Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fayyace maka komai da kuma dik wani shirina... Ina kuma fatan na sami goyon bayanka d’ari bisa d’ari a matsayinka na aminin d’ah na....”
Dikda Baffah baisan shirin Daddyn ba amma sai ya sami kansa da jinjina mar kai yana mai furta “Zaka sameni mai yi maka biyayya da bin umarninka in sha Allah Daddy....”
Daddy yaji dad’i sosai ya jinjina kai yana furta “Shiyasa ban tab’a danasanin kasancewarka abokin d’ah na ba dan nasan kaid’in yaron arziki ne..”
Mugun sanyi jikin Baffah yai ko da Daddy ya karanto masa shirinsa na auren Khalid d’in taryan taryan, ya tina kwanakin baya yanda ya baiwa Ammi da Siyama full support d’insa wajen ganin an raba tsakanin Khalid da Nabilah, ya tina dik fad’i tashin da akai wajen datse tsakaninsu ya bada nasa gudummawar, tabbas sai yaji bai kyauta wa amininsa ba, bai kyautawa abokantakarsu ba, sanin kansa ne tin tasowarsu Khalid bai tab’a soyayya da wata mace ba sai Nabilah, instead ya basa goyon baya yai supporting d’insa like a brother sai ya biyewasu Ammi da son zuciyarsu ganin sun datse k’aunar dake tsakankanin zukata biyu da Allah ya had’a, tabbas maganan da jiya Khalid yai masa yayi gaskiya cewa shid’in bai tara sani da Allah ba, Allah ka iya canza al’amaransa a duk lokacin da yaso, domin kaw shid’in Buwayi ne gagara misali... Ko a mafarki bai tab’a zaton auren Khalid da Nabilah mai yuwu bane sai gashi lokaci guda Allah ya sauya zuciyar mahaifinsa, tabbas ya yarda shi aure nufi ne na Allah kuma wani bai auren matar wani... Yayi alk’awarin baiwa Daddy his unconditional support har burinsa ya cika na ganin auren ya tabbata cikin yardar Allah, ta hakan ne kawai zai sakawa abokinsa butulcin da yai masa a baya....
Bayan sun ida tattaunarwasu da Daddy ya mik’e yanaiwa Daddyn sallama daidai sanda Khalid yai sallama ya shigo parlorn...
Mamaki ya cika Khalid d’in ganin Baffah tareda Daddy har suna sallama da juna, since when suka zama close haka..? Ga wata ‘yar takarda hannun Baffan da sam baiso Khalid d’in ya gani... Kallon kallo sukabi juna dashi sanda Baffan zai fice, Baffah sai sakar masa murmushi yake... Sosai Khalid ya karkata yana duban Baffah dake k’ok’arin ficewa yana mamakin wannan al’amari... Take masa baya yai niyyan yi sai kuma ya sinkayo muryar Daddy na kiransa, dole ya fasa bin bayan Baffah ya komaga kiran mahaifinsa... Daga can gefen k’afar Daddyn ya d’an zauna yanai masa sannu da gida....
Daddy ya amsa masa da yalwar fari’a kana yace “Dama ina nemanka....?”
Gaban Khalid ya fad’i ganin amininsa bai jima da ficewa daga parlorn ba... Badai wani abin yayi ba, tinda shine sarkin laifi a gidan Siyama ce ‘yar lele...
Murya har na sark’ewa yace “Daddy nayi wani abin ne...?”
Girgiza masa kai Daddy yai alamun a’a kana ya d’orada “Bakayi komai ba Son... Wani aiki nake so kamin a can Abuja, toh bansan ko kanada lokaci ba....”
Cikin sauri Khalid ya shiga girgiza kansa yana fad’in “Haba Daddy, ka wuce tambayan lokaci a wajena, umarni kawai kai d’in zaka bani....”
Daddy ya jinjina kai cikeda jin dad’i “Allah shi maka albarka... Akwai gidana na can estate d’in dake Gwarimpa, za’ai renovating... So inaso kai supervision aikin... Idan akwai wasu fittings da kake sona canzasu to your taste sai a canza.... Ka fahimta....”
Khalid ya jinjina kai a hankali kana yace “Daddy su Aunty Daula zaka maida can.. Ko zaka maida Ammi Abuja ne....?”
D’an murmusawa Daddy yai kana yace “Kawai inaso a gyara gidan ne Son Incase of tomorrow... Kasan ance gida biyu maganin gobara....”
Ya jinjina kansa a hankali “Haka ne Daddy... Yaushe kakeso a fara....?”
“Kar ya wuce cikin week d’in nan if possible....”
“Alright Daddy... In sha Allah za’ai yanda kace....”
Daddy ya murmusa cikeda jin dad’i kana yace “Allah shi maka Albarka Son...”
Khalid ya amsada Ameen Daddy kana ya mik’e... A hanyarsa ta ficewa ya had’uda Ammi ta cika tayi fam sai faman danna masa muguwar kallo take... Kafin yai aune ta janyo hannunsa tana fad’in “Shige muje dama shigowarka nake jira...”
Khalid na tambayar “Mi nayi kuma Ammi....? D’an sakar min hannun...”
Bata saki hannun nasa ba bata fasa janyosa zuwa cikin parlorn Daddyn ba take fad’in “Bazan sakeka ba, na gaji da wannan wasan yaran da ake dani a gidan nan ehe....” Ta k’arashe sanda suka iso cikin parlorn gaban Daddy...
Daddy ya d’ago yanai mata duban mamaki...
Har lokacin huci take, ta shiga nuna Khalid da yatsa tana duban mijin nata “Toh gashi nan... Inaga idan yaji daga bakinka zai fi aminta cewa baida mata sai Yesmin.... Na gaji na gaji da yin k’anan muryawa Mahaifiyar Yesmin... Kullum cikin bata baki nake ina sanar da ita za’a tsaida magana k’wakk’wara... Daddyn Siyaam wannan harda naka laifin, gaba d’aya ka zubawa Khalid idanu yana nema ya maida mutane tamkar wasu mutanen banza... Toh wllhi bazan zuba maku idanu ba, maganar aurene dole a tsaida magana d’aya yanzu kam... Na gaji da wannan come gaba come baya da ake....” Ta k’arashe tana bud’e hannayenta alamun fad’a...
Tagumi Daddy ya rapka yana duban yanda Ammi ke falfala masa ruwan fad’a tsaye akansa saikace wata uwarsa...
“Kin gama...?”
Ya tambaya yana dubanta...
Wani kallon wulak’anci ta watsa masa daga nan yanda take tsaye kana tace “So kake na maimaita maka...?”
Girgiza kansa yai a hankali kana ya dubi Khalid yace “Jeka abinka kaji....”
“Toh Daddy...” Khalid yace sanda yake k’ok’arin ficewa...
Ammi ta bisa da kallo baki sake tana furta “Aww yanzu cewa zakai yaje, a maimakon ka tirsasa ya sakama ransa ya auri Yesmin an gama... Haba Daddyn Siyaam Wllhi kai kake d’aurewa yaron nan gindi yake raina mutane... Khalid! Khalid!!..” Tabi bayansa tana kira saidai bata cimmasa ba dan ya jima da ficewa...

Dawowa tai ta kuma yin tsaye akan mijin nata kana tace “Toh yanzu da ka k’yalesa ya tafi sai inji meye shirin naka ai....” Ta k’arashe tana mai zama gefensa...
Murmusawa Daddy yai kana yace “Ko Ke fah Farida.. Shi miji idan anaso yayi abu ba’a nuna masa isa da gadara, indai ta wannan hanyar akeso yayi abu toh fah bazai yi ba, amma idan aka biyo ta hanyar kwantar da kai sai ya kwanta miki ma ki taka gadon bayansa ki shige abinki...”
Ammi tasha jinin jikinta tana duban sabon sauyin data samu daga mijin nata, tinda suke dashi yau sama da shekaru talatin bai tab’a yi mata magana mai kamada wannan ba, kullum dik abinda take so abinda tai niyya shi ake, da alama yanzun hannunka mai sanda yake mata...
“Ban fahimceka ba Daddyn Siyaam...” Ta fad’i tana mai karkatowa zuga dubansa sosai...
Murmushin Daddy ya kuma sakar mata kana yace “Soon zaki fahimceni Farida tah...Kuma na miki alk’awari nan bada jimawa ba Khalid d’inki zai aure.... Ki kwantar da hankalinki kinji koh....” Ya k’arashe yana mai kamo ‘yan yatsun hannunta had’ida murzasu kad’an...
Take annuri ya cika fuskar Ammi, tasan mijin nata bazai tab’a bata kunya ba tanada hundred percent guarantee akansa, dik abinda takeso shi yakeyi, bai tab’a keta dokarta ba a tsawon shekarun da sukai tare, mai ma zaisa taji wannan karon bazai abinda take so ba...? Lokaci guda ta kuma sakin murmushi tana duban Daddyn kana tace “Shisa nake matuk’ar k’aunarka mijina, kana min duk abinda nake so a koda yaushe...” Ta k’arashe tana mai kwantar da kai cikin k’irjinsa....
Lumshe idanunsa kurum Daddy yai, daga shi saiko Mahaliccinsa ne yakeda tabbacin suka san abinda yake ji cikin zuciyarsa...

***

A b’angaren Khalid kuwa abubuwan da suke faruwa a ‘yan kwanakin gaba d’aya sun d’aure masa kai, sun dagula masa lissafi... First canzawar Daddy, had’uwarsa dasu Aunty Daula, kusancin Daddy da Baffah yanzu kuma ga aikin gyaran gidansa na Gwarimpa da ya d’aurasa bisa... Dafe kansa yai a hankali yana furta “What are you up to Daddy...?” Ya fuzar da iska a hankali had’ida girgiza kansa kad’an lokaci guda yaci gaba da shirya kayansa...
Aunty Daula ya kira ya sanar da ita yana hanyarsa ta zuwa Abuja gobe da izinin Allah... Wai zo Kaga murna wajen Aunty Daula da yaranta... Tin a ranan suka soma shirye shiryen tarban Khalid...

***

KANO


Sawwama dake zaune gefen mahaifiyarta ta turo kallabi gaba sai taunar chewing gum take irin na matan da suka makara a bariki... D’aga k’afa tai ta d’aura d’aya bisa d’aya tana wani jijjiga take furta “Magajiya kenan... Ai na riga na samo lagon Hafiz... Zanyi dik abinda yake so daga k’arshe na k’yale shegiyar Zulfa’un ta auka ramina.... Haba ya kike kokonto na saika ba rainonki ba... Kinga nan...” Ta d’aga tafin hannunta tana nuna mata kana taci gaba da fad’in “Na kamasa a nan tinda ya bari nasan lagnosa...”
Dariya sukai itada mahaifiyarta kana Magajiya tace “Kinyi min dadai... Kici gaba karki fasa komai...” Suka kuma saka shewa suna tafe hannaye... Daidai nan Dillaliya tai sallama yara na biyeda ita d’auke da saitin akwatina nik’i nik’i....
“Gafara dai! Gafara dai !!! Inji masu gidan suna nan....?” Dilla iya tace sanda take kwab’e mayafinta tai d’amara dashi...
A tare Sawwama da Magajiya suka fito... Dilalliya na nunima yaran cewa su ije akwatinan a nan tsakar gidan....
Magajiya tabi akwatunan da kallo kana ta isa ta mik’awa Dillaliya tafukan hannayenta biyu suka tafe tana fad’in “Anyiririri Billahillazi na soma jiyo k’amshin amarci.... Kai ta wajena akwatunan nan sunci kud’insu...” Ta k’arashe tana jujjuya ‘yar k’aramar akwatin mai suffan jaka wacce ake zuba ‘yankunne da sark’a ciki.....
Dillaliliya na Washe baki take fad’in “Yo ai na fad’a miki bana kawo kayan banza... Nan da kike gani akwatinan wata yarinya ce sakin wawa, juyasu da kyau ki gani sabbi ne dal ko lamba ba’a cire masu ba....”
Magajiya tace “Wllhi na gani kaw....” Daidai nan wasu ‘yandaudu suka fito daga wani d’aki suka nufo akwatunan suna shewa da gud’a suna fad’in Uwarsu zata amarce, suna gud’a suna d’aga jakkunan....
“Kai ku ije akwatunan nan ban gama biyan kud’inba...” Cewar Magajiya tana fuzgewa hannun ‘yandaudun...
D’ayan ya wani kame zani yana gyara d’aurin k’irji da kallabi yake fad’in “Yo ai Babanmu ne zai biya... Wayyo wa yaga ni Laminde gidan Ubana na bariki....” Suka kuma kwashewa da dariya gaba d’aya kana Sawwama tace “Wai ku dakata, wai auren waye ake batu, Nifa ban gane ba...?”
‘Yandaudun suka had’e hannayensu waje guda suka tafe had’ida yin salo yanda dai sukeyi kana d’ayan ya kame baki yace “Au Tab! Wai Ke bakida labari... Toh uwa guda nawa mukeda a bariki.... Uwarmu dai itace zata amarce mu kuma mu tafi mata zaman d’aki...” Suka k’arashe suna kuma tafe hannaye.....
Sawwama ta dubi mahaifiyarta da mamaki.... D’aga mata gira tai kana tace “K’warai kuwa Sawwama aure zanyi na raya sunnar ma’aiki nima....”
Sawwama da mamaki ya cikata tace “Magajiya aure... Aure kuma da waye...?”
Magajiya na juya idanu take fad’in “Sati Uku ya rage na amarce Sawwama, ranar Bikin zaki San waye angon.... Kunga ku tattari akwatunan nan ku shigar min ciki...” Taceda ‘yan daudun.... Nan suka shiga kwasan kayan suna wani yauk’i su a dole ga mata.... D’ayan har cewa yake “Ni banma San a waye zan bada d’inkin nawa anko d’in ba....”
Sawwama dai kallo ta bisu dashi har suka shige yayinda Dillaliya da Magajiya suka ci gaba da tattauna cinikinsu don harta sauran su kayan d’aki yau take so su kammala cinikin komai tinda biki ya gabato....

***

Aunty B ta numfasa tana duban ‘yar uwar tata kana tace “Sati uku kacal ya rage a d’aura auren....”
Yaya Abida ta d’ago kod’add’un idanunta tana dubanta kana tace “Kije kisan yanda zakiyi ki hana wannan auren aukuwa Bara’atu.... Sanin kanki ne wannan auren daidai yake da maimaita bak’in tarihi.... Ki hana wannan auren aukuwa....!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji tana mai baiwa Aunty Bara’atu baya....
Mik’ewa tsaye Aunty B tai kanta a k’asa kana tace “Yaya banida ikon hana aukuwar wannan auren.... Da ace inada iko hanawa wllhi da kafin nazo gareki da na hana... Ki yarda dani.....”

Juyowa tai sosai tana duban Aunty B kana ta tako gabanta kad’an.... “Bara’atu karki bari ayi wannan aure...!!!” Daga haka bata kuma cewa komai ba sai shigewa k’uryar d’aki da tai ta bar Aunty B nan tsaye cikin tsananin kad’uwar zuciya da mutuwar jiki.....
Wasu hawaye masu d’umin gaske suka gangaro mata.... Fuzar da iska tai kad’an kana ta isa jikin k’ofar d’akin ta dafa, kanta na kife bisa k’ofar take fad’in “Na barki lafiya Yaya... Ubangiji yaci gaba da kareki....!”” Daga haka sa kai tai ta fice daga cikin gidan tana matsan hawaye...

A can cikin d’aki kaw wani hoto dake sanye cikin k’aramar frame ta tsurama idanu, mutum uku ne jikin hoton, Wani dattijon mutumi sai wata matashiyar mace da k’aramin yaro da bazai haura shekaru uku ba... Ta shiga shafa saman hoton tana hango rayuwar da sukai a baya, rayuwa mai dad’i mai cikeda ni’imomi.... Ta rintse idanunta a hankali wasu hawayen suka kuma zubo mata... A hankali ta mik’e ta isa malank’ayin hoton ta kuma ratayesa... Lokaci guda take furta “Ma’aruf bazai biya diyan Ma’aruf ba...!” Tai maganar tana mai k’urama hoton idanu.....
***

Raihanah na zaune k’asa kusan k’afafun Mamani tana warwarewa Mamanin k’unshi a k’afafunta lokaci guda suna kallon maimaicin shirin draman Dad’in kowa da ake nunawa a tashar Arewa24 Sameer yai sallama...
Mamani ta shiga Washe baki tana fad’in “Shigo abinki angon gobe..”
Raihanah kaw gaba d’aya sai ta tsinci kanta da daburcewa musamman dashike kanta a bud’e ne ko d’ankwali babu, jan top ne a jikinta saiko zanin tampa, ida tsifanta kenan Mamani tace ta cire mata k’unshi, gashi hannayenta gaba d’aya b’ace suke da k’unshi, gaba d’aya sai jinta take a tsarge... Tana jin suna gaisawa da Mamani ta kasa koda d’ago idanu ne balle ta gaidashi.....
Shiko Sameer tinda ya shigo duba d’aya yaima bayanta ya d’auke idanunsa gabansa na wani irin yankewa, sam bai kawo Raihanah bace zaune wajen dan shi zai iya rantsuwa baisan yaya suffar jikinta yake ba dikda cewa shi yai treating ciwonta, dashike ba abinda yake dubawa ba kenan, aikinsa kenan yai treating ciwo nothing more....
Mamani sai jansa da firan biki take bai iya amsawa saidai murmushi da jinjina kai kurum da yake mata, ita kaw Rainah banda addu’an samun mafitar yanda zata mik’e ta bar wajen bata komai.. Kaman wacce addu’arta ya amsu taji ya mik’e yana amsa waya... Harda ‘yar ajiyan zuciya ta sauk’e wanda ta tabbata badon tv dake kunne ba da Mamani ta jiyo sautin ajiyan zuciyarta...
Muryar Mamanin ne ya katseta da fad’in “Yauwa sannu ‘yar albarka, maza tashi ki wanke hannun naki ki dama masa furan nan da d’azu Babanku ya aiko....
Ta mik’e tana mai gyara d’aurin zaninta “Toh Mamani...”
D’aki ta nufa daidai sanda ya ida wayar yana k’ok’arin komowa parlorn, ai a d’ari ta fad’a d’akin tana mai kuma sauk’e ajiyan zuciya, bathroom ta fad’a ta wanke hannunta kana ta bud’e wardrobe ta ciro hijabin da ya kusan kaiwa gwiwarta ta zira, kana iya tudun sumarta yanda ta tupke shi tsakiya dashike sumar nata mai yalwan cika ne kuma bata saka mar relaxer...
Idonsa k’yam a k’ofar d’akin da yaga ta shige tamkar mai jiran fitowar nata, dik bayanan da Mamani ke masa ba wani fahimtar ta yake ba, yafi maida hankaliga duban k’ofar... Aiko tana fitowa sukai ido hud’u, tai saurin maida nata idanun k’asa tana gaidashi...
Ya amsa yana mai duban k’afarta mai ciwo da yanayin tafiyar nata....
Ita dai Raihanah kitchen ta shige abinta dan kawo masa damin fura kaman yanda Mamani ta buk’ata....
Tana cikin had’a kindirmon ta cirota kenan daga cikin fridge Marliya ta shigo ta isketa....
“Patient d’in Yaya mi kike a kitchen... Salon Ya Ma’aruf yace an sakaki aiki tinda islamiya ma hanaki zuwa yai...”tace sanda take k’arasowa cikin kitchen d’in...
Gajeriyar murmushi Raihanah tai kana tace “Tinda mashi zanyi aikin bazai hana ba... Kinga shigo ma ki tayani...” Ta k’arashe tana mik’a mata bowl.. Marliya ta kame baki tace “A’a kedai cika ladarki hajiya patient..”
Raihanah ta d’an langab’e kai tace “Kai Marliya yanzu bazaki tayani ba....”
“Cikata ladanki kawai patient d’in Yaya dama Mamy ke nemanki bara naje nace kina zuwa...” Bata jira cewan Raihanar ba tai ficewarta da d’an gudu gudu....

A can parlor kaw Sameer mik’ewa yai da niyyar tafiya Mamani ta tsaidashi da fad’in “Aff ai kuwa Raiha na kitchen tana dama maka fura bazaka tsaya kasha ba....”
D’an sosa k’eyarsa yai da makullin mota “A’a Mamani a barshi har na dawo, ana nemana ne a can asibiti....”
Mamani ta jinjina kai tace “Oh ni yaron nan sam baka hutu saikace agogo... Toh Allah shi tsare amma ka lek’a kitchen d’in ka amsa ko a mota sai ka sha....”
Da toh ya amsa mata dan baiso ya kuma jan zancen yasan tinda ta soma fad’in sai ya amsa toh bazata k’yalesa ba har sai ya amsa d’in.... Yana jiyo muryarsa tanai masa addu’an Allah ya tsare...

Lokaci guda tabi bayansa da kallo tausayinsa na d’awainiya da ita... Anya batai katsalandan ma rayuwarsa ba, ta rasa da wa zata had’asa aure sai d’iyar Haule...? Toh amma ai ‘yar uwarsa ce ta daifi masa wancan ballagazar matar tasa ko babu komai Sahariyya bazata rabasu dashi ba kaman wancan mai zubin awakan, idan ya tuna yanada iyalina gida dole ya waiwayesu....kuma yanzu Haule tayi hankali ta tuba ta gyara halayyanta... Dik d’an adam kuma ajizi ne tinda itama a baya ba haka take ba saida ta nemi yafiyan ahalinta, da wannan tinani ta d’an samu zuciyarta yai sanyi...

Tsaye yai a k’ofar kitchen d’in yana duban yanda take kokawa da ice block saikace wata mai fasa gini duk ta wani daddage k’arfinta....
Abin yaso basa dariya, gyaran muryar da ya d’anyi ne ya sanyata saurin juyowa... Ta daidaita zaman hijabinta tana mai maida idanunta k’asa, sihirtaccen murmushi saman fuskarta “Laa Yaya ka gaji da jira koh... Dama yanzu zan kawo maka...”
Sameer ya ida shigowa cikin kitchen d’in yana duban yanda take gudanar da al’amranta wanda zai tabbatar maka ita d’in ma’abociya hidima da kitchen ne “Is okay, kiyi min packaging kawai zan tafi dashi ne...”
Jinjina masa kai tai kana tace “Ok bara na d’uko jug cikin drawer...”
Gaba d’aya a daburce take gashi ya tsaya ya tsareta da idanunsa... Drawers dake k’asa ta soma dubawa bata sami jug ciki ba, dole tasan suna drawers d’in sama kenan... Sanin cewa tsawonta bazai kai ba dole ta shiga neman abinda zata taka ta ciro jug d’in...
Shiko Sameer harda kame hannaye yana kallon ikon Allah... Toh mai take nema haka...? Bai ida tinanin ba yaga ta d’auko k’aramar kujera irin ta zaman kitchen ta d’ale tana k’ok’arin mik’a tsawonta alamun dai har yanzu tsawon nata bai k’arasa ba... Girgiza kai kurum yai yana mai d’an murmusawa kad’an, sai ganinsa kurum Raihanah tai gefenta ya bud’e drawer d’in... “Wanne zan ciro miki...?” Ya tambaya yana duban jugs d’in dake jere cikin drwer d’in, kusan guda uku...
Murmushi saman fuskarta tace “Ko wanne ma Yaya...”
Dubanta yai yaga wanda idanunta Ke bisa kana yasa hannu ya ciro shi... Daidai saitin kunnenta ya rage sautin muryarsa yana fad’in “Be careful kinsan har yanzu ked’in patient ce...” Bai jira cewarta ba ya ije mata jug d’in saman sink
Wane irin kunyarsa ya rufeta, ta k’araso kai a sanne ta isa ta d’auraye jug d’in kana ta juye damin furan ciki...
idanunsa naga wayarsa sanda ta k’araso ta mik’a masa jug d’in cikeda risinawa... Ya amsa yana fad’in “Da fatan dai baki zuba sugar ba..?”
Girgiza masa kai tai alamun a’a kana tace “Ban saka ba Yaya....”
“Good..” Ya furta yana amsar jug d’in lokaci guda ya shiga magana a wayarsa... Ta bisa da kallo tana mamakin wannan bawan Allah kullum cikin amsa waya yake... Daga nan ta shige amsa kiran Mamy....




SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_






*84*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Sayayya iri guda Mamy taiwa Raihanah da Marliya, jin yarinyar take har cikin zuciyarta... Haka nan Allah ya jefa mata k’aunar yarinyar had’ida tausayinta musamman idan tuna cewa ita d’in marainiyace batada mahaifiya a raye...A hankali ta kuma sauk’e ajiyan zuciya sanda ta jiyo sallama daga parlor tamkar ta ‘Yaruwarta Bara’atu...Mik’ewa tai had’ida amsa sallamar kana ta nufi parlorn.... Aunty Bara’atu ta gani zaune dirshan saman kujera... Gabanta ya tsinke ya fad’i, ta k’arasa a hankali tana mai dafa kafad’ar Aunty Bara’atun...
“Bara’atu...” Mamy ta ambata cikin tsananin sanyin murya...
D’ago kai Aunty Bara’atu tai tana duban Mamy da idanunta da sukai matuk’ar raunana....
A hankali Mamy ta zauna gefenta jikinta na kuma yin sanyi...
“Ke d’in baki kasance mai rauni ba cikinmu... Dik yanda akai akwai abindake damunki... Ki sanar dani ‘yar uwata, shin kinje kinga Yaya Abida ce...?”
Wannan karon d’agowa sosai Aunty B tai tana duban Mamy sai kuma ta kauda fuska gefe, lokaci guda take furta “Mamy haka munaji muna gani zamu bari a aurawa Ma’aruf yarinyar da bai k’auna, kuma munsan yanda mahaifiyarta da ita kanta Sahariyyar suka baida gudummawa wajen tarwatsa rayuwar Zulfa’u... Anya bamu yi kuskuren aminta da wannan auren ba.... Shin bamuda wata hanya da zamu dakatar da wannan aure...?”
Sauk’e ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “A koda yaushe mu kasance masu kyautata zato Bara’atu... Kuma babu yanda banyi da Ma’aruf ba cewa karya tilastawa kansa wannan aure amma sai cemin yai yaji ya gani zai iya.. Toh kinga kuwa banida ikon hanawa haka nan mahaifinsa ma... Addu’a ita kurum zamu ci gaba da yi, dik abinda yake alkhairi ne Ubangiji ya tabbatar dashi... Sharri kuma ya kawar mana... Na sani Bara’atu kin damu dani kin damu da ahalina... Hasalima kinfi fifita damuwarmu sama da taki damuwar, gidan duniyar nan babu abinda zan iya biyanki dashi saidai na miki fatan dacewa na kumaci gaba da addu’an Ubangiji ya karkato miki da hankalin mijinki gareki...” Fasali Mamy ta d’anja kana taci gaba da fad’in “Dik yanda ‘yaruwa ta k’warai takai Bara’atu kin kai... Kina tare dani a dik sanda nake tsananin buk’atarki, yayinda ni bani kasancewa taredake lokutan naki buk’atun... Daidai da rana guda baki tab’a juyama d’aya daga cikin ‘yanuwanki baya ba... Kin rik’i amanar Yaya Abida dika cewa tasha tureki daga gareta dik a sabida baki yanke alak’a dani ba, kina nan a tsakaninmu kina nuna mana zallan k’auna.... Ki amshi girman daga garemu, kece kike kula damu a maimakon mune zamu kula dake... Bara’atu bansan ya rayuwata data iyalaina zaya kasance ba da ace na rasaki...” Ta k’arashe cikin tsananin Murya irinta mai kuka...
Saurin rik’o hannayenta Aunty B tai idanunta suna yunk’urin kawo ruwa itama, lokaci guda take girgiza kai tana duban Mamy
“Ki daina fad’in haka Mamy... Abinda ya dace shi nakeyi.... Hakan ce ya kamata ya kasancega ‘yanuwa.... Mamy ina k’aunarki ina kuma k’aunar zuri’arki... Ina kuma fatan Allah yaci gaba da tsareki da kuma ahalinki...Sannan bazan gushe ba ina addu’an Allah ya had’e kan ahalinmu....”
Lokaci guda tasa ‘yar yatsanta ta goge hawayen da ya d’igo mata, take suka rungume juna hawaye na zarya daga idanunsu...
A haka Zulfa’u da dawowarta kenan daga wajen aiki ta taddasu... Jiki a sanyaye tai sallama ta shigo parlorn....
“Mamy.. Aunty..!”
Ta furta cikin tsananin sanyin murya...
Take ko waccensu ta soma k’ok’arin saita kanta....
Aunty B ce tai k’arfin halin d’aura murmushi saman fuskarta, tana mai duban Zulfa’un take fad’in “Wannan zuwa wajen aikin ya kamata a dainashi haka nan... Kamata yai ace yanzu kuna gida a killace daga ke har Nabilar, dama zuwa nai na tattareku ku koma can a soma maku gyara dan mun gama magana da mai gyaran amaren zatazo cikin satin nan....”
Zulfa’u dai murmushin da tafi kama da yak’e tai idanunta naga mahaifiyarta dake matsan sauran k’walla...
A hankali ta isa aje handbag d’inta saman kujera kana ta k’araso tana mai tsaresu da idanu...
“Aunty Wai meke faruwa ne...? Kuka fah na tadda kukeyi...” Tace sanda take zama gefen Mamy da har lokacin bata d’ago sunyi ido hud’u da d’iyar tata ba...
Murmusawa Aunty B ta kumayi kana tace “Yo ba dole muyi kuka ba Zulfa’u... Irin wannan ni’ima da Ubangiji ya lullub’emu dasu, ace zaka aurar da d’oyoyi har biyu lokaci guda kinga kaw ai kuka ya zamto mana dole, kukan farin ciki muke d’iyata....Allah ya cika min buri ya amshi addu’ata bazaki koma gidan wancan shashashan tsohon mijin naki ba, kinga kuwa ai dole na zubda hawayen Farin ciki...” Murmushi tai tana mai duban mahaifiyarta da itama murmushin ne saman kod’edd’en fuskarta...
Allah sarki Bara’atu, ita dai komai sai ta nemo masa mafita, bazata tab’a ganin damuwa a tattareda Mamy da ahalinta ba har sai tasan hanyar da zata biyo dan taga ta taimaka wajen kawar masu da wannan damuwar... Idan da ace duka ‘yanuwa

Please Login or Register in order to submit comment