Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita a raye.... A lokacinda Mariya tai aure taci kuka sosai na rashin ‘yaruwarta wacce take magajiyar mahaifiyarta a tareda ita... Kun sani Babbar Ya itace tamkar mahaifiya a lokacinda babu mahaifiya.. Ban halarci aurenta ba, haka ban taka yanda take ba... Kuma ita batada ikon takowa yanda nake.... Harta Bara’atu da Dumba duk saida nai masu iyaka da Mariya matuk’a sun zab’i zama dani... Basu d’auki hud’uba ta ba dikda cewa Sun nuna min sunyi na’am da hukuncin da na gindaya masu.... Hakan sosai yake ci masu tuwo a k’warya musamman Dumba wacce suka taso tareda Mariya tamkar k’awaye, a b’oye sukan fita su tafi gidan Mariya bada sani na ba, hakan yasa basu yanke alak’a kwata kwata da ita ba kaman yanda na umarcesu...

D’an fasalai taja kad’an kana taci gaba da fad’in “Wata rana kwanta bacci nai mafarki da mahaifiyarmu tana kuka tana cewa na kasa rik’e mata amanan zuri’arta... A mafarkin nima Ina kuka Ina sanar da ita cewa Mariya itace taci amanata ta salwantar da Zuri’armu... Mama Hajja bata daina kuka tana fad’in bazata tab’a yafe min ba.... Wannan mafarki ya d’aga min hankali sosai, yasa k’iyayyar ‘yaruwata ya kuma tasiri cikin zuciyata, Mama Hajjah ta rasu batasan cewa Mariya ta tsiratar da kanta ta k’yale Fatima da Ma’aruf ta kasa kula dasu kaman yanda ta d’auka min alk’awari.... Koda na sake bacci mafarki na sakeyi Mama Hajja na cemin kece Babba ki kula dasu.... Ranan nayi zurfi cikin tinani na kuma d’au alwashin kula da sauran ahalinmu da suka rage koda ace bazan iya duban idanun Mariya nace na yafeta ba... Koda ace bazan iya kasancewa da ita inuwa guda ba, domin kaw ganin fuskar Mariya ba komai yake haifar min ba face tina iftila’in dana fuskanta had’ida mutanen da na rasa dik ta dalilinta....
Wani rana na tsinci tataunawar Bara’atu da Dumba suna cewa zasu tafi su duba Mariya dan a kwanakin bata gane jikinta... Hankalina ya tashi sosai hakan yasa nabi bayansu a sace har naji dalilin rashin lafiyarta juna biyu gareta, a lokacin tana d’auke da jaririn cikin d’anta na fari.... Koda naji wannan batu gida na koma ba tareda sunsan cewa na fita naji tattaunawar su da Mariya ba... Koda na dawo gida bayan kwana biyu sai naji inason na san halinda ‘yaruwata Ke ciki.... Na d’auki mayafi nayi nad’i irinta buzaye ta yanda babu mai gane kamanni na, na fice na nufi gidan Mariya.... Nan ma lab’ewa nai ina hangota daga tsakar gida tana gudanar da aikace aikacenta.... Shigarta d’aki da wuya kishiyarta Lami ta fito tana ‘yan waige waige tamkar maras gaskiya, ni kuma koda naga haka jikina sai ya bani akwai abinda wannan matar take k’ullawa, bansan mijin Mariya ya k’ara aure ba dik a tinanina Mariya ita kad’aice ashe mahaifiyarka ta tilasta maka auren Lami bayan Mariya ta shafe shekara guda tak a gidanka babu koda b’atan wata...”
Abbah ya jinjina kai cikeda al’ajabi domin kaw anyi haka, Mamani ita ta tilasta masa yima Mariya kishiya dan kawai ta shekara gidan miji babu juna......
Ya Abida taci gaba da fad’in “Hakan yasa mafarkin da nai da Mama Hajjah ya shiga dawowa kwanyata cewa na kula da ahalinmu.... Ana a haka naga Haule matar Alhaji d’an uwanka ta fito daga d’akin Lami suna k’usk’us suna cewa ta shige d’aki mu cika aiki.. Shegiya mai shegen munafunci da iyayi ita a dole ga matar so.... Malam yace wannan biso idan muka bisne a k’ofar d’akinta hardai yana cikin k’asa bai fito ba toh kuwa tabbas bazata haife abinda Ke cikinta ba saidai ya mutu a cikin cikinta amma bazai tab’a fitowa duniya ba kaman yanda wannan laya yake bisne a k’ofar d’akinta... Suka kuma sakin shewa had’ida tafe hannaye a hankali.... Lami taceda Haule maza ta fito tai mata rakiya kafin wani ya gansu... Jin haka yasa na kuma b’oyewa har suka fice... Naga wajen da sukai bison jikin d’akin Mariya, daga nan fitowa nai ina k’ok’arin ficewa a sad’ad’e na b’ata hanya... Toh fah a nan ne na kuma karo da wani tashin hankalin wanda ya tabbatar min cewa tabbas Rayuwar Mariya na cikin had’ari babba bama ita kad’ai ba harda kai Usman da jairinku dake cikin Mariya... Alhaji d’an uwanka da matarda ka girma ka santa a matsayin mahaifiyarka su na hango suna tattaunawa wata muhimmiyar magana da alama basuso kowa yaji kuma shakka babu naji sun ambaci Mariya da mijinta...Jikin yai sanyi sosai da ganin irin rayuwar da ‘yaruwata Ke ciki... A haka na koma gida Ina tinanin al’amarin... Washe gari na kuma b’adda kama ba tareda sanin kowa naje na toni wannan laya na canza da wata layar....”

Jikin Aunty Lami yaci gaba da tsuma maganar Malam ya fito cewa ABU A DUHU, dama ya sanar dasu muddin aka samu tangard’a wajen bisne wannan layar toh fah za’a haifo cikin kuma itama Mariya bazata mutu ba, sannan dik wani shirin da zasuyi bayan wannan haske bazai tab’a bayyana masu ba, sunyita cin karo da Abu a duhu, Wato ashe dai wannan mata ita ta toni wancan layar tasu... Muryar Ya Abidah ta sinkayo yanda taci gaba da fad’in “Koda nazo fitowa a sace na kuma cin karo da Mamani da kuma Baba Alhaji suna tattaunawa wannan karon tamkar shi yake tsoratar da ita, da alama D’an nata yasan wani Sirri nata da bataso kowa ya sani... Lab’ab’awa nai na saurari abinda suke fad’i wanda yai matuk’ar bani al’ajabi

Mamani rok’on Alhaji take tana fad’in “Alhaji ka bar zancen nan a nan Usman bazai tab’a sanin ba nice na haifesa ba domin kaw mahaifiyarsa ta jima da rasuwa kuma shid’in d’ah na ne....”
Alhaji ya kuma b’allawa Mamani harara kana yace “Kin jima kina ci mun fuska akan Usman, ni ne d’anki na asali amma kin d’auki soyayyar duniya kin basa, gabaki d’aya dukanmu ‘ya’yanki babu wanda kike masa soyayyar da kikewa Usman... Yanzu tinda matarsa ta sami juna biyu hankalinki ya kuma karkata kan Usman da iyalinsa...”
A hasale Mamani tace dashi “Toh naga kai dik matar daka aura sai wannan jarabebbiyar matar taka ta koreta... Ni ba matar Usman nake so ba jikana dake cikinta nake so zan kuma bata dik wani kulawa da take buk’ata muddin jikana na cikin jikinta...”
Baba Alhaji ya jinjina kai yace “Ni kuma na miki alk’awarin koda an haife wannan ciki sai na salwantar dashi, kuma baki isa kiceda Usman komai ba, dan wllhi kinji na rantse idan har kikai yanda yasan inada alhakin b’acewar d’ansa toh sai na tona miki asiri sai na sanar dashi cewa mahaifiyarsa ta jima da mutuwa kuma kece silan mutuwar ta... Bazai yuwu Usman yafini nasara a rayuwa ba....”
Ya Abidah ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Ga tsananin mamakina kuka naga Mamani tanayi tana rok’on d’an nata kada ya tab’a sanar da Usman cewa ba ita ta haifesa ba domin kaw mutuwa zatayi tabbas idan ta rasa soyayyan d’anta Usman.... Tabbas basuyi zaman dad’i da mahaifiyarsa ba amma tana jin k’aunar d’an data rasu ta bari tamkar ita ta haifesa.... Sannan k’annensu gaba d’aya sunfi k’aunan Usman samada Babban Yayansu Alhaji, Usman ya zamto tamkar uba a gidan tamkar shine magajin Alhaji Mahmood Mailafiya, girma soyayya da komai mashi ake badawa....”

Goggo Mairo ta Kazaure dake tsananin kuka ita ta katse Ya Abida da fad’in “Mamani dama D’an Yaya Hurera ya rayu bai mutu ba kaman yanda aka sanar damu dashi da ita duk sun mace... Shin dama naki d’an shine ya mutu... Innalillahi wa innalillahi raji’un...!!!”

Sabbin kuka ya ya kaure yayinda Mamani ta kasa d’ago fuskarta sai hawaye masu tsananin d’umi dake gangaro mata....

Ya Abidah taci gaba da fad’in “Wannan ne dalilin da yasa Alhaji ya tsani d’an uwansa Usman da zuri’arsa, Usman d’an uba ne a wajensu da ya d’auke soyayyar mahaifiyarsa da kuma ‘yanuwansa da suke uwa d’aya uba d’aya daga gareshi, hakan yasa yaji duk duniya baida mak’iyi kaman Usman kuma baida buri da ya wuce yaga Usman ya rayu cikin k’unci.... Mamani na hawaye a wancan lokacin taceda Alhaji taji ta gani tabbas bazata ce komai ba amma kada ya tab’a sanar da Usman wannan sirri nata domin rasa Usman na nufin rasa rayuwarta ne.... Wannan rana hankalina ya tashi sosai da jin wannan batu... Tin daga wannan rana Babu wanda yasan cewa ina bibiyan al’amran Mariya, duk wani shirin asiri da su Haule suke ina lalaltawa hakan yasa asirinsu bai tasiri akan Mariya saidai bokansu yace dasu *Abu a duhu* ba kowa yake b’atawa ba illa ni Abida .... A lokacinda aka haifi Ma’aruf nasan wad’annan azzalumai bazasu k’yale Mariya da d’anta ba tinda sun lashi takobin ganin bayansu nima sai na d’aura d’amaran wargaza dik wani shirinsu... Hakan ya hana Bokayensu ganin haske Saudi abu a duhu, wannan dalili yasa su Haule suka razana matuk’a da hidiman Mariya sukai tinanin tanada wani shirin da yafi nasu k’arfi.... Ganin bazasu daina jifarta da asiri ba yasa na yanke shawarin Bara’atu ta koma wajen Mariya da zama tinda ita Allah yayita mafad’aciya maras sanyi da tsoro ba kaman yanda Mariya ta kasance mafi sanyin hali a cikinmu ba.... Na kuma gargad’i Bara’atu cewa ta saka ido kan zaman da Mariya take a gidan mijinta da mutanen da Allah ya k’addara mata zama tare dasu....
A haka Bara’atu ta karanci Lami ta karanci duk wani wanda ke tareda Mariya... Su Lami da Haule basu daina jifar Mariya da d’anta Ma’aruf da asiri ba, dik asirin da sukai Bara’atu zata sanar dani zan kuma San hanyar da zamubi mu warware..... Kwatsam Mariya ta kuma samun ciki sannan har wannan lokaci basu daina jifarta da d’anta da muggan asirai ba, hakan yasa Bara’atu cewa anya bazamu d’auke Mariya daga wannan gida mai tarin had’ari a gareta ba dashike lokacin suna zama ne duka gida guda gidan marigayi Mahmood Mailafiya...
Duban Bara’atu nai kana Nace “Bara’atu bazamu raba Mariya da mijinta da d’anta ba ga kuma wani rabo ya kuma knno kai, mai yuwa farin cikin Mariya yana a cikin wannan ahalin ne.... Abunda zamuyi zamu b’ullo musu ta hanyar da basu tsammani bane bazamu bari suci gaba da cutar da ‘yaruwarmu da ahalinta ba.... Bara’atu tace min toh ya zamuyi Yaya ga tsohon ciki a jikin Ya Mariya kuma ko sati bamu jima da kwance k’ullin da suka bisne k’ark’ashin bola ba wanda aka linke takarda da harufan sunan Ma’aruf har sau uku dashi... Tabbas wad’annan mutane bazasu k’yaleta da d’anta ba, ga kuma wani rabon na zuwa... Ina tsoro kada a haifosa a wannan duniya mai kewaye da tarin miyagun mugaye...
Duban Bara’atu nai nace ta bani kwana biyu zansan yanda zan b’ullowa al’amarin.... Toh fah daga nan ne na tashi na tafi na samu Mamani... Sosai Mamani taji tsoro da mamakin cewa nasan sirrinta da bataso ya isa kunnen Usman har d’anta yake razaninta dashi.... Zama nai nace ta sanar dani gaskiya idan ba tanaso na tona wannan sirriga Usman ba... A haka Mamani ta sanar dani cewa Usman d’an mijinta ne marigayi, mahaifiyarsa auren zumunci akai mata da Mahmood Mailafiya, tabbas sun zuba kishi sosai a lokacinda suke tare matsayin kishiyoyo, koda aka auro mahaifiyar Usman sai Allah ya basu RABO a tare dikda cewa Mamani akwai d’anta Babba mai shekaru uku shine Alhaji.... Haka nan sukai goyon cikinsu tare tare kaman masu haifan tagwaye, wani ikon Allah wata haihuwarsu d’aya sannan Allah ya nufa suka haihu rana d’aya, toh abinka da zamanin wancan lokaci da ba damuwa da zuwa asibiti akai ba ungozoma guda ta karb’i haihuwarsu su duka biyu a gida, Allah mai yanda yaso sai ita mahaifiyar Usman Allah yai mata cikawa ya raya d’anta ita kuma Mamani Allah ya karb’i nata d’an ya kuma rayata... Allah kenan mai yin yanda yaso babu kuma wanda ya isa ya tambayesa dalili domin kaw shid’In buwayi ne gagara misali.....Ya raya wanda yaso ya kuma kashe wanda yaso... Toh nan ne Mamani ta amshi d’an Hurera data rasu ya maye gurbin nata d’an da shima ya rasu, ta shayar da Usman matsayin d’anta... Yayinda kowa yai zaton cewa Harira da d’anta gaba d’aya suka rasu... Bayan ita Ungozoma d’in data san wannan Sirri babu wanda ya sani harta Alhaji Mahmood bai sani ba, bayan wasu shekaru Ungozoma d’in taso su sanar da Alhaji Mahmood wannan batu amma fur Mamani tak’i tace Usman D’anta ne kuma babu wanda zaisan wannan Sirri akai rashin sa’a d’anta Alhaji ya lab’e yaji tattaunawarsu, Toh nan ne tsanarshiga Usman yai k’amari tinda yaji cewa ashe shid’in bama d’an mahaifiyarsu bane amma tafi fifitashi sama da sauran ‘ya’yanta sannan soyayyar da take masa har ya shafi d’ansa Ma’aruf gashi shi koda Haule ta samu cikin d’anta na fari Hafiz batai d’aukinsa ba sannan bata masa soyayyar da take wa Ma’aruf... Hakan yasa Baba Alhaji da matarsa Haule suka dad’a tsananta k’iyayyarsu kan wannan yaro Ma’aruf...
Na dubi Mamani nace nasan bakiso wannan Sirri naki ya isa ga Usman, kuma nasan kina k’aunar jikanki Ma’aruf baki k’aunar abinda zai samesa... Mamani ta jinjina min kai tace hakane... Na numfasa kad’an kana nace idan haka ne inaso mu k’ulla wani aminci na sirri.... Tace dani kaman yaya kenan...? Nace da ita inaso ki sanar da d’anki cewa lokaci yayi da zai kawar da Ma’aruf.. Kin yarda ya kawar da Ma’aruf amma da sharad’i... Sharad’in shine zai k’yale Usman da sauran zuri’arsa da zai haifa nan gaba shida iyalinsa su rayu cikin aminci...
Da mamaki Mamani ta dubeni kana tace bazata iya bari tanaji tana gani a halak’a Ma’aruf ba, zata iya basa rayuwarta... Nace da ita kaman yanda zaki iya basa rayuwarki toh haka nima zan iya basa tawa rayuwar.. Ki bar min ragamar komai nai miki alk’awari ni kuma bazan bari su salwantar da Ma’aruf ba... Zan sa yai nesa da wannan duniyar da aka jima ana farautar rayuwarsa.... INDA RAI wata rana zai kuma dawowa cikin rayuwarki bayan ya kub’uta daga sharrin wad’anann azzalumai.... Abu guda zaki min shine kisa d’anki ya yarda da sharad’in da zaki gindaya masa cewa zai k’yale Usman da sauran iyalansa su rayu cikin aminci... Kinga daga nan bamuda sauran damuwa... Ma’aruf yayi nesa dasu sannan zasu k’yale ‘yar uwata da ahalinta su rayu cikin aminci babu zullumi da d’ar d’ar d’in cutarwa...”
Sosai Mamani taci kuka jin bazata rayu tareda Ma’aruf ba amma hakan yafi mata idan har zai tsira daga sharrin Baba Alhaji wanda batada ikon magana akai sakamakon babbar makamin da yake dashi na sanin sirrinta... Na fad’a mata tin a wancan lokacin zan rufe sirrinta amma tabbas INDA RAI wataran wannan sirrin zai hak’o kanshi ya bayyana kanshi... Muka samu matsaya da Mamani akan haka, daga nan ni kuma na sami ‘yaruwata Bara’atu nace tasan yanda zatai ta sami yardarsu Haule ta nuna masu itad’in tana taredasu d’ari bisa d’ari za kuma ta taimaka masu su kawarda Ma’aruf....
Hakan kuwa akai Bara’atu ta sami su Haule ta sanar dasu tasan basu k’aunar Mariya kuma suna iayaka k’ok’arinsu ganin sun sabautar da ita da ahalinta, toh asiri dai baya tasiri akan Mariya dan Mahaifinsu yanada wani lak’ani kuma ma ita d’aya ya bayar shiyasa asiri baya kamata, shiyasa dik asirin da suke mata bokayensu Ke sanar dasu basa ganin komai saidai ABU A DUHU... Da shike Allah yaso b’atar masu da tinani sai suka yarda cewa Mariya tanada wani shiri na musamman shiyasa asirinsu bai tasiri akanta da d’anta abinda zasuyi su jefata cikin k’unci shine su kawar da Ma’aruf a doron k’asa... Hakan shine kawai zai k’untatawa Mariya... Koda su Haule suka tamabayeni maiyasa ina ‘yaruwarta zasu yarda su had’e kai da Bara’atu ta zamto Aminiyar su ta sirri sai ce masu tai sabida Mariya itace sanadiyar rugujewar ahalinsu fansa zata d’auka ma ahalinta da suka rasa ta sanadiyar Mariya... Da wannan batu su Haule suka yarda da Bara’atu... Mijin Haule ya sami Haule da batun ya bata wuk’a da nama ta kassara rayuwar Ma’aruf... Haule ta kuma jin dad’i dan ita da mijinta shafi guda suke... Bara’atu tazo ta sameni da batun su Haule suna yunk’urin kassara Ma’aruf daga nan ni kuma muka shirya yanda zamu fitar dashi cikin duniyar da ake k’aunar ganin bayansa.... Da fari mun yanke shawarin Dumba ta tafi dashi can k’asar Mali yai nesa da gida har Allah ya kawo sanda zai dawo don munyi imani INDA RAI DA RABON watarana zai kuma dawo mana...

Daidai nan Bara’atu ta cab’i zancen da fad’in “Mun shirya had’uwa dasu a kasuwa yanda na tabbatar masu matar da zan bata Ma’aruf ‘yar k’ungiyar shan jini ce.... Kuma Ma’aruf zai fice a rayuwarsu har abada... Sun yarda dani Sun yarda duk zan aika abinda nace.... A kasuwa na janye hannun Ma’aruf da sauri sanda ake k’ok’arin kawo d’aukiwa Mamy sakamakon haihuwa da yazo mata... A tasha na had’uda Dumba na damk’a mata Ma’aruf sai kuka yake... Nima zuciyata ta karaya... Tsugunawa nai na rungumesa kana nace INDA RAI DA RABON mu sake had’uwa Ma’aruf d’ahna... Na rok’i Dumba kan cewa ta kula dashi da kyau.... Dumba tace dani itama Ma’aruf d’anta ne kuma zatai duk yanda zatai taga ya samu rayuwa mai kyau da inganci... In sha Allahu Allah zai raya Ma’aruf. kuma INDA RAI wata ran zai dawo ya fuskanci kurayen da sukai farautar rayuwarsa a lokacinda basuda k’arfin halak’a shi.... Haka muka rabu da Dumba tana rungume da Ma’aruf da har lokacin kuka yake yana ambaton Mamynsa...”
Ta juyo tana duban Mamy da hawaye suka wanke mata fuska lokaci guda taci gaba da fad’in “Wannan shine dalilin da yasa na d’aukake ahalinki na kuma sadaukar da rayuwata ga ahalinki Mamy... Na sani da zuciya d’aya muka tseratar da Ma’aruf amma daga baya zuciyata ta kasa aminta da cewa hakan ba babban laifi bane... Na kasa saka ma zuciyata hakan ba zalunci bane mai girma .... Shiyasa nai komai dan naga kin kasance cikin Farin ciki... Shiyasa ban tab’a rabuwa dake ba... Sabida girman laifin da na aikata a gareki ‘yaruwata....” Ta k’arashe tana mai duk’awa saman gwiyoyinta gaban Mamy wacce ta kasa tab’uka komai sai hawaye...
Wajen yayi tsit duk wanda yace bai zibda hawaye ba yayi k’arya.... Abbah ma kasa tab’uka komai yai sai jin abubuwan yake tamkar a shirin film, ta ya Mamani zata b’oye wannan babban al’amari a gareshi... Ai girman mahaifiya ta wuce wasa... Ya cancanci yasan wacece mahaifiyarsa ta asali....
Ya Abida ta isa ta d’ago Aunty Bara’atu, hawaye na gangaro mata take girgiza kai tana furta “Idan da mai laifi ba Ke bace Bara’atu... Tabbas nice mai laifi... Shin na aikata haka ne domin ‘yar uwata ta d’and’ani abinda naji na rashin d’ah ko kuwa na aikata hakane dan ina tsoron kada na kuma rasa wani d’a a karo na biyu... Ina tsoron kada watarana makircinsu yai tasiri akan Ma’aruf k’arami... Mariya a yau na rok’eki gafara ki yafe min.... Ki gafarta min ‘yaruwata....!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Sameer dake gefe ne ya share hawayen da suka jik’a masa fuska kana ya k’araso ya d’ago Aunty B ya kuma kamo hannun Yaya Abida ya had’e dana Mamy ya rungumesu gaba d’aya, lokaci guda yake furta “A naku fahimtar kunyi Hakane ne ba don komai ba sai don ku cire Ma’aruf cikin k’ingurumin daji mai cikeda duhuwa da tarin had’ari... Na gode maku gaba d’aya, Allah ya k’addari bazan girma taredaku ba amma cikin rahamar Sa da buwayarsa sai ya kuma dawo dani kama yanda kukace INDA RAI Da RABON watarana na dawo gareku zan dawo... Abinda nakeson ji yanzu shine shin ina Ma’aruf Babba wanda naci sunanshi shin ya akai ya salwanta... Sannan maiyasa aka d’aura alhakin b’acewarsa kan mahaifiyata....?”

Wannan karon Mamy ce ta dubesa kana tace “Ni ce zan baka wannan labarin Ma’aruf domin kaw a hannuna Ma’aruf ya b’ace ko nace ‘yan ta’addan suka kashesu shida Fatima....”
“Wacece Fatima..?”
Sameer ya tambaya
Mamy ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Fatima itace d’iyar mahaifiyarmu k’arama, kaman yanda na sanar dakai a baya cewa mahaifinsu Soja ne zuwansa Mali ya auro mahaifiyarmu, nida Yaya Abidah acan k’asar Mali aka haifemu bayan mun dawo Nigeria aka haifi Bara’atu da Kuma fatima... Sanda mahaifiyarmu ta haifi Fatima girma ya soma kamata dan lokacin har Yaya Abida tai aure a nan Kano ya auri wani Alhaji Abbas Maidubabe kuma har Allah ya albarkaceta da d’anta k’wara d’aya mai suna Ma’aruf sannan Ma’aruf har ya soma girma dan yakai kusan shekaru shida zuwa bakwai a k’alla... Mahaifin Ma’aruf Alhaji Abbas Maidubabe attajiri ne sannan yana yawan tafiye tafiye na kasuwanci zuwa mak’wabtan k’asashe a wancan lokacin.... Mukan taho nan Kano hutu wa Ya Abida daga can Jada garin mahaifinmu.. Wata rana munzo mata hutu ta daga zata bimu Jada taga gida sannan takai Ma’aruf ma yaga garin mahaifiyarsa, dad’ida k’ari ga mahaifiyarmu data kusa haihuwa ko yau ko gobe... Da k’yar Alhaji Abbas ya amince kan cewa ta tafi taredamu musamman da shike harda d’ansa Ma’aruf a tafiyar, yaron da ya k’wallafa ransa akanshi sabida shi kad’ai Allah ya bashi ga girma da ya soma kamashi... Ma’aruf shine magajin shi shine sanyin ianiyarshi shine yake d’aga ido ya kalla yaji sanyin cewa ya haye gorin ‘yanuwansa da suka addabeshi a baya cewa shid’in shine bai haihuwa dan dik matar data aureshi k’arshe tafiya take ta k’yalesa muddin tana son haihuwa. Ashe RABON shi na tareda Ya Abida... Wani zuwan shi Jada sunkai kaya ya ganta ya aureta har Allah ya azirtasu da Ma’aruf, kuma tin daga kan Ma’aruf shikenan ko b’atan wata bata sake ba.... Kaman yanda na fad’a maku cewa mahaifinmu Soja ne, yayi yak’i yasha fama sosai da miyagun ‘yan ta’adda, ashe suna yunk’urin kafawa mahaifin mu tarko ganin shid’in jajirtacce ne akan aikinsa.. Ya kafa masu k’ahon zuk’a ya hanasu sakat... A ranar da muka iso gida Washe gari suka shigo har cikin gidanmu suka kashe mahaifinmu, ga mahaifiyarmu da tsohon ciki... Haka muka fita a fujajan Muna neman hanyar tsira ganin muma sun nufomu suna yunk’urin kashemu... Da k’yar muka samu muka b’uya basu ganmu ba, dan dama koda sukazo kashe mahaifinmu saida ya tabbata yayi yanda zamu samu tsira tinda yasan shi suke farauta.... Tashin hankali maras misaltuwa muka shiga, da k’yar muka samu muka isa asibiti sabida mahaifiyarmu da har ta soma zuban jini... Kan kace mai akace saidai ai mata aiki a cire abindake cikinta... Hakan kuwa akai... Koda mahaifiyarmu ta farka sunan mahaifinmu kawai take kira tana fad’in sun kasheshi, ganin mahaifiyarmu haka ya kuma karyar mana da zuciya.... tashin hankali dai da ba’a saka mata rana., A haka mahaifiyarmu ta barwa Yayarmu Abidah Wasiya cewa ta kula damu ko bayan babu ita dan tanaji bazata tashi ba... Haka Ya Abidah taita kuka tana sanar da ita cewa in sha Allahu zata tashi kuma zamu tsira gaba d’aya... Ita dai mahaifiyarmu bata daina cewa ta kula damu ba.... Ta tabbata mun tsira daga hannun wad’ancan azzaluman... Kud’in asibiti ya k’are mana ga mahaifiyarmu kwance babu lafiya ga shi k’anin mahaifinmu da ya rage mana shima ba wani k’arfine dashi ba, uwa uba a wancan lokacin babu hanyoyin sadarwa masu sauk’i na zamani balle Ya Abidah ta sanar da maigidanta halnda ake ciki... Gashi k’wakk’waran motsi bamu isayi ba dan idon ‘yanta’addan akanmu yake... A haka Allah yaima mahaifiyarmu cikawa..!!” Wannan karon kowa ya tsane hawayen da ya gangaro masa, Mamy taci gaba da fad’in “Toh daga wannan lokaci Baffah Kawure yace mu tafi muyi nesa da ahalinsa kada laifin d’anuwansa ya shafesa... Dan da k’yar ya yarda ya amince suka tsaya shida Ya Abida dan ganin anyiwa mahaifiyarmu sitira an kaita makwancinta na gaskiya... Sanin cewa nemanmu ake ruwa a jallo yasa nace Yaya ta bari mud’in mu fara gaba nida Dumba da kuma yaran gaba d’ai Bara’atu, Ma’aruf saiko ‘yar jaririyar k’anwarmu, sosai Yaya Abida tamin kashedin cewa na kulada Ma’aruf da Fatima... Nai mata alk’awarin cewa zan kula dasu da yardar Allah kuma bazan bari wani abin ya samesu ba... Muka fito a fujajan muka nufi tashan mota jaririyar tana goye bayana yayinda hannuna ke rik’eda Ma’aruf... Ashe basu bar unguwar ba akan idonsu muka fito zamu gudu, ganin haka yasa naceda Dumba mu raba hanya dan mu

Please Login or Register in order to submit comment