Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wifedina,same too u Darling banda tukin ganganci kaji mijina,ya fita yana daga mata hannu ta kwalla da karfi am gonna Miss u Sweetheart kar ka bari a kalle min kai,shima da dan karfi yace Already started Missing u SweetMeenat ya fice dauke da murmushi ya manta ma da fushin da yakeyi Meenat ma murmushi take bazawa kawai.

Bai zarce ko ina ba sai gida wajen Su Abbi,yana zuwa a fusace Ameer bai kula kowa ba ya fara shigewa Bedroom din Abbi Mustapha Baban Ameer kenan ya fara watso kayan matar anci sa'a Abbi yana bayi yana wanka,kasan Bed din ya dage katifar sai ga Wata yar tukunya dauke da tarkacen tsafi a ciki tare da ruwan rubutu,Ameer bai jira ba ya fito ya jefota ta saman Bene tukunyar tsafi ta ragargaje,haka ya fita ya shige dakin Matar Abbi tana cikin gyara kaya taga Ameer ya fado da zureriyar Sandarsa tunaninta dukanta zaiyi ko Ya haukace sai ta fita da gudun tsiya,Abbi na ganin haka ya rufa mata baya dama sai abinda tace Kan tace ne kafin tace ya aikata,nan Ameer ya kulle dakin da key ya shiga bincike a dakin ya dinga samo guru,laya,ruwan rubutu,ya duba kasan bed din ba komai cikin pillow ya duba tare da Sa wuka ya tsarge pillow din ta ko ina ya fito da soson da suke ciki sai ga layu iri iri a Cikin pillow an hada dashi an dinke pillow tsab baza ka taba ganewa ba,yanzu mata abinda sukeyi kenan za a kai Amarya kafin a kaita sai an yanka pillow da razor a tura kulunboto sannan a mayar a dinke yanda ba Uban wanda zai gani sai kaga pillow normal ashe da tarkacen tsafi a ciki,miji yana ta kwanciya a kai,wasu har katifa ake yankawa asa sai a Sa zare da allura a dinke ba me ganewa Allah ka shirya mu.

Ameer yana fitowa ya fada dakin Abbin Yara Duk ya fita a hayyacinsa matar ta sashi sai ya goyata ya dinga zaga Bedroom da ita,gata wata me kiba katuwar gaske suna ganin Ameer da shegiyar wuka suka saki ihu ta fisgi Hannun mijinta suka gudu nan ma haka ya dinga kwakwulo kayan tsafi,sabo da Ameer duk irin wannan harkar ta malamai ya santa tunda suna zuwa da Hajja kafin Allah ya shiryeshi sannan Hajja tana sasu suna yin irin wannan abun wajen iyayensu mata,haka ma da Matar Daddy da kuma Matan Aayan duk irin wannan yasan su shi yasa yake da saurin gane irin wannan harkar,a leda ya kwaso komai ya fito dasu yabi ta baya duk ya warware layun sannan ya yayyaga komai da almakashi into pieces ya konesu tas,Sai ga su Abbi nan take sun dawo hayyacinsu,Hajja kawai suke nema da yaransu,Matar Abbi Mustapha kuwa taci duka hannun Abbi kamar jaka wai ta rabashi da Uwarsa,a wajen duk suka rubuta musu saki dai dai na musulunci Ameer da kansa yasa Securities sukayi waje dasu suna kuka tare da nadamar halayensu.

Da su Abbi tare da Sauran Yara suka dunguma zuwa asibiti wurin Hajja da take fadawa su Khaleel ku taimakawa iyayenku da addua su dawo cikin hankalinsu su dawo da iyayenku mata yan albarka masu biyayya,ni na jawo da nace sai sun sake aure,banyi adalci ba ko a baro sai an turani naje har gida na basu hakuri da kaina zanyi bikonsu ko da kafar katako ce,Mufeeda tare da kannenta suma zan nemi gafararsu,Daddy ne ya shigo a birkice nan Hajja ta damki hannunsa tana bashi hakuri tana kuka ka yafe min ni na jawo nice....Hajja na yafe tuntuni ni dama ban rikeki ba kuma aike Mahaifiya ta ce ba komai ya wuce ki bari kiji sauki ko na fitar dake kasar waje?Hajja tana goge Hawaye tana Allah ya maka albarka Ka yafe min dana,na maka abubuwa suna haka sai ga Aayan da Mufee duk ta kara wani fari tayi kiba da kyau Sabo da cikin dake jikinta,Hajja ta shiga bawa Aayan Hakuri da Mufee,Aayan yace shi ya hakura ta ma daina bata bakinta,Su Abbi su Ukun tare da Ameer suka shugo suma nanfa Hajja bata boye ba tace da kanta ta lalata zumuncin yaranta,To Allah yasa su Abbi sunyi Nadama nan suka shiga Yiwa Hajja fada da nasiha sannan sukace duk itace ta cucesu Amma tun da Allah ya ganar dasu sun yafe suma a yafe musu,a asibitin aka shiga yafewa juna anyi wa'azi tare da Nasiha wa juna an tunatar sosai dama wasu Iyayen da kansu suke bata zumuncin yaransu suna raba kan yaransu,a karshe Hajja tace da kanta zata je bikon iyayen su Ameer babu wanda ya kai su Abbi Murna za a dawo musu da matayensu yan kirki

Su Abbi sai gafarar Daddy suke ta faman roka sai lokacin ya fada musu ya auri Ammah kuma a satin nan zata tare a sabon gidansa daya tsantsara na fitar hankali,sun tayashi murna sosai har Abbi Mustapha na tsokanarsa an samu dangin kyau,Hajja kuwa Allura akayi mata anci sa'a ashe bata kara karyewa ba ta dan bugu dai a wajen Amma Dorin bai lalace ba,Aayan sai murna yakeyi shi da Mufee ashe Daddy ya auri Ammah basu sani ba,nan Mufeeda ta fita waje ta kira Meenat da Ma'eesha ta sanar musu Ammah ta auri Daddy ta labarta musu yanda Daddy ya basu labarin har yanda aka daura aure,Sunyi farin ciki Ammah ta samu me kula da ita,Meenat tace Sis kicewa Darling yataho gida haka na gaji da jiransa,Dariya Mufeeda tayi tace idan yazo me zai miki sarkin jaraba Bazan fada masa ba,dan Allah Mufeen Ammah ki fadawa Ameer dina na kira wayarsa a kashe,tana cikin haka sai ga Ameer ya fito, na mika masa waya nace ga Meenat tana magana,da Sauri ya karbi wayar yana murmushi yace Hello...tuba nake ranki ya dade kaina bisa wuya gani nan yanzu ki bani 15mnt Insha'allah ,Meenat sai Kukan shagwaba take masa ita yayi Sauri ya barta ita kadai.

Documents from AIHAUSANOVELS

Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels

Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels


Yarima da Ma'eesha saura 1wk zasu wuce Us sannan suje saudiya za a kwashi Amarci,dama anan ma Yarima baya daga mata kafa ko kadan,itama ta zama irinsa mayyarsa ce bata zuwa ko ina kullum tana gidanta kusa da Mijinta Office ma kusan kullum da ita suke zuwa,yauma 1pm yana Office ya kasa aikata komai kawai matarsa yake so yaji kusa dashi suna ta faman waya Amma bata gamsar dashi gaba daya,sai kawai yasa Driver ya dakko masa abarsa,ta gama shirya abincin da ake kai masa Office kenan tayi wanka tana shiri ya kirata a waya lallai tabi Driver suzo tare,zatayi Musu Yace dama ai ba sona kike ba yana narkewa kamar mace dole ta hakura ta shirya a mutunce tabi Driver tare da basket din Abincinta,tana zuwa yasa key a Office dinsa yace ya tashi daga aiki yau ko uban waye ya dawo gobe ko knocking kar ayi Masa suka shiga Soyewa da abar kaunarsa Ma'eesha itama ta gama gogewa da rashin kunya biye masa takeyi shi yasa yake kara sonta.

Kwanan Hajja Hudu aka sallameta tana dan digishinta haka tasa Driver ya kaita gidajen matayen su Abbi na farko tare da Daddy suka Bada hakuri da kyar suka amince aka sake daura aure tare da tarewa gaba daya,Daddy ya Mayar da Su Abbi kan aikinsu na da,tare da siya musu motoci na alfarma, Su Ameer da Sauran Yara sai murna iyayensu sun dawo Alhmdllh,lokacin kuma bikin Khaleel da Mujaheed,Sajeeda da Haneefa ya matso tunda ansa rana tuni,Saura Meenal,Sabeer da Aliyu nan gaba,gidan yanzu ya Zama gidan masu tarbiya da hankali kowa ya nutsu yasan mene rayuwa ba wulakanta dan Adam ba komai,mutanen unguwar ma yabonsu sukeyi yanzu sosai ana zaman lfy da mutunci da makwafta ba irin da ba,Su Haneefa gayu ya dawo yaci uban na da Amma yanzu na mutunci akeyin shigar mota sai wacce suka ga dama.
Yau Sati guda cif Sunday yaune kuma Ammah ta tattara nata kaf dama an shirya komai kamar wata budurwa,da wasu dattijai yan matasan iyaye kawayenta su Uku tun na tsohuwar unguwarsu tare da yan uwanta guda biyu sune suka kai Ammah dakin mijinta Daddy cikin lafiyayyun motoci guda kusan biyar,Ammah ba a ganeta sam Sabo da Su Mufeeda sun takura an kaita gidan kwalliya anyi mata,ga gyaran jiki ko ina kamshi fata na sheki gashi etc tasha tsumi iri iri abin ba a magana gata dama Ammah matashiyar Uwa me ji da kuruciya dai dai gwargwado tasha kyau an kaita duk an maida kowa gida lfy sai ita kadai a katafaren gidan sai yan aiki masu kaiwa da kawowa ko ina kamshi na tashi.
8pm Daddy ya shigo Bedroom din Ammah tana gefen Bed suna waya da Inna,tana ganinsa tace zan kiraki gobe Insha'allah ta kashe wayar, ta kalli Daddy dauke da lafiyayyen Murmushi yasha farar Shadda sai yau ta hango tsan tsan kuruciyarsa shima hakan dan sai yau ya tabbatar Ammah ta hadu ta ko ina,Gefenta ya zauna da ita suna shakar kamshin juna jikinsa na gugar nata,kunya ta lullube Ammah ta sunkuyar da kai kasa,Daddy irin Aayan ne sai zumudi yakeyi Da kyar ma ya Umarceta sukayi Sallar nafeela suka ci kayan makulashe Ammah da kyar ta karba Daddy yana bata a baki,Suna gamawa suka sake brush tare da wanka kowannensu yayi shirin Bacci suka haura Saman Bed,Ammah kunya take ji ta kasa sakin jiki,yana janta da Hira Amma da kyar take bashi amsa,Daddy cike da kulawa tare da tausasa murya yace Kin san nifa Bature ne kin sani asalin Bature ne mu ba haka muke rayuwarmu ba,ban saba da hakan ba,Mun zama daya ai ke matatace mene ne abin jin kunyata matsalar Hausawa kunya gaban me gida,am serious ni bana son kunyar nan ki tsaya mu nunawa juna so tare da kulawa shi muke bukata. murmushi tayi tare da juyowa suna facing juna tace na gane me kake nufi ta furta tana me rufe fuska da tafin hannunta,wanne suna kike so na fada miki? Ko wanne ma cewar Ammah,tunani ya shiga yace Honey?dariya tayi tace ai zanji kunyar yarana,yace to Maman Aayan? Taji dadi irin karar da Daddy yayi mata baice ta Mufeeda ko Meenat ba sai dansa ya nuna dansa nata ne nan take Ammah tace kai Kuma Daddyn Mufeeda ko? farin ciki ya lullube Daddy nan labari ya canja Salo suka koma soyewa suka lula duniyar ma'aurata abinsu.

5pm Mufeeda tana zaune ta baje kasa saman Center carpet na gaske Madara da sugar ta hada take faman lasa tana jin dadi Aayan yana gefenta sai cike takaddu yakeyi,Ba tare da ya kalleta ba yace Queen yau kinsha maganinki kuwa na rana wanda Doctor ya baki kafin mu koma Next wk?fuska na hade ina shagwaba tare da tirje tirje ina kuka a hankali nace ni na tsani magani ka sani bana sha sai kana takurawa sai na sha lafiyata kalau,Queen ki taimaka min Dan Allah kisha ya kike so nayi da raina idan baki da koshin lfy kuma kin san akwai Baby na a cikinki,ni dai Bazan sha ba na furta tare da fashewa da kuka,Da kansa ya tashi ya dakko maganin a leda da ruwa ya ballo kala wurin Uku yanda akace a sha ya mika min da ruwa dan Allah kisha My Queen kinji ya shiga lallashina Amma naki sha,yace zan siya miki mota fa sabuwa dal me tsadar gaske,sai lokacin na kalleshi da Hawayena nace da gaske?Yace kin san ai idan nace bana canjawa,Kasuwancinmu zamu dawo dashi idan nasha magani zaka siya min wani abu ko ka bani kudin?Aayan ya dinga dariya yace lallai me hali baya fasa Halinsa ashe har yau da ragowa,Ni ka amsa min kawai pls,yace ae to min dawo da kasuwancinmu kisha magani na baki kudi idan kin sha wannan mota ce guda gobe kudi jibi wani abu haka har ki sauka lfy,Murna ta kamani na karbe na shanye magani tas sannan ya ci gaba da aikinsa,yana farawa nace ni tausa nake so dole ya ajiye aikin ya shiga yi min tausa me dadi ina kwance saman Sofa.

Ma'eesha yau jirginsu ya lula zuwa Us a jirgi ma suna manne da juna ana kissing din juna,Ameer yau ya gaji a Office sosai Meenat kuma ta koma schl University dinta tana zuwa tana tashi daga schl ta wuce Office wurin Ameer tunda Driver ya turo mata wai su biyo su daukeshi su koma gida tare ya gaji,amma tunda yaga Meenat bata kansa yake ba ta Meenat yakeyi wai ta gaji sai lallaba abarsa yakeyi,Suna cikin mota ya kwantar da ita a jikinsa bacci ya sace ta har suka Isa gida tana bacci,Sai daukanta yayi kamar Jaririya suka shiga ciki kana ya kwantar da ita Saman Bed shi kuma ya shiga toilet da niyyar yin wanka,
Ya kusa gama wankan yaji Kukan Meenat da karfi karfi ya firgita da Sauri ya ya daura Towel ya fito,baki ya bude tare da rafka Salati.










AsmaBaffa
[3/4, 11:23 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA







141-150







Official








By
AsmaBaffa










a kasa ya hango Meenat Dafe da Mara jini na bin kafafunta,mamaki yakeyi wata daya da sati Uku da bikinsu Meenat tana da shigar ciki Ashe da Alama bai dade a jikinta ba ya zube,da Sauri ya kamata ya kaita toilet tare da yi mata wanka still jinin na zuba da sauri ya bata pad, Meenat tana kuka tace jini na zai kare zan mutu,duk Ameer ya rude da sauri yasa boxers tare da zura jallabiya a jikinsa ya koma toilet inda Meenat ke zaune Jini na fita a jikinta sai kara karfi ma yakeyi kaya ya sa mata ya dan shirya ta sama sama yanda jinin bazai batata da yawa ba sabo da dankwalinta na atamfa ya linka ya mata kunzugu dashi haka,mota ya sata ya zauna gefenta tana cikin jikinsa sai kuka takeyi tana Salati zata mutu,Ameer yana aikin lallashi Driver na tuki da gaggawa suka isa Katafaren Private Hospital akayi ciki da Meenat wacce ke jin mararta kamar zata balle,Emergency aka shiga da ita,nan likitoci suka rufa a kanta,Ameer yana gefe daga waje an hanashi shiga Kawai zaga wajen yakeyi hawaye ya zubo masa na tsoro karfa Meenat dinsa ko ta mutu,Wurin 3hrs Nurse ta fito tayiwa Ameer magana shiga tana nemanka,Ameer da sauri ya shiga har an canjawa Meenat daki ta warke kamar ba ita ba a zaune ma ya sameta gefen Bed,Ameer yaje da niyyar rungumeta amma taki yarda wai batayi wanka ba,likita ne ya shugo ya musu bayani ciki ne ya shiga baifi 1mnth ba ya zube kuma tunda har wankin ciki anyiwa Meenat,Magunguna ya rubuta musu har na Karin jini da shawarwari ya basu sannan ya rubuta musu Sallama,Ameer daukan Meenat yayi kamar yar Baby ya kaita mota Driver ya jasu suka tafi gida ba tare da kowa yasan me ya faru ba tunda ko a waya Ameer yaki sanarwa kowa.

Suna komawa gida shi ya gyara toilet din da kansa sannan ya hadawa Meenat ruwan Zafi ya gasa ta sosai sannan tayi wanka,tana fitowa ya shirya mata jikinta har Makeup shi yayi mata kana ya bata abinci taci tasha magunguna ta kwanta bacci ya kwashe ta,shi kuma ya kara wanke toilet tare da gyara Bedroom din komai yana kamshi shima yayi wanka ya shirya kayan Meenat daya zuba a washing machine su ya kwaso ya shanya su tas sannan ya wanke nasa Suma a washing Machine ya shanya yana danna system gefen Meenat dake bacci kayan suka bushe ya goge su ya adana su dama Ameer akwai tsafta bai son kazanta.
Ammah ya kira a waya ya sanar mata Meenat tayi bari amma ta warke ba matsala,ya sanarwa Ummansa,ya kira Mufeeda lokacin ina jikin Aayan dina yana shafa dan cikina da yanzu ya turo ana iya jin tudunsa,Ameer yace Anty Mufee Meenat ce tayi Bari yau dazu muka dawo daga asibiti amma ta warke lfy take, cike da tsoro nace yaushe zatayi wani cikin da har zai zube 2mnths fa da bikin,Ameer yace ai Doctor yace watansa daya ya fita bafa wani abu da aka gani kawai Blood ne,Mufee tace to tunda da sauki Alhmdllh zamuzo da dare,Aayan ne yace me ya Samu Meenat din?bari tayi wai na cikin 1mth,Murmushi Aayan yayi yace shege Ameer ai dole ma ya barar da cikin da kansa baya saurarawa yarinyar nan ga ciki dan karami an dameshi da jaraba, na masa hararar wasa tare da cewa kai ai kafi Ameer zaka ce Ameer kai baka ganin me kakeyi,Aayan yace Saura dan duniya Yarima,wasa nakeyi da Kirjinsa ina zaga yatsana a kai,yana shafa min dan cikina.

Maeesha ma an sanar mata da barin Meenat tayi mamaki,da dare duk munje har Ammah Daddy da kansa ya kaita suka duba Meenat,Ammah ta sanarwa Ameer yanda zai kula da Meenat har ta warware sosai,Ni kuwa kawai dariya ma Meenat take bani har yanga takeyi ita ta samu ciki har da bari ga shagwaba da take uban zubawa musamman idan taga Ameer a wajen shike lallaba ta,Muna zaune saiga su Hajja dasu Hanifa kusan gaba daya gidan sunzo Duba Meenat,Daga baya su Abbi suka zo da matayensu harda Umman Ameer sai da ta kawowa Meenat Soyayyun Zabbi cikin wani Bowl.

Bayan mun watse Ameer ya matsa jikin Meenat dinsa yana murmushi tare da zuba mata kallon so kana yace Meenat dina ni kadai sai lokacin ta kalleshi itama dauke da shauki a fuskarta ga wani son Ameer dake Karuwa mata a ranta ko dan yana da kyau ne oho ta kasa ganewa, bakinsa ya shigar cikin nata ya shiga tsotsa,Meenat ta lumshe ido itama tana mayar masa da martani sun dauki tsawon lokaci a haka Meenat ta janye jikinta taga Ameer din nata duk ya hargitse kuma baza ta iya bashi abinda yake so ba bata da lfy,Idonsa jajir ya kalleta da kyar ta iya magana murya a dishe yace pls Baby ba dai hanani zakiyi ba? Hannayensa ta riko da hannayenta a nutse cike da Ladabi tace Honey am so sorry yau kaima kasan baza ka samu ba ko ba komai Yau nayi Bari fa ai yakamata ko ba komai ka bani hutu ko na 1mnth ne tunda shima ai kamar Haihuwa ne yama fi haihuwa wahala ance,Marairaicewa yayi kamar zaiyi kuka yace Dan Allah kin ga fa ba jini kike ba har sallah kinyi dazu,kamar fa haihuwa ce Prince,Ni dai ban yarda ba yana shagwaba kamar jariri,Meenat tace yanzu ni danya ce fa?hakan nafi so ai danyar sharaf,dariya tayi kawai tace kama daina Sa Rai ka bari zan baka labs dina thts all,Ameer yace ni dai ba haka naso ba Amma ya zanyi dake Amma ki min alkawari yaushe zaki bani gobe? 1mnth nace fa,Ameer da kalar tausayi yace dama ance Mata Bedding dinma sai sunga dama zasu baka,kasa kasa Meenat ke dariyar mitar Ameer,mikewa tayi ta barshi ta nufi Sama,Kamar Ummansa haka ya bita a baya kamar jela yana roko Harda komawa bara irin ta almajirai Yara yana Iya... ko dan kanzo...Almajiri bara iya..,Iya ni ban samu ba iya...Meenat tana dariya ta shige Bedroom Amma Ameer bai daina ba Sai ma cewa yayi Iya ni ban samu ba...ko ni Mijinki ki san mini Iya....Meenat tana dariya tace Allah ka daina ce min Iya kamar wata tsohuwa,to kice zaki bani yau ko gobe sai na daina shuru ta masa yace zanci gaba Wahidin Iya....da Sauri Meenat tace gobe ka kawo Kwanonka dan anace,Murmushin dake kara masa kyau ya saki ba tare da ya shirya ba,Dan sajen nan tare da gemu firit suka kara kawata fuskarsa, Dimple dinsa ya loba,Meenat ta saki baki tana kallon haduwa kamar tayi yawa da Aayan kamar Babansu daya,jikinta ne ya mutu Sabo da ta dade tana kallon Ameer musamman da taga ya tube daga shi sai Boxers tana son Surar Ameer matuka,a hankali ta mike ta Isa gabansa sosai suna dan gogar juna kadan a hankali ta zagayo da hannayenta ta cikinsa ta rungumeshi a jikinta sosai,suna kallon juna kowannensu da salon iya kallonsa da suke Aikawa juna,a nutse tace ina Sonka da yawa Mujina,Kara matseta yayi a jikinsa yana rada mata wasu zafafan dalasaman so a kunnenta karshe yace muje muyi wanka muyi bacci ko Sweet Princess? Kai kawai ta iya daga masa ya gama Tafiya da imaninta.

Ma'eesha da Yarima cikin Sweeming Pool na alfarma suna wanka a katafaren gidan su Yarima dake Us,idan kunga Ma'eesha baza ku gane ta ba,kamar baturiya daga ita sai Swimming Dress Kalar Bra da pant,Yarima dan short ne a jikinsa a Cikin Pool din suke shagalinsu kawai,Yana ciki ta shiga saman Bayansa ta makale suna wankansu tare sai dariya sukeyi cike da so,gabansa ya dawo da ita Sabo da Ma'eesha bata iya ruwa ba koya mata yakeyi a tsorace take duk tabi ta makalkaleshi, peace kibi a hankali duk kin wani Tsorata,ni kasan ban iya bafa ta kara manne masa,Kanta ya dago cike da nutsuwa ya tura harshensa cikin bakinta ya shiga tsotsa,Maeesha ta kara matseshi a jikinta tare da maida masa da martani,kasa ta zame a hankali ta nutse a Cikin ruwa ko second bata yi ba ta dago kamar ranta zai fita wai ita ta koyi Swimming,tace Baby kalla na fara iyawa kamar kifi ta kwanta saman ruwa sai ko tayi kasa kamar an jefa dutse ta dago da Sauri tana facal facal da ruwa ita bata yarda ba ta iya ruwa,Yarima dariya yake ya riko ta tare da kunna uban nutso da ita suna kasan ya riketa ya shiga murza Boobs dinta,dago da ita saman ruwa yayi Ma'eesha ta fara tari zatayi kuka za a kasheta a ruwa wai,Sun dade suna murza juna a Cikin ruwan nan sannan suka fita tare da kwanciya saman kujerun hutu suna kora Juice da kayan ciye ciye.

Bayan 3wks Dan cikina ya girma ba laifi har ana iya hangoshi kadan muna mota tare da Aayan Driver na janmu yau gidan Ammah zamuje mu gaishesu,sallama mukayi a palon Ammah na zaune gefen Daddy tana yanke masa farcensa suna hirarsu ta masoya,Har kasa muka gaida su suka amsa da fara'a na koma jikin Ammah na makale Aayan yana hararata,shima ya koma kusa da Daddy suna maganganunsu na aiki,Daddy ne yace Aayan yaushe zaku tafi ne? Sai ta Haihu Bazan yarda ta shiga jirgi da dan cikin nan ba ya zube,Kunya ce ta lullubeni kamar na nutse,shi kuwa ko a jikinsa,Daddy ne ya tabe baki tare da cewa shashasha to ai inda zakuje suke da Doctors manya ka kaita kawai taga dangin kakanka sai ku zauna a can idan Allah ya sauketa lfy sai ku dawo,Ni Daddy ya barmu anan muje kawai mu dawo,Ammah tace to yanda kuka ga dama mu cikin satin gaba zamu tafi Saudiya da Us Insha'allah,farin ciki ya mamayeni Ammah fa an waye an san gari, addua mukayi musu mun dade har dare muna gidan tare muka shiga kitchen da Ammah,Sai bayan Aayan da Daddy sun dawo daga Sallar Isha mun ci abinci muka bar gidan abinmu,Ammah ta bani wasu tarkacen na mata da turaruka na kwanciya.
Kullum muna waya dasu Ma'eesha yayin da Bikin su Hanifa ke matsowa ana ta shirye shirye sosai.
Ammah da Daddy su zasuyo order din kayan lefen mazan da Furniture na mata kaf shi yasa ma zasu bar kasar,Sameera yar Daba anyi bikinta itama da gwaninta suna can suna shan Amarci da katuwar muryarta kamar ta Maza.

Hajja zaune take tayi tagumi tana Jan carbi sai Istingifari takeyi bata gajiya da Nadamar Halinta ga ciwon kafa ya hanata sakat duk kayan dadi an hanata ci a Hospital ba cin jan nama,kaji ma sai dafaffiya ba kullum ba,Yanda take mutunci da Ammah ba a magana kamar zata goyata haka kaf jikokinta ta kara rikesu musamman Aayan sai yanzu take nuna masa so tasan Muhimmancinsa,Matayen su Abbi girmamata dama can

Please Login or Register in order to submit comment