Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baiga amaryar sa ba... Dole na bata labarin gwagwarmayar neman aurenta da aka sha taredamu....”
Murmusawa kurum Khalid yake dan shi kanshi sosai yake son ya sakata a idanunsa... Yusrah Baffah ya kirawo ta sanar dashi suna can gwammaja gidan Aunty Bara’atu, dashike Baffah yasan gidan sabida lokacinda sukazo sunje har gidan wajen Aunty Bara’atu babu wani b’ata lokaci yai jagoranciwa abokan nasu... Khalid gaba d’aya ganin abubuwan da suke kan faruwa yake tamkar a mafarki....
Tuni Aunty B tasa an kuma gyare masu parlorn waje, ga tarban abinci na musamman da aka jere masu, saida suka biya masallacin gefen gidan suka gabatar da sallar azahar kana suka k’araso gidan...
Ita kaw Nabilah tinda aka sanar da ita an d’aura aurenta take kuka tamkar ranta zai fice, gaba d’aya haka ta duk’unk’une cikin farar laffayan da aka d’aura mata tana zabga kuka wanda ita kanta batasan na menene bane. Shin na farin ciki ne ko kuwa akasin Farin ciki.... Shin anya mijin da aka aura mata mai k’aunarta ne... Idan yana k’aunarta maiyasa har rana ta yau ranar d’aurin aurensu bata saka shi a idanunta ba bataji daga gareshi ba... Shin menene makomar aurenta....?”

Kaman daga sama ta soma jiyo k’awayenta su Hameeda dasu Barakah coursemates d’insu k’alilan da suka gayyata suna lek’en window suna fad’in “Ga ango ga ango...” Dumm!!! Sautin da k’irjinta ya bada, tana jiyo muryan maza da dama daga window yanda suke gaisawa da mutane... Tuni Aunty B tasa akai masauk’i a parlor... Babu yanda ba’ai da Nabilah taje su gaisa ba fir tak’i saima sabon kukan da ta fashe dashi... Khalid kaw jin ance tak’i zuwa tanata kuka ya sanyasa mik’ewa tsam ya nufi d’akin yana mai neman izini wajen Aunty Bara’atu... Aunty tace yaje shi ai daga ita amaryar ce saiko k’awayenta... Khalid kaman zai kifa haka ya nufi d’akin... Tanajin su Hameeda na gaidashi bugun zuciyarta ya k’aru, ga k’amshin nan nasa na cikin motarsa da sam ya kasa b’acewa daga hancinta yana tashi cikin d’akin...
Sai faman shan zuciya take sanda ya isa saman gadon ya zauna a gefenta... Bugun zuciyarta ya ninku.... K’uri yai mata yana kallon yanda ta tak’ure waje guda ta kasa koda d’ago kanta ne... A hankali ya d’an kwanto da kansa saitin fuskarta dake kife “Teddy bear.... Look up... D’ago ki kalleni....Kinada labarin ke d’in matata ce yanzu.... Teddy bear yau anyi aurenmu... Mu d’in ma’aurata ne yanzu...” Yanda yake maganar ya kuma sanyata sakin kukan... Kukan da sam baijin dad’in sautinsu cikin kunnuwarsa da zuciyarsa...
D’an gimtsewa yai kad’an kana yace “Nasan maiyasa kikak’i d’ago kai ki dubeni, kika kuma k’i ki daina kuka... You’re still mad at me... Oya tashi ki scolding d’ina yanda kike so kinji koh...” Yai maganar yana k’ok’arin yaye mayafin data kifa kanta ciki...
Janye jikinta tai tana fad’in “Ni ka k’yaleni... Ba kai ne... Ba kai ne ba....” Ta kasa ci gaba da maganan sai Sabon kuka... Wannan karon rungumota yai cikin k’irjinsa yana fad’in “I know teddy bear, ni d’in mai laifi ne... I’m sorry please forgive your Bear... Daga yanzu bazan sake barinki ba, zamu kasance tare har k’arshen rayuwar mu... Your bear is here with you... Hash now...!”
Cikin sigan lallashi mai cikeda kulawa yake maganar yayinda Nabilah ta kasa turesa daga jikinta saima cukwikuye fuskarta da tai cikin babbar rigarsa ga sautin ajiyan zuciyarta dake tashi, zukatansu suna bugawa lokaci guda... Haba su Hameeda sun shagala da kallon irin wannan soyayya, wannan ta tab’a wannan wancan ta tab’a wancan... Barakah harda saita wayarta a sace tana masu video a cewarta wannan soyayya bata gani ita kad’ai ba dole takai gaba....
Khalid dai da k’yar ya lallab’o amaryarsa ta fito parlor da rakiyarsu Yusrah suka gaisa dasu Baffah... Sai zolayan Ango suke suna dariyar yanda gaban rigarsa ya b’aci da kwalliyan Amarya danginsu janbaki da gazal... Ko ba’ace ba kasan Amarya taci kuka a gaban babban garen ango..
Shiko Khalid d’in sai wani tsimewa yake yana b’allawasu Baffah harara...
***
A can gidan Abbah kuwa gama d’aurin auren da kad’an Sameer ya iso, Shamsu ne ya d’aukosa daga can airport, fitowar safe yai dan ya riga ya gama abinda zai a Lagos d’in, baisan daliliba amma sosai yaji zuciyarsa ta karkata zuwa Gida.... Sanda ya isa ya tadda mutane ‘yan d’aurin aure Sun watse saiko d’aid’aiku dake parlorn Abbah suma d’in su Daddy ne saiko Engr da suka tsaya tattaunawa lamarin...
Gaisawa dasu kawai yai kana ya nufi can gidansa dan kintsawa, har wannan lokaci baida labarin wainar da ake tuk’awa, saidai Abbah ya sanar dashi yayi farin ciki da dawowarsa dan akwai muhimmin abinda ya kamata ya sani...

A can cikin gida kaw tinda Mamy tai tozali da Daula hankalinta ya gaza kwanciya, bugun zuciyarta ya ninku babu shiri ta d’aga waya ta sanar da ‘yar uwarta Bara’atu cewa maza tazo taga wannan abin al’ajabi da take gani na faruwa a idanunta... Aiko babu shiri Aunty Bara’atu ta fito ta nufi gidan Mamy afujajan...

A can gidan Baba Alhaji kaw Haule na tsaka da tik’an rawa Lami ta kira wayarta cikin d’imauta da tashin hankali.... Da k’yar ta iya d’aga wayar dan bata fatan abinda zai katse mata wannan farin ciki da annashuwa da take ciki....
Jin muryar Lami d’in a birkice yasa Haule saita kanta kad’an kana tace “Lami ki natsu ki sanar dani meke faruwa.... Mufa yau ranar farin cikinmu ne an d’aura auren Ma’aruf....”
Lami tace “K’warai an d’aura auren Ma’aruf amma fah abu ne a duhu...!”
Gaban Haule ya bada Dumm! Domin kaw ta tsani wannan kalmar *Abu a duhu* kaman yanda bokansu yaita fad’a masu gameda b’acewar Ma’aruf d’in...
“Ban gane abu a duhu ba Lami...? Wane irin abu a duhu..? Shin ba’a d’aura auren Ma’aruf d’in bane....?”

Aunty Lami ya katse zufan da take ya tsartsafo a goshinta kana tace “Haule k’warai abu a duhu domin kaw babu tak’amaimen wanda zaki tambaya yace miki ga matar da aka d’aura mata aure da Ma’aruf saidai kowa yanada tabbacin ba Sahariyya bace matar...”
Tashin hankali gobarar gemu...!!!
Take Haule ta soma gani bibbiyu... Mai kid’a yana kuma k’ure speaker Haule ta malmalo ashariya ta watsa masa... Tamkar wata zararriya take fad’in “K’arya kenan... Wllhi k’arya kenan... Babu ubanda ya isa yaga bayana ni Haule.... Lami bakiji da kyau ba... Wayyo wayyo Wayyo na shiga Uku..!!!” Duniya ta shiga juya ma Haule upside down, Haule ta warware d’aurin kanta tai d’amara tana kururuwa... Haba nan fah mata aka soma kame baki ana ‘yar k’us k’us abin nema ya samu...
Sahariyya kaw ihu take bataji bata gani, ... A haka Baba Alhaji ya shigo yana washe baki tamkar Sabon Ango saidai tashin hankalin da ya tadda gidan nashi ne ya bala’in tada masa hankali domin kaw zani a hannu yaga Haule sai ihu take tsakar gida tana tsalle had’ida kururuwa....

Suna a haka Sahariyya ta fito daga d’aki tamkar zararriya tana kilan Basmah data kawo mata rahoton anyi auren Yaya Ma’aruf amma ba ita bace Amarya.... Bugunta kurum Sahariyya take da sandar crutches d’inta tana fad’in “Dan uwarki sai na halak’aki... Mai mugun alkaba’iri.... Yau sai na cire miki son gulma da munafunci.....Ku barni na karta shegiya mai mummunan fata...!!!” Haba nan fah jama’a akai kan Sahariyya ana k’ok’arin rik’ota had’ida ceton Basmah da take shan duka da sandar k’arfe hannun Sahariyyar...
Naja’atu ce ta k’araso ta fincike sandar hannun Sahariyya... Lokaci guda tana huci take fad’in “K’warai Addah Sahariyya Ya Ma’aruf bai cancanceki ba, kuma idan da wacce zaki daka nice nan ba Basmah...!!”

Gabaki d’aya kallo ya dawo kan Naja’atu....

SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_





*89*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Haule da bataji batun da kyau ba, matsawa kusan Naja’atu tai tana k’are mata kallo shaye da tsananin mamaki “Ke mai kikace....? Maimaita naji dan uwarki....”

Naja’atu dake rungumeda Basmah wacce har lokacin matsan hawaye take tace “Hajiya nasan kinji mai nace, kuma kinfi kowa sanin cewa Ya Ma’aruf bai cancanci zama mijin Addah Sahariyya ba....” Batakai aya ba Hajiya ta shiga salallami tana tafe hannaye “Kice bak’in ciki kike da ‘yaruwarki ta jini Naja’atu... Na shiga uku ni Haule, yanzu Najah sabida tsaban hassada da k’eta kawai dan shi Ma’aruf d’in bai zab’eki ba shine sabida kutungwila irin taki saida kika shiga kika fita kika hana auren ‘yaruwarki yuwa... Haba ai biri yayi kama da mutum kenan dake aka d’aura auren... Toh kaw baki isa ba, idan mutuwa kike sai an kwance an d’aura da Addarki dan mu ba Ke muka bashi ba ehe....!”
Tinda ta soma magana Naja’atu Ke girgiza kai tama rasa abin fad’i ta yarda mahaifiyarta ta gama yin nisa bazataji kira ba... Sahariyya dake tsaye tana huci tamkar zakanya a d’ari tai kan Naja’atu ta shiga fincikarta tana kai mata bugu ta ko ina tana fad’in “Wllhi yau koni ko ke a gidan nan... Munafuka mahassadiya makira annamimiya....!!” Tuni su Fa’iza sukai kan Sahariyya suna k’ok’arin janyeta, ihu kawai Sahariyya take tana bugun dik yanda hannunta ya sauk’a koma wanene, bataji bata gani tamkar sabuwar kamun hauka....
Baba Alhaji kaw tuni ya janyo hannun Haule suka keb’e dan ko takan d’iyarsa Sahariyya baibi ba...
Kwab’e babbar rigarsa yai had’ida maida hular kansa baya, ya dubi Haule data kame kunkumi tana girgiza tana huci...
“Ke Haule Wai meke faruwa ne...? Meye na tadda na faruwa a gidan nan... wane batu nakeji cewa an canza auren Sahariyya...?”

Sororo Haule Ke dubansa kana tace “Shin nada kai waye yafi cancanta ya amsa wad’annan tambayoyin...? Kaida kake wajen bukin d’aurin auren ina ka makara har aka maka wasan kura da yaranka... Idan har kana wajen d’aurin auren ta yaya duk haka ya faru....?”
Gaban Baba Alhaji ya bada Dumm! Tabbas baya wajen aka d’aura auren...

Haule datai sakare tana dubansa jikinta na kuma yin sanyi, gyara tsayuwarta ta kumayi kana tace “Alhaji ina saurarenka, a gidan uwar wa ka makara hakan takasance... Shin ba cemin kai ka fice d’aurin aure ba... Toh idan ba auren ‘ya’yanka ka tafi ba auren uwar waye ka tafi....? Ko kana shirya wani abin ne ba tareda sanina ba...?” Ta k’arashe tana tsattsaresa da idanunta da tuni kwalliyan da akai mata ya soma zazzgowa ya b’ata mata fuska kaman ‘yar wasan tashe...

Tinda ta soma magana yake aika mata muguwar kallo... Cikeda borin kunya yake fad’in “Yanzu ba lokacin nuna yatsaga juna bane, kamata yai mu tafi gidan Usman muji uban waye ya bashi daman yai mana wasan k’wallon kondo da yara...!” Ya k’arashe yana kuma rarumar babbar rigarsa....

Haule tace “Yauwa yanzu naji batu....”
Har sun kai k’ofa Baba Alhaji yaja yai birki yace “Toh amma ai Naja’atu da Sahariyya dik abu gudane... Inaga mubar zancen a haka...”
Muguwar kallo Haule ta watsa masa kana tace “Eh lallai na yarda Kai Hafiz ya gada a rashin lissafi.... Dik yanda akai sunada nasu dalilin na canza auren nan, dole mubi kadin lamarin sannan a tinaninka zamu iya tank’wara Naja’atu mu cika burinmu ne.... Ai Sahariyya itace mabud’in cikan burinmu....”
Baba Alhaji ya jinjina kai yace “Kuma kince wani abu.....”
Take suka fice afujajan suka nufi gidan Abbah, kotakan su Sahariyya basu bi ba, gidan biki ya koma gidan rabon dambe... Ana a haka Su Amara suka shigo gidan da baya da baya suna tik’an rawa sun k’ure kid’an wak’ar nan da ake yayi na AURE MARTABA... Dama ba’a gayyaci Amara da tawaganta ba suna shak’e da haushin Sahariyya dan Bikin ko wata budurwa ya tashi a unguwar dole a aikama Amara anko da katinta itada mutanenta toh Bikin Sahariyya su Fa’iza selecting sukai dan haka ba’a gayyacesu Amara ba, koda sukaji an fasa biki suka shigo d’aukan fansa...
Tashin hankalin Sahariyya ya ninku gashi su Amara hidimansu babu mutunci sun sakata tsakiya sai tik’an rawa suke suna mata lik’ida k’osan rogo da suka shigo dashi ciki kwano.....

***
Dikda cewa batasan mahaifiyarsu sosai ba sabida tanada k’anan shekaru Allah yai mata rasuwa tabbas wannan mata tanada fuska irinta mahaifiyarsu.... A hankali taci gaba da takowa tana duban matar wacce keta faman sakin murmushi tana gaisawa da jama’a, d’abi’unta da murmushinta irinta mahaifiyarsu ce... Aunty Bara’atu tasa hannu a hankali tana goge hawayen da suka gangaro mata, Mamy tana hangota ta k’arasa gareta suka rik’e hannayen juna suna ci gaba da kallon Aunty Daula wacce sam bata kula da irin duban da matan Ke mata ba... Mamy ta janyo hannun Aunty B a hankali suka k’eb’e... Lokaci guda suka had’a goshinsu waje guda suna hawaye.... Aunty B cikin rawar murya take fad’in “Fuskar Mama Hajja... Mamy fuskar Mama Hajjah na gani... Tell me Ya Mariya wacece wancar matar...? Shin munada alak’a da ita ne...? Dikda k’ananan shekaru na bazan mance fuskar mahaifiyar mu ba... Ya Mariya wacece matar nan...?”

Mamy tai k’ok’arin saita kanta kana ta shiga share ma Aunty B hawayenta, lokaci guda take k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarta “Wannan matar da kuke waya mai murya irinta Hajja Mama itace wannan Bara’atu... Daula ba murya kawai takedashi irinta mahaifiyarmu ba, harta fuskarta irin tata ce.... Tambayar a nan shin munada alak’a da ita ne... Ko kuwa dai zallan kamanni ce...?”
Aunty B ta dube ‘yaruwar tata kana ta nunfasa tace “Daula ita kad’ai zata amsa mana wad’annan tambayoyi, a hankali zamu santa zamu San asalinta, ta nan zamu fahimci idan ita d’in tanada alak’a da Mahaifiyarmu....”
Jinjina mata kai Mamy tai kana tace “Haka ne...” Muryarta ne ya sark’e sakamakon sauraro hayaniyar Haule da tai daga tsakar gida tana fad’in a fitina sanar da ita uban da yace ai mata wasan k’wallon kwando da yaranta... Baba Alhaji na biyeda ita...

Babu shiri Aunty Bara’atu da Mamy suka dubi juna... Aunty B tace “Mamy meke faruwa...?”
Girgiza kai Mamy tai kana tace “Wllhi ban sani ba, amma kaman muryar Hajiya Haule nakeji... Muje muji ko menene...”
A d’ari suka nufo tsakar gidan saidai yanayin da sukaga Hajiya Haule ciki saida ya firgitasu, fuskarta gaba d’ai kwalliyar ta cab’e, janbaki ya koma kumayi gazal dasu mascara sun zagwanyo zuwa kumatu, tamkar wata dodanniya haka Haule ta juya, ga uwar d’amara data sha uwa zata tashe, uwa Uba ga d’aurin zaninta daidai k’wanjinta ya tsaya saikace mai haye wuta, ga sumarta da sunan anyi retouching dik na shirin biki sun mimmik’e wasu na kallon gabas wasu na kallon yamma saikace wani k’aho....Sai tsima take tana tsalle, Lami kanta da taga Haule a haka saida taja birki ta koma da baya tana dafe k’irji, dan da ace a hanya taci karo da Haule a haka shakka babu zatace gamo tai... Shiko Baba Alhaji sai wani muzurai yake yana sab’a babbar riga....

Mamy da tsananin mamaki take duban Hajiya Haule kana tace “Hajiya lafiya na ganki haka... Meke faruwa ne....?”

Hajiya na jijjiga take fad’in “Inafah lafiya Mariya... Mijinki ya mana wasan k’wallon kwando da yara wacce aka baiwa d’ansa daban wacce ya aura masa daban....”
Mamy da Aunty Bara’atu suka dubi juna....
Girgiza kai Mamy tai “Ban gane ba Hajiya Haule... Mai kike nufi....?”
Duban mijinta dake tsaye bayanta gaho tai kana tace “Kai mata bayani yanda zata fahimta kai mata bayanin yanda k’aninka ya raina mana hankali, mun baiwa d’ansa auren Sahariyya ya aura masa Naja’atu... Toh bazata saku ba dole a warware wannan aure a maida kan Sahariyya....”
Sai sannan Aunty Bara’atu ta murmusa kana ya matso kusan Haule.... Murmushi bai bar saman fuskarta ba take fad’in “Da gaske Hajiya Haule... Toh amma meye abin tashin hankali, naga dai Sahariyya da Naja’atu duk abu guda ne... Maiyasa kuka dage sai Sahariyya ce zata auri Ma’aruf... Shin kunada wata b’oyeyyiyar al’amari ne da bamu sani ba Haule....? Ko kuwa dai akwai wani abinda kuke shiryawa ne...?”

Huci Haule taci gaba da yi tana rarraba idanu lokaci guda take fad’in “Ke Bara’atu ki shiga taitayinki, babu ruwanki a wannan magana, ‘ya’ya dai ‘ya’yana ne kuma kuma mu ba Naja’atu muka baiwa Ma’aruf ba, Sahariyya muka bada kuma dole, ya zama wajibi a warware wannan auren yanzu ba sai ‘yan d’aurin aure Sun gama watsewa ba a d’aura aure da Sahariyya kowa ya shaida....”
Kaman daga sama suka jiyo muryar Mamani tana fad’in “Auren da Allah ya riga ya k’ulla babu d’an adam d’in da ya isa ya warware... Kuma dama su munafukai ranan jin kunya na nan na zuwa masu....!!”

Gaba d’ai juyawa sukai suna duban Mamani dake k’arasowa Abbah na tafe gefenta, idanunsa k’yam kan d’an uwansa Baba Alhaji yanai masa wani irin duba da idanunsa da suka kad’a sukai jazir...
Haba nan fah Haule ta soma shan jinin jikinta... K’ak’aro murmushin yak’e tai kana tace “Au Mamani baki fahimta bane...”
“Sakani na fahimta Haulatu...” Mamani tace tana mai kuma k’arasowa...
Haule taci gaba da fad’in “Wato abinda faruwa jikarki Sahariyya an yaudareta an maida sadakinta na k’anwarta Naja’atu...”
Murmusawa Mamani tai kana tace “Kinyi kuskure Haule, sadaki dai tabbas na k’anwar Sahariyya ya juya amma kuma ba jininki ba....”
Tashin hankali da ba’a saka masa rana.... Da tsananin mamaki Haule ke duban Mamani, murmushin da yafi kama da yak’e ta soma yi... “Kin mance ai Naja’atu jinina ne... Kuma itace k’anwaga Sahariyya....”
Baba Alhaji da hantar cikinsa ke tsananin kad’awa duban mahaifiyar tasa yai kana yace “Mamani Wai meke faruwa ne... Meke faruwa ne a nan... Kai Manu mai ka aikata da ‘ya’yana..? Waye ya baka izinin canza auren yarana...?” Ya k’arashe yana mai isa gaban Abbah cikeda tsananin huci... Shima Abban huci yake yana duban cikin idon d’anuwan nasa, he can’t believe d’anuwansa na jini zai aika masa irin wannan mummunan aiki.... Cikin karaji Abbah yake fad’in “Ka bani mamaki... Ka bani mamaki Yaya.... Shin har kanada k’arfin halin kallon cikin idona....?”

Jikin Baba Alhaji ya soma sanyi yayinda Haule da Lami suka soma duban juna, hawaye masu tsananin d’umi suka shiga gangarowa daga idanun Abbah sanda yaci gaba da fad’in “For years.... Shekara da shekaru kana kallon yanda nida matata muke shan wahala, kana ganin yanda mahaifiyar tasha wahala amma sabida son zuciya irin naka ka zab’i Kaga mun rayu cikin k’unci da d’aurawa junanmu laifi... Yaya ka fad’a min shin mai na tab’a yi maka da tsanani...? Shin k’oyayyar da kake min har yakai ka rabani da gudan jinina....? Shin wane irin zalunci ne wannan....?”

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Kalaman da illahirin mutanen wajen suke nanatawa kenan a zuciyarsu, sauk’in abu mutanen dake wajen duk na gida ne Gwaggwanyen Kazaure ne saiko Aunty Daula dake d’aki da alama bata ma San wainar da ake toyawa ba, tana dai jiyo kaman hatsaniya daga waje amma da shike ta kasance mace maras shiga hurumin da bai shafeta ba shiyasa ma bata fito ba.....
Su Haule da Lami kaw da za’a tsaga jikinsu tabbas da zai wuya a sami jini sabida yanda suka daskare sakamakon jiyo irin kalaman dake fitowa daga bakin Abbah... Kenan hakan na nufin asirinsu ne ya tonu ko kuwa....?
A daburce Baba Alhaji ya soma fad’in “Kai Usmanu yanzu rashin kunyar naka har ya kai ka dubi tsaban idanuna ka dinga jifata da sharruka irin wannan had’ida wasu kalamai marassa kan gado bayan cin amanan da ka min na canza auren yarana da kai.... Ni ban ma san mai kake nufi da wad’annan kalaman naka ba...!!” Kan ya kai aya Mamani dake zuban hawaye ta katsesa da fad’in “K’arya kake ka sani.... Kasan komai Alhaji Alk’ali bazai maka sharri ba... Kaida wad’annan azzalumai biyu ku kukai sanadiyar rabuwarmu da Ma’aruf...” Tai maganar tana nuna Hajiya Haule da Aunty Lami dake faman rakub’e rakub’e tana raba idanu kaman mage a ruwan zafi, ga wane irin gumi dake faman keto mata....

Mamy data tari zancen kaman wani sauk’an guduma kasa fahimtar komai tai sai bin mutanen dake wajen da idanu da take, take kanta ya shiga huya mata, ita bama ta fahimci abindake wakana ba...

Mamani taci gaba da fad’in “Ku sani Allah baya bacci kuma wasu sirrika dik tilin k’asan da aka aza masu toh fah ran dik Allah yaso bayyanasu toh da kansu zasu tono kansu... Alk’ali ka bani kunya kaci amanan ‘yanuwantaka... Ka biyewa sharrin wad’annan shed’anun matan ka cutarda ahalinka shin har kanada k’warin gwiwar ci gaba da rayuwa cikin ahalinka... Shin har kana iya bud’e idanu ka dubi d’an uwanka da iyalinsa tsawon shekarun nan.... Shin wane irin mugun zuciya ne da muguwar gaba had’ida mummunar k’eta zaisa ka aikata irin wannan bak’in laifi mai tarin zunubi... Shin ta yaya zaku raba k’aramin yaro d’an shekaru uku wanda baida hakkin kowa da iyayensa.... Shin da wasu idanu ka soma duban Ma’aruf a lokacinda Allah ya dawo mana dashi.... Shin dukanku da kuka salwantar dashi da wasu idanu kuka soma dubansa....? Ku fad’a min da wasu idanu kuka soma duban jikana Ma’aruf..!!!??” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana k’ok’arin duk’awa daidai nan Sameer da shigowarsa kenan tareda Engr yayo rakiyawa Engr dan ya gaisar dasu Mamy suka tarar da wannan iftila’i... Cikin sauri Sameer ya taro Mamani Engr na taimaka masa... Cikin sauri Abbah ya mik’a masu kujeran tsuguno na zaman mata a kitchen dake a tsakar gidan suka zaunar da Dattijuwar wacce basai ance maka ba zuciyarta ta matuk’ar raunana....
Sameer da ya tuni ya tsinci abubuwa da dama da Mamani Ke fad’i take idanunsa suka kad’a sukai jazir, dan sai yanzu yake fahimtar wasu abubuwan.... Sai yanzu ne wasu abubuwan suke dawowa kwanyarsa.....Sai yanzu yake samu amsoshin wasu tambayoyi da suka jima suna Yawo a kwanyarsa.... Take idanunsa suka kuma kad’awa suka rine, fatar jikinsa ta juye ta koma jajazir haka nan duk wata k’ofa da gashi ya ratsa cikin jikinsa saida suka mimmik’e ya d’ago yana dubansu d’aya bayan d’aya, gaban Baba Alhaji ya k’arasa sanda hawaye mai tsananin zafi ta ganagro masa, lokaci guda yake duban Baba Alhaji dake faman huci irinta mai borin kunya, cikin wata irin murya mai cikeda tsoro da kad’a zuciyar azzalumai yake furta “Duk abubuwan da naji da gaske ne.... Ku kuka rabani da iyayena da dangi na...? Kuka jefa rayuwar mahaifiyata cikin garari.... Is it true...?!!!” Ya k’arashe yana mai duban cikin idanun Baba Alhaji hawayen k’unan rai har suna rige rigen zubowa daga idanunsa da suka kad’a sukai jazir....
Daidai lokacin Mamy dake takowa gaban Haule da Lami cikin yanayi mai ban tausayi, ta dubi Lami ta dubi Haule tana tina yanda ta rik’i Lami tamkar k’anwa a gareta ba kishiya ba... Lokaci guda take furta “‘Yan uwa na d’aukeku... Ban tab’a d’aukanku da wata muguwar nufi ba... Allah Shi ne shaidata.... Lami... Haule shin kuka rabani da Ma’aruf....? Ku bud’e baki ku fad’a min.... Ku bud’e bakunanku ku sanar dani dalilinku na aikata haka a gareni....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Mamani ce ta kuma mik’ewa da k’yar cikeda tausayin Mamy ta isa gareta ta kamo hannayenta tana mai furta “K’warai Mariya wad’annan azzalumai su suka rabaki da gudan jininki... Su suka nisantamu da Ma’aruf, suka jefa gaba tsakaninmu suka sa muka d’aura miki laifin da bakiji ba baki gani ba bayan mun mance kece mahaifiyarsa da ganganci bazaki tab’a salwantar da gudan jininki ba sabida duk k’aunar da zamu nuna masa a bayanki ne... Mariya ki yafeni, ki yafe min duk wasu abubuwan da na miki keda ‘ya’yanki.... Ku yafeni Mariya.. Hak’ik’a yau d’in bazan iya duban cikin idanunki ba... Ked’in kin cika matar kirki, uwa ta gari kuma abokiyar zama ta kwarai sannan sirika wacce ko wace uwar miji zatai mafarkin samu, Mariya ki yafeni....!!”Ta k’arashe cikin tsananin kuka....
Lokaci guda Mamy dake hawaye sosai ta d’agota, bata iya cewa komai ba sai rungume Mamani da tai su duka biyun kuka suke sosai....

Haule dake faman yatsine yatsinen fuska tana kallon wannan drama a cewarta, shewarta ne had’ida rangad’a gud’a ya dawo da hankalin katafarin jama’an dake wajen.... Gaba d’aya duban Haule suke tamkar sabuwar kamun hauka lokaci guda Haule ta soma fad’in “Munji mu d’in maciya amana ne... Munji mud’in azzalumai ne.... Amma dik muguntarmu da makircinmu a bayan AMINIYAR SIRRI muke.....!!!!”

Da tsananin mamaki suke kuma dubanta... Lokaci guda Haule Ke takowa ta k’araso gaban Mamy... Tana wani murmushi had’ida jijjiga take fad’in “Mariya kenan.... Kin zaci mu muka rabaki da d’anki tsawon shekarun nan koh....? Toh a tinaninki zamu cika wad’annan burika namu babu taimakon AMINIYAR SIRRI NE....?”

Wane irin bugu k’irjin Aunty Bara’atu yai lokaci guda.... DUMBA sunan da yazo zuciyarta kenan

Cikin tsananin rud’ani Mamy tace “Wacece AMINIYAR SIRRI...?”

Haule ta kuma murmusawa kana tace “Kin fimu kusanci da ita....!!!”

Da tsananin mamaki Mamy ke duban Haule, lokaci guda hawayen dake idanunta taji sun k’afe... Tsananin hucinta ya k’aru “Haule kina nufin kice DUMBA itace ta taimaka maku kuka salwantar

Please Login or Register in order to submit comment