Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni kaina da nake labe ina jin hirarsu Allah haka yake ikonsa ka gama Shan wahalar duniya ba sai ya yanka ba wasu ma sai kaji dadinsu,suji kanka lallai ba a san wanda zaiji kanka ba a duniya ba sai lallai danka daka haifa ba.

Ammah duk wannan baya gabanta hankalinta yana kaina dana ki kulata,Haka har suka tafi tare dasu Meenat tayi wanka tare da shirin baccinta suma haka sai suka ci gaba da hirarsu suna ta bata labarina da abubuwan da suka faru bayan bata nan,da halayen yan gidan su Aayan etc da kyar Ammah ta iya bacci sabo da tuna nin naki saurarta na kasa yi mata Uzuri,kuma Danni tayi hakan dan rayuwata ta inganta amma na kasa Fahimtar me take nufi,Kuka nake tayi a daki ni an tozartani a gaban kowa ance ina da son kudi har Uwata tayi karyar mutuwa sabo dani, kuka nake sosai Aayan yana jikin kofar yayi yayi na fito mu kwanta naki yarda,shi kuma bazai iya bacci babu ni ba ya riga da ya saba,kukan nan nawa yana kona masa rai,tun yana rokona na fito mu kwanta har ya hakura yaje ya kwanta amma kasa bacci yayi gaba daya ya shiga damuwa sai tsaki da juye juye yakeyi ya rasa ya zaiyi ya iya bacci ba tare da ina jikinsa a kwance ba,Bai kara Sanin lallai Ashe yana sona kamar ransa ba sai yau,ko baiyi komai ba ace yana ganina a kusa dashi.

Cikin dare wurin 1am ya kara zuwa ya rokeni na bude masa ko bazan je wajensa ba naci gaba da bacci na ina jinsa,har ya gaji ya tafi,2am ya dawo wai dan Allah to na bude ya bani abinci naci tun rana banci komai ba, nan ma naki kulashi Sai ma baccina da nakeyi.
Haka ya kusan kwana a hanyar dakina da dakinsa sai da yayi sallar Asuba sannan bacci ya daukeshi cike da bacin rai.
Washe gari Har Ammah suka shiga kitchen suka shirya abinci ana ta Harka ba Aayan ba ni,shi yana baccin gajiya,ni kuma naki fitowa nayi wanka na da komai yunwa na kwakulata amma naki fitowa ko kadan,Sai haka suka hakura sukayi breakfast har Ameer, misalin 12pm Aayan ya Sha wanka direct dakin da nake ya nufo cike da hasala yace bude kofar nan ko na bude da kaina yanzu kafin na irga 3 tsoro da tausayinsa naji tun jiya yake abu daya na tabbata ko kansa bazai wa haka ba,ina fushi kamar zan fashe na turo baki na bude kofar, shigowa yayi da sauri ya rungumeni a jikinsa yana why? Babyna me yasa haka? Zaki kasa Fahimtar mu,idan laifi ne hakan kiyi hakuri baza a sake yi miki ba amma dan Allah ki Kula Ammah ko zata ji sanyi baki ga yanda ta damu ba sai zancenki take min kullum bata da burin da ya wuce Mufeedanta ranar nan ma fa da kika Dameni ko da budurwa nake waya nace miki watace yar Us Ammah ce fa kuma lafiyarki ta tambaya a lokacin,dan Allah kiyi hakuri ko abinci kici kalli duk har kin rame,ina jikinsa yana ta lallashina ina sheshekar kuka harda na shagwaba,yace ni Allah bazan je wajenta ba tunda tayi min haka ta tafi ta barmu Ashe tana raye kuma ka boye min bazan je wajenta ba,Ok to naji ya isa haka kukan Zauna bari na kawo miki abinci kici kinji mufeen Ammah? Nace Allah ni ba tata bace ka daina fada min,a raina mamaki nakeyi wai Aayan ke nuna min so haka,ashe yana sona haka ai har tsalle nayi da birgima a saman Bed sabo da murna Aayan na so na da yawa.
Ammah ya fara gaisarwa cike da girmamawa,su Meenat suka gaishe shi yana tsokanarsu sun samu Ammah sun manta da kowa,Ammah tace ina mutuniyar? Yace hmm da kyar ta yarda zata ci abinci sai yanzu ta bude kofar da kyar sai da na Sha fama tun jiya nake abu daya,Farin ciki Ammah tayi lallai Aayan yana son yarta sosai kuma yana kula da ita taga zahiri a jikin mu kuma su Meenat sun bata lbr,Abinci Meenat ta hada masa a tire ta abawa Aayan,Ammah tace nasan Halin abata akwai zuciya ka bita a hankali zata sameni ne,Aayan yace to ya nufo dakina, sai da yasha fama kafin ma naci abincin sai da kansa ya shiga bani a baki shima yana ci,da kyar nake karba,sai yace dan Allah ki hadiye pls sannan zan hadiye,idan ya takura min na fashe da kuka,bayan mun koshi nace to sai ya fitar min a daki,yace kai Sweetheart ki Bari ko hira muyi mana naji dadi kinga jiya ko bacci ban iya ba bakya kusa,nace ni ba ruwana ka tafi ko na barma dakin kawai,Haka ya hakura badan yaso ba ya fita,naji tausayinsa sai nace dawo to ka kwanta amma 2hrs kawai zaka tafi,ba musu ya dawo na nuna masa bed tare da cewa kwanta to zan tayaka baccin,Dadi ya lullubeshi nima haka sabo da nayi missing dinsa so nake naji duminsa,key na sawa kofar sannan na kwanta a gefensa ina kunkuni,jikinsa ya jawo ni yana aikin lallashina yana so ya danyi Romancing dina amma yasan bazan yarda ba fushi nake dasu gwara ya lallabani haka kan kace me bacci ya kwashe mu muna makale da juna dama baccin bai ishe mu ba,Ammah duk ta matsu ta bar gidan sabo da kunya take ji Zama gidan yarta jira take Yarima yazo a canja mata gida.
Ameer har sun saba da Ammah kamar ummansa haka yake ji da ita.

Kwanan Ammah uku a gidan nan ban kulata ba ko ganina bata kara yi ba tun zuwan farko,Aayan ma bana sakar masa fuska bana bari ma ya rabeni tun rannan da nace zan tayashi bacci ban kara bari ko yatsa ya rike min ba,ya shiga damuwa har ramewa yake yi,Ammah kuwa har da na sani takeyi da bata shirya hakan ba ta barni da halina,Yarima yace suyi hakuri zan sakko ne,Ammah tace tunda ta huta a kaita gidanta tare dasu Meenat gaba daya,Aayan yace ai shi bai yarda ba baza a dauke masa su Meenat ba,Ameer ma yace gaskiya basu yarda ba,Ammah da kyar ta lallabasu tare da ganar dasu har suka hakura,Aayan yace Mufee fa ai dole a tambayeta,Ammah tace kyaleta ba komai itama zata zo da kanta ne ta neme mu,Yarima suna zaune su Meenat murna kawai sukeyi da zumudi ko ta kaina basa bi suka tattara nasu ya nasu kaf suka shirge a mota,sannan Aayan ya rakasu wajena wai zasu bi Ammah su wani bakin ciki ya kara dirar min,mun saba da rayuwa tare da yan uwana kullum muna tare ina ganinsu ina jin dadi muna abubuwanmu sabo da tare dasu Meenat nazo gidan miji ban san zafin rabuwa da yan Uwa ba sai yanzu gashi mun kara shakuwa,tare muke kashewa mu rufe,su bani shawara na basu,su suke tayani ayyuka da komai ba ruwana da wasu masu aiki sai masu wanki da gyara Compound,nan take na kallesu kawai na fashe da kuka,suma suka rushe da kukan suna bani hakuri,nace Meenat kuma yanzu shike nan kun tafi ni kadai zaku bari?ai sai ku bari sai nan da kwanaki sai ku bi bayan Ammah amma ba komai kuje rayuwa ce, ita Ammah ai ta saba da zama ba mu,ta saba da rayuwa ita kadai shine yanzu daga zuwanta zaku manta dani Ku bi bayanta ko? Meenat tace gani mukayi idan mun barta baza taji dadi ita daya ba,ae Amma ni kuma fa kunyi tuna nin haka? Ita da tayi tafiyar muke tunanin bata raye fa mun hakura ma da ita shine zaku bita tun yanzu? Shike nan mun fasa Binta bari sanda kika yarda shike nan,Da sauri su Meenat suka fita suka sanarwa da Ammah,dariya tayi tace da gaskiyarta lallai Mufeeda na yarda ta Zama Babba ta kara hankali kuje Ku dawo da kayanku ni zan tafi Ku bata hakuri daga baya sai kuzo ku yini kwa dinga yi min.
Haka suka dawo da komai nasu inda yake,Ameer yafi kowa murna,Aayan ma yaji dadi da basu tafi ba sabo da yasan an bar baya da Kura shi zai sha wahala dani kafin na huce.
Ma'eesha ta dawo tace Ammah sun tafi da Yarima sis gamu mun dawo,Good for u nace kawai sannan na juya nayi kwanciyata.

Bayan sati daya da dawowar Ammah Yarima ne ke dawainiya da ita tare da Ameer su suka kaita danginta can kawai tare da Maiduguri duk sunyi murna tayi musu bajinta ta dawo katon gidan da Yarima ya siya mata na alfarma,ga yan aiki mata dattijai masu kwari har biyu,da me gadi namiji daya, gidan ba abinda babu na kayan alatu da ci da Sha.
Haka ta zauna a dan gidanta,Yarima ya kai Ma'eesha da Meenat sau biyu sun mata yini guda,ni kuwa ba ruwana fushi nake da kowa bana kula kowa sai Ameer,Haka Aayan ma kullum da sha'awarsa yake kwana yana tashi,bana kulashi babu yanda baiyi dani ba amma naki lallashi ba adadi,har Ameer yasa ya bani hakuri naki ji ,Yarima yace ba ruwansa sai dariya yakewa Aayan yanda duk ya fita daga hayyacinsa ya rame kullum tunani da damuwa yakeyi,har kasa jurewa yayi ya Sanarwa Daddy wai idan nazo gaisheshi ya bani hakuri ya lallaba ni,Daddy yace ba ruwansa ya kula da matarsa kowa haka yake hakuri.
Ni kaina tausayin Aayan nake ji sosai ganin halin damuwar da yake ciki,kuma shi yake kula da ganin naci na koshi,amma ba ruwana da shi kuma ba wai dan bana sonsa ba sai ma tausayinsa da nakeji.
Sati gudan da mukayi bana kula Aayan kullum gyaran jikina nakeyi tare da Shan tsumi na masu Inganci,ina gyara jikina wanda Maman Sayyah kawata ta koya min hadawa da kaina,maza irin su Aayan sai da gyara sosai kwai kwarzaba,nayi mamakin da naga yana iya daurewa amma nasan a wahala yake kawai na rashina,Meenat ma duk sun fahimci yanda yanzu bana kula Aayan yana cikin damuwa, zuwa wajena suka yi tare da min nasiha sosai ba laifi kuma ta shageni sun tunatar dani ina cikin fushin Allah da Mala'iku, bayan sun tafi na tafi Dakin Aayan amma baya nan,gyara dakin nayi sosai tare da toilet,haka gaba daya part din mu sai dana gyarashi Neat sannan na sauka kasa,Ameer dasu Meenat sai murna sukeyi da alama na daina fushin,da kaina na shirya girki na me shegen dadi,Pounded yam da egusi soup sai farfesun Kaji nayi tare da shirya lemuka kala biyu na gama komai na kwashi na Aayan a flasks na Alfarma na kai tare da shiryawa a bedroom dinsa, lemuka ne kawai na barsu a fridge sai ya dawo zan kai masa.

Ina yin Sallar Isha na shirya cikin kayan bacci na ala tsine ba abinda ba a gani a jikina sunmin kyau,ko ina kamshi nake fitarwa abina nasa Hijab kato da niyyar sauka kasa naci abinci tare dasu Meenat,ina fitowa Aayan kuma ya hauro saman muka ci karo,yana ta kallona ganin haka yasa na juya zan koma Bedroom da sauri,hijab dina ya jawo na dawo baya,ido muka hada ina shirin fara kuka yace me nayi miki wai kike min haka? Shuru nayi yace fine jeki Allah ya gani kuma yana kallonki yayi gaba abinsa ya barni a tsaye,fasa sauka nayi nabi bayansa zuwa Bedroom dinsa yana kallona yayi banza dani ya fada toilet tare da yin wanka ya fito ina kallo ya gama shirinsa ina zaune Saman Bed,na fita na kawo masa lemuka tare da Fruits salat na ajiye,ya kalla tare da cewa kwashe abincin bana ci ni alhalin yunwa yake ji, shuru nayi ban kwashe ba,tsawa ya buga min ba dake nake ba,sai da na tsorata matuka,zuwa yayi tare da hayewa Bed dinsa yace kwashe ki bar min room bana son ganinki pls,Karfa ko ya daina so na haka nake tunani,kuka na fara masa ba tare da nace masa komai ba, idan na tashi sai na ballaki a room din nan bana ra'ayinki fice min da gani, Kukana naci gaba da yi nace an cuceni ace bazan yi fushi ba,kuka boye min Ammah ta bata raye kuma shine aka zo ake ce min ina da son kudi a gaban kowa duk an rainani,bayan ni ba haka nake ba maimakon a lallasheshi shine za a balla ni,barin gidan ma zanyi gaba daya tunda haka ne.
Wanne hakuri ne ba a baki ba? Ya kike so ayi miki? Yarinya ce ke? ai dai na hakura har girki nayi ma kace wani baka ci kai,kuma ka tsaneni baka kaunata baka son ganina ai shike nan bari na tafi.

Shuru yayi a ransa yana me jin dadi wani Sanyi tare da Hamdala ga Allah,muryarsa naji yace zo ki zauna akwai maganar da zamuyi kuma in dai baki karba ba kawai na daina kulaki ba ruwana dake,a raina nima sai murna nake,cike da shagwaba na zauna a gefensa nace gani to ai ko ina turo masa dan lips dina me kyau da birgewa,kallona ya tsaya yi na gama birgeshi.






Wannan page na yan gps ne gaba daya sabo da wannan babban page ne babu wanda yayi zaton Ammah na raye abin mamaki,sai nan gaba za a kara Jin yanda akayi corner dasu Mufeeda ha Ammah ta barsu a zuwan ta mutu dole ba wannan ne kadai dalilin ba akwai wani.


Tnx fans! ayi hakuri da typing errors.










AsmaBaffa
[2/3, 8:36 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA








109-110









Official







By
AsmaBaffa









MAMAN 2 KIDS and MOM INTEESAR wannan page nakU ne sabo da jajircewarki a Sharhi.

HUMAIRA sarkin Sharhi ina gaisuwa me tarin yawa.


AUTA ina kika boye tare da ASYCOOL shuru Allah yasa lfy.

Manya manya maganin kanana Jinjina nake muku
FLOWER
MARCYCOOL
ZAINAB ATIKU SALAMA
SAMEERAN GAYA
HAFSAT KHAIRAN
MAMAN MEENAT
MOM SUHAIL
MRS HAMZA
MRS UMAR
MRA FAROUQ
JANNAT
MAMAN WALEEDA
QUEEN MERMU.







Ido ya lumshe tare da budesu tar a kaina,kallonsa nakeyi cike da so tare da kewa shima hakan,wani kallon so muke aikawa da juna dadi na ratsa mu, magana ya fara yi min cikin nutsuwa,Mufeeda ya furta cikin muryar tausayi da lallashi,Kallonsa nayi sunan da ya furta har kwakwalwata haka naji kamar wata na'ura ce ta ambaci sunan haka nake jin dadinsa.
Magana yaci gaba da cewa tunanina kinyi hankali Ashe ba haka bane,an miki bayani sai ki fassara abu bai bai,kin kasa Fahimtar me ake nufi,yanzu abinda kikayi kin kyautawa Ammah kenan,mahaifiyarki guda,ta miki komai a rayuwa ance ta rasu kin damu kina kewarta ance bata rasu ba ta dawo akwai dalilin da yasa ta shirya hakan,ba wacce take so sama dake,bata da magana sai Mufeedanta,tazo har gidan mijinki da kike aure amma kika ki Kula ta ko kallo bata isheki ba,mutumin da yayiwa Mahaifiyarsa haka waye bazai masa ba,iyaye fa basa laifi wurin yaransu,Meenat su fiki hankali,mahaifiya guda kika ki kulawa,kika wulakanta,tana can da bacin ranki Allah ma na fushi dake,sannan ni ban miki komai ba ina mijinki kalli abinda kika dinga yi min kan abu kalilan kin bani kunya,yanzu gobe zamu je ki bawa Ammah hakuri ki shirya idan kin yarda idan baki yarda ba to,Da sauri nace ni bazan je ba na daina kulata tunda tayi min haka, cike da bacin rai yace to tashi kije nima ba ruwana dake.

Kin tashi nayi tare da yin shuru sai da aka kwashe 15mnt sannan ina kunkuni nace to shike nan ai zanje amma Allah bazan gaishe ta ba tunda tace ina da son Kudi,Hararar wasa ya jefo min yasan na hakura ma tunda na yarda zanje,abincin fa baza Kaci ba? Kince baza ki gaisar da Ammah ba ta ya zan ci abincinki,baki na turo ai dai nace idan Naje kawai zance Sannu da zuwa Ammah amma Allah bazan gaisheta ba,to ruwa kawai zan sha nima,kai dan Allah Nafa sha wahala wurin girkin nan na bata lokaci nayi maka da kaina,baka ji dadinsa ba pls Kaci ko kadan ne? Bazan ci girkin wacce bata gaida Mum dinta ba,da ace kina gaisheta sai naci,shuru nayi sai da naga lallai bazai ci ba nace to zance mata Sannu Ammah ni dai bazan ce ina yini ko ina kwana ba Allah sai in kar Kaci abincin kuma ai nayi kokari ma.
Shi kanshi yasan ma na huce gaba daya sai yace to zanci badan halinki ba,ina murna na cire Hijab dina na ajiye gefe,ya kalleni sama da kasa yaga kayan Harka iya kaya,Nayi kyau ga kayan baccin matsiyata dasu komai ana gani, ina sane nake kara girgiza jikina ko ina rawa yakeyi na zuba masa komai kawai na dauki Hijab dina zan mayar jikina yace noooo pls ki barshi haka zo ki tsaya a gabana,haka ya tsayar dani kamar wata soja yana cin abinci yana kallona na kasa tsayawa waje daya sabo da na tafi da Imaninsa ina sani nake girgiza jikina wai irin na gaji da tsaiwa sai kukan shagwaba nake masa ina dire diren kafafu shi kuwa karfin Hali kawai yake yi tuni hankalinsa baya jikinsa idonsa ya canja da kyar ma yake kokarin cin abincin hankalinsa yana kaina.

Bai ma gama ci ba naga yace kwashe na koshi,na kwashe komai na mayar kitchen sannan na koma dakina na kwanta a bed tare da yin dai dai wai irin Jan aji nasan dole zai biyo ni,Brush da shiri ya sake ya fito yaga bana Bedroom din,Wayata ya kira yaga ban daga ba,ya kara kira shuru ina kallo kuma,Da kansa ya Mike ya nufi inda yasan zai ganni,hango ni yayi na baje ina baccin karya amma tunaninsa baccin gaske ne,wani juyi nayi me Jan hankali,light ya kashe tare da haurowa Saman Bed din,yanda naga yana abu a rude shi ya bani dariya har na kasa rikewa na saki abata,cakulkuli ya fara min muna dariya yace dama kina kallona ko? Nace Oya let's go,ai Bazan iya matsawa nan da can ba kawai mu kwanta a nan, yau ban bari ya fara min komai ba,ni na fara Sabo da nayi Missing din mijina da yawa,kamar zan cinye masa lips tare da tongue haka nake tsotsesu da zafi zafi, dadi ya gama rufe shi kawai wani nishi mukeyi,Bana iya cewa komai sai dai nace Miss u Baby,Shima haka can kasa naji yace yau Dan Ficici za a bani,Lokacin ina jin dadina ya min yawa bana hayyacina nace a'a yau kamfatowa zakayi,yace Allah? Nace ai Kwaso kawai, yace an gama,ba karya kuwa ya kamfanta dan yau nafi ko yaushe jin jiki a hannunsa,ba karamar wahala nasha ba,tun ina kuka dadi sai da na koma na wahala,sabo da ban wani saba ba,kadan na saba Bazan iya dauke yanda yake so ba ba tare da na dan sha wahala ba yanzu sai nan gaba,har yau sabon nawa ba wani me yawa bane sai kuri idan anzo kuma na fara kuka ido ya raina fata,shi kanshi Aayan ya san iya limit din da nake kaiwa ban gajiba,shine yake so dole na saba sai yazo wanda lokacin na gaji sai ya dinga Dragging dina,Kuma ko yaushe yana ganin ci gaba tunda kullum ina kara samun ci gaba.

Sai da ya samu nutsuwa muka yi wanka na gasa kaina sosai mun kwanta again yana Sa min Albarka yana jin dadi yace lallai yan matana yanzu ana ta girma kullum, tnx alot My Queen,jikinsa na shige nace ni ba wani sabawa karka kala min ina yar yarinyata.dariya yayi tare da kara kankameni yana shafa min gashina zuwa gadon baya na yace muyi bacci sai gobe kuma zanga wanne salon za a nuna min naji na yau ya hadu kin ba da style,dukan wasa na masa ina jin kunya na kara boye fuskata a kirjinsa ina dariya kasa kasa,wata Kalma na rada masa a kunne wacce saura kadan ayi second round da kyar na lallasheshi yace to ki daina kunna ni,nace kyis na kasheka to,Dariya mukayi gaba daya hannayensa suna saman Mazaunai na yana shafasu cikin Salo iri iri wanda ni kaina hakan yana min dadi.

Abbi ne kwance saman gadonsa yana nazarin duniya tare da mamakin canjawar komai da ya samesu a rayuwa,gashi har sun lalace suna ramewa sunyi duhu sosai kamar basu ba,dama ance duk wanda ya saba da rike kudi yana shan wahala idan karayar arziki ta sameshi,kuma dama can taimakon su akayi talakawane gaba da baya, duk gashi har sun zama abin tausayi duniya ta juya musu baya,wai sune a wannan matsayi, Hajja ce ta shigo dakin Abbi tana fada mene amfanin kwanciyarka a gida da tsakar rana haka baza ku fita neman na kanku ba,kudin hannuna sun kare saura Naira dari kamata yayi ko yar dubu biyu ina rikewa a hannuna ni bana iya rayuwa ba kudi,Abbi shuru yayi bai ce mata komai ba Sabo da bakin ciki da me zasu ji, Hajja tace au dan Iskanci kana jina ina magana kamar kaga Kashi eyee,ni na daura muku talaucin idan kudin banza ne me yasa baku yi zuciya kunyi ba, Haba Hajja me nace miki kuma,ya kike so muyi kina gani karatun su Sabeer ma nema yake ya tsaya,ba komai bamu da komai sai bashi ma da muke ci ki dinga tausayinmu mana,idan ba sata kike so muyi ba me zamuyi miki? Hajja Hawaye ta share wai an ci mata mutunci,ta fice fuuuu ta bar Abbi yana bakin ciki.
Haneefa ce ta fito ta cikin yan uwanta Maza da mata tace to Jama'a ku kalli atamfar jikina ta gaji da wanki har ta kode tana neman jemewa,dama kayan namu kadan muka ebo,Meenal ce ta fado da gudu tace Bazan ji kunya ba bayin Allah nasan masu hankali ne gaba daya dan Allah me Pad always ta san min ko a min karo karo na kudi na siyo,Sajeeda tace ai duk dan kwalayen Ka kayana sun kare a kunzugu rannan,sai dai kiyi amfani da dankwali, Mujaheed da Khaleel suna dariya suka ce kadan kuka gani Yara tun yaushe muke cewa kuyi aure tun da gatanku samari na rubibinku kuka ki gashi na pad ma ya gagareku.

Meenal ta kalli Khaleel tace dan Allah bani gajeren wandon nan naka da naji zaka jefar naga cotton ne sosai zai sha ruwa a jikinsa,Khaleel yace ko kunya bakwa ji wai a gabanmu kuke irin wannan kalamai ba tarbiya ba komai sai kije yana cikin bakar jakar nan ki dauka,Meenal da Sauri taje ta dauki gajeren wandon Khaleel wani me nauyi cotton tasa reza tare da yankashi kashi Kashi ta linka kamar dai Pad haka ta dinga sawa tana kunzugu dashi.

Matayen su Abbi talauci ne ya ishesu gaba daya suka ga gwara su tafi gida tunda yanzu ko sabulun wanka da wanki Rasawa akeyi a gidan,Nan suka tayar da rigima sai an sakesu,Umman Ameer tace ita dama tana jin Haushi an rabata da Danta Ameer ta gaji,Hajja tace ba shegiyar da za a saki kamar yanda akaci daula dasu dole Asha wahala dasu dama in sun koma dangin nasu ma dai talaucin zasu tarar Sabo da duk kanwar ja ce.

Yaji sukayi wai sun tafi gida sai sun huta zasu dawo,Yaran gida suka ce sama dawo idan sunji Wahala kar wanda ya hanasu,suna shiryawa suka ce mu munyi gaba,Su Mujaheed suka ce a dawo lfy Allah ya kiyaye Hanya,tuna ninsu yaran zasu damu sai suka ga kowa harkar gabansa yake,Sabeer yace mu ai Aayan da Daddy kadai ne zasu ce zasu yi yaji zuwa turai mu damu Amma kawai ba abinda ake tsinana mana ace za a damemu,common toothpaste mu muke siya,sabulun wanka da wanki ba a san a bamu ba,Abbi yace Kai rufe mana baki marasa kunya,Sajeeda tace ai wlh sai daí a godewa Allah Amma ya dace ace a cikinmu akwai Karuwai,akwai yan shaye shaye tare da kasurguman barayi sabo da Halin da muke ciki a gidan nan,kowa kansa ya sani kowa ta kansa yakeyi,Hajja tace ai duniya ce

Please Login or Register in order to submit comment