Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aayan,ko da yaje ma Ameer dama yunwa yake ji a gidan Ammah bai tsaya yaci abincin ba,tnx yace Aayan ya dawo mukayi Nafeela raka'a biyu sannan muma muka ci kadan Namu sabo da a koshe muke, nayi mamaki yau da Aayan ya kyaleni naji yace naga kin gaji ne, ganin na gaji Tausa ma ya shiga yi min ina lumshe ido kawai bacci me dadi ya kwashe ni,shima bai San sanda ya fara baccin ba, Da Asuba ni fara farkawa da sauri nayi wanka tare da brush sabo da naji na fara period,sai da na fito bayan na shirya kaina na tashi Aayan yayi shima wanka da komai ya fito yayi Sallah tare da azkhar nima duk da banyi sallar ba nayi azkhar dina,Juyowa yayi yana kallona tare da cewa Period kike kuma? Nace ae da Asuba na fara,na ma yi tunanin kin samu ciki,nace wanne ciki tun yanzu ai yayi sauri,Murmushi yayi tare da cewa ba wani sauri a rana daya ma zaki iya samu,yanzu ya zakiyi dani sai da na kyaleki jiya kika huta na gama tanadin yau da safe sai kuma ki wani fara period naji haushi ya karasa kamar wata mace tana shagwaba,dariya na shiga yi sabo da ya bani dariya maganar tasa,na kalleshi cike da so shima haka nace sai dai kazo muyi Romancing zansa kaji dadi Allah sai ma yafi wanda kake so,bazai fi wanda nake bukata ba ke kin San dadin dayan kuwa,Yana saman Sallaya a zaune na koma tare da sakalo da hannayena ta wuyansa na kwanta a bayansa,Ajiyar zuciya ya saki,fuskata tana a wuyansa ina goga masa,Saman bed ya daurani ya shiga murzani cike da kwarewa nima haka ba abinda Bana yi masa har wanda ma ban taba yi masa ba duk yau na dage nayi masa sai da na zautar dashi,Sucking na masa last a nan kuma yace yama fi komai sweet,sai Santi yakeyi ya rude gaba daya,Sai da nasa ya samu nutsuwa kwarai da gaske yana ta jin dadi yana sa min albarka tare da zafafan kalamai.

Ina kwance a jikinsa muna hutawa na manna masa kiss a wuya nace na gode My Man ban ma san da me zan fara gode maka ba,ka gama min komai,abinda kayiwa Ammah,dangina,yan Uwa da duk Wanda ya shafeni bare kuma ni kaina,ban san me zance ba kafi karfin godiya a wajena, shiiiii naji yace kin wuce haka a wajena kasa ganewa kikayi lokacin ta kasuwancinki kikeyi,Dariya nayi nace Allah ba wani nan,ai kaima ba so na kakeyi ba da,ni ai ba kece bana so ba aure ne Bana so a lokacin kinji nace bana Sonki?sai dai nace bana son aure kece baki gane ba,gashi kin canja min rayuwa da tsari kin kawo min farin ciki wanda na kasa samu,kin yarda kin zauna dani duk da cewa ina bata miki amma kinyi hakuri,d angina duk abinda suke miki kin iya jurewa ai Alhmdllh
Addua kawai zamuyi Allah ya barmu tare Babyna,nace Insha'allah kuwa,dan Allah kayi ta sona kaji ni bana son ka kula kowa,ke zaki dage ai ki hanani kula kowa ta hanyar yin abinda ya dace ace matar aure ta gari tana yiwa mijinta shike nan.
Yau banyi dogon baccin safe ba,da wuri na Mike na shiga kitchen na shirya breakfast sannan na gyara ciki ko ina,naje nayi wanka naci kwalliya cikin material black and red nayi kyau,sai kamshi nakeyi ina kitchen ina kokarin shirya Dining,naji Kamshin Aayan kafin nayi wani motsi naji ya rungumeni ta baya yana shinshina wuyana,abinda ko kitchen baya wani shigowa sai yau Ashe sabo da su Meenat ne baya shigowa sabo da kunyar idonsu ba komai zaiyi a gabansu ba,lallai Ammah ta iya gyara Harka na furta a zuciyata Ashe a fili nayi maganar,Murmushi yayi me Sauti yace kin ganki baki da kunya fa kema,Juyowa na nayi tare da boye fuskata a kirjinsa,nace Saura Ameer ma,Baki ya tabe yace ai Ameer ba ruwansa shi har ya canja part jiya in baki sani ba yana daya part din tare da Daddy wai yace Meenat basa nan me zaiyi,Amma ya bani aiki abincinfa sai na kai har can da yar tafiya fa,ga mata nan a gidan ma'aikata nace ya zabi guda ta dinga masa,Amma yau dashi fa nayi ka kirashi a waya yaci a nan,Aayan yace zancen kike so Ameer wai danki ne ko yaro ne shi da kike damun kanki ai ni kadai zakiyiwa wannan.
Documents from AIHAUSANOVELS

Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels

Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels


Shike nan muje to tare dashi muka shirya komai a Dining, cup din tea dinmu daya,plate na farfesu tare dasu chips duk daya ne tare muka ciyar da juna.a Binda nakeyi wajen kula da Ameer da Daddy ba karamin birge Aayan nakeyi ba,hakan yana sawa ya kara so na Sabo da yanda wasu matan ke wulakanta dangi da iyayen mijinsu,ko kuma miji yana rike wata ko wani a wajensa abinci ma idan bai ce a bashi ba baza a kula shi ba,ko a dinga takura musu ga aike komai na wahala su za a Sa,bare miji yazo dasu nama tare da kayan dadi irin su gashashiyar kaza,yogourt etc wanda ake rikewa a gidan bazai ji ko kamshi ba sai dai idan danginta ne wannan su za a basu,amma sai gashi ni dole duk abinda zamu ci sai na bawa Ameer nasa duk da cewa Saurayin matashi ne,nasan zai iya siya ma yaci a waje tunda da kudinsa,Daddy ma dan kalar abincinsa daban ne,kuma na turawa yake ci,masu dafa masa daban suke.
Aayan ne ya kalleni tare da cewa yau zanje Office Amma bazan dade ba da wuri zan dawo,Shagwaba na fara masa dan Allah ka tafi dani kaji,ki zauna anjima su Meenat zasu zo miki fa,Ameer zai kawo miki su munyi waya da Ammah,baki na turo nace ai ni na tsanesu yanzu,haushinsu nakeji gaba daya.
Dariya yayi yace ke fa kika ce Ammah ta iya gyara Harka yanzu kuma kina jin haushinsu ina son ranar da zanga Mufeeda tayi hankali ta daina kuruciya,wai shekarunki nawa? 18 fa nake yanzu,dole kiyi yan mata,kai fa? Dariya yayi yace kin girmeni ai,nace lallai Ashe saurin girma kayi amma dai nasan ka girmeni dan Allah shekararka nawa? Yace 20, dariya na dinga yi nace Ashe ma kusan sa'a na ne ai da kadan ka girmeni,gaskiya kayi mugun saurin girma na shafa sajensa da gemu nace harda gemu na kyalkyale da dariya,shi kanshi dariya na bashi taya zan kalleshi na yarda 20yrs yake inba kuruciya ba.

Nace to muyi goyo goyo dama ni ina yarinya banyi wasanni ba sabo da neman kudi kullum a business nake kaga yanzu sai nayi kara'i tunda mate ne kusan ni da kai,Wai kasuwancin nan naki me Dame kike siyarwa? Dariya nayi nace komai,nan na fara masa lissafin irin abubuwan da na siyar,da komai da komai har lokacin dana fara ganinsa na dawo daga kasuwa,da irin Algus din danayi ina zubawa kosai garrin kwaki da jar color a ganshi sutu sutu jajir sai ace yasha kayan miya😍da wahalar da muka Sha har lokacin da yake yawan ganina gidajen yan siyasa,Sai ga Aayan yana hawaye wai na tausayi,ni kaina dana tuna abin sai danayi kwalla,tun daga farkon rayuwarmu na bashi labarin komai, dariyar karfin Hali nayi nace kalli kana kwalla kamar ba namiji ba,da sauri ya goge tare da cewa tausayi kuka bani,amma gaskiya an raina miki hankali ma da muke cewa kina da son kudi, jikinsa ya jawoni na kwanta yana rada min words masu sanyi da kwantar da hankali yace I love u ,love u more My Man,bana son fita ma ina da meeting ne ba yanda zanyi,nace never mind zan iya zama, yace Ok harda tsokanata wai idan na tafi ki cinye abincin nan du tunda bakya iya cin abincin a gabana,dariya nayi nace ka tuna cin abincina a gidanka farko daka sace ni? Dariya yayi shima yace ai naga yanzu kin daina wai dan Allah a lokacin nan kuma kalau kike?nace ras ma kayan dadi ne da ban saba ci ba kuma dama ni inada ci da yawa,lokacin idan naga kayan dadi ko cikina zai fashe sai na cinye,Dariya mukeyi,amma yanzu kin daina ci da yawa amma dai ba laifi akwai cin nan yana nan, ga iya cin abinci abinci a kitchen,sai azo ayi ta min yanga ashe kin gama koshi a tukunya, dariya na dingayi ina rufe fuska tare da cewa ashe ka sani? Ka kureni lallai kamar Aljani haka kake Allah,amma ai gwara naci na koshi ko? Murmushi yayi tare da tura hannunsa a rigata yana wasa da Boobs dina yace ai nafi so wannan su kara girma kullum su zauna a haka kar su rame, oya muje ki rakani zan wuce,Sai da ya kara brush tare da gyara wankansa sannan na rakashi har mota,nan ma a ciki haka muka dinga kissing din juna kamar baza mu rabu ba da kyar na kyaleshi ya tafi ina daga masa hannu.

Ban dade da dawowa ciki ba na gyara upstair dinmu komai kamshi yake a gidan,sai ga su Meenat tare da Ameer sun shigo suna kwala min kira, fitowa nayi cike da murna nace Ina Ma'eesha kuma? Saloon zata je gobe akwai schl,Ameer ka gujeni yanzu gida daya amma su Meenat sun fini ganinka,Haba Anty ni na isa damuna tayi da waya tayi missing dinki nazo na kawota, mene a flask din nan? Ammah ce tace a kawo miki kunun gyada ne,Godiya nayi na karba tare da kaiwa kitchen,Meenat ta kalli Ameer bari na gano Dakinmu Allah sarki nayi missing dinsa,kyaji dashi cewar Ameer, abincinka fa Ameer tun safe baka nema ba,a gidan su Meenat nayi Breakfast fa Anty,nace lallai Ameer dakai ma za a hada baki a gujeni ka kyauta,dariya mukayi gaba daya, nace ban baka labari ba My Man fa ya min kayan lefe baka gansu ba sun hadu,Ameer yace ai Meenat ta bani labarinsu,munafuka har ta fesa maka? Dariya yake yace haba Anty Ba munafunci tayi ba.

Magana nayi ba alamar wasa nace Ameer wai Aayan ya maka mata? Ameer yace ni din? Ban San zancen bama,nace to na rigashi ko yace ya baka mata kace na rigada nayi maka mata ni, Ameer dariya yayi yana tunanin wasa nake,nace wlh ba wasa nake ba,Anty wacece takin da kika Zaba to? Nace Meenat,ido ya zaro tare da cewa a'a gaskiya ai masifa zata ta yi min bakya ganin ta rainani gwara dai naji idan ta Ya Aayan tafi sai na karbeta Amma Meenat kina ganin yanda take iyayi tana ji da kanta,dariya nayi nace to ai kafi Meenat iyayi kai,i dan kuma bata sona fa? Nace a'a kai dai kace kawai Zabin Aayan kake so shine dan uwanka,Ameer yace haba dai ai wlh nafi son zabinki Anty,to ko Meenat dince baka so? Ni na Isa yanda take me kyau haka da tarbiya ai ta fiki kyau ma Anty sai yanzu na gane duk Meenat tafiku kyau,Dariya nayi nace karya kake kuma wannan a wajenka dai zaka ce amma a wajen Aayan nice gaba,haka Yarima kuma Ma'eesha ce,muna Hira sama sama sai ga Meenat ta fito tare da daukan uban wanka,da mamaki na kalleta nace dama kuna da kaya a gidan nan ne? Ina kuma kika samu gown haka? aro nayi cikin na lefenki,nace aiko baki isa ba koma ki cire tun ma kafin Mijina ya dawo ya ganta a jikinki ban masa kwalliya da ita ba,Dariya tayi tace to wasa nake da abata nazo a jaka ko Ya Ameer?yace kwarai yana daga kai da sauri kamar uwarsace na magana.

Gefen Ameer ta zauna tare da masa magana kasa kasa ba a jin me suke cewa sai gani nayi sun Mike wai zamuje mu dawo,nace ina? Ammah ta sani fa gidan kawata, dama ba wajena kuka zo ba ashe,yanzu fa zamu dawo am serious,sai kun dawo to,suna fita sai ga kiran Aayan ya shigo wayata.
Dagawa nayi fuskata dauke da murmushi na rangada Sallama cikin muryar da nasan ina zuke masa numfashi,zaki sa na dawo Sweet Heart,wannan murya me zaki haka ,Ya Office to,Yace alhmdllh,good kace da wuri zaka dawo amma shuru am missing u,Wani sanyi yaji a ransa yace 2pm zan gama just wait for me I wl be thr,Fari nayi da Ido kamar yana kallona nace Allah ya kaimu,me zaka ci? Kin san me nake so just make something delicious for me Baby,alright Insha'allah zanyi,kiss ya sakar min ta waya nima na aika masa,ina kukan shagwabata can kasa kasa nace kaga su meenat sunzo sunyi tafiyarsu yawonsu gidan kawaye dama ba wajena suka zo ba kuma tsoro nake ji Daddy yayi nisa da part dinmu da sai naje wajensa muyi hira. Laifin Ameer ne bari na kirashi sannan ya kashe kamar kar mu rabu,nan take ya kira Ameer yana ta Masifa Lallai su dawo su tayani Zama kafin ya dawo,ko Minti 10 Meenat batayi a gidan kawarta ba ta fito Ameer ya dawo dasu yana bata labarin masifar da Aayan ke yi, suna dawowa na dinga musu dariya, kitchen na shiga na fara shiryawa Mijina abincin da nasan yafi so fiye da ko wanne.

12am cikin dare Hajja ce ta fito direct dakin Mazan gidan ta shiga sabo da wai dole sai ta kama Aliyu da Sabeer,Suna ta bacci gasu nan birjik wasu a shimfida kasa wasu saman katifa,Sabeer yana bacci sai duka yaji a gadon bayansa,yana bude ido yaga Hajja ce sai ya kara shigewa bargo,Hajja ta girgiza shi amma yaki tashi sai ma maganganu da yake wai na mafarki,kan Aliyu ta koma ta fara tashinsa,Aliyu dama ba a tashinsa a bacci magagi ne dashi idan ya farka sai ya rufe mutum da duka kuma a bacci, yana farkawa ya rufe Hajja da duka gashi Namiji hannunsa Zafi ba shiri Hajja ta kwace da kyar ta bar dakin da dan gudunta,Abbi kwana uku kenan yana fita duk inda yasan zai ga Ameer da mutanen da zai tambaya amma babu labarinsa,yauma gwiwa ba kwari ya dawo gida ana Palo a zaune kowa da abinda yakeyi Abbi ya wuce a fusace ta palon ana masa sannu da zuwa ba wanda ya saurara ya kara gaba cikin Bedroom.

Mujaheed ya bude sabuwar Rezarsa yana yanke farcensa tun kafin ya yanke yatsa daya sai ga Meenal tace idan ka gama dan Allah ka bani na yanke wani farce da ya taso min yaki cirewa, Aliyu yace idan kin gama ki bani nima na yanke nawa,Wata uwar Harara Mujaheed ya zabga musu tare da cewa jarabar gida ko Kashi ka taba sai wani yace ka San masa zai taba shima ba tunanin ma cuta ta shige ku ko ina da ita ku kawai a baku.
Yana gama yankewa Sajeeda ta karbe ta gama ta mikawa Aliyu,Aliyu ma ya gama ya bawa Meenal,ta gama ta dan ajiyeta a gefen kujera sai ko yar karama Juwairiya ma ta dauke harda zuwa ta kyasta Ashana ta konata wai ta kashe cutar jiki duk kan rezar ya disashe ba kaifi amma haka ta yanke da kyar.
Khaleel kuwa wanka yakeyi ana ta jiran botiki ya fito ya bayar amma yaki fitowa yan matan duk da daura kirji suna jiran botiki, yana fitowa ya kallesu wai sabulunsa ake jira haka da botiki,sabulun ma duk ya gama narkewa Saura kadan,Ba tambaya ba komai Haneefa ta fisge tare da lakeshi a jikin sosonta,Sabeer ya faki idonta ya fisge har soson nata dama sabulun yana manne jiki bazai fita ba,haka ya shige wankansa yayi da sosonta,Khaleel baki bude yake kallonsu yace wai Ku ina sabulun da aka siya ne shekaran jiya?kowa an bashi nasa fa,sukace to ga wanka ga wankin su Inner wears ya zamuyi duk karewa sukeyi sabo da wanki kasan dai mata ba irin maza bane,kuma wlh gidan nan satar sabulu akeyi da nawa dana Meenal sacewa akayi,Aliyu yana daga Toilet yace nima wlh ina ajiye nawa jiya kafin na je Palo na dawo an dauke kuma Dan masifa ka rasa waye,Abbi ne ya fito tare da cewa wa dauki toothpaste sabo wani karami MyMy a saman gado na? Kowa yace ba shi bane,yace wlh duk Wanda bai fito dashi ba sai na kai sunansa wajen Malami ya mutu kafin safiya,Ko cikinsa ya kumbura dam cikin dare yayi ta tsaga ihu sai ya fito dashi,yan iska barayi,to wlh ban haifi barawo ba,da mu zauna da barawo gwara ya mutu,na gaji da sace sace da akeyi a gidan nan,dan Bala'i ko Guba ce a gidan nan ka ajiye sai an sata,to ko a fito dashi ko gobe wanda ya dauka ya mutu,Dama Juwairiya ce Ashe ta sace bata fi 14yrs ba bata da wayo jin ance mutum zai mutu ko cikinsa ya kumbura sai ta faki Ido ta dakko tace bari na tayaka dubawa Abbi tana shiga dakin ta daga Haukarsa ta sa a ciki,Abbi ya yarda da yarinyar ai yara baza su dauka ba manya ne,tace Abbi ka ganshi kasan hularka idonka ne tsufa ya kamashi,Abbi yace to jeki lallai hankali shi ke gani yarinya,Allah ya taimakesu da yau wani sai ya mutu a gidan nan,yarinya tace Abbi ko yayanka ne?yace kwarai kuwa.

Haka suka dinga layin wanka jikin mudubin dakin matan kowa ke shiga sabo da Vaseline din Meenal duk sun jere a wajen kowa na shafawa mata da maza,Dan Allah Khaleel ka matsa haka duk ka tare wajen sai wani taje suma kakeyi kazama da ita,Khaleel yace da Namu gashin da naku mata waye nasa yafi tsafta mu kullum sai kanmu yaga ruwa,ku fa mata wata ma sai tayi 3wk gashinta bai ga ruwa ba,kazamai shi yasa Bana son mace ta matso min da kanta kusa dani,Kazamai ba cewar Haneefa amma ba irinmu ba,dariya Khaleel yayi sabulu iri daya dai muke wanka hakan ma ni nake baku na wanki,shi dama Khaleel sabo da sabulu ya dade baya siyen na wanka na wanki yake siya yanzu ga araha gashi kato a dade ana wanka.
Da su Sabeer zasu siyo sabulu cikin kudin da suka damfari Hajja Khaleel yace kar a siyo masa sabulun wanka na wanki yake so gaba daya,ai kuwa kowa sabulun wanka daya dana wanki daya amma Khaleel nasa Sabulan wanki har guda Hudu da kudinsa shi yasa yake shanawa da abinsa duk an takura masa da aro.

Washe gari ma sabo na wanki ya fito dashi yayi wankansa,Abbi Sani da Abbin yara duk karbewa sukayi dashi sukayi wanka,dama Khaleel da yaji kira yasan sabulunsa za a karba,shi yasa ma ana cewa Khaleel sai ya dauki Sabulun ya tafi wajen kiran.
Yauma suna zaune a Palo Abbi Mustapha ya kwala masa kira da sauri ya koma daki ya dauko sabulun Sodarsa na wanki yana kumbura baki yaje tare da cewa gashi ai kuwa Abbi yace yawwa dama kiran kenan jeka, Khaleel ya juyo yana masifa dama nasan kiran kenan,Me ake mana a gidan ba asan a bamu hakkin mu ba,muna bukatar kayan sawa,takalma,kudin kashewa,bare azo kan su mota gida da aure duk banyi wannan yanzu ba sai yaushe zanyi kenan gashi kullum tsufa kamamu yakeyi ace na wuce 30yrs sai yaushe zanyi kudin bare aure gaba daya ma basa ta mu ta Kansu sukeyi

Mujaheed yace ai ko su Sabeer sun isa aure to bamu da aikin yi bare mu tallafa musu suma ina ma muka iya da kanmu sabulu yana gagararmu,na buga lissafin yaki bullewa, gashi jarabar dangin duk talakawa bare su tallafa cewar Khaleel,Khaleel yace da ace muna da yan Uwa a lagos da wlh tafiya zanyi na makale a wajen wani ko zan samu abin yi,Sabeer yace ina duk suna kauye Wlh babu wani jinin birni ko ace a kudu suke bare muje neman agaji,Aikin ma yanzu sai da hanya zaka samu siyan Offer akeyi,Aliyu yace Ku Allah ma ya taimakeku kunji dadi kun gama Degree gashi har wasu kasar kunje ko ba komai kunci,mu fa?yanzu mukeyi mota ma lokacin Abbi hanawa yayi Aayan ya bamu wai zamu lalace,kai rabu dashi shi bamu San me yakeyi ba a wayarsa duk hotunan yan mata ne yan dagwas dagwas dasu yake chat,wata rannan duk talaucin nan a waya naji sunayi da Abbi wai zai aika mata da kudi za a bata kasonta, ita kuma tana Darling ayi sauri unguwa zanje fa😍😍,Allah Khaleel? Meenal ta tambaya yace tab ai kune mata kuna gida baku san me su Abbi sukeyi ba,mu mun San komai ke ai duk manyan nan dai dai ne na gari,musamman Abbi Sani kina ganinsa haka yan matan da yake kulawa bamu isa mu masu jini a jika muje ba,ai Duniyancinsu kawai sukeyi shuru mukeyi dan kar su Umma suji gwara a zauna lfy.
Haneefa tace karuwai ne?to mene in ba Karuwan ba cewar Sabeer,rannan zaki ga wasu sanda muna wancan gidan sunzo muke cewa yan maula?ai ciki harda budurwar Abbi Musty,hhhh suka sheke da dariya wato Musty ma? Khaleel ne ya kalli skin dinsa dai dai lokacin Hajja ta fito da kwano a hannu,Khaleel yace rayuwa sai Imani tsohuwa kalli fatata yanda take komawa,yaushe zan ji dadi ne?ga duniya gudu takeyi,maza matasa mutuwa sukeyi tsoro nakeyi kar kwana na ya kare Hajja banyi aure naji me akeji ba,ke kinji dakinki da dan mijinki har kin haifi su Abbi ko? Mujaheed yace kai Hajja ance a zamaninta yar soyayya ce baka ga duk jahilcin mutanen da sai da Hajja ta auri Bature Baban Daddy,Sajeeda tace Allah dai ya biya Hajja anci duniya,s una ta dariya Mujaheed yace ai da munyi rako duniya kuwa idan bamuyi aure ba munji me ake ji muma,Hajja tsaki taja tace yan iskan banza tayi gaba, Mujaheed yace kai yanzu Men cuta ta kama wani a cikin halin da muke ciki ai shike nan kuma sai mutuwa wlh ana kallo zai mutu ba kudin magani,

tagumi Khaleel yayi yace Shege Ameer yana can Allah ya Zabe shi,Haneefa tace idan zamuyi aure yayi mana kayan daki,Khaleel yace a yau naga dama sai na nemo inda Ameer yake wlh amma bazan nemo shi ba duk muci wahalar tare sai kowa ya gane kurensa a gidan nan,Mujaheed yace wlh ana nemoshi tsohuwar nan dasu Abbi zasu koma takurawa mutane kyalesu iyakaci idan mun gaji mu fece wajen Ameer mu barsu.
Sajeeda tace sai na fadawa Abbi,Khaleel yace fadi dan Allah wlh da sai na barar dake a gidan nan dama cike nake da zafin talauci,Hajja ce ta fito tare da cafko wuyan rigar Sabeer tare da cewa ina kudina dan Ubanka,Sabeer yace Hajja wai ance miki kudi ne suka makale a Internet zasu zo ta rigada ta turo su suna hanya,Hajja tana zaro Ido tace yaushe zasu iso? Aliyu yace nan da kwana Uku ko hudu,Hajja tace Allah ya kaimu wlh idan basu zo ba sai nayi maganinku,Su Khaleel suna ta dariya Hajja tace zaku ci ubanku gaba daya a gidan nan wlh sai nayi maganinku,dariya sukayi gaba daya tare da cewa hooo Hajja Rayuwa sai Imani, Banza tayi dasu sannan tayi gaba zuciyarta na suya,

A kwana a tashi tun su Khaleel basa tunanin neman aiki har suka yi shawara gwara su nemi na Kansu wahalar ta ishesu haka,amma kuma ta ina zasu fara neman na kan nasu.
Waye ya daukar min takalmina?Mujaheed yana cigiya,ya fito da masifa Haneefa tace Aliyu ne yasa ya tafi schl,tsaki yaja yanzu sai na jira shi ya dawo gidan nan dan masifa idan kana da abu kowa sai yayi amfani dashi,hakuri zakayi lokacin da muke gidan jin dadi wa yake kula kayan wani kowa da nasa cewar Abbi dake zaune yana jinsu.

Yau Saturday ba schl tunda dama mun koma hutu,Meenat kuwa tayi Candy wata za a nemo mata University, Ina wajen Daddy Muna hira yace 'yata ki daure kiyi min wani aiki,nace Na mene Daddy? Aayan zaki sa ya dawo dasu Hajja gida tare da yan uwansa,bai dace hakan ba,babu wanda ya isa ya shiryar da wani sai Allah,kuma ba lallai wahala

Please Login or Register in order to submit comment