Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d’awainiyarta amma wllhi badai ni ba kinji na rantse bazanyi ba...”
Hajiya ta kafeta da idanu had’ida yin k’wafa, ta dawoda dubantaga Najah wanda a nan take tunanin samun sauk’i...
Tab’e baki Naja’atu ma tai tace “Wllhi nima banzayi ba saidai tayi tsutsa....” Tana ida fad’in haka ta fice abinta...
Sahariyya kuwa gyara kwanciyarta tai ta ci gaba da chatting d’inta...
A dole Hajiya ta d’auki Kausar ta nufi bayi da ita tayo mata wanka ta shiryata gashi Raiha ta sabarwa yarinyar da goyo haka Hajiya ta sab’ata ta nufi kitchen k’arasa dafa abinci don bazata iya barin yaranta su Sahariyya da yunwa ba.....

***

Washe gari suna breakfast suna shek’ewa da dariya, Yesmin tace “Ai na fad’a miki cousin after everything I planned for bazai kuma duban yanda take ba, ita kanta bazata kuma fatan sake ganinshi ba, na tabbata by now ta tsaneshi ta tsani saninshi da tayi shiyasa nace miki ni nasan hanya mafi sauk’i da zamubi...”

Siyama ta kuma darawa kana tace “Kai cousin ai bansan kin iya makirci har haka ba na tabbata Ammi taji batun nan har kyauta sai tai miki...” Dariya suka kumayi a tare had’ida tafe hannaye daidai lokacinda Sameer ya fito cikin shirin fita aiki...
Yesmin ta gaidashi ya amsa babu yabo babu fallasa...
Siyama ta bishi da kallo don tun daren jiya ta lura tamkar wani abin na damunsa saidai sam bai sanar da ita ga abindake damunshi ba itama bataja maganan ba don yanzu gaba d’aya ya canza mata kaman ba Partner d’inta da suke sharing komai a baya ba, tun bayan sab’anin da suka samu Sameer ya canza mata sosai...
Ganin zai fice ya d’an sanyata bud’e murya tace “Partner breakfast fah...?”
A d’an kaikaice ya dubeta kana yace “No zanci a office I’m late already....”

D’an jim tai kana tace “Alright a dawo lafiya....”

Kai kurum ya jinjina mata had’ida k’ak’aro murmushi ya sakar mata kana ya fice...

Tinda ya doshi lab d’in gabansa ke matuk’ar fad’uwa yana tunanin abinda zai gani...
Koda ma’aikacin lab d’in ya mik’a masa zungureriyar takardan da k’yar ya iya sa hannu ya amsa...
Ya juyata yafi sau uku kafin ya soma k’ok’arin bud’ewa yana tunanin wannan takardar ka iya canza rayuwarsa ta har abada...
Da basmala saman bakinsa ya bud’e takardan ya ciro paper d’in dake linke ciki ya shiga warwarewa....
A hankali Sameer ya soma bin takardan yana karantawa daki daki...
Jiri ne yaji na neman kadashi sanda yayi araba da cewa yana d’aukeda jinin wannan bawan Allah kashi casa’in da tara cikin d’ari ma’ana da gaske Abbah shine mahaifinsa na asali....
Wasu irin zafafan hawaye suka shiga gangarowa Sameer wanda baisan na murna bane ko akasin haka....
Lokaci guda ya silale saman benci dake gefe a wajen hawaye naci gaba da gangaro masa.....



SameenaAleeyou 📚





*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*43*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Jiki a matuk’ar sanyaye Sameer ya mik’e ya nufi d’akin da aka kwantar da Abbah, Mamy na gefe saman abin sallah da alama sallar walha take shiko Abbah bacci yake domin kaw idnunsa a rufe suke....
Rakub’ewa Sameer yayi jikin k’ofar yana kallonsu sabbin hawaye na gangaro masa, ganin Abbah na k’ok’arin motsawa alamun zai farka ya sanyashi saurin komawa da baya yana mai rintse idanunsa masu zuban ruwa, wad’annan bayin Allah sune iyayensa, su sukai sanadiyan zuwansa duniya, sai yanzu yake fahimtar dlilan da sukasa yake jinsu matuk’a cikin zuciyarsa, sai yanzu yake fahimtar abubuwa da dama da yaji gameda wad’annan bayin Allah, a hankali ya linke takardan ya jefa cikin aljihunsa, Yana fitowa ne ya kusa cin karo da wata matashiyar mace tana tafe tana kuka da alama d’akin da Abbah yake ta nufa...
Su duka biyu sukai tsaye suna duban juna sannan ko wannensu hawayene kwance saman kyakkyawar fuskokinsu, ko ba’ace maka ba kaga ‘yan uwan juna, kowa ya kasa baiwa d’an uwansa hanya sai kallon juna da suke su duka biyun, k’arasowar wata madaidaiciyar mace data d’an data ne ya sanya Sameer kaucewa yana k’ok’arin basu hanya, for the first time da Aunty B ta kuma yin tozali da fuskar nephew d’inta da ya b’ace shekaru talatin baya, k’irjinta yai wani irin yankewa ya fad’i, wannan fuskar Ma’aruf ce tsantsan take hangowa, har ya gifta ta gefensu ya wuce Aunty B bata daina binsa da kallo ba Zulfa’u kaw tuni ta shige cikin d’akin hankali tashe ta fad’a kan Mamy tana kuka...
Aunty B ta take mata baya jiki a sanyaye tana son tambayar Zulfa’u wanene mutumin data gansu tare...
Sosai Mamy ta rungume Zulfah tana hawaye itama a daidai lokacinda Abbah ya fito daga band’aki, tausayin d’iyarsa da matarsa ya rufesa...
Zulfah taci gaba da fad’in “Mamy ina Abbah na, Mamy ku yafeni dan Allah, wllhi banyi nufin tada hankulanku ba sai don k’ok’arin gujema faruwar hakan, Mamy dan Allah ku yafe mun..” Ta k’arashe cikin shesshek’ar kuka...
Daga bayanta take jiyo muryar Abbah yanda yake fad’in “Zulfa’u baki mana komai ba face biyayya idan akwai wanda zai rok’i gafararki toh kuwa babu shakka mune musamman ni mahaikinki, ni nayi sanadiyar jefa rayuwarki cikin k’unci, na tauye maki hakkinki da addinin musulunci ya baki, na tilasta maki kasancewa da mutumin da baki k’aunarsa mutumin da yaso salwantar da rayuwarki, ki yafeni Zulfa’u ku yafeni daga ke har mahaifiyarki....” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka...
Jiki a sanyaye Zulfa’u ta taso ta k’araso gaban mahaifinta ta duk’a k’asa, cikin hawaye take furta “Abbah ka daina neman gafarata domin kuwa ni baka min komai ba, aurena da Yaya Hafiz k’addarane hakan Allah ya hukunta sai ya faru a shafin rayuwata, Abbah na tabbata burinka ka sama min abokin rayuwa na k’warai ne shiyasa ka zab’ar min Ya Hafiz... Dan Allah Abbah ka daina bani hak’uri kaji Abbah nah...”
Abbah ya kifa kansa yana fidda hawaye masu tsananin ban tausayi...
Itama Mamyn hawaye ke ci gaba da kwararo mata, d’aya daga cikin ranakun da take mafarkin kasancewarsu a rayuwarta, yau ga mijinta ya gane kuskurensa a rayuwa, Allahu Akbar... Wannan shine INDA RAI DA RABO, Sam mai rai kada ya yanke tsammanin yankewar rahamar Ubangijinsa domin shi d’in mai canza al’amra ne a duk sanda yazo, Allahu kasa mu dace, Ameen thumma Ameen...
Hawayen da Aunty B ke mak’alewa ya shiga d’igo mata, sosai suka bata tausayi sanda Zulfa’u taci gaba da sanar da iyayenta irin taimakon da Aunty Bara’atu tai mata, tsawon lokacin nan da Hafiz ya saketa tana zaune hannun Aunty Bara’atu....
Hakan sosai ya faranta ran Abbah da Mamy sukaita jerowa Aunty B godiya tana nuna masu ai Zulfa’u d’iyartace don tai mata wannan ba komai bane hasalima ma kanta tayi....
Aunty Lami tai tsaye daga bakin k’ofa tana kallonsu, zuciyarta kaman zata fito ta fashe sabida tsananin takaici da k’unci, ala dole ta saita kanta ta shiga da sallama hannunta d’aukeda kwandon abinci....


A b’angaren Sameer kuwa kai tsaye office d’insu Shamsu ya wuce....
Daga yanda Shamsu ya gansa yasan babu lafiya, kamosa yai ya zaunar saman kujera mai kallon nasa yana tambayarsa ya akai.....

Sameer bai iya ce masa komai ba sai hawaye dake ci gaba da gangaro masa...
Shamsu ya d’an fuzar da iska kana ya mik’e ya dawo kusan Sameer d’in ya janyo wata kujerar ya zauna, dafa Sameer yai yana mai ci gaba da nazarinsa, murya a kwance yace “Sameer please talk to me.... Meke faruwa....?”
Har lokacin Sameer d’in bai iya ce masa komai ba sai zaro takardan gwajin DNA da yai ya damk’a hannun Shamsu hawaye masu d’umi suna ci gaba da gangaro masa...
Shamsu ya bisa da kallon mamaki kana ya shiga k’ok’arin warware takardan....
Tsananin Shock Shamsu ya tsinci kansa ciki, ya d’ago ya kuma duban Sameer wanda har lokacin kansa ke kife k’asa yana d’igan hawaye....
Da gaske dai wad’annan bayin Allah sune biological parents d’in Sameer, wannan shine ikon Allah, toh ya akai hakan ta kasance....? Ya akai tsawon shekarun nan basu sani ba, mai ya raba Sameer da iyayensa na asali..? Tambayoyin dake yawo a kwanyar Shamsu... Yana cikin tunanin ne ya jiyo muryar Sameer mai cikeda tsnanin rauni yana fad’in “Sune iyayena Shamsu, Alhaji Usman shine mahaifina.... Shamsu bansan mai nakeji ba a halin yanzu, shin jefar dani sukai ko kuwa kyautar dani sukai...?
Shin meye asalin labarina... Mecece gaskiyarta....? Shamsu I need to find out...” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Shamsu ya dafasa cikeda tausayawa, saida ya sauk’e ajiyan zuciya kana yace “Toh yanzu ta ina zaka fara abokina... Shin ka sanar da Abbah cewa shine mahaifinka, kaine d’ansu da ya b’ace...?”

D’ago rinannun idanunsa yai yana duban Shamsu kana ya girgiza kai yace “Not yet, ban sanar da kowa ba face kai, sannan bazan tunk’ari Alhaji Usman da batunba sai naje Kaduna na dawo, inada d’umbin tambayoyi da nakeson yima Mummy da Daddy...” Daga haka mik’ewa yayi yana mai furta “Zan wuce Kaduna yanzu In sha Allah...”

Shamsu ya mik’e cikin sauri ya take masa baya yana fad’in “Sameer are you sure you can drive...?” Yayi maganar cikeda kulawa...
K’ak’aro murmushi Sameer yai ya sakar masa kana ya jinjina kai a hankali yace “Kar ka damu abokina Insha Allah zan iya...”
Cikeda nuna damuwa Shamsu yace “Toh ko dai nai driving naka ne...?”
Nanma girgiza kai yai yana mai sakin murmushi yace “I’ll be fine Shamsu ka daina damuwa...”

Nannauyan ajiyan zuciya Shamsu ya sauk’e kana yace “Shikenan if you insist, drive safe abokina.....”
Sameer ya jinjina kai kafin suka soma sauk’owa daga benen..
Har wajen da ya aje motarsa Shamsu ya masa rakiya yana mai masa fatan sauk’a lafiya da samun nasara...

***

Idan kaga Hajiya a kwanaki biyun nan da babu Raihanah duk ta fice hayyacinta tayi wajaga wajaga, ‘ya’yanta Sahariyya da Naja’atu sam babu mai taimaka mata da aikin gida cikinsu, ga hidimar Kausar dake gabanta...
Tana zaune ta ida sanwar abincin rana ga Kausar da tun daren jiya ke kuka sabida tsananin zafin jikin da take fama dashi, da alama yarinyar batada lafiya, gaba d’aya Hajiya bata samu wadataccen barci ba ta tsaya jinyar Kausar, abin ya mata yawa kanta na neman zaucewa... Kaman wacce aka sinkaya haka ta mik’e ta sab’a Kausar a baya ta fice...
Bata zarce ko ina ba sai gidan Hafiz....
Tun bayan bikin sai yau Hajiya ta taka gidan Hafiz dukda cewa ita Sawwamar bata tab’a d’aukan k’afafu taje gaida sirakanta ba iyayen mijinta...
Hajiya bugun duniya tayi ba’a bud’e k’ofa ba ga Kausar dake sab’e a bayanta tana ci gaba da aikin kuka, sai faman jijjiga yarinyar take....
Bayan shud’ewar wasu mintoci taji ana k’ok’arin bud’e k’ofar don har ta cire rai baza’a bud’e ba ta soma neman mai adaidaita...
A yatsine Sawwama ke dubanta tana wani kanne idanu alamun tashinta kenan daga bacci....
Hajiya baki sake take duban Sawwama domin kaw babu sitirar kirki jikinta don sanye take cikin kayanta na bacci..
Ta kasa furta koda kalma guda sai duban Sawwama da take babu ko k’yafta idanu...
Banda watsa mata kallon wulak’anci Sawwama bata komai, ta lura da mamakin da ya kama Hajiya don haka ta kuma juya jikinta alamun ta kalleta da kyau kana tace “Lafiya...? Bashi ko Tara...?!” Yanda tai maganar cikeda isa da izza yasa Hajiya saurin saita kanta kana ta shiga wage baki tana yak’e tace “Baki shaidani bane...? Nice Hajiya mahaifiyar mijinki....”

Saida Sawwama ta kuma binta da wani wulak’antaccen kallon kana ta d’anyi gajeren dariya tace “Na ganeki mana, shiyasa nake tambayarki, bashi ko tara...? Idan kaw babu d’aya daga ciki uwar mai kikazo mana gida da asubahin fari.....?”

Gwiwoyin Hajiya suka sake tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi tace “Kodai baki lura bane ai gari ya waye tuntuni azahar muke hari...”
Nanma tsuka Sawwama tai tana wani juya idanu had’ida jijjiga ita kad’ai kana tace “Toh naji gari ya waye, yanzu dai ki sanar dani mai ya kawoki....”
Hajiya da k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi harara ta wurgawa Sawwama sanda ta saci kallonta taga wani gefen take duba, tana maido da dubanta ga Hajiya tai saurin saita kanta tanaci gaba da murmushin yak’e wanda bahaushe ke cewa tafi kuka ciwo...
“Aidai da kin bari mun shiga daga ciki, bai kamata matar aure ta lek’o har waje haka ba....”
Dakatar da ita Sawwama tai ta hanyar d’aga hannu kana tace “A’a a’a idan wa’azi kikeso maza ki tafi bakin kasuwa ko tasha ba’a nan ba, don na tabbata wa’azinki bazai karb’u a masallaci ba balle nace kije can ki haye mumbari.... Idan kuma sa ido ne ya kawoki toh ki wanke idanunki da kyau don kinada kallo bakiga komai ba tukun.....!” Ta k’arashe cikin salo na juya idanu...
Baki sake Hajiya ke kallon ikon Allah, kalan rashin mutuncin da bata tab’a gani ba tsawon rayuwarta...
K’arasowar Hafiz wajen ne yasa Hajiya saurin sadda kanta tana mai k’ok’arin saita kanta don bataso ya gano tsantsan tashin hankalin data fad’a, gwara tai k’ok’arin shanye wulak’ancin Sawwama da dai ace ta zama loser....
Yana shafa kai yake duban Hajiyar kana ya saci kallon Sawwama...
Tsuka Sawwama tai ta shige ciki abinta tana binsa da wawan kallo...
Hafiz tamkar wanda dodonsa ya gifta Sawwama na shigewa yai saurin k’arasowa ga Hajiya yana fad’in “Hajiya sannu da zuwa, ya kika tsaya daga waje, shigo daga ciki mana....” Ya k’arashe yana bata hanya...
Kallonsa kurum Hajiya keyi tana hango kalan rama da bak’i da yayi, da ace bataima d’an nata farin sani ba tabbas da tace canzashi akai...
Hankalin Hajiya idan yayi dubu ya tashi...
Tai saurin tare Hafiz da tambaya...
“Hafiz mai ya sameka ciwo ne kayi....?” Tai maganar cikeda tsoro da fargaba...
D’an shafa kansa yai had’ida k’ak’aro murmushi kana yace “A’a Hajiya lafiyata lau mu k’arasa ciki.....” Yai maganar yana mai k’ara sauri don kar Hajiya ta kuma jefo masa wata tambayar....

Da k’yar Hajiya Haule ke iya jan k’afafunta da suka mata mugun sanyi har Hafiz ya yaye labulen parlorn suka shige....
Sawwama na hakimce saman doguwar kujera mai d’aukan mutum uku, k’afafu d’aya bisa d’aya sai faman shafa wayarta take...
Cikeda d’ari Hajiya ta soma lalumar kujera zata zauna Hafiz na fad’in “Bismillah Hajiya zauna mana...”
Kaman mai tsoron kujeran haka take k’ok’arin zama....
Aiko Sawwama kaman jira take ta tari Hajiya da fad’in “A’a a’a ina zaki zauna.... Kinga sauk’a k’asan tile ba kowani shirgi ke d’ale min kujera ba....!” Hajiya ta saki baki tana jira taga hukuncin da Hafiz zai d’auka saima kauda kai gefe dataga yayi yana sosa k’eya...
Shikenan an shanye mata d’ah...
Duban Sawwama da kyau tai wannan karon domin kaw tazo wuya...
Da ‘yar yatsa Hajiya ke nunata kana tace “Amma ke dai bakida mutunci bakida kunya... Ni zaki duba ki wulak’anta in tsuguna in haifi mijinki ki wulak’antani... Kai kuma kana tsaye kana kallo ana min cin kashi baka kikkifawa ‘yar jakar uba mari ba... Toh wllhi kunyi kad’an daga kai har ita... Bokan naki ma yayi kad’an...”
Sawwama ta katseta da fad’in “Ki sake kirata maras kunya zan nuna miki rashin kunya tsirarta don na lura har yau baki tab’a ganin rashin kunya zindir d’inta ba mai sutura kike gani...”
Hajiya ta shiga zaro idanu waje hannaye dafe da k’irji har lokacin bakinta sake yake wai donma Kausar tayi bacci a bayanta...
“Allah....! Eh lallai ikon Allah.... Kai Hafiz saketa ka rubuta saki nace banso ta k’ara ko sakan guda a gidan nan....”

Hafiz ya dubi Sawwama dake faman aika masa harara kana ya maidoda dubansaga Hajiya yace “Hajiya gaskiya kiyi hak’uri bazan iya sakin matata ba gaskiya....”
Hajiya ta dafe k’irji tana fad’in “Na shiga uku ni Haule.... Hafizu ni nake baka umarni kana cewa bazakayi ba...?” Saiga hawaye na gangarowa daga idanun Hajiya..
Jinjina mata kai Hafiz yayi yace “K’warai kuwa Hajiya idan nabi naki bazan zauna da ko wata mace a duniya ba tinda bakida aiki sai datse min igiyoyin aurena gaskiya bazan saki matata ba...” Ya k’arashe yana hura hanci...
Hajiya batasan sanda ta shiga kwance goyon Kausar ba ta dangwala masu yarinyar gabansu tana fad’in “Ga d’iyarka sai kasan gidan uwar da zaka kaita amma bani ba... Shanyayyen banza da wofi... Ke kuma mu zuba nidake, har gaban bokan naki sai kin tafi kina kuka... Haule kikeji baki santa ba...!” Daga haka saita mayafinta tai ta fice tana huci yayinda Sawwama ta saki baki tana kallon Kausar dake kuka Hafiz d’inma Hajiya yabi da kallo har ta fice ga kukan Kausar da ya gauraye gidan gaba d’aya...
“Kaga ka tsayar da ita ka bata yarinyar nan don wllhi bazan iya raino ba kaima ka sani, ba a gidan nan ba wllhi....!” Daga haka sa kai tai ta shige d’aki kaman zata tashi sama...
Jiki a sanyaye Hafiz ya duk’a ya d’auki d’iyarsa ya aza a kafad’a yana jijjigata a hankali wasu irin tunani da wani abu mai kamada tausayi na yawo a kwanyarsa amma shi kansa bazai iya cewa ga abinda yakeji ba....

Har Hajiya ta shigo gida bata daina ashariya tana dannawa Sawwama da uwarta Magajiya tsinuwa ba... Sahariyya da Najah suka kalli juna lokaci guda suka shek’e da dariya don dama sunsan hakan zata faru idan dai Sawwama ce...
Hajiya ta wurga masu harara tana jifa da mayafinta take fad’in “Ku kuma fah uban mai ya baku dariya....?”
Suka kuma tintsirewa da dariya..
Hajiya tai k’wafa tace “Aikin banza aikin wofi kuma kuji na fad’a maku wllhi dole ku shiga kitchen ku girka abinci na gaji da bautan ‘ya’yan da ba gani suke ba... Duk fad’i tashin nan kanku nake amma yau wai Hafiz na gani aka d’ibemin albarka wanda tinda uwata ta haifeni ba’a tab’a min irinta ba ya kasa tab’uka komai.. Ohni Haule na shiga uku....!” Ta k’arashe tana mai kamo bakin zaninta tana share hawayen dake zubo mata...
Sahariyya ta tab’e baki ta shige d’aki tana fad’in “Wllhi idan za’a mutu a gidan nan bazanyi girki ba...”
Najah ma tab’e bakin tai tace “Nidai Allah ya gani karatu nake bazan iya aikatau d’in gidan nan ba...” Ta k’arashe tana mai ficewa waje...
Hajiya tabi d’iyoyin nata da kallo had’ida kurma sabon kuka tana furta ta shiga uku....

***

Suna zaune a lambun dake bayan d’akin Abbah a asibitin suna tartaunawa irinta uwa da d’iya wanda suka jima basuyi ba...
Mamy ta kuma kamo hannayen Zulfa’u tace “Kar ki damu In sha Allahu zamu ceto rayuwar Kausar daga hannun wad’annan azzalumai, duk yanda zamuyi In sha Allah rik’on Kausar zai dawo hannunmu kinji koh, ki kwantar da hankalinki...”
Zulfah ta k’ak’aro murmushi tana mai jinjina kai tace “Toh Mamyna... Allah ya k’addara faruwan hakan...”
Mamy ta amsa da Ameen a daidai lokacinda Aunty Lami ta k’araso wajen tana sakin murmushin da iyakacinta fatar baki....


SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*44*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




KADUNA

Sosai Mummy tasha jinin jikinta ganin yanayin Sameer d’in, gaba d’aya ta kasa sakin jiki dashi kaman ba Sameer d’inta ba... Ita gani tayima gaba d’aya ya canza, Sameer matashi mai yalwan fari’a da son jama’a duk ya koma wani iri, da wuya kaga murmushinsa a yanzu, haka nan magana idan ba ta zame masa dole ba bai yinta, da ace batai ma d’an nata farin sani ba sai tace canzasa akai, gaba d’aya tinda yazo zata iya k’irga maganan da ya shiga tsakaninsu....
Misalin k’arfe takwas na dare bayan an ida sallahn lisha ya shigo sashen Mummy, tuni ta fad’ad’a murmushinta dukda a b’angaren Sameer d’in ba haka bane....
“Son an shigo...” Tai maganar tana mai daidaita zamanta saman kujera...
Daga can kujeran gefe ya zauna ba tareda ya iya amsata ba sai jinjina mata kai da yai alamun eh...
Kafin Mummy ta kuma samun zarafin magana Sameer yace “Daddy fah...? I thought ya dawo gari....?” Yai maganar a tak’aice...
Mummy ta d’an dubeshi cikeda kulawa kana tace “Ya d’aga dawowarsa sai next week... Sameer wai dan Allah meke damunka... Talk to me Son...” Ta k’arashe murya cikeda damuwa...
D’ago rinannun idanunsa yai yana dubanta lokaci guda yanajin wani irin zafi da k’una cikin k’irjinsa, yana son Mummy sosai, soyayya irin wacce d’ah keyiwa mahaifiyarsa amma ace ba itace mahaifiyarsa ba bayan tsawon rayuwarsa kan hakan ya taso, ta tabbata Mummy ba itace mahaifiyarsa ba, shekaru talatin da d’oriya ita ya tashi ya gani matsayin mahaifiya a gareshi, sannan tai masa rik’o irin wanda bazai tab’a kawowa cewa ba itace ta haifeshi ba, gwanda Daddy ma wasu lokutan bai d’aukan al’amaransa da mahimmacin kaman yanda Mummy keyi....
K’uri ta masa tana jiran mai zaice ga k’irjinta dake tsananin bugawa ganin sam babu wasa a tattareda fuskarsa...
Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Mummy I’m going to ask you for the last time.... Mummy tell me, how am I related to you....?”
K’uri Hajiya Fatahiyya ta masa idanunta na k’ok’arin kawo ruwa kaman yanda na Sameer d’in suka ciko da ruwa....
A hankali Mummy ta taso ta dawo kujeran da Sameer ke zaune, kanta a k’asa tana goge hawayen da suka gangaro mata, a hankali ta kuma d’agowa tana dubanshi shid’inma ita yake duba....
“Sameer my Son..... Na sani duk daren dad’ewa rana irin wannan zata riskeni, ranan da zan bud’e baki na fad’a maka cewa banice na haifeka ba...!” Suk’e ajiyan zuciya Hajiya Fatahiyya tai kana taci gaba da fad’in “Amma ka sani badason raina zan sanar dakai labarinka ba saidon dole, sirrin dake rufe shekaru da dama ya tono kansa, zan sanar dakai komai amma sai kamin alk’awari zakacigaba da kasancewa d’ah a gareni....!” Ta k’arashe cikin murya irinta mai kuka wanda yasa Sameer sanda kansa k’asa zuciyarsa na tsananin masa rauni... Ya jima a haka yana jiyo sautin jan numfashin Mummy irinta mai kuka wanda hakan ke tsananin sosa masa zuciya kana yaci gaba da sauraro muryarta tana ci gaba da fad’in “Shekaru talatin baya ka zamto d’ah a garemu nida Daddynka.... A wancan lokacin ahekarunmu kusan biyar da aure nida Daddynka amma Allah bai bamu haihuwa ba, asalina mutuniyar Dutsimma ce ta jihar Katsina kaman yanda ka sani Dad d’inka mutumin asalin garin Gombe ne.... A wancan lokacin dangin mijina sunyita kwad’aitar masa cewa ya sake aure ko zai samu haihuwa amma baiyi hakan ba ko nace Allah bai k’addara ba, kullum ina cikin kuka da damuwa na rashin haihuwa alhali shi Dad d’inka sam bai nuna damuwansa akan rashin haihuwata saidaima yaita k’arfafa min gwiwa yana sanar dani idan da rabo zamu samu gaba, sannan duk abinda kaga Allah ya hana bawansa yasan dalilinsa nayin hakan, da kalaman Dad d’inka masu tausasa zuciya nakan samu natsuwa, dukda cewa sam ban tsira hannun danginsa ba wajen gori habaici da maganganun marassa dad’inji... Ana haka kwatsam watarana mahaifinka ya samu aiki garin Dutse ta jihar Jigawa, wannan shine dalilin da yasa na sami sauk’i daga tsangwaman dangin miji, muka tattara muka dawo garin Dutse da zama ba tareda mijina yayiwa danginsa sallama ba domin kuwa tinda yak’i bin shawarinsu cewa ya sake aure duk sai suka juya masa baya, babu mai shiga hidimarmu sannan babu mai gayyatarmu hidimarsa, sosai abin yayiwa Dad d’inka zafi, mahaifansa duk sun rasu balle ya masu sallama saiko dangi wad’anda suke ‘yan uba......” Hajiya Fatahiyya ta d’anja fasali kafin taci gaba da fad’in “A shekararmu ta biyu a garin Dutse kazo cikin rayuwarmu, wanda ka kasance fitilar da ya haskaka mana rayuwa, mafarin farin cikinmu snnan mabud’in alkhairanmu....” K’walla suka ci gaba da gangarowa Hajiya Fatahiyya sanda taci gaba da fad’in “Dumba....!” Sai ta kuma jan fasali tana duban Sameer d’in wanda shima ita yake duba....
Mummy ta sadda kanta k’asa a hankali tana goge hawayenta kana taci gaba da fad’in “Wata rana Dumba tazo dakai rik’e a hannunta... Kanata kuka kana ambaton Mamynka, lallashin duniya Dumba tai maka kak’iyin shiru, niko ina daga window ina hango dramarku da Dumba, tausayin k’aramin yaron ya kamani sosai, na shiga d’aki yanda nake ajiyan biscuit da alawa na sadaka ma yara don d’abi’atace tuntuni tausayin yara k’anana da kyautata masu, na d’auko maka biscuit guda na bud’e na baka, tuni ka amsa kana ci ka saki hannun Dumba ka kamo hannuna ka kwanta cikin jikina kana cin biscuit d’inka har bacci yayi gaba dakai kana kwance cikin jikina, Dumba ta sami daman tashi ta gudanar da ayyukanta domin fir kukanka ya hanata sakat....”
Cikin rawar murya Sameer ya katse Mummy da fad’in “Wacece Dumba...? Meye alak’ata da ita...?” Yai maganar hawaye na gangaro masa...
Sauk’e ajiyan zuciya Mummy tai kana taci gaba da fad’in “Zakaji komai In sha Allah Sameer...” Lokaci guda taci gaba da fad’in “Na d’aukeka na kaika bisa gado na bayan kayi baccin, na zauna daga gefe ina kallon kyakkyawar fuskarka data cika da tsoro alamun wani babban al’amari ya matuk’ar firgitaka dukda k’aranci na shekarunka...
Sanda Dumba ta ida ayyukanta nan take ce min zata d’aukeka ku tafi... Gaba d’aya Dumba ban gane mata ba a wannan ranan don da alama cikin tashin hankali take itama...
Na tsareta da idanu kana na jeho mata tambaya... Dumba shin ina kika samo yaro...?
Dumba ta shiga rarraba

Please Login or Register in order to submit comment