Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yai na dawo...?”
Daga d’aya b’angaren Mamy tace “Zulfa’u kinsan halin Baban naku waima yanzu abin yayi sauk’i tun bayan bayyanar Yayanku, kinfi kowa sanin halinsa ai....”
Zulfa’u da hawaye ke k’ok’arin cikowa idanunta tace “Mamy wllhi Allah nasan bayin Abbah bane, nasan haka kurum bazaice na tattara na dawo gida ba, Mamy nan fah da can duk d’aya ne, kuma ma nan d’in yafimin sauk’in tafiya Office...”
Sauk’e ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “Zulfa’u nima na fad’a mishi hakan, amma yace lallai lallai gobe ki dawo gida, tinda naga Baba Alhaji ya fice daga parlornsa nasan wani zance ka iya biyo baya tinda gashi ya hura wuta sosai kan maganar auren Yayanku da ‘yar wajensa Sahariyya...”
Shiru Zulfah tai tana nazarin maganganun Mamyn kana tace “Baba Alhaji yazo Mamy...?”
Mamy tace “Yanda kikaji... Banason dogon bayani Zulfa’u ki tattara gobe kizo gida zan nemi Antin taku a waya nai mata bayanin komai....”
A hankali Zulfah ta jinjina kai tamkar Mamyn na dubanta kana tace “Shikenan Mamy zanyi yanda kukace in sha Allah....”
“Yauwa sai kinzo, Allah shi miki Albarka...”
“Ameen Mamy...”
Sukai sallama kana Zulfah tai jigum tana tunanin, yanda Baba Alhaji ya hura wuta kan batun auren Ya Ma’aruf da Sahariyya ko shakka babu akwai abinda yake shirin yi tsakaninta da Ya Hafiz, idan kuwa nufinsa ne maida aurensu da Ya Hafiz gaskiya ba’a kyauta mata ba... Tana tsaka da tinanin Aunty B ta shigo ta taddata...
Tsaye tai tana duban Zulfa’un da tai nisa duniyar tunani....
Aunty B ta k’arasa ta ije kayan gugan data shigo dashi saman gado, gefen Zulfa’u ta zauna had’ida d’an dafata kad’an “Daughter lafiya... meke faruwa naga kinyi nisa cikin tunani haka...?”
Sauk’e ajiyan zuciya Zulfah tai “Aunty, Mamy ce muka gama waya da ita...”
Aunty B ta jinjina kai “Umhum ina jinki....”
Gyara zama Zulfa’u ta kumayi kana tace “Cewa tayi Abbah yace lallai lallai gobe na koma gida, and daga bayananta kaman maganar bazai wuce akan aurena da Ya Hafiz ba... Aunty idan hakan ta kasance bansan ya zanyi ba, tsoro nake kar suce zasu kuma had’a aurenmu a karo na biyu tinda gashi Baba Alhaji ya hura wuta kan batun auren Ya Ma’aruf da Sahariyya...”
Shiru Aunty B tai tamkar mai nazari kana tace “Bazai yuwu ki koma gidan Hafiz ba, bazan bari ba....”
Dubanta Zulfa’u tai da idanunta da sukai raurau “Aunty idan sukace na koma fah... Bazan iya bijire masu ba...”
Girgiza kai Aunty B tai had’ida gyara zama sosai “Toh ke Zulfa’u mai zai hana ki baiwa yaron nan Akram dama iyaye su shiga maganar tinda gashi naji Atika na cewa tin satin da ya shige yaketa damunki da batun turo magabatansa amma kink’i basa k’ofa, na tabbata idan sukaga kin tsaida manemi bazasu miki dole ba, saidai idan kuma har yanzu kina son Hafiz d’in ne....”
Fuzar da iska maras k’arfi Zulfah tai had’ida muskutawa “Aunty bazan b’oye maki ba, da fari bansan mai nakeji ba, I was so confused about Ya Hafiz amma yanzu ina mai tabbatar maki bana son Ya Hafiz, shi ma Akram banjin ina sonsa Aunty... Bansan menene na hanzarin ba, dadai sun barni zuwa wani d’an lokacin to get my head cleared...”
Sauk’e ajiyan zuciya Aunty B tai kana tace “Akram yaron kirki ne Zulfa’u kuma ni nan nasa anmin bincike akanshi and his background, baida wani aibu, mai zai hana ki bashi dama Zulfa’u, idan dai iyayenki sun matsa nidai a nawa shawarin da ki bari su maida aurenki da Hafiz gwara miki wannan yaro Akram... Amma fah shawarice... Ki natsu kiyi tunani kuma ki fad’iwa Ubangijinki ki fawwala masa lamranki domin zab’insa shine maki alkhairi...”
A hankali Zulfah ta jinjina kai kana tace “Toh Aunty zanyi yanda kikace zanyi tunanin... kuma zanyi addu’a dikda cewa cikin yinta nake ko yaushe....Na gode da shawarwarinki Aunty... thank you for always being there..”
D’an rungumeta Aunty B tai kana tace “Anything for you daughter... Allah Ubangiji ya miki zab’i mafi alkhairi...”
Zulfa’u ta amsada “Ameen Aunty na...”
***
Koda Sameer ya sami sak’on Wan mahaifin nasa bai k’asa a gwiwa ba ya amsa kiran nasa, saidai bai sami Baba Alhajin gida ba saiko Haule da yaranta, musamman Haule tasa Najah ta bud’e masa parlorn Baba Alhaji, sai wani nan nan dashi ake, Sameer bai mance farkon zuwansa gidan ba sanda ya buge Raihanah ya tadda Haule da wannan maras kunyar ‘yar nata da ake yunk’urin aura masa matsayin mata sun tasa Raihanah a gaba suna aibantata... Tinda ya shigo gidan gaba d’aya a tsare yake sosai, ganinsu ya kuma tuno masa abinda ya tadda suna ma Raihanah a wancan lokacin, kansa na bisa wayarsa Haule ta shigo tamkar zata zube ta masa sijjada, sai rawa jikinta keyi tana kuma tura k’eyar Najah tana fad’in tai sauri ta ije masa kayan motsa baki dake hannunta...
Najah dai girgiza kai kurum tai kana ta k’arasa ta aje masa tray d’in tana gaidashi... A tak’aice ya amsa sannan har lokacin fuskarsa babu walwala....
Ga mamakin Haule jira take yaji yace ina amaryarsa take, shiru kakeji saima sinkayo muryarsa tai yana tambayar Najah Baba Alhaji...
Najah tace “Ai ba dawo ba Yaya...”
Jinjina kai kurum yai kana ya dubi agogon hannunsa....
Haule ta watsawa Najah harara sanda take ficewa kana ta kutso kai ta shigo parlorn, baki har kunne take sakin murmushi da sallama...
A tak’aice Sameer ya gaidata don tuntuni baisan maiyasa tasu batazo d’aya da matar ba ko bayan da ya fahimci matar yayan babansa ne, ko hakan nada alak’a da saninda ya mata a fari ne sai Allah.... Dik yanda Haule taso tajasa da hira ta kasa samun fuska, harta firan kawo kayan lefe da shirinsa na biki dataita k’ok’arin bijiro dashi babu ko kamun kai Sameer bai amsa mata ba, k’arshe dai data gama kid’inta da rawarta mik’ewa tai tana fad’in “Ka saki jikinka fah kaci komai nan gidanku bara na kira maka Sahariyyar tana can tana shiryawa...”
D’an dakatar da ita yai da fad’in “A’a da kin barta don zuwan ba nata bane...”
Haule bata bari ya dasa aya ba tace “A’a karka damu tindadai kazo dole ta fito ku gaisa...” Kallo kurum yabi Haule dashi yanda take rawar k’afa har ta fice...
A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa “What have you gotten yourself into Sameer... Baka gama da problem d’in Siyama ba ga wani na kunno maka kai....” a hankali ya fuzar da iska mai zafin gaske yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa he’s doing this for the sake of the family, he cannot allow his family to fall apart bayan k’unci da suka fuskanta a lokacin da ya b’ace, he has to sacrifice and do what they ask him to do, for the sake of everybody’s happiness....
Yana tsaka da tunanin wayarsa ta d’auki ruri...
Sanda Sahariyya ta shigo parlorn waya yake dan haka bai amsa sallamarta ba, sai wani sanne sanne kai take ita a dole an fito zance wajen saurayi....
Duba guda ya mata ya d’auke kansa, har lokacin waya yake....
Sahariyya ta k’arasa ta zauna a kujera mai kallon nasa.... Sai faman sakin murmushi take tana k’irga ‘yan yatsunta yawa mutumiyar arzikin gaske...
Lokaci guda taga ya mik’e yana fad’i cikin wayar “I’ll be on my way...”
Zunbur Sahariyya ta mik’e tana binsa da kallon mamaki....


SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................ DA DABO_



*79*





“Yaya ina zakaje kuma bacin ko gaisawa bamuyi ba...” Tai maganar tamkar mai shirin kuka...
Cak ya tsaya ba tareda ya juyo ya dubeta ba, ganin yaja ya tsaya yasa Sahariyya ci gaba da fad’in “Kaga fah ko ruwan da aka kawo maka baka sha ba, dan Allah ka tsaya ko ruwan ka d’an sha...” Tai saurin k’arasawa ta shiga k’ok’arin bud’e drinks d’in tana zubawa a cup...
Yanda tai maganar cikeda girmamawa ya hana Sameer gwaleta, karkatowa yai kad’an yana duban yanda take serving drink d’in har rawa jikinta keyi.... Ta d’ago kai sukai ido hud’u nan taga dai har lokacin fuskarsa tamau, ta maida kanta k’asa tana mai furta “Ina yini...”
Saida ya kwashe wasu sakanni kaman mai nazarin wani abin sai kuma yace “Lafiya..” A tak’aice...
“Yaya ka zauna dan Allah...” Ta fad’i cikin kashe murya, wani duban ya mata ya sanyata had’iye sauran kalaman nata, duk duniya Sahariyya bata tab’a cin karo da wanda takejin bala’in shakkarsa kaman Sameer ba, ikon Allah wai ita Sahariyya kejin shakku da tsoro had’ida fargaban wani bil’adam kaman haka, a iyakacin saninta tsabagen k’aurin suna da tai na rashin kunya da rashin mutunci yasa duk saurayin da yazo wajenta idan halinta bai koresa ba toh kuwa jama’an unguwa sai sun koresa, amma yau ita ke jin azabebben fad’uwan gaba da tsananin shakkun wani mutum haka... Ta had’i miyau da k’yar, har lokacin tana nan duk’a gabansa dikda cewa k’afar tata bai ida warkewa ba amma ko zafin tsugunon da tai bataji....
Sameer ya d’an gyara tsayuwarsa kad’an yana karantarta kana yace “Yaya jikin naki...?”
Nan fah Sahariyya taji maganar tasa tamkar wacce aka jefota, dad’i ya cika zuciyarta ashe har ya damu da ita haka.... Cikeda jin dad’i ta amsa masa da cewa “Da sauk’i Yaya aima saura kad’an ne, gobe muke komawa wajen mai d’aurin dama...”
Jinjina kansa yai har lokacin tsaye gabanta yake hannayensa dafe da kunkumimnsa, saida ya d’an gyara tsayuwarsa kana yace “Menene asalin abinda ya sameki, me ya janyo faruwar ciwon...?”
D’agowa tai tana dubansa wani irin dad’i na mamaye illahirin zuciyarta, a hankali ta furta “K’addara ce Yaya...”
Sameer ya jinjina kai kana ya maimaita “K’addara... Kin yarda da k’addara...?”
Wannan karon a d’an zabure ta d’ago tana dubansa, lokaci guda ta saki murmushi wanda yafi kamada yak’e kana tace “Na yarda da k’addara Yaya...”
“Good..” Ya furta a hankali yana mai jinjina kai yayinda Sahariyya ta shagala sosai da annashuwa, sinkayo muryarsa tai yana fad’in “Idan kin yarda da k’addara kaman yanda kika fad’i maiyasa kika biyewa mahaifiyarki kuke aibanta k’anwarki Raihaan don kawai bata kasance d’iyaga mahaifiyarki ba..?”
Wannan karon azabebben fad’uwan gaba taji ya sauk’a mata, ta tuna farin zuwansa gidan tun Kafin susan cewa shine Ma’aruf, nan fah Sahariyya ta shiga muzurai tana neman abin fad’i lokaci guda ta soma kame kame da inda inda... Sameer ya girgiza kai a hankali yana mai aika mata wani kallo lokaci guda ya sakale hannayensa cikin aljihun wandonsa kana yaci gaba da fad’in “Wacce kika k’ona da ganganci itace ta yarda da k’addara amma bake ba, nasan kinsan wa nake nufi.... Anyways Allah ya baki lafiya, ni zan wuce suna kirana a asibiti.... Idan Baba Alhaji yazo sai ki fad’a mishi nazo ban sameshi ba....” Daga haka bai jira cewarta ba yasa kai ya fice...
Sahariyya dake dab’e wajen tamkar wacce aka dasa kasa motsa koda d’an yatsarta tai, dik a tunaninta Sameer damuwarsa akanta yake nuna mata ashe ba haka bane, magana yaso yab’a mata kuma ba akan kowa ba sai kan shegiyar k’anwar nan nata... Wani irin zogi da rad’ad’i taji zuciyarta na mata, idanunta suka kad’a sukai jazir hawayen da basu shirya fitowa ba suka shiga zarya a kumatunta, wani irin tsanar Raihanah takeji kaman ta shak’eta ta mutu, fuskar Raihanah take hangowa tana mai furtawa a fili “Na tsaneki na tsaneki shegiya stinanniya munafuka algunguma mayya..!” Idanunta na zuban hawaye masu rad’ad’i take maganar cikin tsananin karaji...
A haka Haule ta shigo ta taddata, ganinta a duk’e tana hawaye ya sanya Haule k’arasawa da sauri ta shiga jijjigata tana fad’in “Ke Sahariyya... Lafiya... Meke faruwa.. Ina Ma’aruf d’in....?”
Sahariyya na hawaye take fad’in “Hajiya dik laifin munafukar Raihanar nan ne, annamimiya mai halin munafukan farko, nunawa take itace mutumiyar arziki keda ‘ya’yanki faragurbi... Munafuka wayasan kalan salon munafuncin da take masa can gidan Mamanin... Ni wllhi Hajiya kisa Baba Alhaji ya dawo da ita gida, Allah kad’ai yasan mai take masa acan mai shegen son mazan bala’i....” Ta k’arashe tana goge hawayen da suka wanke mata fuska...
Murmusawa kad’an Haule tai kana tace “Banda abinki mai Ma’aruf zai da wannan banzar yarinyar tausayice kawai take basa, kinsan shi ya mata aiki lokacinda ta k’one kuma Allah yayisa mai tausayi da tausasawa bacin haka ke ko a hanya yayi kama da wanda zai tarayya da Raihanah ne ai Ma’aruf saike naki ne, domin kaw an gama magana ki kwantar da hankalinki yanzu zan kira mahaifiyarsa mujin batun lefe a ina anka tsaya... Karma wannan ya tada miki hankali, ci gaba da shirye shiryenki, ki kirawo Fa’iza yau kuje ku cire ankonku muma ku ciro mana ankon gida iyanin....”
Kalaman Hajiya ya d’an tausasa zuciyar Sahariyya, ta saki murmushi tana mai furta “Shisa nake sonki Hajiyata...” Hajiya ta rungumeta tana fad’in “Aikinfi min wancan shashashar k’anwar taki wacce bata k’aunar uwarta....” Ta k’arashe tana aikama Naja’atu dake tattara wajen hrara... Giriza kai kurum Najah tai ba tareda cewa komai ba ta fice da parantin dake hannunta....
***

Kasancewar washe gari baida zuwa asibiti da wuri ya sanyashi yada zango gidansu abokinsa Shamsu don sun kwana biyu basu had’u ba, Shamsun ma wata k’aramar kwangila ya samu nan cikin gari da wata company shisa shima d’in bai zauna ba kwana biyun.... A parlor Sameer ya samu Mama suka gaisa tana masa tsiyan shida abokinsa aiki duk ya b’oyesu gwarama shi nada iyali amma abokin nasa bai ije kowa ba sai bautan neman kud’i....
Sameer ya d’an sosa k’eyarsa yana mai furta “Zai aje ne Mama....” Yai maganar yana duban k’ofa yanda Shamsu ke k’arasowa cikin parlorn hannunsa rik’eda mug alamun bai jima da tashi ba...
Mama ta dubi Shamsun baki a tab’e kana tace “Allah yasa yaji gori ya aje d’in, mutum gansameme kullum saidai ya tashi ya ishi mutane da tsifface tsiffacen baison cin wannan da safe baison cin wancan, idan kaji gori kai aure muma ma huta da wannan tsirin naka... K’aton kawai...” Ta k’arashe tana yab’a masa muguwar kallo...
Sameer kaw sai sakin murmushi yake yana duban yanda abonkin nasa ya had’e gira sosai....
“Mama fah safiyar da saura dan Allah a k’yaleni haka nan, kofa karin kumallo banyi ba...”
“Tafi can ka rufewa mutane baki, Kaga Sameer ka d’auki hotonsa ka raba a masallatai ko Allah zaisa a dace...”
“Mama neman kai kike dani...?” Shamsu yace yana mai mik’awa Sameer hannu domin yin masabaha...
Mama tace “Ahtoh naga abin naka bana k’are bane ai....”
Sameer dake danne dariyarsa yace “Yanda kikace hakan za’ai Mama...”
“Toh ai ba masallaci ya kamata kukai ba makarantar ‘yanmata ya kamata kukai tallan nawa...” Shamsu yace yana mai zama gefen Sameer...
D’an darawa sukai gaba d’aya kana Mama ta mik’e tana tambayan Sameer mai za’a kawo masa...
Cikeda ladabi yace “A’a Mama nikam a k’oshe nake na gode....”
Mama tace “Aiko dai kaji mai Iyali, wanine dai sai anyita fama dashi....”
Shamsu ya tari zancen nata da fad’in “Nima ruwan tea d’in nan kawai ya isheni Mamana...”
“Kadaiji dashi..” Mama tace sanda take bari masu parlorn...
D’an shaking hannu suka kumayi suna dariyar draman Mama kana Shamsu yace “Doc,ya akai ne... Kwana biyu ko k’yallinka ba’a gani, ko zumud’in angoncin ne ya soma b’oyeka....” Yai maganar cikeda zolaya...
Gajeren tsaki Sameer yai had’ida b’alla masa harara kana yace “Aure ko damuwa....”
Shamsu ya d’an dara kad’an “Yaushe aure ya koma damuwa, ince gashi kaida Mama kun hanani sakat.... Ni gwarama da kazo coz dama inatason mu had’u naji what are your plans...”
Fuzar da iska Sameer yai a hankali had’ida fitowa daga cikin kujeran kad’an, saida ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa kana yace “Wannan kuma saidai ka tambayisu Abbah don ni kaina ban sani ba....”
Dariya mai bayyana hak’wara Shamsu keyi yana mai furta “Sameer kenan, gaba d’aya sai ka juye min Sameer d’in dana sani sanda muke sch kafin ka auri Partner....”
Nanma dai d’an duban nasa kawai Sameer yai wannan karon harda tab’e baki kad’an “Kaidai baka tab’a d’aukan abu serious, na kawo maka matsalata kana dariya...”
“Toh kuka kakeso nayi.., Kai ba d’an gata bane, su Mummy Sun aura maka Siyama yanzu gashi su Abbah zasu aura maka Sahariyya... Ni amin Auren mana idan inada gatan....” Har yanzu dai dariyar bata bar saman fuskar Shamsu ba....
Mik’ewa tsaye Sameer yai yana zira hannaye cikin aljihu...
Shamsu dake sipping tea ya d’ago yana dubansa kana yace “Ina kuma zakaje naga dai shigowarka kenan...”

Agogon hannunsa yake dubawa lokaci guda yake furta “Is pointless talking to you, bazaka tab’a canzawa ba Shamsu kai komai a rayuwa shiririta ka d’aukesa...” Ganin da gaske Sameer tafiya zai yasa Shamsu kamo hannunsa ya maidasa ya zaunar yana fad’in “Haba surgeon abin bai kai nan ba, kasan dai dole na tab’a haline zauna, lets talk...”
Kallon ko inkula Sameer ya aika masa sanda yake zama bisa sofar..... Zamansa yai daidai da soma kiran wayarsa, hannu yasa ya ciro wayar dake aljihun wandonsa, mamakine ya cikasa ganin mai kiran nasa...
Shamsu ya da yaga yayiwa screen d’in waya k’uri yace “Ya dai lafia....?”
Sameer yace “Kana maganar Siyama kaga ga Daddynta na kira...” Ya k’arashe maganar yana mai receiving call d’in, dikda cewa yanajin bai kyauta ba don tin bayan da Siyama ta tafi bai sanar da Daddyn komai ba....
Bayan sun gaisa cikeda mutuntawa Daddy yace “Sameer inason ganinka....”
Duban Shamsu Sameer ya d’anyi Shamsun ma Shi yake duba, jin Sameer yai shiru daga d’aya b’angaren ya sa Daddy ci gaba da fad’in “Ina Kano karka damu basai kaje Kaduna ba, ina nan Tahir kazo ka sameni...”
Harce har na had’ewa yake furta “O... Ok Daddy, zanzo yanzu in sha Allah...”
Daddy yace “Good, saikazo.....”
Datse kiran yai yana mai duban Shamsu...
Shamsu ya d’aga masa gira alamun tambaya...
Fuzar da iska kad’an yai kana yace “I’ve to go, Daddy keson ganina yana nan Kano.... Allah sa ba maganan Siyama zaimin ba don gaskiya zanji kunya tinda ni banje na sameshi ba shi ya taho ya sameni...”
“Kaima kasan bazai wuce hakan ba, bacin haka mai zaisa ya nemeka har Kano...” Shamsu yace yana mai mik’ewa tsaye shima....
Girgiza kai Sameer yake a hankali tamkar wanda yai nisa cikin tunani kana yace “I don’t know... Kaga bara naje na sameshi naji ko menene..” Ya mik’a masa hannu suka d’anyi handshake kana Shamsu yace “Shikenan Abokina sai munyi magana... Zamu had’u later idan kana hospital ne ma sai ka fad’a mun...”
“Ok until later..” Sameer yace kafin ya fice....
***
Daddy ya gyara zama sosai yana mai ci gaba da furta “Sameer, sam ban kiraka nan akan maganar matarka Siyama ba don nasan iyaka hak’uri kayi da Siyama, ni kaina shaida ne don a baya komai tayi bayanta nakebi bana considering d’inka.... Sameer kayi hak’uri ka yafeni bisa duk abubuwan da na maka baya because of my selfishness...”
Cikin sauri Sameer ya d’ago yana duban Daddyn Siyama, lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “No Daddy, dan Allah ka daina rok’ona gafara, baka tab’a mun komai ba ni, har kwanan gobe Uba kake min koda bani auren Siyama sabida kaid’in Abokin Daddy na ne....”
Daddy yai murmushi cikeda jin dad’i kana yace “Allah ya maka albarka Sameer...”
Sameer ya amsada Ameen a hankali, Daddy yaci gaba da fad’in “Wato Sameer abinda yasa na kiraka ba komai bane face kan maganar Khalid da k’anwarka Nabilah... Nasan kasanda batun....”
Wannan karon mamaki ne sosai ya nuna a fuskan Sameer don sam bai kawo hakan a zuciyarsa ba, baiyi zaton mak’asudin zuwan Daddyn ba kenan....Jinjina kai yayi yana mai d’aura murmushi kad’an saman fuskarsa...
Daddy ya jinjina kai yace “Alhamdulillah..” Saida ya kuma gyara zamansa kana yaci gaba da fad’in “Inaso kamin jagora wajen mahaifinka na nemawa d’ah na Khalid aurenta....”
Shiru ne ya d’an ratsa tsakani har saida Daddy yace “Akwai matsala ne....?”
Girgiza kai Sameer yai kana yace “A’a babu matsala Daddy ni zan maka jagora har wajen Abbah na, bakada matsala idan don wannan ne... A koda yaushe fatanmu shine zab’in Alkhairi...”
Daddy ya murmusa kana yace “Toh Alhamdulillah, yanzu na baka wuk’a da nama inaso kafin na bar garin nan na sami mahaifinka muyi magana ta manya, sai ka soma tuntub’arsa muji yaushe yake free, sai ya bamu rana...”
Sameer ya jinjina kai a hakali yace “Shikenan Daddy zan tuntub’esa kaman yana kace...”
Daddy yai masa godiya kafin sukai sallama Sameer ya fice.....

***

A can gidan Abban kuwa Zulfa’u durk’ushe take gaban Iyayen nata Bana Alhaji da Abbah, Baba Alhaji ya kuma gyara zama kana yace “Ke muke saurare Zulfa’u kinyi shiru, shirunki na nufin kin amince da komawa gidan mijinki na fari kenan....”
Abbah yai saurin katsesa da fad’in “A’a Yaya shirun bazaura baya nufin Eh ne, idan baka mance ba ko shari’a cewa tayi Budurwa ce shirunta ke nuni da Eh amma banda bazawara, Yaya karmu mata dole, akwai lokaci, munada nan da wattani biyu gaba idan har tayi shawari ta tantance sai ta sanar damu amma babu batun tilastawa, koda bata tab’a aure ba ma nayi alk’awari bazan kuma tilasta ma d’aya daga cikin yarana ba, ina kuma fata iyaye masu wannan d’abi’a su farga su daina...” Banda uwar harara babu abinda Baba Alhaji ke aika masa... Ala dole ya jinjina kai kana ya dubi Zulfah da kanta ke k’asa tin shigowarta yace “Maza tashi ki shige gida, amma ki sani bazamu zuba miki ido ba kaman yanda Babanki keso mu sakaki gaba muna kallo, kafin wa’adin nan ya cika kizo mana da zance mai dad’i....”
Jinjina kai kurum tai ba tareda cewa komai ba don idan ta bud’e baki tabbas kuka ne zai fito....
Cikeda tausayawa Abbah ke dubanta, cikin muryar mai taushi yaceda ita “Tashi kije mamata.... Allah Ubangiji ya miki albarka ya miki zab’i mafi alkhairi...”
Baba Alhaji ya saki baki yana kallon d’an uwan nasa, k’wafa kurum yai ba tareda cewa komai ba saima karkad’a kai da yake tamkar wani k’adangare....
Zulfah tana shiga gida ta fad’a jikin Mamy sai kuka, haka Mamy taita lallashinta tana nuna mata ko wani bawa da kalan tasa k’addaran a rayuwa ita kuma kalan tata k’addaran kenan....
Koda Sameer yazo ya sami Abbah da batun shikam Abbah mamaki ma abin ya bashi ganin lokaci guda maganan auren yaran nasa ne yaketa kunno kai kaman wad’anda ake ingizawa, da farko Ma’aruf ne da Zulfa’u yanzu kuma ga Nabilah....Shiru yai tamkar mai nazari har lokacin baice komai ba....
Sameer ne ya d’an gyara zamansa had’ida gyaran murya kad’an kana yace “Abbah idan baka shirya tarbansu ba babu matsala ni sai na sanar da Daddyn sai zuwa wani lokacin....”
Girgiza kai kad’an Abbah yai kana yace “Ba nufina ba kenan Ma’aruf, shin tambayan izini zasuzo ko kuwa neman aure zasuzo, idan neman aure zasuzo toh fah dole sai nayi magana da d’iyata, na sani d’anuwan matarka ne kuma babu wani dogon bincike tinda kai ka sansu tare kuka taso amma d’iyata fah? Dole sai anji daga gareta...”
Sameer ya jinjina kai a hankali kana yace “You’re right Abbah...”
Abbah yace “Yauwa yayi kyau daka fahimci hakan, zan sami mahaifiyarta ta tuntub’eta muji nata b’angaren... Idan ta amince tana son D’ansu shikenan sai suzo muyi magana, don burin ko wane uba kenan yaga d’iyarsa data isa munzanin aure a d’akin mijinta... Duk yanda mukayi da mahaifiyarku zan sanar dakai kai kuma saika sanar dashi....”
Sameer ya amsada “Toh Abbah hakan yayi....”
Abbah ya jinjina kai kana yace “Toh kai ya batun naka auren....?”
Gaban Sameer ya yanke ya fad’i, shi harga Allah mancewa yakeyi da wani aure dake gabansa...
Ganin yayi shiru yasa Abbah cewa “Anya Ma’aruf kana farin ciki da hukuncin da ka yanke...?”
Gaba d’aya sai yaji jikinsa ya masa mugun sanyi da tambayar mahaifin nasa, ta yaya zai sanarda Abbah yana Farin ciki da wannan hukunci da ya yanke ma kansa bayan yasan ba hakan bane, toh amma wannan hukunci ne da ya riga ya yanke ma kansa dukda sanin cewa shi kansa baisan ko zai iya ba...Baikaiga bashi amsa ba sukaji sallama daga k’ofa, Aunty Lami ce ta shigo sai washe baki take tana kod’a Sameer da fad’in “A’ah Kaga ashe ma ga angon a nan... Ango mai tagwayen mata dama nemanka nake....”
Murmushin yak’e kawai Sameer keyi yayinda Abbah ya tsare yana dubanta...
“Sameer yace wani abu ne Aunty...?”
Aunty Lami dake k’ok’arin zama saman kujeran gefen Abbah tace “Dama kan maganan lefe ne, kasan Mamy dai ‘yar kunyace ta d’an fari tsakaninku shine ta wakiltani mu tattauna komai, kama daga kayan lefe zuwa duk wani abu na Al’ada da za’a buk’ata kaga sam bamuda wani sauran lokaci wata biyu ne jal ya rage mana baima cika ba...”
Sameer ya d’an shafa kansa kana yace “Wannan duk babu matsala Aunty, duk abinda ake buk’ata a fad’a mun, kayan lefen kuma zan maki transfer din kud’in zuwa account d’inki idan akwai abinda yayi short sai a sanar dani...”
Aunty Lami ta shiga Washe baki tanaci gaba da kod’asa yayinda Abbah yabi d’an nasa da

Please Login or Register in order to submit comment