Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kumayi kana yace “Ba’a kawo breakfast bane...?”
Idanunta naga kayan kallonta tace dashi “Sun kawo amma nace su maida...”
Hafiz ya bita da kallon mamaki kana yace “Ban gane kince a maida ba, toh mai zanci... kokuwa kin dafa ne...”
Galala take dubansa kana ta murmusa a hankali had’ida kuma tauna chewing gum d’inta tace “Aidai kai shaidane ko kantin abincin Mamata kaje kayan dad’i ake cika maka tumbi dashi don haka babu abinda zaisa a nannagomin k’osai da uwar safiya safiyarma na amarcina naci nayita tusa, bazai saku ba...” Ta k’arashe tana watsa masa mugun kallo had’ida maida idanunta ga kallon da take....
Jinjina kai yayi yana dubanta kana ya furta “Yayi kyau...”
Jiki babu k’wari ya mik’e ya shige d’aki ya d’auko makullin abin hannunsa yasa kai zai fice..
Tsaye Sawwama tai a gabansa tanai masa kallon tambaya “Ina zakaje...”
Ya bata wani mugun kallo kana yace “Ki matsa min a hanya...”
Murmushi ta sakar masa kafin ta marairaice fuska tanai masa salo take fad’in “Haba Habibi duka duka fah jiya aka kawoni yau kuma zaka fita so kake ‘yan bak’in ciki su mana dariya...?” Ta k’arashe tana wasa da ‘yan yaysunta saman fuskarsa..
Samun kansa yayi da kasa mata musu saima d’an dubanta da yayi ta kuma kashe masa idanu...
Wannan karon saida ya d’an fuzar da iska kafin yace “Sawwama yunwa nakeji...”
Hannu ta d’ora saman k’irjinsa tanayi kaman tana d’an gyara masa kwalar rigar kana tace “Kar ka damu idan dai abinci ne yanzu za’a kawo maiji da lafiya kaji koh, haba karfa ka mance kantin abinci garemu...”
Ya d’anyi k’arfin halin sakin murmushi kana yace “Toh Amarya a barni naje na gaida Hajiya...”
Wasu salon take kuma masa had’ida langab’e kai tace “Hajiya ta ganka a wannan lokaci ai zatace ba lafiya muke zaune ba, kaga yau gaba d’aya bai kamata ka fice ba a gida ya kamata ka zauna muci soyayyarmu... Muje na wankeka...” Ta k’arashe tana k’ok’arin b’alle masa boturan riga..
Hafiz ya zaro idanu waje ga k’irjinsa da yayi mugun bugawa yanajin yanda har yanzu tin daga gadon bayansa yayi kwankwasonsa zuwa cinyoyinsa gaba d’aya ciwo suke masa a firgice yace “Ki wanki wa...? A’a Sawwama wanka kuma ai saidai na gobe...”
Sawwama ta d’an murmusa kana tace “Nafa sani bakai wankan sabulu ba Habibi muje na cud’eka ta shiga turasa cikin d’akin yana turjewa...
“Sanyi nakeji nida tab’a ruwa bacin alwala sai gobe ke alwalan ma rik’eta zanyi ya k’arashe yana k’watan kwalan rigarsa daga hannunta...
Sawwama bata daina abinda tayi niyya ba take fad’in “A’a a yau a k’alla kayi wanka sau biyar... Kaga muje dan Allah....”
Ya kuma zaro idanu waje ganin abinta da gaske take musamman data dannashi cikin d’aki...
Banda innalillahi da salati baya iya komai, dafe kansa yayi gumi na keto masa, zata hauro saman gadon ya shiga matsawa baya yana fad’in “Kiyiwa Allah ki bani abinci first Sawwama tun jiya da rana babu abinda naci wllhi banida k’arfi....”
Sallaman da sukajiyo daga bakin baranda ya ceci Hafiz, jin abokansa ne ya sanya Sawwama jan tsuka ba tareda ta amsa ba, masu sallama suka soma fad’in kodai babu kowa gidan ne.. D’aya yace kokuma basu tashi ba dai, k’ila mun masu sammako...

A d’ari Hafiz ya mik’e dukda ciwo da jikinsa ke masa yana lek’e ta window yake fad’in “Wa’alaikumussalam... Magaji ku dawo karku tafi... Mun tashi...”
Yana fad’i Sawwama na k’ok’arin janyosa amma tuni ya mak’ale jikin window tamkar wani d’an biri yana fad’iwa abokan su dawo, yanda kasan mai kiran azo a ceci rayuwarsa..

Suna dawowa da baya Hafiz yaji wata relief cikin sauri ya shiga kintsa kansa yana fad’in “Bani waje bani waje inada bak’i....” Sauri sauri yake komai
Sawwama ta bisa da kallo sanda ya fice kana tai k’wafa tace “Bakai kace ka iya kai mace hotel ba har nice zaka rainama hankali ka nemi k’awata, kad’an ka soma gani wllhi wllhi sai na cire maka kwad’ayin duk wata mace... Sawwama nake...” Ta k’arashe tanayin k’wafa a hankali kafin ta fito parlor ta tadda abokan mijin nata sai gwad’ata suke amarya baki laifi
A gefe guda kuwa sam basu gane kan abokin nasu ba kaman ba ango ba, suna ango kasha mai saidai ya kauda kai gefe yana sauk’e haki a hankali..

***

Tinda wannan mutumi ya fice daga gidan Hajiya Najah da Sahariyya ke ci gaba da santinsa suna addu’an Allah dawo dashi,
Najah ta dubi Sahariyya kana tace “Addah wannan guy d’in dai kinsan dani ya dace..”
Banzan kallo Sahariyya ta mata kana tace “Ke Najah ko a gidan giya akwai babba don haka wannan mutumin nawa ne...”
Najah ta tab’e baki tace “Sai mu jira dai muga wace zai zab’a...” Ta k’arashe tana juya idanu had’ida watsa mugun kallo wa Addar tata..
Sahariyya tai k’wafa tana fad’in “Eh lallai yarinyar nan wuyarki ta rik’a da har zanke fad’i kina fad’i...”
Najah ta shiga taku tana juya jiki take fad’in “A duba ko ajiki ansan wacce za’a zab’a ballanta sabbin jini irinmu ake yayi wllhi...”
Sahariyya takai mata jifa da takalmi Najah ta kauce tanaci gaba da taku had’idayuwa Addar tata gwalo...
Duk tattaunawar da suke Raihanah na d’aki na kwance tana saurarensu tana hawaye, gaba d’aya jikinta ciwo yake mata sabida bugun da taci, cikin zuciyarta take addu’ar Allah kawo mata d’auki ya shiryar da Hajiya da ‘yan uwanta idan kuma ba masu shirirya bane Allah ya fitar da ita daga wannan wahala da take ciki...
A b’angaren Hajiya kaw tana can d’aki tana faman safa da marwa tabbas yau taga abinda Lami ta gani....
Ta shiga yarfe gumin dake tsartsafo mata, meke shirin faruwa dasu, sirrin da ya jima a b’oye sama da shekaru 30 yana neman bayyana kanshi..
Ta kuma janyo wayarta hannu na rawa ta shiga neman layin Lami
Bugu biyu a na uku Lami ta d’aga...
Daga yanda Aunty Lami taji muryan Hajiya Laure tasan babu lafiya, aje wuk’ar da take yanka albasa tai kana ta mik’e tsaye tana fad’in “Laure lafiya..?”
Hajiya ta kuma yarfe gumi kana tace “Lami na ganshi wllhi na ganshi yau nayi idanu hud’u da Ma’aruf...”
Aunty Lami ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Laure ki natsu kimin bayani yanda zan fahimta...”
Cikin sark’ewar murya Hajiya take fad’in “Bayanin kenan Lami Ma’aruf na gani, wannan k’wayan idanu nashi bazan tab’a mancewa ba, shin Lami ya akai yanzu yake neman dawowa rayuwarmu, shin Aminiyar Sirri bata tabbatar mana da mutuwarsa ba, ko kuwa dai mutum na mutuwa ya dawo ne, Lami randa duk Mariya tai idanu hud’u da gudan jininta ina mai tabbatar maki cewa zata ganeshi...”
Aunty Lami tai saurin tura k’ofar kitchen kana tace “Abinda nake sanar dake kenan, dolece ta kama mu wanke k’afafunmu muje mu samu aminiyar sirri don wllhi ko Malam zai tabbata yana fad’i mana abu a duhu baiga komai ba bazan yarda saurayin da na gani ba Ma’aruf bane.....”
Haule ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Kinga maza maza ki fito mu tafi, ni da kika ganni ko wanka bazanyi ba zan fito sai mun had’u a mahad’a...”
Daga haka katse wayar tayi tana k’ok’arin shiryawa
Aunty Lami ta kashe girkin da take tana tunani, tabbas idan asirinsu ya tonu sai tafi Haule fad’awa uku sabida ta tabbata koda Mamy zata yafe mata Alhaji Usman Mailafiya bazai tab’a yafe mata ba uwa uba jarabebbiyar tsohuwar nan Mamani tabbas sai taga bayanta tsawon shekarun data jefata cikin k’unci....

Marliya data kawo mata aike daga wajen Mamy tsaye kawai tayi tana maimaita sunan da taji Aunty Lami na ambata “Ma’aruf” shi kad’aine abinda ta iya jiyowa sai kuma taji muryar tata tai k’asa... Tsaye kurum tai tana tunani tabbas idan bata mance ba wannan sunan Yayansu ne da ya b’ace shekaru masu yawa hasalima saidai a hoto suka sanshi yana k’arami d’an shekaru uku....A haka Aunty Lami ta bud’e k’ofar kitchen ta tadda Marliya tayi tsaye tamkar gunki tana aikin tunani, k’iris ya rage Aunty Lami bata dungura k’asa ba sabida tsananin tsoro da taji, ganin Marliya ce ya sanyata sakin murmushin yak’e tana fad’i cikin sark’ewar murya “A’a Marlili kin..kin jima ne a nan..?”
Murmushin Marliya ma tai mata kana ta girgiza kai tace “A’a Aunty isowata kenan... Ga wannan inji Mamy...” Ta k’arashe tana mik’a mata flask d’in hannunta
Aunty Lami tai k’ok’arin saita kanta ta amsa dukda rawa da hannunta keyi, zata bud’e Marliya tace “Kunun nono ne bata jima dayi ba...”
Nanma murmushin yak’e Aunty Lami tai kana tace “Ayya Mamy bata gajjiya tasan abinda nake so kice da ita na gode...”
Marliya ta jinjina kai kana ta fice cikin sanyin jiki...
Nabilah na kwance tana kallon shirin _Crush of the week_ Marliya ta shigo jiki a sanyaye ta zauna..
Nabilah nata mata labarin yanda ake gudanar da shirin tana kora kununta nan ta lura hankalin Marliya baya tareda ita..
Mik’ewa tai sosai ta zauna tana duban ‘yar uwar tata don da wuya kaganta cikin yanayi irin haka kana ta d’au throw pillow ta jifa mata tace “Ke meye haka, tunanin mai kike...?”
Marliya ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Addah Nabilah shin Ma’aruf bashine sunan Yaya da ya b’ace ba years back....”
Nabilah ta jinjina kai kana tace “Toh sai akayi yaya, ko kin samo wa Mamy shine..?”
Marliya ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Kinga yanzu da na kaiwa Aunty Lami kunun nan.... I overheard her talking on the phone kaman sunan take ambata kuma wayar nata kaman na sirri kaman bataso wani yaji...”
Nabilah ta gyara zamanta sosai
“Ma’aruf kawai kikaji ta ambata bakiji komai ba..” Nabilah ta tambaya
Marliya ta jinjina kai kana tace “Addah Nabilah I don’t want to believe this, ban sani ba meyasa zuciyata tak’i aminta da wayar da Aunty keyi... Is like she’s hiding something... Oho I don’t know...”
Jinjina kai Nabila tai tana hura hanci kana tace “Shiyasa na tsani matar nan tuntuni, something about her is fishy, tayita nunawa Mamy soyayya kuma bayan da ba haka take ba, who knows wayasani maybe she has something to do with our brother’s disappearance....”
Girgiza kai Marliya tai kana tace “A’a kada kice haka, Allah shine masanin gaskiyar lamarin tinda banji komai ba bayan suna da naji ta ambata ta yuwu wani Ma’aruf d’in ne.. And please kar kicewa Mamy komai kada mu d’ago mata gyambon dake zuciyarta mu maidasa sabo...”
Jinjina kai Nabilah tai kana tace “Idanma tana b’oye wani abin I’ll find out, kuma wllhi idan na fahimci cewa itace silar k’uncin Mamy sai yanda k’arfina ya k’are...” Ta k’arashe tana mai tsananin huci....

A b’angaren Sameer kuwa tinda ya isa asibitin yake jinsa wani iri, abubuwan da suke faruwa dashi a Kano sun d’aure mai kai, ji yake tamkar wasu memories ne da suka faru lokaci mai tsawo, shin kodai iyayenshi sun zauna a garin ne particularly wannan unguwar da a yanzu yake zaune cikinta, shin kafin suyi zaman Amurka k’ila nan ne garin da suka fara zama idan ba haka ba meyasa yakejin wani abu gameda environment d’in da mutanen cikinta... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya can wata b’angare na zuciyarsa na tuna masa yarinyar nan Raihan da halin da ya barta ciki...
Agogon hannunsa ya kuma dubawa ko lokacin sallah tayi sabida yanada wani surgery da rana, wani tunani ne ya fad’o masa kana ya suri makullensa ya fice...

Dai-dai k’ofar gate d’in yayi parking yana neman yaron da zai aika cikin gidan... Can saiga wani yaro yazo shigewa Sameer ya tare shi da niyyar aikanshi...
Wata leda ya ciro cikin motarsa ya mik’awa yaron yace “Kaga nan gidan...” Ya masa nunida gidan Alhaji Sani mahaifinsu Raihanah...
Yaron ya jinjina kai yace “Eh.. nasan gidan a unguwar nan nake..”
Sameer yace “Good, ka shiga ka bada wannan sak’on wa Raihan...”
Yaron ya d’an subeshi sai kuma yace “Raihan kuma nasan dai akwai Raihanah a gidan, ba ‘yar Hajiya bace shiyasa kullum Hajiya ke bugunta Mamarta ta jima da rasuwa tun tana yarinya shiyasa ta girma hannun Hajiya... Amma tafi kowa kirki a gidan..”
Tinda yaron ya soma zuba Sameer ke dubansa yana jinjina lamarin, tabbas biri yayi kama da mutum, no wonder matar nan take jibgan yarinyar tamkar ba biladama ba ashe ba d’iyarta bace, wani tausayi ya kuma taso masa.. Duban yaron yayi yace “Maigidan na raye...?”
Yaron ya jinjina kai yace “Yana nan saidai baya iyayin komai a gidanshi...”
Shiru yayi na d’an lokaci yana tunanin abubuwan da yaji daga bakin wannan yaro mai yawan magana, tabbas zaiso ya had’uda maigidan nan dukda cewa ba huruminsa bane amma zuciyarsa sosai ta aminta da ya sadu da maigidan nan..
Yaron yana shigewa Sameer ya shiga motarsa ya wuce..
Sahariyya ya tadda tsakar gidan kwance saman tabarma da pillow tana karanta littafi yayinda Raihanah ke kwance har lokacin a d’aki...
Sallama yaron yayi Sahariyya ta amsa mashi a dak’ile ta k’arada “Wajen waye kazo...?” tana maganar tana duban ledar hannunsa...
Yaron yace “Wani mutumi ne yace a bada wannan ma Raihanah...”
Jin an ambato sunanta ya sanya gabanta mugun fad’uwa tana tunanin kardai mutumin can ne ya dawo...
Sahariyya ta aje littafin hannunta had’ida mik’ewa zaune tana mai gyara d’aurin k’irjinta taceda yaron “Kawo nan..”
Yaron ya d’an doje yace “Nifah ma Raihanah akace na bada...”
Sahariyya ta mik’e sosai tana fad’in “Kai banson iskanci kada ka bari na tashi... Waye ma ya aikoka...?”
Yaron ya k’araso ya dangwala mata ledar kana yace “Wani mutumi ne mai kyau had’ida mota mai kyau...”
Ai Sahariyya batasan sanda ta mik’e tsaye ba tana fad’in “Ina yake... Gudu jeka ka taremin shi...”
Yaron ya mata wani kallo kana yace “Ai ya tafi.... Saidai kiyi hak’uri...”
Harara ta watsawa yaron kana tace “Toh uwar mai kake jira kaikuma da bazaka fice daga gidan ba.....”
Yaron na k’unk’unin shima Raihanah akace ya bada aiken ya fice, Sahariyya sai danna masa ashariya take..
Tai saurin bud’e ledar tana zazzagewa abubuwan ciki suna fitowa...
Magunguna ne da na sha da na shafawa danginsu pain reliever...
Take ta kuma yin kicin kicin da fuska kana ta shiga k’wallawa Raiha kira..
Jiki a sanyaye Raihanah ta fito ta tadda Sahariyya
Wani kallo Sahariyya ke watsa mata kana tace “Munafuka duk salon yaudarar namiji kin iyashi k’arama dake, toh kaw kinaji kina gani maganin nan hanyar ruwa zan watsasu bazaki amfana dashi ba, b’ace min da gani anammimiya...”
Hawayen da suka zubo mata ta kuma gogewa kafin ta koma d’aki cikin tafiya da yafi kama da d’ingishi...
Sahariyya ta rakata da mugun kallo...

***

Gaba d’aya sunyi zaune a mahad’a suna jiran k’arasowar aminiyar sirri, Hajiya tace “Lami anya Aminiya zatazo...?”
Lami tace “Dole ma tazo domin kuwa idan asiri ya tonu ba mu kad’aine a rana ba saima ta fimu shiga...”
Hajiya ta jinjina kai tana buga hannayenta a hankali tana waige waigen ta yanda zata hango Aminiyar sirri...
Daga can suka hango mai tasi ya ajiyeta tana k’arasowa yanda suke sai waige waige take tamkar mai tsoron kada wani ya hangota...
A tare Lami da Haule suka kalli juna kafin suka mik’e gaba d’aya sanda ta k’araso....
“Aminiyar sirri ganin ki yayi wahala...” Hajiya tace sanda take dubanta
Murmushi matar ta saki wacce batakaisu a shekare ba kana tace “Haule, Lami shekaru talatin baya babu abinda ya canza a rayuwarku......”
Lami ta nuna mata kujera kana tace “Sirrin dake b’oye shekaru talatin baya yana neman ya bayyana kanshi...”
Murmushi Aminiyar Sirri ta saki kana tace “Mai kuke tunanin zai bayyanashi idan ba d’aya daga cikinku bane ta bud’i baki ta fad’i...”
Haule tai saurin katseta “Tabbas mukeda babban dalili domin kaw Ma’aruf muke gani yana neman dawowa cikin rayuwarmu...”
Ta kuma murmusawa kana tace “Bazaku tab’a canzawa ba.... Amma..” Ta k’arashe tana bud’e zip d’in jakanta...

Kayan k’aramin yaro ta ciro d’aukeda bushesshen jini ta shiga warware masu...
Lami da Haule suka dubi juna tabbas wannan shine kayan dake jikin Ma’aruf sanda suka sabautar dashi...
Aminiyar sirri ta murmusa tace “Meyasa kuke tunanin zanbar Ma’aruf a raye bayan duk duniya babu aninda na tsana irin farin cikin mahaifiyarsa kuma nasan dani daku akan haka mukayi tarayya...”
Haule da Lami suka kuma duban juna kana sukace “Aminiya idan kikaga abinda muka gani kema zaki yarda cewa tabbas Ma’aruf na raye....”
K’uri ta masu kana tace “Laifukanku suke bibiyarku suka hanaku sukuni amma ina mai tabbatar maku ba Ma’aruf kuka gani ba, Ma’aruf ya jima da zama tarihi don haka idan bakune kuke son tonowa kanku ba kada ku bud’e sirrinku da kanku, randa duk aka fahimci akwai aminci na sirri tsakaninmu sanin kanku ne zargi zai mana yawa don haka shawarina a nan shine muci gaba da nisanta kanmu da juna domin tsira da mutuncinmu...”
Haule da Lami suka dubi juna bawai don sun gamsu da ita ba...
Har suka bar wajen hankulansu ba’a nitse yake ba, yauma kaman kullum Lami aka soma sauk’ewa kafin aka wuce da Hajiya..
Nabila da dawowarta kenan daga makaranta taga Aunty Lami ta sauk’a adaidaita guda da Hajiyar Yaya Hafiz, maganar da sukai da safe itada Marliya ya kuma dawo mata Sabo, wannan matar tabbas akwai abinda take b’oyewa ba abin kayi sharing da Mamy ba ba yarda zatai ba saidaima tace rashin kunyarka ne, amma what so ever she’s hiding saita tono shi da yardar Allah.. As they say no secret remains hidden forever...
Cikin sauri ta k’araso murmushi saman fuskarta ganin Aunty Lami d’in zata shige cikin gida..

“Aunty sannu da dawowa...” Tayi maganar fuska fal fari’a abinda bata saba yi mata ba...

Aunty Lami ta dubeta da mamaki don koda wasa Nabila bata tab’a mata hakan ba... Murmushin yak’e Aunty Lami tai kana tace “Yauwa Nabila ‘yan makaranta an dawo...”
Nabilah ta jinjina kai had’ida amsar jakan hannun Aunty Lami ta rik’e mata suka jera tare suka nufi cikin gida Nabilah na fad’in “Lecture d’aya nayi shiyasa ban fita da wuri ba na kuma dawo da wuri..”
Aunty Lami ta jinjina kai tana mamakin yanda Nabilah ta sake tana mata fira, har sashenta Nabilah tai mata rakiya rik’eda jakan Aunty Lami d’in, tai mata tayin abinci tace ta k’oshi, tai mata sallama fuska fal fari’a kana ta fice..
Aunty Lami sai mamakin canzawan Nabilah take lokaci guda....

***

Hankalin Sameer ya gaza kwanciya, sosai yake son tafiya gida sabida d’inbin tambayoyi da yakeson yima iyayenshi, washe gari ya shirya tafiya Kaduna ba tareda ya sanar da kowa ba don koh Siyama bai sanar da ita ba....
Kai tsaye gidansa ya shige don hutawa kafin ya nufi can gidan iyayenshi..
Kai tsaye ya nufi bedroom d’insu ya shiga rage kayan jikinsa donyin wanka, ya k’arasa bedside ya aje agogonsa da ya cire nan yaji k’afarsa ya taka wani abu kaman gidan magani..
Kai dubansa k’asa aiko gidan maganin ya taka...
Ya shiga duk’awa a hankali k’irjinsa na tsananin bugu abinka da likita yana fata cikin zuciyarsa Allah yasa ba maganin da yake tunani bane... Wani irin bugu k’irjin Sameer yayi sanda ya d’auki maganin ya shiga juyawa....



SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_


*28*


*©Sameena Aleeyou...✍🏽*





Jiri ne yaji na niman d’ibanshi daga yanda yake durk’ushe, take idanunsa suka kad’a sukai jazir... Cikin wani irin yanayi yake furta “How could you... How could you do this to me Siyama...” Kasa ci gaba da magana yayi sai k’ok’arin mik’ewa da yake cikin sanyin jiki...
Ya d’aga idanu yana duban picture d’insu dake ajiye gefen bedside d’in cikin k’aramar frame su duka biyun suna cikin tsananin farin ciki, take yasa hannu ya d’auko hoton had’ida k’ura mata idanun da suka koma jajazir, inama ace abinda yake gani ba gaskiya bane, Siyama itace mace guda da ya tab’a so tsawon rayuwarsa, shin da gaske ita bata sonshi to the point that bata k’aunar had’a jini dashi... Shin mai ya mata da tsanani shin menene laifinsa, shin tsananin soyayyar da yake mata ne laifinsa.... Siririyar hawaye mai tsananin zafi ya gangaro mashi...
A hankali ya maida hoton ya ajiye, wankan da bai iya yayi ba kenan yasa kai ya fito daga d’akin, tamkar wanda ruwa ya shanye haka Sameer ke d’aga k’afafunsa,da k’yar ya iya sauk’owa daga staircase yaji jiri na neman kifa shi, zama yayi cikin kujera had’ida k’urama waje guda idanu, fatar jikinsa ta koma jazir haka nan idanunsa, abubuwa da dama ke ziyartar zuciyarsa....

***

Yesmin ba’a sama ba’a k’asa yau dai so ake a birge oga Khalid da alama, gaba d’aya abincin gidan ta d’auki ragama ta hana ma’aikatan saka hannu, Kubura ta cika tayi fam duk wani juyi da Yesmin zatai a kitchen harara kurum take aika mata had’ida tab’e baki musamman idan ta tuna wai duk don a janyo hankalin Khalid d’inta ake wannan abun.. Sai ‘yan wak’e wak’enta take na habaici tana giftawa...
Yesmin kaw ko a jikinta sai rawar kai ake ana kiran Mummy tana kuma turo wasu recipes d’in, dama tun safe driver ya kaita tayo shopping d’inta da kanta abubuwan da tasan bazata samu a store ba...
Ammi ce ta shigo kitchen d’in ta tadda Yesmin kace kace sai aiki take...
Ammi na murmushi take fad’in “A’a lallai yau munada cin delicious babbar chef ce a kitchen d’in namu...”
Yesmin ta murmusa cikeda kunya kana tace “I love cooking Ammi...”
Ammi ta murmusa kana tace “Toh what’s the occasion, what are we celebrating...?”
Nan ma cikeda kunya ta kuma murmusawa kana tace “Ammi I hope Khalid will like it....”
Ammi ta d’an matso kusanta had’ida dafata kad’an kana tace “I’m sure he’s going to love it sweetheart... Mamanki ta fad’a min your passion about cooking tun kina k’arama unlike your own cousin Siyama wacce saidai a dafa a bata, I’m sure d’ana yayi dace..”
Yesmin ta kuma murmusawa cikeda jin dad’i kana tace “Thank you Ammi..” Suka rungume juna cikeda jin dad’i kafin Ammi ta fice ta bar Yesmin a kitchen tana ci gaba da hidimanta had’ida dad’a zak’ewa...

Bayan komai ya kammala Yesmin ta umarci su Kubura su jera komai bisa dining ita kuma ta wuce sama ta tsala wanka had’ida cancad’a kwalliya...
Siyama data dawo a gajjiye nan taga ma’aikatan sai kai komo suke suna jeren had’add’un dishes da warmers...
K’arasawa tayi ta shige bud’ewa ko wanne tana tab’awa tana lumshe idanu had’ida kad’a kunne don santi..
Yesmin ta fito ta taddata a haka, k’arasowa tai ta d’an tab’a Siyama kana tace “How do I look...?” Tai maganar tana juyi gaban Siyama..
Siyama ta jinjina kai tana had’iye abinda ke bakinta kana tace “Um gorgeous, you look just good... So, is my brother here...?”
Yesmin ta d’an murmusa kana tace “Not yet, but I’m sure he’s on his way...”
Siyama ta jinjina kai tace “You cook all this...?”
Yesmin ta jinjina kai tana juya idanu
Siyama ta d’an tab’e baki tana jinjina kai tace “Lallai Khalid is lucky, niko kinga babu abinda na iya when it comes to kitchen, Sameer shikeyin komai... Kinga let me go take shower sai nazo muyima abincin nan cin gaske cos I’m really really starving...”

Jinjina kai Yesmin tai kafin taci gaba da kallon kanta cikin k’aton madubi da aka k’awata dining area d’in dashi...

Kubura na lab’e tana dubanta ta cika tayi fam, jira kawai take Yesmin ta kauce ta cika aikinta...

Suna zazzaune bisa dining d’in saidai basu fara cin abincin ba fira suke kanyi Khalid yayi sallama ya shigo, kallo guda zaka masa ka fahimci a stananin gajjiye yake, kusan komai yanzu sakar masa Daddy yake a company d’in a cewarsa he wants him to grow up, ballanta yanzu da Daddy yake on a business trip komai sakarwa Khalid d’in yake...
Ammi ta sakar masa murmushi kana tace “You arrived just on time son.... k’araso”
Murmushi ya sakar mata kana ya gaidata bata saki hannunsa ba saida ta zaunar dashi saman kujera tana fad’in “Lets eat son,...”
Ammi ta shiga serving d’insa da kanta, Yesmin kaw sai faman sinne kai take musamman da taji Khalid na cewa yunwa dama yakeji amma yaso ya fara yin wanka, Ammi tace a’a shi kawai suke jira sai sunci abinci tukuna...

Khalid na kallon yanda Ammi ke serving d’insa yana murmushi yana tuna a lokutan baya idan yana fushi haka Amminsa ke masa abinci kala kala tana lallashin shi, a nashi zaton sabida maganar da sukayi jiya akan Yesmin ne takeson lallashin shi...
Siyama tace “Ammi da kin bari wacce ta dafa abincin tai serving d’inshi ai...” Ta k’arashe tana kai spoon baki... Cak Siyama ta tsayada zancen nata sakamakon sugar had’ida yaji da taji sun mata sallama saman harshe a dai dai lokacin da Khalid yakai spoon d’in abinci baki ba tareda ya kula Siyama ba Ammi na ci gaba da fad’in “Your Sister cooked specially for.....”Aya Ammi taiwa kalaman nata jin Khalid ya mik’e a zabure yana tsananin tari had’ida watsar da abincin dake bakinsa...
Yesmin ta mik’e a razane tana dubanshi..
Ammi ta mik’e tana masa sannu had’ida rik’e shi...”
Yesmin tai saurin tsiyaya drink a cup ta mik’awa Ammi jikinta har rawa yake...
Ammi ta mik’a masa bakinsa tana fad’in “Sannu son sha ruwa....”
Aiko yana kafa kai yaji barkwanon ya

Please Login or Register in order to submit comment