Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya tana mai bige flour da ya b’ata mata jiki...
Cikin sauri Sameer ya kwab’e apron d’in dake d’aure jikinsa ya nufo parlor yana doka kiran Siyama...

Siyama dake kuka sosai rungume Mummy tai tana fad’in “Mummy tell me please abinda na gani ba gaskiya bane... Mummy Sameer bazai tab’a min haka ba... Pls Mummy kice min ba gaskiya bane...!!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka... Mummy Ke k’ok’arin lallashinta tana fad’in “Siyama just calm down please... Ki saurareni Siyama...” Inaa kuka kawai Siyama keyi kaman ranta zai fita.....Daidai sanda Sameer ya k’araso wajen, a hankali yaceda Mummy taje ta k’yalesa da Siyama... Mummy ta jinjina kai kana ta saki Siyama ta nufi kitchen wajen Raihanah da tsoro da tashin hankali sun gama dabaibayeta dan tuni hawaye sun soma sintiri saman fuskarta... Mummy ta isa ta rungumeta cikeda tausayawa tana lallashinta....

Sameer ya jima yana tsaye wajen yana duban yanda Siyama Ke cazgan kuka mai ban taisayi wanda har saida yaji can k’asar zuciyarsa cewa kaman bai kyauta mata ba, gaba d’aya tausayinta ya dabaibayesa... A hankali ya soma takowa yanda take had’ida rungumarta ta baya... Saidai cikin tsananin kuka ta k’waci jikinta tana fad’in “Don’t come near me... Just don’t touch me....!!How could you Sameer...!! Ta ya zaka min haka...? You are just like my father... You are even worse than him.... All men are the same, all of you are the same...”
“Siyamaaaa!!!!” Sameer ya daka mata tsawa da fad’in haka yana mai rik’e duka hannayenta biyu... Bata fasa dukan k’irjinsa tana fad’in ya saketa ba... Sameer kaw fad’i yake “Just listen to me Siyama... Ki saurareni nace...!!!”
Fincika tai Daga rik’on da yai mata da k’arfin gaske tana dubansa da idanunta masu zuban hawaye lokaci guda take furta “Mai zan saurara Sameer... Bayan dik abinda na gani da idanuna.... Partner... Partner... Please tell me, am I that easy to forget about.... Wannan shine alk’awarin da mukai ma juna...?”
Ta k’araso gabansa da sauri tana mai tallafo fuskarsa da dika hannayenta biyu take fad’in “Partner, I know I’ve wronged you...I know I’m not perfect... But I love you Sameer... I love you with all my heart and soul... Sameer I’m only human....sab’anin da muka samu baikai ka mance dani ko ka kawo wata cikin rayuwarmu ba... Sameer please look into my eyes and tell me dik abinda na gani ba gaskiya bane... Please kaji... Kaji Partner... Tell me ba gaskiya bane..” Ta shiga jinjina kai tana kuma goge hawayen lokaci guda ta shiga janyo hannunsa tana fad’in “Lets go to house... Nai maka alk’awarin bazan sake barinka ba, and zanyi dik abinda kake so... I’m ready to mend my ways... Pls Partner lets go back like before kaji...!!” Ta k’arashe tana kuma rik’o fuskarsa lokaci guda ta shiga janyo hannunsa tanaci gaba da fad’in su tafi gidansu... Saidai cak taji Sameer d’in ya k’ame ko motsawa baiyi... Ta juyo tana dubansa da watery eyes d’inta...
Lokaci guda Sameer d’in ke fad’in “Siyama just listen to me first... Rayuwar da mukai a baya bazamu sake maimaita irinta ba... A lot of things have changed Siyama..”
Cikin sauri ta katsesa da fad’in “No no Sameer please kace min ni kad’aice matarka please kaji partner...!!” Ta k’arashe tana kuma tallafo fuskarsa da duka hannayenta biyu...
Girgiza mata kai yake lokaci guda yake furta “Ba haka naso sanar dake ba... But yes Siyama a halin yanzu mata biyu Ke gareni ba ke kad’aice matata ba.... This is the truth Siyaam...!” Ya k’arashe yana mai kamo hannayenta...

Ji tai duniyar na juya mata... Sameer da bakinsa yake cewa ba ita kad’aice matarsa ba... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Cikin sauri ta shiga jinjina kai dan tama nemi hawayen ta rasa... Lokaci guda ta d’ago tana dubansa cikin tsananin fuci take furta “You know.... I won’t allow this to happen... That girl... Is leaving this house right this moment, she has no place in our lives...!!!” Ta k’arashe tana mai komawa cikin gidan a gigice....
A d’ari Sameer ya take mata baya yana doka mata kira amma inaaa tayi gaba....
Raihanah dake zaune gefen Mummy tayi jigum ganin Siyama ta shigo tamkar wacce jefota ya sanyata mik’ewa zumbur a tsananin tsorace, lokaci guda tai bayan mummy jikinta sai rawa yake....
Mummy ta mik’e babu shiri tana k’ok’arin tare Siyama da tai kan Raihanah gadan gadan tana fad’in “Mummy sai yarinyar nan ta bar gidan nan... Mummy no one can come between us nida Partner... Mummy ki k’yaleni na fiddata...! Ta kuma fincika tana kuma k’ok’arin janyo Raihanah dake tsananin kuka cikeda tsoro....
Dik iya k’ok’arin Sameer wajen ganin ya janye Siyama abu yaci tura... Sai fincika take tana kuma k’ok’arin janyo Raihanah tana fad’in wllhi sai ta bar gidan....
Baiyi niyan marinta ba amma hakan ne kawai zai maidota hayyacinta ganin yanda gab’a d’aya ta fice a giya...

Siyama dafe da k’uncinta ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubansa, cikin rashin yarda da abindake faruwa da ita take furta “Partner... Yau ni ka mara... Sabida kayi aure... Sameer ni ka d’aga hannu ka mara kan wannan kucakar yarinyar da ko a hanya bata isa ta biyo length d’in da nake ba.... Sameer ni ce Siyama fah...?!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Mummy hankali tashe ta shiga tsakankaninsu, rai b’ace take furta “Ya isa haka... Siyama kiyi shiru haka nan... Idan kun dawo hayyacinku sai ku zauna ai magana ta hankali..!”

Mummy bata kai aya ba Siyama taci gaba da fad’i cikin muryar kuka... “Mummy Partner ya daina sona... Wllhi yanzu Sameer bai k’aunata... Sultan was right... Babu abinda Sameer zai dani yanzu...Partner kar ka bari burinsu ya cika... Pls Sameer kar ka bari burinsu Sultan ya cika...!”

Da tsananin mamaki Sameer ke dubanta kana yace “Sultan...? What are you trying to say Siyama....?!” Ya k’arashe sounding curious....

Lokaci guda Siyama ta kuma d’agowa tana duban Sameer kana tasa hannu ta goge hawayen fuskarta... Lokaci guda Laila da Sultan da dik shirinsu akansu ya shiga dawo mata... A hankali take furta “Partner... I’m sorry... Sameer please forgive me.... Please don’t leave me...!”
Mamaki ya kuma cika Sameer ganin yanzu kuma mashi Siyama ke bada hak’uri....
Mummy dai janye hannun Raihanah dake matsan hawaye tai suka nufi upstairs...

Sameer ya kuma gyara tsayuwarsa yana duban Siyama kana yace “Ina jinki.... What does Sultan has to do with all of this... What is going on..?!” Ya k’arashe cikin d’an d’aga murya....

Goge fuskarta ta kuma yi tana k’ok’arin saita kanta, lokaci guda take ci gaba da da fad’in “I have something to confess Sameer... But please karkaga laifina... Dik abinda nayi ban tab’a daina sonka ba daidai da rana guda... Kuma sharrin Laila ce da Sultan....”

Yanzu kam sosai ya zama confused.... Cikin tsananin nuna b’acin rai yake fad’in “Siyama...Stop beating around the bush, and tell me what exactly is going on..!!!”
A hankali tiryan tiryan Ta dinga bashi labarin abubuwan da suka faru har dai yau da asirinsu Sultan da Laila ya tonu taji dik shirinsu akanta... Cikin kuka Ta had’e hannayenta biyu waje guda tana ci gaba da fad’in “Shisa nace kafin Laila ta fad’a maka ni zan sanar dakai... Sameer I’m sorry... I... I was so stupid and naive... I’m sorry for killing your child... Please forgive me...!!!” Ta k’arashe tana k’ok’arin janyo k’afarsa...
kauda fuskarsa gefe kurum yai hawaye na gangaro masa...
Cikin wata irin murya yake furta “How could you.... How could you Siyama....!!”
Lokaci guda ya kaikaito sosai yana dubanta da idanunsa masu zuban hawaye masu matuk’ar zafi....
“After taking all those contraceptions bai maki ba, so har cikina kinje kin cire... Gudan jinina Siyama... Allah kad’ai yasan adadin ‘ya’yan da kika halak’a min Siyama...” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai girgiza kai...
Cikin kuka Siyama ke fad’in “Wllhi d’aya ne kawai Partner... Sameer please forgive na tuba bazan sake ba... !”

Gani tai ya mik’e daga kujerar da yake zaune bisa lokaci guda yake furta “You know what... Just get out of here Siyama... Get out of my sight... Tashi ki fita I don’t want to see your face, you disgust me....!!”

Siyama ta kuma kamo k’afarsa tana fad’in “Partner wllhi na tuba please don’t leave me... Partner wllhi bazan iya rayuwa ba tareda kai ba... Sameer please forgive me na rok’eka... I love you please Partner...!!”

Fincikar k’afarsa yai, cikin tsananin huci yake furta “Did you just say you love me...? Kin kaw san mai ake kira so Siyama... After killing my own flesh and blood har kinada bakinda zaki bud’e kice kina sona... Come on, give me break Siyama... You love no one but yourself... Abinda ranki yake so shi kike aiwatarwa komin muninsa...You never loved me Siyama... Idan da ace kinasona da bazaki k’yamaci wani b’angare na jikina da Allah ya ajiye cikin jikinki ba... Just get out Siyama... Get out kafin na miki abinda zamuzo muna regretting daga ni har ke...!!!”
Ta kuma yunk’ura zata kamo k’afarsa ya darara mata tsawa da fad’in “I said get the hell out of my sight Siyama..!!!!”

Tsawanda saida ya zaburata a gigice tai sama tana doka kiran Mummy danma Allah yasa yau Daddy baya gidan ya d’an samu ya fita sannan washe gari suke shirin zuwa duba jikin Daddyn Siyamar gaba d’aya tinda shi Daddyn Sameer d’in ya d’an sami k’arfi....

Babu shiri Mummy ta nufo downstairs jin irin kukan da Siyama keyi... Tai saurin kamo Mummy tana fad’in “Mummy please Ki bashi hak’uri... Mummy kice kar ya rabu da ni dan Allah... Wllhi ina sonshi dan Allah Mummy...!” Gaba d’aya ta ma birki ta Hajja Fatahiyya...
Mummy fad’I take “Sameer mai kuma ya faru....?”
Ko zarafin amsa Mummy bai samu ba saima k’arasawa da yai ya shiga janyo hannun Siyama da iyaka k’arfinsa yana fad’in “Just get out... Zo ki fita nace, I don’t want to see your face...!!”

Haka ya dinga janyo Siyama tana dogewa tana rok’on Mummy Ta mar magana... Dik kiran duniya da Mummy ke masa ya taya yai mata bayanin meke faruwa inaa har saida ya fitar da Siyama zuwa harabar gidan... Lokaci guda ya juya ya komo cikin gidan ya barta nan yashe tana kuka tana ambato sunansa....

A k’ofa suka had’uda Mummy hankalinta dik a tashe...

“Ina Siyamar...?” Ta tambaya tana dubansa.... Hawayenda yake k’ok’arin dannewa yaji suna zuwa idanuna lokaci guda yake furta “Mummy what if wannan d’an shi kad’ai Allah ya hukunta zan samu... Mummy why..? Maiyasa Siyama zata cireshi... Maiyasa zata hanani ganin gudan jinina... Mummy all I did was to love her.... Abinda zata sakamin dashi kenan....!! Mummy ke shaidace irin soyayyar da naiwa Siyama only to get this in return... Mummy I thought she loved me... I was wrong... Siyama kanta kawai take so.. She doesn’t care about other people’s feelings...She’s so selfish..!”
Raihanah dake mak’ale jikin staircase hawaye suka kuma gangaro mata, lokaci guda Ta juya Ta koma d’aki had’ida kifa kanta tana kuka mai tsuma zuciya...

Cikin sauri Mummy ta k’arasa ta shiga janyo hannunsa har ta zaunarsa saman kujera...
A hankali Mummy Ke fad’in “Sameer kai hak’uri... Haka Allah ya hukunta wannan cikin baza’a haifosa ba... Siyama dai ta zama sanadin fitarsa ne amma ko bata cire ba bazai wuce k’addararsa ba kaji Son... Kai hak’uri ka yafewa Siyama, naji dik abinda kuka tattauna kuma a yanda na kula Siyama zigan muguwar k’awa tabi wacce bata nufinta da komai face sharri... Akwai irin wad’Annan mugayen abokai wanda su a kullum suga ka taggayara d’an rufin asirin da Allah yai maka da ni’imar da yai maka suga ka rasa just like your friend Sultan....”
Wannan karon d’agowa yai yana duban Mummyn, kafin ta jinjina kai tana mai ci gaba da fad’in “Naji komai Sameer... Kuma na yarda Sultan minafikinka ne dan haka kawai Siyama bazata k’ago labari ta fad’i ba, kai kanka shaida ne Siyama nada wasu hali nata na sangarta amma bazata tab’a maka k’arya ba... Kuma tana k’aunarka Sameer, kawai dai rashin sa’a akai ta girma babu kwab’a amma Siyama yarinyar kirkice kai kanka ka sani tinda tare kuka taso...”
Shidai Sameer shiru kurum yai ba tareda ya furtawa Mummy komai ba, ta kuma numfasawa kana tace “Girman kenan Sameer dole sai ana kai zuciya nesa especially now da ka zama family man... Nasan Siyama Ta maka abubuwa da dama but na yarda yanzu ta gane kurenta kuma she’s ready to mend her ways... Sameer my son please kar kayi hukunci cikin fushi.. Ka natsu kai tinani kaji... Ubangiji ya maka Albarka ya shiga lamuranka... Bara naje na Duba kitchen d’in... “

Har mummy ta tashi bai iya cewa komai ba sai k’ura ma waje guda idanu da yai dan har wannan lokaci zuciyarsa bai daina suya ba...
***

Siyama kaw tana ficewa gidansu da Sameer ta nufa... Ko ina yayi k’ura tsaban an jima babu kowa ciki.... Tai tsaye a parlor jikin madubin console, lokaci guda tasa hannu Ta d’auki hoton nasu dake cikin k’aramar frame....
K’uri taima hoton tana tina rayuwarsu na baya... Wasu hawayen suka kuma gangaro mata... Cikin parlorn ta k’araso ta zauna tana tina wasu moments masu dad’i da suka kasance cikinsu a gidan nasu.... Shin ta ya ma zata iya ci gaba da rayuwa ba tareda Sameer ba.... Haka ta tak’ure saman kujera rungume da hoton nasu dikda yunwa dake azalzalan cikinta, tana kallo Sultan na kiran wayarta wani sabon kuka ya kuma kufce mata....

***

Iyaka Laushi da galabaita su Ammi Sun gama yi, ga yunwa ga zafin store ga tsananin tashin hankalinda Ammi ke ciki... Sai wajajen la’asar su Khalid da Nabilah suka soma dawowa gidan dan rashin ganin Ammi a asibiti ya d’a damesa gashi bata d’aga wayarta, dikda cewa yayi tinanin ko har yanzu fushin ne take dashi amma dai yanaji can k’asar zuciyarsa kaman babu lafia.....

Wani abinda ya kuma saka su Ammi a uku shine yau ranan chanjin securities masu tsaron gate ne, wanda ya kwana ya riga ya tafi kuma wanda zai chanji aikin yau bai iso ba wannan dalili yasa babu kowa a gate balle aji kururuwarsu....

Ammi dake zaune gefen buhun shinkafa tana jin k’arar tsayuwar mota ta tashi da k’yar ta nufi window tana ihu... Ganin motar Khalid ya kuma sanyata sakin wani sabon k’ara tana fad’in kada ya shigo...

Khalid da Nabila da tuni sun soma jiyo tamkar kururuwa duban juna sukai kana suka fito daga motar babu shiri....



SameenaAleeyou 📚





*INDA RAI*
_...............DA RABO_





*105*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Babu shiri suka nufi yanda suke sauraro muryan... Ta window store d’in kitchen suke hangen Ammi da tai sharkaf da zufa, dan tashin hankali ko d’ankwali babu akanta... Da iyaka k’arfinta take fad’in “Khalid kamin rai kada ka shigo cikin gidan nan, na rok’i arzikinka ka fice kada ka shigo..!!!”

Khalid da mamaki ya cikasa, duban juna sukai shida Nabilah kana ya d’an soma takowa kad’an cikeda tashin hankali... Kafin ma ya sami zarafin maganan Ammi ta kuma doka wani uban ihun tana fad’in “Nace kar ka shigo.. Kada ka shigo Khalid... Ka koma nace.... Kamin rai ka fice daga gidan nan... Nabilah Ki ceceni ki fitar dashi daga gidan nan... Kada ki barshi ya shigo na rok’i arzikinki..!!!”

Yanzu kam ba mamaki kawai abin Ke basu ba harda tsoro.... Nabilah tai saurin rik’o hannun Khalid dake k’ok’arin kuma kutsa kai cikin gidan yana fad’in “Ammi Wai meke faruwa ne... Meke faruwa cikin gidan... Ki barni na shigo na fiddaki Ammi na...!” Cikin tsananin tashin hankali yake maganan...

Ammi na kuka take fad’in “Khalid my son ka yafeni... Kamin rai kada ka shigo cikin gidan nan....!!!”
Girgiza kai kurum yake, cikin tsananin tashin hankali yake fad’in “Ammi I’m sorry... Bazan iya tsayuwa a nan ina gani kina cikin tashin hankali na k’yaleki ba... Zan shigo na fiddaki... Koma menene cikin gidan saidai ya sameni amma dole na shigo na fiddake....!!!” Ya kuma nufan k’ofa cikin sassarfa...
Hannu biyu Ammi ta d’ora aka tana ihu tana fad’in “Nabilah..!!! Nabila kada Ki barshi ya shigo... Idan kinama Allah ki hanasa... Idan kina k’aunarsa Ki hanasa.. Wayyo ni Farida... Nabilah Ki ceceni kada ki barsa ya shiga..!!!”

A d’ari Nabilah da jikinta Ke tsananin rawa ganin irin wannan tashin hankali ta k’arasa tasha gaban Khalid tana kuka sosai take fad’in “Please just don’t enter tinda tace haka... Kabi umarninta please..!” Tai maganan tana had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o...

Cikin tsananin huci yake fad’in “Kin ko san mai kike fad’a Nabeela... Mahaifiyatace fah a ciki... Kuma ga dikkan alamu taimako take nema, tsananin soyayyar da take min yasa take cewa kada na shiga dan kar abindake cutar da ita cikin gidan ya cutar dani... Who knows meke faruwa cikin gidan..! I’m sorry Nabilah but I can’t just sit back and do nothing... My Mother needs me..!!!” Ya k’arashe yana k’ok’arin kaucarda Nabilah gefe.... Ammi ta kuma d’aura hannunta aka tana sabon ihu...
Cikin sauri Nabilah ta kuma shan gabansa tana kuka take fad’in “Ni zan shiga, you stay right here kaji... Ni zan shiga naga meke faruwa...!!”
Cikin rashin yarda yake girgiza kansa kana yace “Are you kidding me teddy bear...? Ta ya zan barki ki shiga cikin had’ari... Kema kinsan ko mafarki kike hakan bamai yuwa bane... Just stay right here kinji koh...!!”
Janyosa Nabila ta kuma yi tana kuka sosai take fad’in “Bakajin mai Ammi ke cewa ne... Dan Allah ka k’yaleni ni na shiga....!!!”
Wani irin tsawa ya daka mata da fad’in “Nabeeeelaa!!!! Just get out of my way...”
Bata matsa ba bata daina kuka ba... Ammi daga window tana hangosu tana kuka... Lokaci guda taceda Khalid... “Khalid kafin ka shigo gidan inaso kazo na fad’a maka wani abu... ka k’araso nan d’ah nah....!!”
Juyawa yai yana duban Ammi daga yanda take ta ramin window... Girgiza kai kurum yai kana ya nufi kiran Ammi...
Nabilah kaw yana shigewa ta arce a guje ta shige cikin gidan had’ida maida k’ofa ta rife kif... A kid’ime Khalid ya waigo ya nufo k’ofar yana doka mata kira inaaa ko saurarensa batai ba ta nufi kitchen wajen su Ammi..
Dik jijjiga k’ofa da kiran Nabilah da Khalid keyi bata sauraresa ba... Kai tsaye store d’in kitchen ta nufa ta bud’e su Ammi jikinta har lokacin rawa yake....
Ammi na hangota Ta k’araso a guje ta rungumeta tana kuka sosai take fad’in “Na gode... Na gode miki Nabila... Thank you for saving my son... Thank you Nabilah... Bazan tab’a iya biyanki ladan abinda kika min ba....!!!” Ta k’arashe cikin kuka sosai tana mai kuma kifa kai cikin jikin Nabilar...
Nabila dai gaba d’aya wane irin sanyi jikinta yai da ganin irin wannan bak’on al’amari daga wajen Ammi... Cikin sauri kuma Ammin ta mik’e tana fad’in “Maganin... Maganin... Muje mu share kafin ya shigo... Muje muje...!” Ta shiga janyo hannun Nabila tana tambayar yanda tsintsiya da sandar mop yake... Babu shiri Nabilah ta isa ta d’auko tsintsinya da sandar mop... Dik wani lungu da sak’o da Ammi ta barbad’a maganin nan saida suka share tsaf suka goge, Ammi harda bulbula ruwan hypo sosai dan tabbatar da ko burbud’in maganin bazai zauna ba....

Aunty Hanne ce ta fito fuska sharkaf hawaye cikeda borin kunya tazo zata wuce, Ammi ta d’aga mata k’eya tana fad’in “Allah shiga tsakanin na gari da mugu... Nidai daga yau na tuba kema Allah sa ki gane ki tuba Hanne...!”
Aunty Hanne dai mayafi a hannu ta fice jiki a matuk’ar sanyaye...
Ita dai Nabilah sai kallon wannan ikon Allah take... Abu saikace wani a film...
A k’ofar fita ta tadda Khalid wanda ke faman bugu Nabila ta bud’e masa... Tsaye yai yana duban Aunty Hanne cikeda mamaki saikace kazar da aka tsamo cikin ruwan zafi, tafiya ma da k’yar take ga zufa sharkaf jikinta... Cikin muryar kuka Aunty Hanne ke duban Khalid d’in kana tace “Saifullahi wallhi bazan iya kasheka ba kai kasan haka ai...!”
Da tsananin mamaki Khalid ke subanta kana yace “Kisa kuma Aunty..?”
Aunty Hanne na matsan hawaye ta shigesa ko zarafin amsa masa bata samu ba... Khalid ya d’an take mata baya yana kiranta amma inaa ko tsayawa Aunty Hanne batai ba saima Ammi data fito tagajan magajan tana fad’in “Kada ka bita... Ka dawo nan Khalid... K’yaleta Ta tafi kafin tai maka wani mugun abin... Aniyarki Ta biki Hanne... Wllhi idan Khalid ya rasa mata babu abinda zai da d’iyarki... A sauk’a lafiya...!” Ta k’arashe tana tafe hannaye...

Da tsananin mamaki Khalid ya waigo yana duban mahaifiyarsa, lokaci guda Ammi ta k’araso gareshi a guje ta shiga Shafa jikinsa tana fad’in “Babu abinda ya sameka dai koh....!!”

Khalid da mamaki ya kasa sakinsa girgiza kai kurum yake cikeda rashin yarda kana yace “Wai Ammi Wai meke faruwa ne... What’s all this....??”
Kasa magana Ammi tai sai rungumesa da tai hawaye na gangaro mata... Lokaci guda take furta “Khalid ka yafe ni... Ka yafe min d’ah nah..” Ta k’arasa ta janyo Nabilah ta had’esu duka biyu ta rungume tana fad’in su yafeta... Gabaki d’aya taananin mamaki ne ya cikasu....

Ammi na tsakiyarsu rungume dasu suka nufi cikin gidan, Nabilah da Khalid basu daina duban juna ba suna duban Ammi cikeda mamaki... Shigarsu gidan da kad’an su Aunty Daula dasu Aunty Bara’atu suka dawo....
Har lokacin Ammi hawaye take tana neman gafaran su Khalid....

Su Khalid basu ida shan mamaki ba saida sukaga Ammi ta nufi gaban Aunty Daula da k’irjinta ke tsananin bugu, ga mamakin Aunty Daula hannayenta Ammi ta kamo tana hawaye sosai take fad’in “Ki yafeni... Ki yafeni Daula... Nayi niyyar maki mugunta sai reshe ya tashi juyawa da mujiya... Na gina miki ramin mugunta keda ‘ya’yanki sai na tashi afkawa ciki nida nawa d’an.... Da ace yau na rasa Khalid tabbas da nima halak’a zanyi... Daula ki yafeni, wllhi na yarda abinda shuka a duniya shi zaka girba...” Take Ammi ta labarta masu dik abinda ya faru babu abu guda k’wakk’wara data b’oye masu...
Yesmin dake kallon wannan tashin hankali wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe dashi... Aunty Daula ma kukan take had’ida kamo Ammi dake k’ok’arin duk’awa ta hanata k’arasawa...... Lokaci guda suka rungume juna suna hawaye sosai... Aunty Daula fad’i take “Ki daina bani hak’uri Ammi kema tabbas ba’a kyauta maki ba... Amma tuni Allah ya hukunta hakan... Ni baki min komai ba wllhi kuma nafi kowa jin dad’i da Allah ya k’addari kika fahimci hakan... Ubangiji ya yafe mu gaba d’aya ya kuma tashi kafad’un mijinmu..!”

Allah sarki duk wanda zaice bai kuka ba a parlorn nan sai wanda baida zuciya cikin k’irjinsa... Gaba d’aya baka jin komai sai sautin fitan kuka a hankali, harta Aunty Bara’atu saida k’walla ya zubo mata had’ida tausayin Ammi... Kai harta Kubura da Karimatu dake lab’e Daga k’ofar kitchen saida sukai hawaye... Allah sarki babu abinda yafi zaman lafiya yafiya da yad’a soyayya sama da k’iyayya dad’i a duniya... Hak’ik’a wane irin sanyi da aminci ne ya sauk’a a wannan ahali had’ida sakeenaah....

Aunty B ta k’araso ta kamo hannun Ammi da na Aunty Daula tana hawaye itama kana tace “Alhamdulillah...! Mijinku zaifi kowa Farin ciki idan yau ya tashi ya wayi gari ya ganku haka... Yau Allah ya cika masa burinsa...!”
Ta juyo tana duban Aunty Daula sosai kana tace “Daula banida haufi akan zakiyima abokiyar zamanki biyayya a matsayinta na wacce ke gaba dake a haife da kuma a zamantakewar aurenku...”
Cikin sauri Aunty Daula ke jinjina kai tana hawaye alamun tabbas hakane...

Aunty B Ta maida dubantaga Ammi kana taci gaba da fad’in “Toh nima dai zan rok’i yafiyarki Ammi... Amma kafin nan inaso na sanar dake zuciyata taji wasai sanin cewa abokiyar zaman ‘yaruwata ta fahimci gaskiya kuma ta gane cewa Allah shikeda cikakken iko akan komai ba boka ko Malami ba... Allah shike k’addarawa kuma shike badawa ya kuma hana ga wanda yaso... Boka ko Malami basu isa suyi maka abinda Allah bai maka ba.. Basu isa su hana faruwan abinda Allah ya riga ya hukunta ba...”
Ammi na hawaye take jinjina kai tana fad’in “Wannan haka ne Bara’atu.. Wllhi na yarda kuma na tuba tuba na gaskiya..!”
Aunty B tace “Alhamdulillahi... Tinda kin fahimci haka... Yanzu zan sanar daku dik yanda abin ya faru...!”
Gaba d’aya sukai jigum suna duban Aunty B had’ida saurarenta....

Nan Aunty Bara’atu ta labarta masu dik yanda abin ya kasance... Sukaita al’ajabi wannan hikima irin na Aunty B da hangen nesanta... Lallai ita d’in ta cika jajirtacciya wacce takai a yaba mata... Cikin salama ta wargaza mugun nufin su Ammi kuma tayi k’ok’arin karkatoda hankalinsu da tinaninsu zuwaga fuskantar gaskiya da kuma k’auracewa sab’o...

Kubura da shashashanci daga yanda take tsaye ta k’yak’yace da dariya tana fad’in Inama tana wajen.... Ganin kowa yaimata zuru yana dubanta ya sanyata had’iye

Please Login or Register in order to submit comment