Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Contract sukayi Deal aka biyasu kudi suka kyale zancen,sun san kuma zamu iya kwace kudinmu tunda a tafin hannunmu suke,sabo da sun San baza su iya sawa a sakeki ba an rigada an biya shi yasa suka zuga Hajja tace ki dawo gidan nan da Zama,wannan securities din ma duk Aayan ne yasa suke tsaro na sabo da makircinsu,to Daddy dukiyar taka fa? Tana hannun dana Aayan na bar masa komai tuntuni shine me kudin shi yake komai kawai taimaka masa nake da shawara,mijinki young millonier ne da an San abinda yake dashi a duniya to da duk duniya sun San da zamansa,amma duk da haka da dama sun sani kasashe nayi suna shima haka.

Yarima Bobo fa Daddy?shi kadai ne abokinsa dan Nigeria da sukayi karatu tare kuma ya yarda dashi sun aminta da juna,ranar danaga ya Zane su Haneefa fa? Waya tayiwa Abbi kuma yasan ba mai iya taka musu birki sai shi shi yasa yace yaje ya Zane masa su.babu wanda suka tsana yanzu sama da mijinki da kuma wanda suke tare da shi,suna nan akan bakansu karki ga suna miki dariya ko sunyi luf kice sun shiryu wlh wani kullin suke kullawa,da bana raye da tuni Aayan ya bar kasar nan tunda ko tayi masa baki bazai bishi ba to amma ina raye ni zata yiwa kinga akwai matsala,ki nutsu yata shi yasa na baki labari ki san yanda zaki zauna dasu da basira tare da gogewa,fada da zage zage ko duka ba shi bane use ur Upper ki kwaci yancinki da na mijinki, idan kuma Kun shirya rabuwa baku da matsala Ku kuke zaune sa juna ba ni ba,yanda kukayi dai dai ne,a takaice na baki labari dan na yaba da tarbiyarki,nasan Aayan bazai fada miki ba shi yasa na sanar dake,idan kin zabi business za a biyaki ko nawa ne karki damu tashi kije a sannu kuma zaki ci gaba da gano halayensu daya bayan daya,abinda da ma ban sanar dake ba duk zaki gane nan gaba,a takaice na sanar dake.

a raina naji tausayinsu sosai har kwalla nayi sannan sai naji tausayin kaina da yan uwana,garin neman gira zan rasa ido,haka kawai son kudin jaraba ya kawoni inda za a ruguza mana rayuwa,yanzu ya zanyi?Me zanyi,lallai fada da masifa ba shine kadai zai kwace mu ba,ashe Aayan yana da gaskiya da baya saurarsu yake cewa na sharesu kawai,irin wannan kiyayya haka wacce zuciya ce dasu,ba a saduda ba dana sani tun tuni kayi ta abu daya akan wani,har Aayan suka batar dashi lallai,to tunda suka Yiwa yan Uwa haka ai nasan ma wajen Kudus zasu cilla ni shike nan zan bace ko a halakani,a raina nace ni na fasa auren na hakura da Kasuwancin kawai bari ya dawo ya sake ni kawai mu tafi,bazan iya wannan rayuwa ba wannan gidan ai sai su ni kam yafi karfi na.

Muryar Daddy naji yace tunanin Me kikeyi yata?nace ba komai kawai mamaki nake yanda kuka iya Hausa haka bayan ba anan kuke ba,yace lokacin Hajja bata wani jin turanci da Hausa muke magana har na kai 5yrs daga nan ina son yaren akwai wani bahaushe abokinsa yaci gaba da koyamin na iya sosai,Aayan ma na koyawa Mamansa duk da bata wani iya ba haka muke masa Hausa ya tashi da yare biyu,da ya dawo nan kuma sai ya kara gogewa da yaren.

Me kike so kiyi da kudi yata idan kin samu da har kika amince da wannan aure ba tare da bincike ba duk da cewa Aayan ya min bayanin halin da kuke ciki? Daddy Sabo da muyi Karatu Meenat ta zama Likita,Maeesha ta zama lauya,sannan nayi mana gida me kyau,mu dinga cin kayan dadi,sannan idan munyi aure mu dankara kayan daki masu kyau shike nan,Murmushi yayi yace to wannan tunanine me kyau,me yasa kike son Kanwarki tayi likitanci ke kuma fa? Nace ni abinda yake birgeni da Likita Daddy naga sun gwalewa mutum ido sai ayi zuruuu ana kallo sai ace yana da cuta Kaza hhhh na karashe ina dariya shi kanshi Daddy yaji kuruciyar tayi yawa sai dariya yakeyi.

Yace Allah me iko to Lauya fa? Shi Lauya Daddy Allah hular nan da suke sawa wata tum tum kamar gashin tinkiya itace take bani dariya,kuma da glass dinsu yana birgeni,sannan idan suka tsaya suna zuba karya gaban alkali sai ka rantse gaske ne,shine suke birgeni sun iya sheko ta,Daddy yayi dariya to ai ba kowa ke yin karyar ba a cikinsu,amma dai sunayi ga shedar zuuur a karbi kudin mutum,Yace Allah ya shirya su,ke kuma fa me kike so ki zama ?nace ai ni nawa yafi nasu dadi malamar Makarantar primary na dinga shiga aji gaba daya a mike ace Good morning Aunty,nace morning student How are u,suce we are fine thnk u Ma,sannnan ni kuma ina bata rai ina yanga tare da tsawa nace Sit down,kuma na dinga koya musu A babba a karama,Baba ya tafi Gona,malam yana karatu,Inna tana Girki.Daddy ya dinga dariya yace ah lallai naki yafi dadi,tashi ki tafi Yata gashi 4pm tayi Sallah zanyi, 8pm Aayan zai dawo yau daga Umrah,cikin Kasuwancin naku da kukeyi ki dafa masa abincin gargajiya yana son wainar shinkafa da miya.

Na mike nayi masa sallama zan tafi yace Yata yau kin sani nishadin da na dade ban samu ba shekarunki nawa ne haka? Tunda kaine Daddy na gaskiya zan fada ma 16 nake saura wata biyu na shiga 17yrs Amma karka fadawa kowa Sabo da har Aayan 17 nace masa bana so a dinga min kallon yar yarinya.
To Bazan fada ba sai kin sake zuwa yata nace to Daddy Allah kara lfy na fito na dawo part dinmu.

Sallah nayi na fada kitchen na fara hadin wainar shinkafa da Miya,Su Meenat sun tafi karbo mana dinkunan da muka kai wurin tela, bani na gama Wainar ba sai wurin 7:30, ina kitchen su Meenat sun dawo tare da Driver duk na zuba musu sunci har Driver,Ni kuwa ina kitchen a kaskon ma naci na koshi da naga na soya wata tayi min kyau sai nace wannan tawa ce ni zan cinye ta,saai na jefata a plate na zuba Miyar taushen na cinye ina yarfe hannu,ga zafi ga Dadi,miyar tayi dadi harda naman Rago,ina gamawa na masa kunun gyada,na yanka masa Fruits a wani glass Bowl me kyan gaske nasa a fridge,Meenat da Ma'eesha ne suka wanke abubuwan dana bata tare da gyara kitchen fes bayan sun gyara ko ina na gidan sosai yana kyalli ko ina kamshi ke tashi,Dakin Aayan na kara gyarawa duk da cewa sun gyara sai da na kara tisawa na kunna Ac ga sanyi ga kamshi,na kulle,nayi Sauri na shiga wanka,na fito yau Salo zan canja a gidan nan.

Meenat ce ta gyara min gashi da mayuka,na shafa lotion me kyau da kamshi,dama gashi na kara haske abinka da fara dama ta samu waje, yar kiba da kyau nayi Sabo da ina ci ina koshi a kan lokaci,Cikin dinkunan na zabi wani Lace me kyau pupple and Brown riga da skert nasa,yanda na fito a dinkin ba a cewa komai,mazaune sun cika fam dinkin das a jikina,Meenat ta shafa min powder sama sama ban son kwalliyar nan me yawa ni,maroon jambaki ta sa min sai kwalli tare da samin eyeliner a saman ido harda nayi tsananin kyau,gira kuwa na hana tayi min da brush na taje na gyarata ba tare da na kara komai ba Sabo da girarta baka ga yawa,tace saura sarka aka Sa min wata yar karama pupple da dankunnenta,nasa agogo na wani me kyau na yan gayu da muka siyo Brown,Meenat tace sai na Sa zobe ma yana kara kyau a hannu,haka nasa wani me kyau,ta zauna ta tsantsara min dauri tare da sakin gashina ta baya kyau ba a magana ni kaina sai yanzu na kara son kaina,naji kamar na lashe kaina Sabo da yanda na hadu,nace kai ashe nakai haka kyau,Meenat tace bakya fito da kyan naki ne ai ke kullum ke kike maida kanki baya.

Nace a haka dai duk kwalliyar taki aka hadu da Kwaja kuma,Dukana tayi a baya da wasa muna dariya,tace Allah sai na kai kararki,nace yawwa gobe zan kaiku ku gaisar da Baban Aayan,Allah ya kaimu.
Nace bari nasa takalmi ko?tace ae kisa me tsini ki Bada mamaki yau,ai ko na dakko cikin sabbabinmi wani Brown me tsini wow wow na gama birgewa yau ko uban waye ya ganni yau sai yawunsa ya tsinke indai Namiji ne.

Ina cikin gwada yanda zanyi Tafiya Meenat tana gyara mana dakin muka ji Karar motoci,nan take na zaro Hijab Meenat ta fisge ke wai mene haka bayan kin gama kwaye cinya ya gani dan Allah muje palo,duk sunyi kwalliya Meenat cikin Doguwar rigar arab,Maeesha English wear tasa riga da Wando suma sababbi sun sha kyau,mun baza turaruka,ni kuwa kamshin nawa daban ne da nasu.
Knocking muka ji nace wayyo kunya nakeji gashi nan zai ce sonsa nake,Meenat taja tsaki tace tonawa kanki asiri ki huta,Maeesha ce ta bude kofa ni kuma na hakimce a kujera na maze ina danna yar nokia ta ka rantse wata shegiyar waya ce nake chat ko wani abu.

Wow wani Balarabe ne ya shigo Aayan sanye da farar fitted jallabiya yasha kyau kamar me don ya canja style din gyaran gashi na ala tsine uwar me karya.

Kamshi ya cika gidan,cikin Securities wani ya taho zai shigo masa da akwatuna sai muka ga ya juya da Sauri ya bude kofar yace jeka daga nan ma is ok,da kansa ya shigo da akwatuna har Uku masu kyau na gaske.
Sallama muka amsa Meenat ta kifta min ido na mike jin karar takalmina ya kalleni muka hada ido,na tafi da shi Amma sai muka ga ya tamke fuska,naje har gabansa na makale murya can kasa nace sannu da zuwa Aayan.

Bina yayi da kallo yanda na sheka kyau ba a cewa komai,akwati daya na karba,Meenat ma tazo tace Sannu da zuwa yaya,da fara'a ya amsawa Meenat yace ya gida ya schl,tace lfy,Maeesha kuwa hannu ya bata suka tafa har suna dariya,tace yaya dama tuntuni Meenat take nemanka zata kawo ma karar Sis Mufee wani me Katon ciki ne cikinsa kamar Randar Ammah yake zuwa wajen Meenat wuyansa Allah kamar bulalar malaminmu,shine Sis take ta tsokanarta tana mata dariya.da gaske ya tambaya yana kallon Meenat da yake duk yarane da Sauri Meenat tace ae wlh tun rannan kullum sai ta min dariya har da dare dan Allah yaya ka koreshi in yazo,ba damuwa in yazo ki fada min yace tare da Haurawa Sama,daya bayan daya na dinga kai masa akwatunan har Bedroom,ya shiga wanka lokacin na sakko kasa naji ana buga mana kofa nasan bazai wuce jarabar yan gidan ba,ina lekawa na hangosu kuwa mata da maza manya da yara na bude tare da cewa lfy? Basu gane ni ba sabo da kyau,Ke dalla matsa gidan ubanki ne? Juyawa nayi dan su kara ganin yanda na hadu,gaba dayansu da kyar suka gane ai nice, da mamaki sukace wajen dan Uwanmu muka zo ko kina da gado ne a gidan nan? Na yatsina fuska nace ku koma sai gobe da Safe a halin yanzu Bazan iya Barin me gidana yaga kowa ba dan karma a bata mana Mood, yanzu na boye abina na Adana mijina,na killaceshi baza kuzo ku Sa masa tention ba aikin banza sai roko da san abin duniya duk abinda ake muku bakwa gani sai kun shiga hakkin iyali ba dama mu gabatar da Sunna cikin kwanciyar hankali Naja tsaki kafin suce komai na banke kofa na kulle nasa lock nayi tafiyata.









AsmaBaffa
[1/13, 12:33 AM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA






51-55






Official






By
AsmaBaffa








Ina matukar baku hakuri fans na rashin posting dina jiya ayi min Afwa bana nan unguwa naje,yau kuma baki nayi shi yasa ban samu dama ba.






Wannan page dina ne AsmaBaffa🤣🤣🤣nima na bawa kaina da kaina.









Meenat suna ta karatunsu na wucesu na shiga kitchen tare da shiryo abincin Aayan na kai har Bedroom dinsa yana wanka bai fito ba dama wankansa dade wa yake sosai,ina zaune Saman Bed dinsa sai gashi ya fito daga shi sai dan gutun towel a kugu karami a wuyansa,jikinsa abin kallo ne ya hadu da yawa ko kai waye sai ka kalleshi sabo da kyau,dan kar yace ina kallonsa kawai sai na sa yatsana na tsakiya a baki ina ta tsotseshi na sadda kaina kasa,har ga Allah ban san ma na sa Yatsan a bakina ba, ina ta yi ya juya baya yana ta shirinsa don bazai iya kallon tsotsar yatsan nan da nake ba bilhakki abin so childish.

Tunawa nayi da salona na wayo da zan masa tunda na Canja taku na,sai na Mike a hankali na taka har gabansa dama na cire takalmin dana sa Already,kunya da tsoro suka taso min sai na dake na matso lotion din da yake tsafawa na murza a hannuna cikin wata murya da ban san na iya ba nace kawo na tayaka baka iya bama sam kawai ban jira amsar sa ba na daura hannuna a kirjinsa tare da cewa mutum kato bai iya kula da kansa ba,suman tsaye yayi amma kuma sai naga yaja baya da sauri ya matsa tare da cewa kee mene haka,na nuna ban gane ba nace da akayi me? Ka tsaya mana na kara matsawa da sauri yaja baya again kamar yaga dodo, na bishi zan kara damkoshi sai naga ya ja da baya da gudu,na fara dariya ina binsa yana guduwa,na bishi muka fara zaga dakin da gudu dan sosai yake guduna kamar kamar yaga wani zaki ko Damusa,ina ta binsa ina dariya shi kanshi dariyarsa yake kunshewa yana yin kadan yana ke wai mene haka bana so, nace Allah sai na shafa ma,muka zaga ta bayan sofa ya daga kafa zai haura ta saman Sofa lokacin na kamo Damtsensa da hannu biyu sai ya fada saman Sofa nima na bishi muka fada kai gaba daya ba shiri ya saki dariyarsa,nima haka na cikwikwiyeshi yana so ya cireni a jikinsa amma na rikeshi kam gaba daya a jikinsa na Dafe,da kyar dai ya kwace ya Mike ya gudu Saman Bed gaba daya ya shige blanket,sai kansa a waje,nace dan Allah ka tsaya mana wai mene? Yace ke tsaya a nan karki matso nan,Na tsaya a hankali nace shike nan tunda baka so bari na zauna a gefen Bed din naka,yace no sai dai in baza ki taba min jiki ba to ki zauna,ai nace na fasa Zama kawai zanyi.

Ka tashi ka karasa shirinka Kaci abinci sai kayi baccinka,kaje wurin Daddy? Harara ya mako min ke wai nan nufinki wata mace ce har wani sani abu kikeyi kina tambayata abu kanki tsaye,ni da Daddy na me ya shafeki a ciki ki daina min shishigi tam.

Allah ya baka hakuri dama tuna ma nayi,sakkowa yayi daga saman Bed din ya karasa shirinsa cikin kayan bacci masu kyau na maza ruwan toka,s aman carpet ya zaune dake dan gefen bed din,yana bude flask din yaga Waina da miya nan take ya dinga zuba murmushi maimakon ya min godiya kawai sai yace dan sunkuyo zatona wani abu zai ce kawai sai na ji rankwashi a kaina kwasss Gift ne wa ya fada miki ina son wannan? Anyway tnx da sauri na Dafe wajen nace ouchhhh ina turo baki cike da shagwaba nace da zafi Allah yanzu da kai na yiwa haka da tuni ka fara fada,abincinsa ya fara ci bai ce min komai ba,har ya gama yayi Brush ya fito tare da yin Nafeela raka'a biyu,lokacin na kwashe kwanikan na maida tare da gyara wajen,lokacin yana shafa addua ya idar.

Saman Bed ya haura bai ce min komai ba dan ni Jarida nake ta buduwa ina kallon hotunan labarai,tunawa nayi ban fadi me ya kawoni ba,nace dazu mun dade da Daddy Muna ta hira,gaskiya Daddy yana da kirki sosai,kayi sa'ar uba Allah yaja kwana ya kara masa lfy me amfani,sabo da na yabi Daddy tare da masa addua sai naji yace dawo nan ki bani labari me yace miki ya furta yana nuna min gefensa da Hannu,naso naki zuwa amma kwarjininsa baza su bari na masa musu ba Sam,haka na Mike naje tare da hawa saman Bed din sosai har tsakiya kusa da jikinsa,kawai naji yanayina yana canjawa sai na tsinci kaina da son kwanciya a jikinsa musamman da naji laushin fatarsa dazu ga kamshi,du sai na diririce abinda nazo da niyyar na fada cewar a sakeni na fasa auren sai na kasa na manta ma da zancen Sam,sai naji kuma shagwaba ta motsa ba abinda nake so irin nayi abata na samu me biye min amma ba dama,a raina nace ke kina yar yarinya haka,muryarsa ce ta katsemin tunani da cewa ina jinki, kawai sai na susuce na rude abinda ya rambayeni daban abinda nake bashi amsa daban na riga da na zauce sabo da ya hadu da yawa.
Na jingina da jikin Bed din nace hmm dama Ashe Umrah kaje bamu sani ba? Yace ae mana,me kika yi wa Daddy? Nace kudina ya kare nazo nan na dauki 5k ciki ka irga abinka kar kaga babu kace nice shima ba yanda zanyi su Meenat zasu je schl,yace Ok Daddy yace miki wani abu? Ni dai ko jinsa bana yi wani iri nake jin jikina nace uhm...uhm...turarenka ma jiya nazo na fesa maka,amma kadan na fesa kar kaga ya kare kace nice, kalau kike kuwa ko aljanun sun motsa, kamshinsa ya gama gigita min rayuwata sam na kasa gane kaina,duk Ac da ke wajem gumi na fara yi,a hankali jiki ba karfi na zame dankwalina gashina me uban tsayi ya watsu ya kara wani kyau, bai kawo komai a ransa ba tunda yasan shirmena kuma kallon yarinya yake min har na Isa ma wani feeling,a hankali ya juyo kamar me rada yace ko baki da lfy?, Nace ni ina zan sani lfy nake ko kalau bazan iya ganewa wanne yanayi ake ba,sanyi ne ko Zafi,zamewa nayi tare da kwanciya a saman bed din tare da lumshe ido nayi shuru ban kara magana ba nayi shuru,tasar min a bed ki tafi to tunda ke ba a abin hankali da ke,shuru bance komai ba,ya matsa na bar masa bed ni kuwa tuni jikina yayi weak da yawa bana son ko nayi motsi ina daga kwance nace kawai labarin gidan nan fa Daddy ya bani, to shine kike min shirme abinda na tambayeki daban amsarki daban? Banza nayi dashi,shima bai sake magana ba ya juya min baya tare da kashe light ina jinsa yace tunda baza ki tashi ba sai ki shekara a bed din,shuru na masa har ban san bacci ya kwasheni ba shima haka.

Karfe daya na dare na farka na tuna maganar da zan fada masa ni ko dama komai dare idan na tuna zan fadi magana ban fada ba indai mutum na kusa dani sai na tashe shi,ba bata lokaci na kai hannu saman gashinsa na ja da dan karfi firgit ya tashi da masifa,hannu na kai da niyyar nace Aayan zan dan bigeshi,caraf ya rike min hannu tare da juyowa daf dani muna facing din juna har muna jin numfashin juna,a hankali yayi magana ki daina taba min jiki,kinzo kin dameni menene,sai na kara mantawa da maganar da zan fada ta a sakeni,yanda naji hannunsa cikin nawa me laushi ga kamshinsa dake kashe min jiki sai nace ruwa zan sha,Ke haka kike dama kamar yar 4yrs ki hana mutum sakewa kuma haka kike kwanciya da kayan jikinki ke? Nace a'a yaune kawai,haka kawai kizo ki takura min ya Mike tare da kunna light ya miko min robar ruwa daya,ba shiri na bude na Sha ta dole,akwatin da yazo dasu daga Saudiyya ya bude tare da Zaro min wata sabuwar rigar bacci hadaddiya amma fa tayi tsaraici gata fara wata silk ce yar guntuwa me hannun bra,in kasa komai sai an gani duk wani tudu da gangare,ina gani nace zan tafi Dakinmu ni,Murmushi yayi tare da komawa jikin kofa na dauka bude min zaiyi na tafi sai naga yasa lock ya dawo yace ungo tashi maza ki cire kayan nan,a ransa yace zaki takura min gwara nayi maganinki.

Hade rai yayi kamar baya dariya ba yanda na sanshi tun farko,na tsorata yace get up ko yanzu nazo na fara ball dake tunowa nayi da yanda ya taba min farkon ganina dashi,da sauri na Mike na karba na kasa cire kayan na tsaya kawai,a hankali ya matso tare da rungumoni na kwanta a jikinsa ina ta salati a raina don wani zirrrr nakeji tun daga kaina zuwa kafa ta,zip din rigata ya zuge na kwace jikina da sauri na ja da baya zan tsere da zafin nama ya biyo ni tare da jawo rigita na dawo baya ina dariya shima haka,har mamaki nake dama yana dariya,ido muka hada sai naga idonsa kamar ruwa a ciki yayi dan red,ganin ina kallonsa kawai sai ya dauke kai tare da juya min baya yace na baki 2mnt ki canja idan kika sake na juyo wlh sai na miki sintir.

Da sauri na cire kayana daga ni sai pant nace kar juyo na kusa da sauri na zura rigar a jikina dukiyar Fulani na yan matasa ana kallonsu da adadin girmansu,Na ninke kayan dana cire harda bude Sip side daya na adana abina kun San ni akwai tattali sabo da an saba da babu don wata tsaftar ma akwai babu a cikinta.

Juyowa yayi yaga yanda nayi mugun kyau a ciki yace cire min a bata na fasa dama lefen wacce nake so zan aura na fara hadawa shine na baki daya sai naga ma bata miki kyau ba Ciro min a bata ba size naki bane nata ne, wani bakin ciki ya kamani tun ba ayi nisa da business ba za a ce aure za a kara,sai na tuno dama fa yayi aure ba sau daya ba yana saki,a raina nace me auri saki ne nima Sakina za ayi,da kyar na daure bacin raina na kakalo murmushi nace Allah ya sanya alkhairi kace zamu Sha biki ai ranar za a ga yanda zan kwashi rawa,kai amma naji dadi sosai kaga an samu me Kula da kai wacce rake sonka kake sonta haba ai Alhmdllh naji dadin wannan magana ka kuma birgeni da sauri da sauri nake maganar ina murmushi harda yar dariya kamar na zare, muryarsa naji yace tnx lallai kina da hankali na yaba da hankalinki kwarai ba ruwanki baki dauki duniya da zafi ba,sai ki dinga min abin cin gargajiya tunda nan kika kware ita kuma dama tafi iya na bature,cikin bacin rai da fusata na hayayyako masa da masifa dake ni tsinanniyace ko? Sama na zaga ko me? Kanwa na kawo? Wlh bazan kara kulaka ba bare har nama girki,auren Kasuwanci mukayi dan haka duk kudina ka tattarosu ka biyani gaba daya na kara gaba,kawai ka sakeni na gaji dama sai kawai na fashe da kuka sosai,da mamaki ya kalleni,cikin kuka nace bani takadda ta,wannan gidan naku bakin gida du ba na gari a ciki sai Daddy kawai gaba daya bakin Uwa ne a gidan banda Daddy,dariya ce ta kamashi ya dinga yi ni kuwa ina ta jin haushinsa,yace to kwanta gobe Insha'allah zan baki komai da kike so har sabon gida sai ku koma can da zama sannan na baki takarda abinda kike bukata yanzu,k karki damu kwantar da hankalinki indai wannan ne baki da damuwa,tunowa nayi da maganar Daddy cewar duk Wanda ke son rabuwa ba

Please Login or Register in order to submit comment