Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa rik’e zumuntarsu balle su d’aura yaransu bisa... Shin wannan wace irin rayuwa ce mai cikeda rashin yafiya....!” Tai maganar tana mai dafe k’irjinta... A d’ari Abbah ya tashi ya tallafota yana mai bata baki da sanyaya mata zuciya, shima Baba Alhajin kasa fita yai sukai chaa kan mahaifiyar tasu ganin tana numfashi da k’yar...
Sameer da tashin hankali ya nuna sosai saman fuskarsa, tuni ya umarcesu su kwantarta saman kujera a matsayinsa na likita.... Ruwa Mamy ta kawo ta mik’awa Sameer ya shiga baiwa Mamani yana fad’in ta d’auki a hankali....
Mamani ta bud’e idanunta da k’yar ta d’aura kan ahalinta... Baba Alhaji Abbah Mamy da kuma Sameer wanda gaba d’aya sannu suke mata... Bud’e baki tai da niyyar magana, Sameer yai saurin damk’e hannunta had’ida girgiza kai alamun kar tace komai, cikin nutsuwa da kwantar da hankali ya soma fad’in “Mamani bazamuso wani abu ya sameki ba, ban jima da sake had’uwa dake ba, ina fata Allah ya ara mana kwanaki masu tsawo wanda zanyi taredake Kakata... Duk dai ni ne matsalar a nan....” Ya d’ago yana duban Abbah kana ya dubi Mamy ma... Dawo da dubansaga Baba Alhaji yai kana yace “Baba na amince da zab’inka.... Zan auri d’iyarka kuma k’anwata idan hakan zai kawo peace a wannan family d’in....” Ya maido da dubansaga Mamani murmushi kwance saman fuskarta, a hankali ya kuma damk’e hannunta cikin nasa kana yace “Zan auri jikarki Mamaninah... Muna sonki muna son ki kasance cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali....”
Hawayen Farin ciki ya sauka fuskar Mamani yayinda Baba Alhaji ya shiga Washe baki yana ayyanawa a ransa burinsa ya kusa cika... Abbah da Mamy kallon juna sukai kana suka dubi d’an nasu cikeda tausayawa... Tabbas sun sani d’an nasu sadaukar da farin cikinsa yai ga family d’insu... A hankali Mamy dake danne hawayenta tasa kai ta fice daga parlorn sim sim... Abbah duk’awa yai kad’an ya dafa kafad’an Sameer kana ya furta “Allah ya maka Albarka....”
Mamani da Baba Alhaji a tare suka amsada Ameen Baba Alhaji naci gaba da fad’in ai sai a soma shirye shiryen biki a tsai da rana.....

Daga yanda suke lab’e jikin window wani irin dad’i ne ya dabaibaye zukatansu... Haule tamkar tayi jifa da sandar hannunta ta buga tsalle haka taji, shikenan yanzu basuda wata matsala, Ma’aruf ya amince zai auri Sahariyya wacce a wajensu daidai take da ajalinsa... Ko wannan shu’umar matar bata basu had’in kai ba ga d’iyarsu zatai masu komai...

Lami ta janyota suka koma gefe... Shewa suka saka had’ida tafe hannaye.... Haule ta gyara sandarta tace “Ke ni dama wannan shegiyar matar tasa da ganin yanda take kallon mutane nasan bazamu samu wani qofa ta wajenta ba... Yanzu komai zai zo mana cikin sauk’i....”
Lami ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Anya kuwa Haule... Toh mai zai faru idan d’iyarki ta juya mana baya... Kuma nayi imani babu macen da zata sami wannan had’edd’en saurayi ta salwantar da rayuwarshi... Anya kinaga Sahariyya bazata fara son Sameer ba...?”

Tsuka Hajiya taja kana tace “Uwar soyayya ce, yo sai mai, ai ita kanta bazata san tuggun da muk’e had’awa ba, ke nida mijina mun riga mun gama tsara komai, kinga idan Sahariyya ta auri Ma’aruf zamu sami k’ofa mai sauk’ine wajen tsunduma cikin rayuwarsa, idan bamu cimma burin hallak’asa ta wannan ba, ma’ana idan ya haye tuggunmu ko asirinmu yazo ya tonu daga baya kinga abin zaizo mana da sauk’i tinda mun zama sirakansa....”
Lami ta d’anyi shiru tamkar mai nazari kana tace “Toh ni kuma fah... Da wane ido Alhaji Usman zai kalleni....?”
Haule ta murmusa kana tace “Toh Banda abinko ai naki tonan sililin mai sauk’i ne akan Aminiyar sirri... Idan har za’a yafewa Aminiyar Sirri kinga kenan ya zama dole a yafe miki tinda duk kusanci da Ma’aruf tafimu..... Kinga idan wannan aure ma ya tabbata zamu had’asu fad’ane yasu yasu mu had’e mata baki mu d’aura duka laifi akanta... Kinga shikenan mun had’asu fad’a mun fita da fitarmu...”
Lami ta shiga juya maganganun Haule tana jinjina basira irinta Haule kana tace “Kai amma kin birgeni Haule, Wato idan baka iya kama b’arawo ba shi b’arawo sai ya kama ka... Wannan shawari tayi daidai Hajiya Haule....”
Haule ta dara kana tace “Babu wani shegen bokan da zai sake ci mana kud’i tinda duk Malamin da muka kai masa koke ce mana yake abu a duhu, da makirci kawai zamu kauda Ma’aruf a karo na biyu mu kuma b’adda Aminiyar Sirri tinda amfaninta ya k’are mana....”
Shewa suka kuma sawa had’ida tafe hannaye, duniya tai masu dad’i...


SameenaAleeyou📚





*INDA RAI*
_................DA RAO_



*76*





Marliya da Nabilah ya tadda a parlor sunyi jigum sakamakon hawaye da suka gani fuskar Mahaifiyarsu dawowarta daga parlorn Abbah, duk a tunaninsu hakan ya faru ne dalilin zuwan Siyama matar Ya Ma’aruf....
Sameer ya dubesu yanda sukai jigum jigum kana yace “Ina Mamy...?”

Sai sannan sukaji shigowar tashi, suka had’a baki wajen cewa “Sannu da shigowa Yaya..” Kana Nabilah ta amsa tambayar tasa da cewa “Mamy tana d’aki tun d’azu tak’i sanar damu meke damunta....”
Marliya ta k’arada “Kuma tace mu fita mu bata waje she wants to be alone...”

Shiru yai tamkar mai nazari kana ya jinjina kai yace “I’ll check on her...” Bai jira cewarsu ba ya nufi corridor da zai sadaka da d’akin.... Saida yai knocking da sallama saman bakinsa kana ya nemi izinin shiga...
Saita kanta ta d’anyi had’ida goge hawayen fuskarta kana ta masa izinin shiga....
Tai k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarta tana nuna masa wajen zama...
Idanunsa akanta ya k’araso ya zauna kana ya sadda kansa k’asa... Zuciyarsa sai faman tafarfasa take sanda ya tuna kalan rashin mutunci da Mamani tace Siyama tayi a gidan, kansa na kife k’asa jijiyoyin goshinsa sunyi rud’u rud’u, shi kad’ai sai dunk’ule hannunsa yake yana murzasu, kaji tsoron mutumin da bai faye saurin fushi ba, idan yayi fushin nasa babu kyau....
Mamy ce ta katse shirun nasa da fad’in “Baban Abbah an shigo...”

Sameer ya d’ago jajayen idanunsa wanda siririyar hawaye ke sauk’a ya sauk’esu kan mahaifiyarsa.... Ganin hawaye idanun d’an nata sai ya kuma d’aga hankalin Mamy, tai saurin tasowa daga wajen zamanta ta dawo yanda yake, hannayensa ya kamo ta rik’e kana tace “Na sani ka yanke hukunci mai tsauri ma kanka,... Ma’aruf idan baka son wannan aure da suke shirin maka dan Allah ka barni na tsaya maka d’ana for the first time, bana buk’atan komai face Farin cikinka.... Kaji d’ahna....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya....
Rungume Mamy yayi lokaci guda kuka mai k’arfi ya kufce masa... Wanda har saida yasa jikin Mamy yin sanyi.... Cikin muryar kuka yake “I’m sorry Mamy... Dan Allah ku yafe min.... Ban tab’a danasanin auren Siyama irinta yau ba... Amma Mamy na muku alk’awari Siyama bazata sake tozartaku ba, ku yafe min....!!!” Ya k’arashe cikin shesshek’ar Kuka....
Jikin Mamy a sanyaye ta d’ago fuskarsa tana fad’in “No Ma’aruf, matarka bata tozartamu ba, kasan Kakarka akwai tsufa a tattareda ita shiyasa, rashin fahimtace kawai, kuma wannan shine zuwarta na fari... Amma idan mukace ta tozartamu mun mata k’age... Tasa hannu tana share hawayen da suka wanke masa fuska wanda ya koma jazir kana tace “Don’t take any drastic measure kaji koh, ka zauna kayi magana da matarka na tabbata zakuyi sorting komai, ai bata san damu ba, itama abun yazo mata ba zata ne... So ka bata dama da lokaci ta san family d’inka kaji d’ahna....”

K’uri kawai yaiwa Mamy cikeda jinjina dattako da hak’uri irin nata... A hankali ya furta “Mamy are you covering up for her...?”
Girgiza masa kai tai murmushi kwance saman fuskarta kana tace “A’a D’anah, haka abin yake, Siyama bata mana komai ba, ka tashe kaje gida ka sameta , dan d’azu da na shigo ina nemanta Nabilah tace min ka shigo ka janyota waje bata kuma dawowa ba....”
D’an kauda fuskarsa yai yana duban wani gefen kana yace “Ki kwanta ki huta Mamy, and karki sa damuwa a ranki, ni nace zan auri d’iyar Baba Alhaji idan har hakan zai kawo tsakanin iyayena....”
Mamy ta dubeshi cikeda tausayawa kana tace “Ka tabbata Ma’aruf...?”
Jinjina mata kai yai a hankali kana yace “Na tabbata Mamy... Ki daina sa damuwa ma ranki, hakan bazai kyau ma lafiyarki ba...”
Murmusawa ta kumayi kana tace “Ubangiji ya shiga lamuranka ya kuma maka Albarka...”
A hankali ya amsada Ameen Mamy na... Dan ta kawar masa da zancen na ta kawo zancen iyayen goyonsa su Mummy, Sameer ya kirawosu a waya ya had’asu suka gaisa dukda cewa sun tab’a gaisawa amma yanzu an riga an zama d’aya... Mamy ta tambayi jikin Daddy yanda Mummy ta tabbatar mata na samun sauk’i sosai cikin yardar Allah, da zaran an sallamesu a asibitin ma zasuyi umrah su godewa Ubangiji kafin su dawo Nigeria.... Sosai Sameer da Mamy sukaji dad’in samun lafiya da Daddy keyi... Mummy ta tambayi ‘yan uwansa nan Sameer ya kirawo Nabilah da Marliya suka gaisa da Mummy, mata mai dattako da son mutane injisu da fad’i.. Sameer d’an gata mai iyaye biyu... Daga wajen Mamy kai tsaye gida ya wuce lokacin dare ya d’anja, a parlor ya tadda Siyama sai faman cika take tana batsewa tana hura hanci.... Ko takanta baibi yasa kai zai shige....
Saurin tare gabansa tai bata daina cika tana hura hanci ba lokaci guda take furta “Partner yanzu bayan dik abinda kamin kana nufin bazaka bani hak’uri ba, kuma na zaci daka sami family d’inka a ni zaka soma sanarma... I was so wrong...” Aya ta dasama kalaman nata sakamakon hango yanayin da taga fuskar mijin nata ke ciki....
Wani irin duba mai cikeda gsrgad’i yake aika mata, ga idanunsa da suka koma ja.... Hannunsa dake b’ari ya d’ago yana tsananin huci yake nunata da yatsa guda “If you’re still my wife today is because of Mamy... Bazan sakeki ba Siyama sabida umarnin Mamy amma first thing tomorrow morning ki koma yanda kika fito, ki koyo tarbiya da sanin darajan iyaye, duk randa kika koyi wad’annan nida zamu ci gaba da zama matsayin ma’arauta...!!!” Daga haka bai tsaya saurarenta ba yasa kai ya nufi d’aki kaman zai kifa....

Siyama tabisa da kallo cikeda mamaki.... Innalillahi tayi zaton soyayyarsu tayi k’arfin da zata raba Sameer da iyayensa.... A hankali ta silale ta zauna wajen saman sofa k’irjinta na tsananin bugu... No no this can’t be happening, bazai yuwu ba, she can’t lose Sameer.... Wasu irin hawayene taji suna neman ciko idanunta, Laila k’awartace kawai ta fad’o ranta....

Washe gari ko takan Siyama baibi ba ya fice daga gidan, a b’angaren Siyama wannan karon batabi shawarin Laila ba dan batayi shirin rabuwa da Partner ba jin Lailar na bata shawarin ta rabu dashi for good kawai kowa ya huta tinda gashi she cant stand his family kuma Ammi ma batai na’am da sabon familyn Sameer d’in ba... Khalid ne ya fad’owa Siyama, tasan shine kawai zai iya baiwa Sameer hak’uri su sasanta, da dabara sai ta rabasa da wad’annan mutanen.... Hakan yasa sassafe itama tai shiri ta d’auki hanyar Kaduna.....

***

KADUNA

Khalid ya dubi Daddy da mamaki kana yace “Daddy business trip kuma, ka mance I’m not longer working for the company...”
Dafasa kad’an Daddy yai kana yace “Zamuyi tafiya ne not because you’re not longer working with the company but because you’re my son...”

A hankali Khalid ya jinjina kai yana mai ganin kuskurensa a matsayinsa na d’ah mai biyayya...
“Kayi hak’uri Daddy ba nufi na ba kenan to make you feel this way... I’m sorry, kanada duk wata dama da zaka umarceni nai koma menene matuk’ar bai kauce hanya ba....”
Daddy ya jinjina kai cikeda jin dad’i kana yace “Naji dad’i daka fahimci haka Son, Allah shi maka Albarka....”
Khalid ya amsada Ameen Daddy....

“Kwana biyu zamuyi, so get your things ready before 12:pm zamu wuce in sha Allah....”
Jinjina kai Khalid yai kana yace “Alright Daddy right away...”
Murmushi Daddy yai kana ya fice ya nufi sashen Ammi....
Suna zaune itada Laila k’awar Siyama Lailar na mayar mata yanda sukai jiya da Siyama a waya, sai dad’i Ammi takeji cikin sauk’i Siyama zata rabu da Sameer tinda gashi bayan family d’insa yabi... Sunaci gaba da k’ulla yanda zasu kuma karkato hankalin Siyama sallaman Daddy ya daki dodon kunnuwarsu....
Laila ta risina ta gaida Daddy kana ta fice cikin sauri tana fad’in “Ammi zan wuce anjima yanda mukayi zan kiraki na sanar dake...”

Ammi tace “Yauwa Laila, yanda kukayi d’in duk saiki sanar dani tinda ni bazata d’aga wayata ba...”
Laila ya jinjina kai tace “In sha Allah Ammi...”
Ammi tace ta gaida gida kafin ta maidoda dubantaga mijinta sai faman hura hanci take...
Daga yanda yake tsaye ya d’anyi gyaran murya yace “Ina kwana Farida.... Tinda ni ban kai ki gaidani ba....”
Stegege Ammi ta dubesa kana tace “Idan yau na wayi gari gidan nan ban gaida kai ba sabida ina k’ok’arin kashe wutacen da yaranka suka kunno mana ne tinda kai bazaka nema masu mafita ba....” Ta k’arashe tana huci...

Tab’e baki yai kad’an kana yace “Duk yanda kika d’auka, zuwa nayi na sanar dake zamuyi tafiya nida Khalid, kuma tafiyar ba kan komai bace face kan maganar aurensa....”

Haba nan fah Ammi ta mik’e sosai ta shiga washe baki tana duban Daddy... “Da gaske kake Daddyn Siyaam...?”
Murmushi yai a hankali kana yace “Yanda kikaji haka ne, zanje maganar auren Khalid once and for all....”

Tasowa tai tsaye ta rungume mijin nata tana fad’in “Kai amma naji dad’i Daddyn Siyaam, at last labari mai dad’i ya riskeni.... Tareda Khalid d’in zaku tafi...?”
Jinjina mata kai yai kana yace “Yes tare zamu tafi da Khalid and zamuyi like 2days in sha Allah....”
Ammi ta kuma Washe baki tace “Hukuncinka yayi daidai, Kaga yanzu mahaifin Yesmin zai tabbatar da gaske muke kuma mu ba mutanen banza bane....”
Khalid dake tsaye bakin k’ofa mamaki ne ya cikasa jin Daddy ya canza zance wajen Ammi, abinda ya sanar dashi yasha bambam da wanda yake sanarda Ammi... What’s going on here, maiyasa Daddy zai masa haka...? Wata zuciyar tace he’s still your father, he has his own reason na aikata abinda ya aikata, maybe sabida yasan baka son auren da suke niyyan maka ne.. Maybe sabida sun umarceka ka kai Yesmin gida kak’i shiyasa ya fito maka ta wannan hanyar... Koda ya shigo sallama wa Ammi take kuma ja masa kunne gameda Yesmin d’in bai nuna mata sunyi wata magana ta daban da Daddy ba, hasalima ya bita akan tafiyar neman aurensa zasuyi kaman yanda yabar Mahaifin nasa kan tafiyar Kasuwanci zasuyi bai nunawa d’aya daga cikin iyayen nasa akwai wani b’oyayyen lamari gameda tafiyar tasu ba...
A haka suka d’auki hanyar Abuja, Khalid da kansa ke driving Daddy bai d’auki koda driver ba a cewarsa tafiyar tasu ne su biyu...
Koda Siyama ta iso gida ta iske Khalid baya nan bataso hakan ba, Ammi ta sanar da ita Abuja suka tafi kan maganar auren Khalid d’in, matsalolinsu suna kan warwaruwa a hankali dikda Siyamar tace mata batai shirin rabuwa da Sameer ba hasalima ita yanzu bata auren Yesmin da Khalid take ba, neman hanyar gyara nata auren take don ta haka ne kawai zata samu Partner ya dawo gareta ya rabu da wad’ancan mayun....

***


Yamma lis suka isa garin Abuja, kai tsaye wani gida mai d’ankaren kyau dake Jabi suka nufa, a iya sanin Khalid Daddy baida gida a Jabi, yasan gidajen Daddy guda biyu na Abuja babu wannan a ciki, kuma ba gidansu Yesmin bane, toh gidan waye nan..? Baikaga samo amsar tambayarsa ba wani security man mai sanye da blue uniform ya k’araso ya bud’e masu yana mai risinawa had’ida gaida Daddy... Shi dai Khalid shigewa gidan kawai yai bayan maigadin ya bud’e masa k’ofa, wani b’angare cikin parking lot d’in Daddy ya nuna masa yace yai parking a nan.... Babu musu Khalid yai kaman yanda Daddyn yace sai k’arema gidan kallo yake yanajin kaman wani abu na shirin faruwa a wannan gida.... Muryar Daddy ne ya katse masa tunanin nasa “Muje Khalid...”
Babu musu Khalid yasa k’afa ya fito daga cikin motar yayinda security d’in ya k’araso yana fito da luggages d’insu daga bayan booth...
D’aga kai Khalid yai yana duban gidan wanda yake bai faye girma ba d’an cute haka dashi, idanunsa suka sauk’a kan kayan wasan yara dangisu motoci da kekuna daga chan gefe... A hankali ya saki murmushi don Allah yayisa mai son yara gashi kuma shi shine k’aramin a gidansu, yanada burin idan Allah ya k’addari yayi aure ya cika masa gidansa da yara shi kuma zai cika gidan da kayan more rayuwa wa yaran... Hannayensa na sakale cikin aljihun jeans d’insa ya kuma sauraro muryar Daddy yana fad’in “Bisimillah shigo Khalid...”

Gaban Khalid yaci gaba da fad’uwa sand’a ya sa k’afarsa a bakin k’ofar da zai sadaka da main parlor na gidan.... Gabansa bai gama fad’uwa ba saida ya hango dank’areren hoton mahaifinsa manne cikin parlorn gefe dashi wata matace wacce bazata wuce shekaru 39 a duniya ba, wacce sam ratan dake tsakanin shekarunta da Siyama bazai wuce shida zuwa bakwai ba shi kansa bata basa yakai shekara goma ba... Da k’yar yake iya d’aga k’afafunsa yana kutsa kai cikin parlorn.... Wani sabon tashin hankali daga d’aya angle na parlorn ya hango wani hoton da ya kuma d’aga masa hankali... Daddynsa da wancan matar a tsakiyan hoton, yara ‘yanmata guda biyu sun sakasu a tsakiya d’aya bazata wuce shekaru goma ba k’aramar bazata wuce shekaru bakwai ba, fuskokinsu sun cika da annuri.... K’afafun Khalid suka kasa d’aukansa, ji yayi kansa na juya masa cikin sauri ya maidoda dubansa ga Mahaifinsa dake tsaye yana kallonsa...
Cikin rud’ani Khalid ke fad’in “Daddy what is this.... What is all this.... Meke faruwa Daddy.....?”

A hankali Daddy ya dafasa kana yace “Sit down first and try to calm down....”
Girgiza kai Khalid yake cikin rashin yarda da abinda yake gani kana yace “No Daddy... Are you really asking me to calm down after what I’m seeing... Daddy who are these people... Who’s this woman... Tell me Daddy do you really have another family...?” Yayi maganar yana mai k’arasowa gaban mahaifin nasa cikin rashin yarda da abindake faruwa.....
Kasa furta komai Daddy yai sai duban Khalid d’in da yakeyi....
Lokaci guda Khalid ya shiga girgiza kai kana ya soma furta “So is that why you told Ammi neman aurena zakaje...? So bayan Aunt Helen da take America, you have another wife here... Tell me Daddy, be honest with me for once in your life... How many wives do you really have.... Bayan Ammi, Aunt Helen and now ga wata kuma.... Mata nawane kaci amanar mahaifiyata dasu...?!!” Baikai aya ba yaji sauk’an mari da saida ta kaisa k’asa a kumatunsa.....
Khalid ya d’ago dafe da k’uncinsa yana duban mahaifinsa dake tsaye yana sakin huci cikin tsananin b’acin rai.....
Nuna Khalid yake da yatsa cikin tsananin fushi da fad’a yake fad’in “Ban tab’a cin amanar mahaifiyarka ba, kuma idan na auri mace samada guda Ubangijina ya halatta min na auri daga d’aya har zuwa hud’u... If I keep it from your Mum is because I know exactly the type of woman she really is....” D’an sassauta muryarsa yai kana yaci gaba da fad’in “Khalid for the past few weeks na kula kaid’in ba kamar mahaifiyarka da ‘yar uwarka kake ba, zuciyarka tafi nasu taushi da kyau, Khalid wannan shine dalilina na fayyace maka gaskiya sabida akwai rayuwa akwai mutuwa, yau idan bana raye kasan kunada wasu ‘yanuwa...” Ya k’arashe maganar idanunsa na kallon makeken hoton nasu....
Daddy yaci gaba da fad’in “And about Helen banida mata a k’asar Amurka nayi haka ne sabida kar mahaifiyarka ta zargi inada mata cikin k’asar nan, na sani muddin ta sani zatayi komai don ta rabamu shiyasa na karkata hankalinta zuwa nisan duniya can America....
lokaci guda Khalid ya d’ago idanunsa mai zuban hawaye yana duban mahaifin nasa lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “But still that doesn’t justify your actions Daddy, we have the right to know our siblings, Siyama ta cancanci tasan tanada wasu k’annen... Why Daddy...?” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa...
Dafasa kad’an Daddy yai kana yace “I wish I can do that son....”

Juyawan da Khalid zaiyi yayi ido hud’u da matar jikin hoton nan, tana takowa tamkar mai tsoron yanda take aje k’afafunta.... Cikin sand’a ta k’araso kusan mijinta, cikeda yanayi na tsoro take duban Khalid d’in kana tace da Daddy cikin sigan rad’a “Why did you bring him here....?”

A hankali shima ya furta “Na cika miki burinki ne zan bari Humaira da Ijlal susan ‘yanuwansu....”
Ta saki murmushi a hankali dukda cewa har lokacin d’ari d’ari take da Khalid d’in
“Sannu da zuwa... Please K’araso ka zauna....” Ta furta a hankali kaman mai tsoron magana fuskarta d’aukeda kyakkyawan murmushi, tana maganar tana k’arasawa cikin parlorn had’ida nuna masa kujera...

Kaman mai tunanin wani abu, fuskar matar a zahiri ya masa kaman ya tab’a saninta wani waje... Samun kansa yai da k’arasawa ya zauna a nan yanda ta umarcesan... Ganin bai gwaleta ba ya sanyata samun k’warin gwiwa, ta dubi Daddy fuska fal fari’a kana tace “I’ll set the table...” Ta k’arashe tana nunida dining area... Jinjina mata kai Daddy yai kana ta wuce kitchen cikeda jin dad’i...
Har lokacin shock d’in bai rabu da Khalid ba.....
Tana cikin had’a plates taji wayarta na k’ara ta k’arasa da sauri ta d’aga still bata daina shirya plates d’in saman dining table ba...
“Da gaske Ya Ma’aruf...? Gaskiya naji dad’i su Humaira zasuji dad’in ganinsu Irfaan sosai, na zaci siyasa ya b’oyeku gaba d’aya...?” Shiru ne ya biyo baya alamun ana magana daga d’aya b’angaren.... A hankali kuma ta nufi balcony tana mai ci gaba da amsa kiran.... Sauk’e ajiyan zuciya ta d’anyi kana tace “Toh Yaya ka sanar da Muhibbar ce....?”
Daga d’aya b’angaren sauk’e ajiyan zuciya ya d’anyi kana yace “Not yet, shiyasa idan yaran sunzo wajenki sai mu samu dama muyi magana....”
Jinjina kai tai a hankali kana tace “Haka ne Yaya, yafi idan ka sanar da ita don aure a sirrancen baida wani amfani tinda gashi nan ni yanda nake fama da nawa auren har yau ya kasa had’amu yayi introducing d’inmu... Ko dashike yau ya kawo min d’ansa kuma ga dukkan alamu bazan samu matsala dashi ba....”
Gyara zama sosai Engr yai kana yace “Daula are you sure you’re happy...? You know you’re my only sister kuma hakkina ne na kula dake koda kina gidan aurenki don nayi rantsuwa ma iyayenmu zan kula dake bayan ransu....”
Hawayene suka ciko idanunta, tasa bayan hannunta ta goge kana ta saki murmushi tace “I’m happy Yaya, I’m very happy musamman yanzu da mijina yake shirin gudanar da al’amra yanda suka kamata....”
Murmushi ya d’anyi kana yace “Gobe in sha Allah yaran suna hanya....”
Daula ta amsa masa da fatan Allah kawosu lafiya kana sukai sallama....

Parlor ta dawo yanda ta tadda Khalid tsaye jikin hotunan yana shafa fuskokin yaran da akace sisters d’insa ne, Daula tai tsaye tana dubansa, lokaci guda taga ya saki murmushi yana mai furta “Who’s Humaira among you and who’s Ijlaal......?”


*Toh fah! Masu iya magana sukace sannu sannu bata hana zuwa... Mai karatu da sannu da sannu tafiya tana kan yin nisa, b’oyeyyun al’amra suna dad’a bayyana, idan mukaci gaba da tafiya a sannun nan zamu kuma gano wasu abubuwan da izin Allah ciki harda tambayar da ya jima yana maku Yawo WACECE AMINIYAR SIRRI...? Da sannu zamuji ko wacece ita da kuma gudunawar da ta bada wajen salwantar da Ma’aruf had’ida sanin dalilinta na aikata hakan... Na gode da yanda kuke hak’uri Kuke bibiyata dukda rashin samun post akai akai....Alkhairan Allah ya kaimaku duk yanda kuke..!*


SameenaAlleeyou📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_




*77*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Bayan ya gama shirinsa a nan yanda aka sauk’esa guest room kasa fitowa yai parlorn domin cin abincin, tsaye yai a window yana mai nazarin rayuwa, sallaman Mahaifinsa ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi....
“Khalid, kai muke jira, fito muci abinci...”
Cikin taku a hankali ya k’araso had’ida zama saman gado...”Daddy you go ahead and eat ni inaga ba yanzu ba....”
Bai amsa shi ba saima zama da yai gefensa, shiru ya ratsa tsakani kaman babu mai cewa komai...
Gyaran murya mahaifin nasa yai kafin ya soma fad’in “Akwai abinda kake buk’atan sake sani ne...?”
Fuzar da iska ya d’anyi had’ida kauda kai gefe yana mai murza tafukan hannayensa tamkar mai murza mai kana yace “No Daddy, I’m in no position to question any of your decisions.... Kuma kan abinda ya faru d’azu a parlor kai hak’uri....”
Dafasa kad’an Daddy yai zuciyarsa na masa sanyi, tin tasowar Khalid yake ganin Khalid

Please Login or Register in order to submit comment