Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu ma kofa a bude take zaku iya komawa Karuwanci da shaye shaye,sace sace kuwa na wanda kuka gani shi zaku dauka dan ni nawa yafi karfinkuπŸ˜…, Abbi Sani yace Haba Hajja addua ai zaki yi musu ba kice suje suyi ba ai yarane yanzu idan mune zaki so yaranki su dawo haka?.
Kai Sani ka rufe min baki shegen kunne kamar malafar Kwadi,Dariya aka dauka gaba daya har yaran Sabo da kunnen Abbi Sani kamar Malafa haka suke kuwa,Abbi Mustapha ne ya buga musu tsawa,shima Abbi babba yace zaku bar palon nan yan Bantan uban Yara.

Khaleel ne yake ta masifa a tsakar gida an sace masa sabulun wanki wanda da kyar ya hada kudin ya siyo na wanki dan Naira Hamsim wani kato zai dinga cancanawa yana wanka dashi,daga ajiyewa ya juya baya zai dauko bokiti kafin ya dawo har an dauke sabulun yan mintuna kadan,Nan ya fara fakon wanda ya dauka duk wanda ya shiga wanka ko me wanki sai ya duba sabulunsa mata da Maza,Meenal tana fitowa daga wanka ya ganshi a hannunta ashe ita ta sace ta wanke panties dinta tunda period take dole sai da wanka da wanki,Kamar zai cinyeta haka ya kwace abinsa,dan ya bar mata tace kazanta ta na wanke dashi fa period ne duk na shafa masa na wanke da kyar ake gane kalar sabulun dazu wlh dan baka gani ba yanda ya rine kamar jar color aka Sa,abin kyankyami har wari yakeyi, Khaleel ya gano so take ya bar mata shi du, yace ai ko a Abbatuwa mayankan dabbobi aka jefa shi cikin kogin jini bani abina dan Uwarki mayya wlh idan na kara ajiye abina kika dauka sai kin gane kurenki,Meenal tace jaraba akan sabulun wankin?Yace ae din,to yi hakuri dan Allah ka bani na karasa wanke daya pant din nawa yanzu na tuna ban gama ba kaima kasan sanda muna daula bakwa sanin ma time din da muke period yanzun ma babu ce tasa ba yanda zamuyi dole muke yage yar kunyar.
Khaleel yace ungo badan halinki ba dan dai kawai kina san min Vaseline dinki ne Allah gashi nan saura ki karar dashi,Na gode cewar Meenal ta koma toilet ta gama ta fito ta bashi sabulunsa,Mujaheed ma da shi yayi wanka haka mata da mazan kaf ba yanda Khaleel ya iya haka kowa ke zuwa yana rokarsa dashi sukayi wanka,Abbi ma yace kai Khaleel bani sabulun sodar nan naka zan cude jikina dashi ina so na fita neman Ameer ruwa a jallo dan ubansa ya zai manta da iyayensa,Khaleel yace kune fa kuka koreshi ai ni ya birgeni wlh,gashi sabulun dan Allah nasan wankanka dadewa kakeyi karka silleshi Abbi.

Harara Abbi ya zuba masa ya wuce yayi wanka sannan ya kwalawa Meenal kira tana zuwa yace Bani Toothpaste naji ance kece me shi a gidan nan,Meenal tace Vaseline gareni ni Katon gaske wlh ko wanka zaka yi dashi ina dashi kamar tulu yake Sabo da girma saurayina nasa ya kawo min shi maganin gidan yawa,Meenal Me Vaseline kenan,Abbi yace dauko min shi na shafa,wace to me abin goge baki?Haneefa ce me su manya manya ita take matsowa kowa da kanta duk yanda kuke da ita sai daΓ­ ta Matsa ma da kanta kar ya kare da wuri,Abbi yace kirawota ta bani,Tunanin Abbi ai shi Babbane Haneefa zata bashi ya matsa da kansa yanda yake so sai kuwa yaga tace kawo Brush din,da mamaki ya kalleta ta kuwa bude ta dan difara masa kadan tare da cewa kar ka raina Abbi rayuwar sai da tattali,Hajja ma tazo tace Haneefa ashe kece me makilin matso min a nan na goge bakina,Haneefa tace rayuwa sai Imani Hajja ku tsofaffi har wani goge hakora kukeyi idan ba iyayi ba da ganin arahar Sa me zaki goge hakora kamar Tsinken tsire duk sun zube saura dai daiku kici goronki shima yana wanke muku baki tayi tafiyarta,Hajja tace ni me na tare musu da aka rainani,ta fara kiran Khaleel sai da yazo jikinsa ba riga, tace wai kai kullum baza ka Sa riga ba kai kenan daga dogon wando sai gajere,Khaleel yace Am too sexy ne Hajja wlh shi yasa nake nuna muku baiwa ya fada yana dariya,Hajja tace ina wata baiwa a nan Da Ameer dina ne ya fada sai na yarda dalla bani sabulu na wanke jikina, Khaleel yace Rayuwa sai Imani Hajja wa zaki wa wanka ke ba miji ba,yo ko miji gareki me zai ci da ke ki sha zamanki haka da Allah wannan Asarar sabulu zaki mana,Hajja ta balbale shi da masifa ko wanne dan iska bani da iko nayi magana sai yace wani Rayuwa sai Imani wata sara kuka samo kuma ko kuwa ni kuka raina.

Khaleel dai yayi tafiyarsa,Mujaheed ne yazo ya wuce Hajja shima ba Riga sai 3qtr ya tattaro hantsar Wando ya rike gaba daya yana tattalewa yana tafiyar yan gayun samari ga uwar suma duk ta cukurkude,Hajja tace haka dai aka iya yan iskan Yara ayi aure tun tuni kuka ki yi sai aikin rike hantsar Wando Sabo da jarabarbu ne ku mayun mata,Hajja bata san gayu bane ta dauka sha'awa ce ko Iskanci ne ke damunsu,Mujaheed yana Jinta yace Hajja sai Imani ai ko Ya kika ce,Tsaki ta ja tare da tauna
Goronta,Sabeer da Aliyu ne wanda sun kai 24yrs yanzu su kuma boxers ne dan karami suka Sa da yar Singlet ga abar tasu nan a Wando ana gani duk ta mike da wata yar kwarababbiyar waya karama a hannusu suna dannawa suna kallon pics din yan matan turawa kusan tsirara suke,Hajja nan ma ta rasa uwar da suke sai kus kus suke suna dariya suna kallon waya,ta kalli wandonsu a ranta tace na shigesu ni Hajja kar fa a fara cikin shege a gidan nan ayi yar gida tunda ga yan mata nan kuma ba muhararram juna bane wasu to matan ma ya suke bare Maza,Ganin Hajja na Sa musu Ido Sabeer yace Allah wadaran karamin gida sanda muna gidanmu babba wa yasan me wani yakeyi Amma yanzu komai kayi akan idon wani,Aliyu yace muyi maganinta suka samu Hajja tare da cewa Hajja kinga wasu dan Allah sun hadu? Nan Hajja ta kalli waya ai sai taga Mata kusan tsirara,Sabeer yace wannan zan aura Hajja tayi? Duka Hajja ta rufeshi dashi tare da cewa wlh in dai ina raye baka Isa ka auri wannan ba,Aliyu yace musulma ce sunanta Rasheeda,Hajja ta dauka da gaske ne ta dinga tsine tsine ba a Isa ba,kuma tace sai ta fadawa su Abbi,Sabeer yace Hajja masu kudi ne fa yar gidan shugaban kasar Ethiopia ce fa kinga mun washe,sabo da son kudi Hajja sai tace ya sunanta kace? Yace Rasheeda,Hajja tace ayyo yanzu naji zance ai tun daga sunan ma kasan musulma ce,a ina kuka hadu a Internet din naku?Sabeer yace ae tace kwanan zata zo ma kuma zata Aiko min da yar million goma na sha ruwa,kirji Hajja ta dafe tare da cewa kace ina gaisheta kakarka Hajja sunana,yaro kayi dabara wlh kafi su Khaleel hankali ina kallonku yara ashe kune manyan,Aliyu yace Hajja kinji tana kira ma a waya kash Amma bamu da kudin Sa kati kuma dole sai da kati so muke mu tura mata accnt Number tace Sauri take zata turo kudin gashi bamu da sisi,Hajja da Sauri tace zan baku rance ina jin kamar Ina da dubu biyu a hannuna nawa ne Katin da zai isa? Sabeer yace tab ai sai dubu biyar yanzu kuma babu sai daΓ­ ayi asarar milliyan goma kenan Hajja ki taimaka idan ta turo zamu baki milliyan Uku a ciki kyauta,Hajja dadi ya rufeta tsohuwa da son kudi nan tace to dama dubu shida ce ta ragemin a duniya ga biyar sai na rike daya ni kuma,Nan Hajja ta zaro dubu shida a jikinta wanda da haka kawai ne sai daΓ­ a mutu a gidan baza ta iya siyan ko sabulu ba.

Sabeer suka karbe dubu biyar da Sauri suka dauki dubu daya daya,dubu Uku kuma suka siyowa kowa na gidan sabulun wanka da wanki,suka bawa matan kudin kitso,mazan kuma na aski,har pad aka siyawa matan kowacce biyu biyu Sabeer yace gashi naga Alama boxers dinmu an fara sace mana ana kunzugu dasu, har da Sauran dan abinda ba a rasa ba duk sun dan siya me araha,karshe dai Sabeer dari biyu biyu ce ta rage musu,Duk yaran gidan sunji wayon dasu Sabeer suka hadawa Hajja sai dariya akeyi a boye kowa ya washe yau a gidan har kifi soyayye suka Dora a saman shinkafa da wake kowa daya,su Abbi da Hajja basu san me akeyi ba,dama matayen su Abbi sunyi yaji su Haneefa ke girki duk da basu wani iya ba wahala tasa har sun saba.
Kwana biyu Hajja taga su Aliyu shuru ba 5k dinta ba milliyan Uku sai nemansu take Amma sunki yarda ma su hadu wasan buya sukeyi.Idan taje dakinsu sai su Khaleel su boyesu kowa yace basa nan sun fita,Hajja ta koma me gadin dole a Palo take kwana wai zata ga wucewar Aliyu ko Sabeer amma sai su wuce ma bata ganesu ba.

Washe gari da Safe ma sai da Aayan ya kwashi Harka ba daga kafa kamar ma baya tausayina, kamar yanda su Meenat suka saba haka sukayi komai girki da gyaran gidan su ma yan aiki suna nasu,sai 11am muka fito bayan Aayan ya shirya ni yayi min komai,ba su Meenat gidan shuru sai guntuwar paper na gani sun ajiye min,.......wai mun tafi gidan Ammah tare da Ameer sai dare.
Aayan yace ina suka je? Gidan Ammah na bashi amsa a takaice, da kansa yayi Feeding dina muna hira sama sama yana tsokanata wai jiya naji dadi na fara sabawa,na fara Kukan shagwaba ina Ni ba wani dadi,yana mun dariya har muka gama,yace je ki shirya muje gidan Ammah sauri ya furta ba alamar wasa,da Sauri na tashi na je sama nasha wata dakakkiyar shadda yar Senegal tasha aiki Dark purple aikin kuma da light blue and pink na fito kamar wata Hajiya,Shi kuma shadda Light blue kamar munyi ango sosai muka yi kyau.

Jerawa mukayi wow yau abin kallo ne mu, nace muje wajen Daddy mu gaisa,Daddy ba karamin farin ciki yayi ba da ya ganmu haka sai albarka yake sa mana sannan yace mu gaishe da Ammah, yau ba Driver bane zai tuka mu kuma ba escourt mu biyu kawai,da kansa ya zagaya tare da bude min gaban motar yace ranki ya dade Allah ya taimakeki shiga,Kafadarsa na dan buga kadan ina dariya na shiga ya rufe sannan shima ya zaga ya shiga yaja motar cike da nutsuwa muka bar gidan,Ba wani nisa me yawa bane sai gamu a wani gida dan babba me kyau sosai yayi kyau gaskiya,me gadi ne ya bude mana gate ya Cinna hancin motar Sa cikin gidan,gidan yasha tiles da flowers yayi kyau sosai,jikin wata katuwar Bishiya muka hango su Meenat tare da Ammah zaune a katuwar tabarma suna hutawa,Ameer da Yarima suna gefe suma,Hajja da Katon tire a gabanta tana kwada musu zogale da Kuli yaji hadi sai nishadi sukeyi abinsu.

Aayan ya kalleni yaga ina murmushi ni kadai ina ta kallon Ammah muryarsa naji yace muje ko? Da sauri na dawo hayyacina na daure fuska irin ba dadi naji ba,murmushi yayi yace kinfi kyau a haka muje dama naji jiya Ammah tace duk tafi so taga kina fushi dariya kike bata,da Sauri na washe bakina nace na fasa fushin tunda tana so,na fito ina ta fara'a ina murmushi wai Ammah ta gani kar taji dadi ma,Aayan yana ta dariya a ransa,a hanya yace Ammah tace tana so taga kina fushi kinki gaisheta,nace aiko sai na gaisheta din,Aayan yace ke duk abinda bata so shi zakiyi ko? To ki daure dan Allah ki nutsu tana son ta ganki a nutse cib dake,Nace haka tace?Yace ae,na girgiza kai nace za a gani wlh Bazan nutsu ba sai na koma kamar bera wasa zan tayi ba nutsuwa.Aayan yana ta dariya mugunta yake hada min.
Muna karasawa mukayi sallama kowa Murna yake yi nazo na huce,a kunne ya rada min tace ita bata son a durkusa mata da Sauri na durkusa nace ina yini Ammah kuna lfy ya gida ya aiki?irin na bata haushi bata so a gaisheta,sai naga tana ta murna ta Amsa da fara'a harda Sa min Albarka,ni kuma sai yashe baki nake ina fara'a wai ance tana son nayi fushi shine bazanyi ba ni fara'a zanyi,har hannu nake sawa ina kara bude bakina sosai,Aayan yana ta dariya a boye,shima cike da ladabi ya gaishe da Ammah ta amsa da sakin fuska suna hira sama sama,tunowa nayi ance tana son ta ganni a nutse to Bazan nutsu ba,Sai mutsu mutsu nakeyi muna hira da Ameer tare dasu Ma'eesha duk nafi kowa surutu,dan karma ace na nutsu nace Ma'eesha jibi akwai schl kema kin sani ki tabbatar kin mana wanki da guga na furta da masifa kuma da sauri irin ba nutsuwa,Ammah hirarsu sukeyi tare da Aayan da Yarima,Na dauko wayata ina dannawa,na mike na dauko wata kujera fara naki Zama waje daya naki yin shuru kar wai ace ma ina da nutsuwa, ita kuwa Ammah dadi take ta ta ji tana kallona irin na saki jikina a gidanta sai harkata nake yi,Meenat ma da sauran haka suna ta kin dadi.
Aayan ya zo gefena ya rada min Ammah fa bata so a shigar mata Palo da Bedroom shi yasa tunda taji na mata waya zamu zo sai ta zauna a nan wajen sabo da kar ki je mata dakinta.
Da gaske kake?yace ina miki karya ne ki kiyaye abinda zai bata mata rai zamu fita da Yarima zan dawo anjima mu tafi, Yarima tashi muje,Yarima yace Madam yau an manta damu? Sai lokacin na tuna bamu gaisa ba da sauri na gaishe shi ina bashi hakuri suka fice daga gidan a motar Yarima.

Na tuna Ammah bata so a shigar mata Palo da dakinta kawai na tafi na shige can ciki ina ganin haduwar gidan da furniture din gaba daya,Ina haka naji Muryar Ammah a bayana tace Mufeeda ta wai kamar ba ke ba? Tausayi ta bani kawai naje na rungumeta harda hawayen farin ciki,nace kiyi hakuri Ammah kece nan kika yi mana haka me yasa haka? Kin samu kuka da damuwa,kuyi hakuri haka Allah ya tsara da ace banyi hakan ba baza ki taba yarda da auren nan ba,yanzu gashi kina zamanki da mijinki,nasan halinki Mufeeda kamar yunwar cikina,ko kin yarda anyi auren baza ki zauna ba matukar kin San inda zaki ganni,kuma cewa zakiyi sai kin kula dani,zaki dinga dorawa mijinki nauyi yayi tunanin baki da tarbiya,kuma ai gaskiya ce har fa auren kasuwanci kikayi da ina raye yana hanaki kudin zaki barshi,haka kuma akan kudi nasanki ba mutunci,har auren Kasuwanci kika yarda kika yi,shi yasa yana fada min kin yarda da auren kasuwanci nasan kawai son kudin naki yayi yawa shi yasa kawai nace ace miki na rasu naga yanda kudin zasu amfaneki,nayi tunanin tun daga Ranar zakiyi nadama Ashe sai kika ci gaba da son kudin ki dole sai kin ci kudinsa,yanzu ba gashi Mufeeda na ta Zama Babba ba,ta girma,tayi hankali,da mijinta,tana zamanta lfy,tana karatu,ba ruwanta da harkar son kudi rayuwarki ta gyaru Alhmdllh.

Tafiyar da nayi nace ace muku na rasu nan ma ba iya akan kanki bane akwai wani abu a kasa amma zan fada muku sai lokaci yayi zaku sani insha'allah,Yanzu Aayan ya sanar dani rashin lafiyar babansa akwai wani me maganin gargajiya can kauyenmu Insha'allah wani satin zamuje a kaishi ko za a dace,Allah ya kaimu nace Ammah wai Allah yanzu kece? Na furta ina shafa jikin Ammah,tana dariya tace nice ko kin tuna sanda kike kaini toilet ki dauko ni? Sannu Ammah kinji kinga yanda kika kara kyau da haske Ashe kema fara ce Ammah amma da kinyi duhu, bedroom muka kule da Ammah ta bani labari kaf tun daga yanda Aayan da Yarima sukayi ta dawainiya da ita a turai,Aayan ya kashe mata kudi,yanda ya dauketa kamar Uwarsa yake kula da ita kullum sai sunyi waya ba fashi,gashi komai akan lokaci,abinda Aayan yayiwa Ammah ko uwarsa ce abinda zai mata kenan,Ammah ta fada min irin jin dadin rayuwar da ta shiga a turai,tunda naji haka Aayan ya kara shiga raina,na kara bashi wani matsayi na daban,sonsa da kaunarsa ya kara mamayeni,nan take na fara kukan dadi nace Ammah Allah ya taimakeni ban taba wulakanta mijina ba,shi yasa ake son ko yaushe kayi me kyau,da yanzu kunyarsa zanji,Murmushi Ammah tayi na manya tace abinda naji irin son da kike masa har muna waya ina jiyo muryarki wai wace? Macece?kyakyawa ce? Dariya nayi tare da rufe Idona da tafukan hannuna,Mufeeda an girma,nima na zauna na bata labarin kaf bayan rabuwarmu wanda su Meenat basu bata ba na sanar mata,tace Allah ne yake tsare min Ku Allah yaga halin da muke ciki kuma yaga zuciyar kowa,sai mu kara dagewa da addua,yini mukayi muna ta hira da Ammah ba ji ba gani ina kwance a cinyarta muna labari,tana kara koya min yanda zan kula da mijina da gyaran jiki,Wasu magungunan tsumi data hada min ta bani katuwar leda guda da yanda zanyi amfani dasu,tace ga akwatunan lefanki can ki tambayi Meenat suna dakinsu guda goma sha biyar mijinki yayi miki a wajena ya hadasu can turai ni na hana a baki wancan lokacin sabo da baki hankali ba,yanzu kuma ya hada komai ya barsu wajena,akwati biyu kuma tsarabarki ce ni na siyo miki,Sauran kuma guda hudu nasu Meenat ne nayi musu baya min komai na nuna musu,Ammah to kayanki na gani cikin Sip na sawa ga wasu a akwatuna yaushe kika dinka? Aikin Mijinki ne gaba daya tare da Yarima.
Ammah Yarima fa Ma'eesha yake so,ae na sani ai ya fada min rannan ma babarshi tazo wajena mun dade da ita mutanen kirki ne ai,yanzu Ammah Meenat ce kadai ta rage,dariya tayi tace tun yaushe Mijinki yace min yayi mata miji wai shi ya samo mata ban san dai waye ba,Nace ni gaskiya a'a wlh Ameer zan bawa ita sun dace kuma baki ga taimakon da yake mana ba,to Aayan ya rigaki zabin Aayan zata aura Insha'allah cewar Ammah,kamata yayi ma su dawo gida wajena Mufeeda kinga an takurawa mijinki bazai sake ba,kai Ammah ni ki bar min su dan Allah,Bakya gane me nake nufi Mufeeda sabo dake fa nake komai da bakya min musu duk abinda nace shi kike yi me yasa kike haka yanzu?kiyi hakuri su dawo zaki gane me nake nufi,to shike nan Yaushe kike so? Yanzu suje su kwaso kayansu idan nace gobe kuka zakiyi in zasuyi miki Sallama gwara kina nan gidan,Nan take kuwa suka tafi da Ameer suka kwaso nasu ya nasu tas har akwatunan da Ammah ta ciko musu da kaya,na gani kaya masu kyau da tsada duk gasu nan iri iri,nawa kuma an bar min su a gidana.

Aayan ne ya basu Driver guda da mota dalleliya ta gaske za a dinga kai su Meenat schl da kuma unguwa har Ammah.
Su Meenat ne sukayi Dinner Ameer yace dama shima a barshi a gidan Ammah da yafiye masa,nace ai kuwa baka isa ba sai dai ka dinga zuwa kullum,Bayan munyi sallar Isha Ammah tace bana son shaye shayen maganin matan nan barkatai,wanda na baki sun isa ni na hada da kaina da yayan itatuwa,zan koya miki wasu ki kiyaye kinji,nace to,Dauko ki fara shan wasu yanzu ko period kikeyi cike da kunya nace a'a,ta bani wasu nasha tace nayi matsi da wasu duk nayi ina zaune muka ci abinci da komai,ba na so ma na koma gida nafi so na kwana wurin Ammah muyi ta hira ina jin dadi,nace Ammah Abbanmu fa?, Nan take Ammah ta bata rai karki kara yi min zancensa,gidan nan kuma da kike gani na sa an siyar dashi na kai kudin wajen danginsa dama shike nan abinda ya mallaka tare da yan uwansa mukayi shawara,Ammah idan ya mutu fa ya Zama gado fa? Nan gaba zan muku baya ni karku damu,nace to ba damuwa.

8:30pm sai ga Aayan ya shigo da Sallama idonsa na kaina, yace Ammah Yarima yace bazai samu Damar shigowa ba sai gobe zai zo,ba damuwa ai yana kokari ma kullum sai yazo,Aayan ya kalleni yaga ina jikin Ammah a kwance nayi rashe rashe ina danna waya,tashi mu tafi gida,Baki na turo gaba ina shagwaba nace anan zan kwana ni sai nayi kwana uku zan dawo,Su Ma'eesha duk sakin baki sukayi suna kallon irin yanda nake kashe murya,Ammah tace tashi ke ku tafi bana son shashanci shi yasa nasan da ina kasar nan zaman auren ma gagararki zaiyi gashi daga dawo wata zaki fara,Ameer kuwa shima tuni ya tafi gida yace sai gobe.

Aayan na kalla nace dan Allah fa nace sai gobe to ka dawo mu tafi,Har gida Ammah tazo yanda zaki ganta kika ki yarda sai yanzu zaki ce wani kaza kaza,tashi mu tafi kin ma san bazan iya kyaleki ba,Ammah tace ka daina bata bakinka tasar min a cinya ku tafi, gani Ammah tayi ina bata lokaci tace Meenat kuje Ku kwanta suka tashi suka wuce tare da ce min sis sai da safe zamu zo,Na Galla musu Harara nace dalla...dalla..dalla kuje can ku rufe min baki,ance muku bazan iya zama ni kadai ba ko aikin nawa bazan iya ba na gida,Dariya sukayi suka wuce suna yiwa Aayan sai da safe.
Ammah ma tureni tayi daga jikinta ta shige dakinta sukayi Sallama da Aayan tace ka rufe mana kofar,Daukan kayan da Ammah ta bani yayi tare da mayafina ,jakata da takalmina har dankwalina,cikin mota ya kaisu ya dawo ya daukeni cancak tare da cewa zaki san kin min musu yau Allah ya kaimu gida,ina magana kina min musu ko,nace wayyo na tuba Allah ni na isa,wlh wasa nakeyi na tuba pls My Man bazan kara ba,yace ai kin jawowa kanki yau.
Kin san dai Bana son ina magana ana min musu dan kinga Ammah na wajen ko? Da sauri nace a'a am so sorry bazan kara ba.







AsmaBaffa
[2/5, 4:50 PM] Asmabaffa: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–
πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–

KASUWANCI NA







111-112








Official







By
AsmaBaffa




AUNTY SUMEE and NAFI ga page nakune an kara muku.

KASUWANCI NA FANS ina godiya da Jinjina gareku,masu Sharhi kuna birgeni sosai.😍😍😍









Gaban mota Aayan ya bude tare da sani a hankali ya gyara min Zama tare da rufewa,komawa yayi ya shiga shima sannan ya figi mota muka bar gidan,sai da yayi mana take Away na kayan lashe lashe sannan muka nufi gida,Allah sarki Ameer yau ba abokan hirar tasa duk gidan sai yaji ba dadi,sai yanzu ya tuno da yan uwansa Frnds dinsa Su Mujaheed,Ummansa ya tuna tare dasu Abbi amma me zai musu tunda sune suka koreshi da kansu,Muna dawowa ni na kwashi wasu kayan shima ya dauka muka shiga ciki,a Bedroom muka ajiye komai muryarsa naji yace tashi muyi wanka,kunya nakeji amma haka na dan daure muka cire kayan mu tare da daura Towel, Aayan so yake kawai ya fisge towel dina ni kuma naki yarda,sai da ya shammace ni ya fisgo dan towel din Allah yasa na rike kam ina kallonsa ta gefen Ido,Dariya nayi nace woo ai ina kallonka dai, da gudu na matsa ya biyoni dole sai ya cire min Towel dariya mukeyi gaba daya har muka shige Toilet,Wanka mukayi tare kusan ma ni nayi masa komai sannan muka fito,bayan mun shirya tsaf damu Nafeela zamu fara nace tsaya a bawa Ameer takeaway dinsa shima kar yayi bacci,kyaleshi yanzu ma maybe yayi bacci kuma yaci abinci gidan Ammah.

A'a amma ai alhakinsa a kanmu yake tunda kai kake masa komai ko bazai ci ba a bashi shima,kawo na kai masa cewar

Please Login or Register in order to submit comment