Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda kikace haka na fasa shawarar Haihuwa nake so kuma dole a daina Planning ai ni naga dama.
Ni da jikina sanda zanyi ma ka sani ne,har muka karasa gida cacar baki mukeyi har ya shareni kowa ya fita daga motar a fusace,ko dakinsa banje ba nayi kwanciyata a dakina,shima haka Amma gaba daya tunaninsa nakeyi kuma nasan shine da gaskiya kawai neman fada ne irin nawa,Kowannenmu da kyar ya samu bacci ya daukeshi,ba abinda yafi damuna irin yanda ya daina cin abincina,ya daina kula ko kallo ban isheshi ba har muka kwashe 1wk a haka kullum sai nayi kuka na godewa Allah,yau nayi niyyar bashi hakuri naga ya sakko yana jan Trolley yasha kana nan kaya masu tsada da mugun kyau,ba karamin kyau yayi ba kamar a saceshi,sai dai da gani yana cikin damuwa,bai ko kalleni ba ya nufi wajen Fadeel dake kwance yana wasa yana wutsil wutsil sai dariya yakewa Aayan yaga Babansa,ina kallo ya daukeshi suka danyi wasa sannan ya kwantar dashi ya sa masa farar takarda a hannunsa ya rike kam sannan yaja akwatinsa ya tafi,gabana ya fadi sosai yana fita na karbe takardar da Sauri na bude an rubuta gabana yana faduwa nasan ko bai sakeni ba to sai ya ci min mutunci a ciki ga abinda na gani a rubuce:
Na tafi Saudiya Nextwk zan dawo Insha'allah Bazan dawo nan ba Abuja zan wuce idan kun gama sanda kika ga dama ki koma schl,ke wato baki da kunya tsagera ce ke ko? ki tabbatar kin Daina planning din nan kafin na dawo ciki zan miki Sabo ki Haihu,Yarinya ba a Isa da ke ba sai rigima iri iri.
Love u,am gonna Miss u Darling bae.

Ina gama karantawa ban san sanda Hawayen farin ciki ya zubo min ba,ina dariyar jin dadi Kaji fa manya,masu Ilmi da wayewa,ba a fada ayi ta gaba ana fushi a kullaci mutum a zuciya,komai cikin ilimi akeyinshi ba irin mutanenmu ba,a fuska mutum ya nuna baya jin haushinka ko ka bashi hakuri yace ya hakura sai ya dinga gana ma azaba iri iri sai ya rama abinda ka masa,wasu kuma abu kadan sai a maida shi babba ayi fushi,baza a danne zuciya a hakura ba,ga Aayan duk yanda na bata masa naki bashi hakuri na daina zuwa dakinsa bai Sa yayi fushi dani ba,sai ma ya maida abin wasa,ni da kaina naji kunyar kaina,naji ban kyauta ba,kuma ko yanzu nasan Aayan ya gama wayewa ya nuna shi me Ilmi ne ba irin wasu ba ga Ilmi Amma Jahili ya fisu hali me kyau,gaba daya naji Bakin cikina ya yaye,nan take na jawo wayata da Sauri na danna Number dinsa,lokacin yana Airport ana screening bai samu damar dagawa ba,sai Text na tura masa ga abinda nace:
Allah ya kiyaye Hanya Mijina,Allah ya kaika lfy ya dawo mana da kai lfy,kayi hakuri ka yafe min a bisa bijirewa Umarninka da nayi,na tafka kuskure dan Allah ka yafe min My Man,Fadeel yana gaishe da Abbansa.
Love u much more Dear,already started Missing u My Husband.
Yana ganin sakon ya cika da farin ciki marar misaltuwa gashi har anyi solving case din,dama fushi ko masifa ba lallai su kawo gyara ba.
Tunda ya tafi yaki yarda muyi waya dashi sai text kawai kullum ba adadi,Kwanansa biyar nayi booking flight muka koma Abuja na shiga gyaran jiki ba ji ba gani zan tarbi Ango na.

Sajeeda ta Haihu da sati Biyu matar Khaleel me sabulu ma ta sauka lfy duk Maza suka haifa,yayin da su Sabeer suke kwasar Amarci,Sameera ma ta haifi mace tuni.
Lokacin kuma Daddy da Ammah sun tafi Us wai acan zata Haifa masa dansa ko yarsa.
Meenat uwar yan shiga kitchen yau ma tana kitchen tana girki Fadeela na Rarrafe ta biyota kitchen din Ameer ya shigo cikin 3qtr da yar t-shirt yau a haka ya fita ya dawo Sumar nan ta kara yawa yanzu ma yake ji da daukan wanka,Fadeela tana ganinsa ta dinga washe yan hakoranta wai ya dauketa tana mika masa hannu,Meenat tace wane ke yarinya sai ya fara da Uwarki tukun,dariya Ameer yayi ya fara Huging din Meenat tare da dagata Sama ya direta suna dariya har Fadeela kamar ta san me suke itama ya dauketa yana mata rawa tana dariya gwanin sha'awa,
Ameer Tafiya yayi da yarsa har wanka shi yayi mata ya shiryata cikin kaya kanana masu tsada da kyau har kwalliya yayi mata harda jambaki,shima yayi wanka ya dakkota suka fito Meenat tana ta dariya yanda ya mata kwalliya harda Jambaki kuma tayi kyau,Meenat tace Babyn Fadeel ce ai wannan,Ameer yace na bashi ita ma sukayi dariya,suna cin abinci na kira Meenat a waya nace zan kawo Fadeel yaye wajenku,Meenat tace Sister Kukan dan yaye nake tsoro wannan yaron naku miskili ga masifa yazo yana hanamu bacci wlh wajen Hajja can zamu maida shi,dariya nayi nace koma ina ne ku kaishi kawai,kwana Uku na sanarwa Aayan na masa text baiyi musu ba na shirya Fadeel da kaina nabi Flight na kawoshi gobe Aayan zai dawo,lallai aka tsantsara min gashi naci gyaran jiki ina sheki na koma Abuja da dare,washe gari na shirya abinci iri iri ina jiran isowar Aayan dina,Meenat ta kirani tace abin mamaki Sis ko kuka Fadeel baiyi ba kamar nice Mamansa kuma yana cin komai ko nono sau biyu ya nema na bashi milk shike nan Amma fa Fadeela tana cin duka a hannunsa,Dariya mukayi gaba daya tana bani labarin Fadeel.

Wanka nayi na shirya cikin fitted Gown Black and Golden color Ready made ce tayi kyau,kamar Wata balarabiya haka na fito,Gidana da jikina kamshi kawai yakeyi ina cikin gyara fuskata naji dirin Motoci nasan ma Aayan ne ya dawo,palo na sakko na tsaya jikin kofa ina jin Door Bell na bude da murna,dukul na tsaya ganin Ma'eesha da Yarima tare da Ashman dinsu,Daga ina kuke haka yanzu ko waya babu ku shugo ina murna,suna shigowa sai ga Aayan ashe yana bayan Yarima ban san dashi ba na juya baya naji ya rungumeni kamar zai maidani cikinsa,cike da murna na juya na kara makaleshi ina murna na bashi kiss a lips mun dade a haka yana kare min kallo,ga Lallena ya tafi da Imaninsa,a kunne ya rada min Abban Yarima ne ya turo shi Abuja zai masa Wani aiki na 1wk anjima zasu tafi gidansu ziyara suka kawo mana,a kunne nima na rada masa na gane yanzu muje kayi wanka kaci abinci,Yarima suna Palo basu san ma me mukeyi ba,Maeesha tace yunwa mukeji mu dan Allah kizo ki bamu abinci,Hanyar Sama Aayan yabi ni kuma na shiga kitchen na shirya Dining komai da Komai Yarima yace to mu baza mu jira ku ba ci zamuyi,dariya nayi nabi bayan Aayan lokacin ya shiga wanka.
Da kaina na shirya Mijina na bashi yaci ya koshi nima haka,bayan munyi Sallar Isha Yarima ya dauki matarsa da dansa suka tafi masaukinsu,Suna Tafiya Aayan ya jawoni jikinsa,nace jibi Allurar da akayi min date zai cika kaga ba sai mun kara yi ba tunda Haihuwar kake so,Murmushi yayi sannan yace ai ba yanzu nace ba daga yayewa sai an kara kamar ta 3mnth sai a bari,dadi naji sosai ina masa godiya ina bashi hakuri, bakinmu ya hade waje daya muka shiga sarrafa juna kamar ba gobe,kusan kwana mukayi muna abu daya gaskiya baza mu manta da daren yau ba mun jiyar da juna dadi wanda bazai misaltu ba.
Bayan wata Uku Ammah Haihuwa ko yau ko gobe tana shan wahala a Us Daddy kuwa ji yake da ita kamar itace wacce ya fara aura a duniya,Wata ranar asabar Ammah ta tashi da Nakuda suka tafi asibiti tare da Daddy kamar jira akeyi suna shiga da 5mnt ta Haifi Namiji kato kyakyawa 15mnt tsakani wata sabuwar nakuda ta kama Ammah ta Haifo Mace ta biyu,Yayanta biyu ta Haifa manyan gaske Namiji da Mace abin sha'awa,Tunda labari ya iske mu muke faman Murna,Babu wanda bai taya Ammah Murna ba,sai a Pics da video call muka gansu gwanin birgewa,ranar suna Aka Sa musu Hameed da Hameeda.
Sai da Ammah suka kwashe 2mnths yaran sunyi wayo sannan suka dawo gida,tattarowa mukayi da Aayan muka zo Kano munsha kallon kyawawan yan biyu,Aayan yayi kanne muma munyi kanne abin murna Fadeel dina ya kara girma da wayo yana yawonsa ko ina,Haka Fadeela ta Meenat tana Tafiya Ashman din Yarima sun saba Sosai da Fadeel.
Su Khaleel dasu Haneefa duk da yaransu dagwas dagwas kowa na ji da gayu,Matan su Sabeer ma sun kusa Haihuwa abin ba a cewa komai Zuriyar Hajja tana yaduwa Babban abin farin cikin Family din duk sun gyara halayensu,Hajja tafi kowa Murna da hakan sai dai lfy bata isheta ba jikin tsufa yau fari gobe baki.A mmah ta dakko Inna da wata Kawarta sun dawo Kano gidan da Yarima ya siya mata tace su zauna a ciki suma.

Bayan Shekara Biyu tuni Meenat ta gama Degree dinta ita da Ma'eesha,nima ina daf da gama nawa,lokacin Na kara Haihuwar yata mace sunan Umman Aayan taci Amma muna ce mata Royal Angel,haka Ma'eesha ta Haifi Namiji again Fhudal,Meenat ciki ne da ita kawai bata haihu ba,Su Hanifa ma daga me ciki sai wanda suka kara Haihuwa.
Bayan 1yr na gama Degree dina mun dawo kano yanzu hutawa muke zuwa Abuja kawai lokacin Ammah ta kara Haifo Namiji kato sunansa Muhsin.
Meenat ce kwance ita da Fadeela da Danta Ahmad dan karami sunyi rubdugu a jikin Ameer yana aikinsa a System duk sun Hanashi yi har bacci ya kwashesu duk suna saman cinyarsa,Meenat tayi matashi da kafadarsa Allah yasa sunyi shirin bacci,Saman Sofa ya kwantar da Meenat sannan ya dauki Fadeela ya kaita Bedroom ya kaita tayi fitsari sannan ya sa mata sabuwar Pampers Sabo da tsaro ya kwantar da ita saman dan Bed dinta dake jikin nasu,Jariri dan 4mnths ya dakko shima a shirye yake kawai dan Bed dinsa shima dake jikin nasu ya kwantar da shi,Wasu suna gangancin saurin Barin Yara su kadai a dakinsu wai gayu ko ace haka turawa sukeyi wani abu ya samu Yara kina can kuna bacci,ya kamata ana dan bari Yara suna kara dan girma da wayo, ko kuma a hadasu da Nanny suna kwana tare wannan duk bai dace ba a dinga bari Yara suna wayo kafin.
Ameer wajen da Meenat ke kwance ya je ya koma ya dakkota kamar Jaririya itama ya kaita saman Bed din su kato ya shimfidar da ita zai bar saman Bed din yaji hannayen Meenat ta sakalosu ta wuyansu tare da jawoshi ya fado kanta ciki mayen bacci tace Dan Allah mu kwanta ka hakura da aikin nan tunda kayi shirin bacci,Ok ai dama yanzu time dinki ne sakeni na dawo,Kayan wuta ya kashe ya dawo suma ya kashe musu light suka kwanta bayan yayiwa yaransa adduar bacci,Meenat ta shige jikinsa Ameer ya canja Salo na daban,bata san sanda ta biye masa ba suka Tsunduma a tafikin so addua dauke a bakinsu.
Ammah dai tun daga wannan Haihuwa guda uku Allah ya yaye mata bata kara Haihuwa ba.

Ma'eesha tana kitchen tana shirya girkin dare Ashman shuru ko motsotsinsa ba a ji ashe yana Palo Computer din Ma'eesha yake wasa da ita ya fasata yayi mata kaca kaca,ya dakko Handrier ma nata ya fasa,Body Cream ya kwaso yayi faca faca dashi a jikin kaninsa dake kwance wai shafa masa yayi,Maeesha ta fito kenan tayi arba da abinda yakeyi,takaici ya rufe ta tama rasa me zatayi masa, ai kawai sai ta fashe da kuka taga ta kanta zai gudu yasan yayi laifi ta cafkoshi tare da cire takalminta daya ta masa Flat ta Zane masa Duwawu yana ihun Kuka sai Dad yake kira,Suna haka sai ga Yarima ya shigo da Sauri kamar zai tashi sama yana masifa ya karbe Dansa yana tambaya lfy? Ma'eesha tace kalli kalla pls abinda yayi min gwara ka bani shi na ballashi,Harara Yarima ya zabga mata kuma shine zaki dukar min yaro karki kara taba min dana,ki fadi kudin na biyaki,ban hana ki masa hukunci ba ko ki masa fada Amma ban son duka kina masa kuka so kike ya lalace Uwarsa na zubar da Hawaye a kansa,yaro ai ba a masa fada ta haka,Nasiha zaki masa,ko zaki dakeshi ba irin wannan ba,kaima idan ka kara lalata abu a gidan nan Tiger zan siyo ta cinyeka Oya bata hakuri,da Sauri Ashman ya durkusa kasa yace kiyi Hakuri Mummy na daina,Maeesha bata ce komai ba ta dauki Danta ta sake masa wanka ta shiryashi,me aiki ta gyara wajen da komai,Maeesha yau sai fushi takeyi sai da Yarima yace zai siya mata duk kayan da dansa ya fasa sannan ta dan hakura kadan,Da dare ma fushi takeyi kuma da Yarima take fushin,Suna kwance da yayi niyyar riketa sai ta matsa gefe,da Sauri ya fisgota ya hade bakinsu ya shiga Tsotsa yana lallashinta tare da fada mata Sweet words har ta sakko ta Bada kai Bori ya hau.
Alhmdllh Family da kowa ana zaune lfy cikin so da kaunar juna,ba wani fada etc,ga zumunci anayi ana zaman lfy da kowa,Haka kawaye da abokan arziki lfy ake rayuwa dasu,gaskiya kowa ya gammu sai yayi sha'awa bamu da wata matsala.

Wanka Aayan yasha cikin wata Shadda light blue me matukar kyau da tsadar gaske dinkin zamani fitted na Maza,sai kamshi yake ba karamin kyau yayi ba kamar a saceshi yaro yake kara dawowa,fitowa nayi daga Bedroom dina sanye cikin wasu kana nan kaya ba karamin kyau nayi ba,jean Black da t-shirt white and Blue gashina yasha gyara sai sheki da kamshi ke tashi a jikina,Magan nayi cike da Salo na lankwashe Murya kana nace My Man ba dai fita zaka yi ba? a hankali yace ae gashi ma almost 9pm,Dan Allah ka fasa muyi hira ka dan jira na gama abinda nakeyi na dawo na kula da kai bana son fitar nan taka kaji My Man na karasa cike da shagwaba,tsigar jikinsa ta tashi yaji wani yarrrrrrrr wanda yasashi komawa sama kawai ya fasa fita,Baba Me kula da Yara ta kawo minsu ta gama shiryasu gwanin sha'awa yan gayu a gidan yan gayu,iyayensu ma yan gayu,Fadeel yana bina a baya ina dauke da yata mace muka haura Sama,Fadeel da gudu ya fada jikin Aayan ya wani kwanta mala mala sai tumurmusa Aayan yake yana Ihun wasansa,Bari Fadeel bana son shirmenka sauka ka tafi dakinku wurin Baba sai tsalle kake min a Bed sai ka lalata min Bedsheet,Aayan yace kaji Me Mummy tace,Kafada ya makale shi a nan zai kwana dama da gadonsa kawai na dakko na danna abu sai ga Bed din Fadeel ya bude ya Zama gado na Yara hadadde, jeka kwanta kuma kayi bacci ban son wasa,kwanciya yayi itama Kanwar Fadeel Angel na kwanta na daura ta saman cikina tana bacci,Aayan duk hankalinsa ya tashi shigar dake jikina da kamshina ya gama ruda shi,matsowa yayi jikina a hankali ya rada min a ajiye Baby girl din nan a bani lokacina Honey,Nima a hankali nace kasan dai Fadeel baccinsa baiyi nisa ba,dan Allah tashi ki duba idan yayi bacci ki kaishi dakin Baba,Kwantar da Royal Angel nayi saman Bed dinta,Aayan yace tsaya na kaishi da kaina ya furta yana dauke da Fadeel ya kwankwasawa Baba ta karbeshi tare da kwantar dashi,har dakin ya shiga da kansa yayiwa Fadeel adduar bacci sannan ya fito yana Yiwa Baba sai da Safe.
Kafin ya dawo nayi shirin bacci na Angel tana bacci abinta nayi mata addua shima Aayan yazo yayi mata tasa sannan ya hauro Saman Bed,Direct Samana ya haye ya sani a corner ya shiga Kissing din Goshina,saman hanci na,zuwa lips dina da wuyana,duk ya rude ganin Albarkatun kirjina sai kara kyau sukeyi basu da alamar zubewa kamar ban taba shayarwa ba,muryarsa na rawa yace I love u My life,kullum sabuwa kike dawowa Darling,Kaima haka Darling Bae Bazan daina Sonka ba bana gajiya da kai,ajiyar zuciya muka saki a tare lokacin da yake shigata dauke da addua a bakunan mu,Ba abinda mukeyi sai Nishi da Kukan Dadi Kalamai masu sanyi da gardi suna fita ta ko ina sai da muka tabbatar mun raya wannan dare wajen daffaka Sunna.
Aayan sai addua yake min yana Sa min Albarka nima haka a zuciyata ina alfahari da samun miji irin Aayan samun irinsu sai an tona,ba abinda na nema na rasa shi yasa ko aiki bama yi na Gomnati ko Company komai mazajenmu suna mana kuma muna godewa ba hadama da son zuciya.
Mun kara gogewa mun zama matan attajirai masu ji da kansu kowa ya kallemu sai ya koka musamman ni yanda ba a magana ma,fadar yanda na koma bata baki ne,ko yaushe mune Abuja,Saudiya,Us da Sauran kasashe muna zaga duniya,M otoci sai wanda muka ga damar hawa Ameer mota har biyu ya siyawa Meenat,Maeesha ma haka ni kuwa sai yanda nayi da motocin Ogana,yace zai siya min nace motocin sunyi yawa haka iya na gidan sunfi kala goma na alfarma.
Muna taimakawa na kasa damu da dangi abokan arziki sosai muna taimaka musu har Alummar Musulmi indai munga wani a wani Hali sai mun tallafa musu, gaskiya Allah ya zuba mana baiwar kyau gaba dayanmu dasu Meenat sai ka rasa wacce ce tafi Haduwa ma,muna kashe wanka.

Bayan wuya sai dadi haka Allah yake ikonsa baka zama wani sai ka sha wahala,idan akayi hakuri komai sai ya wuce kamar ba ayi ba,dama rashin hakuri shike jawo barna iri iri,wani kullum cikin rana yana neman na Halak bai samu ba,wani sai kaga Bai shiga ranan ba Allah ya bashi ya kara masa,kyauta ce ta Allah,wani kullum addini yana bin dokokin Allah sai ganshi bashi da cin yau bare na gobe Ammah sai kaga me sabon Allah gashi attajiri na gaske,Sai ayi Hatsari kaga Malami me tsoron Allah yayi kaca kaca ya rasu ka Hango Karuwa a gefe can tana cin chewgum dinta ko rauni bata ji baπŸ˜…πŸ˜… haka Allah yake ikonsa,duk halin da ka tsinci kanka ka gode masa,sannan aci gaba da addua karki ga Mufeeda da Aayan tare dasu Meenat kamar Allah ya basu komai na duniya kice kema sai kin dawo haka,kowa da Kaddarar Sa kowa da jarabawarsa kuma questions na kowa daban ne idan kikace zaki copy jarabawar wasu to zaki fadi Zero Katon kan jaki zaki ci πŸ˜…Sabo da ba questions dinku daya ba kowa da kalar nasa wani yafi wani,kuma bawai Su Mufeeda za ace shikenan baza a kara jarabtarsu ba no zasu ci gaba da karbar jarabawa daga Allah sai ko in su samu me sauki.

Aayan karki ga me kudine da lafiya ga kyau kice kema dole irinsa zaki samu ko mijinki sai ya dawo Ameer ko Yarima πŸ˜…duk Halittace ta Allah sai kiga dan Mummanki yafiye miko ko wanne namiji a duniya Halitta ce ta Allah kuma kowa yana da tasa baiwar ta musamman,mata a kara hakuri da juriya sannan mu kara jajircewa wajen kula da mazajenmu tare da tarbiyyantar da yaranmu.

NAN ZAN AJIYE ALKALAMINA NA KYALE SU MUFEEDA HAKA.

ALHMDLLH da Allah ya bani dama da ikon kammala wannan Novel,ina matukar Godiya gareku masu kaunar wannan Novel,ina jinjina ga masoyana kaf duk a inda kuke ina kaunarku da wanda na sani da wanda ban sani ba,Masu kirana ta waya,text etc na gode Allah ya bar zumunci.

Ina neman Afwarku na rashin karasa muku Novel da wuri da banyi ba na samu kaina da rashin son Typing da fatan zakuyi hakuri ni kaina ban so hakan ba.

Documents from AIHAUSANOVELS

Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels

Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels


Naso ace duk masoyana dana sani na baku kyautar page ko na kwala muku kira na gaishe daku a Cikin Novel dinaπŸ˜πŸ˜… Amma hakan Bai samu ba,ayi hakuri ina kaunarku fans.

Groups wanda suka fi kowa birgeni wajen yin Sharhi Har na Samu na gama typing ina jinjina da godiya:
ASMABAFFA FANS CLUB
KASUWANCINA TRUE FANS
HOUSE OF HAUSA NOVELS
TASKAR SURAYYARMS
TASKAR FIDDAUSI SODANGI
LATEST NOVELLA
UWARGIDA da Sauran Gp na gode Allah ya bar kauna.

Sai kurakurai dole za a samu da yawan gaske wanda ku masu karatu zaku fi gane hakan,da su Typing error ayi min Afwa wannan Halayyace ta dan Adam wanda ya Zama dole tunda dole za a samu wani abin da bai muku ba,ga kuma halin mantuwa shima sai anyi mana Uzuri.

Kuskurenmu a ciki Allah ya yafe mana,darasin da muka koya Allah ya bamu ikon yin aiki dashi Ameen.
Fans Allah ya biyaku ya saka muku da alkhairi baki daya.❀❀😘

Sai mun sake haduwa a sabon Novel dina nan gaba Insha'allah idan Allah ya kaimu da rai da lfy zan sake Sambado muku Sabo idan na huta da dan yawa.😍😍😍❀❀❀❀❀❀😍😍 Kar naji an tambaye ni sabon Novel da wuriπŸ‘ŠπŸ‘ŠπŸ‘Šsai na huta da yawa.

Zanyi Missing dinku fans musamman masu Sharhi yanda muke rakashewa muna wasa da dariya😍😍😘😘😘😍🀣wayyooooo.

AsmaBaffa loves u all.....







AsmaBaffa
COPY BY ZAINAB BUTALAWA

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment