masa kana yace “Idan don wannan ne karma ki d’aga hankalinki, na riga na gama magana da Hafiz, kafin nazo nan ma maganar da mukai kenan, aurensa da Sawwama mutuwace kawai zata raba muddin ina numfashi... Ki kwantar da hankalinki kuma ki sanar da ita Sawwamar ta kwantar da hankalinta babu uban da ya isa ya raba aurenda na maida koda kuwa Haule ce....”
Wani shu’umin murmushi Magajiya tai kana tace “Da gaske Alhajina...?”
Jinjina mata kai yai yana mai janyo parantin cake da aka ije gabansa....
Dad’i kaman ya kashe Magajiya cikin sauri ta mik’e ta d’uki tray d’in tana wani kareraya take k’arasowa gabansa had’ida fad’in “A’a yi zamanka Alhajina bara na mik’a maka wannan ai aikina ne....”
Baba Alhaji ya kuma Washe baki yana kad’a kai cikeda jin dad’i yake fad’in “Allah ko Magajiyata... Anya kuwa bazaki sa na soma jina kaman saurayi d’an ashirinda ba....”
Ta kuma rausayar da idanu tace “Ai kafi haka a wajena, Allah dai ya nuna mana ranan da zan shiga gidanka Kaga soyayyar da baka tab’a cin karo da irinta ba....”
Haba nan fah Baba Alhaji yaci gaba da washe baki yana k’yak’yata dariya cikeda nishad’i yana mai ci gaba da kod’a Magajiya....

***

Wayar na manne kunnenta na hagu tayi shiru alamun tana sauraren magana daga d’aya b’angaren, cikin sanyin murya irin tata tace “Mamy Abbah kuma..? Mamy cewa

Please Login or Register in order to submit comment