Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai rijiya idan guganmu ya fada da ita muke amfani mi Ciro gugan,mutane suna zuwa aro sosai nan ma nace kudin aron Kura Naira talatin wasu haka dole suke bayarwa suna dauko Guga,Ammah ta hanani Amma naki ji,su Meenat ma dole suyi abinda nace ko bana nan idan aka zo to fa sai an Bada kudin nan,komai nawa idan zaka taba na kudi ne.

Haka na kama kafa naje har gidan Adam counsilor neman Alfarma a sani cikin masu tallafi,yace Mufeedata ki. Makara wlh an gama daukan sunaye amma na miki alkawari akwai na wani watan kizo Office ki sameni a secretariat zan sa sunanki a wasu da za fara bayarwa na manoma,ban kawo da wata manufa ba kawai na dinga Murna ina godiya cewar zanje in Sha Allah.

Bayan kwana goma Zaune muke gaba daya tunda anyiwa Su Meenat hutun schl muna ta Hadin Zobo nan nace suje su ebo robobi a wanke suna Tafiya na watsa Maroon color tare da makawa Zobo ruwa na hadashi da su Flavour yasha uban Barkono a ciki,sabo da aji yaji sosai sai na zuba citta da kaninfari kadan na ebi Barkono na watsa a ciki na tafasa dashi Sabo da aji yajin ya fito sai ka rantse yajin cittane da kaninfari me uban yawa,gaskiya na iya taba sosai ni kaina ina jinjinawa kaina yanda nake tabka tsiya a sana'oi na ba a magana watarana nakanji haushin kaina nima ba da son raina nakeyi ba Amma Sabo da neman rufin asiri,su Ma'eesha suna kawo robobi Meenat tace sis wannan uban zobon fa dazu fa dan kadan ne bai kai rabin botiki ba amma yanzu ya cika botiki,Maeeshah ma tace nima haka na gani kamar na Aljanu,Harara na zabga musu sannan sukayi shuru.

abin takaicin da kyar na hada dubu Sittin da Bakwai kudin Ammah na asibiti,haka nace su shirya mu tafi,har kofar gida na kira Napep muka hadu tare da daukan Ammah muka sata cikin Napep muka kulle dan gidanmu da yar kofar da ta kusa ballewa ma haka na zarge ta muka shiga Napep Sai Asibitin Murtala na cikin Kano,Munje Dr Naseer ya duba lafiyarta ya dinga fada me yasa ba a kawota da wuri ba tuntuni yace a kawota ayi aikin to gashi ciwon nata ya kara karfi yanzu dole wasu magunguna zasu rubuta mana mu siya na dubu Hamsim da biyar sannan idan ta shanye bayan sati Uku mu dawo da ita za ayi mata aiki.

Bakin ciki da tsoro tare da firgici suka kamamu gaba daya,nayi Zuru Zuru kamar wacce ta shekara taana zawo haka na koma nace Doctor yanzu nawa ne kudin aikin? Yace ai kudinku da yawa,likitan da zaiyi mata aikin nan baya zama a kasar nan sam Sabo da aikinta zaizo yayi mata ya koma,don haka idan yayi muku sauki ku biya dubu dari takwas da Hamsim domin ciwon ya girma,da ace tun farko kun kawota da tuni baifi ku kashe dubu dari ba Amma yanzu danma da wannan Doctor dinne Amma wannan aikin kasar waje muke tura mutane masu irin cutar ayi musu aikin anfi dacewa,a nan kuwa sai dai mu dage da addua,kuje ku dawo lallai nan da 3wks tare da kudade in ba haka ba kuna kallo wlh zata kasa ko motsa yatsa dake gabarta nan gaba sankamewa zatayi ku daure ku dawo ayi mata aikin kunji.

Likita na bayani Hawaye na sintiri a fuskata tunanina ina zan nemo kudin nan ko kaina zan siyar wlh bazan yi wannan kudin ba,Innalillahi nake maimatawa Doctor kuma na kwantar min da hankali yana cewa cuta jarabta ce daga Allah,idan Allah ya jarabceka sai hakuri aci gaba da addua Amma tana cikin hadari,Meenat dake kusa dani itama Hawaye takeyi,da kyar na Lallashi kaina nice babba Amma kuma nice me raguwar zuciya bana iya rike Hawaye na saurin kuka gareni ammafa a bangaren abin tausayi,ko ya naga abin tausayi yanzu zan yi kuka,kanmu da Ammah nake tausayawa kawai,Meenat karki fadawa Ammah me Doctor yace kawai kiyi shuru da bakinki Sabo da bana so hankalinta ya tashi,muce kawai aiki za ayi mata nan da 3wks sai kudin zamu fada mata,amma karki fada mata Doctor yace zata iya rasa ranta ba lallai ta tashi ba kinji,ok Sis Bazan fada ba cewar Meenat dake shesheka,hawaye na share mata nace muje kawai muk ayiwa Dr sallama muka tafi,Ma'eeshah da Ammah suna jiranmu a can waje, magunguna muka siya sauran kudin na siyo mana wasu kayan abinci da Cefane,Su Meenat kuwa tuni na hadasu tare da Ammah nace suje gida zanzo daga baya,Ina cikin Napep kawai tunani nake ta ina zan samu kudin nan,lallai Zafin nema baya kawo Samu,gashi dai na gama Ha'incina a sana'ata na cuci mutane da dama ta hanyar siyar musu da gurbataccen abun ci kuma karshe kudin anfaninsu kadan ne a wajenmu abinda nayi don shi ba a dace ba,amma duk haka ban hakura ba kuma ban damu ba matukar zan samu kudin da Zan nemawa Ammah lfy.

Tunani nake bana ganin komai bana ji har Napep ya saukeni a gida na shiga da kaya Niki niki,Meenat ta karba ta shigar dasu ciki,tsabar bakin ciki da muke ciki yau bamu iya daura kaskon Awara a kofar gidanmu ba,duk muna zaune kowa da tunanin da yake banda Ma'eeshah da yake ita ba wani girma da hankali tayi ba sosai bacci ma takeyi,abincin da muka dafa ba wanda ya iya kai ko loma daya bakinsa,musamman ni gaba daya na rude na rikice,idan kuka ya taho min sai na shiga toilet naci uban kuka na wanke fuskata na fito haka na kwana inayi kafin Safiya tayi idona ya kumbura yayi jajir, ga addua muna tayi, mura ta kamani muryata har ta dashe Sabo da Hawaye na kawo Mura yawan kuka,da sassafe kamar me aikin Gomnati 8am nayi shiri da kumburarren idona tare da jansa na maka hijab kowa ya ganni yasan ba lfy,tunani nake ina zanje neman kudi Office din yan siyasa ko gidajen masu kudi?ko kuma kasuwa zanje wajen masu kantina,domin banyi tunanin kaiwa gidan Radio ba ko wani waje,kaf makwaftanmu haushina sukeji Sabo da kan Sana'a ta ba mutunci idan maganar kudi ce ba kawaici don haka ba da wanda muke shiri sai daí daiku duk sunfi jin haushina,don haka babu me bamu shawara ko gidan Radio ko wani waje to idan ba business ba babu abinda ke hada mu dasu Sabo da ba a kula mu ance dan munga muna da kyau sai mu dinga yanga mu ba yayan uban kowa ba,sannan tunaninsu ma ni yar Iska ce Sabo da yawan fita da nake kullum ina gantalin neman Kudi tunaninsu ai iskanci nakeyi kullum ina titi,haka suke zagina ba abinda ba ce min.

A fusace na fito daga gida ka Rantse mutanen garin ne suka min abin haushi domin kowa haushinsa nakeji kamar zan make mutane haka nake tafiya fuuuuuuu fuska ba annuri,duk motar dana gani sai na harareta na harari na ciki dake tuki irin ga mutane da kudi ba taimako,common arna ko church kaje a tallafa ma amma musulmai ko a masallaci basa iya bada Sadaka me tsoka sai biyar,goma,ashirin katon me kudi kaga ya mika Hamsim,mafi akasarin Hausawa haka suke bare har wani ya dauki nauyin karatun wasu ko ci da Sha bare na magani sai dai dai ake samun masu haka,amma arna sai kaga mutum daya ya kwashi yan unguwa da yawa ya fitar dasu kasar waje karatu etc.






AsmaBaffa
[1/1, 10:20 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA






6-10







Official






By
AsmaBaffa







AUTA kema wannan page Sadaukarwa ce gareki.







Tafiya nake ina tunani har na Isa bakin titi ina jiran na shiga Napep shuru shuru ba taxi ba Napep kowacce a cike suke,wata dalleliyar motace tayi parking a gabana tunanina Namiji ne irin samari yan iska masu ragewa mata hanya a nemesu nan take na kara tamke fuska na dauke kaina na kalli can gefen hanya,wani kamshi naji ya cika wajen sakamakon bude murfin motar dake Saitina da akayi sai lokacin na kalli me fitowar ba kowa bane face yan matan nan na gidan Saurayi Aayan wanda suka min dukan tsiya sune su biyu suka fito a zafafe kida na tashi a motarsu sunci uban kyau ko ina zasu je oho,ina cikin wannan tunani sai ji nayi an sharara min ruwa a jikina me sanyi,a firgice na kallesu da mamaki,nan suka sheke min da Dariya dayar ta fusgo min Hijab tare da shakeni,dayar ta duro min ashar tare da cewa ubanwa kika zaga har gidanmu?dama nace wlh duk ranar dana ganki sai kin San wa kika yiwa rashin kunya wato har iyayenmu ko?

Dayar data shakeni ta tsandara min mari tace Wai ke face to face harda zagin ya Aayan ke din banza kucaka yar matsiyata kin San su waye ubanmu har zaki bude rubabben bakinki ki zagi kakarmu who are u me kwakwalwar dusa banza gaja.

Wani bakin ciki da bacin rai ya taso min duk saurin kuka na haka na danne shi,dama cikin haushin masu kudi nake ga bacin ran halin da muke ciki,nan take na kasa hakuri nima nace kune dai gajoji yan iska tsinannu na shaki wacce ta shakeni nima na zuba mata Mari me lafiya,nan take ta shakeni tare da Dafe kuncinta, dayar ta taso a fusace kafin ta karaso na tsuguna tare da kwaso kafafunta ji kake Tim ta fadi gefen titi,na bita kuwa tare da jawo kafarta kaiiiii kowa yana kallo ina janta a kasa tana ihu,na hau kanta tare da Zama daram na rufeta da duka tako ina,wacce na mara kuwa da sauri tazo kaina itama ta hau dukana,muna ta faman yi,ga yara da mutane sun taru ana kokarin rabamu amma Sam munki Hakura yi kawai mukeyi,
Wata motace dalleliya ta kara parking a gaban ta yan mata wata budurwa itace wacce muka samu tare suna rawa ranar da muka je gidan Polio da gudu ta taho tana yiwa yan Uwanta magana Ku kyale matsiyata Ku zo mu tafi pls wannan ba Class dinku bace Ladies pls,babu wanda ya kulata da takalminta me shegen tsini,gani tayi babu me hakura kawai ta daga waya ta kira Babansu tare da fada masa Address din inda muke,Nan take sai ga arnayen Motocin Aayan sunyi parking sun kai su bakwai da securities,yana zuwa ya fito cikin Takun mashahurin Namiji yau sanye yake cikin farar shadda dinkin fitted dai dai jikinsa ya dau matukar kyau ga wani arnen glass Brown a fuskarsa ba karamin kyau yayi ba,ganinsa yana tahowa nayi matukar firgita kamar zanyi fitsari sabo da na tsorata bazan manta da dukan da yayi min ba,ban San sanda na hantsilar da dayar daga jikina ba na tashi daga kan dayar da nake zaune na gyara hijab dina na kwashe da uban gudu kamar zan tashi sama,ina danyin nesa dasu na tsaya ina maida Numfashi,shi kuwa baima tunani ba Sam bai gane ni ba amma ya tabbata ya sanni.

Ina kallonsa ya karasa wajensu ya kama yan matan nan ya dinka kwada musu mari ba ji ba gani yana ball dasu sai da ya canja musu kamanni sannan ya fada mota yace Securities su kamo ni,banyi tunanin wajena zasu zo ba ina ta kokarin tare Napep amma babu,kawai sai motoci na gani sun zagayeni,kafin kace me Sojoji sun zagayeni ba hanyar guduwa.
Saurayin ne ya fito cike da jin kai ya kalleni da kyawawan idonsa,kwarjininsa da haibarsa sun cika min zuciya nayi kasa da kaina har gabana ya matso tabbas nice ya gane nice naje har gida na zagesu da Iyayensu,nan take yace a sa masa ni a mota ko ta wanne Hali,Kuka na fashe dashi me karfi ina rokonsa wayyo uwata wlh ni ba yar uwarku bace baka da dalilin hukuntani,yana jina ko kallona baiyi ba nan take suka jefani a mota suka figi motocinsu dani a ciki,Su kuma yan matan da kyar suka shiga mota daya me jarabar son girma ta jasu sannan tayi waya aka zo tare da daukan motar tata da ta bari gefen titi,Hospital ta wuce dasu aka yi musu Dressing tare da magani sannan suka tafi gida.

Ina cikin bayan wata mota Sanyin Ac sai kadani yake na dunkule waje daya ina ta faman Rusa kuka cewar an saceni za a yanke min kai,ta window naga mun shigo wani katafaren Building na gasken gasken komai glass ne fadin tsaruwar wannan building bata baki ne ashe wai Office din wannan hadadden saurayin ne,harda su Lifter, ko ina Flowers kamar wani Hotel don a Hotel din ma sai shahararre,ina kallo suka sa Lock tare da kulleni ni kadai a motar tun 9am suka shige ciki ina ta sa ran zasu fito gashi motar taki budewa,na rasa yanda zanyi,11am shuru,12pm tuni nayi bacci a cikin motar,3pm dai dai na farka daga baccin daya saceni a cikin motar tun 12 na fara baccin,yunwa taci har ta cinye amma banga Alamar zasu fito ba Sam,tun ina kuka har na hakura gashi banyi ko Sallah ba ni da bana kauna na hada Sallah sabo da gaskiya Allah yasa min son Addini sosai,ganin basu da niyyar fitowa kawai na fara karatun Qurani a hankali sai da nayi ya kai izu biyu sannan na koma tasbihi da sauran Zikhri dana iya,ina ta yin abina bilhakki da gaskiya ina adduar Allah ya kawo silar samun kudin asibiti na Ammah kuma Allah yasa ta warke,yunwa ta addabeni da kishirwa,5pm naga hadadde ya fito cikin shigar 3qtr fari da riga Armless red kamar ka saceshi ka gudu sabo da haduwa ta ko ina,kallonsa nake tayi ina tasbihi ga yanda ya zubawa wannan Saurayi baiwar kyau,sura, ga iya daukan wanka,uwa uba ga nutsuwa Kwarjini da haiba,Securities suna take masa baya yana gaba da robar ruwa a hannunsa,da sauri suka bude masa mota ya shiga ga yan Jarida suna binsu da gudu suna jefa masa tambayoyi amma ko bude baki baiyi ba bare ya basu amsa haka aka bude masa mota ya shiga sannan Securities suka shiga nasu harda motar da nake ciki suka figa muka bar wajen,ina ta mamaki ko ya manta dani gashi nasan Ammah da yan uwana yanzu sun shiga wani a kan rashin dawowata,

Wata katafariyar Unguwa ta masu Hanu da shuni muka nufa ina mamaki nan kuma kamar a turai wacce GRA ce wannan haka?domin nasan Ba Unguwarsu bace wannan,Harga Allah wannan Saurayi wato Aayan ya manta dani a cikin mota,direct Gidansa wanda babu wanda yasan dashi nan ya nufa,gidan fadin haduwarsa da tsaruwarsa bata baki ne ya wuce duk inda ake tunani,gidane na fada wanda kafin a sami irinsa sai dai ko a turai ko Abuja watakil,sunayin parking a compound duk suka firfito aka bude masa ya kallesu tare da basu Umarnin su kwashe motocin su kaisu main Family House tunda yana da motoci iri iri a cikin wannan gidan kalarsu daban masu shegen kyau jibga jibga,daya daga ciki ne ya sanar dashi yarinyar fa? Sai lokacin ya tuna da ina ciki,tsaki yaja sannan yace a fito masa dani su kuma su tafi Gida.
Nan take aka yo waje dani suka figi motoci suka bar gidan daga ni sai wannan Matashi Aayan me cikar zati da kwarjini.

Shuru nayi tare da sunkiyar da kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna jikina yana bari kamar mazari,Kallo daya yayi min wani na mugun wulakanci tare da rainin hankali yana yatsina fuska kamar yaga kashi,nayi mugun raina kaina domin bani da maraba da Almajira mara galibu,juyawa yayi cike da takama hannunsa cikin aljihun wandonsa daya hannun kuma yana latsa waya yace let's go,bana jin turanci amma na gane go din kawai nabi bayan sa kamar Munafuka burina kawai ya kyaleni na tafi gida abina.

Code number ya danna nan take kofar ta bude ya shiga nima haka,Wow ai ciki Aljannar duniyace kawai komai na Alfarma abin ba a cewa komai domin shagala nayi wajen kallo ina mamakin kudin wannan matashin komai Allah ya bashi.
Steps ya hau na bene,har na taka zan bishi ya daga min hannu alamar na tsaya tare da zabga min uwar Harara yana tsaki,a tsorace na kame a wajen,tunda ya shiga ya mugun dadewa har ana shirin Magrib sannan ya fito sanye da farar jallabiya fara fitted a jikinsa yana sheka uban kamshi,ina tsaye kamar gunki yazo ya wuce ni kamar Allah bai halacci dan Adam ba haka ya wuce ya fita daga palon sai karar mota naji da alama ya fita Ashe Sallah ya tafi masallaci,nan take naga tsaiwa baza ta kaini ba kawai na fara duba dakuna gaba daya dake cikin palon kasa Allah ya taimakeni ina bude wata kofa na hango makeken daki dauke da lafiyayyan gado da mudubi tare da sip na Alfarma komai milk and Brown color ne a dakin,kofa na gani a cikin Bedroom din nan take na Murda Handle din toilet ce ta yan gayun gaske ban taba ganin irinsu ba dan Allah yasa a birni muke da bazan iya gwada yanda ake kunna tap din ba,ina shiga wajen sink na nufa abin mamaki ina mika hannuna sai ruwa ya fara zuba shaaa idan na janye hannuna sai ruwan ya dauke haka shower ma kai abin kamar Aljanu,ban San lokaci ya ja ba na shagala na manta da kowa ina ta tabe tabena har na gaji nayi fitsari da tsarki sannan na daura Alwala na fito Palo da sauri dan kar mugun ya dawo ya isheni na shigar masa wani waje,ina fitowa na duba gabas na shimfida dankwali na sai na fara jero salloli,Magrib na fara yi sai la'asar da Azahar ina zaune ina azkhar na Mike na gabatar da Sallar Isha da kyar kasancewar yunwa taci karfina gaba daya a kasa a zaune ina adduoina.

Motarsa naji da Alamar ya dawo lokacin ina yanda nayi Sallah ina adduo ina wanda ban san ma a fili nakeyi ba ina fadawa Allah ciwon Ammah da halin da muke ciki Allah ya yaye mana,kamshinsa naji alamar ya shigo da mamaki ya kalleni da alama Sallah nayi karfa ko Bedroom na shigar masa,wata mahaukaciyar tsawa ya buga min da tasa nan take na saki kuka,Keeeee a ina kika samu Ruwan Alwala? Jiki na rawa na nuna masa Bedroom din dana shiga da yatsa na, tsaki yaja tare da cewa Allah ya taimakeki wata leda ya wurgo min a jikina sannan ya haura Sama da nasa a hannu.

30 mnt ya fito da lemon gwangwani a hannunsa yana korawa nan ya fada saman kujera tare da nutsewa a ciki ya dauki remote yana kunna Tv ya kamo tashar wakokin turawa na yan Iska kusan ma kamar tsirara ake nuna su su Nicki Minaj etc.
Da kyar na Mike na karasa kusa da kafafunsa a hankali cikin ladabi da kwantar da murya nace Sir....Shuru ya min kamar bai San ina magana ba,Nace Sirr.....shuru,Sirrrrrr.....da wani mugun Bala'i ya juyo ba tare da yace komai ba,nan dai na daure da kyar sabo da kwarjininsa nace Dan girman Allah kayi Hakuri ka barni na tafi gida dan Allah,Ammah ta tana gida bata da lfy da kannena yanzu suna cikin damuwa dan Darajar Allah Sir,idan ma baza ka barni na tafi ba to ka kira min su a waya ka hadani dasu na kwantar musu da hankali kafin Lokacin da zaka barni na tafi.

Shuru naji yayi kamar ma ba dashi nake magana ba,na daure ina hawaye nace Sirrrr....sai lokacin ya juyo ya kalleni tare da dauke kai can yace me kike so kice? Wato duk maganar da nayi ma bai ji ba,wani bacin rai ya kamani cike da fushi na hayayyako masa nace ka barni na tafi idan baza ka barni ba ka kira min sis dina na fada mu......wani gigitaccen Mari naji a kumatu na,kafin na bude Ido ya kara min wani marin me masifar Radadi nan ba shiri na barke da kuka,mikewa naga yayi sai gashi ya fito da dalleliyar wuka a hannunsa,a wuyana yasa ta yace will u close tht ur dirty mouth or...kafin yayi Magana na hadiye kuka na sai shesheka duk da bana jin turanci amma na gane Close da mouth tunda Su Meenat suna koya min.

Dan kinga ban miki komai ba shine zaki raina min hankali am I ur mate or what?,baki da tarbiya na gama ganewa dama ina nemanki ke gaki marar kunya ke har kin isa ko kalleni ki zageni har gida,kin San ko ni waye who do u think u r? Murmushin takaici yayi tare da cewa dama bari nayi naga karshen rashin kunyarki,har kina min fada ni zaki kalla ki min maganar banza bayan kina hannuna ko yankaki nayi na yanka banza, shi dama Aayan haushin mata yake ji har jira yake mace ta masa abu yaga ya ci mata mutunci domin mata sun masa abinda bazai manta ba.

Ina gefe nayi mukus fuskata tayi jajir sai yatsunsa kwance a fuskata,wancen abincin ubanwa zai ci miki?da sauri na rarrafa na dauka na bude ledar jiki na mazari na bude Fried rice tasha hadi tare da kaza sai lemo,ruwa da Yogourt a ciki nan take na bude na kai lauma da bismilla kamar mayunwaciya haka nake afka abinci 5mnt kamar waccen ta zubar har na lashe abincin na shanye yogourt tare da lemon sannan na daga ruwan na shanye du,yana zaune mamaki ya rufeshi yana kallon ikon Allah ci kamar jaka,ya tabbata ko da yunwa ya kwana bazai iya cinye abincin ba,na gefensa ya kara jefo min a jikina nufinsa na cinye,ni ko dama ji nake kamar banci ba domin ba laifi akwai ci,haka na dauke na kara budewa yana bude baki da mamaki yaga na kara cinye nasan ruwan ne kawai ban Sha ba amma har yogourt din na shanye ta,da hannu ya min Alama na mike,zumbur na Mike tsaye,yace naje can bangon na dawo haka da sauri naje na dawo,yace yi tsalle na gani nayi tsalle ba shiri sabo da tsoronsa da nakeji,shi tunaninsa bazan iya tashi ba wannan uban abinci dana cinye amma sai yaga ras dani,a zuciyarsa yace bari ya kara gwadawa ya gani,nan ya Mike ya shiga kitchen ya fito dauke da fura tasha hadi a katuwar roba tare da Fruits a wani bowl,nan take yawuna ya tsinke naga dadi ban saba cin irinsa ba amma da shinkafa da wake ce ko plate daya bazan iya cinyewa ba,ko tuwo bazan sauraresu ba amma wannan kayan dadi haka ina zan barsu ko cikina zai fashe bare wannan dan abinci na take away kamar an roko gaba daya bazai plate daya ba,

Furar ya miko min ya tamke fuska yace shanyeta,da mamakinsa yaga na dauke da sauri har ina murmushi don ina son Fura a duniya,kawai na fara Sha cikin nishadi har lumshe ido nake ina addua ga Allah ina inama Ammah na kusa,ina Sha ina Santi a raina gata tayi sanyi a raina nace ah lallai wannan yana so aci a koshi Ashe ma bai cika mugu ba yo ni badan su Ammah ba ai da na rokeshi ya dauki rikona a gidansa,ina ta santina sai gashi na shanye harda lashe spoon din,wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke abinfa ya daure masa kai karfa ko Aljana ce,Nan ya mika min Bowl din Fruits dama su nake kallo cike da kwadayi nan ma na karba harda godiya na koma gefe na fara lunkuma su kankana a baki nace kai Allah me iko na yini banci ba Ashe tanadi Allah ya min harda kara'i yana kallo yaga na tashi Fruits tsaf,karkuce abubuwan masu yawa ne basu da wani yawa kun San dai Harkar yan

Please Login or Register in order to submit comment