Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad’a kan gado tana juyi, Allah mai iko wato dai cikin sauk’i labarin auren mijinta ya shirirnce, lallai ita d’in mace ce mai sa’a... Wayarta dake gefe ta janyo ta shiga neman layin k’awayenta su Shamzy dan yau dole suyi party na murnan nasarar wargaza al’amarin auren mijinta, yau dole ta had’iyi strong k’wayoyi da zasu kaita can sararin samaniya....

Koda Akram ya gama jera lambobin sai akai rashin sa’a babu network a wajen, gashi yana hango d’ayan ya soma motsawa alamun ya kusan tashi, k’irjin Akram ya kuma bugawa, a hankali ya soma lab’ab’awa ya isa jikin wani dutse da yake hangowa.... Cikin sand’a ya samu ya haura saman dutsen,ya shiga k’ok’arin neman service, sai faman jefa wayar sama yake , da k’yar ya samu ya kamo service..... Bugu d’aya a na biyu wayar ta soma ruri....

Engr dake zaune owners corner cikin hamshak’iyar Ford d’insa nan yaga kira na shigo masa da bak’uwar lamba, wayar da yasan mutane k’alilan ke da lambar... Mamaki ya cikasa, ya k’urama wayar idanu har ta kusan tsinkewa kana ya d’aga....
Daga d’aya b’angaren cikin tsananin tashin hankali Akram yake fad’in “Sir... Sir it’s me Akram...You need to hear me out...”
Gaban Engr ya yanke ya fad’i, cikeda karaji ya dakatar dashi da fad’in “You’ve got some nerve... How dare you Akram.... Bayan dik abinda na gani you still have something to say... After making me look like a complete imbecile, after making the fool out of me... After betraying my trust har kanada guts d’in da zaka kirani... Har kana....”
Katse sa Akram dake waige waige yai da sauri yana furta “Sir you have to believe me... Duka wannan makai nakeyi... Sir you need to read that letter nasan baka karanta ba, amma idan ka karanta you’ll understand me... I wrote everything there... Every single thing... Sir please read that note we’re running out of time...”

Girgiza kai Engr yake cikeda rud’ani yana fad’in “What letter Akram.... Wani letter kake magana....?”
Suna maganan network na seizing...
Akram yaci gaba da fad’in “Sir kar ka tab’a mance wannan... Ni d’in zan iya baka rayuwata....Never doubt that.....”D’if wayar ta katse...
Engr yaci gaba da fad’in “Hello..! Hello Akram... Can you hear me... Hello Akram are you there...?” Shiru ba’a babu amsa...
Cikin sauri Engr ya kuma dialing layin... Saidai ji yai bata shiga.... Kalaman Akram sun d’aure masa kai, wane letter kenan Akram ke magana... Take ya tina katin Bikin Akram cikin envelope Yusuf ya kawo masa, he need to go back and check that envelope.... D’an duban Jalo yai kana yace “Jalo juya kan motar... Mu koma gida....”
Cikeda risinawa Jalo yace “Ok Sir....” lokaci guda yabi umarnin ubangidan nasa...

A can daji kuwa sauk’ar k’asar bindiga Akram yaji a k’eyarsa saida wayar ta fad’i ta tarwatse... D’an ta’addan yasa hannunsa duka biyu ya d’ago Akram ya shiga kilansa kaman an aikosa lokaci guda ya shiga janyosa a k’asa yana doka kirama sauran ‘yanuwan nasa yana sanar dasu Akram tried to escape...Aiko gaba d’aya suka tashi a firgice suka nufosu nan suka had’u suka shiga dukan Akram ta ko ina jini na bin jikinsa gwanin ban tausayi....

***

Kan kace mai ‘yan d’aurin aure sun soma hallara, gidan Abbah ya soma cika da bak’i ‘yan d’aurin aure... Abbah sai sab’a babbar riga yake yana tarban mutane, gaba d’aya k’ofofin babban parlornsa aka hangame... Dik wannan d’awainiya na amsan bak’i da yake bai saka d’an uwansa Baba Alhaji a idanunsa ba saiko sauran k’annensa su Baffah Wada da Baffah Ado saiko Hafiz da bai sama bai k’asa bakinsa ya gaza rufuwa, jinsa yake ko aurensa na fari baiyi Farin cikin da yake ciki a yau ba... Sai wannan nan nan da Abbah yake, su Baffah Wada har mamaki suke irin kwalliyar da Hafiz ya chab’a Magaji abokinsa ma abin mamaki yaketa basa, gashi karaf abokansa ya gayyata, koda Mukhtari ya tanbayesa baya kishi Zulfah wani zata aura sai ce masu yai su tsaya suyi kallon show yanda auren Zulfah zai tashi daga kan munafukin d’an siyasan nan ya dawo kansa... Su Mukhtari dasu Magaji dai kallon ikon Allah kurum suke suna mamakin anya abokinsu bai sami tab’in hankali ba, ta ya za’ace ranar aure an sauya shek’a an dawo kansa... Hafiz yace sudai suyi kallo kawai....
Huzaifah yace “Munaji muna gani muna kuma saurare angon Zulfa’u....” Gaba d’aya abokan suka sa dariya idan ka d’auke Magaji da zuciyarsa ta kasa natsuwa... Anya ba wani mugun abin Hafiz ya k’ulla ba dan yasan yanda ya d’auki Akram da muguwar gaba....Fatansa dai Allah sa ba abinda yake tinani bane....
***

A can gidan Baba Alhaji kaw tuni Hajiya tasa an k’ure mata kid’a dan cewa tai a banbance gidan biki da gidan makoki, harta kwalliyar nan irinta zamani saida Hajiya tasa aka tsara mata itama, ga wata uwar gwaggwaro da aka d’aura mata dan cewa tai yau d’in na musamman ne, gidan shak’e yake da k’awayenta ana tayata murna yanda kasan itace amaryar.... K’awayen Sahariyya kaw su Fa’iza sai dad’a d’aura Hajiya suke keken aljanu suna haukatata suna fad’in irin kyaun da tai....
Najah ta kuma kai dubantaga mahaifiyarta yanda take tik’an rawa tsakar gidan, a hankali ta lumshe idanunta had’ida sauk’e nannauyan ajiyan zuciya... Saida takai k’ofar gidan kafin ta kuma huyowa ta dubi Hajiya, cikin zuciyarta take furta “I’m sorry Hajiya... Ki yafeni....” Daga haka sa kai tai ta fice a gidan....

Sanda ta isa sashen Mamani ta tadda ‘yanmatan gidan sai gugan ankonsu suke tare a parlorn Mamani, su Raihanah su Marliya dasu Sadiya... Sai kacaniya ake baka ma d’aukan zancen kowa sabida yanda hayaniyarsu ya cika wajen....
Najah ta k’arasa tana tambayar Raihanah Mamani...
Raihanah tace “Inaga suna can wajen kitchen itadasu Umman Kazaure kije dai ki duba....” Ta kuma duban Sadiya tace “Sadiya dan Allah ga rigata a goge min...”
Sadiya ta d’an jefa mata hararan wasa tace “A nawa....?”
Karaf Marliya tace “Chab aiko Ya Ma’aruf ne zai biyaki kinsan patient d’insa ce ya hanata aiki....”
Gaba d’aya suka sa dariya Karima na fad’in “Chapd’i aiko ku rufa mata asiri kafin Addah Sahariyya uwar kishi tajiku...
Marliya ta tab’e baki tace “Yo ba sai taji d’in ba wake tsoronta ince dukanmu nan Yayanmu ne, sai mai dan ya nuna kukawarsa akan Raihanah...”
Ita dai Raihanah batace komai ba sai girgiza kai da tai ta janyo hannun Najah tana fad’in “Muje na tayaki neman Mamani....”

A can hanyar k’ofar da zai sadaka da sashen Abbah suka hango Abban tareda Mamani da alama muhimmiyar magana suke tattaunawa... Daga yanda suke k’arasowa suka soma jiyo muryar Abban na fad’in “Wllhi Mamani bansan yanda Yaya ya tsaya ba, abin nima ya bani mamaki ace auren yaranmu nawa har uku ga nashi guda amma ko k’yallinsa babu... Toh ina yaje a irin wannan rana mai matuk’ar mahimmanci....?”
Mamani tace “Alk’ali kasan halin d’an uwan naka, yanzu haka wani sabgan ya shiga amma ina mai tabbatar maka zuwa jimawa zaka gansa....”
Abbah yace “Toh Allah yasa...”
Juyowar da zai ya tarar Naja’atu da Raihanah na gaidashi cikeda risinawa...
Abbah ya amsa masu da sakin fuska, suka gaida Mamani ma....
Ganin dai suna tsaye kaman da magana a bakinsu yasa Abbah cewa “Ya dai yarana akwai wani abin ne...?”
D’an duban Raihanah Naja’atu tai ga k’irjinta dake bugu kana tace “Abbah dama Mamani nake nema...”
Abbah yace “Toh toh kuce Kakar taku kukazo gaidawa ashe ba Abbah ba...”
Gaba d’aya suka d’an saka dariya kana Raihanah tace da Najah bara taje taji halinda gugan kayanta Ke ciki....
Mamani ta dubi Naja’atu tace “Yaya dai ke ‘yar gidan Haule... Inji lafiya...?”
“Lafiya Mamani magana dama nake so na maku...”
Abbah da tuni ya sab’a babbar riga zai shige Naja’atu tai karaf tace “Abbah maganar harda kai...”

Abbah ya juyo cikeda mamaki, itama kanta Mamani mamakin ne ya cikata...
Abbah yace “Toooh, amma lafiya kuwa Naja’atu koh...?”
Naja’atu tace “Abbah akan b’acewar Ya Ma’aruf ne... Abbah nasan su waye suka b’atar dashi, kuma har yanzu ma sunada wata shiri...””

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Kalaman da Mamani da Abbah suke iya nanatawa kenan kurum..... Mamani ta had’iyi wani miyau da ya tokare mata mak’oshi da k’yar.... Ganin Mamani na k’ok’arin zubewa yasa Abbah saurin rik’ota Naja’atu na taimaka masa... Duban Naja’atu yai kana yace “Taimaka min mu k’arasa da ita can yanda babu mutane sai ki sanar dani komai...”
Naja’atu ta jinjina masa kai sukai yanda Abban yace, can gefe bayan sashen Mamani yanda babu kowa sai tabarmai yanda ‘yanmatan gidan sukai zaman yin k’unshi, nan suka samu suka kwantar da Mamani a wajen Naja’atu nai mata fifita suna binta da sannu itada Abbah...
Duban Mamani Abbah yanda take numfasawa da k’yar kana yace “Mamani zaifi kyau idan bakiji wannan labari ba, ki bari ni naji komai, hakan bazai kyau ma lafiyarki ba...”
Girgiza kai Mamani tai kana tace “Alk’ali zanji komai... Inaso naji komai, inaso naji wasu azzalumai ne suka jefamu cikin wannan uk’uba da k’unci tsawon rayuwarmu... Inaso naji komai Alk’ali...”
A hankali Abbah ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya jinjina kai... Duban Naja’atu dake duk’e wajen tana kallon Mmani cikeda tausayawa Abbah yai kana yace “D’iyata muna saurarenki... Sanar damu mai kika sani... Daga ina kikaji kuma waye ya sanar dake....?”

Naja’atu tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka siraro mata, lokaci guda ta gyara zamanta kana ta shiga karanto iyaka abinda taji d’aga Hajiya Haule da mahaifinta Baba Alhaji da kuma Aunty Lami, ta kuma sanar dasu shirya aurama Sameer Sahariyya dasu Hajiya da Baba Alhaji sukai don su cimma burinsu na kawar da Ma’aruf a karo na biyu...
Tinda ta soma magana hawaye ke zarya a fuskokinsu gaba d’aya... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Wannan wane irin al’amari ne, idan ance Haule da Lami zasuyi haka bazaiji mamaki ba sabida kishi...Amma Baba Alhaji fah... Ta yaya d’an uwansa zai masa haka...? D’an uwansa na jini... Yana ganin yanda suka rayu shekara da shekaru cikin k’unci da alhini na rashin d’ansu.... Shin wace irin rayuwa duniyar yau ta tsinci kanta ciki... Ace d’an uwanka na jini zai aikata maka mugun aiki irin wannan... Kaicon rayuwa mai cikeda mugunta da k’iyayya had’ida muguwar hassada da k’yashi.... Mamani dafe k’irjinta dake tsananin mata zafi kurum tai tana mai girgiza kai idanu a lumshe ga hawaye dake gangaro mata, lokaci guda take furta “Sun cutar damu... Sun zalunci baiwar Allah Mariya...Sun rabata da gudan jininta tsawon shekaru... Sunsa mun d’auki laifi gaba d’aya mun aza mata tsawon shekarun nan... Mariya ki yafeni... Ki yafe min baiwar Allah.....!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka...
Naja’atu ma kuka take tana furta “Mamani Abbah ku yafeni... Tin kwanki naso sanar daku amma na kasa, banida k’arfin Zuciyar yin hakan har sai lokacinda nake tinanin lokaci ya k’ure... Ku yafeni su d’in iyayena ne...”
Saurin rungumota Mamani tai kana tace “Baki makara ba Naja’atu... Wannan sadaukarwa da kikai Kika zab’i ki sanar damu gaskiya dikda sanin cewa sud’in iyayenki ne, Ubangiji Allah ya saka miki da gidan Aljannah, ya baki rayuwa mai inganci a gidan duniya... Kuma yanzu da mukaji gaskiya jikana bazai had’a iri da Haule ba... Tashi kije abinki Allah ya miki albarka... Kinyi abinda ya dace...”
Jiki a sanyaye Naja’atu ta mik’e ta fice...
Mamani ta dubi Abbah tace “Ma’aruf bazai auri d’iyar Haule ba kaji na fad’i maka....”
Abbah ya jinjina kai ba tareda ya iya koda duban mahaifiyar tasa ba...
lokaci guda ya soma k’ok’arin Mik’ewa yana fad’in”Zanje na bada auren Nabilah da Zulfa’u, shi kuma Ma’aruf an fasa nasa auren....”
Dakatar dashi Mamani tai da fad’in “Babu aure guda da za’a fasa...”
Abbah ya dubeta da tsananin mamaki... Jinjina masa kai tai tace “Ince dama sabida ni ya amince da auren d’iyar wajen Haule...? Toh na tabbata dik wanda zan canza masa da ita baza’a sami matsala daga garesa ba... Kuma ina fatan hakan ya zame masa Alheri ya kuma izna da ishara gasu Haule....”
Jinjina mata kai Abbah yai kana yace “Dik yanda kikace Mamani...”

***

A yayinda ya rage saura mintoci a soma d’aurin aure su Khalid suka samu isowa, har yanzu ya kasa daina jinjina lamarin cikin zuciyarsa yana ganin abin tamkar mafarki... Ta ina layinsu Teddy Bear zai b’ace masa dikda cincirindon mutanen da yake hangowa tin daga bakin layin nasu... Ya dubi Daddy dake zauna gefensa Jafaru driver d’insa na jansu yayinda motar su Aunty Daula da yara Ke biyedasu... So yake ya tambayin Daddyn amma ya kasa saima sakin wani irin ajiyan zuciya da yakeyi... Like shin mafarki yake ko gaskiya, idan har mafarki ne baya fata a katse masa wannan mafarki nasa har sai yaga abinda ya kwancewa buzu nad’i... Shin dama aurensa da Nabilah Daddy Ke shiryawa all this while... Waidai da gaske ne abinda yake ganin na shirin faruwa...? Bai gama shan mamaki ba saida yaga su Baffah da wasu tsiraru cikin abokansu sun k’araso sunaima Daddy sannu da isowa... Khalid kaw aikama Baffah wata muguwar kallo yai wanda yake nufida ka jira had’uwarmu.... Baffah dai k’unshe dariyarsa yake yana kuma yima Daddy sannu da sauk’a, Khalid sai b’alla masa harara kurum yake yayinda sauran friends d’insu su Misbahu D’anisa suka k’araso suna zolayan ango... Ga wani annuri na musamman dake haska fuskar Khalid d’in....

A b’angaren Aunty Daula kaw tinda suka iso wannan gari gabanta ya tsananta fad’uwa, gaba d’aya wani iri takejin kanta ta rasa maike mata dad’i, a yayinda su Daddy suka shige babban parlorn Abbah Aamiru d’an wajen Baffah Wada yaimasu Aunty Daula jagoranci zuwa sashen Mamy, k’irjin Aunty Daula ya tsananta fad’uwa... Haka sukaita gaida mutane ‘yan biki hardai suka k’arasa cikin parlorn, yanda wasu Gwaggwanyen su Zulfa’u na can Kazaure suka tarbi su Aunty Daulan da Mamy basuma ganta ba abinka da hidiman biki...

***

A can parlorn Abbah kaw auren Nabilah da Khalid aka soma d’aurawa, sanda kunnuwan Khalid ya jiyo masa ana d’aura aurensa da Nabilah a hankali ya lumshe idanunsa, can k’asan zuciyarsa na samun wani natsuwa da bai tab’a samun irinta ba, siririyar hawaye ta gangaro daga idanunsa guda... Daddy dake dubansa taisayin Khalid d’in ya kamasa tabbas d’an nasa yasha gwagwarmayar soyayya... Allahu Akbar wannan shine INDA RAI tabbas DA RABO... Yau d’in Allah ya cika ma d’ansa wani babban buri cikin burikansa... Fatansa Allah ya albarkaci sabuwar rayuwar da d’an nasa ya tsinci kansa ciki a yau d’in....

Wani ikon Allah shine har wannan lokaci babu labarin zuwan masu auren Zulfa’u, abin har ya soma damun Abbah, ya waiga nan ya waiga can, ya dubi Baffah Wada su d’anyi magana k’asa sannan ya dubi Baffah Ado ma, su kansu duk abin ya damesu...
Hafiz ya k’araso had’ida ciro sadakinsa cikin aljihun babbar riga yana fad’in “Abbah na fad’a maka dama wannan d’an siyasan wllhi babban mak’aryaci ne yaudarar Zulfa’u kurum yai Abbah... Abbah ni ne mijin Zulfa’u, ni d’an uwanta ne Abbah... Abbah wllhi muna k’aunar junanmu ka taimaka ka maida aurenmu... Abbah kar mu bari mahassada su mana dariya...”
Mamaki ya cika illahirin mutanen dake wajen... Kallo ya koma kan Hafiz da Abbah, wani irin al’amari ne tamkar film suke gani na faruwa....
Tamkar gunki haka Abbah ya zubawa Hafiz idanu... Hafiz yaci gaba da sab’a babbar riga yanayin kalan tausayi dan jama’an wajen su tausaya masa... “Abbah Zulfa’u matata ce... K’addara ta rabamu kuma yanzu ma k’addara zata maida aurenmu... Abbah please ka duba lamarin nan ko dan ‘yanuwantakanmu kar ka bari bare suji kanmu.... Abbah ka dubi girman Allah kaji tausayinmu ka maida aurenmu... Wad’annnan mutane ba zuwa zasuyi ba...”

Baffah Wada da takaici ya ishesa nan ya katse Hafiz da fad’in “Kai Hafiz bamu son shashanci kanaji koh... Ya ranar auren yarinya zakazo da wani batu wanda hankali bazai kama ba... Mu k’ara masu lokaci Suna nan tafe na tabbata...”
Hafiz ya kuma sab’a babbar riga tamkar zararre ya isa gaban Baffah Wada yana fad’in “Baffah wllhi manemin auren Zulfa’u gawurtaccen mak’aryaci ne nai maka imani idan zamu kwana a nan bazai bayana ba, domin kaw aikinsa kenan Yaudara....”
Baffah Wada ya girgiza kai yace “Bama san hauka Hafiz ka tashi ka daina wannan rashin hankalin Naka...!”

Cikin tsananin huci Hafiz Ke duban Baffan nasa yana fad’in “Baffah dana kune ‘yan bak’in ciki kar matata ta dawo gareni...Toh Allah ya nuna min kuma kana gani za’a maida aurenmu... Idan ba mayaudari bane toh ina yake maiyasa bai bayyana ba, maiyasa bamuga masu amsar masa auren ba...Ina suke idan da gaske ne...?!!!”

Kaman daga sama suka jiyo wata murya mai cikeda k’warjini tana fad’in “Gamunan mun iso....!!”

Ba Hafiz da tuni ya daskare ba harta su Abbah da tsananin mamaki suka juyo suna duban bakin k’ofa....


SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_.................DA RABO_



*88*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Mamaki ya cika Daddy ganin Engr na kutso kai cikin parlorn, mutane kaw sai faman bud’a masa suke, Jalo na biye dashi har suka isa mazaunin su Abbah suka zauna suna masu yi masu masabaha.... Mutane kaw sai k’asa k’asa da murya suke suna ambato sunan Engr suna fad’in shid’in ne dai da gaske, abinka da sanannen d’an siyasa....Marok’a kaw tuni suka soma wasa shi suna fad’in Alkhairansa.... Mamaki ya cika Abbah dikda cewa shi d’in ba ma’aboci siyasa bane yasan Engr Ma’aruf Mutallab matsayinsa na d’an takaran gwamanan jiha da yai fice, kuma ko shakka baiyi sanda Mahaifin Khalid yazo nemawa Khalid d’in auren Nabilah tare sukazo da shi Engr d’in... Toh amma abinda bai gane ba... Shin dama Engr Mutallab yanada alak’a da mai neman auren Zulfa’u ne...? Wannan tambaya shi yaketa yawo a kwanyar Abbah, gaba d’ai ya gaza fahimtar meke faruwa har saida ya sinkayo muryar Baffah Wada yana tambayar Engr
“Rankashi dad’e shin kune masu amsar auren Zulfa’u....?”
Murya a dake Engr yace “K’warai mune....”
Baffah Ado yace “Toh ai sai aci gaba da gudanar da d’aurin aure....”
Hafiz da jikinsa Ke tsananin karkarwa had’ida tsuma cikin sauri ya katsesu da fad’in “Ta ya za’a aura mata mutumin da ya b’oye kanshi ya kasa bayyana kanshi... Baffah kar azo ai auren da za’azo ana danasani a baya....”
A zuciye Baffah Ado ya mik’e yana nuna Hafiz da d’an yatsa yake fad’in “Kai Hafizu wllhi billahilAzim idan baka shiga taitayinka a wajen nan ba zan maka rungumar buhun dawa na fiddaka da k’arfin gaske, ka shiga hankalinka tin wuri ka daina maida mutane k’anan mutanen... Cikinmu babu sa’anka....”
Hafiz yaci gaba da huci yana rarraba idanu ga gumi dake keto masa.....

Baffah Wada ya dubi Engr yace “Kuyi hak’uri d’an yau ne ka haifeshi baka haifi halinshi ba, Malam Imam muci gaba da abinda ya taramu.... Imam ya jinjina kai, yana mai kuma tambayar Baffah Wada wanda shine Alwalin Zulfa’u... Yana k’ok’arin tambayar Engr kenan sukaji wata murya tana fad’in “Ku dakata...!”

Gabaki d’aya juyowa sukai suna dubanta, mahaifiyar Akram ce sai Yusuf da Kawunan Akram guda biyu da sukazo suka tambaya masa auren Zulfah....
Mamaki ya kuma cika mutanen parlorn, wannan wane irin al’amari ne.... Aka bada hanya ma Umma da tawagarta suka shige....
Baffah Wada yace kece wace...?”
Umma tace “Ni ce Mahaifiyar Akram... Wad’annan da kake gani k’annena ne kuma su sukazo suka tambayawa Akram auren Zulfa’u...”
Kawu Jafaru yace “Tabbas mu mukazo muka tambaya mashi auren Zulfa’u... Amma kwana biyu da suka shige yazo ya sameni ya sanardani yana so ranar aurensa sadakin da ya bayar da sunan aurensa da Zulfa’u ya juya ya zama sadakin Ubangidansa yana so auren ya tashi daga kanshi ya koma kan Ubangidansa Engr Ma’aruf Mutallab... Koda na tmbayeshi dalili sai cemin yai na mishi wannan alfarmar mai yuwa zai iya tafiya wani waje mai nisa a wannan ranar dan bazai iya fuskantar Ubangidan nashi ba....”
Umma ta k’arada “A kwanakin nan d’ah na Akram ya sauya k’warai, babu yanda banyi ba ya sanar dani abinda ke faruwa musamman tsakaninsa da Gwamnan gobe.... Sai bayan da muka nemeshi muka rasa Yusuf abokinsa ya sanar damu komai, ya sanar damu cewa Gwamnan mai jiran gado shine asalin manemin wannan yarinya Zulfa’u, kuma tabbas ya wakilta d’ah na Akram yai masa jagoranci ne... Ina mai rok’onku da ku baiwa wannan bawan Allah auren d’iyarku shid’in mutumin kirki ne....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye suna gangro mata....
Girgiza kai Engr yai kana yace “Ummah ki barni na karb’awa Akram aurenta ni mai iya sadaukar masa da komai ne....”
Girgiza kai Ummah take ta kuma had’e hannayenta waje guda tana fad’in “Kai d’in kai kafi kowa cancanta ka zama mijinta... Gwamana dan Allah kabi wasiyyar Akram ka amsawa kanka auren Zulfa’u a yanzu... Na rok’eka....” Ta k’arashe tana hawaye...
Daddy yai saurin dafa hannayen Engr yana mai sakar masa murmushi yake fad’in “Kai d’in mutumin kirki ne, mutumin arziki ne da kowa yai maka shaida ta k’warai...Wanda kowa zaiso had’a zuri’a dakai....”Daddy ya kuma kai hannunsa kan na Abbah da ya koma tamkar gunki yana kallon wannan ikon Allah lokaci guda Daddy yaci gaba da fad’in “Alhaji Usman ka bani dama na tambaya kuma na karb’awa K’anina Ma’aruf auren d’iyarka.... Shi d’in mutumin kirki ne... Kar ka mance fad’in ma’aiki ne... Idan na gari yazo neman auren d’iyarku toh ku bada, rashin bayarwan ka iya haifar da fitina... Alhj Usman ni Engr. Ahmad Madi Mailafiya Ina tambayawa K’anina Engr. Ma’aruf Mutallab Maidala auren d’iyarka Zulfa’u... Shin ka bashi a d’aura auren yanzu...?”
D’agowa Abbah yai yana dubansa yayinda Hafiz Ke faman girgiza kai yana adu’an yaji kalmar a’a daga bakin Abbah... Su Baffah Wada Baffah Ado da sauran jama’an wajen dake fatan amasar Abbah ta zamto eh gaba d’aya tsit parlorn tai ana jiran amsar Abbah.... Maida dubansaga Engr Abbah yai, dikda cewa Engr ya kasance sanannen d’ansiyasa amma baisan dalili ba sosai mutumin ya kwanta masa a rai tintini dukda cewa shi d’in bai kasance mai hidima da ‘yan siyasa ba.... Fuska a murtuk’e Abbah ke duban Engr kana ya soma fad’in “You take care of my daughter... Ka kular min da d’iyata... Itad’in ta kasance d’iya mai biyayya, kuma taga iftila’i da yawa na rayuwa... Ta cancanci Farin ciki....”

Jin abin yake tamkar a mafarki... Allah ya isa buwayi kuma gagari misali... Tabbas shid’in shine mai sauya al’amara a lokacinda yaso ya kuma ga dama... Yazo nan wajen da niyyan amsawa Akram auren Zulfa’u ne sai gashi aure ya tashi daga kan Akram ya koma kansa... Shin waye ya isa ya juya wannan idan ba mai mulkin sama da k’asa ba... Lokaci guda Engr yake fad’iwa Abbah “Nayi maka alk’awarin d’iyarka bazatai kuka ba in sha Allah... Zan knaunaceta da duka zuciyata dan dama tuntuni zuciyar mai k’aunarta ne, mai k’aunar sauraren muryarta ne.... Ni Engr Ma’aruf Mutallab Maidala nayi maka alk’awarin kular maka da d’iyarka har k’arshen numfashi na....”
Haba nan fah parlor ya kacame da farin ciki, wane ikon Allah harta mutanen da basu San kan labarin ba irinsu Khalid sai abin yai matuk’ar burgesu... Farin ciki da annuri ya cika fuskokin mutanen... Take Engr ya wakilta Daddy ya amsa masa auren Zulfa’u... Ikon Allah kenan, Daddy ya taho Kano da niyyar amsawa d’ansa Khalid aure sai gashi ya amshi aure biyu, wannan abin farin ciki da yawa yake... Nan fah Hafiz yaji duniyar tana juya masa... Babbar rigarma baisan sanda ya cire yayi wurgi da ita ba, ji yake tamkar ya k’arasa ya shak’o wuyan Engr saidai bodyguards d’insa guda biyu kawai sun isa suyi watandan Hafiz...Al’ajabi ya cika illahirin jama’an dake wajen, nan fah hargowa da kacaniya ya kacame tsakanin Al’umma tuni labari ya famtsama cikin gida, ga kuma wani k’ishin k’ishin da sukeji cewa auren Sameer bada Sahariyya aka d’aura ba, da k’anwarta aka d’aura dan haka kowa sai cewa yake da Naja’atu aka d’aura auren Yaya Ma’aruf....
Tinda Hafiz yasa kai ya fice babu wanda yaga koda wulk’awarsa, Magaji sai sauri yake ya samu ya cimmasa kafin yai wani abinda zai janyo masa kwanan police station tinda yasan idan yayi haukarsawa Akram yasha bazai wa Babban mutum kaman Engr yasha ba...

Shiko Khalid tinda suka fito daga taron d’aurin auren ya tsare Baffah da tambayoyi...
Baffah na k’ek’yata dariya yake fad’in “Haba ango dika wad’annan tambayoyin ta ina zan soma amsa su... Kaga muje chines restaurant ka shirya mana gajeriyar liyafa, Ko ya kukace guys....?” Ya k’arashe yana duban su Misbahu.....
Baba Ali yace “Nidai dik ba wannan ba, tinda yak’in neman auren nan dani akai, ya kamata a kaini naga amaryar nan kafin na bar garin nan...”

Baffah ya dangwari k’eyar Baba Ali yana fad’in “Toh Sarkin ‘yan magana, fad’a masa dakai akai yak’in neman aurensa...”
Baba Ali yace “Yo ba gaskiya nake fad’i ba... Kaga da Allah muje nasan shi kanshi angon ya matsu

Please Login or Register in order to submit comment