Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k’aru, ya fuzar yana ci gaba da tari had’ida duk’awa...
Ammi ta dubi Yesmin tace “Yesmin mai kika saka a abincin..?”
Yesmin da gaba d’aya ta daburce tace “Ammi wllhi ban saka komai ba, Siyama even tasted...” Aya tai wa kalaman nata ganin Siyama ma na tari had’ida fito da harcenta waje tana hurawa...
Saurin d’aukan spoon Yesmin tai ta d’ibi abincin takai bakinta, bata iya had’iyewa ba itama ta wuce kitchen a guje ta zubda abincin bakinta tana neman abin shashe baki sabida tsananin barkwano had’ida tsami da zak’i...
Kubura dake lab’e sai buga tsalle take tana cin dariya a b’angare guda kuma tausayin Khalid d’inta ya kama ta amma ko babu komai Yesmin tasha disgi kwalliya ta biya kud’in sabulu...

Khalid ya d’ago a galabaice yana duban Ammi kana yace “Ammi yaushe Siyama ta iya girkin da za’a bar mata girkin gidan nan tayi...?”
Siyama ta d’ago tana dubanshi magana k’unshe a bakinta saidai itama har yanzu barkwanon bai saketa ba, kafin ta samu zarafin magana Kubura tai karaf ta nuna Yesmin da fitowarta kenan daga kitchen taje ta watsar da abincin bakinta kana taci gaba da fad’in “Gata nan... Ga wacce tai girkin gidan yau gaba d’aya kuma musamman sabida kai tayi...”
Wani irin kallo kurum Khalid ke aika mata, bai kuma cewa komai ba sai tattara car keys d’insa da folder had’ida wayar salulansa ya fice ya nufi b’angarensa..
Yesmin dake tsaye tamkar ruwa ya shanye take ta fashe da wani irin kuka tana fad’in wllhi wani ne ya b’ata mata abincinta kuma bata zargin kowa sai Kubura...
Haba nan fah Kubura ma ta dinga rantse rantse ita ba itabace sharri Yesmin take mata don ta tsaneta...
Ammi ta daka masu tsawa sukai shiru kana tace “Yesmin wuce sama, ke kuma Kubura ki wuce ki tattara dining d’in nan idan kin gama ki sameni d’aki...” Daga haka Ammi ficewa tai ta nufi b’angaren Khalid...
Yana ganinta ya d’an rausayar da idanunsa had’ida fuzar da iska yasan bazai wuce maganan Yesmin tazo mashi dashi ba...

“Ammi not now please...” Ya fad’i cikin kasaltecciyar murya

Harara ta wurga mashi tana mai fad’in
“Khalid kana jina ka saurareni da kyau, abinda ya faru ba laifin Yesmin bane sannan idanma laifinta ne ya kamata kai appreciating effort d’inta, all she’s doing tanayi ne sabida tana sonka Khalid, babban abin takaicin kai baka ma fahimtar hakan... Khalid wai mai ya shige kanka ne... Haka kakeso mu zuba maka idanu babu aure, mai amfanin zaman naka tinda ka kammala karatu ga aiki da yanzu ka kama ba dama what else bayan aure...Inyi...?”

Sauk’e deep breath yayi had’ida zama cikin sofa kana yace “Ammi kin sani fah I don’t like being pressured... Please mana Ammi, how many time do we have to talk about this.... Ammi sau nawa zance banason yarinyar nan... Idanma auren kuke so nayi then ku barni na zab’i wacce nakeso kaman yanda kuka bar Siyama ta zab’a... But please Ammi don’t force me into an arranged marriage.... I don’t like that girl period...”

Zama tayi gefenshi kana ta kamo hannayensa tana dubanshi, cikin kwantar da murya tace “Khalid... I only want what is best for you, meye laifin Yesmin, she’s beautiful, intelligent... family d’inta sanannu a garin Abuja gata ‘yar uwarka ce kuma tanada hankali and above all she’s deeply in love with you, Khalid mai kake nema sama da wannan...”
Tinda ta fara magana take dubanta kana ya girgiza kai yace “Ammi duk abinda kika lissafo doesn’t matters idan dai har bana sonta... Do not pressure me please Ammi....” Ya k’arashe yana mai lumshe idanu had’ida kishingida cikin kujeran...

A kufule ta mik’e tana fad’in “Rayuwarka ce ai sai kayi yanda kaso da ita, amma ka sani bazaka d’aukomin ko wacce irin shirgi kace zaka kawo min ita matsayin sirkaba kaji na fad’a maka....” Daga haka ficewa tayi fuu kaman zata tashi sama...
A hankali yake ambaton sunan Allah wani haushin Yesmin da tsanarta na kuma taso masa....

Siyama kam bata kuma bi takan kowa ba saima tattara kayanta da ta shigayi ta had’esu waje guda don tanaso ta maidasu gida ta canzo wasu sets d’in..
Kubura ta ganta na tattara kaya tace “Aunty badai tafiya zakiyi ba...?”
Harara Siyama ta galla mata kana tace “Kubura nafah sanki sarai akan Khalid, nasan babu abinda bazakiyi ba, nasan kece kika b’awatawa Yesmin abinci, wllhi ki shiga hankalinki idan ba so kike na sami Khalid na sanar dashi sonshi kike ba...”
Kubura tai saurin k’arasowa cikin d’akin had’ida tura k’ofar kana ta risina gaban Siyama tace “Aunty Siyama kimin rai ki barni a haka nake kallon shi inajin dad’i yanzu kika fad’i masa ai saidai ya koreni gidan nan na daina ganinshi gaba d’aya, kofah magana bai tab’a min ba ni har tsoron gaisheshi nake... Ita wancan dai bata dace ba billahillazi Aunty...” Ta k’arashe tana wani gyara rigar jikinta irin itace daidan shi..
Girgiza kai kurum Siyama tai had’ida jan gajeren tsuka tace”Au bata dace dashi ba... Toh wace ta dace dashi ke...?”

Kubura ta murmusa had’ida sinne kai tace “Wllhi kuwa Aunty”

Dariya Siyama tai don abin dariya ya bata kana tace “Ni dalla banson sakarci zoki fitar min da jakkan nan....”
Kubura ta d’auko jakan tana rok’on Siyama kada ta koma gidanta suyi zamansu a nan tinda Dr bai dawo ba...
Siyama bata tsaya biye shiriritan Kubura ba ta tada mota ta wuce abinta...

Tin daga gate d’in compound d’in nasu taji kaman k’irjinta na bugu bata gama aminta da bugun da k’irjinta keyiba saida ta hangi motarsa a parking space d’insu...
Mamaki ya kamata shin yaushe Sameer yazo kuma ko waya bai mata ba, wata zuciya tace k’ilan yayi niyyan surprising d’inki ne.. Murmushi ta d’an saki kana ta janyo trolley d’in ta shige cikin gidan...

Hangoshi da tai zaune saman kujera yasa gabanta kuma fad’uwa, gashi dai zaune kurum sannan TV na kashe kuma bawai aiki yake bisa computer ba ko danna wayarsa, a’a zaune kawai yake shi kad’ai, cikin zuciyarta tace this is not like him, koma surprise zai bata da ba’a parlor zata ganshi ba sannan da ace ma yana parlor d’in da yanzu ya taso ya bata hugs, tamkar mai sand’a haka take tafiyar har ta isa ta taddashi yanda ta hangi fatar fuskarsa tayi jajazir haka nan idanunsa da ya k’urasu ma waje guda...
This isn’t the Sameer she used to know, yanayi ne da tinda take a rayuwarta bata tab’a ganinsa cikin makamancinta ba...
Tai k’arfin halin k’ak’aro murmushi kana ta rungumeshi tana fad’in “Partner wane irin surprise ne wannan, oh I missed you....” Ta k’arashe tana kuma k’ank’ameshi saidai abinda ya bata mamaki shine bai maida mata martanin rungumarta ba saima b’anb’are hannayenta da ya soma daga cikin jikinsa cikin wane irin zafin nama....

Da tsananin mamaki Siyama ta d’ago tana dubansa ga wani irin huci da yakeyi...
Murya na rawa tace “Partner what’s all this about... Wai meke faruwa ne...?”

Da wasu irin idanu yake dubanta kana yace “Don’t touch me again...!”

Kallonsa ta kumayi cikin rashin yarda da abinda take gani hawaye na neman ciko idanunta don duk wani sab’ani da zasu samu bai tab’a mata irin hakan ba, cikin muryar kuka take furta “Sameer wai meke faruwa don Allah...?”

Cikin dakakkiyar murya ya kuma ceda ita “How long have you been lying to me...?”

Duban idanunsa tai tana iya hango tsananin b’acin rai cikinsu had’ida tashin hankali, take jikinta ya d’auki rawa ta shiga girgiza masa kai tana hawaye, cikin murya irinta mai kuka take furta “I don’t get you Sameer, please what’s happening...?”

Cikin karaji ya matso kusa da ita, fuskarsu dab na juna tana iya jiyo tsananin hucin da yake...
Da iyaka k’arfinsa ya finciko hannunta ya d’aura mata gidan magani saman tafin hannun nata kana yaci gaba da fad’in “I know you’ve been taking contraceptions Siyama....And you know, I don’t need your damn explanation... The only thing I need to know shine meyasa kika min k’arya, why did you make me believe that you love me.... Why Siyama...?”

Kuka take tana girgiza masa kai had’ida furta “Sameer please let me explain...”

Cikin tsananin d’aga murya jijiyoyin jikinsa suna tashi yake furta “I told you I don’t need your explanations... Just tell me your reason for making a fool out of me... Tell me Siyama....!!” Ya k’arashe hawaye na gangarowa daga idanunsa guda wanda da gani na tsananin b’acin rai ne...

A hankali ta furta “Partner...”

Katseta yayi da fad’in “Don’t you dare call me Partner again, just answer the damn question...!!”

Kasa furta komai tayi sai kuka da take harda shesshek’a bata tab’a zaton haka abin zai kasance ba....

Jin ta kasa furta komai sai aikin kuka yasa Sameer dake watsa mata mummunar kallo ci gaba da fad’in “I’ve shown you nothing but love.... Wannan shine abinda zaki sakamin dashi, ki hanani ganin gudan jinina, claiming you love me... Idan haka ake soyayya Siyama bana k’aunar irin soyayyar da kike mun, bansan reasons d’inki ba kuma banaso na sani...Amma ki sani ko ba dad’e ko ba jima zanga gudan jinina da yardar Allah...” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai mik’ewa da yayi ya fice daga gidan gaba d’aya...

Siyama kaw kwanciya tayi a wajen tana kuka sosai, ganin kuka bazai ficceta ba ya sanyata mik’ewa ta nufi gida a fujajan..
Ammi saida ta razana da ganinta haka..

Cikin tsananin kuka da tashin hankali ta rungume Ammi tana fad’in “Ammi I cant lose him, I love him so much.... Please do something Ammi...”

Ammi ta rungumeta sosai cikeda tashin hankali take fad’in “Mai ya sami Sameer d’in... Talk to me Siyama, ina Sameer d’in...”

Siyama ta kasa furta komai sai shesshek’an kuka da take, da k’yar ta iya fad’iwa Ammi duk abinda ya faru kana ta k’arada “Ammi ban tab’a ganinshi cikin yanayin fushi irin wannan ba, Ammi ki ceceni kada ya rabu dani...” Ta k’arashe tana jijjiga Ammin...

Rungumeta Ammi ta kumayi tana lallashi “Siyama irin abinda nake jiye maki kenan amma shegen taurin kunne irin naki kikak’i ki saurareni, kin gani koh maganin hana d’aukan ciki kawai ya gani yayi fushi dake irin haka, inaga yasan cewa kin cire mashi cikinshi.. Mai kike tunanin zaiyi...?”

Cikin kuka Siyama ke fad’in “I don’t wanna think about that Ammi, nidai kawai save my marriage please...”

Jinjina kai Ammi tai kana tace “Ki kwantar da hankalinki ki daina kukan haka, karma ki bari Daddynki yaji wannan batu, ni nasan mai zanyi...”

Da wad’annan kalamai Ammi ta kwantar da hankalin Siyama har ta d’an samu tayi shiru amma kam ta k’ule a d’aki can k’asar zuciyarta bata daina fargaba da zullumin hukuncin da Sameer ka iya yankewa akanta ba dukda tasan cewa duk tsananin fushi dole ya yafe mata tinda yana sonta...

Bayan sallan Magrib Ammi tayi gidansu Sameer da k’orafin cewa Sameer na wulak’anta mata d’iya ko Hajiya Fatahiyyah ta d’au mataki ko ta fasa k’wai ta sanar da Sameer komai...

Hajiya Fatahiyya Momyn Sameer ta d’ago idanu a firgice tana duban mahaifiyar Siyama kana tace “Farida kar kimin haka bamuyi haka dake ba......”



SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_



*29*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Ammi ta murmusa kana tace “Idan kaw haka ne ki kirawo d’anki kija masa kunne akan Siyama, bai isa ya wulak’anta min d’iya ba...”

Momy ta murmusa kana ta zauna saman kujera tace “Shin ke maiyasa bazakiyi fad’awa d’iyarki ba wacce ko girki batasan tayiwa mijinta, shin Farida bazaki tambayi naki d’iyar ba mai takeyiwa mijinta.... Sanin kanki ne Siyama is a spoilt brat bacin soyayya babu abinda Sameer zaiyi da ita...”

Murmushi Ammi tayi kana ta mik’e tsaye tana gyara mayafi tace “Hajiya Fatahiyya this conversation won’t take us anywhere, inaga lokaci yayi da Sameer ya kamata yasan komai, koshi wanene... Sirrin da ya kamata ya sani 30 years back...”

Momy ta mik’e a fusace tana fad’in “Ke Farida ki iya bakinki, kijida taki d’iyar amma karki kuskura ki gusarwa d’ana farin cikin dana gina rayuwarsa bisa...”

Hajiya Frida ta kuma murmusawa kana tace “Let’s see mai Sameer zaice idan ya fahimci matar da ya d’auketa da tsananin daraja da mahimmacin has been lying to him his whole life.....”

Momy na tsananin huci take fad’in “Don’t even try that Farida, wllhi karki kuskura... Sameer is my son...”

Daidai lokacin da sukaji an bud’e k’ofa an shigo....
Gaba d’aya suka juya a tare suna dubanshi, idanunsa suna kuma zuban wasu irin ruwa mai tsananin zafi....
Momy da tuni hawaye sun soma k’ok’arin ciko idanunta saurin kauda fuskarta tai daga barin dubansa....

A hankali Sameer yaci gaba da takowa cikin parlorn tamkar wanda ruwa ya shanye haka yake tafiyar....
“Mummy...” Ya kirawo sunanta a hankali cikin wani irin raunanniyar murya...
Kasa juyowa ta dubesa tai saima dad’a rintse idanunta da tayi tana mai k’ok’arin saita kanta...
Sameer yasa hannu ya share hawayen da suka zubo masa kana ya kuma cewa “Mummy is that true, Mummy please talk to me.... Da gaske ne baku kuka haifeni ba....?”

K’ok’arin saita kanta tayi kana ta k’araso ta rik’o hannayensa guda biyu, a hankali take furta “Sameer kada ka yarda da abinda take cewa, we are your real parents, I’m your mother... Bansan meyasa take fad’in haka ba... Shin sab’ani kuka samu da Siyama...?”

K’uri ya mata idanunsa babu alamun wasa ya kuma furta “Momy tell me the truth... Ki fad’a mun gaskiya, who my real parents are....”

Kamo hannayensa tai suka zauna bisa sofa don already lokacin Ammin Siyama ta fice...

“Son look into my eyes, I’m telling you the truth....Sameer kai d’ana ne... Please believe me Son...” Ta k’arashe tana shafa fuskarsa hawaye na k’ok’arin ciko idanunta...
A hankali ya rungumeta badon ya yarda da abinda take fad’i masa ba sai don bazai juri ganinta cikin hawaye ba sannan baiso zuciyarsa ta k’aryata masa ita macen da yake tsananin k’auna sama da kowa a duniya, wacce ya girma ya santa a matsayin mahaifiya a gareshi...
Jin hawayenta saman kafad’unsa ya kuma karyar masa da zuciya...
A hankali yake furta “I believe you Momy please ki daina hawayen nan....”
Momy ta d’ago tana dubansa kana tace “Bansan maiyasa Farida tace haka ba Son, kodai sab’ani ka samu da Siyama...?”
Shiru yayi tamkar mai tunani kana ya k’ak’aro murmushi ya sakar mata yace “Momy idan wani baison had’a jini dakai maybe kanada wani bak’in tabo ne... Ki kwanta ki huta you this isn’t good for your blood pressure...” Daga haka mik’ewa yayi jikinsa a sanyaye ya fice yayinda Momy ta bishi da kallo har ya fice daga parlorn tana tunanin mai Sameer yake son fad’i....

Yana ficewa sashensa dake cikin gidan ya nufa yai zaune a parlor yana tunanin rayuwa, a hankali ya lumshe idanunshi had’ida d’aura hab’ar shi saman hannayenshi guda biyu....
Zancen zuci ya shigayi shi kad’ai yana nazari.... What if da gaske su Momy basune iyayenshi ba, what if Ammin Siyama ta sanar da Siyama cewa shid’in maras asaline kar ta bari rabo ya ratsa tsakaninsu sabida bak’in fenti da rayuwarsa ke shafe da ita....? Wasu irin hawaye masu d’umi yaji suna gangaro mashi, shi kad’ai sai tauyin kanshi ne ke taso mashi, ya rasa tunanin meye zaiyi, shin abubuwa da suke kan faruwa dashi a garin Kano zaiyi tunanin warwarewa ko kuwa na nan gida Kaduna...?
Baisan da wanne zai fara ba sabida kwanyarsa gaba d’aya ji yayi ta cushe, wani tunani ne ya fad’o masa ya mik’e jiki babu laka ya fad’a bathroom ya d’an watsa ruwa ko zai d’an wartsake, yana fitowa sashen Momy ya nufa yanda ya tadda bata a parlorn da alama ta haura sama hakan sai yafi masa sauk’i, cikin sauri ya k’arasa ma’ajiyan keys na gidan ya zari key d’in sashen Daddy ya fice....
Sauri sauri yake gudanar da al’maran nasa tamkar mai tsoron kada wani ya tadda shi, kai tsaye master bedroom d’in Daddy ya nufa kana ya shige bathroom, ma’ajiyan kayan wanke baki na Daddy ya nufa ya d’auki toothbrush d’in Daddy...
Ya jima yana juya toothbrush d’in kafin ya bud’e ‘yar k’aramar jaka ta leda transparent mai d’an zip ya saka toothbrush d’in ciki, sauri sauri ya fito ya kulle sashen ya maida mabud’in ma’ajiyansa...
Ko sashen nasa bai koma ba ya nufi motarsa da ‘yar jakar da toothbrush d’in ke ciki ya fice....
Bai zarce ko ina ba sai asibitinsu da a baya yake aiki....
Sameer ya jima zaune cikin mota yana tunanin abinda yake niyyan yi, tuhumar kansa ya shigayi anya yayi dai dai, shin idan yaga abinda zai karyar masa da zuciya fah....?
Ya kuma lumshe idanu yana tuna abinda Siyama ta mishi, his heart’s already broken gwara kawai ya k’arasa abinda ya fara, da alama ya jima cikin duhu lokaci yayi da haske zai bayyana cikin rayuwarsa.....
Ajiyan zuciya ya sauk’e kana yasa hannu ya tsinko sumar kansa guda ya nad’eta cikin leda kafin ya nufi cikin asibitin....
Kasancewar biyar na yamma ta gauta shiyasa ya tadda ma’aikatan wanda suka gama morning duty nakan tafiya, gaba d’aya sai murnar ganinsa suke, wani matashi ma’aikacin laboratory ne ya tsaya suna gaisawa da Sameer don tuntuni sosai suka saba ya d’auki Dr Sameer tamkar Yaya....
Auwal yace “Dr banjin lab d’in na bud’e wani abu ne kake so...?”
Sameer ya mik’o masa ‘yar jakan hannunsa kana yace “Auwal I need a DNA result of this ASAP....”
Auwal ya d’anyi shiru kana ya jinjina kai yace “Ok Dr first thing tomorrow morning, the result will be ready in sha Allah....”

Sameer ya jinjina kai kana yace “Good... Idan ya zama ready kawai ka kirani zanzo na karb’a...”
Auwal ya d’an shafi sumarsa yace “Haba Dr ai location kawai zaka fad’i min na kawo maka...”
Sameer ya d’an murmusa kad’an kana yace “Kar ka damu kawai ka kirani zanzo na karb’a... Na gode koh...” Ya k’arashe yana d’an bubbbuga kafad’unsa...
Auwal ya jinjina kai kana yace “Alright Dr yanda kace, sai kaji daga gareni....”
Daga haka sallama sukai Sameer ya nufi motarsa kira na shigo mashi, ganin Siyama ce mai kiran ya sanyashi saka wayan a silent....Har Auwal ya soma tafiya ya kuma kiran sunansa yace “This is confidential, ko Sultan banso ya sani....”
Auwal ya jinjina kai yace “In sha Allah Dr...”
Sameer ya kuma jinjina kai kana yayi key wa motarsa....
Bai zarce ko ina ba sai gidansu Sultan don Auwal ya sanar dashi Dr Sultan yau trough out bai shiga asibitin ba....
Wayan Sultan d’in ya shiga kira sanda yayi zaune saman bayan motarsa....

***

“Ammi ya kukai, ina Sameer....?” Siyama ta tambaya tana duban Ammin da gaba d’aya ta zamto wata iri....
“Ammi talk to me dan Allah...”
Ta d’an k’ara fad’i tana kamo hannayen Ammin cikeda damuwa...
Kallo Ammi ta bita dashi kana tace “Siyama na goyi bayanki d’ari bisa d’ari kada ki tab’a yarda ki d’auki cikin Sameer, ki ci gaba da shan magani kada ki fasa....”

Siyama ta bita da kallon mamaki kana tace “But Ammi.... Ba kece mai min fad’an shan magungunan hana d’aukan ciki ba, idan ban mance ba akan na zubda ciki saida kika kwana biyu bakimin magana.... Why the sudden change of mind...?”

Hannayenta Ammi ta rik’o kana tace “I’ve my reasons Siyama, sannan ki sani duk wani dalilina don na kareki ne....”

Wannan karon da tsananin mamaki Siyama ke duban mahaifiyarta....
“Ammi you making me nervous.... Is there anything I need to know...?”

K’uri Ammi ta mata kana ta girgiza kai a hankali tace “No, babu komai.... I just feel like supporting your idea ne as my daughter.... Ki tashi ki tafi gidanki and make sure kinci gaba da shan magani....”

Jiki a sanyaye Siyama ta mik’e tana mamakin mahaifiyar tata, toh meyasa ta canza ra’ayinta, mai Momyn Sameer ta fad’i mata....?
Still tai tana murza mabud’an motarta a hankali kafin tasa kai ta fice daga gidan bata zarce ko ina ba sai gidansu Aminiyarta Laila....

***

Sultan ya dube shi a karo na biyu kana ya girgiza kai yace “Sameer ko zaka kwana kana fad’a min babu abinda ke damunka... Just tell me please maybe I can help...”

Shafe fuskarsa yayi da duka tafukan hannayensa kana yace “Sultan how does it feel ace mutanen da kafi so a rayuwarka sun maka k’arya...?”

Sultan ya gyara zama had’ida murmusawa an tab’o yanda ke masa k’aik’ayi...
Kafad’ar Sameer ya dafa kana yace “Sameer this life has never been fair, and it will never be... Ka yarda.....?”

D’ago rinannun idanunsa yai yana duban Sultan d’in kana ya jinjina kai yace “Yeah na yarda....”

“Mai Siyama ta maka...?” Sultan ya jefo masa tambayar kai tsaye, shiru ne na d’an lokaci ya gifta kana ya girgiza kai yace “It’ll be better if we don’t talk about it...”
Sultan ya masa k’uri yana nazarinsa, jin jina kai yai kana yace “Is ok if you don’t wanna talk about it... But whenever you feel like, don’t forget that I’m here bro....”
Jinjina kai Sameer yai yana mai furta “Na gode abokina...”
Sun d’an d’ibi lokaci Sultan ke jansa da fira dukda ba wani amsawa Sameer d’in keyi ba, yamma lis Sameer yayiwa Sultan sallama ya wuce...
Tafiyar Sameer da kad’an wayar Sultan ta d’auki ruri, ganin mai kiran ya sanyashi sakin murmushi kana ya d’aga yana mai furta “Kaman nasan update d’in da zaki bani...”
Shiru ya d’an biyo baya alamu magana ake daga d’aya b’angaren....
Sultan ya kuma murmusawa kana yace “Saura k’iris burina ya cika, idan kuwa ya cika kada ki manta kinada babban kyauta domin kaw kin taka muhimmiyar rawa...”
Ya kuma murmusawa yana mai mik’ewa tsaye had’ida sakala hannu guda cikin aljihu alamun yana sauraren mai magana daga d’aya b’angaren...
A hankali yake shafan sajensa kana yace “INDA RAI burina gab yakeda cika...”
Ya saki dariya mai ‘yar sauti kafin sukai sallama ya katse wayar....

***

Kano

Nabila ta d’aga appointment letter d’in tana kuma duba cikeda murna, baki har kunne take fad’in “Addah Zulfah gaskiya nai miki murna ubangiji yasanya alkhairi ya kuma sa a fara a sa’a...”
Zulfah ta murmusa tana duban ‘yar uwar tata cikeda k’auna tace “Ameen Nabyn Mamy, amma ai ba yanzu zan soma zuwa ba sai na gama iddah...”
Nabilah ta d’an tab’e fuska tace “Oho dai at least kema zaki tsara rayuwarki yanzu babu tak’urin Yaya Hafiz balle na Hajiya da watsattsun k’annensa...”
Murmushin k’arfin hali Zulfah tai ba tareda ta furta komai ba...
Nabila ta dubeta a kaikaice tace “Kar kicemin har yanzu tunaninsa da mafarkin komawa gidansa kike..?”
Murmushin Zulfah ta sakeyi wanda da gani mai ciwo ne kana tace “Nabilah kenan, Yaya Hafiz bazan tab’a goge shi cikin tarihin rayuwata ba amma ki sani kaman yanda na ambaci tarihi tabbas ya zama tarihin, he’s already in the past, sannan koda ace babu dangantaka na zumuntan jini tsakaninmu aure ya had’a sannan kar ki mance akwai rabo tsakaninmu, Kausar ta kuma had’amu Nabilah... Hafiz Uban d’iyata ce Nabilah, we cannot change that...”
D’an rausayar da idanu Nabila tai kana tace “Haka ne amma nidai bazan daina k’irgen sauran kwanakin da suka rage aurensa ya sauk’a gaba d’aya akanki ba, Kausar kuma muddin Raiha na nan banida haufin zata kula da ita fatana dai kar yace zai d’auki d’iyarsa ya damk’a hannun wancan ‘yar tashan matar tasa ba...”
Zulfah tai shiru tana sauraren Nabila domin kaw ta tab’o mata yanda ke tsananin ciwo a gareta, duk randa ta tuna Hafiz na iya damk’ar rik’on d’iyarta hannun wata matar...
Kaman Nabilah tasan abinda take tunani ta d’an dafata ta shiga calming d’inta, a haka Aunty B ta shigo ta taddasu tana fad’in “Ga k’osai ‘yar la’asar da zafinshi yanzu Tatu ta sauk’e...” Ta k’arashe tana dire masu k’aramar parantin...
Aiko nan Nabilah ta dirk’o k’asa ta shiga cin k’osan tana dandalan barkono, Aunty B tace “Kidaici barkonon nan a hankali don zafi ne dashi...”Takai dubanta ga Zulfah tace “D’iyata zakisha kunun ne ta dama kafin ta tafi...”
Zulfah ta girgiza kai tace “A’a Aunty zan sha kunun ayan d’azu dai inaga dakwai saura a fridge..”
Ai bata gama rufe baki ba Nabilah ta mik’e ta nufi fridge tana fad’in “Su Aunty an iya waraya d’iyarki kawai kika sani, dama akwai kunun aya a gidan shine ko amin tayi toh wllhi rabona ne nasha nayi guzirin sauran..”
Aunty B tace “Eh dai so so ne amma son kai yafi, kiji na fad’a miki nafison Zulfah tah..”
Zulfah sai dariyansu take itako Nabila sai kwankwad’an kunun ayarta take tana lumshe idanu ko kulasu batai ba... Wayarta dake ringing ne ya d’auki hankalinta, ta nufo handbag d’inta a guje tana lalumen wayar take fad’in “Toh Mamyna na nemana nima, taga yamma tayi....” Aya ta sakawa kalaman nata ganin mai kiranta, tasan ba kowa bane illa bugun zuciyarta, domin kaw ganin bak’uwar lamba d’aukeda had’add’un lambobi yasa taji k’irjinta na bugawa, tasan shi kad’aine zataga kiransa taji hakan dukda bata d’aga wayar ta tabbatar da ko wanene ba..
Balcony ta shige sanda ta k’ara wayar a kunnenta su Aunty B da Zulfah suka bita da kallo ganin yanda kiran ya sanyata

Please Login or Register in order to submit comment