Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuci me dadi,murna suka dinga yi suna tsallen murna tare da godiya,Nace kuje mana Gashi karbi Meenat kece babba kuyo mana Cefane muyi miyar egusi da tuwon shinkafa ki taho da nama na dari Uku muma muci dadi ko Ammah? Murmushin farin ciki Ammah ta saki tare da kallona tace Allah ya muku albarka dai yaran nan,

bayan sun tafi na gama siyar da kosai na ya kare kaf ,ina ta faman murna na lallaba jikina na gyara gidan fes na tattaro kayanmu har na Ammah da kannena na wanke su fes na shanya,Ammah wacce ta rarrafo ta zauna saman tabarma tace Mufeeda me za a dafawa yan makarantar ne yau? Na gaji taliya zan dafa da mai da yaji kafin dare sai muyi tuwon,eh hakan ma yayi ai tunda muna samun na sawa a bakin Salati ba kamar lokacin baya ba,tashi ki kokarta ki gama ke ma ki kwanta ki huta idan sun dawo yau ba Islamiyya sai suyi girkin daren,amsawa nayi da to na mike nayi abinda ta Umarceni,na hada mata ruwa na kamata har Nayi tayi wanka fes na koma na riko ta muka dawo naa tayata shiryawa tsaf muna hira.

ina gamawa na hada yaji me dadi yasha hadi na soya manja,na gyar dan kitchen dinmu wanda yake na karfen langa langa ne,Ammah na zubawa na kawo mata tare da ruwa,taimaka mata nayi ta zauna nima nasa hannu muka ci muka koshi muna Bada dunkulen Maggi star,Sallah muka gabatar ta Azahar,sai ko mukaji Sallamar Yan makaranta su Meenat,da gudu suka shigo suna sallama suka rungumeni,Ido na waro mene hakan? Sis wlh wani ne yace yana son Ma'eeshah mu kuwa muka zabgo da gudu,ke kin ganshi wlh in banda wari ba abinda yakeyi wai yanzu Ammah duniya ta lalace me kudi bazai Hulda da talaka ba komai kyanka indai ku talakawa ne babu me kulaka sai talaka dan uwanka,Ammah tace ai duniya haka ta koma idan da gate a gidanku to me mota ne zaizo idan babu kuwa sai dai dan uwanka talaka,Yanzu kalli irin kyawu da Allah ya zuba muku Amma babu me zuwa wajenku talakan ma ya gagara sabo da talakan ma gudun talakawa yake Allah kayi mana magani,dan baki na na turo Ammah ke komai kice aure wai shekarunmu nawa,dan gidanku gata nake nema muku yanzu ko idan da kunyi aure ai kuna da yancinku ko ba komai sai kiga kun huta shine burina,Ammah wa zai kula dake to aini aure bai taso ba a wajena Ammah wlh Bazan iya aure na barki a haka ba ko da kuwa zan dawwama ba aure ne a duniya,ki daina zancensa indai kina so hankalina ya kwanta,Maeeshah tace Sis manya bari muyi girkinmu,harararsu nayi nace kuje dai ku cire Uniform kuci abinci kuyi sallah ku huta sai kuzo ku fara aikin,ni yanzu kun san kasuwa zanje siyo kayan da nake siyarwa citta,kaninfari,barkono,wake,kanwa,Sabulu,omo,maggi kala kala,har su Aya duk siyarwa nakeyi duk wasu kana nan Abu na amfaninmu kayan girki ina siyarwa a gidanmu,haka ina saida su Aya,ridi,kantu,alewar Madara,albishir etc su Ma'eeshah nake sarowa suna Tafiya min dasu makaranta su siyar min,ina kosai na siyarwa,da rana na siyar da su Zobo kunun zaki da dare kuma nayi Awara,ina kitso da zanen lalle sosai kudi idan sunzo zanyi na karbi kudina,sannan ina cikin masu polio rigakafi,duk wani neman kudi na Sana'a kanana na gida ina yi,kusan komai ma siyarwa nakeyi,kullum bani da lokaci bana zama sam sai neman kudi dashi muke ci muke sha,muke Sutura tare da makaranta,

biyawa Ammah kudin magani,yanzu kasuwanci a duniya shine buri na wanda har ya kai ga dasa min matsiyaci son kudi tare da tattali,iya lissafi da planning,sabo da yawan Hulda da mutane yasa na kara gogewa na waye sosai,akan kudi ba mutunci ko bashi ya shiga tsakanina da mutum akan dan Kasuwanci na to fa zan iya rufe ido dole a bani ma,kamar zanyi sata haka nake matukar neman kudi.

Yau Monday Su Meenat suna schl na gama komai na fita naje wajen saro kayan Yara na sha,ina siyowa kala kala har su tuwon madara na wuce schl na kaiwa su Ma'eeshah domin su siyar,ina zuwa na hango Malam ya sa Ma'eeshah kamun kunne ya hanata ko shiga aji wai sun makara.




Ina matukar Jaje gareku fans da raguwar shekaru da muka samu domin ba karuwa shekarunmu suka yi ba raguwar suka yi,ana ta happy new year a daina addua ya dace muyi Allah yasa mun shigeta a Sa'a tazo lfy ta wuce lfy,Allah yasa ta Zama shekara me amfani a Rayuwar mu,ta zame mana farin ciki da samun ci gaba a cikinta,Allah ka kara mana lfy da Nisan kwana me amfani,Allah ka kara mana imani,Allah yasa muyi karshe me kyau idan tamu tazo,Allah ya azurtamu da mutuwar shahada,Allah ya rufa mana asiri duniya da lahira Ameen.





AsmaBaffa
[1/1, 10:20 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA








2-5






Official





By
AsmaBaffa











Wannan page naki ne HUMAIRA Allah ya bar kauna.











Wajen malamin naje da kyar na rokeshi ya kyaleta yace tayi Sauri ta karbi sakon ta shiga aji, nima ina mikata mata na kama hanya sai gida,washe gari kuwa da sassafe na shirya na barwa su Ma'eeshah suyar kosai da Komai nayi shirin Tafiya rigakafin Polio dama indai ina rigakafin nan to dole Meenat ce zata zauna tayi dukkan abin da nake siyarwa har na gama Polio sannan taci gaba da zuwa,Sabo da Ammah bata yarda da talla ba shi yasa Sam bama fita talla a gida muke sana'armu, Ma'eesha kadai ke zuwa yanzu kafin na gama Vaccine.

Inda muke haduwa da ma'aikatan unguwar da mukeyi naje na samesu cikin Napep na sauka cike da fara'a da murna muka gaisa da juna,sannan na dauki akwatin da kwalaben Allurar suke ciki ga kuma supervisor dinmu da sauransu,sabo da box carrier ce ni ba a biyanmu da yawa dubu hudu da dari biyar muke dauka idan an gama,bani da ilmin da za bani Babban matsayi,haka mune da wahala mune muke daukan kudi kadan,a kafa muke Tafiya muna shiga gidaje ana house marking,sai 2pm muka tashi,washe gari ma bangaren unguwan da mukaje daban,a kwana na Uku kuwa da muka fara GRA din nan da na taba ganin Saurayi Aayan ya zaneni yau gidajensu zamu shiga aikin Vaccine duk da cewar ban taba shiga gidan ba,amma bana fatan shigarsa,ina ji ina gani muka zo jikin gate dinsu,

takadda aka rubuta sannan akayi knocking,Sojoji sunfi biyar ne suka fito kamar zasu masgemu,sai da aka basu takardar cewar yan Polio ne suka zo ga me unguwa a tsaye kuma dole sai an digawa yaro dan kasa da 5years,takardar suka karba sannan suka koma ciki zasu nunawa me gidansu,tunda suka shiga muna tsaye a wajen gate har sai da suka kwashe fin hour guda sannan suka fito sukace ance mu shiga,ma'aikatan sai murna suke zasu gano haduwar gidan,ni kam cikina ya duri ruwa bana fatan shiga Amma ba yanda zanyi haka na fara binsu kamar kwai ya fashe min a ciki sanye nake da red hijab dina me hannu har kasa duk da cewa nayi kyau Amma sam na raina kaina,

Muna shiga muka firgita domin ma'aikata da Securities ne ko ina,gidan ko ina kamshi ke ratsowa yana sheki,ga wasu motoci sunfi ashirin a gidan lafiyayyu,har round ne a gida kamar wani Babban titi tsakiyar youturn din ruwa ke tsiri sama yana shararowa a kasa kuma yana komawa kasan yana fesowa,a film ake ganin irin wannan gida jen,can gefe ga wasu sweeming pool har kala biyu,ko ina flowers ne a gidan,duniya guda ce a gidan domin wani part din ma ya dace ka hau mota sannan ka Isa in kuwa ba haka ba zaka gaji,wani soja ke mana jagora muna binsa a baya har muka zo wani garden ba abinda babu a garden din nan domin har da filin ball da Sauran wasanni iri iri,kida ne na wakokin Naija ke tashi har tsakiyar kai a manyan speakers,yan mata su Uku kyawawa yan gayu ne sanye cikin English wears Wando short da yar vest suna ta faman taka rawa ,hannunsu rike da kantama kantaman wayoyi,gefe wasu Yara ne sunkai su hudu mace daya da Maza su Uku sun sha kyau cikin kana nan kaya yan yayi suna ta faman buga ball, abin mamaki ko kallon inda muke basuyi ba kamar ma basu san mutane sun wuce ba, haka muka ci gaba da Tafiya muna yin gaba kadan sai ga wasu Maza zaratan samari suma hadaddun gaske baza su wuce 29 yrs ba su uku suna zaune a wasu kujeru masu malafa a sama game kawai suke bugawa suna dariya,ko wanne yasha kyau cikin kana nan kaya kamar a England,kaina nidai yana kasa Amma suma samarin inda muke ma basu kalla ba balle musa rai za a kula mu,tafiya dai muke muna bin Soja can wani wawakeken fili ne fetal yasha tsari da haduwa carpet dan gaske ne a kasan wajen da wasu manyan pillows ko ina yasha flowers ga wasu grass carpet wata mashahuriyar Dattijuwa tsohuwa tukuf muka hango kwance tayi kwanciyar Isa kamar sarauniya fatarta lumis fara kar duk da cewa ta tsufa Amma akwai hutu kayan marmari sun ratsata.

Mu matan da muka shigo dama mu Uku ne,da hannu tayiwa Soja Umarni nan muka ga yace gasu nan yayi gaba abinsa,har kasa na durkusa na gaisheta cike da girmamawa,su kuwa sauran matan cewa sukayi ai ma'aikata ne wlh baza su durkusa ba duk wulakanci da akayi musu ba wanda ya musu ko sannu bare kallon arziki,gata ita wannan ta tsufa ma Amma bata saduda da duniya ba har wani jin dadi take.

Kallonmu tayi tsohuwar ko amsa gaisuwata bata yi ba tana yatsina fuska tana kebe baki tare nuna Isa ta fara magana kuje dan Allah kun tsaya min a kai wari yana hawa min kai,da mamaki muke kallon ikon Allah,can ta jawo waya ta danna kira tana jan tsaki,sai ga wata da Alama yar aiki ce harda Uniform dinta dauke ta fito da ruwan roba tare da wani liquid soap me kamshi tace kuzo muje ku wanke hannunku sai a diga musu polio,Tsohuwar nan cike da izza tace wlh badan Hukuma da suke hadawa da ita ba baza a digawa jikokina ba sam,kazanta abinda ana kaisu asibiti ayi musu me kyau ko kasar wajene ma sai suje a diga musu Amma a dinga turo mana kazamai gidaje jasu can kuje,ina jin haka na daga kaina ina kallon sararin samaniya tare da kallon tsayi da girman building din nasu kamar baza a mutu ba katanga ma tayi tsiri sararin samaniya kai kace Mala'ikan daukan rai bazai iya tsallakawa ba,a raina nace to yaje har fadar shugaban kasa ma ya dauke Yar Adua,yau Ina sani Abacha?

Ina wannan tunani sai ga wasu dattijan Maza farare suma su Uku sun fito harda Abbi wanda na taba gani zama sukayi kusa da tsohuwar suna magana,lokacin mu kuma an jamu part din yan aiki nan aka dinga dirje mana hannu sannan suka fito damu, wajen yaran dake Garden tare da yan matan nan masu rawa da Wando 3qtr muka koma,nan fa da kyar aka jawo mana yaran ana cewa Hajja ce tace ayi musu suka bude bakin su tas dasu cikin taka tsantsan na diga musu yanda akeyi sannan nace to Alhmdllh mun gama mun gode,me rubutu ta cike talley sheet din,muna jiranta tana rubutu yan matan nan dake rawa dauke da cup a hannu suna shan lemo suna rawa suna bige mu Amma ko kallon mu basayi bare mu Sa ran ko Sorry zasu ce,gefe dasu muka matsa,wata ce ta fito cikin shiga ta alfarma zata kai 40years da Alama da yaranta a ciki domin munga suna daga mata hannu bye Mum,tayi murmushi Tare da shigewa mota Driver ya jata ta daura kafa daya kan daya tana karanta Jarida,Numfashi ne ya kusa daukewa sakamakon wasu motoci da suka keto cikin gidan a kalla sun kai guda biyar suka Parker zunzurutun Securities ne suka fito tare da zagaye motar kamar wani Shugaban kasa ne zai fito,bude motar sukayi muna tsaye muna shan kallo Wani arnen takalmi ya zuro waje nan take kamshinsa ya cika gidan me dadi,ya dan jima a haka kafin daga bisani ya fito cike da takama kamar wani Sarki,cikin kana nan kaya yake yau ma farin Wando pencil sosai rigarsa Silver color da Golden rubutu,takalminsa Silver yasha masifar kyau,duk wanda ya ganshi zai rantse ba mutum bane Sabo tsabar baiwar sura da kyau,ga iya daukan wanka yanda yake matukar kyau,yan matan nan ne muka ji sunce Hi Ya Aayan,ko kallonsu baiyi ba sai ma wani kallon Banza da muka ga ya watso musu kamar yaga kashi,sabo da nima gwanar mugunta ce a raina nace Allah ya kara shegu ga ubanku a girman kai gwara haka,

Matar da muke aiki da ita wato Salima itace ta kalli yan matan tayi dariya wai irin ta tura musu haushi,ai kuwa ba zato muka ji karar Mari a fuskata domin suna rawa tunaninsu nice na musu dariya shine daya a ciki kawai ta daukeni da shegen mari wanda ya jawo hankalin wannan Saurayin da Sauran Ma'aikata kaina,Kuka na fashe dashi a wajen nan take na fadi a wajen na dinga shure shure,wanda muke Polio ne suke bani baki kan nayi shuru mu tafi,cikin kuka nace Wlh sai na rama mikewa nayi a hasale na cakumo daya a Cikin yan matan wanda ban san wace ta mareni ciki ba nidai na kama daya tare da makalkaleta na cisgo gashinta na murde na ja da karfi,sannan na dalla mata mari har biyu na sake ta na zura da gudu domin sunyo kaina da kwaben lemon me tsada da suke sha zasu fasa min a kai,daya ciki ta jawo Hijab dina ta baya,Securities sun taho Saurayin nan ya dakatar dasu cewar a kyalesu,suna kallo sun rike min Hijab na sunkuya tare da zare Hijab dina na bar musu a hannunsu na Arce jikin gate ina rokon a bude min,Saurayin nan yace kar wanda ya bude min,Har yan matan nan suka zo kaina na kara runtumawa da uban gudu amma saida suka kamani suka rufarmin suka dakeni sosai naji jiki sai da suka gaji dan kansu sannan suka tafi ina yashe a kasa,sai Hawaye nakeyi abokan aikina suka dagani da kyar sannan naga wannan Saurayin yace a bude mana mu bace a ganinsa ya tsani mata ko da yan uwansa ne baya kaunar ganinsu,sai da na tabbatar an bude mana nasa kafa ta daya ciki daya waje sannan nace kai yan mata?duk kuwa suka juyo suna kallona nace Allah ya Isa kuma sai na rama watarana idan kanwata ta zama Doctor ko Lauya,kallon banza suka min tare da tabe baki,nace zaku gani wlh kyaleki nayi dan ba a kan KASUWANCI NA kuka tabo ni ba,rigimar ba akan kudi bace Amma da akan kudi ne ai da sai daí a mutu a gidan nan shegu,tsinannu tambadaddu,arna,jahilai,dabbobi kuma dukkan yan gidan nan na zaga na nuna Saurayin nan dake tsaye nace harda kai da wannan tsohuwar dake zaune a carpet a sanar mata dazagina da iyayenku baki daya,sannan kuma ina tunatar muku Mala'ikan mutuwa na nan zuwa watarana,sojoji ne suka yo kaina na Arce da uban gudu tare da cewa Allah ya isa dana gaishe da tsohuwar nan kekakashashiya,na dinga zura uban gudu Allah yasa time din tashinmu yayi kawai na fada Napep ina haki sai gida tazarce kawai tun daga Cikin gidan nake gudu har nazo bakin titi na hau Napep,su kansu abokan aikin nawa dariya suke min da kyar wani cikin wanda ke jiranmu a waje ya karbi box din hannuna Sabo da uban gudun da nake kamar na fanfalaki.

Bayan na koma gida sallah na gabatar tare da fara harkar kasuwancina har Awara nayi ta dare bayan na siyar na gyara komai tare da irga kudin na cire ribar na zuba cikin asusun da nake tarawa Ammah kudin asibiti na magani tare da ware na gida da yan abubuwa,washe gari haka muka je wata unguwar mukayi polio abokan aikina su Salima sun sani gaba suna min dariyar abinda ya faru damu a gidan masu kudin jiya,sai dariya muke muna Bada labarin,Salima tace ammafa sun hadu da yawa a gidan kowa me kyau ga iya kwalliya musamman dan Iskan da yasa aka dakeni domin ni tunanina shine yasa a Zane ni tunda shi ya hana a bude min gate,Salima tace lalle Mufeeda ashe haka kike da rashin kunya idan an tabo ki,kina da Silent falava wlh,u like too much falava,murmushi nayi kawai domin bana jin wani turanci ni kam,karatun Hausa da Arabic kawai na iya Amma Ilmin turanci sai dai kalmomi dai dai domin bani dashi,h akan ma don ina dagewa ne su Meenat suna koya min amma da ba karamar dakikiya za ayi ba ni kam.

Yau cikin nishadi muka gama Polio na dawo gida da Sauri naci abinci na shirya sai kasuwa siyayya ina tsoron bi ta cikin GRA Kawai sai na hau Napep naje na dawo lfy, bayan mun gama suyar Awara mun siyar wanka muka kara yi tare da Sallar Isha,Su Meenat Assignment sukayi na schl tare da karatu nima na zauna suna koya min karatun turanci da rubutu haka Arabic ma duk da ina da Ilmi domin Uzu na ashirin cif haka wasu litattafan duk nayi wanda Kannena su Ma'eeshah sunyi Sauka tuni littafin da suka sani kam ko kafarsu ban kama ba danma ni gwanar jin wa'azi ce nasan duk wasu hukunce Hukunce na addini da dama Amma su suke koya min karatun,da badan haka ba da anyi kungurmar Jahila ni,

Part of speach suke koya min common adjective sun sha fama dani kafin na iya fada Sabo da ba laifi kwakwalwata da saukin ja tunda ni dai iyakacin Jss 2 makaranta ta gagareni Allah ma yasa Makarantar Arabic da boko mukeyi a hade shi yasa muke dana addini,su Meenat kuwa ai akwai Ilmi,shi yasa da munyi fada zasu ce to Sis me kika sani ma in ba neman kudi ba musamman Meenat uwar iyayi da son kwalliya domin duk wata kwalliya ta yan Zamani ta iya ta komai nata na harkar son gayu,Maeeshah ma haka suyi ta faman iyayi ni kuwa sai dai na siya musu kayan yi suyi ta zuba kwalliya ina kallo tunda har cosmetics na talakawa ina siya musu iri iri,kayan wanke gashi na talaka ni dai barni da jarabar tsafta amma ba ruwana da wata kwalliya gani nake bata lokaci ce kawai kudi nake nema dan mi tsira da mutuncinsu,
ni kullum sai daí na labta Hijab na fita neman kudi ba sauki wanda yanzu Unguwarmu sun samin suna Yar Kasuwa,sabo da bani da lokaci sai na neman kudi akan kudi ba daga kafa.

Duk inda naji wata Sana'a ko harkar samun kudi to fa yanzu zan cusa kaina ciki dole sai na samu domin mu samu na ci da sha tare da Sutura,ina da karancin wannan shekarun Amma na shaku da kudi,yanzu abinda ya dameni bai wuce kai Ammah Hospital ba domin dubu Sittin da biyar zamu je da ita za ayi mata wani aiki a Ciwon dake kugunta zuwa kafafunta shi yasa na gigice yaki Halak yaki Haram haka nake tara kudin,
Akan wannan yanzu kam na koyi ha'inci a Sana'a ta domin Awara da ina yinta me kyau da dadi Amma yanzu dan na samu riba da yawa na daina alkintata idan na tashi tacewa Bazan matse ruwan da yawa ba,kadan nake dan matsewa kana ci zaka ji ciki lumtsum da ruwa da mai,haka yajin na daina me dadi sai na gabza uban gishiri a ciki dan yayi yawa,haka ake siye Sabo da tsaftarmu Amma sun daina karba da yajinmu,haka kosai na ma da wata taba da ha'inci ya taso min sai na siyo garin kwaki tare da jar kala bayan na dauko markaden saina zuba garrin kwaki a Cikin markaden waken kosan nawa tare da jar color yayi wani jajir sannan kosan ya kumbura yayi sutu sutu dan na samu riba na samu kudi sai kiga ana ta siye Malam kosai yasha kayan miyar color gashi har wani Danko yake Sabo da yaji garrin kwaki ciki ba a sani ba ayi ta siye ina samun riba tunanina dai dai duk kuwa da cewar nasan ba kyau sai daí nayi Istngifari domin ko Ammah da kannena basu san tabar da nake aikatawa ba gara awarar gida idan zan soya musu daban nake tace ta tas tsam ba ruwa sai su zata ma wacce ake siya haka take.

Hattana Alewar madarata dasu kwakwimeti tare da kafi tsire in dai zanyi sai na san tabar dana yi a ciki Sabo da kawai na samu riba me yawa,gullisuwa idan zanyita sai na tankade garrin masarara me Laushi na kara a cikin Madarar Sabo da tayi yawa,haka ma Zobo na siyarwa sai na samu jar color na tafasa zobon kadan na narka uwar Color a ciki nayi hadinsa a ganshi kamar gaske ayi ta zuka ba a san rabi color ce kawai da ruwa ba,kuma bana sa sugar dan zaki wato sugarin nake dan yafa kadan sai kaji zaki cai.

Ina zaune kusa da Ammah ina tufke mata gashinta muna sauraren Radio kawai sai muka ji cewar Gomnati zata raba tallafi ga marasa karfi Naira dubu sha biyar biyar tare buhun shinkafa da taliya sugar da man gyada tare da waken Suya a ja jari,nan take na mike zumbur naji kudi,Ammah ta kalleni tace sarkin neman kudi dan Allah ki hutawa kanki zafin nema baya kawo samu haka duk kin damu kanki Allah yana rufa mana asiri dan Allah ki rage takurawa kanki ayi amfani da abinda ya samu,baki na turo Ammah kina gani kudin maganinki har yau basu hadu ba fa,to ta wacce hanya zaki bi ki samo mana tallafin? Ammah wajen counsilor din Unguwarmu Adamu zanje na nemi Alfarma ya nemo mana hanya,ai yana da kirki Amma fa kija mutuncinki duk da nasan irin tarbiyyar da nayi muku ki kiyaye Mufeedata sannan kinga girma ya fara kamaki idan kika bari Namiji ya rike miki ko yatsa shike nan kinyi ciki an gama,da Sauri na zaro ido waje a tsorace nace Ciki Ammah?ae ai indai Namiji ya rike maka ko farcene to shike nan ciki ya shiga,da tsoro na firfito da ido waje,nace Ammah su Meenat nake tsoro bari su dawo na fada musu gaskiya kar suje su yarda da Maza su rike musu hannu.

Su Meenat suna dawowa na taresu da Sauri tare da jansu dan Bedroom dinmu nace dan ubanku karku bari Namiji ya rike ko yatsanku,Meenat tace Sabo da me?ba kyau kuma Ammah tace ciki ake dauka,Dariya naga Meenat ta kyalkyale tare da cewa Allah ya bamu kudi Sis ki koma schl kema wlh ba haka bane ke baki da labarin abinda ake a aure ana samun ciki,ai Ammah wayo ta miki kar mu kula Maza mu lalace shi yasa ta fada haka Sabo da taga mun fara girma,shuru nayi ina Nazari Amma naki yarda da Meenat Sabo da nasan Ammah baza ta fada mana karya ba,kyalesu nayi kawai na fita abina naci gaba zuba kwakwimeti na à leda,bayan na gama na fara daura su citta dasu kanwa,kaninfari etc,kusan duk makwaftanmu a wajena suke siyen kayan miya,idan suka siya kawai sai su zauna a gidanmu suce bari su daka kayan miyar ko jajjage da sun shiga gida kawai sai daí su fara girki,sabo da son kudi na nace to daga yau na kafa doka cewar ko wacce idan zata yi daka a turmin gidanmu to sai ta bayar da Naira goma kudin turmi,ganin haka yasa Bazan basu tabarya ba sai an miko goma shike nan suka daina daka a gidanmu,Muna da wata Kura da yake gidan mu

Please Login or Register in order to submit comment