Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya watsar... Ta k’araso tana mik’a had’ida hamma alamun har yanzu akwai bacci a idanunta... Gefe dashi ta zauna had’ida kwantar da kanta cikin jikinsa, cikin murya irinta wanda bacci bai ida sakesa ba Muhibbah Ke fad’in “Excellency na ashe ka dawo, inacan inata bacci I didn’t expect you to be home this early, na zaci meeting d’inku da party chairman yau ne...!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin hamma... Jin ko gizau bai kulata ba ya sanyata saurin d’agowa tana dubansa, kasancewar kansa a kife yake yasa bata fahimci halinda fuskar nasa Ke ciki ba saidai ta hangi takardan dake hannunsa wanda ya kifa masa idanu, bata kawo komai ba don a zatonta batada alak’a da takardan....
Murmusawa ta d’anyi tasan dik gajiya Ke damunsa tinda mijin nata bai samun wane isasshen hutu da lokacin kansa sai na mutane... A hankali ta kuma kai hannayenta saman kafad’arsa tamkar mai massage... Cikin salo na kashe murya take fad’in “Excellency na baka son hutu... Waima tsaya, have you eaten..? Should I bring you something to eat...?”
Cikin wane irin razananniyar murya yace da ita “Get your hands off me...!”
Muhibbah data nemi baccin idanunta ta rasa a zabure ta mik’e tana dubansa cikeda tsoro....

Tai far da idanu “Excellency na mai kuma ya faru.... Ko wani ne waje ya b’ata maka rai...?” Ta k’arashe tana zaro manyan idanunta.... Bata ida razana ba saida ya d’ago fuska, nan ta hango tsananin b’acin Rai dake kwance cikin idanunsa... K’irjinta ya shiga bugawa ta soma tinanin kardai dubunta ne ya cika Engr ya san tana shan drugs... Toh amma she’s been very careful bata basa wani k’ofa da zai fahimci hakan ba tinda shi bama mazauni bane, Toh kodai yasan itada k’awayenta safaran miyagun k’wayoyi shine sana’arsu... Wata zuciya tace kai da zai sani da tuni ya Sani k’ila dai wani abin ne daban....
Muryarsa ne ya kuma dawowa da ita daga duniyar tinaninda ta tafi...
“Why did you do that...? How dare you lie to my face...?!” Ya k’arashe cikin wata irin murya mai razanarwa yayinda Muhibbah ta shiga willi willi da idanu k’irjinta naci gaba da bugu.....


SameenaAleeyou📚



*INDA RAI*
_................DA RABO


*94*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





Take ta soma rau-rau da idanu tamkar mai shirin kuka, lokaci guda take furta “Haba Excellency na wani abin nayi ne... Kodai wani ne ya b’ata maka rai wajen taro....?”
Tsaye ya mik’e yana dubanta sosai kana ya mik’a mata takardan dake hannunsa...
Gaban Muhibbah yai wani irin yankewa ya fad’i, toh wannan kuma takardan minene...? Ta tambayi kanta, ta kuma d’agowa tana dubansa, gani tai ya tsume sosai babu alamun wasa a tattare dashi, ga idanunsa da suka kad’a sosai alamun b’acin rai...
Ta k’ak’aro murmushin da tafi kama da yak’e “Excellency na wannan kuma na menene...?”
“Ki karb’a ki karanta sai kimin bayanin dalilin da ya sakaki sikata abinda kika aikata, and don’t you dare lie to me....!”
‘Yan hanjinta suka kuma kad’awa gashi ya tsareta da idanunsan nan masu firgita marassa gaskiya...
“Ki karb’a nace..!!!” Ya kuma fad’i cikin daka tsawa Wannan karon...

Jiki har na rawa Muhibbah ta amshi takardan ta soma karantawa, k’irjinta na bugun tara-tara... Wato Akram tona masu asiri yai wajen Engr, lallai tayi wauta data yarda Akram can betray Engr... Jujjyya takardan ta shigayi tana fad’in “Excellencyna ban fahimci komai ba fah ni... What’s all this...?” Ta k’arashe cikin murya mai kalan tausai...
Girgiza kai yai kad’an yana dubanta kana yace a hankali“The nerve...! Har kinada k’arfin gwiwar k’aryata abinda kika karanta yanzu... So tell me where’s Akram... Since you’re his ally na tabbata kinada masaniyar yanda ya tafi fad’a min ina yake....!”
Muhibbah ta kuma turo baki kana tace “Ni dai wllhi bansan yanda yake ba... I have no idea....”
Engr ya kuma jinjina kai kana yaci gaba da fad’in “So, are you happy now...? Kina farin ciki tinda kin lalata auren mijinki....? Fad’a min kina farin ciki da hakan...?” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu...
Yatsina fuska tai kana tace “Toh mai kake tinani Excellency na... Na zauna na zuba idanu ka kawo min wata mata cikin gidan nan, kaima kasan da nace maka na amince dan banida option ne, kuma da na fahimci kunyi tarayya da Akram wajen sonta sai nai amfani da wannan damar, haba Excellency na, wannan yarinyar ba class d’inka bace... How in the world ma zaka soma neman aure kana takara da yaronka... Ai ni taimakon ka ma nai na rabaku cikin salama, Kaga ‘yan adawanka na siyasa bazasu sami abin tsegumi ba...”
Tsawan da ya daka mata ya sanyata had’iye sauran maganganun nata... Ya kuma takowa gabanta kad’an kana yace “Don’t you dare talk about her like that ever again, wannan ya zama gargad’i na k’arshe... Don’t push me to the wall Muhibbah....!” Ya k’arashe yana mai rab’awa ta gefenta ya nufi bathroom da niyyan d’auro alwala....
Muhibbah ta juya idanu had’ida yin jifa da takardan, a fili taja wani uban dogon tsaki kana ta tintsire da dariya tace “Ko a yanzu dai ni ce da riba tinda baka aureta ba batun auren yabi ta shanun sarki... Ma’aruf kenan, ai gidan duniyar nan baka da mata sai ni Muhibbah...!” Ta kuma tintsirewa da dariya kana ta kad’a k’afarta ta fice tana wani juya jiki take fad’i a hankali... “Idan ka matsu dani ka biyoni har b’angarena...”

***

Washe gari kaman yanda suka shirya had’uwa gaba d’aya gidan babbar yayarsu Abidah hakan ce ta kasance, koda Aunty Bara’atu takaimasu Zulfah labarin abubuwan da suka faru a jiya d’aurin auren nasu ba k’aramin mamaki abin ya basu ba, Aunty Bara’atu ta sanar dasu komai dik abubuwan dasu Haule suka jima suna k’ullawa da yanda sukaita warwarewa da sirrikan da suka bayyana a jiyan, saidai bata sanar da Zulfa’u cewa aurenta ya tashi daga kan Akram ya koma kan uban gidansa kuma d’an uwanta ba, mamaki da al’ajabi yaita kamasu, Nabilah ta kad’a kai yafi abinda yafi kana tace “Wllhi Aunty ni dama na jima da karantar matan nan mugayen munafukai ne, Ke kiga Aunty Lami d’in nan yanda take kaffa kaffa da Mamy dama nasan naci na ciki mugayen banza azzalumai...”
Zulfah ta d’an harereta tace “Ke kuma ya isa haka kafin ki fara...”
Aunty B tace “Batta ta fad’i cikinta ai ba k’azafi aka masu ba... Kunga ku tashi mu shirya yanzu his Excellency zai turo motoci a kwashemu mu tafi can gidan Ammah (Ya Abidah)...”
Nabilah tai far da idanu tace “Kai ashe dai munada RABON shiga gidan gwamnati... Ayyye mun zama k’annen his Excellency....!”
Atika ta mik’a mata hannu suka tafe tace “Fad’i dai ki saka fad’i...” Gaba d’aya darawa sukai kana Aunty B ta kuma duban Atika tace su had’e kayan Zulfa’u waje d’aya dan daga can bazata dawo nan ba gidanta za’a wuce da ita... Atika tace “An gama Aunty...”
Zulfah dai har yanzu abin mamaki yaketa bata, ashe dai bawan Allahn nan jini suka had’a dashi shisa tinda ya fito siyasa taji bata tab’a cin karo da d’an siyasan dake matuk’ar bugeta ba kaman shi dikda cewa alkhairansa ga Al’umma ne yasa ya zamto gwaninta a fagen siyasa ashe dai harda jini suka had’a, Allah sarki wannan shine ikon Allah, Kullum tana burin ganinshi ido da ido sai gashi yanzu zata ganshi a arha tinda ya zamto d’an uwanta, in sha Allahu kaw sai ta bashi labarin ita babbar fan d’insa ce d’aya daga cikin magoya bayansa... Tana jin Aunty Bara’atu da Atika na magana k’us k’us batabi takansu ba ta mik’e ta nufi bathroom da niyyan d’auro alwala kafin su shige dan ita mace ce mai yawan zama cikin alwala muddin tana cikin tsarki...
A b’angaren Nabilah ma har yanzu abin al’ajabi yake bata jin cewa Aunt d’in Khalid matar Babansa k’anwar mahaifiyarsu ce, lallai wannnan shine ikon Allah mai gudanar da Al’amransa yanda yaso, bata tab’a zaton hakan mai yuwuwa bane saidai tabbas ba’a mamaki da ikon Allah domin kaw shid’in ne mai cikakken iko akan komai.... Kasancewar jarabawa suke shisa nata k’awayen babu ko k’wara harta Yusrah ma ta tafi da safe sunyi dasu Safwan zasu shiga tutorial da safen, sauk’in abin ma ita nan gidan Aunty Bara’atun zata dawo tinda ba yanzu zasu tafi can Abujan ba sai ta gama jarabawarta, ga wannan al’amari kuma da ya b’ullo kai, tana ganin Khalid na kiranta tak’i d’agawa tasan zancen bazai wuce yace zaizo su tafi gidan Ammah tare bane dan haka tama k’i d’aga wayar nasa, tsaf tasan halinsa yanzu sai yaje yaita bata kunya gaban iyaye, maganin bari karma a fara bazata d’aga ba saidai su had’u can gidan Ammahn....

Bayan shud’ewan wasu mintoci kaw hamshak’iyar Jeep d’in ta faka k’ofan gidan Aunty Bara’atu driver na jiran fitowarsu, ita dai Zulfah ta kasa aminta kasa yarda cewa Atika bata b’oye mata wani abu, dan ta kula falli da murnan Atika yama ninka lokacin da akace an saka aurenta, gashi har yanzu basuji daga Akram ba amma ko a jikin Atika... Saima wani Farin ciki da annashuwa data lura ya k’aru mata, wata zuciyar tace tinda kikaga haka toh ko shakka babu Akram na cikin k’oshin lafiya, k’ila wasu sabgogin nasa suka sha gabansa, amma fah ace kayi Amarya abin da kamar wuya da mamaki ka kasa koda d’aga waya ka kirata ne... Ta k’arashe tinanin tana mai sauk’e ajiyan zuciya a daidai sanda motar ya paka... Atika itace a front seat yayinda Aunty B Zulfa’u da kuma Nabilah Ke zaune daga bayan motar... Zulfah ta d’aga idanu tana duban ginin gidan tana iya tinowa a shekarun baya tun tana k’arama sun tab’a zuwa da Mamy taga Mamy ta fito tana kuka shikenan kuma bata sake jin d’uriyar matar daga Mamy ba, Allah sarki ashe dai rana irin wannan na zuwa masu ranan da zasu dunk’ule waje guda... Tinaninta ya katse sanda taji Aunty Bara’atu tana fad’in su k’araso Hajja mai aikin Ammah na amana ta nufosu tanai masu lale lale baki har kunne ganin gidansu da ya mutu shekara da shekaru yau ya dawo cikin rayuwa, rayuwa mai cikeda tarin albarka... Atika ta janyo trolly d’in Zulfa’u ta nufi bayan Hajja dake fad’in suje ta nuna mata d’akin da zata ije jakar... Atika dai sai zanzali da falli take tana kuma jinjina lamarin Wai yau Zulfa’u ce ta zamto matar Engr Mutallab daga gidan Hafiz, lallai Allah ya isa mai jujjuya al’amara yanda yaso ya kuma ga daman su gudana... Tabbas mahuk’urci mawadaci, ita tana mata Farin cikin ta rabu da Hafiz ta samu Akram ashe fin Akram tama samu, wannan shine INDA RAI tofah akwai RABO..... Ji take tafi kowa farin ciki ma Zulfa’u k’awarta...Tuni ta soma hango Zulfah a Office d’in First Lady dan tasan Zulfah ta kusa bankwana da station d’insu...

Can suka taddasu Mamy su Aunty Daula, Aunty Daula tana ganin Nabilah ta tafi ta rungumeta tana fad’in ko ba’a ce mata ba ga ‘yar gidanta amaryar d’an gidanta Khalid... Tuni su Ijlaal ma suka nufosu suna rungumarsu one by one, kan kace mai Zulfa’u Sarkin kuka idanunta sun shiga k’ok’arin kawo ruwa, yau gasu da zuri’arsu gaba d’aya a tare... Nan fah d’aukacin mutanen dake wajen ma idaniyansu suka shiga zuban hawaye.... Yaya Abidah ta isa tsakiyan Nabilah da Zulfah, tana hawaye ta rungumesu gaba d’aya suma hawayen suke... Mamy, Aunty B da kuma Aunty D suka isa suka rungumesu gaba d’aya suma... Aunty B ta mik’e tana amsa wayan Sameer da alama sanar da ita yake zai biya ya d’auko Raihanah da Marliya dan su biyu ne basu a wajen saiko Engr Ma’aruf da nasa family d’in su Muhibbah da yaransa da har yanzu suma basu samu isowa ba...
Aunty Bara’atu tace “Sameer Sarkin aiki, kai har weekends d’inma bazaka huta ba....?”
Daga d’aya b’angaren Sameer yace “Aunty dole ce ta kama emergency aka samu kuma ni ake buk’ata a wajen...”
Aunty B tace “Allah dai ya dafa maku gaba d’aya, aikin naka is not easy... Kodashike taimakon Al’umma ne, Allah ya baka ladanka...”
Sameer ya amsada Ameen Aunty na... Ku bamu mintina kad’an gamu nan isowa in sha Allah...”
Aunty Bara’atu tace “Take your time shima babban Yayan naku har yanzu bai iso ba, k’ila wani uzurin ya rik’esa....”
Sameer yace “Alright zan kirashi naji...Kinsan Excellency mai hidima da jama’a ne sosai....”
Aunty B tace “Toh shikenan sai Kun iso, Allah ya tsare...”
Sameer ya asmada Ameen Aunty kana sukai sallama....

***
A can gida kaw har yanzu gaban Raihanah bai daina fad’uwa ba, gashi Mamani tin safe babu wanda ya sakata a idanu, itakam sosai ta damu da Mamani dikda abubuwan da suka faru, dan d’an zaman da tai gabanta ta kula Mamani mutuniyar kirkice in her own ways dikda cewa tanada nata hayyan mabanbanta, ko kusa bazata had’a zaman gaban Mamani da zaman da tai gaban Haule ba... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya tana duban rantsetsiyar doguwar rigar da Mamy ta bata tace ta saka, tasan dai can gidan Yayar Mamy zasu tinda yanzu maganan is all over babu wanda baisan Mamy sun had’eda zuri’ararsu gaba d’aya ba, amma koda wasa batasan cewa ita d’in matar aure bace har yanzu, auren ma yayansu Ma’aruf mijin da Yayarta Sahariyya was about to marry him....
Sosai rigar tai mata kyau ta zauna a jikinta d’as, Marliya ta tak’urata sai ta d’anyi kwalliya a fuskarta... Murmushi kawai Raihanah tai kana tace “Toh Wai a waye zanyi kwalliyan ne...?”
Marliya tace “Gidan biki fah zamu tafi, kika sani ko ki had’uda naki Prince Charming d’in mu kuma shan nik’i soon...” Ta k’arashe tana kashe mata idanu...
Harara Raihanah ta d’an aika mata kana ta girgiza kai tace “Ke koh... Zaki sani ne...”
Marliya ta kuma darawa tace “Eh dai naji....”
Gyara d’aurin kwalinta take gaban mirror lokaci guda take ci gaba da fad’in “Na kasa daina tinanin abubuwan da suke kan faruwa, Wai yau Mamy da family d’inta gaba d’aya a had’e waje guda.... Allah mai iko...”
Raihanah dake nad’e mayafin rigar akanta tace “Ikon Allah kenan Marliya, ya wuce gaban tinanin d’an adam... Mamy ta cancanci Farin ciki Bayan dik tulin k’alubalen data fuskanta a rayuwa, ita d’in tanada zuciya mai kyau , dole duk wani masoyinta yai mata Farin ciki....”
Marliya tace “Haka ne kam, Kinga tsaya na d’an shafa miki koda powder ce kawai kafin Ya Ma’aruf ya iso....”
Juya idanu kawai Raihanah tai had’ida girgiza kai kana tace “Wllhi Marliya kin faye fitina, Nabilah ce maganinki, Ana ganin itace mafad’aciya fad’arta batayi saida dalili, kece mai damunta da fitina, kija gefe ki nok’e kaman ba ke ba....”
Marliya ta tintsire da dariya tace “Allah sarki Addah Beels d’ina wllhi zanyi kewarta sosai...”
Raihanah ta murmusa a daidai lokacinda sukaji sallaman Yayansu Ma’aruf a k’ofa... Wani irin fad’uwan gaba Raihanah taji ya sauk’ar mata lokaci guda...

***

A can gidan Engr kaw bai sanar da Muhibbah yanda zasuje ba saidai ya umarceta data shirya yaran gaba d’aya dan duk tare zasu fita, ga wani kwalliya na musamman da mijin nata ya buga, saikace wani sabon ango, ta lura yanayin da yake ciki a yau d’in zata iya cewa bata tab’a ganinsa ciki ba tsawon rayuwarsu saiko lokutan data haifo masa yaransu, Toh what’s he up...? Ta tambayi kanta sanda ta hangosa na sauk’owa daga bene waya manne kunnensa... Zumbur ta mik’e gabanta na wani irin yankewa dan wani irin azabebben kyau ya mata ga k’warjininsa da ya kuma fitowa sosai, haka kurum taji hankalinta bai kwanta ba.....
Ya k’araso yana mai saka wayar a aljihu daidai sanda su Najma Irfaan da kuma Samha suka k’araso suna rungumesa suna fad’in “Daddy you look handsome..!” Ya d’auki Najma ya azata a kafad’a yayinda ya shafa kan Irfaan da Samha yace maza su shige Patrick ya bud’e masu mota....
Muhibbah ta raka yaran nata da muguwar kallo a cewarta munafunci ke sa suke nuna sunfi son ubansu sama da ita, bacin haka dik gayu da tasha basuce ta masu kyau ba sai Ubansu, munafukan banza kawai... Duban Engr ta d’an kumayi kana tace “Wai ina ne kam zamuje my Engr....?”
Ba tareda ya dubeta ba yace “It’s Sunday, after all... Idan munje zaki gani...” Daga haka sa kai yai ya shige Najma tana fad’in zata sha ice cream d’in cold stone...
Muhibbah dai tab’e baki tai kana tace a zuciyarta k’ila sabida weekend ne shiyasa zasu fita gaba d’aya da yaran tinda sun jima basu d’an fita haka ba kullum hidiman siyasa bai bari ya zauna, wata zuciyar kuma tace K’ila sabida misunderstanding d’in da kuka samu jiya ne kikai banza dashi shiyasa yau ya shirya maku fita to make it up to you... Ta wani murmusa ita kad’ai tana jin kanta, a hankali ta shiga buga kafad’anta tana fad’in “Ke d’in amanarsa ce dole dik yanda yakaiga fushi ya sauk’o ya baki hak’uri..!” Ta kuma murmusawa kafin ta d’au handbag da mayafinta saman sofa ta take masu baya...


SameenaAleeyou📚






*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*95*



*©️Sameena Aleeyou✍🏽*


Suna tafe cikin motar yake sanar da ita yanda zasuje da kuma dalilin zuwan nasu, mamaki da al’ajabi ya cika Muhibbah... Gyara zama ta d’anyi tana dubansa sosai, lokaci guda take furta “Anya kuwa Excellency na... ‘Yan uwanka fah kace...? Mai yasa tintini basu nemeka ba, sai yanzu da sukaga ka zama mai fad’i aji, Nidai inaga kud’inka suke kwad’ayi babu wani ‘yanuwankan nan....”
Wane irin duba da yake aika mata ya sanyata had’iye sauran maganganun nata.... Ta d’an muskuta tana yatsina fuska lokaci guda taci gaba da fad’in “Ni dai shawari nake baka ka bincika da kyau, Frauds sunyi yawa...!”
Ba don shid’in bai kasance daga cikin maza masu dukan mata ba tabbas da ya shasshafeta da mari masu kyau, sannan yaransu dake bayan motar baiso su d’ago wani abu, shisa ma yai mata shiru, amma kam duba guda zaka masa ka fahimci tsananin b’acin rai da maganganun Muhibbah ya jefasa ciki, ta yaya zai kawo mata wannan labari mai dad’in gaske da yaso surprising d’inta dashi ta karb’i zancen a haka... A matsayinta na matarsa abokiyar rayuwarsa, tsawon shekarun nan ya zaci zatafi kowa nuna Farin cikinta, ya zaci zata tayasa Farin ciki bayan tulin shekarun nan da yayi cikin duhun rashin sanin ina asalinsa... Tareda ita akaita gwagwarmaya lokacin da ‘yan adawa sukaso b’ata masa suna cewa baida asali wanda badon Allah ya kiyaye ba da maganan yai tasiri, amma dik Muhibbah ta mance wannan, ya yana sanar da ita mahaifiyarsa na raye kuma ya sameta amma tana cewa Allah sa ba ‘yan wanki bane... Bai iya furta mata komai ba sai murza tafin hannunsa a hankali da yake sabida tsananin b’acin rai....
Ta d’an saci kallonsa had’ida tab’e baki kad’an, ita dai dikda cewa ya sanar da ita tinaninsa da ya b’ace sanda yake k’arami ya dawo amma bata yarda wad’annan mutanen ba dukiyar mijinta suke bibiya ba dan haka kawai taji sam bata yarda dasu ba, tin kafin tayi ido hud’u dasu taji ta tsanesu sosai...

*****

A tare Marliya da Raihanah suka gaidashi, ya amsa idanunsa kan Raihanar, ta masa kyau sosai, rigar ta amsheta... Har saida yaji ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta, dikda cewa itad’in nata idanun a k’asa suke... Bud’e murya ya d’anyi kana yace “Kun shirya...?”
Suka jinjina kai a tare Marliya na fad’in “Eh mun shirya Yaya....”
Jinjina kai shima d’in yai kana yace “Alright kuje mota ku jiran barin duba Abbah Ina zuwa....”
Amsa mar sukai da toh kana yasa kai ya juya, sai sannan Raihanah ta d’ago ta dubesa sanda yake ficewa... Yau d’in shadda ce dakakkiyar wagambari mai ruwan sararin samaniya da akai mata d’inkin jampa jikinsa saiko hula zanna bukar mai kalan shud’i wato dark blue wanda ya dace da zarenda akai ado ma kayan dashi, yayi kyau matuk’a kaman wani sabon ango... Koda Sameer ya isa sashen Abbah bai tadda Abbah ba, dan rufe ya tadda sashen nasa, Toh Ina Abban ya tafi kuma ai yau d’in weekend ne....? Kasa samo amsar yai hakan ya sanyashi juyowa yana tinanin yanda Abbah ya tafi, daga nan sashen Mamani ya lek’a nan ma sammakal bata nan kaman yanda bak’in Kazaure ma dik sun tafi da alama wasu kuma suna b’angaren su Baffah Ado.... Ajiyan zuciya ya sauk’e a hankali kana ya nufo waje ya taddasu Raihanah, alamun bud’e mota da sukaji ya sanya Marliya saurin kaman marfin backseat ta shige abinta... Raihanah tai rau rau tana duban Marliya dake mata alama da ta shiga gaba.. Girgiza kai kurum tai dan ita yanzu ta gama gane Marliya neman magana ne da ita had’ida jin baki, haka nan ta kama marfin front seat d’in ta shige dik tana jinta wane iri... Itakam maiyasa dik sanda suka kasance tare take jin wannan yanayi...? Tambayar da ta tabbata bata da amsar sa, hakan sai ya tuna mata d’aukota daga islamiya da yai kwanakin baya, tana jin sanda ya daidaita saman driver’s seat bugun zuciyarta ya k’aru gaba d’aya a tak’ure take, Allah ya sani mugun nauyinsa takeji... Zata iya cewa har suka isa yanda zasuje a d’arare take... Tanajin sanda ya ida parking ya bud’e central lock, Marliya ta kama marfin motar ta fice yayinda itakam Raihanah ta shiga kiciniya da seatbelt dan sanda zasu wuce road safety ya umarceta ta d’aura seatbelt, gaba d’aya sai kokawan zame jikinta take daga cikin seatbelt d’in... Sameer yai mata k’uri yana duban yanda take kokawa da seatbelt... A hankali ya d’an rank’wafo had’ida kai hannu yana k’ok’arin cire mata, yanda fuskokinsu sukai dap da juna ya haifar masu da fad’uwan gaba mai tsanani, dan gaba d’ayansu bugun zuciyarsu saida ya k’aru.... Tai saurin janye fuskarta k’irjinta bai daina bugu ba, gashi ya kasa janye jikinsa saima k’ura mata idanu da yai abin har sai ya soma bata tsoro, maiyasa zai mata haka...? A iyaka saninta shid’in ba mutumin banza bane... Tana tsaka da tinanin taji ya mik’e ya daidaita zamansa saman nasa kujeran tamkar wanda ya tuno wani abin... Murya a hankali taji yana furta “Kina iya fita, be careful next time kar Ki had’a seatbelt da rigarki...”
Ita dai kai kurum ta jinjina masa dan har yanzu jikinta a mace yake, da k’yar ta iya ficewa daga cikin motar k’afafunta sai rawa suke tamkar wanda zasu gaza d’aukarta....
Shiko Sameer jingina cikin motar yai had’ida lumshe idanu... God! Wai yau shi Sameer ke jin wani abu gameda wata mace ba Siyama ba..? Ya d’an ware idanunsa kad’an yana mai murmusawa a hankali, shi kad’ai yasan zancen da yakeda zuciyarsa saiko mak’aginsa...A haka su Engr suka k’araso, Sameer yai saurin daidaita kansa kana shima ya fito daga motar tasa, kai tsaye wajensu ya nufa suna gaisawa, take Engr ya soma introducing family d’insa ma Sameer... Muhibbah dai da alama hankalinta dik bai wajen dan tin a mota Shamzy ta isheta da waya bata d’agawa saidai ta danna a silent... K’arshe Shamzy text ta turo mata cewa dik yanda za’ai su had’u anjima dan Oga Bash yace kaya masu yawa zasu fitar a satin da za’a shiga, so itama dole ana buk’atarta.... Rausayar da idanu kurum tai sanda ta ida karance sak’on, yanzu dik basa samun attention d’inta sosai tinda ta soma prioritizing zaman aurenta sama da business d’insu... She can’t afford to lose this millions dole dik yanda za’ai tasan wata hanyar da zasuke had’uwa dasu Shamzy su Bash a store d’in Bash na saida garin siminti a zahiri amma a bad’ini waje ne na hada hadan miyagun k’wayoyi...
Shi kansa Engr ya kula gaba d’aya mind d’in Muhibba was somewhere else amma baice mata komai ba saima jerawa da sukai shida Sameer suka nufi cikin gidan suna fira, Sameer d’aukeda d’iyar Engr k’arama... Basu kaiga main k’ofar shiga gidan ba Daddy da Khalid suka iso, hakan yasa Engr da Sameer dakatawa dan gaisawa dasu Daddyn.... Muhibbah dake tsaye daga can b’angaren da suka parking motarsu tana amsa waya lokaci ta ida wayar nata tana sanarda Shamzy cewa gidan biological parents d’in Engr sukazo dan ya sanar da ita dik abindake faruwa cikin mota saidai bai bata labarin auren nasa ba dan shima magana ne mai zaman kansa...

Muhibbah ta janyo hannun yaranta guda biyu suka nufi gidan sai wani yatsina fuska take tana mak’ale da hannayen yaranta, ko takan su Engr batabi ba.... Tana shiga cikin gidan Daula ta mik’e ta tarota tanai mata sannu da zuwa dashike sunsan juna, babu b’ata lokaci Daula ta shiga introducing Muhibbah masu Mamy su Ammah, su Zulfah dai suna daga can d’akin da aka sauk’i Zulfa’un, sun barbaje abinsu Atika

Please Login or Register in order to submit comment