Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asibiti kuma Bai dace ace anyi aure ba wasu shedu ba babu Sanin mutane ai babu dadi a ganina bai dace ba,shi yasa nace dole Muzo sharp sharp su gani su San inda muke da zama duk da cewa dangin Aayan sun min kallon wulakanci ganin inda muke da zama har dariya suka yi masa dama sun San ai sai talaka ce zata iya aurensa.

Ni dai ko a jikina tunda kudi zan samu gani nake kudi sune maganin komai,sai gashi tun ba aje ko ina ba an saukar min da Aya,Meenat ce ta jani gefe tace Sis ya naji ana ce miki Amarya?ki Bari baki su tafi zan sanar daku komai,da gaske kinyi aure? No ki Bari idan mun nutsu zaki ji.Bayan anyi sadakar Bakwai muna zaune Dangin Ammah suka samu a tsakiya cewar zasu dauki Meenat da Ma'eesha su tafi dasu kauye ni kuma tunda nayi aure na zauna dakin mijina duk da cewa abin ya daure musu kai rashin ganin angon nawa a wajen janaizar Ammah,amma sai nace dasu baya kasar yayi tafiya kasar waje,cikin ladabi nace Ni bance karku tafi dasu ba dama Ku ya dace Ku rike mu,amma sabo da karatunsu kuma kauye ba schl baya ga haka basu saba da rayuwa acan ba,kuma nima zan shiga damuwa na rashinsu ga rashin Ammah me zai hana a bar min su mijina zai rike su ba matsala zai musu komai sai mu zauna tare,Dangin Ammah dama kadan suke jira nan suka fara masifa to ai gaki gasu in dai rikon dadi gareshi,sannu yan Birni Ku yan boko ko to dama dan mu fita hakkinku mukace zamu tafi daku amma tunda haka kuka Zaba shike nan, a cikin matan ma daya tace a'a haba a bisu a hankali ai yara ne ga rashin Uwa sunyi amma har ita Mufeeda kanta nawa take kuruciya ce kawai,nayi mamaki a birni guda amma kamar Mufeeda wai Fatima ta yarda tayi aure tana yar Sha bakwai a shekaru,duba fa yan Birni da sai su kai shekara talatin yarinya na yawo a titi wai karatu take.
Daya cikin maza kanin Ammah yace to Alhmdllh ai mijinta me kudi ne da alama zai iya rikesu da Amana na tabbata amma ya dace ace munje munga gidan mijin naki,gumi ne ya keto min nan take na rude.

Karya na kakalo nace ai ba yanzu zan tare ba,dazu munyi waya dashi jibi zai dawo daga turai sannan zasu sa ranar da zan tare sai na fada muku a waya ko nazo har gida na kawo kati sai kuzo ayi komai da Ku,ganin mijin nawa me kudi ne tunda sun ganshi tare da danginsa ba karya gashi sunsha kyautar kudi kawai sai suka washe baki tare da cewa to Allah ya kaimu ki tabbatar kin yo mana waya,da sauri nace Insha'allah,to yanzu abinci fa da sauransu wa zai baku kuma Bai dace Ku zauna Ku kadai ba a wannan gidan ba,nace ai masu gadi zai kawo mana yace suna kan hanya ma sojoji ne,da mamaki sukace lallai kunyi dacen me kudi ke ko yar nan kin huta a duniya dan Allah a dinga tunawa damu dangi kar a samu a manta damu,nace haba dai ai daku za a ci komai,nan dai suka yi ta kauyancinsu na Fulani daga nan suka tattara gaba daya suka mana Sallama zasu tafi,har kudin mota na basu muka rakasu har tasha sabo da bamu saba dasu ba ko kuka bamuyi ba sabo da sun ishemu dama sai bata mana gida sukeyi suna samu aiki.
Suna tafiya mu Ukun muka tsaya a wani gidan yan haya,gidan haya ne Babba,daki daki ake bada hayar kowa da dakinsa sunfi mutum ashirin a gidan kuma toilet daya garesu,Meenat tace me zamu yi a nan? Ko magana banyi ba nace suzo muje,muna shiga muka gaisa dasu suna ta mana ta'aziyya,dakin wata Dattijuwa Uwaliya na shiga tana zaune gefe tana Shan kunu,Uwaliya bata taba haihuwa a duniya ba,danginta duk suna kauye sana'ar aikatau wanke wanke da shara ce ta kawota birni,bata yi dacen gidan da take aiki ba kuma bata son zaman kauye sabo da babu sana'ar kirki a can,sai ta kama hayar daki a birni tana zuwa gidan aikin haka da safe ta dawo da yamma kullum,da fara'a ta tarbeni muna gaisawa nace Uwaliya idan baza ki damu ba ki dawo gidanmu da zama mana kyauta na baki daki daya mu kuma sai mu dauki daki biyun,dama gidanmu daki Uku ne sai dan kitchen da toilet ammafa bashi da wani kyau gidan gidane na talaka amma nasan yafi wanda Uwaliya ke haya a ciki,da murna Uwaliya ta dinga godiya,haka mutane suka tayata murnar daina biyan kudin haya zata zauna kyauta a gidanmu,wasu suka dinga mamaki wai duniya ta juya min baya duk son kudin Mufeeda yarinyar da komai nata na kudi ne yau gashi taji uwar bari kar a hauro ayi musu fyade har roko take a zauna musu kyauta a gida lallai duniya tun ba a je ko ina ba kenan.

Uwaliya ta kwaso kayanta kaf tare da sanarwa me gidanta ta dawo gidanmu sabo da gida ba Babban gida bane gashi mijin kasuwancin nawa ya kashe min Uwa ya gudu ban kara ganin sa ba,ya barni da igiyar aure mara amfani a kaina,idan bai nemeni ba ya zanyi wayyo neman kudi ya jawo min.

Dare yayi Uwaliya tana dakinta ta gama cin abincin da na siyo mana har ita na bawa tana ta godiya sabo da Uwaliya mutuniyar kirki ce ba ruwanta da kowa ba gulma ba sa ido.
Na tasa kannena a gaba Meenat da Ma'eesha nace dole suci abinci naga duk sun rame,duk da cewa na fisu ramewa sosai,Bani da karfin gwiwar da zan mana girki duk cikin kudin Sadakina nake cinyewa,Meenat tace sis kici mana idan baza kici ba mu taya zamu iya ci,duk kin rame dan Allah ki kara hakuri kullum fa sai kinyi kuka cikin dare muna jinki,Maeesha tace kuma ance ba kyau ana yiwa wanda ya mutu kuka yanzu Ammah kina kara mata azaba fa,wani hawayen tausayin kanmu ne ya zubo min na share ina kakalo Murmushin dole tare da sa hannuna a abincin muka fara ci badan muna so ba,kawai tunanin Ammah nake da kanmu tare da igiyar dake kaina,miji bai San me nake ciki ba,kaico na nikam na tafka kuskure dana sani nakeyi da nadama,ganin basa ci da yawa na shiga basu da kaina ina ciyar dasu suma suna bani abin haushin na fisu saurin kuka kawai hawaye nake ina ci har sai da na karya musu zuciya suma suka fara,Maeesha tace Wai Ammah baza ta dawo bane? Wai Sis ba a dawowa? Nace baza ta dawo ba ina shesheka na kara fashewa da kuka babu me lallashi,muna ta tuno Rayuwar da mukayi da Ammah me dadi tun tasowar mu,dan ma Allah yasa gaba daya kayan Ammah na sawa na kwashe na bawa Danginta dan kar ma na gansu bakin ciki na damuna da yawan kuka,sai pics Namu da nata amma komai nata na kwashe na bayar,masu amfani kawai na ajiye tunanina ko da kuwa Allah zai bayyana mana Abbanmu watarana.
Uwaliyace ta shigo ta zauna kusa damu ta fara yi mana nasiha tana lallashi tare da kwantar mana da hankali har mukayi shuru,sai ta fara yi mana labaran tatsuniya na abin dariya muka dinga ta faman dariya kamar ba mune dazu muke kuka ba,mun dade sosai sannan nace muyi bacci ta tafi dakinta,nima na kulle mana daki,muna kwance mun cure waje daya,cike da nutsuwa nace Meenat Ku tashi muyi magana,da sauri suka Mike zaune a saman katifar domin ko arzikin gado bamu dashi.

Rungumesu nayi a jikina sannan na kwantar da Ma'eesha saman cinyata ina shafa kanta,Meenat ma tana jikina ta jingina,nace Meenat nasan kinfi Ma'eesha hankali zan baku labari akan zancen da kuke ji nayi aure,ba wai bane tabbas da gaske Meenat nayi aure nan na kwashe labarin duk yanda akayi tun daga fitar da nake nemo kudin maganin Ammah har haduwata da Aayan,Yarima tare da Aurena kaf na basu Labari Ma'eesha nasan duk da ta fahimci komai amma baza ta kai Meenat fuskanta ba,gani nayi Meenat tana ta murna tana dariya,nace mene haka ke kuma? Sis wlh kin cikawa Ammah burinta shi yasa,kuma Alhmdllh kin samu me kudi Allah yasa na gari ne sis ya tallafa mana,kawai ni shawara mu dage da addua kamar yanda muka saba sai kiga Allah ya canja masa zuciya from bad to good,kuma am serious bashi ya kashe Ammah ba domin kina fita aka fito da Ammah lfy an mata aiki tuni kinga lokacin ma baki je wajensa ba bare yace miki baza a hada ta ba sai kin aureshi kawai wayo sukayi miki, naji dadin zancen Meenat sosai da ta ganar dani amma da haushin Aayan nakeji cewar shi ya kashe Ammah amma duk da hakan ban wani yarda ba kawai shi ya kashe min Uwa.

Meenat tace lokacin da Ammah ta farfado Sis tana ta nemanki bakya nan,sai tace mana naji a jikina wani abin Alkhairi zai samu yata Abin alfaharina Mufeedata yau Alkhairi zata hadu dashi,naso ace zanga wannan lokaci da Idona amma kash,sai muka ga tayi shuru,ta kara rike hannuna tace Meenat kuyiwa yar uwarku biyayya idan kuka saba mata bazan yafe muku ba,ku hada kanku karku taba rabuwa sai aure,Mufeeda zata rike min Ku da Amana kamar ina raye,ta Zama madadina,sai tayi tari taci gaba kuce ina son Mufeedata Allah ya bata miji na gari me kaunarta wanda zata huta taji dadi a hannunsa,sannan Ku fada mata nace duk Wanda ta aura ko waye tayi masa biyayya,ta kara hakuri sannan ta kula dashi da rayuwarsa tare da komai nasa da ya shafeshi,karta bari a take mata yanci duk Rintsi ta kwace yancinta,Mufeedata nasan ba me tsoro bace dan haka kar taji tsoron fadan gaskiya a duk inda take,taji tsoron Allah a duk inda take,tabi Allah,ta kula da ibada,ta tsare mutuncinta na ya mace,sannan tabi mijinta ta kula da iyayensa,ku rike addua, kuyi Zumunci dangina dana babanku baku da kamarsu, ba da iya Mufeeda nake ba,gaba dayanku yarana wannan shine abinda zan bar muku,shine a matsayin gadonku tunda ban bar muku komai ba,karshe Ku fadawa Mufeeda idan Allah ya bayyana babanku kuce masa duk abinda ya min na yafe masa baki daya,ni nasan ban zalinceshi ba amma shima ya yafe min,naso ace na aaaabaku labari akan zamana da babanku har zuwa sabanin da muka samu,da dalilin sabaninmu amma idan ya bayyana nasan zai sanar da......Nan mukaga Ammah tayi shuru Sis sai ga Doctor ya shigo yayi aune aune sai muka ga ya lullubeta suna magana da turanci da wasu nurses nan take mukaji ashe mutuwa Ammah tayi,gaba dayanmu kafin Meenat ta gama bamu labari mun jige rigarmu da hawaye..Nan Ma'eesha tace Sis Meenat kin manta tace mu fadawa Mufeeda wai tayi aure shine burinta sannan idan tayi aure ta fadawa mijinta Ammah na gaisheshi kuma ga Amana nan ta yarta Mufeeda abin sonta me share mata hawaye,ya daya tamkar da Dubu,mace me kamar maza ya riketa Amana ya bawa mufeedanta farin ciki shine bukatar Amman Mufeeda,nan take da jin zancen Ma'eesha sai muka koma muna dariya muna hawaye kamar Ammah ce ke maganar,dama Ma'eesha akwai iya bada labari gashi bata mantawa yanda ka fadi abu haka zata bada labari. Haka mukayi ta hirar Ammah har dai na sa Ma'eesha a tsakiyarmu muka kwanta abinmu har bacci me nauyi ya kwashe mu.

Sati biyu da rasuwar Ammah cikin kudin Sadakina na kara jarin sana'oina,cikin Sadakin na canjawa su Meenat makarantar Kudi aka yi musu transfer a secondary schl me Saukin kudi sunfi na Gomnati karatu ni kuma bani da burin da ya wuce suyi karatu,Komai har su Uniform nayi musu har kala Hudu hudu su schl bags littatafai etc,haka nayi mana sababbin dunkuna masu dan kyau,na kara siya mana abincin gida domin tuni na cire rai da auren da nayi na gama tabbatarwa cutata Aayan yayi sabo da haka kawai nayi watsi da wani aure,na manta ma ina da igiyar aurensa sam duk da cewa abin na raina amma na hakura na rungumi rayuwarmu ace anfi sati biyu da daura aure amma kamar wanda ya auri karya ai idan da gaskiya sai yazo ya biya ni kudin kasuwancina dana yarda na aureshi bisa sharadi.

Haka na kwashe wata guda da aure amma babu labarin Aayan abin takaicin kuma duk na karar da kudin sadakina,gashi kuma sana'ar tawa yanzu Sam bata tafiya ba kudi a hannun mutane,sai a yini guda ba a zo ance za a siyi ko Wake ba,duk na shiga damuwa ina tunani idan komai ya kare mana ya zamuyi ina zan sa kaina,abinda ya Dameni shine nayi Nadamar Halayena na Algus a sana'a ta tuni yanzu tsakani da Allah nake yinta bana kara komai marar kyau,kuma Istigifari nakeyi Allah ya yafe min,Amma Kuma dana gyara halina sai ma na daina ciniki,komai ya tabarbare,ba riba,lokacin kuma da bana yin ingantacciya komai tafiya yake min dai dai ina samun ciniki da riba,ikon Allah kenan yanzu Kusan duk sun karye ma,idan ya kare sai dai na iba a cikin Sadakina na kara dama duk kudin ma sun kare sabo da nayi mana abubuwa ciki da dama.
Sai da nayi dana Sanin canjawa su Meenat makarantar Kudi yanzu da uban me zan biya musu idan shekara ta kare,nidai haka nake ta yawon saro kaya da siyarwa ina sana'ata tunda ba labarin angon,ni kuma bazan je gidansu ba,ga rasuwar Ammah kullum sabuwa ce a wajenmu ko yaushe muna kuka muna tunaninta.

Yau juma'a na kai wata daya da sati daya da Aure kuma haka da rasuwar Ammah,tun safe na sallami su Meenat suka tafi schl,Uwaliya ma ta tafi gidan da take aiki,ni kadai ce a gidan sai da na gyara ko ina dake gidan fes fes tare da kunna turaren wuta,na kunna turaren wuta har Toilet sannan na dawo tsakar gida jikin Rijiyar gidanmu ina wanke mana kayan sawarmu ina shanyawa ga girki ina yi jullof din shinkafa taji kayan hadi harda kifi sabo da bamu da yawa shi yasa girkinmu ke dadi,sai dana cika igiya da kayanmu kana na shanya tare da kara wanke wajen,kwashe abincin nayi a wani foodflask me dan kyau sabo dana siya mana shi set biyu.

Lokaci na kalla naga bani da abinda zanyi kawai na kwashe yan kudin da suka rage min na zuba cikin Aljihun tight wando na na ciki,sabo da ni duk tight din dana ke sawa cikin kaya to sai na kaiwa wata tela ta dinka min aljihu da zip a jikinsa sabo da ko ina zanje a duniya da kudi a jikina kaf nake tafiya tun Ammah Nada rai,bare yanzu da nake tsoro kar na barsu a gida wani cikin yan iskan gari su shiga su yashemu tas mu rasa inda za muyi shi yasa kamar me aikin Hajji kudina na jikina wanda zanyi amfani dasu kawai nake rikewa a hannuna,kulle gidan nayi tare da tafiya gidan kawata Nawwara sabo da tana ta zuwa ni bana zuwa,da Sallama na shiga muka gaisa da Ummanta tare da Yayanta Hammad,tunda na shiga Hammad yake ta kallo na har kunya naji,Umma tace shiga ciki mana Mufeeda mutuniyar taki yanzu zata dawo ai,ina Zaune sai ga Nawwara ta dawo dama Salat aka aiketa ta siyo,Da gudu ta fado palon tare da miko min hannu muka tafa,tace shegiyar gari sai yau zaki zo, nace ke dai bari ba lokaci wlh yanzu ma dan kar na karya alkawari nazo miki sauri nake na koma kafin su Meenat su dawo kin San yau Friday,Nawwara tace hakane uwar mata,Wlh ina tausaya muku musamman ke da kike komai it's not easy ace kamarki ke kula da gida just 17yrs,ni abinda ma ya Dameni Mufeeda auren nan naki kinji yanda ake gulmar a unguwa dan abin ya shafeku ne ba za ayi a gabanku ba,wasu sunce karya ne dama,wasu kuma sunce ai auren kudi kika yi sabo da son abin duniya gashi wai ya gudu yaki zuwa ko kallonki baya yi,wasu ma sunce bature kika aura,wasu kuwa wai ciki yayi miki shine aka zubar dan kar a gane shine akace ya aureki,wasu kuma sukace ai ana daurawa ya samu ya kwanta dake shine ya fece,ke kowa da abinda zaice,murmushin takaici nayi nasan ni na jawowa kaina sai nace can da matsalarsu zasu gani ai watarana gaskiya zatayi halinta,yanzu gulma ba kauye ba birni kowa yinta yake.

Ita kanta Nawwara karya take tace tasan sirrina ni dama can ban damu da kawaye ba bare duk sirrina na kwaso na fada musu a dinga gulmata sabo da mutum mugun ice wani jira yake yaji sirrinka yaje yayi ta yadawa a duniya shi yasa ni bana so wata ta fada min sirrin rayuwarta kuma nima bazan fada miki nawa ba kawai ayi hirar duniya,duk inda mutum ya kai da gulmarsa bazaice ya San sirrin gidanmu ba,shi yasa ko ita Nawwara tayi tayi taji gaskiyar Aurena da halin da nake ciki amma naki yarda ma Sam ta sani daga ni sai yan uwana suma kuma haka Ammah ta tarbiyar damu,sirrinmu iya mu kawai family,share zancen Nawwara nayi na saki wata hirar can ta duniya daban,daga nan na Mike nace yan makaranta sun kusa dawowa ni zan wuce,Hammad yana Jin haka ya mike tare da fitowa waje,saida ta rako ni har waje muka yi Sallama,ina cikin tafiya Sai ga Hammad yana cewa Mufeeda na amsa a mutunce,Yace wai da gaske kina da aure dan Allah? Nace ae,da gaske ko wasa ni fa ban yarda ba na dawo daga service naji labari,murmushi nayi nace wlh yaya Hammad da gaske ne, bata rai naga yayi tare da cewa to gaskiya wannan ba mijin kirki bane kisa ya sake ki kawai ai gwara ki zauna ba aure,nace to idan ya sakeni wa zan aura?Ni ina son mijina bazan iya rabuwa dashi ba,komai shi yake daukan nauyinmu,Hammad yayi wani dariya kamar Boss yace sannu yar karya da ba a San Asalin balbela ba da sai ace daga masar take,ance me kudi ne ya akayi kike sana'a?kina ci da kanki,wa ya taba ganinsa yazo wajenki?makaryaciya rufa miki asiri zanyi kisa ya sakeki na lallaba Na aureki Ku ba gata ba,ba yayan uban kowa ba sai shegen iyayi wai ku kyan da kuke dashi ne yake rudarku ko?

Nima fa bani da hakuri watarana nace ina ganin mutuncinka Hammad karka bari na yaga ma mutunci a unguwar nan,ka gyara kalamanka,ni yanzu me daraja ce da tsada domin ina da aure kuma da ace kasan wa nake aure da sai ka raina kanka tare da yin nadamar kalamanka,ni nafi karfinka wlh ko ace bani da aure hankalinka da nutsuwarka sun min kadan a matsayin mijina,ina fadar haka na juya cike da Raunin zuciya ina son fara Kuka... dum gabana yayi mugun faduwa ganin motocin Aayan sun kai su Bakwai a jere kofar gidanmu,juyowa nayi na kalli Hammad kana nace ga dan Halak can, zo ga mijin nawa sai ka mutu na juya ina tafiya,na barshi nan tsaye,kusa da inda suka yi parking akwai me salat ba ruwana na tsaya na siya mana salat da tumatir sannan na rike ledar zan shiga gida,muryar su Meenat naji da fara'a suna sis mun dawo ina kika je?da sauri suka karaso tare da rungumeni ina musu Kiss a goshi domin mun saba da hakan ma,Ma'eesha ce ta karbi ledar salat dake hannuna ni kuma na karbi jakankunan makarantarsu muka nufi shiga gidanmu,ko kallon motocinsa banyi ba,yana ciki duk abinda mukeyi yana kallonmu,yasha mamakin ganin ko kallon motocin banyi ba kuma yasan na gane shine saima gida yaga mun shige,ni kuma cike da bakin ciki na banko kofarmu da karfi da niyyar na rufe dan Ubansa tunda baida mutunci nima zan nuna masa abin haushi da kunya kawai sai kofar ta balle baras ta fadi kasa rigijif ai ko har securities dinsa sai da suka barke da dariya yanda na shiga gidan cikin fushi da hasala tare da mako kofar kuma sai ta balle.

Aayan ma sai da ya dara duk kuwa da kuncinsa,muna shiga na taimaka musu suka cire kayansu,nace suje suyi wanka muyi sallah sai muci abinci, shi kuwa Aayan ganin masallaci za a fara sallar Juma'a sai yace suje suyi sallah sai su dawo,a nan masallacin unguwarmu sukayi Sallar, kafin su fito na gyara salat na yanka mana,Bayan munyi sallah na zuba mana a tire kato kun San dai akwai ci ni kam,a tsakar gida saman tabarma na wani baje cinyoyina,sanye nake da Vest red,sai skert din atamfata yayi mugun Dameni gani da hips tare da da tudun Mazaune kamar babbar mace,haka nayi wani cas dani ga skin dina jajir da ita fara,ko dankwali ban daura ba sabo da ni dama a gida bai Dameni ba,jelar gashina har yaso wuce tsakiyar baya na,sajena da gashin gaban goshina sun kwanta luf,ina ta bawa su Meenat abinci a baki kamar wasu yara nima ina ci suma suna bani muna hira.

Wani yaro ne ya shigo da Sallama wai Mufeeda tazo sauri yake zai tafi,nasan bazai wuce Aayan ba cike da masifa nace kace bata da lokacinsa,yaro ya je ya fada sai ga yaron ya dawo yace wai idan ya iskeki sai kin gwammace kida da karatu,Mufeeda tace kace nace yazo din koma mene yayi idan zai iya,yaro yace ni dai tsoro nake ji bazan iya fada masa ba,Mufeeda tace to dan uwarka nice sa'arka zaka zo ka fada min fice min a gida,yaro ya fice da sauri yana kuka Mufeeda ta zageshi,can sai ga Oga Aayan da kansa ya shigo gidan cike da bacin rai yana huci,kamar ance wani ya mutu yanda yake kunci,yanda ya hadu yau ba a cewa komai,yayi masifar kyan da ban taba gani ba,cikin kana nan kaya yake hadaddu duk gidanmu ya gauraye da kamshinsa.

Wani Kwarjini ya min tsoronsa ya kamani na fara da na Sanin maganar dana fada masa,Ma'eesha sarkin Surutu tace sis gashi nan ya shugo ko shine mijin naki? Meenat ta kalleshi ta kalleni haka take yi sannan sukace ina yini? Da kyar ya iya bude baki yace am fine tare da kare min kallo ta kasan ido,

ni dai naci gaba da basu abinci a baki ina cewa kuci abinci akwai Islamiyya kun sani, ganin su Meenat a ransa yace har kanne gareta Ashe,muryarsa naji yace ina Mum naki,cike da zafin rai nace taje inda ka aiketa, ba wannan ne ya kawo ni ba ina da aikin yi,kizo muyi magana dake,Meenat tace Sis kije mana,sai da na ebi abinci a hannuna sannan na Mike da abina ina ci kamar mayya,ya kalleni yana mamakin jarabar ci na ko micijin ciki ne da ita oho,hannuna da shinkafa a ciki na dunkuleshi nace shigo wannan dakin,ya wani yatsina fuska yana tabe baki haka dai ya shiga yana wani makale jikinsa irin zai kwashi dirty,

Ji nayi yace ba a gidanmu zaki zauna ba yanzu,wani gidan za a kaiki daban,kiyi fixing Date da kike so su Abbi sunce ba yanzu zaki shiga family house ba sai nan gaba,so gidan dana kaiki rannan kike gyarawa nan zaki shiga,ki sanarwa Mum naki,wani farin ciki ya kamani kamar na taka rawa wannan hadadden gida ga kayan dadi zanci na koshi, ban san sanda na fashe da murmushi ba tare da cewa wannan gidan me kayan dadi? sai kuma wani bakin ciki ya tsaya min wato bai ma San Ammah ta rasu ba,kuma ko irin yace min ya me jiki ko ta warke Sam,nace aiko ya me jiki kace min ko? Au bata warke ba?kamar na mareshi haka naji,nace ta rasu,Allah yaji kanta ya furta irin ko a jikinsa,nace daga ni sai kannena mu uku,yace then? kuma ni yanzu na fasa auren ka sakeni kawai yafi min bashi da amfani sam,murmushi yayi yana daga tsaye yace kin makaro kinci Sadaki,kuma na biya kudin Magani na cika alkawari dole ki cika

Please Login or Register in order to submit comment