Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka kutsa dashi cikin dajin, a k’alla sunyi tafiya mai nisan kilomita ashirin da k’afafu a k’iyasin Akram dan shi dai ba ganin komai yake ba hannayensa d’aure suke sannan kanshi rufe yake...
Bayan sun share tafiya mai tsawon gaske yaji sunja sun tsaya, guda d’aya yasa hannu ya zame jakan da aka rufe masa kai dashi....
A hankali Akram ya soma bud’e idanunsa yana gani dishi dishi... Fincika yaci gaba da yi yana fad’in “Su waye ku, mai kuke nema a wajena...?”
D’ayan yakai masa naushi a ciki yana fad’in “You never learned your lesson... Ance maka kai shiru ka faye surutu da yawa...”
Daga can Akram ya soma sauraro wani familia voice yana fad’in “Shisa ka iya siyayasa sosai sabida surutu irin naka...!”
Da tsananin mamaki Akram ke dubansa, Hafiz ya K’araso har gabansa yana murmushi kana yace “Kaji mamaki koh.... Ka zaci ka mallaketa an gama ko... Well, you’re very much mistaken... I told you countless time babu mai raba tsakanina da Zulfa’u, amma taurin kunnenka ya hanakaji... Dama na fad’a maka dan kana a matsayin d’ansiyasa ba kai kad’ai kasan ‘yan iskan gari ba... Mu da masu daji muke huld’a ba k’ananan ‘yaniskan da k’waya ya haukata ba...” Yana murmushi yakai hannu saman kafad’an Akram yana d’an bubbugawa yake fad’in “Ango ango... kar ka damu zan d’auko mata hotunan amarya nazo har nan na nuna maka....”
Fincike kafad’arsa Akram yai yana tsananin huci yake furta “You coward... Why would I even be surprised, abinda ka iya kenan... Bazaka iya fuskantar matsalarka head on ba, bazaka iya sayan soyayyarta da zuciyarka ba saidai kayi amfani da hanyar ta’addanci abinda kafi wayo akai... Babban matsalar a nan shine kai dak’ik’i ne na k’arshe ka kasa fahimtar ita soyayya ba’a mata dole...!”
A zuciye Hafiz yakai mai naushi a hanci, yana mai ci gaba da huci yake furta “K’arya kake... Zulfa’u tana k’aunata if only baka hure mata kunnen ba da k’arerayinku na ‘yansiyasa... And let me remind you this Zulfa’u was mine, she is my mine and she shall remain mine....!”
Dariya Akram yai yana mai tsartar da jinin dake bakinsa yanda Hafiz ya naushesa “I promise you, even if you’re going to end my life right this moment bazata kuma dawowa gareka ba... Kaman yanda hannun agogo yake tafiya clockwise Toh haka rayuwar Zulfa’u dakai yake, babu komawa baya....Tai maka nisanda har abada baza kuma mallakanta ba....!” Naushi Hafiz ya kuma kai masa yana mai furta “Shut up... Shut the hell up... Baka San mai kake fad’a ba, Karen farautar ‘yansiyasa.... You’re now under my custody sai yanda nai dakai... And I promise you sanda zaka fice a dajin nan Zulfa’u ta koma gareni, sai kaje kaci gaba da k’arerayinku na ‘yansiyasa ma wata.... Have I made myself clear..?” Ya k’arashe yana kamo hab’ar Akram had’ida d’ago kansa....
Murmushi kurum Akram Ke masa ba tareda ya furta komai ba....
Lokaci guda Hafiz ya d’anjada baya ya dubi yaran Babba Duna yace “Keep an eye on him...”
Gaba d’ai jinjina masa kai sukai kana yasa kai ya kutsa ya fice daga dajin....

***

Tsananin mamaki ne ya cika Engr, toh ina Akram zai tafi ba tareda ya sanar dashi ba....? Ya kuma juya envelope d’in sak’on Akram d’in yana mai duban Yusuf da kansa ke k’asa... “Ina yace maka ya tafi...?”
Yusuf ya had’iyi miyau da k’yar “Dama cewa yai k’auyen mahaifiyarsa zai tafi kuma ko ka kira bazaka samesa ba dan babu network na waya a wajen....”
Cikeda rud’ani Engr ya jinjina kansa a hankali kana yace “Amma bai sanar dakai komai ba...?”
Gyara zama Yusuf yai kana yace “Iyakacin abinda ya sanar dani kenan sai kuma sak’on nan da ya bada a baka....”
Engr ya numfasa a hankali yana mai k’urama envelope d’in idanu.... “Shikenan na gode k’warai, kana iya tafiya...”
Yusuf ya mik’e cikeda risinawa yai sallama wa Engr....
A hankali ya soma ware envelope d’in, katin gayyatar aure da ya soma cin karo da ita shi yafi komai d’aure masa kai, k’irjinsa na bugu da sauri da sauri, sam baima kula da wasik’ar dake bayan katin auren ba... A hankali ya soma zaro katin Bikin yana warwareta... Wane irin bugu yaji k’irjinsa na masa, badon yaga sunan Akram b’aro b’aro jiki ba da sai yace k’ila ba Akram d’in da ya sani bane... But what is all this...? Ta ya za’ace right hand man d’insa zai aure a basa short notice irin haka..? Ya za’ace auren Akram baida labari sai ana gobe d’aurin aure.... Wane irin al’amari ne wannan....? Gabaki d’aya kansa ya k’ulle, ko kulada sunan amaryar bai ba har saida Muhibbah ta shigo cikin parlorn dan dama tinda taga shigowar Yusuf abokin Akram ta lab’e daga bakin k’ofa, dik kuma taji abinda suka tattauna....
“Excellency na, meke faruwa ya na ganka haka...?” Tai maganar cikeda kulawa....
Kai kurum ya d’ago yana dubeta da idanunsa da tuni sun canza launi zuwa ja... Har saida gaban Muhibbah ya d’an fad’i dan tasan kalan b’acin ran mijin nata... K’arasowa tai a hankali idanunta kan invitation card d’in dake rik’e hannunsa guda... Hannu ta amshi card d’in tana mai karantawa, zuciyarta na mata wani irin dad’i, ji take tamkar tai shewa ta nuna tsantsan Farin cikinta amma babu halin yin hakan.... Zama tai gefensa mamaki kwance saman fuskarta lokaci guda take furta “Akram ne zai aure....? Shine baka sanar dani my Excellency na... Haba ai da na baida nawa gudummawan... Akram ai d’an gida ne ya wuce normal employee....”
Dik wannan maganganu da take Engr bai tankata ba hasalima yai nisa duniyar tinani, kaman daga sama ya kuma sinkayo muryarta tana karanto sunan amaryar... Da tsananin mamaki ya d’ago yana kuma dubanta, cikin sauri ya fuzgi katin hannunta, ga k’irjinsa dake tsananin bugawa tamkar zai fice... Sunanta kenan... Tabbas he cannot be mistaken, sunanta kenan... Toh kodai ba ita bace... What is all this...?
D’agowa yai yana duban Muhibbah da tai sakare itama tana dubansa, kan kace mai yasa kai yabi bayan Yusuf yana mai doka kira ma securities na gidan kan cewa su dakatar da Yusuf... Ai a take Muhibbah ma ta take masa baya tana tambayarsa lafiya....

Masu gadin main gate ne sukai waya first gate suka sanar da securities d’in first gate d’in cewa su dakatar da mutumin da ya fice yanzu....
“Em Sir, muje ana nemanka a ciki...” security guda d’aya ya fad’i yana mai nunawa Yusuf d’in hanya alamun su koma cikin gidan...
Yusuf ya d’anyi jim kana yace “Toh mai kuma ya faru...?”
Security man d’in yace “I don’t know sir, I’m only following orders....”
Jinjina kai Yusuf yai kana yasa kai yabi umarnin security d’in...

Engr da k’arasowar sa kenan cikin wani irin huci yake furta “Where is Akram...!!!? Tell me where the hell is he..? I need to speak to him right this moment... So tell me where the hell is your friend..??!!” Cikin tsananin karaji yai maganar wanda gabaki d’aya mutanen dake wajen saida suka razana... Muhibbah ma dake gefe sai k’yafta idanu take kaman taci kud’in aika, kai kace bata San komai gameda al’amarin ba..
Yusuf ya shiga kai cikin razani “Rankashi dad’e... Wllhi bansan yanda Akram yake ba... Iyakacin gaskiyata na fad’i maka... Bansan ko kuma wajen Ummansa zamuji takaimu garin nasu ba... But I swear na rantse iyakacin gaskiyata na fad’a maka..”
Jinjina kai Engr yai kana yace “Kaje gidan nasu ka sami mahaifiyarsa ka tambayeta gameda batun... Idan itama batasan komai ba ta sanar dakai inane k’auyen nasu... Ka fahimta...?”

Jinjina kai Yusuf yai kana yace “Zanyi yanda kace your Excellency...”
Jinjina kai Engr ya kumayi kana ya tako gaban Yusuf kad’an cikin murya mai cikeda gargad’i yake furta “Ina son amsoshi kafin rana ta fad’i... And one more thing... Don’t you dare think of betraying me kaman yanda abokinka yamin....”
Yusuf ya d’an dubesa ganin yanda yake turiri alamun ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci kana yace “Sir believe me... Akram bazai tab’a cin amanarka ba... Whatever he’s done, I’m sure he has his own reason for doing that...”

A zuciye Engr yace “I did not ask for your opinion... Kawai kai abinda na saka ka...”

Jinjina masa kai yai kana yace “Yanda kace, Sir...” Daga haka sa kai Yusuf yai ya fice daga gidan cikin sauri... Yayinda Engr Ke tsaye kameda kunkuminsa cikin tsananin mamakin d’an adam... Securities kaw gabaki d’aya kowa ya sanne kai ya kama gabansa ganin Ogan nasu cikin wane irin yanayi da zasu iya cewa basu tab’a ganinsa ciki ba....
Muhibbah dake murmusawa cikin zuciyarta a fili kaw k’arasowa ga mijin nata tai had’ida d’an dafasa kad’an tace “Excellency na... Wai meke faruwa ne...? What’s going on... What’s all this, dan Allah ka sanar dani...”
Baice da ita komai ba saima sa kai da yai ya nufi cikin gida, yanayin tafiyarsa kad’ai zaisa ka fahimci tsananin b’acin ran da yake ciki....
Muhibbah tabi bayansa da kallo kana ta tintsire da dariya tana mai furta “Akram kaid’in na daban ne... Ka cancanci duk wani kyauta daga gareni... Lallai ka iya buga game... Wasan tana buguwa yanda nake so...” Ta kuma tintsirewa da dariya kana tabi bayan mijinta tana fad’in “Excellency na please wait... Talk to me please....”

A parlorn k’asa ta taddashi ya had’e hannayensa biyu ya d’aura hab’arsa bisa hannayen alamun yai nisa cikin tunani... A hankali ta isa ta zauna gefensa, dafasa kad’an tai tana mai tattaro natsuwarta waje guda “Excellency na... Dan Allah ka sanar dani mai Akram yai maka haka da taanani... Ban tab’a ganinka cikin irin wannan yanayi ba...”
Fuzar da iska yai a hankali kana yace “It’s so painful ace mutumin da ka aminta dashi ya yaudareka...”
Ta sauk’e gajeriyar ajiyan zuciya had’ida kamo yatsun hannunsa “This world is full of fake people Excellency na.... Mutane suna taking advantage d’inka kasancewarka mai tausayi da tausasawa, idan ka janyo mutum inuwa shi sai ya turaka rana... But I’m here for you Excellency na... Ko menene ke damunka nai maka alk’awari together we’d overcome it.... I promise you...”
D’ago rinannun idanunsa yai yana dubanta kana yace “Ya sanar dani zai nema min aurenta, ya sanar dani zaimin yak’in... Only to get this in return.... I trusted him my whole life... He’s practically brother to me, daidai da dak’ik’a guda ban tab’a tsammanin haka daga gareshi ba....”
Sauk’e ajiyan zuciya Muhibbah ya kumayi tana mai kuma janyo hannayensa alamun rarrashi “Excellency na... Kar kaga laifin Akram... What if ku biyu d’in Kun aukawa soyayyarta lokaci guda ne...?”
Cikin sauri ya dubeta kana yace “Then he should’ve at least told me, ba wai ya k’yaleni kaman wani soko ba... A yanda nakejin Akram ni mai sadaukar masa da soyayyatace... But I was wrong about him...!” Cikin karaji yake maganar....

Muhibbah ta kuma gyara zama kana tace “What If Akram was been loyal to you... What if ita yarinyar ita ta tsara haka.. Maybe in the process na yana nemawa Uban gidansa aure kwatsam ita matar ta kamu da sonsa... Kasan mata akan abinda suke so, kawai ce masa zatai suyi aurensu don ita shi take so bakai ba...Maybe Akram yaso ya sanar da ita yin haka like cin amanane amma tak’i yarda ta yaudareshi da kalamai na soyayya har hakan ta kasance... Baka tunanin duk wannan na iya faruwa Excellency na...? Bawai kishi nake ba, no I’m telling you this because ni d’in kai nakeso kuma na damu dakai, bana kuma so na ganka cikin damuwa...”

D’agowa yai yana dubanta lokaci guda kalamanta na Yawo a kwanyarsa... Ganin tarkonta kaman ya d’anu ya sanyata mik’ewa tana mai furta “Kai tinanin dik abinda na fad’a maka... Kaida Akram kun had’u da sharrin mace ne... Amma na tabbata Akram bazai tab’a aikata hakan a gareka ba, domin kaw da ace zai aikata hakan da tuntuni tsawon shekarun nan da yayi, amma koda wasa baka tab’a samunsa da shaidar cin amanarka ba... Wannan ba sharrin kowa bane illa ita matar....Bara naje na kawo maka something to calm you down....”
Bai iya cewa komai ba har Muhibbah ya fice daga parlorn... Maiyasa yake ji a k’asan zuciyarsa Zulfa’u bazata tab’a yin abu makamancin abinda Muhibbah Ke fad’i ba... Maiyasa yake jin ya yarda da ita koda ace bai tab’a kasancewa da ita ba....? A hankali ya mik’e tsaye yana mai zarya a parlorn had’ida tinanin yanda zai shawo kan lamarin...

Koda Yusuf ya dawo babu wani haske, da alama Umman Akram ita kanta batasan da tafiyar Akram ba, sannan a cewarta basuda wani k’auyen tik’is bayan garinsu Rano, kuma anyi waya Rano baije can ba....Ita kanta Umma abin ya soma damunta gashi gobe ake shirin auren Akram d’in...
Engr yace ta kwantar da hankalinta In sha Allah zasu samu Akram za kuma suji dalilinsa na yin abinda yayi....

***
RANAR D’AURIN AURE, RANAR DA ZATA KASANCE MAFARIN FARIN CIKIN WASU HAKAN A B’ANGAREN WASU TA ZAMTO AKASIN FARIN CIKI,RANAR DA WASU SIRRIKA ZASU BUD’E KAWUNANSU DA KANSU...

ABUJA.

Sam Khalid baisan Daddy ya iso garin a daren jiya ba, sai a masallaci sallan asubahi suka had’u... Gaisawa sukai suka nufo gida tare, sam Khalid bai mamakin ganin Daddyn ba tinda gidansa ne zai iya zuwa ko k’arfe nawa ne....Suna tafe Daddy yace “Fitar sassafe zamuyi Khalid, nasan Auntyn taka bata sanar dakai ba koh...?”

Mamaki ya kama Khalid “Daddy wani waje zamuje... Ko kaduna zamu koma...?”
Murmusawa kad’an Daddy yai kana yace “Ina zuwa...”
Jim kad’an ya shigo rik’eda wata jaka ya mik’a masa.... “Akwai kaya a ciki inaso idan kai wanka sai ka saka su...”

Mamaki ya cika Khalid, ya kasa yarda da abinda yake gani na faruwa... Daddy bai kuma bi takansa yai ficewarsa, murmushi kwance saman fuskarsa....
Da tsananin mamaki Khalid Ke bud’e jakan... K’irjinsa ne yai wani irin yankewa ganin kayan dake cikin jakan, saida ya kwashe sakanni yana mai k’urama kayan idanu kafin ya soma cirosu...
Shadda ce ‘yar Ubansu, babbar Getznar sai yauk’i da shek’i take, fara k’al mai d’aukan idanu... Saida ya ida cirowa kana ya shiga warwarewa, Babbar riga ce sai ‘yar ciki da wando.. Kallo guda zakaiwa kayan kasan duk mad’inkin da ya d’inka kayan ya k’ware wajen iya d’inka kayan hausawa ta zamani....
Khalid ya fuzar da iska kad’an yana mai kuma juya kayan... Tabbas hasashena ya tabbata Daddy aure zai masa da Yesmin... Toh mai yasa zasu b’oye masa irin haka, shin suna tinanin bazai masu biyayya bane... Abubuwan da suka faru a ‘yan kwanakin suka shiga dawo masa daki daki... Wannan shine manufan Daddy na canza masa lokaci guda... Why Maiyasa Daddy zai masa haka...? Wata zuciya tace ka bishi a haka don tabbatar da abinda zuciyarka Ke raya maka... Zato kawai kake har yanzu tinda bai bud’i baki ya sanar dakai komai ba... Koda yayi wanka umarnin mahaifinsa yai ya shirya cikin wannan manyan kaya na alfarma... Tsaye yai yana kallon kansa cikin full-length mirror, shi kansa wani girma yaga yayi ma kansa had’ida wani k’warjini na musamman, dan har saida ya tsinci kansa da matsananciyar fad’uwan gaba, yanaji ajikinsa yau d’in ranace ta musamman a garesa dikda zuciyarsa dake ayyana masa cewa idan har aurensa da Yesmin ake shirinyi, toh yau d’in zata iya kasancewa rana mafi tashin hankali a rayuwarsa... Ya lumshe dogayen idanunsa a hankali daidai sanda Aunty Daula ta soma knocking k’ofar d’akinsa... Bata izinin shigowa yai yana mai d’an takowa daga cikin closet d’in... Aunty Daula ta shigo sallama saman bakinta tana fad’in ya fito su karya su d’au hanya...
Daskarewa tai tana dubansa yanda ya fito sak ango... Aunty Daula ta gaza b’oye Farin cikinta tana fad’in “Masha Allah Yayansu... Ka fito ras dakai...”

Murmusawa yai kad’an kana yace “Aunty wai meke faruwa ne... Dan Allah ki sanar dani...”

Ta kuma murmusawa a hankali kana tace “Ba’aji mutuwar sarki a bakina ba... Amma before anything, we’re all waiting for you downstairs, Daddy yace baiso mu makara... Muna jiranka...” Bata jira cewansa ba ta fice cikin sauri tana kuma murmusawa...

A hankali ya fuzar da iska mai d’umi kana yasa kai ya nufo k’asa....Su Humy har suna had’e baki wajen cewa “Woow kayi kyau Yaya...”
Ijlal tace “Kaima yau ka zama Daddy ne, ka saka irin kayanshi...” Gaba d’aya suka d’an dara..
Humaira ta kuma cewa “I’ve never seen wanda babban kaya ya mishi kayu irinka ba Yaya.. Pls ka dinga sakawa kaji...”
Murmushi kurum yai had’ida shafa kanta, idanunsa naga mahaifinsa da ya kasa janye nashi idanun daga Barin duban Khalid d’in, ga wani musulmin murmushin Farin ciki saman fuskarsa... Shi kanshi d’an nashi ya masa kyau har ya gaji, ga wani girma da k’warjini na musamman da suka sauk’ar masa... Aunty Daula tana satan kallon d’ah da mahaifin yanda suka zubawa juna idanu gwanin ban sha’awa da tausai... Cikin sauri ta shiga serving Khalid d’in tana tambayar shi idan akwai wani abinda yake so...

Shidai Khalid gaba d’aya bai wani iya cin abincin ba, ya k’agu baiji shirin Daddy akansa ba... Aunty Daula ta dubi su Ijlaal da suka ida cin abinci tace maza suje Karima ta ida shiryasu, idan zasuyi fitsari ma duk suyi kafin su d’auki hanya.. Itama dai mik’ewa tai dan ta lura d’ah da mahaifin suna buk’atan kad’aicewa suyi magana...
Dining area ya rage saura su biyu, Khalid sai juya spoon yake cikin mug, da ganinsa kasan hankalinsa bai jikinsa... Kaman daga sama saijin hannun Daddy yai saman nashi...
Ya d’ago a hankali yana duban mahaifin nasa
A hankali Daddy yasa duka hannayensa ya kamo kafad’un Khalid ya mik’ar dashi tsaye suna fuskantar juna....
Murmushi saman fuskar Daddy, kana iya hango kwantattun k’walla cikin idanunsa lokaci guda yake furta “You look very handsome my son.... Kai d’in a yau zaka kuma cika babban mutum, idan ban tab’a fad’a maka ba Khalid toh yau zan fad’a maka... I am very proud of you Son, kai d’in ka cika d’a mai biyayya... Na gwadaka ta hanyoyi daban daban kuma duk kaci jarabawarka.... Ko yanzu na bar duniya nayi imani kaidin zaka iya kulamin da ahalina... Allah Ubangiji ya maka Albarka, ya albarkaceka da zuri’a d’ayyiba masujin k’an iyayensu da yi masu biyayya kaman yanda kai mana....Ina kuma fata zakai Farin ciki da zab’in da nai maka da kuma hukuncin da na yanke a gareka...”
Izuwa lokacin zuciyar Khalid tai rauni sosai.... Cikin sauri ya kamo hannayen Daddy, cikin k’ok’arin dakewar murya dukda rauni da yakeji daga can k’asar zuciyarsa ya soma fad’in “Daddy dik abinda ka yanke akaina kayi daidai... Kuma bazan tab’a questioning d’inka ba... And zaka sameni ina mai yi maka biyayya.. I know you love me and bazaka zab’a min abinda zai cutar dani ba....Na sani our family isn’t perfect, we have our differences, if there’s one thing da mutum bazai zab’a ba shine family d’inshi... We don’t choose our family... Haka Allah yake gudanar da al’amarinsa... Saidai mu wayi gari mu ganmu tareda mutanen da yaso ya ganmu dasu ya kuma zab’a mana a matsayin family d’inmu... Daddy inaji a cikin zuciyata cewa nid’in mai sa’a ne da Allah yasa na kasance d’anka.... Thank you for everything Daddy....”
Hawayen da Daddy Ke mak’alewa suka ziraro, lokaci guda ya rungume d’ansa sosai cikin jikinsa yana jin k’aunarsa na ratsa zuciyarsa...
Aunty Daula dake hangosu daga kitchen share hawayen da suka gangaro mata, tausayin d’ah da mahaifin ya cika zuciyarta....

Murmushi Daddy ya sakar mashi yana mai gyara masa zaman hularsa kana ya warware agogon dake d’aure hannunsa ya shiga d’aurawa Khalid d’in da kanshi... Murmushi kwance saman fuskarsa, shima Khalid d’in murmushi yake...
Daddy yaci gaba da fad’in “There... Now you look even more handsome...”
Khalid ya kuma sakin murmushi kana yace “Na gode Daddy...”
Shafa fuskarsa Daddy yai kana yace “Khalid a yau zamu tafi amsar aurenka da macen da Allah ya zab’a maka a matsayin abokiyar zama... Are you happy...?”

K’ak’aro murmushi yai dikda tsananin bugu da k’irjinsa keyi kana yace “Yes... Yes Daddy... I’m very much happy...”
Kana ganin yanda yai maganar zaka fahimci k’arfin hali ce kawai...

“Well, sai mu d’au hanya kar mu makara...” Ya k’arashe yana mai kiran matarsa Daula...

***

Kai da Kaga Hafiz Kaga ango, sai watsa k’amshi yake yasha wanka cikin dakakkiyar shaddarsa, bakinsa kaw ya gaza rufuwa tamkar gonar auduga, Sawwama dai bata tankasa ba har ya ida shirinsa, koda yace mata babu fatan Alheri sai ce masa tai fatan alherin kenan ta gama masa da ta had’asa dasu Babba Duna.... Ya isa yai kissing goshinta yana murmusawa kana yace “Tabbas kin bani gudumawar da tafi ta kowa....Bazan tab’a mantawa ba, nai miki alk’awari...”

Murmusawa tai kana ta mik’e ta d’au mayafinta dake lank’aye saman k’ofa...
“Rakiya zakimin...?” Ya tambaya yana dubanta...

Murmusawa tai kad’an kana tace “A’a kaje bikinka...”

Hafiz ya d’anyi rau rau da idanu cikeda shagwab’a kana yace “Bazaki raka mijin naki tarbo k’anwarki ba... Kinsan fah kece Yayar....”
Nanma murmusawa tai kana tace “Zanso nai maka rakiya amma nima wani auren zan tafi... Mahaifiyata da mijina zasuyi aure rana guda...”
Da mamaki Hafiz ke dubanta kana yace “Kina nufin Magajiya yau take aure...?”

Jinjina masa kai tai kana tace “K’warai kuwa, Kaga dole na tafi can na k’yaleka da amaryar ka kusha shagali nima na taya nawa mahaifiyar nata shagalin....”

Ya murmusa ya shafi fuskarta kana yace “Kice ina mata fatan alheri, kuma nayi murna sosai... Daga baya zanzo har gida nai mata murna...”

Sawwama ta jinjina kai tace “Zan isarda sak’onka in sha Allah...” Daga haka sakai tai abinta ta fice, tabar Hafiz shi kad’ai sai shafan hab’a yake yana sakin murmushi.....

***

Cikin dabara ya samu ya tsinka igiyar da tin jiya yake k’ok’arin b’allata da akai amfani da ita wajen d’aure masa hannu...Hannayensa gaba d’aya sunkuwa b’aci da jini alamun yaji jiki wajen kwancen hannun... Ya waiga yaga har yanzu dai masu tsaron nasa bacci suke basu farka ba dan jiyan tatil sukai da barasa, tinani ya somayi, mai zaiyi yanzu, idan yace zai gudu a wannan daji da baisan yaya aka shigo dashi ba baisan ta ina zai soma bi ba, baisan wata hanya zai soma bi ba tinda kanshi cikin buhu aka shigo dashi... Ya dafe kansa kad’an yana tinanin abinyi, kuma dole yai acting very fast kafin su tashi, aljuhun d’aya daga cikinsu data d’an zame ya hango wayar salula... Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ya lab’ab’a ya d’auki wayar da k’yar da sand’a....
Dubawa yai yaga chaji ya kusa k’arewa one percent ne... Dole yai dik yanda zai yayi making call d’in cikin sauri....


SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_




*87*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Kasancewar k’aramar wayace yasa Akram baisha wahala wajen bud’eta ba, sauri yake ya shigar da lambobin dan sai warning battery d’in yake masa yana nuna alamun low battery....
Wani ikon Allah lambar da ko nashi lambar waya bai haddace kamanshi ba sai yaji yana k’ok’arin kufce masa tsaban tashin hankali da ya tsinci kansa ciki... Ga wayar gab take da d’aukewa gaba d’ai danma Allah yasa Nokia akwai amanan rik’e chaji ne.... A hankali ya soma k’ok’arin saita kansa yana jera lambobin a natse....

****

Tsaf ya ida shirinsa cikin manyan kaya dan tuni Daddy ya sanar dashi cewa yau ake d’aurin auren Khalid, sam bai kawo gidan da Khalid Ke neman aure gidansu Zulfa’u bane, all he knows shine Akram ya yaudaresa zai kumayi k’ok’ari ya mance da komai, dan haka ya yanke tafiya auren Khalid maimakon amsawa Akram aure kaman yanda Akram d’in ya buk’ata ta bakin abokinsa Yusuf....

Muhibbah dake zaune gefe tana dubansa tamkar ta zuba ruwa a k’asa tasha dan Farin ciki, a hankali ta taso daga yanda take zaune ta iso garesa, links d’in da yake mak’alawa hannun rigarsa ta amsa taci gaba da saka masa, har lokacin tana iya karanto tashin hankali kwance cikin fuskarsa tasan kawai daurewa yake matsayinsa na jajirtacce mai shirin zama shugaba ga d’unbin al’umma...
“Excellency na yanzu auren Khalid dai zaka tafi kenan....?”
Tamkar bazai amsata ba haka yai, saida ya kwashe wasu sakanni kana yace ta mik’a masa turare... Babu musu ta isa gaban dressing mirror ta d’auko turaren, zai amsa ta girgiza masa kai alamun a’a kana ta shiga fesa masa... K’uri kurum yai mata ba tareda ya tankata ba har ta ida abinda take....
Murmushi saman fuskarta tace “Wow yau d’in kayi kyau na musamman mijina karfa kaje kafi ango yin kyau... Ka ganka kuwa...?” Yanda tai maganar sai taso basa dariya, yasan k’ok’ari kawai take to cheer him up... Gefen fuskarta ya d’an shafa kana yace “Toh ni na wuce... Jalo will drive me....”

Muhibbah ta kuma murmusawa kana tace “Toh a dawo lafiya Excellency na... I love you...”
Bai tsaya amsata ba yasa kai ya fice... Aiko yana ficewa tai tsallan murna ta

Please Login or Register in order to submit comment