Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

b’atar da tinaninsu, Dumba ta rik’e Bara’atu suka soma gudu yayinda nima na rik’i Ma’aruf muka d’au wata hanyar ga jaririya Fatima a bayana... Da k’yar muka samu muka isa tashar mota... Bayan motoci sun tashi ashe suna biyedamu saida mukai nisa da tafiya kana suka tsaida motar da muke ciki, nan na hangesu sai lek’en motoci suke suna neman mace mai goyo da yaro.... Ganin haka yasa na razana sosai, na kwance Fatima na mik’ata hannun Ma’aruf nace su b’oye k’asan kujera kunsan manyan motoci irin na da har sai mutum ya zauna k’asan seat ma... Yayinda suka umarce duk wani wanda Ke cikin motar ya fito.......suka turamu daji da alama basu gane ina d’aya daga cikin mutanen da suke nema ba kuma basuga yaro da goyo a tare dani ba... Babban tashin hankalin da na tadda bayan sun sakomu daga dajin shine babu Ma’aruf babu Fatima a mab’oyar dana b’oyesu....Ta k’arashe cikin wane irin sauti mai ban tausayi...
“Jama’an dake wajen suka tabbatar min ‘yanta’addan sunyi awon gaba da wasu tsirarun mutane dake cikin motar kuma ga dikkan alamu sun kashesu.... Hakan na nufin iftila’in ya ritsa da Ma’aruf da kuma Fatima...”

Ji yayi bakinsa ya bud’e ya soma kwararo bayanai tin daga lokacinda ta b’oyesu k’asan kujerar motar hannunsa rungume da jaririyar... Cikin tsananin mamaki da al’ajabi had’ida rud’ani illahrin jama’an dake wajen suka maida dubansu gareshi....
Idaniyansa sunaci gaba da zuban ruwa yaci gaba da fad’in “A lokacin da kika tabbatar Ma’aruf da Fatima sun samu mab’oya mai kyau tsoro da firgici had’ida tashin hankali ya sanya Ma’aruf ya fice a guje rungume da Fatima, babu wanda yaga wulk’awarsa sai gudu da yake falflawa cikin k’ungurumin daji rungume da jaririyar... Ma’aruf bai tsaya ko ina ba sai tsakankanin wasu duwatsu da yake tinanin Sun tsira kenan daga azzaluman mutanen.... A wannan tsakankanin duwatsu wani bawan Allah ya tsincesu har suka zama ‘ya’ya a gareshi...!” Yana ida fad’in haka ya d’ago fuskarsa da ya jik’e sharkaf da zufa ya kuma gauraye da hawaye yana mai bin illahirin mutanen dake wajen da kallo d’aya bayan d’aya har saida idanunsa suka sauk’a kan matar da ta kasa daina takowa izuwa gabansa cikin wane irin yanayi mai ban tausayi....



SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_


*92*



*©️Sameena Aleeyou....✍🏽*



*Beautiful Comments everywhere.... Masha Allah😍🥰 Sameena na maku fatan alkhairi a dik yanda kuke....🤝*



Kasa furta komai tai sai takowa izuwa gabansa da take, fusakar k’aramin yaron shi yake gizo a idanunta... Rayuwarsu yana k’arami shi take hangowa... Shin ta yaya zata mance wannan fuska, fuskar da kullum take kwana ta tashi da ita cikin idon zuci... Ma’aruf, Ma’aruf take gani gabanta... Tabbas shi d’in ne... Gashi nan da gaske a gabanta, tanaso ta tab’a fuskarsa ta tabbatar hakan ba d’aya bane daga cikin mafarkan da take... Allahu Akbar, Mai Rai baya cire tsammani daga rahamar Ubangijinsa... A haka ta k’araso har gabanshi su duka biyun duban juna suke cikin wane irin shauk’i mai ban tausai, hannayenta suna matuk’ar rawa take k’ok’arin d’agowa kana ta shiga shafa fuskarsa har lokacin bata iya furta koda kalma ba sai kallonsa da take da idaniyanta da suka matuk’ar raunana.... Shid’inma dubanta yake idaniyansa basu daina zuban ruwa ba... Da gaske dai itace a k’wayar idanunsa... Tabbas what he went through as a child wasn’t easy... The traumatic experience da yai going through yana k’arami shi ya tafiyar da tinaninsa yasa ya mance komai, amma wannan fuska jigo na rayuwarsa da kaman yanda sunansa bai b’ace masa ba bai tinanin wannan fuskar ta b’ace masa na har abada... Mamy da Aunty Bara’atu na hawaye suka dubi juna cikin wane irin shauk’i suna mai kuma duban wannan buwayar Ubangiji da suke kallo na aukuwa a gabansu, Allah sarki tabbas INDA RAI toh fah akwai RABO, bayan duka wad’annan shekarun yau ga Ma’aruf ya dawo garesu, ga Ma’aruf Babba ga kuma Ma’aruf k’arami, kai lallai Allah mai lullub’e bawansa da tulin Rahamoninsa ne, bayan cire tsammani sama da wad’annan tulin shekaru yau saiga Ma’aruf Allah ya dawo masu dashi garesu, family d’insu sun kuma had’ewa waje guda, bayan tilin iftila’in da suka fuskanta, bayan sab’ani da rashin fahimta da yai tasiri cikin rayuwarsu yau gashi komai ya bayyana masu, komai ya fito sarari....Which of the favors of your Lord will you deny...!

Cikin rawar murya take k’ok’arin ambato sunansa har lokaci bata daina shafa fuskarsa zuwa k’irjinsa da hannayensa ba, dik yanda hannunta ya sauk’a ajikinsa bin hannun nata kurum take da kallo tana mai tabbatarda cewa Eh shid’in ne dai gashi nan gabanta, ba gizo bane yake mata... A haka hannayenta suka iso izuwa yatsun hannunsa lokaci guda ta d’ago yatsun hannayen nasa tana dubawa, idanunta suka sauk’a kan d’an wani mark k’arami dake a cikin hannunsa wanda yake exactly irin na mahaifinsa ne, kuma tin yana k’arami shima yanada wannan tabo...Take taji wani irin kuka yazo mata mai k’arfin gaske, zuciyarta ta gama raunana, k’arfin jikinta yai rauni, k’afafunta suka gaza d’aukanta lokaci guda ta fad’a jikinsa tana wani irin kuka mai ban tausai.... Take Engr ya rungumeta sosai shima yana cazgan kukan da tinda yazo duniya bai tab’a irinsa ba... Allahu Akbar gaba d’aya illahirin jama’an dake wajen sai suka zamto masu tamkar tv, kowa hawaye ne kurum Ke gangaro masa mai gauraye da murmushin Farin ciki had’ida tarin al’ajabi... Harta su Haule saida jikkunansu ya sanyaya... Tabbas yau d’in sun yarda da K’udurar Ubabgiji ta wuce gaban wasa, buwayarsa ya wuce gaban tinanin d’an Adam... Akwai darussa mai tarin yawa a rayuwar wad’annan bayin Allah... Abida tayi sadaukarwa ga ‘yar uwarta Mariya, ta kuma fidda d’anta daga cikin ramin da azzalumai suka hak’a dashike da zuya d’aya tai hakan sai gashi Allah yaji k’anta ya dawo mata da nata d’an gareta.... Tabbas wannan ya isa ya zamto izna da ishara ga masu hali irin tasu, mu kasance masu yad’a soyayya sama da k’iyayya, mu kasance masu sadaukarwa a duk lokacinda mukeda ikon yin hakan, Allhairanmu Sufi sharrinmu yawa, tabbas idan muka rik’e wad’anann bazamu tab’e ba da izinin Ubangiji....

Ya Abidah kuka take sosai tana k’ank’ame da Engr yayinda shima Engr d’in ya kasa sakinta, sosai shima ya k’ank’ameta yana kuka tamkar ba shi d’inba... Allahu Akbar yau ina Babansa yaga wannan rana mai tarin alkhairi a garesa.... Cikin murya irinta mai kuka take furta “Ma’aruf d’ah na.... Ma’aruf ka dawo.. Ka dawo gareni.... Da gaske kaine ba mafarki nake ba.... Da gaske kaine nake rik’e dakai yau.... Da gaske bazan farka daga wannan mafarki ba.....!!” Kuka ya kuma cin k’arfinta...
Cikin kuka shima Engr yake jinjina kai yana mai furta “Ammmah nah.... Ni ne da gaske ni ne.... Ni ne Ma’aruf d’inki.... Ba mafarki kike ba ni ne right in front of you... Ubangijinmu ya cika Rahamarsa a garemu, Ya sake had’amu bayan wasu shekaru... Bayan na mance rayuwar da mukai a baya, bayan na mance komai gameda ahalina.... Amma Ke d’in jigoce da zuciyata da ruhi bazasu tab’a mancewa ba, randa dik sukai arba da kyakkyawar fuskarki dole su tina hakan.... Ammah na tino komai... Kallon fuskarki ya maidoda tinanin yaron da ya b’ace sama da shekaru talatin da bakwai baya...!” Zuciyoyi suka kuma raunana... Allah Akbar abin godiya, baka jin komai wajen sai sautin fitar kuka daga can k’asan zukata.... Lallai wannan ahali yau rana ce mai matuk’ar mahimmanci a garesu... Daula data fito dan tambayar ta ina zatai alwala dan already magrib ya sako kai, tin bayan sallan la’asar ake gudanar da wannan warware warware basu suka ida warwaran ba sai goshin sallan magrib, abubuwa da dama ne suka auku tsakanin sallan la’asar da kuma sallan Magrib....
Ganin mutane cirko cirko yasa Daula shan jinin jikinta har sai take tinanin dama bata fito ba ashe, sam batai tsammanin ganin mutane haka a tsakar gidan ba dikda cewa gida ne na biki amma batai zaton ganin manyan mutane haka ba harda maza, kuma ya dukkan alamu mihimmin abu suke tattaunawa, ga wani irin yanayi da d’aukacin fuskokinsu Ke ciki..... Har tasa kai zata juya ta hango wani tamkar Yayanta rungume da wata mata yana share mata hawaye., Yanayin data gansa ciki bata tab’a ganinsa cikin irin yanayin ba tsawon shekarun da sukai tare....
Jiki a matuk’ar sanyaye Daula ta soma takowa tana mai bin jama’an dake wajen da duba a matuk’ar d’arare... Toh lafiya... Badai wani abin bane ya sami Khalid ko Daddy tinda tasan hakan ne kawai zai kawo Yayanta gidan sirakan Khalid... Toh amma tambayar anan shine wacece Matar da Engr Ke rungumeda ita ya kasa sakinta....
“Yaya...!” Ta furta tana mai dubansa jiki a sanyaye sanda ta k’araso garesu... Sai sannan Ya Abida ta karkato tana duban wacce tai magana sakamakon sinkayo murya irinta mahaifiyarsu da tai, su Mamy da Bara’atu bugun zuciyarsu ya kuma k’aruwa sanda suke kuma dubanta, tabbas sunji da kyau Yaya ta kira Ma’aruf da bai jima da bayyana masu ba.... Kodai hasashensu ne ya zamto gaskiya...? Basukaiga bashi amsa ba sukaga Engr Ma’aruf ya nufeta yana kuma janyo hannunta lokaci guda yake furta “Daula finally... Yau mun had’udasu... Come zo, zo kigani da idanunki.....!” Gaba d’aya kallo guda zaka masa ka fahimci har yanzu Shock d’insa bai sakesa ba dikda juriya da k’arfin hali da yake k’ok’arin nunawa....
Daula da jikinta ya gama sanyi duban Engr take tana duban mutanen da ya kawota gabansu mata guda uku Mahaifiyar Nabilah saiko wasu guda biyu wad’anda kallo guda zaka masu ka fahimci ‘yanuwan juna ne dan ga wani sihirtaccen kamanni da sukedashi.... Ganinsu su uku haka a gabanta take ya haifar mata da wani irin fad’uwan gaba, taji k’irjinta tamkar an sauk’e mata guduma... Kai tsaye bazatace ta tab’a sanin masu irin fuskokinsu ba amma sai tanaji can k’asan zuciyarta kaman sunsan juna tinda jimawa, like they’re connected somehow.... Cikin rud’ani take duban Engr da ya kasa sakin hannunta kana tace “Yaya what is going on here...? Is something wrong...? Wani abu ne ya samu Daddy da Khalid...? Please talk to me...!” Ta k’arashe cikin tsananin nuna damuwa, yayinda Yaya Abida, Mamy da kuma Aunty Bara’atu suka kasa d’auke idanunsu daga barin dubanta.... Wannan tabbas ‘yaruwarsu ce Fatima, domin kaw mahaifiyarsu ziryan suke kallo a gabansu.... Engr kansa kasa furta komai yai sai kallonsu su hud’u d’in da yake yau Allah ya kuma had’asu gaba d’aya... Sameer da sassanyar murmushi ta kasa barin fuskarsa takowa yai kad’an ya tsaya daga gefen Engr wani ikon Allah sai kamanninsu da Engr ya fito k’arara... K’wayan idanunsu yai shige da juna dan irin k’wayan idanun su Mamy suka d’auko... Sai yanzu suke fahimtar abubuwan da sukaji gameda juna had’uwarsu ta fari ashe sud’in tushe ne guda...
Abbah dake gefe matsan k’walla ya kumayi farin cikin da yake ciki ya gaza b’oyuwa, dole ne ma ya taya Mariya Farin ciki bayan irin gwagwarmayar rayuwa data fuskanta, a hankali ya silale ya fice sanda zuciyarsa ta shiga tino masa abubuwan da yaji gameda Mamaninsa, babban abinda yafi d’aga masa hankali tana sane da duka wannan ta d’auki karan tsana da tsangwama ta d’aura kan Mariyarsa bama ita kad’ai ba harda Zulfa’u da take jinjira ce a lokacin kuma ba ita ta haifo kanta a wannan rana ba, Mamani bata tsaya a nan ba tasa shima kansa ya dinga ganin laifin Mariya duk da sunan yana biyayyawa mahaifiyarsa...Shin ta ina zai soma d’aukan girman hakkin Mariya da Zulfa’u....Dole ne ya nemi waje ya keb’e shikad’ai, Mariya yau d’in cikin Farin ciki take bai kamata ya aza mata nasa damuwar ba, bayan tilin iftila’in data fuskanta a rayuwa yau d’in ta cancanci farin ciki... A daidai hanyar fita idanunsa suka sauk’a kan Lami dake sanne sannen kai tamkar tsohuwar munafuka... Idanunsu kaw suka sark’e waje guda... Duba guda Abbah yai mata ya d’auke kansa kana yai shigewarsa.... Wani irin k’ugi da cikin Lami yai da ace akwai wani gefenta tabbas da sai yaji wannan sauti... Suna murnan yau zai kansancega Mariya da ‘yaruwarta ranan tozarta ranan bak’in ciki sai gashi ya faru akansu, sai gashi ya juye ya koma kansu, ashe farin ciki mai d’orewa da aukaci burin samu a yau d’in ashe ba nasu bane, wacce suka kafa mata tarkon bak’in cikin ashe itace dai mai samun farin ciki.... Lami taji duniyar gaba d’aya tai mata d’aci...Ji tai inama ana iya maida hannun agogo baya tabbas da ta maida ta gyara kuramuren da tai, tabbas da bata biyema Haule sukai son zuciya ba... Yau wa gari ya waya...? Ita batada tsuntsu batada tarko, ko Abbah bai koreta ba bata tinanin zata iya ci gaba da zama tana fuskantar Mariya da Ma’aruf harma dashi kanshi Abban... Ita ba zuri’a ne da ita a gidan ba balle su kasance tareda ita... She’s all alone now, Tai imani Haule ta jima tana munafunatarta kenan dikda cewa tana nuna mata tare suke aikata komai, ashe tana b’oye mata wasu abubuwan... Sai yanzu ta fahimci nufin Haule na aurawa Ma’aruf d’iyarta Sahariyya Wato ita da mijinta idan Ma’aruf ya auri d’iyarsu su sun tsira ita kad’ai za’a bari a rana.... Lallai Haule ta cika makira butulu....! Tamkar kazar da aka tsamo cikin ruwan zafi haka Lami ta janye k’afufunta ta nufi nata sashen zuciyarta na mata d’aci.... Ga goggonayen Kazaure sai b’alla mata harara had’ida Allah wadar suke har Lami ta bar wajen....
Su Baffah Wada da Baffah Ado kuwa sun kasa aminta da wannan al’amari da ya bayyana kansa yau, koda ace mahaifiyarsu tsananin soyayyar Usman yasa ta rufe sirrin cewa shid’in ba d’anta bane sunaga Ya Usman ya cancanci yasan gaskiyar Al’amari yasan wacece mahaifiyarsa ko dan ya dinga isar da addu’arsa gareta, girman mahaifiya ya wuce wasa koda ace haihuwarsa kawai tai rainonsa da shayarwansa dik na wuyan Mamani amma dikda haka ya cancanci yasan asalin labarin, hakan baikai ya baiwa Mamani dama ta rufe wannan babban Sirri a gareshi ba... Ya Usman mutumin k’warai ne d’an uwa da kowa zai alfahari dashi, shid’in shine katangan family d’insu shine kuma Uba a garesu... Tsananin tausayin d’an uwan nasu ya kamasu, suna gani Baba Alhaji ya rab’a ta gefensu ya fice sim sim cikeda borin kunya... Suma d’in waje suka nufa dan gabatar da sallahn magrib suna fatan su tadda Abbah a masallaci su kuma supporting d’insa a irin wannan lokaci mai matuk’ar wahala a gareshi... Sameer da Engr ma a tare suka fice suka nufi masallaci jama’a ‘yan unguwa sai kawo masa gaisuwarsu suke suna fad’in yau ga his Excellency har unguwarsu kaikace already yaci zab’en ne sabida yanda jama’a Ke tururuwar zuwa gaidashi, har wad’nda basa zuwa wannan masallacin yau saida sukaje... Sameer kaw na taredashi sai sakin murmushi yake yanajin dad’i har k’asan zuciyarsa na kasancewarsa tareda d’an uwansa...

A cikin gida kaw banda tafasa babu abinda k’irjin Haule keyi, tabbas da za’a tsaga k’irjin Haule watak’ila aji yanda zuciyarta ke tafarfasa sabida tsananin k’unan zuciya... Ji take tamkar ta k’arasa ta shak’e Mariya da ahalinta gaba d’aya su mutu ta huta da wannan bak’in rana da take gani.... Idanunta suka sauk’a kan Yaya Abida yanda ta had’e ‘Yanuwanta gaba d’ai ta rungumesu gaba d’ai suna hawayen Farin ciki ga annashuwa da annuri da ya kasa barin fuskokinsu.... Haule tamkar zakanya haka take huci tana dubansu yanda kasan zatai tsalle ta wantsalo ta capkosu ta cinye d’aya bayan d’aya haka nan take dubansu, tamkar d’an wasan Dambe a filin kokawa haka Haule Ke bud’e hannaye tana haki tana duban bayin Allahn nan da duniyarsu ta yalwatu da Albarka... Wato Bara’atu da Abida sun cuceta sun jima suna tarwatsa duk wani shirin da take... Idanunta suka sauk’a kan Bara’atu da itace ta munafuncesu ta k’ulla aminci k’arya dasu... Tabbas sai yanzu take ganin wautansu.. (Niko nace Haule ai shi mugunta fitsarin fako ne... Kuma kece dai baki sani ba amma dik kalan asirinki da imani da ‘yan tsubbu da kikai bawa baya tab’a yiwa d’anuwasa bawa abinda Allah bai k’addara masa ba.... Asiri da sihiri gaskiya ne tinda har yai tasiri akan fiyayyen halitta babu wanda yafi k’arfin sammu ko sihiri ya kamasa saidai duk wannan zai faru ne da izinin Ubangiji... Mariya batada wani makari sai Allah data rik’a Wanda yafi k’arfin bokayanku da malaman tsubbunku... Su Haule sai a koma islamiyya a yak’i jahilci idan kinada sauran RABO)...

Tasa kai cikeda takaici zata fice dan wani irin haushin mijinta ne ma ya taso mata, wato shima ya munafunceta ne ashe yasan wani sirri da ita bata sani ba, yasan Usman ba d’an Mamani bane amma bai tab’a koda gigin gaya mata ba tsawon shekarun nan da suka jima suna k’ulla makirci tare... Lallai ta yarda namiji ba d’an goyo bane... K’wafa tai tasa kai zata fice dan yau ji take dik wanda ya tink’areta kansa zata huce duk wani takaicinta.... Kaman daga sama Aunty Bara’atu ta hangota zata fice cikin sauri ta k’arasa gaban Haule had’ida shan gabanta, dakakkiyar murmushi saman fuskarta “Haba Haule har zaki fice babu sallama... Akwai sauran buduri fah dan nasan har yanzu bakisan wacece matar Ma’aruf ba... Kuma sai ki tafi babu ko sallama duk irin wannan kwalliya da kika cab’a... Haba Haule ni ce fah AMINIYARKI ta sirri...!” Ta k’arashe tana kuma sakin murmushi kana tace “Ko yanzu Kasuwa ta watse Haule d’ankoli yaci riba... Mariya dai gata nan daram dak’am saidai gani daga nesa ga ‘yanuwanta kewaye da ita, ga d’anta Ma’aruf tareda ita... Bugu da k’ari ga ‘ya’yanta sun samu zaratan Maza na k’warai wad’anda Al’umma Ke alfahari dasu.... Wa gari ya waya yanzu Haule....?....”
Ta kuma murmusawa kana tace “Barka da shiga duniyar k’unci Haule, aci gaba da girban shuka na tabbata duk abubuwan da kikaji kika gani yanzu na gaba sai sunfi d’imautaki.... Sai a tanadi ruwan barekata a gefe na rage k’unci....” Ta k’arashe tana mai kuma murmusawa had’ida juya idanu lokaci guda ta d’agawa Haule yatsa guda tace “Chau.... Aminiyar Sirri..!”

Haba Haule kaman ta yanki Jiki ta fad’i ta mutu ta huta haka nan taji tsaban bak’in ciki dake cazganta... Tanaji tana gani yanda Mamy da ‘yanuwanta suka cika da farin ciki..... Tamkar wacce ake hankad’ata haka ta fice fuuu tanaci gaba da huci tagajan magajan...
Yara Almajirai sai gudu suke a hanya suna kauce mata a tinaninsu mahaukaciya ce sabuwar kamu.....

Wani kayan tashin hankalin had’ida mamaki Haule ta tadda gidanta,gungun ‘yan daudu ta gane shak’e a k’ofar gidan ga mai gurmi da garaya na kad’a masu sun nufi cikin gidan ga wata mata tsakiyarsu lullub’eda mayafi, sai tik’an rawa suke suna kad’a kafad’a da kwankwaso suna tururwan shiga gidanta... Mamaki ya cika Haule tai birki tana kallon ikon Allah Mai gurmi kaw bai fasa kad’awa ba...
Su Amara da ayarinta dake tsakar gidan suna wak’e Sahariyya da ta fice a hayyacinta tana kuka tamkar ranta zai fice ai birki sukai da nasu shagalin ganin iyayensu Sun faso taro.....

***

A can gidan Aunty Bara’atu kaw dik wainar nan da ake toyawa amaren basuda labari, Zulfah ce ma gabanta ya tsananta fad’uwa musamman dataga ango Akram bai kirata ba kuma bataji daga garesa ba gashi Atika ta kira wayan Yusuf taji ko lafiya yafi abinda yafi amma wayar Yusuf bai shiga, itama Atikar dik abin ya soma damunta musamman da sukaga angon Nabilah ya kasa barin gidan, dan koda suka fice da rana rakiya yaima friends d’insa zuwa masauk’i amma gashi yanzu haka ma ya dawo yana jiran Nabilah a parlor.. Haka dai Atika taita bata baki tana cewa lafiya Akram yake in sha Allah.. K’ila dai kan ango ne yai zafi tinda aure ba wasa bane...

Da k’yar Nabilah ta kuma ficewa wajen Khalid sai faman ture turen baki take tana fad’in itafah an tak’ura mata... Yusrah tana mata rakiya zuwa k’ofa ta juya tana fad’i k’asa k’asa “A sha love lafiya amaryar Bear...”
Harara Nabilah ta galla mata kana tace “Wai bazaki shigo ba kina nufin ni kad’ai zan shiga...?”
Yusrah ta kuma k’unshe dariyrta tace “Wa ki rufamin asiri kada oga Bear yai jifa dani ta taga... Kedai Ina wajen su Addah Zulfah idan kun gama...”Bata jira cewan Nabilah ba ya juya a guje....
Nabilah na kiranta inaa Yusrah ko waigowa batai ba ta shige cikin gida abinta.... K’irjin Nabilah yaci gaba da bugawa... Amma Yusrah tasan kan tsiya datace zatai mata rakiya ta koma... Zatai maganinta ne.... Ta d’aga kai ta dubi k’ofa tasan yana ciki yana jiranta, wani ikon Allah Wai Khalid ne take matuk’ar jin nauyin Keb’ewa taredashi a yau d’in saikace ba Khalid d’in data saba tsefesa da masifa ba... Da k’yar ta iya saita kanta ta gyara mayafinta ta nufi parlorn sallama saman bakinta cikin muryrta da bai fitowa sosai....
Khalid dake zaune yana shafa wayarsa saurin janye idanunsa yai daga wayar had’ida k’urama k’ofar idanu... Teddy bear d’insa ya hango shirye cikin shiga irinta matan aure, yalwataccen mayafi wanda yakai har gwiwarta, tana sanye cikin leshi golden yellow da yai matuk’ar mata kyau dikda fuskanta kife yake a k’asa... K’uri yai ma k’afafunta yanda take takowa a hankali yana kallon zanen flower na lalle da aka rangad’a mata wanda ya dace da kyakyawar fatarta da ya amshi gyara sosai.... Har yanzu ganin abin yake tamkar mafarki Wai Nabilarsa ta zama matarsa... Haka ya dinga tino tun farkon had’uwarsu da irin gwagwarmayar da suka sha kafin su mallaki juna... Tsan tsan k’aunarta na kuma ratsa duk wani k’ofa na zuciyarsa.... A hankali ya mik’e tsaye sanda ta iso cikin parlorn... Har lokacin kan Nabilah na k’asa ya kasa d’agowa ta dubesa sai bugu da k’irjinta keyi... Khalid ya tako a hankali har zuwa gabanta.. Ganin ya taso ya nufota ya sanyata d’an saurin d’ago fuska sai kuma ta maida kanta k’asa... Ta lura ya sauya shiga shima, half Jampa ce dark ash jikinsa kansa babu hula sai sumarsa da yasha gyara ga k’amshin nan nasa ya cika parlorn gaba d’aya...
Shiko Khalid cikin zuciyarsa cewa yake yanzu haka had’o masifar da za’a masa ake tinda gashi ko gaisuwa har yanzu bai samu ba... Kaman wacce taji zancen zucin nasa nan ta soma gaishesa cikin tsananin sanyin murya wanda har saida ya sanya Khalid jin wani abu na tsagar masa, gaisuwa mai cikeda wani irin ladabi ta masa ba irin wanda ta saba masa a baya ba, tabbas ya kuma yarda sud’in ma’aurata ne... Take yaji kimanta na k’aruwa cikin idanunsa a hankali....
A b’angaren Nabilah kaw har ta cire ran Khalid bazai amsa mata gaisuwarta ba ta sinkayo muryarsa na fad’in “Mu zauna mana first... Ko sauri kike ne....?”
Satan kallonsa ta d’anyi tanaso ta danna masa harara amma ta kasa ga k’irjinta dake matuk’ar bugu.... Bata ankaraba saijin tattausan hannunsa tai saman nata, bugun k’irjinta ya k’aru, tamkar rak’umi da akala haka ta shiga bin bayansa har saida ya zaunarta saman kujera... Shima yai masauk’i ma kansa a gefenta... Ta d’an matsa gefe kad’an tana mai gyara zamanta... Yai kaman bai kula da abinda take ba saima k’ok’arin ciro wayarsa da aka soma kira cikin aljihu da yake....




SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_





*93*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Magaji da fitowrsa kenan daga masallaci an ida sallan lisha, yana k’ok’arin bud’e shago ‘yar wak’ensa a bakinsa sai cin karo da mutum yai zaune gefen shagon ga duhun dare da ya soma shiga...Baiji mamakin ganin Hafiz mak’ale wajen ba saidai yanayin da yaga Hafiz d’in ciki ya d’aga mar hankali.... Tak’ure yake gefen dakalin shagon Magaji very miserable, duba guda zaka masa ka fahimci Hafiz ya fice hayyacinsa gaba d’aya, a idanunsa Engr Mutallab yaita alkhairima jama’an unguwarsu, ya tabbata salon munafunci ne kawai irinta ‘yansiyasa...
Magaji ya d’an dubeshi kana yace “Wai dama nan kazo...?”
Bai amsashi ba saima kauda kai gefe da ya kumayi sakamon hasken wutan lantar da nepa suka dawo dashi ya haske fuskan Hafiz.... Zama gefensa Magaji yai yana mai furta “Abokina, hak’uri da saka ma zuciya dangana da amsar k’addaran cewa Zulfa’u yanzu ba taka bace shine kawai zai ficceka.. Amma duk wannan shiga damuwa da tada hankali babu abinda zai haifar maka illa....” Baikai aya ba Hafiz ya katsesa da fad’in “Kaga dalla Malam ya isheka... Idan wa’azi kake so ka tafi bakin masallaci mana ka d’au speaker, ka wani Zo nan zaka cika min kunne, da wanne zanji da k’watan matata na fin k’arfi da akamin ko da wannan surutur naka... Kuma da kake cewa

Please Login or Register in order to submit comment