Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kud’ad’ensa....


Saida suka tik’i rawa sukai lis kafin aka shige da Sawwama parlorn Hajiya aka soma bada amana....Su Sahariyya suna daga waje ana faman cashewa Yayansu yayi auren gata auren masuyi ba aure irin na Zulfah ba da aka lik’a masa jaraba....

A can gidan Aunty B kuwa Zulfah na zaune tayi jigum tana tunanin rayuwa, a kullum tunaninta da mafarkinta shine INDA RAI DA RABON aurensu ya d’ore itada Ya Hafiz, tabbas ba auren soyayya sukai ba aurene na had’i tsakanin iyaye amma har k’asan zuciyarta tanajin zafin ace ta rabu da mijinta kuma uban ‘yarta, taso ace sun rayu tare sun raini d’iyarsu tare sai dai Allah bai k’addara hakan ba, ta kuma yi imani zab’in Allah shine zab’i na k’warai... Bata tab’a kawowa Ya Hafiz bazai maidata d’akinta ba bata tunanin saidai taji labarin aurensa daga sama ba sai gashi duk hakan ne ta kasance, tabbas mutuwar aure jarabawane mai tsananin wuya koda ace baka k’aunar mijin, fatanta Ubangiji ya bata ikon cin wannan jarabawa bazata kuma ta daina addu’a wa d’iyarta ba Allah ya inganta mata rayuwarta a duk yanda zata tsinci kanta....

Tana cikin wannan tunani ne taga kiran Mamy na shigo mata, jikinta ya kuma yin sanyi, a hankali ta d’aga wayar saidai kafin ta iya furta koda kalma kuka ya kufce mata, lallashi da shawarwari na gari Mamy ta dinga bata har saida Zulfan taji tausayin kanta dana mahaifiyarta sanin cewa mahaifiyarta batasan da mutuwar Aurenta ba har rana mai kaman ta yau, yinin ranar haka Zulfa’u tayishi jiki a mace...

A can gidan biki kaw Hafiz da kansa yazo ya d’auki matarsa suka tafi gidansu bai bari ko wata mata ta kai mishi ita ba.. Suna isa Sawwama ta yaye lullub’in dake kanta don dama tuntuni ya isheta da nauyi k’awayen Magajiya ne suka hanata cire lullub’in tuntuni...

Mik’ewa tai ta shiga bin gidan kallo ta fito da sauri tana hangen ta yanda zata hango uwar gidanta, wayam bataga kowa ba.... Dawowa parlor tai ta samesa yana kwance k’ullin kaza da ya shigo dashi kana tace “Ina matarka...?”

Ba tareda ya dubeta ba yace “Tayi tafiya....”

Sawwama ta kuma dubansa kana tace “Tafiya.... Tafiya fah kace.... Kasa jure amsar amaryar tata tai shi ya sanyata yin tafiya koko dai salon nata kishin kenan....?”

Bai tankata ba yaci gaba da abinda yake....

Sawwama ta gyara tsayuwa tace “Magana fah nake maka...”

“Toh ai maganar taki ne batada amsa...” Ya fad’i nan ma ba tareda ya dubeta ba...

K’wafa tai tana watsa masa mugun kallo kana ta nemi waje ta zauna tana sakin hamma....

Ya ida warware ledar kan yayi wani aune Sawwama takai hannu ta cafko tsoka guda ta wuga a baki sai sautin taunarta ne kawai ke tashi....

Hafiz ya d’ago idanu yana dubanta tsaban takaici saida yaji dama bai warware ledar ba...

Tsame hannunsa yayi kana yace “Kije ki d’auko plate a kitchen a haka ai bazai maki dad’in ci ba....”

Ba tareda ta kallesa ba sai aikin tauna take tana gwaguyan k’ashi tace “Wayace maka kazar amarci a plate akeci, idan baka sani ba na k’ara maka ilimi a ledarta akeci...” Ta k’arashe tana kuma karyo cinyar kazar ta shiga dannawa a bakinta...

Tamkar wanda ruwa ya shanye haka yayi zaune dirshan a wajen yana kallon ikon Allah, ya tuna aurensu da Zulfah k’in siya mata kazar yayi har saida abokansa suka sai mata kuma ko da ya kawo batamaci ba hasalima da safe ya tadda ta d’uma masa kazar ta saka masa a flask idan bai mance ba da kazar marcin Zulfah yayi breakfast maiji da lafiya...

Guntun tsaki yayi kana ya mik’e ya nufi kitchen d’auko plate, babban abinda ya bashi mamaki shine daga fitarsa zuwa kitchen veranda kawai ake tsallakewa amma koda ya dawo ya tadda Sawwama ta gama da kazar nan tas sai curin k’asusuwa da ya hango....

Tamkar maraya haka ya shigo da plate a hannu yana dubanta...

“Ina kazar....?” Ya tambaya sanda yai mata tsaye aka...

Wani kallo tai masa a dak’ile kana tace “Ban gane ina kaza ba, dama kazar na waye...? Ince tawace toh na cinye kayana...” Ta k’arashe tana sakin gyatsa mai k’arfin gaske....

Tsabagen takaici bai kumabi takanta ba ya shiga d’aki yayi shirin baccinsa...

Haka nan ta shigo ta taddasa kwance da alama bacci ya soma yin gaba dashi...

Dariyar rainin hankali ta saki kana tace “Eh lallai dole kazo ka bajemin a gado kana bacci, idan kasan wata bakasan wata ba....”

Hannu tasa ta shiga bubbugashi tana fad’in “Hafiz... Tashi fah zakayi don yau ba ranar bacci bane....” Ta k’arashe tana juyi gabanshi had’ida zuge zip d’in rigarta....

Dirshan ya tashi ya zauna ga d’an banzan yunwar dake azalzalarsa, ko d’an sallahn nuna godiya ga mahalaccinsu da ni’imar da ya azirtasu dashi Sawwama ba bari sunyi ba ko dashike shima gogan aurenshi na fari Zulfa’u ta tarsasa masu yin sallah, dashike shima ba gwanin son sallar bane tuni ya shiga biyewa amaryarsa suka lula duniyar ma’aurata...

Tun ango na zak’ewa had’ida nuna k’warewarsa har dai ya fahimci shi jariri gaban amaryar tasa, tun yana fahimtar mai ake ciki har dai ya rasa gane da wacce yake tare amarya tasa budurwa ce ko kuwa akasin haka, a dole Hafiz ya sakarwa amarya ragamar komai ya koma sai direction d’in da tabi dashi...

Daren aurensa da Zulfah ya tuna dukda cewa a shaye ya dawo mata dare ne da bazai tab’a shafewa ba a tarihin rayuwarsa, sam babu had’i tsakanin Zulfah da Sawwama, jikin dake tsole masa idanu a waje ashe duk hotone ta gama sakwarkwacewa ko Zulfah data haihu ta shayar da d’iya jikinta yafi na amaryasa zama zamzam....

Gaba d’aya zuciyar Hafiz a cushe yake gashi bawai enjoying kasancewarsu yake ba ga uwar yunwa da gajjiya da suka kuma sauk’ar masa lokaci guda ga amarya batasan gajjiya....

Da k’yar Hafiz ya samu ya k’waci kansa kiran sallan farko ya tsarkake jikinsa ya d’auro alwala ya nufi masallaci abinda bai saba ba fita sallar asuba sai gashi a sahun farko yana jiran liman ya k’araso...

Wasu daga cikin mutanen unguwar saida abin ya d’aure masu kai, idan yaga suna dubansa saidai kawai ya kawda kai gefe don bazasu gane bala’in da ya baro a gida.....

Koda aka idar da sallar asuba kasa komawa gida yayi ala dole ya tsaya sauraren karatun bayan sallan asuba, bashi ya dawo gida ba saida gari ta soma haske, gaba d’aya jikinsa ciwo yake masa yawa an masa duka....

Cikin sand’a yake takowa tamkar mai tsoron kada wani ya jishi, a haka ya tura k’ofar parlorn ya shige sad’af-sad’af ya d’an yaye labulen k’ofar d’akin yana hangenta yanda ya hangota sai sakin minshari take ta barbaje tana bacci ko shakka babu bata gabatar da sallan asuba ba...

Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya yayi kafin ya dawo parlor da k’yar yake d’aga k’afafunsa da kwankwasonsa da suka masa mugun tsami ya zube saman doguwar kujera tuni bacci yayi awon gaba dashi...

Sawwama kaw tana tashi rana tsege-tsege ta shige band’aki ta jajjab’a wankanta ta fito tayi sallah a gaggauce kaman yanda ta saba, zuciyarta fari tas ta tsala wankanta ta cancad’a kwalliya ta fito parlor ta tadda Hafiz tamkar gawa sabida yanda ya sake jiki saman kujera yana baccin huce gajjiya, murmushi tai a zuciyarta tace duk yanda akai matar taka raguwace...

Batabi takanshi ba ta kunna radio sautin wak’ar marigayiya Barmani mai coge ya shiga tashi, sai tik’a rawa take tana bin wak’ar dake tashi duk iya sallaman da ake bataji ba Sahariyya ta kalli Najah kana tace “Ke bazasujimu ba mu shige kawai...”

Kai tsaye suka kutsa kai cikin parlorn sallama saman bakunansu....

Kallon arziki basu ishi Sawwama ba don ci gaba ma tai da tik’ar rawarta ta barsu nan tsaye da flask d’in abinci suna kallon ikon Allah....

Hango Yayansu kwance magashiyan saman kujera ya sanyasu kuma duban juna...

Sahariyya tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi ta isa gareta tana gaidata had’ida sanar da ita karin kumallo suka kawo....

Sai sannan Sawwama ta rage sautin kafin ta juyo ta dubesu a dak’ile

“Toh da kuka kawo karin sai akace sai kun sanar dani, nan ba fili bane da bazaku ajiye ba, koko dai salon ku katsewa mutun jin dad’insa inyi...,?”

Sahariyya ta kasa daina mata kallon mamaki, Najah tai k’arfin halin sakin murmushi kana tace “Wai dama Hajiya ce tace mu gaidaku mu dubo mata yaya kuka tashi....”

Batakai aya ba Sawwama tace “Toh kun gani ai garau muka tashi, yanda kukazo kuka tadda matar gidan ya tabbatar maku da hakan idan kuma ba salon gulma ce irin taku ba...”

Sahariyya ta had’iyi k’atutun bak’in ciki, a dak’ile tace da ita “K’warai munga kin tashi garau Yayan namu kuma fah munaso muji yaya ya tashi don muje mu sanar da Hajiya, sannan kud’in zuwa kawai ta bamu ba dawowa tace mu amsa wajen Yaya...” Ta k’arashe tana juya mata idanu itama....

Murmushi mai shewa Sawwama ta saki kana tace “Ke banson rashin kunya babu ubanda ya isa ya tayar min da miji lokacin tashinsa baiyi ba don haka ku wuce ku fice min a gida tunda sauran raha a fuskata, wacce ta aikoku d’in idan bata baku kud’in adaidaita ba kwa koma da k’afafunku...”

Sahariyya zatai magana Najah ta janyo hannunta tana mai girgiza mata kai alamun tai shiru kana tace “Kinga Addah mu tafi kawai...”

Sahariyya tai k’wafa kana ta janyo hannun k’anwarta suka sa kai zasu fice a dai dai lokacinda Sawwama ta janyo foodflask d’in da k’afafunta ta bud’e tai tozali da soyayyiyar k’osai nasha-nasha amaimakon wainar k’wai da kaji ko kifi kaman yanda tai tsammani hakan ya tabbatar mata flask d’in ruwan zafin da tai tsammanin ruwan shayi ne kenan ruwan kunu ne, tabd’i aiko bazata sab’u ba har sun isa veranda ta k’walla masu kira

“Kai Kai ku dawo nan....!”

A tare suka juyo suna dubanta...

Sawwama ta gyara d’aurin kallabi kana tace “Meye wannan...? Waye kuke zaton zaici maku wannan abin, ku tattara ku maida ku kawo abincin da ake baiwa amare...” Ta k’arashe tana shura masu foodflask d’in da k’afarta....

Sahariyya da tuni hak’urinta ya gaza banda huci bata komai a zuciye tayo kanta sai kuma Najah tai saurin rik’ota....

Sawwama tai tsaye tana murmushi mai kamada ki kwatanta, Najah tace “Addah Sahariyya d’auka don Allah mu tafi aka gane muna fad’a da ita dariya za’ai mana tinda ansan yanda mukeda Zulfah....”

Banda harara babu abinda Sahariyya keyi, itako Sawwama tuni ta tura k’ofar parlornta ta shige ta barsu nan tsaye da abincinsu suna iya juyo yanda ta k’ara sautin wak’arta tana ci gaba da tik’ar rawarta...

Haka suka tattari kulolin suna mamakin wane irin bacci Yaya Hafiz yake duk wannan bidiri da ake baiko motsa ba balle ya tashi...

Haka suka komo gidawa Hajiya nik’i-nik’i da sanyin gwiwa...

Hajiya tana hangosu ta fito tana washe baki tana tambyarsu yaya ankai, yaya suka sami surkarta da d’anta....

Najah ta kalli Sahariyya da tuni ta saki tsuka ta dangwal kwanon hannunta tai shigewarta d’aki...

Hajiya ta bitada kallo cikeda mamaki kana ta maido da dubantaga Najah tace “Wai juye abincin sukai suka baku kwanukan ku dawo dashi... Allah sarki kaji d’iyar albarka har wanke kwanon tai...”

Batakai aya ba Najah ta katse ta da fad’in “Hajiya.. Abincinki akace mu dawo miki dashi amarya bataci snnan d’anki kuma kwance magashiyan muka taddasa don har muka shiga muka fito ban tsamman yasan munje ba, sirkarki kuwa ras take donma rawa mukaje muka taddata tana tik’a...” Daga haka sakai Najah tai zata wuce ta bar Hajiya rungume da kwanon k’osai tana k’are masa kallo...

Har Najah ta isa bakin k’ofar parlor ta juyo taceda Hajiya “Aw na mance Amarya tace wainar k’wai da kifi ko kaza zataci had’ida shayi maiji da lafiya...” Tana ida fad’in haka ta saki labulen parlorn ta shige...

Hajiya da zuciyarta ke faman bugu daurewa tai ta shiga masu sababi da fad’in “Yo ko ta fad’i haka ai batai k’arya ba, idan abinda takeso kenan ai sai a mata ba wani abu bane... Kudai shegen rashin hak’uri ne irin naku... Ince d’azun da rawar kanku kuka banne ni zaku kai mata kari don ku saba.. Kunje kuna masifa da rawar kai irin taku da kuka saba yo ba dole ku gundireta ba...” Ta k’arashe tana jefa k’osai guda a baki nan ta hangi Raihanah dake bakin famfo tana wanke wanke a gabanta akai komai, suna had’a idanu Hajiya ta sakar mata dak’uwa tana fad’in “Kin kalli uwarki mayya kawai.. Taso ki wuce ki tafi bakin babban kwalta ki sayo kifi yanzu ki d’aura idanma masu kifin bakin hanya basu fito ba ki wuce kasuwa ko tasha... Taso mana ina miki magana kahura kawai...” A d’ari Raihan ta k’arashe kashe famfon wanda da k’yar ake d’aure bakin hasalima ita kad’ai ta iya rufewa idan bata rufe da kyau ba ta bari ruwa yayita zuba haka zata fice mak’ota d’ebo ruwa a rijiyan mak’ota...

Jiki na rawa ta k’araso wajen Hajiya ta amshi kud’in ta d’auko hijab d’inta ta fice sai zuba sauri take tsoron kada tayi latti Hajiya ta jibgeta...

Daga yanda take tafiyar tana zuba sauri zaka fahimci sam ba’a nitse take ba tsoro da fargaba su suka cika mata zuciya, alla alla take ta samu masu kifin babban kwalta sun fito, aka kuwa yi sa’a mai teburi d’aya ya fito..

Sauri sauri Raiha ta sayi gammo guda na kifin kaman yanda Hajiya ta aiketa ta shiga zuba sauri don ta samu ta isa gida da wuri ga goyon Kausar a bayanta don dama haka take kusan yini da yarinyar a bayanta tana rainonta koda aikin gida zai kasheta tinda yaran Hajiya bayi zasuyi ba..

Kaman daga sama haka yaga giftawarsu ta gabansa, yayi saurin danna birki yana karanto innalillahi...

Cikin sauri Sameer ya fito yana duba mutanen da ya kusa kad’ewa idan zai iya tunawa irin haka ne kwanaki ya kusan faruwa dashi sanda ya kuskuri wata budurwa d’aukeda k’aramar yarinya...

Kausar na kuka Rainaha na kuka, ita Kausar kukan razana take yayinda Raihana ke kukan gammon kifin Hajiya da ya watse cikin culvert mai d’aukeda gurb’ataccen ruwa....



SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_




*26*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*





Sameer ya k’araso tamkar mai sand’a yana k’ok’arin duk’awa had’ida duban fuskar budurwar nan dake shesshek’ar kuka a hankali tana jijjiga yarinyar dake bayanta, duk sai yaji babu dad’i musamman da yaga gaba d’aya suke kukan babu babbar babu k’aramar, dama shi tuntuni mutum ne wanda kuka ke tsananin d’aga masa hankali musamman yaga mace ko k’aramin yaro na kuka duk yaji hankalinshi ya tashi...

Murya a hankali ya furta “Sannu koh.... Bakuji ciwo ba...?”

Sai sannan Raihanah ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubansa, maimakon ta masa magana sai kuma ta k’ara tintsirewa da kuka had’ida kifa kanta bata daina jijjiga Kausar da tuni ta bar kuka ba sai sakin ajiyab zuciya da takeyi.....

Sameer ya d’an shafi sumarsa cikeda damuwa kana ya kuma kai dubansa ga budurwar mai tsnanin k’arancin shekaru a iyaka duban da ya mata....

Duk’awa ya kumayi gabanta wannan karon kana yace “Akwai yanda ke maki ciwo ne....?”

Nanma shiru bata bashi amsa ba saima dad’a had’e hannayenta biyu datai waje guda tana matsan hawaye...
Har ya cire rai bazatace komai ba sai kuma ta shiga girgiza masa kai alamun a’a....
Samun k’warin gwiwar dad’a tanbayarta yayi...
“Inane gidanku...?”

Wannan karon d’ago watery eyes d’inta tai tana duban mutumin sai kuma ta dad’a kai dubanta ga kifin da tuni watse cikin ruwan dotti kana tace “Ni bazanje gida ba Hajiya duka zatamin....”

Yanda tai maganar yasa Sameer kuma dubanta sosai kana yace “Maiyasa zata bigeki.....?”

Sabon kuka ne ya kuma zuwa mata bata iya bashi amsa ba sai nuna masa culvert da ta shigayi tana mai ci gaba da shesshek’an kuka, Sameer yakai dubansa sosai ga culvert d’in yana kallon abinda take k’ok’arin nuna masa, maido da dubansa gareta yayi kana yace “Idan na fahimceki aiken Hajiya ne ya zube a nan koh...?”
Tai saurin jinjina masa kai tana mai share hwayenta...
“A ina ake saida kifin...?”
Ya tambaya yana dubanta...
Alama kurum ta masa da hannu tsallaken titi ba tareda tace komai ba....
Sameer ya jinjina kai kana yace “Just wait for me here kinji koh, I’ll be right back...”
Batace masa komai ba sai sadda kanta k’asa da tai tana matsan sauran hawayenta had’ida tausayin kanta da takeji don tasan yau dole ta daku hannun su Hajiya donma Sahariyya yau tanaji da nata k’unci da ta nad’i na jaki wajenta...

Jim kad’an ya dawo da gammon kifi kusan guda biyar cikin leda kana yace “Shiga mota na kaiku gidan naku...”

Dubansa ta d’anyi kana tace “A’a ni bazan shiga ba an hanamu....”
Sameer ya d’anyi shiru tamkar mai tunani kana yace “Idan na tare maki adaidaita zaki shiga...”
D’ago manyan idanunta masu tsananin haske tai tana dubansa sai kuma ta kauda kai gefe tace “Ai gidanmu babu nisa k’asan layin can ne....” Ta k’arashe tana mai nuni da hannunta...
Sameer yakai dubansa ga yanda tai masa nuni ya d’ago left hand d’insa yana duba time sabida surgery da yakedashi a asibiti, bai kuma ce mata komai ba sai komawa motarsa da yayi ya zaro key d’in had’ida sakata a security lock sannan ya dawo yanda Raihanah ke tsaye tamkar wacce ruwa ya shanye...
Duba guda Sameer ya mata kana yace “Muje ni zanyi maganawa Hajiyar bazata dakeki ba kinji koh...”
Raihanah da k’irjinta ya bada sauti saurin girgiza masa kai tai kana tace “A’a ka barshi kawai zan koma dakaina...”
Kallon da ya mata ya sanyata yin shiru, Sameer ya kuma fad’in “Muje..”
Wannan karon babu musu ta shige gaba yana biye da ita har suka iso layin nasu...

Koda suka iso k’ofar gidan kasa shiga Raihanah tai sai kallon ledae dake hannunsa take alamun tanajin tsoron shiga babu aiken kifin Hajiya...
Sameer na hankalce da ita, mik’a mata ledar hannun nasa yayi yana mai dubanta...
Hannu ta d’an mik’a zata karb’a sai kuma ta fasa..
Sameer ya gyara tsayuwarsa yace “Amsa ki kai mata sai ki sanar da ita ana sallama da ita a waje...”
Girgiza kai Raihana tai kana tace “Kifin gammo gudane ai kawai...”
Sameer ya jinjina kai yace “Babu damuwa ki kai mata ki fad’a mata sak’ona...”
Jiki a sanyaye ta amsa had’ida masa godiya kafin tasa kai zata shige gidan cikeda fargaba da tsoro nan ta jiyo muryarsa yana tambayarta sunanta...
A hankali ta juyo kaman mai tsoron magana tace dashi “Raihanah...”
A zuciyarsa ya maimaita sunan kana yabi bayanta da kallo cikeda tausayawa, sau tari yakansha mamaki idan yaga iyaye na dukan yaransu kaman basusan cewa yara babban kyautace daga Allah wanda ba kowa yake badawa, yanaji a ransa duk randa ya haifi nasa yaran bazai dasa masu tsoronsa cikin zuciyarsu ba saidai tsoron mahaliccinsu, yaransa zasu zama abokansa ta yanda bazasu b’oye masa komai ba zasu sharing komai dashi, rayuwa mai cikeda jin dad’i yake hango masu shida Partner da kuma yaranda zasu haifa in feature...
A hankali ya saki murmushi had’ida daidaita tsayuwarsa yana jiran fitowar Hajiya...

Duk daga nesa Hajiya ke aika mata dak’uwa da ashariya tana fad’in uwar mai ta tsayayi sai yanzu zata dawo, tuni ta janyota ta shiga rank’washi Raihanah na bata hak’uri, tuni su Sahariyya da Najah suka fito kallo suna dariya don dama idan Raihana tayi laifi idan Hajiya na bugunta tsallen da take tamkar ‘yar kenwace ke basu dariya

Cak Hajiya ta tsaya da bugun nata tana kallon damin kifin da tasan bata bata kud’in sayo kifi mai yawa haka ba...
D’ago fuskarta Hajiya tai tana kallo kana tace “Ke tsaya badai karuwanci kike da masu saida kifin ba suke arha maki haka....” Ta shiga doka salati tana tafe hannaye had’ida kuma mak’uro Raiha tana fad’in “Raiha... D’ago ki kalleni don ubanki ki fad’amin mai kike basu suke maki arha... No wonder shiyasa kika dad’e mana kin shige shagon mai kifi ya gama matseki dole ki dawomin da damin kifi toh kuwa a kunnen ubanki don nidai bazaki janyo min zagi a gari ba...”

Su Najah da Sahariyya an tab’o yanda ke masu k’aik’ayi tuni suka fito suma suka mata caa suna binta da kallon k’yama..

Cikin kuka Raihana ke fad’in “Hajiya ki tsaya kiji Hajiya wllhi ba haka bane babu abinda nayi Kausar itace shaidata...”
Haba nan fah su Sahariyya suka kwashe dariyar rainin hankali kana Sahariyya tace “Kunji shegiya wai Kausar shaida a gidan uban wa kika tab’ajin yarinya k’arama ta bada shaida ke annabiya ce kokuwa salon iskancinki ne haka, ma uban wa zaki raina hankali... Hajiya ki kwab’e mata fatari ki gani idan ba’a gama bud’ata waje ba... Shegiya k’aramar karuwa...” Ta k’arashe tana kai mata rank’washi mai tsananin zafi wanda ya sanyata sakin k’ara..
Hajiya na huci take fad’in “Naja mik’o min muciya naci uwarta da kyau sai ta fad’imin uban da take shagon masu saida kifi...”
Raihana ta bud’e baki zatai magana Hajiya ta gwab’e bakin da hannunta Sahariyya ta finciko Kausar daga bayan Raihanah ta ijiyeta k’asa, Kausar ta saki kuka mai k’arfi a daidai sanda Najah ta taho da muciyar tuk’a tuwo ta dank’awa Hajiya, Hajiya ta shiga shima mata tamkar an aikota..
Allah sarki Raihanah da ba’a bata dama tayi bayani ba sai ihun azaba take tana rok’on Hajiya da tai hak’uri zata fad’a... Abin tausayin shine dagaji kasan tsananin azaba ne kurum ya sanyata cewa zata fad’a ita kanta batasan mai take fad’i ba..

Daga yanda yake tsaye yaji shiru shiru bata dawo ba ga kunnuwarsa dake jiyo masa sauti kaman na kuka da hayaniya, gabansa ya fad’i ya yanke kardai dukan yarinyar nan ake...
Bai wata wata ba ya yanke shawarin kutsa kai cikin gidan ceton yarinyar nan....

Hango Mace da yayi sai jibganta take tana ihu ga wasu gefe suna shewa ya sanyashi saurin k’arasawa ya amshe muciyar daga hannun Hajiya yana fad’in “Idan kika kasheta koda ace ‘yarkice sai na maka ki a kotu...!” Yanda yayi maganar gaba d’aya hankulansu ya dawo gareshi..

Ido cikin ido Sameer ke duban Hajiya, wani irin fad’uwan gaba had’ida firgici suka dirar mata lokaci guda... Ta tuna sanda ta toshe bakin Ma’aruf dake tsananin kuka yana kiran Mamynsa da tsumma ta jefashi bayan bus suka bar gari, ta tuna yanda ta damk’ashiwa Aminiyar sirri bayan ta gama azabtar da yaron... K’wayan idanun bazasu iya b’ace mata sabida k’wayan idanu ne masu tsananin wahala ace mutum ya mance, Hajiya ta kasa koda motsawa sannan ta kasa bud’e baki ta furta koda kalma guda ta kuma kasa janye idanunta daga duban wannan mutumi da gani take tamkar d’an marayan azikine Allah ya tayar da abinsa..
A b’angaren Sameer ma kallon fuskar matar yake kaman yanaso ya tuna yanda yasan mai irin fuskar saidai sam ya kasa tunawa, tamkar ya tab’a cin karo da muguwar mata mai tsananin kamanni da wannan matar a can wasu shekarun baya su kuwa su Sahariyya da Najah mutuwar tsaye sukayi suna santin wannan had’edd’en saurayi d’an gayun had’ida mamakin mai ya shigo dashi cikin gidansu....

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_..............DA RABO_



*27*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Haule da gaba d’aya gumi ke tsartsafo mata k’ok’arin daidaita kanta tai kana tace “Toooh kaikuma asuwa... Wane uban ne ya baka izinin shigowa kan matan aure...? Bakai zubin masu saida kifi ba da sai nace kaine daduron nata, aikin banza aikin wofi...”

Tinda ta soma magana Sameer ke dubanta, bai tankata ba sai duk’awa k’asa da yayi yana duban Raihana cikeda tausayawa yanda jikinta yayi luhu luhu ya tara jini... Sahariyya ma batasan sanda ta duk’a ba had’ida rafka uban tagumi tanai masa mayen kallo kaman zata lasheshi....

Kasa furta koda kalma yayi saima tsananin tausayin yarinyar da ya kuma rufeshi, d’agowa yayi yana ma Hajiya wani irin kallo mai tsananin firgitata kana ya mik’e tsaye yace “Duk yanda akai ba kece kika haifeta ba.. amma ki sani yatsa guda idan kika sake d’aurawa akanta....”

Hajiya ta katsesa da fad’in “Mai zakayi... Nace mai zakayi... Hukuma zaka kiramin toh kira gwangwani uwar d’amara...”
Bai furta komai ba sai duban da yake mata, ruri da wayarsa ta d’auka ya sanyashi tuna ashe jiranshi ake a asibiti...
Wani kallo ya kuma baiwa Hajiya wanda ya k’irjinta bugu kaman an sauk’e guduma kana yasa kai ya fice daga gidan zuciyarsa bai daina masa wasu irin tunani sarara ba....

***

Hafiz bashi ya tashi sai wajajen k’arfe goma na hantsi, ya yunk’ura zai motsa yaji k’ashin bayansa na amsawa, banda sarawa babu abinda kansa keyi...
Tsaye ya hangi Sawwama da kwaskwon turaren wuta sai zagaya gidan dashi take tana ‘yar wak’enta, hammar yunwa ya kuma saki ga k’amshin turaren sam bai masa ba, yayi k’arfin halin mik’ewa ya nufi band’aki, jim kad’an ya fito ya taddata a parlor tana kunna kayan kallo k’afa guda akan guda sai taunar chewing gum k’araras....
Zaune yayi gefenta yanata faman jira ta gaisheshi amma shiru baiji alamun zata gaishe shi d’inba....
Shafe goshinsa ya

Please Login or Register in order to submit comment