Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kake ban sani ba...?”

Statement d’inta na k’arshe ya sanyashi d’agowa yana d’an dubanta, sai kuma ta basa tausayi sakamakon hango k’walla tab idanunta da yayi, ya sani Muhibbah ta canza sosai akan yanda take da idan zai mata adalci ya kamata ya zamto mai yafiya a gareta tinda duk d’an Adam ajizine, daidai da yaransu yanzu takan d’an basu kula fiyeda yanda take balagazantar dasu a baya don har wani sabo ne da SHAK’UWA ya soma shiga tsakaninta da yaran wanda ko shakka babu yaji dad’in hakan.....
A hankali yasa hannu ya tallafota ya fad’o jikinsa, kaman jira take Aiko nan ta saki kuka mai tsuma zuciyar mai saurare... Ya shiga lallashinta yanda salon nasu ya soma canzawa, aiko nan ta sami damar janyo hankalin mijin nata har saida ta sami kulawa da soyayyarsa wanda ta jima bata sami irinsa ba.....

***

Mamani taci gaba da salallami tana duban Sameer
“Ikon Allah yanzu shi yaron nan Haladu ashe d’anuwan iyalinka ne...?”
Sameer ya jinjina kai yace “Su biyu ne wajen iyayensu Mamani...”
Mamani ta jinjina kai tace “Allah sarki Aiko Haladu yaron kirki ne, ni ai tuni munyi sabo dashi, lallai kaje gidan mutunci kayi aure Ubana, na tabbata matar taka ma mutuniyar arziki zata zama, yakamata yanzu kam ka kawo mana ita nan mu ganta mu saba, dama nayi magana da mahaifinka sashen gefena nan za’a gyara maka ku d’an zauna ko na k’ank’anin lokaci ne musan matar taka mu saba, Kaga ai yafi ta shigo cikin dangi a santa a saba da ita tinda Allah yayika D’an zuri’a....”
Murmushi Sameer ya sakar mata kana yace “Babu damuwa Mamani yanda duk kikace hakan za’ai....”

Mamani ta Washe baki cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa Ubana Allah dai shi maka Albarka, kai naji dad’in yin na’am da hukuncina da kayi.... Allah ya shiga lamuranka....”
Sameer ya amsada Ameen Mamaninah ... Yai maganar yana d’an waige waige ganin baiji d’uriyar Raihanah ba... Kaman wacce ta kula yana neman wani abin tace “Akwai wani abin ne Ubana...?”
D’an girgiza kai yayi kana yace “Em nace ina Raihaan take ne ban ganta ba...?”

Mamani ta yab’e baki tace “Aw Raihanatu ai kuwa d’azu Marliya da Naja’atu suka shigo suka jajib’eta Wai sun tafi islamiya, babu yanda banyi ba ta bari jikin nata ya ida warkewa amma sai cemin tayi zata iya zuwa Wai hadda ya taru mata gwara taje ta rage....”

D’an girgiza kai yai yana mai mik’ewa tsaye yake fad’in “Ciwon nata da saura bai gama warkewa ba she might catch infection out there... Ina ne islamiya nasu....?” Yanda yai maganar sosai damuwa ya nuna a fuskarsa har saida Mamani ta fahimci damuwar da fuskar nasa ya nuna....
“Nan layin baya ne, masu jajayen kaya zaka gansu....”
Jinjina kai kurum Sameer yai kana ya nufi k’ofa yana fad’in “Sai na dawo Mamani.....”

“A dawo lafiya...” Ta fad’i tana mai bin bayansa da kallo yanda ya fice cikin sauri.....


SameenaAleeyou📚



*INDA RAI*
_...............DA RABO_




*74*



Layin bayansu ya nufa kaman yanda Mamani ta sanar dashi islamiyansu Raihanah nan yake, Aiko nan ya hangi wani dogon gini yanda sautin karatu ke fitowa ko shakka nan ne makarantar sannan ga baburan malaman a pappake a waje... Lokaci guda Sameer ya nufi ginin, a gefe ya paka motarsa kana ya sauk’a ya nufi cikin makarantar, wasu malamai ya samu kusan su hud’u a k’ofar wani aji tamkar tattaunawa suke, Sameer ya k’arasa ya masu sallama, gaba d’aya suka amsa mashi suna mai basa hannu alamun masabaha....
Nan Sameer d’in ya sanar dasu abindake tafe dashi... Malam Isyaku d’aya daga cikin malaman yace “Amma kuwa Raihana yarinyace mai k’wazo idan dai har zata iya zama inaga babu laifi a barta taci gaba da zuwa makarantar sabida ko d’azu da zan shige ajinsu naji tana bada haddarta tiryan tiryan harma tafi wad’anda suke zuwa makarantar, irinsu datse masu karatun babu dad’i....”
D’an murmushi da gefen bakinsa Sameer yai kana yace “Wato Malam ba nak’i ta zauna bane, shi ciwo musamman k’una idan bai gama warkewa ba sam ba’a so ana shiga wajen da k’wayoyin cuta zasu iya shafan ciwon, ayi hak’uri a barta ta k’ara samun sauk’i sosai kafin ta dawo makarantar mai gaba d’aya...”
Su Malam Ayuba suka shiga jinjina kai suna fad’in “Wannan gaskiya ne, ai komai saida lafiya....”
Malam Isyaku da yaji hujjojin Sameer yafi nasa yana murmushi yake fad’in “Amma dai rankashidad’e kai d’in likitane... Don idan ba likita ba babu wanda zai tsaro wannan bayanai...”
Gaba d’aya d’an darawa sukai kafin Malam Ayuba ya mik’e yana fad’in bari a kirawota....
Sameer yai masa godiya yanda sauran Malaman sukaci gaba da tattaunawarsu....
Mamakine ya cika Raihanah jin cewa Yayanta ne yazo d’aukanta, hartasu Marliya da Najah suma mamakin ne ya kamasu, gaba d’aya ma sai suka rasa wane yayan nasu ne yazo d’aukan Raihanah tinda abu ne mai kaman wuya kaji wani nasu yazo makarantar a baya, ko PTA meeting ne saidai suga ana zuwama wasu amma banda su shiyasa sosai abin ya basu mamaki..

Suna tafe tana d’an jan k’afar tata da bai ida warkewa ba tana sak’e sak’e da zullumin waye yazo d’aukanta har islamiya.... Bata ida tunanin ba ta hangosa gefen malamansu kansa kife bisa wayar salulansa, yana sanye cikin k’anan kaya, navy blue check wato riga mai zanen gidan dara long sleeve, haka jeans d’in jikinsa ma blue d’in ne, da matuk’ar wuya kaga Sameer da t-shirt idan dai ba check bane, akasarin kayan nasa check ne masu dogayen hannu da masu gajerun hannu, ta yanda da yawa wasu a asibitin nasu ma suke banbancesa kenan, wasu har lak’abi suke masa da Dr-check, duk ranan juma’a kuwa shigar dogayen kaya yake harda hula, saiko wani zubin yakan saka suit musamman idan zai halarci wani taron....
Wani irin muguwar fad’uwar gaba Raihanah taji, ko mai yasa Ya Ma’aruf zaizo d’aukarta...? Sai kuma ta soma tunanin Salma nurse mai mata dressing tasha sanar da ita irin k’aida da kaffa-kaffa da Dr Sameer ke dashi dashike akasarin hiran da Salma zata mata akan Sameer d’in ne, Salma batada zance saina Dr Sameer dukda cewa shid’in baisan tanayi ba...
Kanta a k’asa ta k’araso tana gaida sauran malaman, suka amsa mata da sakin fuska had’ida mata sannu da jiki, ta d’an maidoda dubantaga Sameer wanda har lokacin idanunsa nakan waya.... A hankali ta furta “Ya Sameer ina yini....”
Ya amsa mata a tak’aice kana yace “Ki k’arasa mota ina zuwa...”
Jinjina masa kai kurum tai kana tace “Toh..” A tak’aice....
Saida ta d’anyi nisa da tafiya kafin ya ida abinda yake cikin wayar kana ya k’araso yaiwa malaman sallama...
Tana nan tsaye jikin mota taji k’aran security lock alamun an bud’e motar, Aiko shid’inne ya k’araso fuskarsa sam babu walwala, bata tab’a ganinshi cikin yanayi irinta yau ba...
K’asa k’asa take dubansa, tana jin sanda yace “Shige muje....”
Babu musu ta bud’e marfin motar ta shige a d’arare,sai faman cije leb’e take a hankali bata son ya fahimci halinda take ciki don gaba d’aya wandon islamiyan nata data saka ya sosa ciwon ya fama kad’an....
Yana kunna motar sautin karatun Alk’ur’ani mai girma yaci gaba da tashi cikin muryar Sheik Sa’oud Shureim, da alama karatun yake saurare dama, ga wani k’amshi na musamman dake tashi cikin motar tasa, haka kurum taji wani irin nutsuwa ya sauk’ar mata cikin zuciyarta, da gefen idanu take satan kallonsa har wannan lokacin babu walwala saman kyakkyawan fuskarsa... Ta janye idanunta a hankali zuciyarta nabin k’ira’ar cikin suratu Yaseen yayinda ta maida dubanta gaba d’aya zuwaga window.... K’arar ringing d’in wayar salulansa k’irar Samsung shi ya sanya Sameer rage sautin karatun Alk’ur’anin.... Ya d’aga wayar wanda daji kasan daga can asibitin nasu ake nemansa.....
Cikin muryarsa mai cikeda charisma da dad’in saurare yake fad’in “Ni kuma gashi bana kusa, ina Awwab yake... Contact him mana....”
Magana akai daga d’aya b’angaren sai jinjina kai da yai yana furta “Ok ok gani nan zuwa, prepare the patients....” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai canza hanya da yai.....
Raihanah ta dubesa da tsananin mamaki ganin ya canza hanyar gida, kaman yasan duban nasa take nan ta sinkayi muryarsa yana fad’in “Meyasa kika fita ba tareda sanina ba...?” Batakaiga basa amsa ba ya kuma jefo mata wata tambayar “Salma bata sanar dake k’a’idojina bane wanda duk patients d’ina dole subi wad’annan k’aidojin....?”
Sai sannan ya d’an cire idanunsa daga kwalta ya kaikaito kad’an yana dubanta, gani yai idanunta a k’asa tana wasa da ‘yan yatsuna hannunta, a hankali ta furta “Kai hak’uri Yaya bazan sake ba....”
Maida idanunsaga tuk’in dayeke yai ba tareda ya kuma cewa komai ba saima d’an k’ara volume d’in karatun da yai sakamakon ragewa da yayi sanda zai amsa waya...
Raihanah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida lumshe idanu, ita duk damuwarta ma hanyar asibiti taga sun nufa ne, kenan ba yanzu zasu koma gida ba... Haka nan dai idanunta na lumshe taketa bin sautin karatun cikin zuciyarta da sam batasan bakinta na furtawa ba....
Sameer yakai dubansa gareta yaga yanda bakin nata ke furta karatun a hankali idanunta masu yalwan girma a lumshe, bai tab’a samun daman k’arema fuskarta kallo ba sai yau, Raihaan kaman yanda shi yake kiranta, bata a layin mata masu haske sannan kai tsaye bazaka kirata b’ak’a ba, hancinta ba mai tsawo bane hasalima ya d’an baje kad’an daga k’asa, full lips gareta dikda cewa bakin nata madaidaici ne kana iya hango d’an tudu kad’an da bakin nata kedashi haka nan tanada yalwan idanu da dogayen gashin ido wanda ya k’ara ma idanun nata kyau sannan tanada lostawar kumatu wanda ko magana take zakaga suna lotsawa karatun da take bi yanzu ma sai faman lotsawa suke, daga nesa ma bazakai mata kallon kyakkyawa ba harsai ka matso kusanta, haka nan suke ita da Nabilah sam basu d’auko haske irin na sauran family members d’in nasu ba, ita Raihanah kam ma bata ragewa mahaifiyarta komai ba sam bata kama da dangin Baba Alhaji wannan yasa kamanninta ya fita daban da sauran ‘yan gidan..... Shiyasa ma Haule ke mata lak’abi da dangi mayu...
Tana jin alamun tsayawa ta bud’e idanunta, nan ta gansu a farfajiyan asibitin.....
Sameer ya bud’e central lock kana ya mik’a hannunsa bayan motar ya d’auki wasu files da farar labcot d’insa...
“Muje...” Kalmar da ya fad’i mata kenan....
Babu musu ta kama marfin motar ta fice tabi bayansa cikin sauri ga yanayin tafiyar tasa sassarfa ne ita gashi gaba d’aya tafiyar nata d’ingisawa ne...
Yana tafe ma’aikatan asibitin na jefo masa gaisuwa duk yanda ya shige...
Saida zai d’auki wata hanya ya tunada Raihanah... Juyowa yai yana dubanta yaga tana jan k’afarta da k’yar da k’yar.... Tsayuwa yai yana observing d’inta kana ya girgiza kansa a hankali, yasan hakan ka iya faruwa... Saida ta k’araso kusansa kanta a k’asa, duk a tsarge take ganin yanda ya k’urawa k’afarta idanu, hannu yasa ya amshi jakar islamiyar nata yana mai furta “Give me that....” Ita dai sakar mishi kawai tai tana mai tambayar kanta ko maiyasa ma ta fito da jakar oho dama barinta tai a mota...
Wani office taga ya bud’e masu wanda ga dukkan alamu mallakarsa ne....
Ya shige ciki tabi bayansa, Office ne maiji da lafiya gashi ya had’uda gayu don mai office d’in ya k’ure wajen tsafta da gayu... Tai tsaye sororo yayinda Sameer ke jikin table yana duba laptop d’in dake bisa table d’in... Saida har ya gama abinda zaiyi ya juyo ya ganta nan tsaye sai rarraba idanu take kaman taci kud’in aika....
Sofa dake gefe ya mata nuni dashi kana yace “Ki zauna acan...”
Babu musu tai yanda yace....
Tana gani ya tattari wasu takardun da labcot d’insa ya nufi k’ofa, har yakai k’ofa ya juyo ya d’an dubeta kana yace “Idan zakiyi sallah ga bathroom and akwai abin sallah a gefen wancan drawer d’in... I won’t take long kinji... Ki jirani a nan...”
Cikin sauri ta shiga mana masa kai sai faman muzurai take...
Har ya kuma juyawa zai fice ya d’anyi birki ya kuma juyowa, kai tsaye jikin k’aramar fridge dake a cikin Office d’in ya nufa ya bud’e ya ciro goran fresh yogurt ya ije gefenta, daga haka bai kuma cewa komai ba ya fice cikin sauri had’ida jan k’ofar office d’in....
A daidai k’ofa ya had’uda Awwab yana fad’in “Dama zuwa nai na fito da kai don ance min ka iso ka nufi Office....”
Suna tafe cikin sassarfa Sameer yake fad’in “Wai dama kana nan shine sai an nemoni...?”
Suna nufa wata k’ofar Awwab ke fad’in “Ai tinda kaga an dage a nemoka is serious kuma ba mutum d’aya ba kusan three patients ke jiranmu, na shiga na gansu gasu yara abun babu dad’in gani, Allah ka tsaremu daga sharrin wuta duniya da lahira..”
Ameen Sameer ya amsa dashi daidai sanda suke isowa d’akin theatre d’in....

Raihanah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ta sami daman k’are ma ofishin kallo, takai dubantaga lallausar carpet d’in da k’afafunta ke bisa tana mai ayyanawa cikin ranta _Wannan ma ai ya isheni sallah basai na d’auko abin sallah ba_ don already lokacin magrib ya kusa....
K’ofar da ya nuna mata matsayin bathroom nan cikin office d’in ta nufa, saidai hoton da ta hanga saman table d’insa cikin k’aramar frame ya mugun jan hankalinta, ta k’arasa jikin table d’in tana mai k’arema hoton kallo, murmushi saman fuskarta ta d’auki hoton tana duba, ko ba’ace ba wannan ce matarsa, sunyi kyau har sun gaji sannan sun bala’in dacewa da juna, duk yanda gayu yakai wannan mata tasa takai sannan ko ba’ace ba kasan suna matuk’ar k’aunar junansu.... Sun mata kyau har sun gaji... Ta jima tana duban hoton kafin ta maida ta aje saman table d’in.... Can gefe kuma jikin gini an k’awata wajen ne da tarin Awards and Medals na shaidan d’inbin nasarori da ya samu, nan ta k’arasa tana bi tana karantawa d’aya bayan d’aya, duk wanda ta karanta sai ta saki murmushi hardai ta jiyo ana kiran sallah daga masallacin cikin asibitin, nan ta nufi bathroom d’in tayo alwala kaman yanda ya nuna mata....
Har ta ida sallan magrib babu Sameer babu dalilinsa....
Haka nan tai zaune ta rabka uban tagumi tana zaman jiran tsammani....

***
K’arfe bakwai da rabi na dare ta shigo garin Kano, Allah ne kawai ya kiyaye mata hanya amma kam ita kanta tasan tayi rough driving yau d’in, wai donma tayi gamo da checkpoints da dama yau d’in a hanya amma da tuni ta tsufa garin Kano....
Kai tsaye unguwar nasu ta nufa, tana ganin gidan da Sameer ya kama masu da sunan nasu gidan ta tab’e baki ta nufi gidan da takeda tabbacin na sabbin iyayensa ne....
Koda ta ida parking saida ta tsaya tana k’arema gidan kallo fuska a yatsine, Wai yanzu nan shine mahaifar Partner d’inta, Wai yanzu wad’annan sune tushen partner... Kai haba Haba inaa da sakel, Wllhi alwashi ta d’auka duk yanda zatai saita raba Sameer da wad’annan mutanen... Lokaci guda ta fito daga cikin motar kana ta d’auki handbag d’inta dake bisa d’aya seat d’in, ga mayafin dama da ba wani na kirki bane an sab’asa bisa kafad’a.... Sai faman kad’a d’an makullin mota take, Aiko nan almajiran dake zama k’ofar gidan suka mata chaaa suna fad’in “Hajiya Allah ya kiyaye... Hajiya Allah ya kare.....” Sunayi suna kallonta tamkar a zuba masu ita a kwanon baran nasu sun cinyeta, wasu na faman shafa motar tata.....
Siyama kaman ta had’iyi rai don takaici... Sai faman toshe hanci take tana k’yank’yan da jikinta... Wani uban tsawa ta dararawa Almajiran nan tana fad’in “Kai ku matsa min a hanya kafin ku shafa min wani cutan....!!”
Tai maganar tana mai ci gaba da toshe hanci had’ida jan skirt d’inta sama ga takalaminta mai uban tsini da take taku dashi cikin k’warewa...
D’ayan Almajirin yace “Basaida na fad’a maku ba karkuje arniya ce gashi kun gani ai....”
Suka kwashe da dariya suna duban yanda Siyama ke taku sauran har suna kwaikwayon yanayin tafiyar tata.... D’aya da bai ida cin tuwo miyar kukan dake cikin kwanon baransa ba jikin farar benz d’in Siyama ya isa Aiko nan ya mata fenti da tuwo miyar kukan nan.... Yaran suka kuma tintsirewa da dariya kana suka bar wajen gudun kada a gansu..:

Ko darajan sallama basu samu daga Siyama ba, tana tsaye tsakiyar verandar Mamy sai faman yatsina fuska take tana kuma k’arema gidan kallo don wancan zuwan nata ana makokin Kausar sannan zuwan na Nabila ne shiyasa sam bata samu ta k’arema gidan kallo ba, hannu a kunkumi take kuma juya kai tana jinjina kai baki a tab’e take bin lungu da sak’o na gidan da kallo
“Tabb! I can’t believe this... Wai wannan gidan tantabarun shine gidansu Partner, wllhi sam bazata saku ba, dole na raba mijina da wad’annan matsiyatan...” Ta k’arashe tana mai kuma yamutsa fuska....

Fitowar Mamy kenan daga kitchen ta hangi mata tsaye k’ofar parlornta sai faman kalle kalle take....
Mamaki ya kama Mamy tana tunanin toh ko wace wannan..... Lokaci guda Mamy ta nufota tana mai furta “Sannu baiwar Allah.... Lafiya....? Daga ina....?”
A tare Mamy ta jefowa Siyama wad’annan tambayoyi...
Maimakon ta bata amsa ko ta sami darajan gaisuwa saima kaikaitowa da tai tana mai k’arema wacceke mata tambayoyin kallo daga sama har k’asa....
Hasken wutan lantarkin da ya gauraye cikin gidan shi ya baiwa Siyama daman ganin cikin k’wayar idanun Mamy wanda hakan ya bata tabbacin wannan matar tanada alak’a mai k’arfi da Sameer d’inta don ga tabbaci daga k’wayan idanunta wanda yake baisa maraba dana Sameer, cikin bak’in nasu bai cika bak’i sosai ba ya d’anyi kalan ruwan k’asa kad’an maimakon bak’i.... A hankali Siyama ta saki murmushi bayan ta ida duban Mamy daga sama zuwa k’asa kana tace “Mijina nazo nema....”

Karaf a kunnuwar Nabilah da fitowarta kenan daga parlor hannunta rik’eda plate d’in data ida cin abinci....
Aiko Nabilah ta saki murmushi sakamakon hango Siyama da tai, daga yanda take kafin Mamy ta sami zarafin baiwa Siyama amsa ta bud’e murya tace “Finally our unbearable sister in-law has arrived...” Tai maganar tana dariya lokaci guda ta iso gaban Siyama wacce k’irjinta ya soma bugu tinda ta sinkayo muryar Nabilah....
Mamy duban Nabilah dake murmusawa tana k’arewa Siyama kallo tai kana tace “Kin santa ne...?”
Nabilah ta kuma murmusawa kana ta dubi Siyama tace “A gidan nan mun girma da mutuntawa da daraja na sama dakai, but unfortunately Mamy Sirkarki ba haka take ba...!” Ta k’arashe maganar tana mai watsawa Siyama muguwar kallo...
Mamy da kanta gaba d’aya ya d’aure d’an bud’e murya tai taceda Nabilah “Wai meke faruwa ne... wacece wannan Nabilah...?”

Gyara tsayuwa Nabilah tai still idanunta naga Siyama da suke faman aikawa juna muguwar kallo tamkar su shak’e juna kana ta saki murmushi a hankali tana mai k’arewa Siyama kallo daga sama zuwa k’asa kana tace “Wannan ba kowa bace Mamy face sirkarki matar Yaya Ma’aruf d’anki...”
Allah sarki Mamy nan da nan murmushi ya cika fuskarta ta shiga d’aga labulen parlor tana fad’in “A a lale lale bismillah, Aiko Ma’aruf bai sanar damu zuwan naki ba, yi hak’uri da rashin fahimtar da na maki, ke Nabilah maza ki kirawo Auntyn ku.... Ta k’arashe tana gyarawa Siyama yanda zata zauna....
Nabilah kuwa dad’a matsowa kusan Siyama da tai tsaye tana hura hanci tai, murmushi saman fuskarta take kaiwa Siyama runguma lokaci guda take furta “Welcome to the Family Sister in-law...” Cikin sigan rad’a saitin kunnen Siyama take rad’a mata “I’ve got a lot of surprises for you Aunty Siyama... Get ready to receive them...” Tana ida fad’in haka ta saki plate d’in hannunta aiko sai jikin mayafin Siyama sauran miyan dake jikin plate d’in ya b’ata mayafin nata gaba d’aya.... Siyama ta d’ago idanunta da suka kad’a sukai jazir tana duban Nabilah dake ci gaba da murmushi, sai kuma ta zaro idanuwa waje tana fad’in “Aw sorry sorry, wayyo I’m too clumsy.... Gashi kuma bakicin miyar kuka na b’ata miki jiki dashi... I’m sorry... K’arasa ciki sirkarki na jiranki... Bara naje na kirawo sauran sirakan naki don ku gana da juna....” Tana ida fad’in haka ta tintsire da dariya kana tasa kai ta wuce tana wani kad’a jiki irin yanda takeyi idan ‘yan shak’iyancinta suna kusa....

Siyama data koma tamkar mutum mutumi shaye da tsananin mamaki take duban gyalenta da ya koma koriya koriya ga k’amshin kuka da daddawa dake tashi jikinta.....

Sai faman yatsine yastine take har saida Mamy ta kuma mata iso kafin ta shigo parlorn shima ba don taso ba sai don wani irin k’warjini da matar tai mata kuma wani ikon Allah ta nemi duk wani courage na watsawa matar rashin mutunci ta rasa musamman da taji Nabilah na cewa sirkartace....
Kan kace mai tuni Mamy ta cika gaban Siyama da kayan motsa baki wanda ko kallo basu ishi Siyamar ba....K’afafu d’aya bisa d’aya take ci gaba da yatsine yatsine tana faman k’yank’yan da jikinta tamkar wacce ke zaune cikin bola....

***

Tin tana karanta calendar dake manne jikin bangon Office d’in har dai ta soma gyangyad’awa, babu Sameer babu dalilinsa, har aka kirawo isha ta tashi tayi, nan yanda tai sallar ta d’an kishingid’a gyangyad’i na sand’arta....

***

A can gida kuwa sai tururwar zuwa ganin matar Ma’aruf ake, su matan Baffah Ado da yaransu, su Sakinah Basma Sadiya da sauransu, su Sakina iyalan gulma abin nema ya samu dama ana son ganin matar Ya Ma’aruf duk wannan gayu da ajin nasa, harda d’aukar takalminta sukai bakin k’ofa suna k’arema takalmin kallo harta lambar size d’in takalmin saida suka duba, Basma kaw har saka takalmin saida tai, Siyama dake hangosu daga cikin labulen parlorn tamkar ta d’aura hannu aka ta zunduma ihu haka taji, ina zata iya standing wad’Annan halittun da sunan dangin mijinta, ko a mafarki bata tab’a hasasho tsayuwa inuwa guda da irin wad’annan mutanen ba.... Muryar Aunty Lami da tun shigowarta ta kasa motsawa daga kusan Siyama ya dawoda Siyamar daga duniyar tunaninda ta tafi....
Saida ta murmusa ta kuma gyara zama had’ida waigawa gefe da gefe ta tabbata babu kowa a parlorn sai su biyu kana tace “Sirkarmu kenan... Ai na fad’a miki indai mutanen gidan nan ne saidai fah kiyi hak’uri don gaba d’aya haka suke, wasu irin mutane ne nima nan da kike gani da k’yar nai adopting zama dasu... Amma karki damu with time zaki saba zaibi jikinki and if you really loves Ma’aruf, then you’ve to put up with his family....”
Batakai aya ba Siyama dake faman watsa mata kallon k’ask’anci ta tari zancen da fad’in “I love him more than love itself, kuma mun riga mun tsara rayuwarmu babu ku cikin rayuwarmu and I assure you I’ll do everything in my power naga na rabashi da wannan rayuwar da ya jefa kansa ciki sabida he doesn’t belong here...” Ta k’arashe tana mai juya idanu cikin salo na harara....
Wani irin dad’i ne ya mamaye zuciyar Lami, suna neman hanyar kauda Ma’aruf a karo na biyu toh ga dama cikin sauk’i ya samesu, indai har shida wannan shed’aniyar matar tasa soyayyarsu mai k’arfi ne tsaf tayi imani zata rabashi da kowa nashi suyi nesa dasu....Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai duban Siyama da hankalinta yafi tafiya zuwa ga kiran da taketa dannawa a waya ba’a d’agawa, sai faman huci take tana hura hanci, ta kirasa yafi sau babu adadi bai d’agawa, kuma ita haka take idan tana son abu toh fa sai ta samu, dan haka ci gaba tai da kiran nasa...

Raihanah da tuni bacci b’arawo ya saceta cikin baccin nata takejin ringing d’in waya yak’i k’arewa, ta bud’e idanunta a hankali yanda taji wayar naci gaba da ruri kuma ba’ada niyyan daina kira...
A hankali ta mik’e ta isa jikin table d’in nasa yanda ya mance wayar nashi gashi bai kashe ba... K’urama screen d’in wayar idanu tai yanda taga sunan wandake kiran ya bayyanada Partner, “Partner..” Ta nanata a hankali, nan ta shiga tunanin kalmar tana sosa idanunta da bai ida wartsakewa daga d’an baccin da tai ba, sam tunaninta bai kawo mata tace matarsa bace Partner, saima tinanin nata ya tafi wani wajen daban ta soma tunanin toh kodai work partner d’insa ne...? Toh ko dai yayi zaton a wani wajen ya mance wayar ya amshi na abokin nasa dan ya kira yaji ina ya barta bacin haka wannan kira tai yawa, bata ida tunanin ba kiran ya kuma shigowa... Still tai tana kallo wata zuciyar na cewa toh ki d’aga kiji wannan kira k’ila ba lafiya ba... A hankali tasa hannu ta d’aga wayar sallama saman bakinta ga muryar tata da sauran bacci a ciki....

Zumbur Siyama ta mik’e daga d’aya b’angaren jin mace ta amsa wayar mijinta zuciyarta na

Please Login or Register in order to submit comment