Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani irin tsinkewa....




SameenaAleeyou 📚





*INDA RAI*
_................DA RABO_



*75*




“Wacece ke...?” Kalmar da Raihana taji an fad’i kenan daga d’aya b’angaren... Tamkar wacce aka zabura haka tai zumbur ta ware idanunta, ragowar baccin taji ya watse, lokaci guda ta nemi baccin da takeji ta rasa... Kasa furta komai tayi sai raba idanu da take tamkar mage a tukunya....
Siyama da tuni jikinta ya d’auki rawa sabida tsananin tashin hankali da kishi da suka sauk’ar mata lokaci guda, cikin wani irin murya mai cikeda kaushi take kuma furta “Nace wacece ke...? Sannan mai ya had’aki da wayar mijina..?!!!”

Jin Siyama ta ambaci wayar mijinta ya kuma sa gaban Raihana fad’uwa, k’irjinta tamkar wacce aka ije mata k’aton dutse... Cikin sauri ta cire wayar daga kunnenta tana duban screen d’in, k’ara karanta sunan tai Partner... Da sauri ta rintse idanunta tana mai dafe kanta da jinjna wauta irin tata, sam bata kawo sunanta Partner matarsa ya sakawa ba... Tana jiyowa daga can b’angaren Siyama naci gaba da fad’in hello hello... Bata iya amsata ba sai katse kiran da tayi cikin sauri, ta koma mazauninta da sauri tana mai ci gaba da rarraba idanu don haka kurum muryar matar tasa ya mugun firgitata....

A can kuwa Siyama tsaye ta mik’e tana kuma neman layin Sameer but still ba’a d’agawa, k’oluluwan tashin hankali takai, a iya rayuwarta abinda take tsoro ace Sameer ya soma biye biyen mata, a yanda take da muguwar kishin mijinta tabbas tasan zata iya yin komai to keep him all alone for herself.... Aunty Lami ta kafeta da idanu kana ta d’an gyara zama had’ida matsowa kusan Siyama da gaba d’aya bata a hayyacinta kana tace “Ya mijin naki....?”
Wani irin duba Siyama ta watsa mata ba tareda tace komai ba....
Aunty Lami ta murmusa, tsaye ta mik’e ta matsoda bakinta saitin kunnen Siyama, cikin sigan rad’a take furta “Kiyi hattara da ahalin gidan nan suna gab da rabaki da Sameer, amma shawarice idan kin d’auka....” Tana ida fad’in haka ta saki murmushi kana ta fice salin alin.... Kallo Siyama tabita dashi har ta b’ace ma ganinta kafin ta fuzar da iska mai zafi...
Muryar wata Dattijuwa ce ya katseta daga duniyar tunanin neman mafitawa rayuwarsu ita da Partner da tai.....

Nabilah na rik’eda Mamani yayinda Mamani taci gaba da dogarawa tana fad’in “Wai ina kishiyar tawa takene...? Tinda kishi ya hana ta shigo ta gaidani gani nan ni zan shigo na gaidata da kaina.... Ke Mariya ina kika b’oye min kishiyar tawa ce...?”
Nabilah dake rik’eda ita tana murmusawa take furta “Kedai mu shiga daga ciki Mamani kinsan kishiyar taki taci uwar gayu tafiya ma wahala ke mata....” Ta k’arashe maganar sanda take taimakawa Mamani ta zauna saman kujerar gefen Siyama...
Banda huci da tururi Siyama bata komai, sai aikawa Nabilah kallon tsana da take, Nabilah kaw ko ajikinta murmushi ne fal fuskarta....
Gyara zama sosai Mamani tai had’ida kaikaitowa tana fuskantar Siyama, ta kuwa washe baki takai duka hannayenta biyu ta kamo hannayen Siyama, cikeda jin dad’i take furta “Allahu Akbar... Oh ni Halimatu ashe dai rana irinta yau zatazo... Ashe zanga matar Ma’aruf kafin na bar duniya... Saura kuma naga d’iyoyinsa.... Sannu kinji ‘yar nan...” Ta d’anja fasali jin Siyama ta mata dinkim bata amsata ba saima ta mujiya data zuba mata tamkar taga wani halitta daga wani planet....
Juyowa tai ta dubi Nabilah dake k’ok’arin k’unshe dariyarta Marliya na girgiza kai wa Nabilar kana Mamani tace “Ke Nabilatu Wai bata magana ne...? Kodai kishiyar tawa bihim ce... Ya ina mata magana ta zuba min wannan pici picin idanun nata kaman ni na sammata, wannan badon tsufa danai ba ma nawa idanun sunfi nata girma...”
Ta k’arashe tana mai gwalalo idanunta a fuskar Siyama wacce lamarin Mamani ya soma bata tsoro...
Daga Marliya har Nabilah kasa rik’e dariyarsu sukai...
Mamani ta juyo garesu tana fad’in “Kai bani son k’aniya... Ku fad’a min meke faruwa a nan... wacece wannan...? Idan kuma yaren da nake ne bataji kuzo ku mata wanda zataji kafin na tashi na sassab’a maku...!!”
Nabilah tai k’ok’arin saita kanta kana tace “Mamani kinsan kishiyar taki girman turai ce yawo cikin gajimare k’ila dai bata fahimtar abinda kike fad’i ne... Ki canza mata harshe...”
Mamani ta maida dubantaga Siyama wacce ta kasa d’auke idanu daga barin duban Dattijuwar kana tace “Auho kice min dangin nasara Ma’aruf ya auro... Ke kaw kinsha bamabam da Haladu yaron arziki... Da kika tashi zuwa cikin danginsa sai ki koyo yaren da suke fahimta... Fi’ilin banza da wofi, yo har ni za’a nunawa yaren jajayen kunne... Ke barikiji na fad’i miki sanda Mammadu na ke raye babu kalan hazon da bai k’etara dani ba... Yo maima kuka samu ‘yan k’arshen zamani....”
Ganin Mamani ta saki layi ta fara zuba masifa yasa Marliya duban ‘yar uwarta Nabilah da duniyar tai mata dad’i gamon da takeso Mamani da Siyama, girgiza kai kurum Marliya tai kana tace “Mamani Aunty Siyama tana saurarenki kawai dai baki bata dama tayi magana bane tintinin ke kiketa magana tin shigowarki babu ko hutawa..... Kuma zataje gaidaki kenan sai gaki nan kin shigo...”

“Ke dalla chan rufe min baki, uwar kinibibi, yo gani zabiya ko mai...? Inyi...?” Tai maganar tana mai tsare Marliya da idanu....
Cikin sauri Nabilah ta kamo Mamani tana fad’in “Mamani muje kinji zata shigo har sashenki ta gaisheki idan bata gaisheki a nan ba, wanda zai sata na dole na zuwa....” Ta k’arashe tana mai watsawa Siyama muguwar kallo....
Mamani ta mik’e tana ci gaba da sababi da yab’awa Siyama mugayen maganganu...
Suna tafe sashenta take ci gaba da fad’in “Inyi kajimin ja’irar yarinya, yo wannan badon Yayanku yace min ‘yaruwar Haladu bace sai nace babu abinda ya had’asa da wannan mai k’irar zabon, Banda Farin fata da dogon hanci banga mai Yayanku ya gani tattareda wannan mai k’irar itacen ba, ko ni nan a haka nafita kyaun gani....”
Nabilah ta gyara mata cushion tanaji Mamanin naci gaba da sababi har ta zauna kana ta umarceta ta nemo wayar salulanta ta kirawo mata Yayansu Ma’aruf gashi su Najah sunce shine yaje makaranta ya d’auki Raihanah kuma har yanzu basu dawo ba, ga wannan matar tasa mai suffan karan rake data kuma b’ata mata zuciya....
Sake kira Nabilah tai tace da ita wayar bata shiga....
Mamani ta jinjina kai tace “Ko wata duniyar yakaimin jika oho.... Kodashike jika na yaron arziki ne bazaiyi wani abu maras kyau ba, Allah sa dai lafiya suke yanda yanzu duniyar tamu ta koma....”
Nabilah ta amsada Ameen dai Mamani, k’ila kiran gaggawa akai masa daga can asibitin nasu sai ya wuce da ita....ta k’arada kinason wani abu ne...?”
D’an dubanta Mamanin tai kana tace “Kunna min talabijin na rage takaicin wancan zabuwar matar Yayan taku....”
Dariya ya kusan kufcewa Nabilah, kunna mata TV d’in tai ta silale ta fice don tanaji har lokacin sababi take....

A can parlorn Abbah ma jajen rashin dawowar Sameer d’in da Raihanan suke ga kuma wayarsa da bata shiga, sannan ga matarsa data bayyana wanda sam Sameer d’in bai sanar dasu zuwan nata ba.....
Mamy ta kuma dialing wayar amma bata shiga... Jigum tai tana mai furta “Allah sa dai lafiya suke...”
Abbah dake faman zagaye parlorn hannayensa hard’e a baya iska ya fuzar kana yace “Amma ai koda emergency ne ya taso masa sai ya kira ya sanar damu don kar mu damu, ba ya d’auki yarinya ya tafi da ita...”
Mamy tace “Alhaji Raihanah fah patient d’insa ce ta yuwu zuwa asibitin da ita ne ya kama shisa ya tafi da ita...”
Abbah yace “Wannan duk ba hujja bace....”
Bata kuma cewa komai ba sai sadda kanta k’asa da tai....
Abin magana da bai kasawa a gidan, tuni an soma yayatawa tsakanin sashensu Basma su Sakina, Ya Ma’aruf ya d’auki Raihanah daga islamiya ba’asan yanda sukaje ba ga matarsa ma nan gidan tana jiransa.... Lami ma tuni tayi waya ta shafawa k’awarta Haule halinda ake ciki.....
Haule kaw tace bataga ta zama ba, dama ya samesu, dole suyi amfani da wannan damar....
Sahariyya da Hajiya ta ida wayar a gabanta bore ta dingayi tana fad’in wllhi sai taci uwar Raihanah muddin bata janye idanunta kan Ya Ma’aruf, shegiya k’onanniyar banza....
Najah dai batace uffan ba saima mik’ewa da take k’ok’arinyi.... Sahariyya ta janyota daga nan yanda take zaune tace “Munafuka hardake kuke had’e kai da wancan k’onanniyar... Shine dan munafunci ko ki fad’a min shi yaje islamiyar taku ya d’auketa.... Toh wllhi idan za’a mutu ni ce nan zan aureshi kuma sai na mata iyaka da mijina....”
Najah kallonta’yaruwar tata take kana ta tintsire da dariya tace “Addah Sahariyya kina bani dariya Wllhi, shin duk fah wannan kunfan baki da hura hanci da d’aga jijiyan wuya da kike shifa Ya Ma’aruf d’in baima San kinayi ba, kuma ai inaga ba akan Raiha zaki d’aga hankali ba, kan matarsa data iso zaki d’aga hankali, indai Raihanah ce na rantse miki bai d’auketa matsayin komai ba face ‘yar k’aramar k’anwa kuma patient d’insa da yai treating d’inta....Ki tada hankali kan Aunty Siyama wacce taji gayu tasha gayu ta k’oshi, ki soma tunanin yanda zakiyi gogawa da ita wajen kishi amma ba Raihanah ba...” Ta k’arashe tana mai janye hannunta had’ida kuma tintsirewa da dariya....
Jikina sanyaye Sahariyya ta sakar mata hannu, tana mai k’arewa kanta kallo maganganun Najah na mata yawo a kwanyarta cewa tai tunanin idan zata gogawa da matarsa wacce take ‘yar gayu wajen kishi.... Kai dole koda d’ingishi ne sai taje taga matar Ya Ma’aruf taga kalanta.... Ta d’aga kai tana duban Hajiya dake faman cangwala k’afafu da k’yar tana kuma aza mayafi lokaci guda ta dubi Sahariyyar tace “Idan Alhaji ya dawo kice na tafi can gidan....” Ai bata kai aya ba Sahariyya ta katseta da fad’in “Nima zanje Hajiya...”
Haule ta dubeta shek’ek’e kana tace “Da wannan k’afar taki da bata ida warkewa ba, idan abin gudu ya biyomu a hanya nayi yaya dake...?”
Sahariyya batako kulata ba ta rarrafa ta d’auko wata sandar gora da Hajiya ke jinginewa bayan k’ofa ta dafa tace “Wllhi sai naje naga matar tasa naga mai zata nuna min....”
Tsaki kurum Hajiya tai don ta yadda Sahariyya ta gama haukacewa kan Ma’aruf, ita batama san a halin yanzu so take ta janye yunk’urin had’in yaranta da Ma’aruf d’in dataso ayi muddin ta sami hanyar salwantar dashi cikin sauk’i.... Ko sauraren Hajiya bata kumayi ba ta soma dogarawa tai gaba abinta... Hajiya ta take mata baya cikin cangwala k’afafu itama don dukansu biyu basu warke daga jinyar da suke ba....
Kallo Najah tabisu dashi had’ida girgiza kai tanai masu addu’an shiriya...

Tana zaune Sahariyya ta shigo tana faman kumbure kumbure tana mitan Baba Alhaji ne ya korota yabi Hajiya suka tafi gidan Abbah

Najah dai batace komai ba sai k’unshe dariyarta da tai, Sahariya ta galla mata harara tana fad’in “Dariyar mai kike...?”
Najah tace “Allah baki hak’uri ta Ya Ma’aruf...”
Wannan suna da Najah ta kira Sahariyya dashi sai taji gaba d’aya bak’in cikinta ya yaye...

***

A can asibiti kuwa tinda ta amsa kiran matarsa mistakenly bata kuma bi takan wayarsa ba, ta matsu baizo sun tafi ba, babu kalan tagumin da batayi ba, alla alla take yazo yakaita gida... Tana nan zaune tana tunanin taji an turo k’ofa, muryoyinsu takeji wanda ko ba’ace ba shida abokin aikinsa ne, tanajin abokin nai masa sallama had’ida masa tinin wani conference na likitoci musamman surgeons da zasu halarta gobe....
shab shikam yama mance da wata Raihanah, har saida ya danno kai cikin Office d’in kafin ya tuna ashe tare sukazo, yai saurin kusto kai cikin Office d’in yana tunanin halinda ‘yar mutane da ya barta a ciki take....
Aiko tana ganinsa ta mik’e zumbur tamkar wacce aka zabura...
Idanu suka k’urama juna kafin Raihanah tai saurin sadda nata idanun k’asa.... Fuzar da iska ya d’anyi kana yace “Sorry na barki jiran office, bansan zan jima haka ba... Aikin ne yazo da complications...”
Cikin sauri ta soma girgiza kai kana tace “A’a babu komai Yaya.... Idanma ka jima ai ceton rai ka tsaya yi, nasan ciwo da rad’ad’in k’unan wuta wanda bana fata ko mak’iyina ne yayi experiencing abinda naji... Da fatan aikin naku ya tafi yanda kuke so....?”
Idanunsa akanta tamkar mai nazari kana ya jinjina kai a hankali yace “It was successful....”
Yana kallon bakinta yanda take furta “Alhamdulillah” a hankali....
Kaman babu mai cewa komai cikinsu sai kuma yace “Muje nakaiki gida nasan suma sun damu....”
Tamkar wacce take kan k’aya tai wuf ta nufi k’ofa tana mai jinjina kai....
Sameer ya kuma binta da kallo kana ya knarasa table d’insa ya d’auki wayar salulansa da ya mance nan.... Baiji mamakin ganin tarin kira ba don hakan ne wasu lokuta kan kasancewa dashi idan ya shiga aiki ya mance wayar a kunne... Jefata a ljihu kurum yai kafin ya takewa Raihanah baya ya rufo office d’in....

Suna tafe yana observing d’inta yanda take taka k’afar nata... Sunanta taji ya ambata for the first time wanda ya haifar mata da fad’uwan gaba ta kasa ci gaba da tafiya....
Sameer ya k’araso bai janye idanunsa daga k’afar nata ba....
“Sau nawa Salma ta miki dressing yau..?” Ya tambaya still idanunsa akan k’afar nata wanda ke rufe cikin uniform d’in islamiyarta....
Ba tareda ta d’ago ta dubesa ba tace “Yau batazo ba dama taje akwai yanda zataje yau d’in bazata samu zuwa ba....”
Jinjina kai yai a hankali kana yace “Kenan yau ba’ai dressing ba...?”
Nanma jinjina masa kai kurum tai still idanunta na k’asa....
Still yai tamkar mai nazari sai kuma yace “Biyoni....” Yai maganar yanabin wata k’ofa....
Babu musu ta take masa baya dikda bugu da k’irjinta keyi, tana mai zullumin ina kuma suka nufa...
Dressing room taga an rubuta a k’ofar yanda suka nufa, kasancewar dare ne shiyasa babu jama’a sosai a asibitin, nurses d’inma wanda suke duty basu da yawa kaman na rana, da alama ma babu kowa cikin d’akin.... Offices d’in da suke wajen ya d’an lellek’a ko zai sami wacce zata mata dressing amma shiru bai samu ba...
Ita dai kallon ikon Allah kurum take, tana gani ya isa jikin wasu drawers ya soma d’ibo kayan aiki, innalillahi ai nan bugun zuciyar Raihanah ya k’aru, mai Ya Sameer ke k’ok’arin yi... Kaman wanda yasan tinanin da take... Idanunsa naga bandage d’in da yake had’awa yace “Tsorona kike...? I can hear your heartbeat.... Don’t worry I promise to be gentle....” Ita dai batace komai ba saima kallon hannunsa da take yanda yake shirya kayan dressing d’in... Sameer ya murmusa da gefen bakinsa still idanunsa naga abinda yake yace “Next time idan Salma ta sanar dake bazata sami zuwa ba ki sanar dani right away kinji koh, ya riga ya fara healing idan an bari aiki zai koma baya...” Jinjina masa kai kurum take amma sosai k’irjinta ke bugawa....
Ya d’ago idanunsa yana dubanta, sosai tsoro ya wanzu saman fuskarta, idanunta suka kuma firfitowa waje... Tinani take ta yanda zata fara bud’e k’afarta gashi kuma wando ne jikinta... Innalillahi itakam bala’in kunyarsa takeji, tsaye yayi yana nazarinta kaman wanda yasan tinanin da take.... Suna a haka muryar Awwab da wata nurse Christian wanda suka fito daga theatre tare ya katsesu... Mamaki ya cika Awwab ganin Sameer a d’akin dressing
“A a Doc you still here, baka tafi ba wai....I thought ka tafi tuntunin.... Wait what are you doing here....?” Sam bai lura da Raihanah dake zaune gefe ba yaketa jerowa Sameer wad’annan tambayoyi...
“Kaman muryar Margret naji, ko ba tare kuke ba...? Sameer ya bid’a ba tareda ya amsa d’aya daga cikin tambayoyin Awwab d’in ba....

“Eh tare muke she’s on duty....” Awwab yace yana mai duban Sameer d’in
“Akwai wani abu ne...?” Ya tambaya yana kuma suban Sameer d’in....
D’an turo baki gaba kad’an yai had’ida duban cikin d’akin yanda Raihanah ke zaune... Le k’asa Awwab yai ya hango Raihanar....
“Who’s she...?” Awwab ya tambaya yana mai duban Sameer d’in..... Turasa Sameer yai suka fice gaba d’aya yana fad’in “Zaka kiramin Margret d’in ne tai mata dressing... I’ve to take this call...” Ya k’arashe yana k’ara wayar Abbah a kunnensa
Da fad’a Abbah ya soma masa cewa ina ya d’auki Raihanah ya kaita, ga dare kuma bai sanarda kowa ba....
Sameer ya d’an sosa k’eyarsa kad’an kanshi a k’asa kaman Abban na kallonsa “Em Abbah ai hak’uri, kiran gaggawa na samu daga asibiti, amma gamu a hanya in sha Allah....”

Abbah yace “Naji wannan, matarka kuma fah...? Kasan da zuwanta baka sanar damu ba....?”
Sameer ya ware idanunsa a hankali “Abbah matata kuma...? Kana nufin Siyama tazo gida....?”
Daga d’aya b’angaren Abbah yace “Baka san da zuwan nata ba kenan....?”
Sam baiso iyayensa su fahimci wane irin zama suke da Siyama, k’ok’arin saita kansa yai kana yace “Oh...Har ta iso kenan... Kuyi hak’uri Abbah ban kawo maku ita da kaina ba amma gani a hanya in sha Allah....” Daga haka sallama sukai da Abban yana mai duban Mamy da tai jigum tana jiran ya ida wayar....
Mamy tace “Asibiti yake koh....?”
Jinjina mata kai kurum Abbah yai kana yace “Mariya akwai abinda na fahimta a rayuwar auren yaron nan.... Kaman auren nasa cike yake da tarin matsaloli....”
Ajiyan zuciya Mamy ta sauk’e a hankali “Nima nayi tunanin hakan tin sanda nai ido biyu da iyalin nasa, kuma bai kawo mana ita duk tsawon lokacin nan ba... Nayi tunanin na tambayesa sai kuma naga ba hurumina bane...”
Jinjina kai Abbah yai a hankali kana yace “Wannan hakan matsalarsu tasu ne, ina fata su zamto masu warware matsalolinsu da kawunansu basai wani yaji ba...”
Ta jinjina kai ba tareda ta furta komai ba sai nazarin abin da take....

***


Tsare Akram tai sosai da manyan idanunta tanai masa kallon tuhuma,lokaci guda kuma ta saki murmushi ta mik’e ta nufo yanda yake.... Gefe dashi ta zauna tana wani karkad’a jiki murmushi bai bar saman fuskarta ba....
“Akram I’m a business woman, sanin kanka ne ban dogara da dukiyar da mijina keda ita ba, inada tawa dukiyar.... Kuma ina mai tabbatar maka I can make you what your boss fails to make you.... Idanma baka son wannan I can offer you something more than that.....” Ta k’arashe tana kashe murya had’ida kashe masa idanu guda....
Mik’ewa tsaye yai yana mai murmusawa da gefen bakinsa kana yace “Duk ba sai kinyi wad’annan ba Hajiya, never bazan tab’a cin amanan Excellency irin haka ba, but rest assure auren da mijinki yake nema bazai tab’a yuwa ba.... Here is my plan....” Ziryan ziryan ya zayyano mata yanda abin zai kasance.....

Ta saki murmushin jin dad’i kana tace “Who’s she... who’s the girl, sanar dani...”
Nanma murmushin yai da gefen bakinsa kana yace “Sanin ko wacece ita to you is not necessary, just trust me, auren bazai tabbata ba....”

Mik’e k’afa guda tai tana mai ci gaba da kad’a k’afar tata take furta “And I’m ever ready to support you financially, duk wani abinda ake buk’ata daga lefe zuwa sadaki zan baka kai har gidan da zaka ajeta ni nan zan baka....”

Nanma dai murmushin yai kana yace “Karki damu Hajiya I’ve everything under control, idan bazaki damu ba ni zan wuce....” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye....
Muhibbah ta kuma sakin shu’umar murmushi kana tace “Naji dad’i da muka kasance on the same page.... And let me remind you this, ka tabbata ka cika alk’awarinka idan ba haka ba, you’ll both lose her daga kai har boss d’in naka... Coz when it comes to my husband I can be very dangerous.....” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta...
Shid’inma murmushin yake kafin ya d’an tako gabanta kad’an, murmushin bai gushe saman fuskarsa ba hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa na jampa yake furta “You don’t want to have me as an enemy, coz I can expose your little secret... I know exactly the kind of business you run.... So idan baki so mijinki yasan musabbabin yawon k’asashen da matarsa keyi da sunan business trips, kada ki kuskura ki shiga hurumin Zulfa’u...”

Zaro idanu waje tai tana dubansa da tsananin mamaki, ta had’iyi miyau da k’yar don batai tsammanin Akram zai iya sanin wannan sirri nata da ko danginta basu sani ba...
Bai daina murmushin ba ya furta “Just a piece of advice, do not double cross me...” Daga haka sa kai yai ya fice daga parlorn cikin sauri.....

Muhibbah ta sauk’e huci mai zafi ga kanta da ya d’auki chaji lokaci guda... Cikin sauri ta haura sama ta nufi drawer d’inta ta d’auko k’wayar had’ida tsura masa idanu... Lokaci guda ta shiga b’allewa tamkar zararriya haka ta shiga afawa a baki, saida ta afawa kusan hud’u lokaci guda kafin ta zube saman gado had’ida lumshe idanunta....

***

Daga bakin k’ofa yaja ya tsaya ganin har Sawwama ta dawo gidan, hularsa a karkace ya hard’e hannaye k’irji had’ida jinginuwa jikin k’ofar yana k’are mata kallo, kana ganinshi kasan yau a Hafiz d’insa ya fito....
Sawwama dake faman goge kayan kallo sam bataji motsin shigowarsa ba har saida ta mik’e zata nufi d’aki nan ta ganshi k’ik’am tsaye akanta ya kafeta da idanunsa masu sumar da ita....
Sosai ya mata kyau don tayi kewarsa sosai, tai saurin mik’ewa ta nufesa tana mai furta “Hafizina bansan kana tafe ba da na girka maka wani abin.... Muje ka kwanta ka huta yanzu zan shiga kitchen na dafo maka abinci mai sauk’i, kar ka damu Magajiya ta had’oni da duk wani abin buk’ata....” Kasa k’arashe maganan nata tai jin ko motsasa daga yanda yake ta kasa... Ta d’ago tana dubansa da mamaki, ta d’an saki murmushi kad’an....
“Lafiya dai Hafizina...?”

“Uwarki ne ba lafiya...”
Kalmar data sinkaya kenan daga bakin Hafiz, gabanta ya yanke ya fad’i... Sai yanzu ta tuna babu wani shirin asiri data dawo dashi gidan.....
Ta saki murmushin yak’e “Haba Hafizina na riga na baka hak’uri, nasan muna son junanmu.... Mu baiwa maras d’a kunya muci gaba da zaman aurenmu, nai maka alk’awarin duk wasu abubuwa marassa kyau da nake a baya na dainasu daga yanzu, zan kula dakai yanda baka tsammani Hafizina....” Ta k’arashe tana marairaicewa.....
Tamkar wanda ya tina wani abin ya murmusa da gefen bakinsa, ta gefenta ya rab’a ya shige cikin d’ajin yana wani faman k’obarewa.....
Sawwama ta bisa da kallo dikda cewa tasha jinin jikinta da ganin yanayin Hafiz d’in.......

***

A can gidan Abbah kuwa a parlorn Abban Mamani ta ritsa Sameer da iyayensa, ta yanda take shiga bata nan take fita ba, fad’i take “Inyi toh Wllhi sam bazata saku ba, wannan ai gubace ba macen zaman aure ba, ni nasan irin wannan matan barikin sam ba kunya bace dasu.....”
Baba Alhaji ya tari zancen da fad’in “Hajiya ni dama na gama magana ga k’anwarsa Sahariyya zaune gida babu miji kawai sai a had’a aurensu don bazamu zuba idanu wannan yarinya da ya auro matsayin mata ta rainamu ba kuma Mamani ina mai tabbatar miki wannan yarinya da kike gani zata iya rabaki da jikanki a karo na biyu, tun kafin abin yakai nan mu aura masa ta gida kinga mun d’auresa....”
Abbah duban Baba Alhaji kurum yai had’ida girgiza kai, yayinda Mamy ta kasa furta koda kalma guda, har lokacin kanta na k’asa...
Sameer d’ago kansa yai yana duban wan mahaifin nasa da tsananin mamaki.... A hankali ya furta “Baba ku bani dama nayi magana da Siyama please...”
Mamani ta katsesa da fad’in “Yo wani dama, wannan batu naka yayi daidai Alk’ali, yanzu basai anjima ba a soma shirye shiryen biki....”
Abbah ya d’anyi gyaran murya kana yace “Amma Yaya, Mamani bawai nak’i maku bane wannan had’I, kaman yanda Ma’aruf ya buk’ata a basa dama yayi magana da iyalin nasa... Sannan Yaya baku tunanin abinda ya faru damu baya gameda had’in Hafiz da Zulfa’u ya maimaita kansa... Ni dai a ganina da an janye wannan batu...”
Haba nan fah Baba Alhaji ya soma kumfan baki yana fad’in “Toh kinji koh, Mamani... Kinji abinda d’anki yake fad’i koh, a kullum anaso mutum ya kasance mai kyakkyawan zato amma banda Usman... Minene aibun yara na... Maiyasa zai dinga dawo da abinda ya riga ya wuce....Idan har haka ne wannan ya kuma tabbatar min bai d’aukeni matsayin d’anuwa ba kuma wanda yake gaba dashi... Na tabbata da ace d’aya daga cikin yaran Ado ko Wada ne tsaf zai amince amma dashike d’iyata ce shiyasa zai nuna k’yamarsa... Tinda haka ne ni na cire kaina da ahalina daga wannan zuri’a... Usman daga rana mai kaman ta yau ka mance kanada D’anuwa mai irin sunana...!” Daga haka yasa kai zai fice...
Mamani dake hawaye tai saurin tare gabanshi tana fad’in “Shin sai na mutu ne ku sami jituwa tsakaninku...? Shin bazaku mance komai ku rik’e ‘yanuwantakarku ba.... Shin kuna tunanin mahaifinku dake kwance a k’asa zaiji dad’i da ace za’a tayar dashi a nuna masa yaransa sun

Please Login or Register in order to submit comment