Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya har Bedroom dinsa yana Saman Bed ina kasa a tsugune yana ta faman cika yana batsewa ga jarabar takama,yace gobe ki shirya 8am kuje ku gaisar da Hajja kakarmu ko me zata ce karki mayar mata da martani kiyi biyayya,nace to Insha'allah,yace muje yanzu wajen Abbana,nace au kana da Baba mahaifi? Yace of Course ai ni dan gata ne Umarninsa nake bi,murmushi nayi nace kuna kama? Yace mene kika tambaya? Idan kuna kama to nasan Babanka ma me kyau ne ko Ummanka ka biyo?ke dadina dake shirme,Ummanka ta rasu ita? Ya daga kai tare da cewa kuma nafi son Abbana ba tun farko,Nace tab ni kuwa nafi son Ammah,Abbanka yana Sonka kenan da yawa gani nayi yana ta farin ciki kawai akan nayi zancen Abbansa lallai yana sonshi,fuskarsa na leka nace Dan Abba zan dinga ce ma yanzu,muje na ganshi ma zan dinga kai masa abinci,yace ai ba komai yake iya ci ba,bashi da lfy ya fada kwalla kamar zata zubo masa,nace eyya ai Insha'allah zai warke ne,lets go kawai yace min,nabi bayansa falau falau da hijab muna ta sheka uban tafiya yana gaba ina bayansa har muka je wani building a Cikin gidan katafaren me kyau,ciki muka shiga kafin ma mu Isa inda zamu hau steps duniya ce guda ko ina kuma Securities ne masu tsaron Daddyn Aayan, sannan muka haura sama can wani Bedroom shima nan duk sune suke tsaro har cikin dakin,saman Bed na hango shi dattijo kyakyawa irin Aayan suna kama sosai sai daí Aayan ya fishi farar fata,sallama mukayi masa da mamakina naji ya amsa yana murmushi tare da cewa My Son kazo ke nan,Aayan ya karasa jikin Bed din tare da rike hannunsa yace Daddy ya jikin? Alhmdllh Son yanda kasan jikin kullum haka yake ina so na taka kamar kowa Amma bazai yuwu ba,kana gani komai sai dai ayi min haka nake ba inda ke motsi a jikina sai baki na,addua kawai itace Mafita tunda ba inda ba aje ba ciwo yaki ci yaki cinyewa,to hakanma mun godewa Allah.

Ina mamaki yanda yake fes haka cikin koshin lfy ace wai baida lfy komai nasa baya motsi gashi shar dashi muryarsa ras haka,a hankali naga Aayan ya rada masa magana a kunne nan take ya fara murmushi tare da cewa Yata matso kusa ya kika tsaya nesa,Da Sauri na karasa gaban gadon tare da durkusawa har kasa nace Ina yini ya jikin?Yace Alhmdllh,nace Allah kara lfy,Ameen yata Gashi nan sai kinyi hakuri kin ganshi baya jin magana na dade da cewa ya kawo min ke sai ya dinga min hanya hanya,Murmushi nayi ina jin kunya nace ai yanzu ya kawoni kuma kullum zanzo ba sai ya kawo ni ba yanzu tunda na gane hanya,Murmushi yayi tare da cewa na gode Allah ya muku Albarka,ya albarkanci aurenku ya baku zuria ta gari,Ya sunan yar tawa nace Mufeeda,Alhmdllh naji ance da kannenki ko?nace ae yace to Allah rayasu ya musu Albarka nace Ameen,Allah yaji kan mahaifiyarku nace Ameen Daddy, ki kara hakuri kinji,zaman gidan nan sai hakuri,wannan dan nawa baya ji kin ganshi ina fama dashi sai kinyi da gaske saurin fushi gareshi ga zurfin ciki,ki rike min shi da Amana yata kinji,nace Daddy ai shine sai ya dinga fada yana fushi, Dariya yayi sannan yace to zan masa fada,nace to Daddy,Harara Aayan ya zabga min nayi shuru dani,Mun dan dade a dakin Aayan suna ta hira sannan yayiwa Daddy sallama muka dawo part dinmu,na wuce dakinmu shima yayi samansa.

Cikin dare 2am na farka da ciwon Mara sosai naji kamar abu ya zubo min a pant,mikewa nayi da Sauri na shiga toilet,sai naga period nima na fara dan ban taba yi ba sai yanzu,Meenat kanwata kuwa ita tun tana Jss 2 ta fara dama ta fini kiba, fitowa nayi tare da tashin Meenat nace Meenat tashi ki bani pad nima na fara period,cikin magagin bacci tace Sis ta kare tun last month wacce kika siyo min na karar da ita,To fa yanzu ya zanyi kenan,ki Sa tsumma kafin gobe,ke da rushing na fara fa wlh tsumma bazai daukeni ba kinji yanda yake tsiyayowa kuwa,to yanzu ya za ayi kenan,nace bani dankwalin tsohuwar a tamfar nan taki na Sa naje Wajen Aayan ya san ya zaiyi dani,Meenat tace baki jin kunya? Kuma kin san bazai je ba sai dai yasa me gadi,a'a zai iya karbo min ko wajen yan matan gidan nan ne kema kin san Bazan iya kwanciya haka ba gashi dare yayi dole tunda lalura ce kuma yasan mata sunayi ai dole gunsa zan je.
Haka ne kam jeki to muji,nan na karbi karamin dankwalin na koma toilet tare da gyara jikina don nasan kafin naje sama Na dawo na bata kayana ko ma ya dinga saukowa saman tiles.

Cike da tsoro na masa knocking shuru har sai da nayi yafi sau goma sha sannan naji yace Am coming yana jan tsaki ya bude min kofar daga shi sai wani dan tight short karami ko riga babu a jikinsa,daki ya koma nabi bayansa Sabo da ya kunna light din haske ya gauraye dakin,lfy ciki dare? Na fara ina ina uhm...uhmm..na juya baya tare da tamke idona kawai na maze kamar bani na fada ba nace ehmmm wai..Wai,yace to fitar min tunda baki da abin fada,da Sauri nace period na fara kuma bamu da pad gashi dare yayi ko zaka karbo min wajen kannenka na karasa tare da matse idona kam na juya masa baya.

Tsaki yaja tare da cewa sai ki bari sai gobe kya siya ni me ya shafeni a nan fitar min a daki na zata wani abu ne,Marairaicewa nayi ina rokonsa dan Allah Dan Abbansa ka amso min pls haba Na Daddy,kallona ya tsaya yi yanda nake shagwaba kamar yarinyar yaye, hannu ya daga min hey..hey Hold it thr ban son shirme see u ko kunya baki ji kina min shagwaba ya fice fuuu ya barni,murmushi nayi tare da cewa oho dai ni dai ka karbo min shike nan.
Yana fita na fada saman Bed dinsa nace sai na more naji dadinsa yau dai na dinga birgima a kai ina tunanin zaman da zamuyi wanne Hali zan aro na daurawa kaina dan naga karshen yan iskan gidan nan,tsawa naji keee...Ban san sanda na fado kasa ba dan na manta a Bed dinsa nake,yace Iskancin naki har ya kai Bed dina nan take ya bude wardrop tare da dauko sabon bedsheet ya jefo min tare da cewa cire min wannan kazantar zaki shafa min a Bed shimfida min new, ban bata ma bafa kalla ba komai a kai fa,i wl slap u,ba shiri na cire wancan na shimfida masa wanda ya bani tare da dame masa yayi kyau,wani turare ya miko min ungo fesa a saman Bed din,haka na fesa,yace to jeki da wannan ki wanke min gobe ki dawo min da Abuna Kazama,nace haba Ranka ya dade ka rage irin wannan ni fa matarka ce Amma kwata kwata baka kyautata min,ko Auren business ai ka bari dai mu rabu lfy Amma ba komai bani abun na tafi,naje sunyi bacci ban samo ba,To su manyan matan su Abbi fa? Ko lokacinsu ya cika basa yi su? Baki ya tabe tare da cewa bama shiri taya zanje nace su bani sun san ke zan bawa baza su bani ba,kuma dare yayi bare a siyo,sun tsofe ma wanne period zasuyi ai sai yayansu, nace to ni yanzu ya zanyi na fada kamar zanyi kuka ina doka kafafu,tafi ki san me zaki Sa sai gobe,ni Bazan tafi ba ya kake so nayi dan Allah,tunda farko ne ai bazai miki da yawa ba kije kawai,nace to ni nawa ba haka yake ba kana ta sani ina fadar badala da rashin kunya a baki na,baka san yanda nake ji ba idan ina ambata irin wannan lafazi na Badala a gabanka, murmushin da bai shirya ba ya saki,oh nan kunyata kike ji kenan,wlh da kyar nake iya magana lalura ce ta kawo ni dan Allah a san yanda za ayi dani Na Daddy Allah dai yaji kan Mommynka ya dauraka akan makiyanka,jin nayiwa iyayensa Addua sai naga ya saki ransa kamar wanda aka Yiwa Bushara da Aljanna yace to yanzu ya za ayi kenan? A raina nace na gano lagonka,nace babu 24hrs ne a Kano?Yace da dai Abuja ne sai a samu kuma kinga 2am ba kyau fita ko fitsari tsakar dare nace haka ne,amma muje mana wajen yan matan ka rakani ni zan san yanda dole ma su bani.yace to muje a Cikin wardrop ta jikin Bed suke ajiyewa,nace an gama muje.

Tiryan tiryan muka je har kofar dakin daya,yace wannan dakin Hanifa ne,ai ko na dinga knocking kamar dakina ta bude sai ta ganni tare da Aayan da har zata min masifa ganinsa yasa tayi mukus don tsoronsa suke ji,ni kuma da tsokana kawai nayi ciki da ita tare da tureta na banka cikin dakin,direct na bude wardrop Aiko na gansu a jere na dauko sinki daya na bude na kwashi guda uku sannan na watsar da ragowar a kasa nazo zan wuce na bata rai,tace wlh baki Isa ba ni zakiyiwa wulakanci har Bedroom,na kalleta sama da kasa nayi irin gwanar nan nace How Dear u zaki na min magana any how duk wanda yaji zaice na gama kwarewa da Turanci,taki Sakina kuwa,na kira Aayan Babyna da Sauri ta sakeni tana hararata na fito nace masa muje to,muna Tafiya a hanya nace nayi fashi da makami kaga abinda baza ka iya ba,kai kullum sai ka dinga zura musu ido kamar wanda suka Yiwa asiri danma suna jin tsoronka ai da tuni ina ga kowa ma taka ka zaiyi.

Ki shirya gobe zasu zo daukan fansa wlh harda iyayensu,nace dan Allah ina son muyi magana da kai Na Daddy Allah ya karawa Daddy lfy da nisan kwana, ina binsa a baya da Katon Hijab dina har Bedroom dinsa,ya fada saman Bed dama yasa jallabiyarsa,a hankali na zauna a gefen Bed din ina jin tsoro,ina jiran naji tsawa sai naji shuru,ina zama ina cewa Fatana Allah ya bawa Daddy lfy wlh a gidan nan,da anga yanda zaifi kowa Sonka ai da kafi karfin kula mu ma Sabo da ka zama Gold,yanda naga Daddy na Sonka abin sai wanda ya gani inama Abban mu haka yake irin naka na furta tare da kwanciya na mike sambal a gefensa,tunanina wayo zan masa shi kuwa tuni ya san me nake nufi Amma sai ya shareni ya gama ganin iya wayon nawa me nake nufi.

Dan Daddy wai ya maganar schl din tawa,yace anzo wajen,nace dan Allah Oga kwata kwata ka kaini schl,yace hmm yana dariya a ransa wai shi yar wannan Jaririyar zata Yiwa wayo,yace dama Arabic da boko kika shiga a hade tunda naga kinfi kokari a Arabic sai ki hada biyu abinki,nace ah gaskiya a'a nima nafi son na zama yar boko sosai,to ki zabi wacce kike so sai na biya miki,Nace to, Amma ai sai dai wani ya kaiki,bani da time ki samu wani a yan uwanki ko frnds su kaiki zan baki kudin,nace to zanje Amma dan Allah kasa a kaini a mota kaga raina ni za ayi a gidan nan,yace an gama,duk tunanina da gaske yakeyi sai murna nake yi nayi masa wayo,nace saura kayan sawa zamuje shopping Sabo da goge raini,yace nawa ne zai Isa a goge rainin?nace ko dubu goma sun isa,ya kyalkyale da dariya ku Uku dubu goma to kaya kala nawa zaku dinka kenan nace kala Uku Uku ko hudu,yace lallai dasu zaku goge rainin kenan? Nace to ni ban san kaya ba tunda ai kasan ba siya muke sosai ba.kawai biye min yake yaga iya wayon nawa.

Dan ya nuna min na masa wayon sai yace bude can,naje na bude wata Wardrop,nan take na kusa sumewa kudi ne a jere a jere bundles da yawa na Dubu dubu da dollers,yace ebi yanda zai isheku,nan take gumi ya keto min na rude na rasa yanda zanyi jikina yana rawa na ja baya tare da cewa ni dai sai dai ka bani da kanka, ba yanda baiyi dani ba kan na dauka Amma na kasa sai ma shagwabewa danayi zanyi Kuka kudin sun tsoratani,mikewa yayi tare da kwaso Bundles goma yan dubu dubu ya zube min a gabana yace jeki dasu ai sai na fashe da kuka nace bana so ni,kamar naga wani Dodo na dinga ja da baya,yana dariya a ransa a fili yace kefa kike son kudi,nace ni ba irin wannan nake so ba,tunda kace sai na Eba da yawa to bani dubu ashirin sun ishemu komai da Komai,yace naga ai an baki kudin Sadaki har dubu dari Uku ya kikayi dasu?lokacin ai bana cikin hankalina Sabo da rashin lfyar Ammah da rasuwarta duk a nan suka kare.

Bundle guda ya bani na yan dubu da kyar na karba na tsaya ina tunani,kafaduna biyu ya rike tare da bude kofa ya jefa ni waje tare da rufe kofarsa,Bedroom dinmu naje da murna na nunawa Meenat tace gaskiya Sis tsakani da Allah kin damemu a wannan tsakiyar dare 3am ta wuce kinki bacci sai labarin mijinki kike mana ki kwanta mana ki huta,ni dama idan labari na Cina to komai dare sai na tashi mutum na fada masa,bayan na shirya kaina duk sun koma bacci har na kwanta nima na tuna ban fadawa Meenat labarin Daddy Baban Aayan ba.

Tashinta na fara yi Meenat Meenat ku tashi kuji banza suka min nace wai ina magana kun rainani ko,muna ji ki fada mu wlh bacci muke ji ke bakiyi ba kin hana kowa yi,ina basu labari suna uhm..eh...to...har bacci ya kwashe mu,kafin asuba wayata tayi kara ta tasheni ban dauka ba Amma sai na tashi Meenat,kawai sai ta fashe da kuka wai na hanata bacci,nace to yi shuru kwanta jaraba bakwa jin maganar Ammah tace kuyi min biyayya Amma bakwa yi,Maeesha ta farka itama tayo fitsari muka koma bacci,ni dai banyi wani baccin kirki ba sai na dinga tunanin Mijin Kasuwanci na.

Washe gari da Safe lafiyayye tea na hada mana Sai kwai na hadashi murtuk dashi naga banza ta fadi irin muci rabonmu kafin yasa a kwashe mu koma Koko,sun sha Uniform dinsu ni kuma doguwar riga da dan hijab karami,tun Safe yan gidan suke ta buga mana kofa ina ji naki budewa,bugun duniya naki budewa sai ma kara Sa lock da nayi,Ina jin Abbi yana zunduma mana ashar akan naki budewa yaransa kofa,wai nice ma zan musu breakfast kuma abinda suke so haka kowa zai fada na dafa musu,ai kuwa bugun duniya muka ki bude kofa gashi suna jin motsinmu,Abbi na gani ta jikin window ya leko yace sai kun bar gidan nan wlh tunda ba yar arziki bace ke,yar Iska,guntuwar shegiya haka ya dinga zagina ta window,na kalleshi ido da ido tare da Galla masa harara na murguda masa baki,yace zaki ci ubanki wlh sai naga waye ubanki a kasar nan,tafi nayi da hannuna na kara Harararsa ina gatsina masa goshi da gira,ni dai bance komai ba,yana ta zagina,ke yarinya ki shiga hankalinki,a nan nayi magana nace Yarinya tana bayan Uwarta ni dama haka nake idan naji haushi bani da mutunci ba kowa nake iya dagawa kafa ba ko za a kasheni,Meenat tana ta dariya Abbi ya kara kulewa,ya bar wajen a fusace yana baza babbar riga.

Aayan ne yake saukowa yasha wankan gaske cikin kana nan kaya,kamshi na tashi,Meenat tace ina kwana suka gaisa,Maeesha ya rikewa hannu tare da cewa ba gaisuwa yau?tace ina kwana tana dariya,tace kayi kyau Yaya,tnx yace sannan ya kalleni tare da cewa Abincina fa? Ai ban san zaka ci ba bari na hada ma tea,yace a'a Kunun gyada nake so ko Koko ni,idan babu kuma sai ki bani Tea,ai dole nayi maka,yo Allah na tuba ko ba gasara ai dole a nemota kamar Dan Daddy guda yana so akanta ba sai ayi yaki ba a gidan nan,Dariya na bashi sosai yanda nake maganar cike da girmamawa kamar Ina gaban Sarki,kun san wasu mazan akwai son a yabesu ko a girmamasu,wasu kuma suna so a daraja musu iyaye ya dace mata su dinga fahimtar mazajensu.

Shi Aayan a ransa yace zan gama kure wayonki yarinya har yaushe aka haifeki,Kitchen na shiga dama jiya na tace mana markaden koko,sharp sharp nayi masa tare da soya masa Chips tunda ba time din yi masa kosai,a Dining na ajiye masa sannan na dawo palo wajensa nace Ranka ya dade an gama,a ransa yace zanyi maganinki soon wai ke me wayo.

Ni na zuba masa da kaina,yana shan abinsa yayi nisa nace da sha nace Dan Allah ina neman wata Alfarma idan da hali ba damuwa kuma ban takura maka ba,yace ina jinki,nace so nake ka bani Driver daya da mota za a kaini unguwa zanje shopping sannan zamu je schl din da zan shiga,waya naga ya dauka tare da danna kira Malam Garba shugo ina son ganinka,minti kadan sai ga Malam Garba Driver yazo,Key din mota ya miko min na karba,yace gasu nan daga yau in zasu je unguwa zasu dinga kiranka kana kaisu inda suke so,ga key din mota nan a hannunta idan zaku fita ka karba idan kun dawo ka bata key din a hannunta,har schl zaka na kaisu,Malam Garba yace an gama Alhaji,nace ga key din ka kaimin su Meenat schl da yamma kuma zamu fita na fada ina wani mazewa irin matar Alhaji,Aayan yana kallona duk abinda nakeyi.
Yana gamawa ya mike tare da kara ajiye min Bundle guda na yan dubu yace gashi ki biya kudin schl din ragowar ku kara a shopping karki dawo da kwandala gidan nan duk ki tabbatar kin karar dasu a shopping,nace da gaske mu kashe duka zaka kara mana na cefane?Yace yes.

Yana fita na dinga tsalle da ihu tare da su Meenat,nace ai na fada muku ni ba a ja dani duk jarabarka sai na ma wayo,gashi dai kwana biyu har na samu abinda nake so,Meenat tace to bari mu dawo muje shopping wlh za a buga damu har mota ya bayar ana kaimu unguwa fa,Meenat tace Sis yau sai munje tsohuwar Unguwarmu a motar munyi musu birga,nace ke banza ce ba yanzu ba sai mun siyi kaya masu tsada mun koma yan gayu sai muje a gaisa ayi zumunci
Muje na rakaku mota daga nan mu ganta,gaba daya muka fita har inda Aayan ke ajiye Cars nasa,Malam Garba muka hango a wata shegiyar Benz yar gaske sabuwa dal wai itace zamu dinga hawa,su Meenat suka gaisheshi ya amsa yana me fara'a don gidan kaf babu wanda ke Saurarar dan aiki bare a gaisar dashi komai girmanka.

Meenat suka kame a gidan Baya,sai ga yan matan nan sun fito zasu tafi schl suma ina ganinsu nace pls Baba Driver ka kular min da motata ,ido suka zaro yaushe na samu matsayi har Aayan ya bani mota.da Sauri naga Hanifa ta koma ciki tana zuwa ta zayyanewa kakarsu dasu Abbi.
Ina ciki ina aiki naji bugun kofa na leka ta yar kafa na hango su Aiko naki budewa bugun duniya naki aikina kawai nakeyi.
Aayan na gani ya dawo yace na bude ina budewa Hajja kakarsu ta wankeni da Mari,ga hannunta kamar jikin bishiya Sabo da fatar duk ta tsofe ta bushe.
Zata kara min na goce,nayi niyyar magana haka nayi shuru ganin Aayan na kusa.

Abbi da Maza da mata sun kai su goma kowa da kalar zagin da yake min,Aayan na gefe ya kalleni na kalleshi,matar Abbi tace ke har kin Isa matsiyaciya daga kawoki cin arziki,na kalleta idona a bushe nace yo ai bake kika auroni ba,kema ai ba gidanku bane aure ne ya kawoki,kuma wlh Bazan ragawa kowa ba tunda ba aurenku nakeyi ba,Hajja tace iyye au Iskancin naki ya girma haka ina magana kina magana kin san dawa kike magana,nima ai baku san wace ba,Aayan ta kalla tace kai saketa yanzu na bada Umarni,maza rubuta mata saki,nace ku kuke tsoron saki idan an sakeni sai me rayuwa zan fasa ko me,Kaka tsohuwa Hajja ta rike baki dan tunda take babu wanda ya taba mata ko musu Amma gashi ni tana fada ina fada,tace saketa nace,Aayan yace baku kuka Sa na aureta ba ni ne naga dama kuma da dalilina Bazan saketa ba ya juya yayi ficewarsa tare da cewa idan kin gama ki kira Malam Garba a waya na ajiye miki Number dinsa a Dining,nace to Ranka ya dade a dawo lfy Allah ya tsare min kai,yace Ameen,nace Million dayar daka bani sunyi kadan Yanlabai,yace kin san inda suke kije ki kara yanda zasuyi,na Gode Allah ya kara budi,yayi gaba na kalli Matar Abbi Hajiya Karima nace kiji dan Allah Baby bashi da dama wlh common shopping a baka yafi million ga kyautar gida ga mota yau da Safe,tsaki naji sunja Hajja tace a sannu zan shayar dake mamaki wlh sai na canja miki kamanni ba a takani da yarana a zauna lfy.

Na kalleta nace aiki ya ganki ga tsufa ga shiga rayuwar wani Allah ya taimaka,wlh dan ina ganin girmanki ne ko ba komai zaki ci darajar tsufa da kuma matsayinki na Mahaifiyar surikina kakar Mijina idan da mutunci ke kakata ce Amma baku san haka ba,ku tambayi wace Mufeeda a Unguwarmu kowa yasan yarinyar kirki ce kuma ta wanni fannin bani da mutunci wlh da ace haka kawai ne da kun san wace ni Amma kunci darajar Mijina,ba tabani a zauna lfy dan ma ba akan kudi bane,bana yarda a taba lafiyar hanyar cin Abincina akan wannan bana dagawa kowa kafa.

Matar Abbi ce ta fisgoni suka hadu da Sauran matan suka fara dukana,sai da suka fasa min gefen bakina kadan hakan ma dan na gudu ne da Allah yasan irin Illar da zasuyi min.

Daki na fada na kulle nayi Kukana boye a fili nace wlh kun jawowa kanku dan ni indai ba lallabani akayi ba to kara lalacewa nakeyi, musamman akan kasuwancina dan yanzu auren nan ta hanyarsa muke ci muna sha shine kasuwancina kuma kowa yasanni akan Business ba mutunci zan iya ja da kowa.










AsmaBaffa
[1/9, 4:55 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA





41-45






Official







By
AsmaBaffa




Documents from AIHAUSANOVELS

Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels

Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels





MMN BASMA,SALMAT BASHEER,SUBYUSMAN ga page na baku Sabo da kauna ina Godiya.

Gaisuwa cikin Trailer zuwa ga
HAFSAT KHAIRAN
OUM FAROUG
MUM SUHAIL
MAMAN HAIDAR
HAJIYA JAMILA
MAIMOUNA MATER ta NIGER.

Kuna Raina
MEENAL SIDI
YA SALAM
DJU LUV
NANA KHADIJAH
OUM SALM@
Ina jinjina muku da Sharhi na gode.






Bayan na gama gyara gidan kaf ko ina yana sheki da kamshi,tuwon danyar shinkafa nayi tare da miyar egusi harda naman Kaza Sabo da a kwai a fridge,a dining na shirya mana komai cikin Food flask masu shegen kyau,wanka nayi na shirya cikin material cotton riga da skert nayi kyau sai ka rantse me tsada ne,dan Mayafi kawai na Sa a saman kaina wanda yasha gyara,1:30pm Sabo da a motar gida ne ba bata lokaci sai ga su Meenat sun dawo suna kwala min kira,Ku karaso mana ina ciki kuma sai kirana kukeyi,Sis yanzu muka ga Yaya Aayan a Compound su Abbi sun sashi a tsakiya tare da tsohuwar nan kakarsu sai masifa suke masa,ko saurararsu baiyi ba kawai jinsu yakeyi,Baki na tabe nace saji dashi can kuje kuyi shirin Islamiyya ga abinci nan a Dining,Bari na kira Malam Garba ya karbi abinci yaci sai muje unguwa, a waya na kirashi ya shugo na bashi abinci a flask dama na ware masa nasa daban Aiko yaji dadi sai murna da godiya yakeyi don ba a basu abincin gidan yan aiki suke burkuta musu ko wanne kwamacala ko dadi babu,fita

Please Login or Register in order to submit comment