Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

furucinta nasan sai ta aikata,ina jin ba Meenat nayi tunanin itace sabo da sunyi fada a wurin party Aayan yace sunyi ma da Wannan marar jin ya furta yana dungure min keya.

Na dinga tsinewa Sameera kuwa,Meenat tace to sarkin Mita yau kwana za ayi ba bacci kina nanata zancen nan,ai kuwa Ameer har ya tafi idan na tuno sai nace Ohhh ke duniya Allah dai ya tsinewa Sameera,Aayan yace addua zaki mata,bazan bata bakina ba nace,Meenat sun kwanta nima munyi shirin bacci ina kusa da Aayan yana zaune Saman Bed yana danna waya, nace Hmm Amma Sameera Allah ya wadaran Halinta,kallona yayi yamin shuru har ya gama abinda yake yace kwanta ki daina damuna da wata Sameera,nace Allah ai Sameerance yar Iska ta bani haushi na kwanta a jikinsa,munyi shuru har bacci ya fara tafiya dani na tuna nace Wai Sameera tana da iyaye,tsaki yaja ya juya min baya,juyowa ya sakeyi tare da rungumeni ya fara Romancing dina na zare hannunsa daga jikina tare da cewa kyaleni naji da jimamin abinda ya Dameni Sameera Allah ya kwaso jarabar duniya data lahira ya.....bakinsa baji cikin nawa,Na kwace baki na nace inba sai naci uban Sameera ba Allah ya....Ni ba Uban Sameera ba dai cewar Aayan,sai na tuna me yake nufi nayi shuru duk yanda yaso na bashi dama mu Sha murje murjenmu naki yarda ni jimami nakeyi,muryarsa naji cike da haushi yace Allah ya isa tsakanina da Sameera tazo kawai ta Rusa min Harka,Dariya nayi tare da cewa kaima ka dawo hanya ke nan? Yace yau kwana zanyi ina kwashewa Sameera Albarka ta cuceni.
Zancen muka Dena amma ya hanani sakewa da tabe tabe ban san sanda na mika wuya ba muka Sha romancing dinmu cikin nishadi da jin dadi.

Kwana biyar tsakani yaune kuma Hajja ta tasa keyar Ameer suka tafi karbo magani dole ba yanda zaiyi gudun kar ta gane ya bita sai da suka gama zagayensu dama duk ta sanar musu a waya an hada komai, duk wajen Malamin da suka je sai Ameer yace Malam to kuma me zamuyi wannan magani ya karye ko munyi aiki dashi bazai ci ba?ya dace mu sani gudun kar mu bata rawar mu da tsalle,Hajja har murna take Ameer me kaifin basira ne,bata San so yake duk ya karya maganin ya watsar dasu ba,bai so ya kona kar azo wani abu kuma ya samu Su Mufee,gwara komai da ilmi.

sai da suka huce gajiyar Hanya tace to Ameer gasu ka tafi dasu duk nayi ma bayani yanda zakayi amfani dasu,dana abinci,dana sawa a cikin pillow,kasan gado,da wanda zaka samu ka yafa mata a jiki ba tare da ta gane ba,Ameer yace an gama ya wuce da magunguna,cikin dare duka ya fito dasu wani Malamin yace ana musu fitsari sun karye,nan Ameer ya fada toilet ya tsula musu fitsari ,wasu Kuma akace idan aka kona etc duk yabi yayi musu yanda Malam yace in anyi baza suyi amfani ba sun karye, sannan ya juye komai a toilet yayi Flowshing gaba daya suka tafi.
Kwana biyu tsakani ya samu Hajja yana murna yace aiki ya kammala na gama komai sai saurare,Hajja tace badai su kamaka ba ko?yace haba ai na girmi tunaninsu.

Kusan kullum sai na je na gaisar da Daddy haka Su Meenat ma, yau ma na shiga Bedroom din Aayan domin mu kwanta na tadda suna waya da Yarima,Aayan yana dariya da gani a raina nace ta mugunta ce wannan, sai naji yace Saura kadan da kanta zata San inda ta nufa ai komai ya tabbata na gane ta gama fadawa sai kuma yanda zan tarwatsa komai,baki na bude a boye na kara danne kirjina sabo da tsorata da nayi ba Shakka ni suke nufi, wani kuka yazo min a raina nace sai an sakeni,yana gama wayar kamar me Aljanu na fada kansa Saman Bed ina kuka sosai na fara cizonsa da yakushi ina kuka nace sai an sakeni wlh bazan zauna ba,yana kokarin cireni a jikinsa ya kasa,Mari ya kwada min har biyu wanda yasa nan take na dawo haayyacina amma ban daina kukan ba,kallo na kawai yakeyi da mamaki bai San me ke damuna ba,shi yasan bai min komai ba,ni kuwa kukana nakeyi,ya kasa cewa komai duk nasa fatarsa tayi jajir inda na yakusa da cizo,jikina yayi Sanyi kuma naga ban kyauta ba,da alama na bata masa rai matuka Allah sarki ina son mijina ni dai Bana fata a sakeni bacin Raine kawai da zuciyar banza me kai mutum ta baro sai an aikata ayi dana sani marar amfani,Shesheka nakeyi naga ya Mike tare da cewa miko biro da takarda a fusace,Nan take jikina ya fara bari ina addua kar ya sakeni,a hankali na kalleshi shima ni yake kallo,nace Dan Allah karka sakeni kaji? Tsaki yaja yace kawo min nace ko,nace dan Allah ni dai dan Allah pls na fasa wlh kuskurene ina son Aurena,Yace ni ance miki mahaukacine ko yaro ne irinki da zakice nayi abu ba tunani nayi,dakko min biro nace ko ya daka min tsawa,jiki na bari nace gashi na dakko na mika masa kuma na rungumeshi tare da dabaibayeshi ta ko ina,a hankali nace in dai akan na yakushe ka ne kayi hakuri bari na biyaka fatarka,Toilet na nufa ya Bini da kallo kawai,ruwa me Zafi a bowl tare da dan towel karami fari na dakko,ban kulashi ba na cire masa riga tare da kwantar dashi tunda yana daga Zaune, yana kallon ikon Allah na gasa masa jiki,yace kin gama?nace ae,yace to kawo min takardar da biron a rude na fara ina ina da soshe soshe na kashe light duf na cire kayana duka na shige masa jikinsa gaba daya na sukurkutashi,yace ba abinda kike nufi zan rubuta ba fa abu zanyi Jotting na Office nace ni gobe kayi banda yau,Sai salo nake masa,yace fada min me yake damunki?idan baza ki fada ba kuma fitar min a room,cike da shagwaba na sanar masa komai da na naji suna fada,Dariya ya dinga yi tare da cewa amma ke anyi sakarai,kin jawo na mareki A banza, to a kan Business muke magana wanda ya hadamu da wata take shirin damfarar mu wai zata mana wayo mu kuma mun fita wayon shine fa kawai,dariyar jin dadi nayi nace budurwa ce ko bazawara? Yace Bazawara ce mene? Hmm ba komai dan Allah tana da kyau? Yace ae mana sosai,baki na tabe jikina yayi Sanyi nace nifa?Ina da kyau? Dariya shima yayi sosai yace ae kina da shi mana,nace hm yaudara dai ko,am serious ya furta nace taya zaka ce tana da kyau nima kace ina dashi ai daya zaka dauka.
Kina da kyau to,nan ma nace ban yarda ba na fara ja da baya zan Mike na bar room din,ya fisgoni na fado jikinsa yace banda Negative thinking Baby ya hade bakina da nasa yana min zafafan kisses idon na lumshe ina mayar masa da martani tare da bashi hakurin abinda na masa shima yace kin jawo na mareki am so sorry,kumatuna na shafa cike da shagwaba nace amma na Maru wlh da zafi kayi min











AsmaBaffa
[1/24, 8:17 PM] Asmabaffa: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–
πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–

KASUWANCI NA







91-95







Official











By
AsmaBaffa









HAFSAT KHAIRAN, NAFEESAT UMAR,CATTY,SUBYUSMAN10 jinjina gareku tare da gaisuwa me tarin yawa ina godiya da Sharhi.


Page na HADIZA MUKTAR yar albarka ina godiya.












Dariya Aayan yayi kadan tare da cewa bakya jine sai kin Sa mutum ya zaneki kin jawo yanzu Bazan taba yafewa Hannuna ba, ba wani nan dama ka saba Marina tun farko ba Imani ka min Dukan tsiya kamar nayi accident da mota ko ina muka hadu sai ka Mareni bai ma dace ace na kulaka ba shine Sabo da banyi ma tunani ba na aureka, Murmushi yayi tare da cewa na daina to ko me zakiyi as from today hannuna bazai taba jikinki da niyyar duka ba,sai da niyyar me to? Romancing,Caring etc ya furta wai dole bazai ce love ba shi, har yau ban gamsu ba ni nafi so a dinga cewa ana sona Amma sai na hakura nayi shuru.
Na manta ban fada ma ba na bawa bakina kudi da kayan kwalliya cikin wanda ka siya mana sai an siyo min wasu na bayar da nawa Sababbin, nawa kika basu,nace hm nayi Barna fa ni kaina naji kyautar nan da nayi har tunani nakeyi ban kyauta ba kayi hakuri Dan Allah dubu goma na kwasar maka,murmushi yayi yace me yasa kika basu har goma bayan ke nasan baza ki iya kashewa kanki goman ba? Hmm kawai naje ne naga kudin naka sunyi yawa wlh gasu a jere a jere suka birgeni naji nima yau so nake na kankaro mutunci na, na zama Hajjaju kawai shine na irga na basu,amma fa a schl suna koya min abubuwa sosai kuma ko me nake so suna min musamman Sayyah,ina wannan rigunan baccin dana dinga sawa masu kyau har kala biyar ka tuna su? Yace ae na gane to Maman Sayyah ce ta bani su da naje gidan,shine na basu dubu biyar biyar ita da Mardiyya,Badan Allah kika basu ba ke nan? Dan ki kankaro mutuncinki kika ce,kin basu kuma kina jimami kina tunanin kyautar da kikayi bata dace ba dama baki basu ba,kinga ba lada kenan kuma Sabo da suna miki kema shine kika rama musu,ba haka ake kyauta ba,iya wacce kikayi niyya ita zakiyi kuma da zuciya daya kisa Iklassi dan Allah kawai ba wani tayi min bari na mata ko ki Bada ki koma kina tinanin kudinki dama baki bayar ba,kinga ba lada sai ma ko Zunubi,kuma 10k ma tayi kadan nayi tunanin ma sunfi haka,amma abinda bana so shine indai kaya ne ni na siya miki to bana so baki amfani dasu ba ki bayar wata tayi,ke na siyawa ke nake so kiyi kwalliya dasu Sabo da ina so naje na siyo da hannuna wasu ma baki san tsadarsu ba shi yasa,idan kina son kyauta to ki karbi kudi wajena kije kisiyo ki ajiye duk wacce zaki bawa ki bata a naki,wanda na siya miki sai in kinyi amfani dasu ko na canja miki new sai ki bayar da wanda kike amfani dasu, haka akeyi ba a daukan kayan miji da ya siyo ki masa kwalliya ko amfani baki dashi ki dauke ki bawa wasu in kina haka Bazan kara bari Frnds dinki su zo.
Mata wasu don son gwaninta sai miji ya siyo miki kaya dan ki masa kwalliya ki birgeshi sai a dinga gayyato Frnds ana basu maza basa Jin dadin hakan.

Sai kuma tambayata yaushe kika je gidan su Sayyah ban san zancenba baki fada min ba? Jikina yayi sanyi nace daga schl rannan mun tashi frnds da yawa suka ce ba nisa daga schl zuwa gidan su Sayyah zasu je gaida Mamanta shine nima na bisu muka tafi tare,su basu da aure ai?ae duk yan mata ne,ke kuma fa? Ina da aure mana, sai akace miki matsayinku daya yanzu? Zaman kanki kikeyi da zaki je wani wajen ban sani ba? Da kika dawo baki fada min ba mala'iku na tsine miki,shi yasa mazaje da yawa basa so matansu suyi aiki ko makaranta idan sun aure su sai a fake da wajen aiki ko schl ayi ta yawo mara amfani,wasu ma daga can suke samun hanyar bin malamai da bokaye ko tarbiyyarsu ta lalace yanzu badan Allah ya kawo zancen ba baza ki fada min ba kenan? Kuka na fara yi masa to kayi hakuri Bazan sake ba tunanina ba wani abu bane,Shi yasa har kasuwa na raka wasu ma daga schl,munje gidajen wasu ma siyo wasu abubuwan da yawa Ban fada ma ba kayi hakuri na daina,kishi ne ya kama Aayan harda kasuwa ma gidajen mutane Maza nata kallonki kamar budurwa? A rude nace ai ban kula su ba Allah duk da yawa sun tareni wai suna sona nace ina da aure,Aayan takaici ya kara rufeshi ana gane masa mata wasu sunji muryarta ma yace daga yau ko an koma schl kin daina zuwa tunda bakya jin magana ni bana son irin wannan, kuka na nakeyi nace ni me nayi to dan Allah? Kayi hakuri Bazan kara ba daga schl wlh sai gida, na yafe miki ai Amma karki sake ki san kina da aure bana son irin shirmen nan na student,kamar an matse bakikin ki gashi kinzo kin fada min ana miki fada ki fara wani kuka,

nace to yanzu duk abinda kaine ka siya min kar na bawa kowa? No ba haka nake nufi ba,sai kinmin kwalliya dashi sosai idan na canja miki wasu sai kwashe sauran ki bayar tht's what I mean, na gane Insha'allah ba matsala,dama kana son kwalliyar tawa ne? A'a kawai dai ke kiyi kyau,wani haushi ma naji kawai nayi shuru har bacci ya kwashemu.
Sati biyu tsakani Meenat ta gama Exam tare da Ma'eesha suka shirya zasu tafi can kauyen Ammah wajen dangi za suyi sati daya daga can su Wuce Maiduguri nan dangin Abba za suyi sati daya, na hada musu goma ta arziki tare da Driver suka tafi abinsu,ni kuwa ina gida tare da Aayan,sai Ameer da yake dan shigowa idan yaga dama bai son yazo yaga muna tare da Aayan kunya yake ji,na tambayi Aayan ya bani kudi na fara zuwa gidan su Sayyah wajen Mum dinta gyaran jiki,haka take gyaran tana bani kayan tsumi,duk na kara cikowa skin dina sai sheki,santsi tare da kyalli ga uban laushi.

Nawwara ta min waya zata zo min again nace bana gida munyi Tafiya bana so tazo,amma Sabo da naci yau Saturday ina kitchen Aayan ya ce na mishi Shawarma na gane yana son Kalar tawa,knocking naji sai da na leka ta yar kafa naga Nawwara ce,abin ya daure min kai to uban me tazo yi nace mata bana nan ana dole ne,komawa nayi kitchen naki budewa tayi ta danna Door Bell shuru.
Khaleel yazo wucewa ta wajen ya ganta a tsaye tsawa ya buga mata wanda ta kusa sumewa uban me kike mana a gida kamar na ubanki anki bude miki ki tafi mana kin cika mana gida Nonsense,jiki na rawa Nawwara ta kama gabanta,Haneefa tana kallonta ta saman Bene tunaninta daga wajena take zata tafi shine taji Haushi an fara cika musu gida da baki,Sajeeda ma tana wajen suna kallo akwai ruwa a hannun Sajeeda roba guda ta dakko zata sha sai ta fasa sha ta saita kan Nawwara ji kake Gaf zafi ya ratsa Nawwara tunaninta Bom ne ya fashe ta kurma ihu ta fadi kasa tana Bom...Bom...ta mike da kyar tana faduwa tana tashi da Rarrafe ta Isa bakin gate,Haushi ya kama masu gadi ta ruda su tana Bom tsawa suka buga mata tare da turata waje suka jefar kamar wanki suka kulle kofa.
Nawwara tana karasawa gida ta fada Toilet tare da barkewa da zawo ga gefen gashinta ya fashe.

Na gama hada masa Shawarma na shirya komai a tire na wuce Bedroom dinsa zan kai masa na bude zan shiga kenan Naji Aayan yana amsa gaisuwa da Alama da mace suke waya da Sauri na shiga Amma sai naji yaci gaba da wayarsa, kwana biyu kiyi Hakuri Ban kira naji ya kike zama a kasar ba,Da Sauri na zauna a gefensa tare da gwara kaina da nasa na jonesu waje daya wai so nake naji Muryar macen ko Budurwa ce Amma bana jin komai,Ya matsa nima na kara matsawa jikinsa,ya matsa na kara matsawa again,kasar akwai dadi yana Murmushi harda wani Ladabi yakeyi na musamman ina jinshi ya gama wayar sannan yace min Allah ya shuryeki nace Ameen ina turo baki idan wayar gaskiya ce a fadi sunan wacce ake waya da ita Mana aji,yace to yar Us ce Sarkin zargi, wa kake dashi a can me jin Hausa na furta nayi kicin kicin,ki bari zata zo Soon kasar nan zan kawo miki ita idan tazo sai ki fada mata haka in kin Isa, baki na turo tare da cewa ni mutunci gareni an cema Allah bata Isa ta zo nan gidan ba ko wace sai na balla yarinya,murmushi ya saki tare da cewa ai ni zan tare mata fadan,da kai zan hada ai sai na mayar mata da fuska ta koma baya,keyarta ta dawo itace fuskarta,Dariya yayi yace Allah ya kaimu dan baki san wace ba shi yasa, ki shirya min kayana zanyi tafiya,gaba na ya fadi rass nace ina zaka je?Us daga can zan wuce Saudiya,Hawaye na fara tare da turo baki cike da shagwaba nace yanzu ni kadai zaku bari? Amma kasan Tsoro nake ji ko ni kadai ban iya zama a gidan nan,Ga Ameer nan zai dinga zuwa yana tayaki Hira Amma da dare kuma sai dai ki kwana ke daya,Yarima na jirana tare za mu tafi zanyi 2-3wks, ganin kamar bai damu dani ba nima kawai na share shi nace a dawo lfy bari na hada ma kayan, zuciya ta a jagule gaskiya baya so na ya kasa sanar dani zai Tafiya sai yau da zai tafi kuma ko ajikinsa irin bai damu da rabuwa dani ba,Allah ya gani nayi kokari na da zan iya,da ace bana sonsa da tuni na fita daga harkarsa Amma zuciyata ta kasa hakura dashi na rasa me yake damuna gaba daya,shi kuwa shawarmarsa ma yake ta ci ko a jikinsa dama Already naga yayi shiri tare da hadewa cikin kana nan kaya.
Harda goge yar kwallata ina hada masa kayansa na gama komai tsab yanda ya dace na ajiye a gabansa, yana cin abincinsa na dauki paper da Biro nayi dan dogon rubu a takardar me Santayana mutum zuciya amma fa ba na love ba,na adduar Tafiya sannan na Sa a tsakiyar kayansa ba tare da ya sani ba.

Yana gama ci ya mike yana kara shiryawa ni kuma na sauka kasa ina palo a zaune saman kujera duk raina a bace yake kadan nake jira sai gashi ya sakko cikin shiri ya kalleni tare da zuwa gabana ya zauna a gefe na jikinmu na Gugan na juna a hankali yace zan tafi Baby, ban san sanda na zabga masa uwar harara ba nace Ina ruwana to ni na nasan da wata tafiyarka ne,Kallona yayi tare da cewa shirya mu tafi tare am serious wlh i wl be missing you is Better na tafi dake,Harara na kara watsa masa ae ai dole kace haka tunda zaka tabe min jiki to Bazan je ba,ba Us ba ko birnin Sin ne Ban zuwa,Har fa Germany? ban san sanda nace Allah yasa Agadaz zamu je hhh ya dinga dariya in bake shashasha ba kin taba ganin inda Agadaz tafi Germany zaki Hada Niger da Germany ne,ina turo baki nace to ko Birkinafaso ce ehe,Dariya yayi yace ke ana maganar Europe kina kawo África,nace to ko Egyft ce harda Morocco kai ko Algeria ce,nan ma yana ta dariya,yace to Saudiyya fa? Nace ko Qudus ce,dan Allah shirya a yau za miki komai mu wuce bana son bana ganinki kusa dani,uhm sai kayi kuma zancen kake so Karuwa taji me Wa'azi tace aiki ne bai isheka ba, Marairaice min yayi sai da nayi mamakinsa kamar wanda ke so na da yawa, wai sai kuma naji tausayinsa Amma na rantse Bazan bishi ba,nace ni Bazan je ba fa,wai harda jin haushina ya juya tare da fara Tafiya,nace Aayan... Juyowa yayi nace zo pls,tunaninsa zance zan bishi ya dawo nace nasan me kake so a jikina tattaba ka tafi abinka kaji,wani haushina yaji me nake nufi?au tunanina ma jikina yake so shi yasa yake taba ni etc Amma tunda haka nake tunanina zai nuna min,tsaki yaja ya juya abinsa,nace a dawo lfy Allah ya kiyaye Hanya ayi addua me yawa Sabo jirgi zaka shiga ba dabara ga wanda aka kwashewa kafafu kasan duk wanda aka kwashewa kafafu kana sama to dabara ta kare sai du'ai,dariyarsa ya danne kawai yayi gaba,Yana fita Ameer ya shigo nasa Katon Hijab dina,jefi jefi muke hira yana ta bani labarin yan matansu da suke yaudara muna dariya, gaskiya Anty gidan ba dadi Ba Maeesha da wannan yarinyar da na sani ma na bisu munje tare naga Kauyen,Bani Address na bisu Allah zanje,Ni kuwa ya ban mamaki kawai dai na bashi Address din, tun daga Lokacin Ameer yacewa Abbi da Hajja tare da yan gidan kaf wai ya tafi Abuja interview Zai nemi Visa a wani Embassy idan ya samu,Hajja tace bazai tafi a mota ba Amma yace a mota zai je,Nufinsa tunda Rimin Gado zai bi su Meenat sai ya kaisu a mota har Airport su shige jirgi sai Maiduguri gaba daya har da shi,Hajja ta damu ita bazai je har Abuja a mota ba sai a jirgi haka ya hakura Driver ya kaishi har Airport,Driver na Tafiya ya shige Napep har inda zai hau motar Rimin Gado ya shiga Drop fyalleliyar mota karama ya biya kudi shi kadai har Cikin kauyen Rimin Gado can rugar fulani.

Da tambaya ya gane gidan da su Meenat suka sauka yan fulani sukace yan matan Larabawa yan birni ga gidan can,Ameer sai wani make jiki yake yana karkabe kayansa tare da tabe baki yana kyankyami wai,a kofar gidan ya tura yaro wai Meenat da Ma'eesha suzo inji Ameer dan Birni,Meenat ce ta fito kofar gidan tasha Atamfa riga da Zani me style tayi kyau,tasha mamaki ganin Ameer ne da gaske to ko lfy ko Mufee ce wani abu ya sameta Meenat ta tambaya da tsoro a fuskarta, kin wani tareni da tambaya zuwa nayi naga kauyenku to Anty ce ta bani Address bakwa gida duk ba dadi shine nazo,Murmushi Meenat tayi tare da cewa kayi Kokari bari na fadawa Inna to,
Wajen Inna tsohuwa tazo ta sanar mata,Inna tace to kuma sai ki barshi a waje gidan tsohuwa ne kice ya shigo,Maeesha ce ta fita tana dariya tace lallai ya Ameer kayi Kokari ina motarka?ke zan mareki ko wacce sai tambayar tsiya,shugo to ciki,Ameer yabi Bayan Meenat suka shiga gidan,komai na kara ne dakuna Uku irin na ruga,Tsohuwar yayar Ammah ce ita kadai ce a gidan sai jikanta babba kuma ya tafi kiwo can wani daji sai shekara ta zagayo zai dawo gida tare da shanunsu.

Gidan Babba ne me dan fadi tare da katuwar bishiya a tsakar gidan,yasha shara tsaf dashi,Ameer da Ladabi ya gaisar da Inna,da Fara'a ta Amsa sannan tace to ajiye kayan naka ga dakin da zaka zauna can,ke Meenatu kai masa kayansa,Meenat ta rakashi dakin tabarma ce katuwa sai katifa yar siririya dai dai mutum daya ko juyi sai daΓ­ ka mike sannan ka juya,Ameer ya dinga dariyar katifar tare da cewa sai kace ta jarirai wannan har katifa ce,ni Yanzu ya zan iya kwana a nan kato dani? Daki yasha tsafta dai ba laifi Amma katifar nan gaskiya kice ta canja min wata,Meenat da Sauri ta sa Hannu tare da toshe masa baki tare da cewa rufa mana asiri kunnenta kamar micijiji yake masifaffiya ce wlh ta gaske bar ganinta haka kunyi faran faran yanzu tayi mana tatas a gidan nan.

Hannunta ya janye a saman bakinsa tare da cewa ke baki da kunya ni kamata zaki toshewa baki kamar yaronki kato dani,ni gaskiya ki fada mata ta canja min katifa,Ai ko karaf a kunnen Inna sai muryarta suka ji tace Iyyeeeeeee... Kai kake bani kudin?ko jikana yana gari ai bazai canja ma katifa ba,duk girman wannan makekiyar katifar yo ni Allah na tuba duk ranar dana kwana a saman ta kasa Sallar asuba nakeyi,har makara nakeyi sai rana ta fito nake tashi Sabo da laushi da girmanta,ba karamin daraja mutum nake Ba zan barshi ya kwanta saman wannan katifar tawa,ai wlh ko su Meenatu basu Isa ba,amma zaka nuna min kai dan birni ko kinibibinka ne? Murmushi Ameer yayi jin yanda

Please Login or Register in order to submit comment