Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunk’arota ba.... Kaicon rayuwa mai cikeda tarin son zuciya... Lallai yau ta kuma yarda makirci makaranta ne mai k’unshe da azuzuwa iri daban daban... Ta kuma yarda da wannan hausar da akace duniya tafi gabaruwa iya jima....

Naja’atu dake rakub’e gefe tana kuka sosai, k’arasowa tai ga mahaifiyarta tana fad’i cikin kuka “Hajiya lokaci yayi da zaki yada makaman yak’inki Ki tuba kibi Allah Ki yarda shikeda cikakken iko akan komai....!”
Haule na tsananin kuka wanda bata tab’a yin irinsa ba ta rungumo Najah tana ci gaba da fad’in “Naja’atu Yayanku Yayanku Najah... Najah sun k’ullawa Hafiz d’ina sharri.....!”

Ta zabura da sauri tana janyo rigar Baba Alhaji take fad’in “Alhaji karka bari wannan azzalumar da d’iyarta su k’ullawa d’anmu sharri... Kai kanka kasan Hafiz ba d’an ta’adda bane koda ace yanada muguwar zuciya... Alhaji ka taimaka kaje kaima jami’an tsaro magana... Laifin garkuwa a k’asar nan ya zama babban laifi karka bari a kama d’anmu da ita....!”

Fincikewa Baba Alhaji yai yana watsa mata muguwar kallo daga yanda take duk’e k’asa “Uban da ya aikesa ya aikata laifin... Dama tinda naga ya nace sai ya maida Zulfa’u nasan cewa bak’ar zuciyarsa da yayi gado a wajenki bazai barsa ba, dan haka tsuntsun da ya janyo ruwa shi ruwa ke bugu, babu hannuna ciki... Wayasani ma ko tare kuka k’ulla kedashi tinda dama kowa ya sani bak’ar makirace ke....!”
Magajiya na murmushi ta shiga janyo Baba Alhaji tana fad’in “Muje Dalin Dalin... Muje karma ranka ya b’aci kaji koh....!”
Ta waigo tana duban Haule dake duk’e tana duban mijinta cikeda al’ajabi kaman ba tare suka jima suna k’ulle k’ullen makircinsu ba..... Magajiya tai mata gwalo had’ida kashe mata idanu guda ta janyo hannun Baba Alhaji yabi bayanta kaman wani soko....

Haule dake duk’e wajen wane irin kuka ne mai ban tausayi taji na fito mata, Sahariyya da akai komai gaban idanunta itama, kuka ta fashe dashi daga yanda take kwance mai ban tausayi.....

****



Tsaye Engr yai cikin parlorn yana amsa kiran jami’an tsaron, bayan sun ida wayar ne yaji shigowarta tana tafiya tana karo da k’ofa ita kad’ai.... Mamaki ya cikasa ganin irin yanayin da Muhibbah ke ciki na tsananin maye.... Engr yayo kanta da sauri ganin zata kifa a k’asa garin tangad’i.... Saurin tallafota yai yana binta da kallon mamaki....
Murya can k’asan mak’oshi yake furta “Maye.... Muhibbah...!!”

D’agowa tai a galabaice cikin tsananin maye tana dubansa, lokaci guda ta tintsire da dariya tana mai nunasa da ‘yar yatsa take fad’in “Wai da gaske ka auri wannan kucakar yarinyar....? Ma’aruf da bakinka kake fad’a min kayi aure....??” Ta kuma fashewa da dariya tana mai ci gaba da layi, har lokacin Engr na rik’eda ita yana duban ikon Allah, abinda yakeji wai Wai akwai mata mashaya sai gashi nan har cikin gidansa..... K’ok’arin janyota zuwa cikin parlorn ya soma amma tak’i shigewa sai faman nunasa da yatsa take tana fad’in “How... dare you... Ma’aruf.... How could you.....?” Tana maganan tana nunasa da yatsa tana tangad’i.... Lokaci guda hawaye suka soma gangaro mata sanda taci gaba da fad’in “You’ll never be Happy Ma’aruf... Nai maka.... Alk’awarin bazan tab’a barinku ku kasance cikin farin ciki ba.....is a promise.... Kuma bari kaji na fad’a maka, bazan bar maka ‘ya’yana ba... I’m leaving with them, kaima ka sani ni ba matsiyaciya bace... Inada dukiya... Kuma dik k’asar da nakeso mu rayu da yarana zan tafi dasu.... Horon da zan maka kenan shine bazaka sake sakasu a idanunka ba..... Wannan alk’awarine....!!!” Ta k’arashe tana mai zubewa cikin jikinsa alamun bacci yayi gaba da ita....
Azata yai a kafad’arsa ya haura da ita sama d’akinta... Saman gado ya shimfid’ata had’ida gyara mata kwanciyar.... Yai zaune gefenta had’ida k’ura mata idanu tausayinta na d’awainiya dashi... Ya sanya ma ranshi zafin kishi ne ya sanyata aikata abinda ta aikata, baiji har cikin zuciyarsa ta jima tana ta’ammudi da miyagun k’wayoyi.... Sauk’e ajiyan zuciya yai had’ida k’urama drawer dake gefe idanu.... Kaman wanda aka sinkaya ya k’arasa ya janyo drawer d’in.... Gabansa ne yai mummunar fad’uwa sakamakon ganin tulin gidajen kayan maye da akai amfani dasu suna zubowa.... Mamaki ya cika zuciyarsa ya shiga d’aukan ledoji da kwalayen yana gani mamaki da fargaba fal zuciyarsa..... Cikin sauri ya kaikato yana duban Muhibbah dake bacci wasted zuciyarsa na kuma tsinkewa, lokaci guda yaci gaba da juya kwalayen yana ambaton Allah a hankali... Hakan na nufin Muhibbah ba wai yau bane ta saba ta’amuddi da miyagun k’wayoyi kenan... Ya dafe kansa a hankali yana mai karanto innalillahi.... Zuciyarsa naci gaba da harbawa... K’aran shigowar sak’o cikin wayarta da ya jiyo daga cikin jakkanta ya sanyashi saurin janyo jakkan kana ya ciro wayar... K’ura ma sak’on idanu yai zuciyarsa na kuma tsinkewa...
Bash ne ya turo mata sak’on yana sanar da ita rana iti yau zasu fitar da huge amount of chocolates ta shagonta so ta zama ready.....

Ya karanta yafi sau abinda yafi yana nanata chocolates cikin zuciyarsa... Haka kurum yaji kalmar chocolates bai kwanta masa ba tinda yasan Muhibbah Manyan shagunan kayan k’arau na mata takedasu har guda biyu babu wani shagonta da ya danganci abin ci.... Ya kuma juya wayar yana mai kuma karance sak’on.... Take wani tinani ya fad’o masa, yai saurin k’arasawa ya d’auki yatsarta ya shaga jikin wayar nan wayar ta bud’e.....

Engr yaci gaba da duba sak’onni da tarin kira dake cikin wayar wanda akasarinsu daga Bash ne saiko k’awarta Shamzy.... Sosai sak’onnin suka basa tsoro da mamaki... Kenan Muhibbah bawai shan miyagun k’wayoyi take ba har safaransu zuwa k’asashen k’etare take... Wannan shine sana’arta, shine sana’ar data b’uya bayansa.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... This is a serious crime... This is terrible, abinda yake gani is just horrible...!!! Matarsa uwar ‘ya’yansa itace mai safaran k’wayoyi.... Take yaji wane irin gumi na karyo masa... Ya maido da dubansaga Muhibbah da har lokaci ko motsawa batai saima minshari da take sakewa d’aya na bin d’aya.... Take yaji zuciyarsa nai masa wane irin k’una.... Safaran miyagun k’wayoyi... Matarsa criminal ce kenan.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Mai take nema haka a duniya da tsanani da har zata jefa kanta cikin irin wannan musiba... Ya mik’e a hankali hannayensa hard’e a bayan ya k’arasa har gabanta yana duban kyakkyawan fuskarta.... Ya duk’a a hankali had’ida kamo hannayenta... Har lokacin bai janye idanunsa daga barin duban nata ba...
Cikin wata irin dashesshiyar murya yake furta “Why...? Why Muhibbah...? Mai yasa kika zab’i wannan rayuwar... Maiyasa kika zab’i jefa kanki a halak’a... Menene bana miki da har sai kinyi sana’ar saida miyagun k’wayoyi... Ta ina na rageki Muhibbah...? Tell me na rageki da wani abu ne...? Meyasa Muhibbah...? Meyasa bakiso na cika ma Baba alk’awarin da na d’aukar masa....Why are you so stubborn...?!” Ya k’arashe cikin d’an d’aga murya tamkar tana saurarensa....
Ya jima a haka yana tinani kala kala had’ida sak’e sak’e da warware warware... Shid’in jagorancin Al’umma yake yunk’urin yi... Gyara daga kansa ya kamta a soma gani... Zai dik yanda zai ya tabbatar ya kawo k’arshen wannan ta’addanci da matarsa ta tsinci kanta ciki... Fatansa Allah yasa Muhibbah batada hannu cikin fitar da k’wayoyin watak’ila hukuncinta yayi sauk’i... Fatansa Allah yasa amfani kawai k’awayenta masu fitar da k’wayoyin suke da shagonta... Muddin aka kama Muhibbah da laifin fitar da muggan k’wayoyi baisan ya zaiyi ba zaiji tamkar yayi failing Babansa ne.... Ya dafe kansa a hankali yana ambato Allah... Lokaci guda ya tsinci kansa yana mai d’aurawa karan kansa laifin halinda Muhibbah ta tsinci kanta ciki... Ji yake tamkar gazawarsa ne watak’ila ya jefata cikin wannan mummunar k’addara.... Da wannan tinani ya mik’e ya fice daga d’akin....

***

ABUJA

Daga yanda Daddy ke kwance cikin d’akin saman gado suna iya hangosa idanunsa a lumshe suke har yau, kana iya hango na’urorin da sukai k’awanya wa Daddyn....baka sauraren komai sai k’aran sautinsu dake tashi a hankali....

Nabila takai dubanta ga Khalid dake tsaye gefenta yayi k’uriwa mahaifin nasa... A hankali takai hannunta had’ida d’aurawa saman nasa, ya d’an juyo yana dubanta, lokaci guda yakai d’aya hannun nasa ya d’aura saman nata... Nabilah ta k’ak’aro murmushi ta sakar masa lokaci guda take furta “I know you can make it through... I know my bear is very strong...” Ta d’an kuma matsowa kusansa kad’an kana tace “I’m here for you.... Kaji....!”
Saurin rungumeta yai tsam cikin jikinsa kana ya soma fad’in “I don’t know what I do without you teddy bear... Thank you for being here... I love you....!”
A hankali taji bakinta na furta “I love you too my bear....”

Ammi, Siyama da kuma Yesmin da k’arasowarsu cikin ICU d’in kenan tareda jagoranci wata nurse mutuwar tsaye sukai suna kallon Khalid da Nabilah dake rungume cikin jikin juna.....


SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_





*100*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*







K’aranda Yesmeen ta saki ya sanyasu waigowa babu shiri a tsananin firgice, daga Nabilah har Khalid dubansu suke da tsananin mamaki dan basu tsammaci ganinsu kwatsam haka ba.... Nabilah tai saurin matsawa daga jikin Khalid tana k’ok’arin sadda kanta k’asa....
Yesmin taci gaba da nunasu da yatsa tana fad’in “Ammi kin gani koh... Mayyar nan har taji labari ta biyosa mu bamuji ba.... Wllhi Ammi yau karki yarda ki bari ta fice a asibitin nan ba tareda kin masu iyaka na k’arshe ba...” Ta had’iyi sauran zancen nata akamakon wane irin muguwar kallo da ya jefa mata, a hankali yake takowa har ya k’araso gaban Ammi yana k’ok’arin had’o kalaman da zai soma mata dasu.... Sukam Ammi da Siyama har yanzu dai mutuwar tsaye sukai suna dubansa shayeda tsananin al’ajabi....

Khalid ya d’an fuzar da huci a hankali kana yace “Amm...Ammi barka... Da zuwa... I didn’t know you were coming... Jikin Daddy da sauk’i... Come muje ki ganshi....!” Ya k’arashe dik a d’an daburce yana k’ok’arin janyo hannunta saidai ko gizau bata motsa ba..... Cak shima ya tsaya yana duban Nabilah da yake facing d’inta daga yanda take tsaye ga hannunsa rik’eda na Ammi amma ko motsawa tak’iyi.... Saida ya had’iyi wata miyau kafin ya iya kaikaitowa a hankali yana dubanta ga tsananin bugu da k’irjinsa keyi, shi kanshi yasan kawai yau ko mai ta fanjama fanjam ne... Siyama ce ta sami zarafin cewa “Ba sai kace mana jikin Daddy da sauk’i ba, wanda suka fika damuwa su sanar damu jikin nasa da sauk’i sun sanar damu... Khalid what’s all this.... Meke faruwa a nan ne wai...?”
A kaikaice ya dubeta fuska babu walwala yace “Wait Siyaam... Are you seriously asking me that..? Baki ganin Daddy a kwance... ... Well, let me remind you idan kin mance mai ya kawo Ki nan.... Our father got into an accident Siyama, look kalli cen, gashi cen a kwance...!” Ya k’arashe yana nuna mata d’akin da Daddy Ke kwance wanda suna iya hangosa ta cikin glass...Cikin fad’a fad’a yai maganar...

Siyama dake faman aika masa mugun kallo tace “Don’t you dare take it out on me, ba wannan nake tambayarka ba... Mai wance tantiriyar maras kunyar k’anwar Sameer d’in takeyi a nan... And why are you two together...?”
Yesmin dake k’ok’arin lab’ewa bayan Ammi tace “And they’re even hugging each other...!” Ta k’arashe murya can k’asan mak’oshi tana kuma b’oyewa bayan Ammi da har wannan lokaci bata tanka ba....

Dafe da kunkuminsa kurum yake dubansu, yama rasa mai zai masu banda dannawa Siyama da Yesmin muguwar kallo da yake... Siyama ta kuma ambato sunansa, saidai kafin takaiga cewa wani abu Dr Hameed ya shigo cikin ICU d’in Aunty Daula na biyedashi yana ci gaba da fad’in “Zamu iya cewa mijinki is out of danger a halin yanzu, sabida munga jikin nasa na amsar treatments..... “ Dr Hameed yai birki ganin mutane tsartsaye carko carko a lobby d’in.... Ita kanta Aunty Daula tsaye tai tana kallonsu gaba d’aya wanda ko ba’a ce mata ba tasan su Ammin Khalid ne dan tasansu a hoto... Gabanta yai wani irin yankewa ya fad’i.... Siyama da ta kuma kaikaitowa sosai tana k’are mata kallo daga sama har k’asa a hankali ta soma takowa har ta K’araso gabanta... Ta juyo ta kuma duban Khalid dake faman aika mata mugun kallo, murmushi Siyama ta saki a hankali tana kuma duban Aunty Daula... Lokaci guda take furta “So, is she the one...?” Tai maganar tana nuna Aunty Daula da yatsarta manuniya a wulak’ance.... Saurin takowa gabanta Khalid yai yana k’ok’arin janye Siyama yake fad’i a hankali “That’s enough Siyama, don’t make a sin here...!”
Fincika Siyama tai tana huci take furta “Don’t you dare Khalid... Let me go... Ka sakar min hannu nace... Tell me is she the one... Itace matar Daddy da yaci amanar Ammi da ita... Yarinya k’arama haka, yarinyar da bata shige ta zama d’iyar cikinsa ba... Tell me Khalid is she our father’s wife...?!!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji tana huci...

A zuciye Khalid yace “Yes... Yes!! She’s our father’s wife Siyama, and don’t you dare disrespect her..!!!”
Girgiza kai kurum Siyama take tana duban Khalid da kuma Aunty Daula, lokaci guda take furta “Unbelievable..! This is crazy... This isn’t happening...!!!”

Khalid dake tsananin huci har lokacin hannun Siyama na cikin nasa janyota ya somayi yana fad’in “Lets get out of this place.... We need to talk...!”

Ganin haka yasa Nabilah saurin k’arasawa kusan Aunty Daula dan tana iya hango tashin hankali k’arara saman fuskar Aunty Daular....

Siyama kaw wani irin fincika tai ta fuzge hannunta daga rik’onda Khalid yai mata tana binsa da wani irin duba, lokaci guda ta maida dubantaga mahaifiyarta da har lokacin ganin abin take tamkar a film... Siyama ta k’arasa kusan Ammi da sauri tana fad’in “Ammi kina ganin abinda ke faruwa... Ammi kina ganin irin cin kashin da Daddy yai mana... How dare he zai auri k’aramar yarinya irin wannan... Yarinyar da he’s old enough to be her father..!”

“SIYAMAAA!!!” Khalid ya daka mata tsawanda har saida ya tuna asibiti suke kuma asibitin ma ICU....

Dr Hameed ya d’anyi gyaran murya kad’an kana yace “Ammm inaga zaifi kyau idan kuka fita kuka tattauna a waje, coz this is an ICU please....”

Siyama ta watsa masa muguwar kallo kana tace “Kai dalla yiman shiru... Sai mai idan ICU ne... So what..!!” Ta k’arashe tana mai kuma takowa gaban Aunty Daula saidai tuni Nabilah tasha gaban Aunty Daula tana fuskantar Siyama dake tsananin huci kai kace kwand’arawa Aunty Daular mari zatai...

Siyama bata daina huci ba take aika masu muguwar kallo lokaci guda take furta “Ke kuma asuwa da zakizo kisha gabanta.. Ko so kike na had’a dake...?!”

Nabilah ta murmusa kad’an kana tace “Kiyi hak’uri akwai majinyata cikin wajen nan, ciki harda Daddy... Kiyi saving dik wani hayaniyarki har mu fice daga nan please...!”

Da tsananin mamaki Siyama ke duban Nabilah baki sake, bama ita kawai ba, harta Yesmin kallon mamaki take bin Nabilah dashi... Bud’an bakin Siyama sai cewa tai “Ke k’aramar karuwa mai bin maza har gida... Ke bakiji kunya ba, mu kamaki kina manne jikin namiji.. Har kinada bakin fad’i ma wani gaskiya...!”

Khalid da zuciyarsa Ke tsananin tafasa ya tari zancen da fad’in “Siyama idan baki respecting Aunty Daula a matsayinta na matar babanki ba zaki bata girma a matsayinta na Aunt d’in mijinki Sameer... And don’t you dare... Kar ki kuskura ki sake kiran matata karuwa... Wannan ya zama na k’arshe...!”

Yanzu kam gaba d’aya sun kuma shiga duhu... Daga haka janyo hannun Nabilah yai yana mai fad’i mata a hankali ta fice da Aunty Daula sai handle situation d’in.... Nabilah ta jinjina kai kana ta isa ta kamo Aunty Daula da har lokacin bata iya tab’uka komai ba sai duban abin take tamkar a film...

A d’ari Siyama ta tare hanya tana fad’in “Suje ina... Suje ina... Khalid what’s all this please... Please tell me ba gaskiya bane... Khalid kana so kacemin wannan matar k’anwar mahaifiyar Sameer ce... Sannan kaikuma kayi aure... Ka auri k’anwar Sameer... Khaleed please... Juts what are you trying to tell us...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.....

Jinina kai Khalid yai a hankali kana yaceda Nabilah su fice... Nabilah rik’eda hannun Aunty Daula da ko shakka babu hawayene Ke d’iga a idanunta suka rab’a ta gefen Siyama suka shige....

Khalid ya dubi Siyama dake tsaye tana bin bayansu Nabilah da Aunty Daula da kallo da har saida suka b’ace mata “Haka ne Siyama... Dik abinda kikaji gaskiya ne....” Ya tako gaban Ammi dake tsaye wajen tamkar ruwa ya shanye kana ya d’an risina ya kamo hannayenta “Ammi...! Ammi d’ago ki kalleni please...!”
D’agowa tai tana duban Khalid tamkar wanda aka canza sa, duban rashin sani take masa da idanunta da suke tab da tarin k’walla....
Jikin Khalid yai matuk’ar yin sanyi, hannayenta cikin nasa yake furta “Ammi... I’m sorry, you had to find out like this.... I’m sorry I couldn’t tell you earlier, and I take full responsibilities of everything that’s happening, let’s talk somewhere kinji Ammi na...!” Ya k’arashe cikin murya mai rauni...

Ga tsananin mamakinsa shafa fuskarsa Ammi ta shigayi tana binsa da kallo tamkar wanda ya b’ata ya dawo, lokaci guda take girgiza kai tana furta “Khalid kace min ba gaskiya bane... Son kace min k’arya suke Daddynka baida mata bayan ni... Kuma kaima bakai aure ba koh... Kamin magana Khalid..!!” Ta k’arashe tana jijjigasa hawaye na gangaro mata...

Khalid da jikinsa yai matuk’ar yin sanyi jinjina mata kai ya shigayi a hankali yana mai furta “Ammi da gaske ne... Dik abinda kikaji da gaske ne... Ammi Daddy yanada wata mata bayan ke, and not only that... Daddy yanada wasu yaran bayan nida Siyama... And...” Ya d’anyi birki kana yaci gaba da fad’in “And Nabilah is my wife Ammi... Matata ce yanzu..!”

Girgiza kai kurum Ammi take tana dubansa cikin rashin yarda, ga wane irin huci da take sakiwa... Lokaci guda ta finciki hannayenta cikin nasa kana ta nufi d’akin da Daddy ke kwance, dafe glass d’in dake jikin ginin d’akin tai tana hangosa ta cikin glass d’in daga yanda take tsaye... lokaci guda wane irin kukan da babu zato b’alle tsammani na fito mata, cikin karaji take furta “How dare you... How could you.... Ta ya zaka min haka... Ta ya zaka min haka Ahmad.... Ka tashi,,,,Nace ka tashi ka sanar dani duk wad’annan abubuwan dake faruwa ba komai bane face k’arerayi....!” Ta shiga bugun glass d’in da iyaka k’arfinta tana ci gaba da fad’in “Ka tashi Ahmad... Ka tashi ka sanar dani k’arya ne... Wllhi bazaka mutu ba sai ka tashi ka sanar dani da bakinka kalan cin amanar da kamin... Ka tashi nace..!!!!” Ba Khalid dake k’ok’arin janyeta tana tarjewa ba harta Siyama yanda Ammi ta fice gaba d’aya a giya ya firgitata... Babu shiri ta taho tana taya Khalid suna k’ok’arin janye mahaifiyarsu..... Yesmin kam har yanzu ganin abin take tamkar almara Wai her Kay ne ya auri yarinyar nan...? Ai tuni ta fice tabi bayansu Nabilah....

Nabilah da Aunty Aunty Daula cirko cirko sukai reception Nabilah na maida yanda abubuwa suka faru ma Aunty Bara’atu da bata jimada k’arasowa ba.... Aunty B ta kama Daula ta zaunarta saman kujerar dake jere a wajen kana ta d’an dafata kad’an tace “Daula are you alright...?”

Hawayen da take mak’alewa ta d’an saka yatsun hannunta tana gogesu lokaci guda take k’ok’arin k’ak’aro murmushi tana jinjina kai take furta “Yes... I’m fine Aunty B... Kar ku damu dani...” Ta k’arashe tana kuma goge fuskarta....
Nabilah da Aunty Bara’atu suka d’an dubi juna kana Nabilah tace “Aunty you’re not ok... Inaga zaifi kyau idan muka tafi gida kawai....”
Aunty B ta jinina kai tace “Gaskiya mu tafi kawai tinda dama dare yayi....”

Basu kai aya ba Yesmin da k’arsowart wajen kenan ta taresuda fad’in “Ku tafi Ina..... Ai Wllhi babu yanda zakuje sai My Kay yazo ya baki takardan sakinki... Mayya jarabebbiya kin lik’e mishi kinga jan fata zaki lashe shi... Toh Wllhi sprit d’insa mai k’arfi ne barikiji na fad’i miki....!!”
Ta k’arashe tana shan gaban Nabilah sai wani jijjiga take tana huci....

Aunty B ta dubi Nabilah ta dubi Yesmin... Lokaci guda taceda Yesmin “And you are....?”

Yesmin na faman yamutsa fuska tana aika masu muguwar kallo take furta “Ni ce matar Khalid... Kuma Wllhi Wllhi sai ya saki wannan mayyar dan baida mata bayan ni....”

Mahaukaciya suka d’auki Yesmin, Nabilah tace “Aunty don’t mind this lunatic, muje kunji.....!!”

Batakai aya ba saiji tai Yesmin ta janyota ta dawo da ita baya tana fad’in sai ta nuna mata ita mahaukaciya ce.... Waigowan da Nabilah zatai ta had’a mata da mari mai shegen kyau wanda yasa Yesmin sakinta babu shiri, ta kame fuskarta tana ihu tana tsalle ta kuma yowa kan Nabilah saidai tuni hankalin receptionists da wasu nurses yayo kansu suka shiga kokawan rik’e Yesmin dake bore tana tsalle tana fad’in su bari ta nunama wannan k’aramar ‘yariskar tsan tsan hauka....
Nabilah kaw ta shiga b’oyewa bayan Aunty B tana fad’iwa malaman jinyan su taimaka su kame Yesmin su wuce da ita psychiatric ward dan da gaske haukarta ne ya tashi....

Yesmin na fincika tana fad’in su cikata, inaaa kaman cewa take su kuma kameta.... Sai tsalle take tana furta “Wllhi k’Arya take ni ba mahaukaciya bace... You’ve to believe me....!” Ta k’arashe tana mai yankawa nurse guda data rik’eta cizo a hannunta...

Nabilah kaw fad’i take “Kun gani koh she’s dangerous please take her out of here... she might harm someone...!”

Yesmin taci gaba da tsalle tana k’ok’arin zillewa tamkar wata ‘yar biri tana fad’in ita ba mahaukaciya bace.... Saidai tuni wata nurse ta k’araso da Allura... Yesmin taci gaba da ihu tana fad’in kada sui mata allura ita da hankalinta... Takai dubantaga Khalid da k’arasowarsa wajen kenan... Ta shiga k’walla k’ara tana fad’in “My K tell them ni ba mahaukaciya bace... Please tell them su sakeni da hankalina....” Basu saketan ba saima k’arasowa wajensa da Nabilah tai cikin sauri ta mak’ale jikinsa tana fad’in kalan tsoron da Yesmin ta bata... Shiko tuni ya mak’alata cikin jikinsa yana fad’in “I’m here now teddy bear... Bazan bari ta cutar dake ba....”
Yanda Nabilah tai rau rau da idanu tai kalan tausai sai ka rantse har cikin ranta tsoron Yesmin take....
Yesmin kaw kaman Ta had’iyi zuciya ta mutu yanda ta gansu mak’ale da juna ga Khalid na kuma ririta munafukar yarinyar nan haba nan fah ta kuma doka wani ihun tana fad’in sai ta kashe Nabilah.... Tuni nurses d’in nan suka cazgwad’a mata allura had’ida fitarta daga wajen....

Nabilah ta saki rigar Khalid a hankali dan ita sai yanzu abinda tai ya soma bata kunya... Shiko d’an d’ago fuskarta yai kana yace “Are you alright...?”

Jinjina masa kai tai cikeda kunya kana tace “I’m fine... Ina Ammi...?”
D’an sauk’e ajiyan zuciya yai kana yace “She... passed out...!”
Nabila tai saurin d’agowa a zabure tana dubansa...
Dafata yai kad’an kana yaci gaba da fad’in “But she’s going to be alright... Dr yace Shock ne yasata sumewa, ga kuma stress... So sun kwantarta ta huta... Tana ma bacci yanzu haka, Siyama na tareda ita....!”
Nabilah ta dubesa cikeda tausayawa, zatai magana ya k’ak’aro murmushi ya sakar mata kana yace “Don’t worry I’m fine... Muje mu sami su Aunty Shayibu ya kaiku gida it’s late already...!” A hankali ta jinjina masa kai tausayinsa bai saketa ba, kaman rak’umi da akala ta shiga bin bayansa har suka iso suka tadda Bara’atu naci gaba da baiwa ‘yaruwarta baki....

Khalid ya d’anyi gyaran murya kana yaceda Aunty B... “Aunty inaga kuje Shayibu ya maidaku gida... I’ll be staying here...”
Aunty B ta jinjina kai kana tace “Khalid kai hak’uri kaji... Na sani this isn’t easy for you, tsaka mai wuya kake amma kai hak’uri in sha Allah komai zai wuce...” Cikeda tausayin Khalid d’in tai maganar....

Cikeda k’arfin hali irinta maza ya jinjina mata kai had’ida k’ak’aro murmushi yace “Don’t worry Aunty, I’ll be fine... Just take care of Aunty Daula please...”
Jinjina masa kai tai kana tace “In sha Allah...!”
Aunty B ta kamo hannun ‘yaruwarta suka fice...
Nabila ta d’ago a hankali tana duban fuskan mijin nata cikeda tausayinsa, murya mai cikeda rauni tace “Do you want me to stay...?”
Khalid ya kamo yatsun hannunta yana kallon lallen biki da sun d’an fara fading, takai dubantaga yatsun hannun nata yanda ya rik’esu yana duba... Sosai ta kula shi mutum ne mai son k’unshi dan so tare muddin suna tare toh yayita juya yatsun hannunta kenan yana kallon k’unshin.... Sinkayo muryarsa tai yana fad’in “No kije gida teddy bear... You need to rest as well...”
Murya a hankali tace “Are you sure...?”

Ya d’aga mata gira kana ya d’an sauk’o da bakinsa saitin kunnenta yace “Unless kuma za’a bani wani abu da zai keeping d’ina company while I’m here missing you....” Ya

Please Login or Register in order to submit comment