Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basa gajiya bare yanzu,itama ta rikesu da mutunci,Sai yanzu take so ta gyara zumuncin tana kokarin hada kan su Abbi da Daddy Amma sai dai ayi Amma basu shaku ba,ta rigada ta raba,sai dai komai suyi sama sama duk da cewar ba wata matsala Amma abinda take nema bazai samu ba a yanzu.
Sabeer,Aliyu da Meenal ma sun gama University dinsu yanzu saura Yara yan Secondary da Primary kawai.

Ameer ne ya shigo a gajiye yau ya dade a Office yasha wahala,lokacin Meenat tasan lokacinsa yayi na dawowa wanka ta dauka Cikin kana nan kaya Wando Short Jean blue ko Mazaunai da kadan ya rufe mata su da yar riga karama ko cibi bata rufe ba,Ameer tunda yayi tozali da ita hankalinsa ya tashi,kamshi kawai ke tashi ta ko ina a gidan sabo da yasha gyara ga matar gidan ta cakare,cikin salon tafiyarta ta jan hankali ta karasa wajensa a hankali kafin ma tace ko a ya fisgota jikinsa ya kankame abarsa yana sakin ajiyar zuciya,nan take ya birkice mata kissing dinsa ta fara cikin kwarewa Meenat ba sanya fa,Daukanta yayi zuwa Bedroom da kyar Meenat ta kwaci kanta wajen lallabashi ya bari sai yayi wanka yaci abinci sai ma yayi ko me yake so,yaki yarda Meenat tace haba mana dan Allah so kake yunwa ta kama min kai?Ka rufa min asiri kaci first abun nan ba guduwa zaiyi ba yana jiranka ai naka ne,ta dade tana lallashinsa sannan yace sai dai ita ta masa wankan idan yaci abincin,Abincin kuwa ya fara ci, da kanta ta ciyar dashi ya koshi sannan ta kaishi toilet tare da taimaka masa yayi wanka da Brush,mai ta shiga murza masa kafin a gama Ameer ya kasa jurewa ya shiga wani Salon na daban.

Hankali kwance muke shan Amarcinmu,Kwanaki suna shudewa Ma'eesha da Yarima sun dawo daga turai da dan karamin cikinta na wata 3, ciki na ya shiga 7mths muka sha bikin su Khaleel da kyawawan Amarensu Aayan ne ya bawa Khaleel da Mujaheed gidaje dankarere ,Haneefa da Sajeeda suma da angwayensu ya musu kayan daki na fita kunya,saura bikin Sabeer da Aliyu Sabeer Meenal zai aura,auren zumunci za ayi musu suna son junansu,Aliyu kuma yar kanwar mamansu zai aura an Sa bikinsu cikina yana 9mnths dai dai ba wani girman ciki gareni ba,kullum addua mukeyi tare da Aayan Allah ya saukeni lfy, ba sosai yake fita ya barni ba Sabo da cikin ya girma ko Haihuwa zata taso min,Ammah ta turo min Dattijuwa guda bayan yan aikin da suke gidan zata dinga kula dani Sabo da Haihuwa, Baba nake cewa da ita Sabo da bata girmanta,da kyar na lallaba Aayan kan yaje Office tunda Haihuwar taki zuwa,cikin rashin Sa'a ya samu Tafiya ta kamashi zuwa Turkysh wani Meeting kan harkar Business dinsu,a gurguje ya shirya na hada masa kaya yace 1wk zaiyi ya dawo Sabo da cikin da nake dauke dashi.
Na damu matuka ban so tafiyar tasa ba Amma sai ban nuna a fili ba na boye nasan idan yasan ban so zai fasa Tafiya kawai,Nace Zan bika airport yace a'a yamma tayi sosai ga Babyna zai sha wahala ki hakura kinji,Hawaye ne ya shiga sintiri a fuskata gani nakeyi kafin ya dawo ko na mutu ma Maybe,Fuskata ya leka Oh...Common Sweetheart mene abin kuka zaki Sa na fasa tafiyar nan ko me zai faru ya faru,Da Sauri na shanye Kukana tare da share hawayena ina murmushin Dole,Nasha Lallashi kafin ya yarda zaije da kyar muka rabu da juna ya tafi cikin zugar motocinsa,suna zuwa jirgi ya kusa tashi kawai yaje da Sauri ya wuce ciki,ba a dade ba jirginsu ya daga.

Ina nan ina kewar Mijina,ranar kuma na fara ciwon Mara sama sama,yana sauka ya kirani a waya yaje lfy,cikin dare ma mun dade muna waya dashi,tunda Aayan ya tafi kullum sai munyi waya har ya cika 4days a can duk da haka ina dan jin Ciwon marar sama sama,yau tun asuba bayan nayi Sallah kafata ta rike na kasa tashi,Baba na shiga kwalawa kira iya karfina ta fado dakin da gudu tana lfy Hajiya? dake ta manyanta sai ta gano Haihuwa ce nan ta fita ta sanarwa Driver,Ita da Abu me aiki suka kamani zuwa mota Driver ya kaimu Private Hospital din da muke zuwa da Aayan,Sunce na kira Aayan nace a kyaleshi kar hankalinsa ya tashi,ciwo sai gaba yake yi Baba tana a fadawa yan uwanki da mijinki sai nace a'a bana son hankalin Mijina ya tashi,ciwo yana ci gaba duk na fita a hayyacina ban ma san me nakeyi ba nace a kirashi din Hankalinsa yayi ta tashi ina ruwana,ban dade ba Allah ya taimakeni na Haifo dana katon gaske Namiji kyakyawa, bayan an gyarani har wanka Baba me aiki tayi min na shirya,shima Jariri an shiryashi tsab cikin kayan sanyi farare masu tsada da kyau, Ameer na kira nace kar ya fadawa Aayan komai,Ameer na fadawa Yazo asibiti na haihu,15mnt sai gasu Shi da Meenat,addua da komai shi yayiwa jaririn,nima nayi masa Meenat ce ta koma gida ta shiryo min girki iri iri ta kawo lokacin anyi min Allurai ina bacci,Sai yamma lis na tashi naji karfi sosai a jikina ga yunwa na ci na,Abinci naci na koshi kamar ciki na zai fashe,Doctor tazo ta bamu takardar Sallama muka tafi gida gaba daya tare dasu Meenat,gidana muka je na kwaso kayana akwati guda dana jaririn da muka tara har gadonsa muka tafi gidan Ammah baki daya, sai ganinmu tayi da jariri,Murna takeyi kamar me,Daddy yana dakinsa ta kirashi ya dauki Jariri shima sai murna ga yaro kyakyawa kamarsa daya da Aayan,Nan Ammah ta dinga min fada ban fadawa mutane ba,har Aayan ta kirashi da kanta tana sanar masa yace Ammah shi yasa nayi ta kiranta tun jiya bata shiga Ashe bata da lfy bata fada min ba,Murna Aayan yace shi tahowa gida zaiyi ya fasa kaiwa sati guda,da kyar Ammah ta bashi baki ya hakura,su Hajja,Abbi da matayensu duk sai gasu,Maeesha me dan karamin ciki ita da Yarima sun zo suma,Su Hanifa Amare tare dasu Khaleel duk sun cika gidan Ammah ana ta hira ana Jin dadi.
Bamu muka samu Saukin mutane ba sai dare suka tafi sannan Ammah ta hada min ruwa na sakeyin wanka da kanta ta gasa min jikina shima Jariri anyi masa wankan an shiryashi cikin kayan baccinsa yana dan bed dinsa yana bacci,lotion na shafa me kamshi na shirya nima cikin kayan baccina lokacin masu aiki sun kara Gyara ko ina,zan kwanta Ammah tazo da abinci lafiyayyu tasa dole sai da naci da yawa nayi Brush sannan na kwanta,har bacci ya fara daukana Ammah ta shigo tana fada wai Mufeeda baki da hankali ne ko me kin kashe wayarki mijinki yana ta kira bata shiga kuma ke baki kirashi ba ko laifi yayi miki ko wani abu ne ya faru?bafa na son irin wannan ban son neman rigima,yanzu baki tambayeshi ba kin kwaso jiki kin dawo waje na,idan baya so fa? Da bamu dawo daga kasar waje ba wajen wa zaki?ai dole ki zauna a gidanki,bana son ki zubar min da mutunci a gaban suruki ki kiyayeni,kiyi Hakuri Ammah mantawa nayi yanzu zan kirashi,tsaki taja ta fice daga dakin,Da sauri na jawo wayata na kunna kana na shiga kiran Aayan na kira yakai sau biyar sannan ya daga Cike da bacin rai yace ina jinki ya akayi?

Naji haushin maganar amma ai nice da laifi sai nace barka da dare Yanlabai Allah ya taimaki ranka ya Dade Baban Baby,tuba nake nayi laifi Mijina uban dana a yafe min,duk wani fushi da Aayan keyi nan adtake ya yaye baki daya sai ma farin ciki da ya shiga yi na gama kashe masa jiki,yace ba wani kinyi laifi zaki min dadin Baki dama ai haka kike min kullum sai ki dinga cutata dan kin San ina da hakuri,Dariyar jin dadi nayi nace Hakurin da ka saba yi dani shi zakayi Dad din Baby, Hmm to ya jikin?dana ya fito lfy ko?cike da shagwaba nace da sauki bayan ya bani wahala kamar zan mutu ai ni fushi nakeyi dashi,Aayan yace dan Allah? Nace sosai ma dan kawai baka ji bane aka ce sai nayi nishi na daddage nayi daya yaron nan dake bashi da kunya yaki tahowa sai ya makale kafada yace bazai fito ba wai,Aayan ya sheke da dariya yace a ina kika ji sanda ya makale kafadar? Ina dariya nace a cikin cikina naji wani bangare yayi min bake bake wani kababa a nan na gano me yayi ai ko nace zanyi maganinsa na kara yi da karfin tsiya yaji na shakeshi da yawa yace zan dan fito shine ya taho kadan,Ina yin na hudu yaji wuya ba dadi sai ya fito yana tsala uban ihu,Dariya Aayan yayi tare da cewa to Alhmdllh tunda kin sauka lfy ai ba matsala,Duk abinda kuke so Na fadawa Ammah baki da prob nima jibi zan dawo Insha'allah,Ina Baby Boy dina da wa yake kama?nace gashi baccinsa yakeyi ma ko Na mintsineshi kaji Kukansa,da sauri yace a'a ko da wasa Karki fara,Dariya nayi nace kamarku daya baka ganshi ba wlh na iya haihuwa zukekene yan mata zasu dinga rubibinsa idan ya girma,Allah yasa ya samo min suruka ta gari kyakyawa kaga ya gaji Ubansa,dariya Aayan yakeyi sosai yanzu daga haihuwa har kin fara zancen Suruka,nace ae idan Meenat ta haihu nasan kyakyawa zata haifo ko Ma'eesha sai a bashi matarsa,Aayan yace baki isa ba babu me yiwa dana auren dole, sai ya Zaba ya darje, haka muka dinga musu,kaji yana motsi,Ko Nono yake son sha? Ya tambaya, hannu nasa na daukeshi ya fara kuka Aayan yana ji ta waya sai murna yakeyi baki yaki rufuwa nace bari na kara masa waya a kunne kayi masa magana,Jariri na kuka ni kuwa na manna masa waya a kunne Aayan kuma ta waya yana Hello My Son,Dad dinka ne,Abbanka ne Be quite yaro bai San me akeyi ba,na shiga bashi Nono yayi shuru kuwa muna waya da Aayan.

Yace muyi video call haka na kunna light na kirashi ta Skype muka fara Video call yana ganinmu ni da jariri,muna ta hira cikin Jin dadi mun dade sannan muka rabu da juna muka fara baccinmu cikin nishadi,washe gari ma haka gidan ya cika da yan Uwa da abokan arziki,kamar ba ni na haihu ba haka nake shiga cikinsu muna hira ga waya Aayan ya Dameni da ita muntuna kadan zai kira yaji ya muke muna haka har na kwashe Kwana hudu da Haihuwa tunanina ma sai bayan suna Aayan zai dawo tunda naga an kusa, 8pm Ammah tayiwa Jariri wanka tare da shiryashi tsab cikin kayansa masu kauri da kyau nima na bashi Nono ya koshi yana yin Bacci na kwantar dashi saman Bed dinsa nima nayi wanka nayi shirin bacci kamshi ne kawai muke zubawa ni da jaririn,Sallamar Aayan naji ya turo kofar bayansa kuma mata masu aiki ne suka shigo da Akwatuna har uku suka fita,wani sanyin dadi ya kamani naga Rabin raina ya dawo yanzu zan na ganin abina a kusa,Cike da murna ina zaune tsakiyar Saman bed nace Oyoyo ina murmushi ga wani Mashahurin kyau dana kara sabo da samun kulawa,Kallona yakeyi tun daga sama har kasa kamar ba nice na Haihu ba sai ma kyau da na kara,Saman Bed din ya hauro ya bani zaffafar Runguma da Kiss sannan ya Koma gadon Jariri dake bacci ya daukeshi yana zuba masa adduoi,Sai da ya gaji sannan Ya kwantar dashi daga bisani ya shiga wanka,Ammah ce ta kirani a waya wai naje kitchen na dauko masa Abinci,Mamaki nayi wai Ammah Ashe tasan Aayan zai dawo shine ba wanda ya fada min har ta masa Abinci da kanta,Kitchen na shiga abinci na Alfarma na gargajiya dana zamani Ammah ta gama shiryawa na dakko masa komai da kayan sha masu sanyi, bayan yayi shirin bacci ya zauna dirshan yaci yasha,yace shine baza ki bani a baki ba?nace na sani ko zakayi kyankyami na kasan wasu kyankyamin matarsu sukeyi idan ta haihu,Fuska ya bata ke ni zaki bata min rai ke zanyi kyankyami?kin Zama jinina fa bana son irin maganganu nan ko ni Bahaushe ne? Yi hakuri na daina,Brush yayi yasha Ruwa sannan ya kashe Light ya kwanta gefe na,Nace Ammah fa zatayi fada,wa yace ki dawo nan? Kin fada min zaki dawo ko kin nemi Izinina? Kince nan da can dayane to mene ko dan kin haihu sai akace miki kar na kwanta Bed daya da matarsa? a'a amma ai ni dai Allah tsoro nake ji,shuru yayi min da kaina naga kamar baiji dadin maganar ba sai na juya na rungumeshi kamar jira yake ya makalkaleni a jikinsa muka Sha baccinmu.

Kwanci tashi yau ranar suna Ammah ba taron Suna Aayan dan Ahlul sunna ne ba a taron Suna yace a masallaci yaron yaci Sunan Abbanmu Abubakar Saddiq Aayan yayi min kara naji dadi,haka Ammah dasu Meenat har godiya muka yi masa,Fhadeel muke ce masa.

Bayan 1mnth Aayan ya kaini Hospital aka bamu shawara na family planning shi baya son Haihuwa kamar tattabara duk mace ta ragargaje ta fita daga hayyacinta sabo da kwanika a samu ciki kafin a yaye daya ya Kamu da cuta ga na ciki ba a da tabbas zaizo da rai,Da kyar ya barni muka zaga dangi yan Uwa da abokan arziki munje har Maiduguri da Kauyen su Ammah,gidajen frnds duk munyi Zumunci tare dasu Meenat.

Gidanmu gaba daya ya canja komai na gidan da kyar ake ganewa ya kara tsarashi,Direct mukayi Sallama da kowa muka dage zuwa Us daga can zamuje aikin Hajji mu kuma zaga wasu kasashen tare da jaririnmu Fadeel.
Ma'eesha ciki yana ta girma ya shiga wata Bakwai,Yarima da Ummansa suna ji da ita kusan ma a gidan su Yarima ta tare gaba daya tare dashi suna soyewa watarana Umman ta koresu idan suka dameta,Abban Yarima kuwa Bai cika Zama a kasar ba sai lokaci lokaci yake zuwa ko matarsa ta bishi can, yanda Yarima ke Lallaba Ma'eesha har yayi yawa ta gama sangarcewa dake ya nemo mata Wata Private University tana karatu kusan tare suke karatun ma har ta gama level 1 idan sun dawo Hutu zata shiga level 2,Yayin da Meenat ta gama level 2 zata shiga 3,ni kuwa ina Zero level sai mun dawo Aayan zai kaini wacce yaga dama komai a karatu jaraba nice a karshen baya ina takaicin wannan abu amma haka Allah ya tsara ya zanyi.

Meenat ce kwance saman Bed tayi shirin bacci Ameer yana kasa jikin Bed yasha shirin bacci sai rubuce rubuce yakeyi na Office kafin gobe sabo da Aayan ya bar masa aiki,juyi Meenat tayi ta kara juyi ta matsu yazo su kwanta,y ana jinta sauri yake ya gama yasan Halin Meenat yanzu zatayi zuciya da kyar zai lallasheta ta hakura,bai karasa ba ya hakura ya Mike tare da kwanciya a gefenta gani yayi har tayi baccin karya wai dan kar yace ta damu dashi,Shuru kowannensu yayi kawai shima yayi baccin karya kamar da gaske,Meenat taji shuru ko hannunta bai rike ba,fuskarsa ta leka ta shiga mamaki ganin yana bacci a fili tace bacci yayi a wannan situation din da ni Meenat kamata ina kusa dashi bai ji komai na feeling ba ya fara bacci,Kwanciya tayi a fili ta kuma cewa ko Hannu bai iya rike min ba ina kusa dashi wannan me ya faru ko ya daina sona ne?wayyo karfa ko wata ya hango Ameer yana jin Meenat tana surutunta dariya ta cika masa ciki,shuru tayi ta rufe ido ta bude taja dan tsaki sannan ta kara rufe ido itama,cikin nutsuwa da muryarsa me dadi taji yace ya akayi My love? Na isa Hamshakiya tana kusa na kasa tabata a hankali ya sa hannunsa cikin nata ya juyo tare da hayewa samanta a hankali ya shiga matsawa da fuskarsa hancinsa yana Gogan nata ya hade bakinsu waje daya ya fara tsotsa kamar zai cinye bakin ya huta,hannayenta ya rike da hannayensa ya maida su saitin kanta ya bankareta kamar me shirin yi mata fyade Meenat dadi yana ratsata a hankali ta zare masa riga tana shafa shi ta ko ina musamman kirjinsa Nishi kawai sukeyi Sweet words na tashi daga bakunansu,Basu gama gigicewa ba sai da ya shiga Murza Albarkatun kirjinta yana shansu Meenat kamar wata me shirin hawa Bori Gogan kuwa ka rantse Aljanune bakake dashi masu Zafi suka motsa kusan raba dare sukayi suna jiyar da juna dadi kafin su sararawa Kansu basu ma San sanda bacci ya kwashe su ba.

Cikin Ma'eesha ya shiga wata tara Haihuwa ko yau ko gobe,Wata ranar Juma'a ta fara Nakuda aka kaita asibiti kamar zata mutu Yarima ya dinga Kuka ana bashi hakuri yan Uwa da abokan arziki jiki yayi Sanyi asibiti ya cika ana tunanin da kyar Ma'eesha ma zata tashi,muna Can Russia dama Saura 1wk mu dawo Nigeria Meenat ta fada min tana kuka,da sauri Aayan ya hada mana komai muka sauka a Nigeria,Asibiti muka wuce muna zuwa tana Haihuwa ta santalo Danta Namiji katon gaske kowa ya kalli jaririn yasan ansha wahala kafin a haifeshi,sai ga Ma'eesha ta farfado aka gyara ta da jiriri tare da canja musu daki,Yarima ya riga kowa shiga yana kuka idonsa ya koma red sai yaga Ma'eesha tangargar abinta,Munsha murna muka koma gidanmu mukayi baccin gajiya,gaskiya Aayan yana kashe min kudi a duniya ba abinda na nema na rasa,sutura kuwa ko matar shugaban kasa sai ta jinjina min, Fadeel ya girma yayi wayonsa gwanin sha'awa kamar dan Bature jajir dashi.

Yarima bakinsu daya da abokinsa Aayan shima ba a bikin suna dan ma kar a damesu sai ya dauke Ma'eesha da Jaririn suka hau jirgi zuwa Cairo wai sun tafi hutawa suna can akayi yanka aka radawa yaro Suna Ashman,acan Cairo sukayi jegonsu yana kula da abarsa,basu dawo ba sai da suka kwashe 3mnths lokacin Meenat a fara laulayi sosai,cikinta wata hudu,Duk inda Ameer yayi tana tare dashi Har masallacin juma'a tare suke tafiya tayi sallah cikin mata ta jirashi a mota,Ko taki binsa sai ya matsa sun tafi tare wai kar ya barta ita daya a gida tana laulayi,Ammah tayi fadan har ta gaji,ni ko Aayan ya samomin private university a Abuja can zamu koma dashi gaba daya mu da kano sai dai muzo Hutu,Daddy yace bazai yuwu ba sai dai mu dinga zuwa akan lokaci baya so mu tafi mu zauna ba zumunci.

Na fara lecture da wata biyar matan su Khaleel duk suna da ciki haka Su Hanifa ma an kusa Haihuwa, tuni anyi bikin Sabeer da Meenal,Aliyu da yar uwarsa shima, Meenat ta Haifo yarta mace kyakyawar gaske, Su Ameer har Dinner akayi hadaddiya a katafaren waje yan AsmaBaffa Fans club duk sunzo,Kasuwancina true fans duk gasu nan anci an Sha an cashe yarta taci Suna Fadeela.

Bayan Sunan Meenat muka koma Abuja ni da Aayan sai ga Kiran Ma'eesha wai Ammah ta samu ciki,Kunya ta kamani na saki Salati Aayan ya sameni na zuba tagumi.
Meenat kuwa harda rawa Ammah zata haihu,Hajja ma taji labari sai murna takeyi,Ammah kunya takeji wai Yayanta na haihuwa itama haka,Daddy yafi kowa kamar zaiyi hauka Sabo da Murna ya rasa inda zai Sa kansa.






Kwana biyu bana muku posting kuyi hakuri kawai gajiya nayi sam ban son Typing din shi yasa bana yi akan lokaci kun san Jiki da jini dan Adam ajizi ne sai Hakuri.










AsmaBaffa
[3/6, 10:54 AM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA





151-160











Official







By
AsmaBaffa










FINAL










Daddy murna tasa ya rasa inda zai sa Ammah yace sai ta zabi abinda takeso a duniya yayi mata taki fada wai ita kunya,Hajja tunda taji cikin nan ta kara son Ammah kusan kullum sai tasa an kawota a mota ta duba lafiyar Ammah,h aka ni dasu Meenat ko yaushe muna hanya nice ma ban cika zuwa ba sabo da nayi nesa dasu ina Abuja,Aayan ya Kira Daddy a waya yace Congrat Dad, Daddy ya shiga dariya yana godewa Aayan da ya matsa lallai akan a auri Ammah gashi ya Zama alkhairi.

Meenat yarta Fadeela tayi dan wayo kadan,Yarta ta shirya ta kawo mata ita gaskiya Fadeela tana da kyau ta hadu karshe,tsakanin ita da Fadeel dina ban san ma wa yafi wani kyau ba,Ameer ne ya fito cikin takunsa yasha wankan wani farin yard ba karamin kyau yayi ba,mikewa tsaye Meenat tayi tare da cewa Ina kuma zaka fita da yamma haka? Sarkin kishi ba inda zanje Aayan ne ya aikeni gidanmu yanzu zan dawo,to muje tare mana ba musu yace shi yasa kika shirya kema kenan dakko mayafin mu tafi,Ba musu ta dakko harda jaka da takalminta me tsini ta bishi suka tafi shi ya dauki Fadeela yana mata wasa,bayan sunje gidan suka ji Matar Mujaheed ta haifi mace,sunje sunyi barka suka wuce gidan Ma'eesha a can har dare suna gidan,sai 9pm suka dawo gidansu Meenat ta shirya Fadeela tare da lallabata wai tayi bacci lokacin Ameer ya fito daure da dan Towel fari a kugunsa yana goge jikinsa da wani karami gefen Bed jikin Meenat dinsa ya zauna wacce ke aikin jijjiga yarta,ki bata tasha Milk dinta mana sai ki ta wani mata wayo a haka yarinyar nan bata wani koshi da Nono kike hanata,ko na baka ita ka bata naka ne maybe zata fi koshi,Murmushi yayi tare da cewa ba sai kin fada min baka ba,kuma kema kin san da ina dashi har amai sai ta dinga yi yanda zan na cika mata ciki,ga Fadeel nan Har ya fita kiba,ai dama to ya girmeta yaro zaka ce wani abu,Nine yaron? Kalli yata katuwa,Fadeela taki bacci kawai ta zuge zip na rigarta ta fara bata Nono tana sha,Ameer har ya tashi ya nufi Wardrop ya dawo ya zauna shi burinsa yaga ana bawa jariri nono yana sha abin birgeshi yakeyi,Sai kallonsu yakeyi kamar maye,A hankali shima ya kwanta saman cinyarta ba shiri ta matsar da jaririyarta shima ya kwanta kadan,tana taje mata gashinta bata san me yake ba babu zato taji shima yana zuke daya Breast din kamar maye,da Sauri ta gama bata ta gyara rigarta tasan Halin Ameer sai ma ya shanye du ya zuke mata nutrients dinta.

Bayan wata Uku cikin Ammah ya girma sosai zama da kyar Sabo da cikin yana bata wahala, ina gidan Ammah Aayan yazo daukana muna cikin mota ya bani shawara Honey tunda naga kinyi dan nisa a karatun kuma gashi an kusa yaye Fadeel me zai hana a daina planning din kafin ki samu wani cikin kinga an yayeshi tuni,sai mu kara Haihuwa Allah shi ke rayawa Amma baza mu zauna ayi ta planning ba tunda bamu ke da kanmu ba ya kamata ace nima na tara Yara ko Uku ne sai ki huta da yawa,ko dan lafiyarki ma idan mace tana Haihuwa tafi lfy ko? Fuska na bata nace banfa gama karatu ba,ni gaskiya ko zan haihu sai na kara 3yrs sai na daina planning kaine fa kaki kaini schl da wuri yanzu kuma ga schl ga ciki ni Bazan iya ba,Baki ya bude Yanda yaga ina masa masifa daga kawo shawara yace Iyyeee lallai kinci abinci Mufeeda ke kike aurena ko ni? Kinga ina biye miki zaki rainani dama ance mata basu san kadan ba idan kana biye musu sai su fara rainaka suna takaka,Shawara fa na bayar baza ki fada min direct ba kema a shawarce zaki fada min sai a gane a dauki wanda ya fi dacewa yanzu ma Umarni kika bani sam ga abinda zakiyi ke kinje University ko?kuma ni zaki ma shouting kamar danki? Ransa ya baci sosai Amma zuciyata bata kawo komai ba sai ma cewa nayi Oho ni dai Bazan yi wani ciki yanzu ba,duk wahalar da na sha,kasan zafin haihuwa kuwa dole kace haka,a hasale yace Ok to zamuga me iko

Please Login or Register in order to submit comment