Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bobo.hh

Ina ta nema amma ba a dagawa sai na tuna abokinsa Aayan ne nan take na shirya da yamma wurin 5 lis na rubuta yar takarda na tafi har gidan su Aayan nasan ba lallai a barni na shiga ba kawai na mikawa wani security nace ya bawa Aayan,yace ai yana gida ma jira ya kai masa abinda yace sai na fada miki,nan ya tafi ciki ni kuma ina daga wajen gate ina faman jira cike da tsoro kar yan matan nan su dakeni ko Aayan ya wulakantani.
15mnt sai gashi ya dawo yace wai ki shiga yan mata,yace ayi miki iso,a tsorace na bi bayan Mutumin mukayi tafiya me uban Nisan gaske kamar zamuje wata unguwar yan aiki kawai muke wucewa har muka isa wani part wanda ban san dashi a cikin gidan ba ya kai karshe wajen tsaruwa har Palo aka shigar dani sanyi da kamshi ya daki hancina har wani bacci nake ji.
Daga shi sai dogon wando ya fito jikinsa ba riga wow...wow Innalillahi ko wace sai taso ta kwanta a kirjin Aayan sabo da tsananin kyansa wayyo,nidai nayi kasa da kai ina jin kunya,cike da Izza ga masifa yace karki kara zuwa gidan nan da zummar kina nemana wajensa kika je can da matsalarku,ni da kika ganni dana taimaka miki gwara na zubar da kudin,kuma sai na baki punishment na aiko min da takarda da kikayi wai na fadawa Yarima Number kaza ta kirasa ya kiraki back ni zaki aika? Look at u Nonsense yaja tsaki a gabana ya zura farar riga ko kunya babu yace follow me,haka na bishi kamar Rakuma,abin haushin duk kusan mutanen gidan kowa ya fito a wannan lokaci duk part in muka zo sai mun iske mutane mata da maza dattijai duk yan uwan Aayan,kowa baki bude yake kallonmu yana gaba ina baya,shi kuwa Gogan ko kallonsu baiyi ba bare su sa ran yasan da zamansu kayi masa magana bashi da mutunci dole sukayi shuru sai kallo da mamaki kucaka kusa da Aayan kuma a part dinsa to karuwa ce? Nan take yan matan da suka dakeni suka ce Mommy wlh akan wannan yarinyar ya dakemu rannan kamar zai kashe mu karuwarsa ce,Abbi dake fitowa shima yace haka zancenku yake yaran nan.
Hajja kakarsu Tsohuwa me ji da kai da kudi tuni labari ya kai kunnenta cewar maganar Abbi gaskiyace cewar Aayan mata yake bi na banza don haka ya Zama dole a dauki mataki a kansa tsatsaura,ranta ya baci amma tace zata yi maganinsa.

Ni dai a tsorace nake har muka karasa wajen mota yace get in the car,ba shiri na fada ciki sabo da na matsu na bar gidan a tsorace nake,Driver ne yaja ina baya,Aayan yana wata motar daban wannan gidan nasa muka shiga,da sauri ya fito nima na fito ina murna Allah yasa ya bani irin abincin ranar nan,ban San me yasa Bana Jin tsoron komai idan ina tare da wannan masifaffen Aayan ba.

A baya na bishi har ciki yace Oya fara gyara gidan nan,da sauri na fara aikin sai da na gyara komai yana sheki duk da cewar dama ba wani dirty kawai mugunta ce,sai da na gama ya sani kneel down hands up na Sha wahala sannan ko ruwa bai bani ba ina kallo yana ta cin abun dadi da lemo haka yace na tashi na bar masa gida,ba shiri na Mike da sauri domin magrib ta kusa ina tsoron Ammah,har zan fita sai na dawo gabansa yana daukan wani abu kamar hanta yana ci yana kora lemo na faki idonsa na dauke ledar zan kwashe da gudu ya sa min kafa nayi muguwar faduwa a kasa,a fusace yayi kaina nasan duka zanci kawai na fara kuka amma ko tausayi yana huci zai mareni sai kuma ya fasa hannuna yaja tare da jefani waje ya banke kofarsa,sai da na ci kuka na sannan na Mike tare da karkabe jiki na,zan fita kenan wani cikin yan aiki yace kiyi hakuri kinji ki daina shiga sabgar Oga wlh baya kaunar mata ki kiyaye ba abinda bazai miki ba kuma bazai taba nadama ba,ke naga yana daga miki kafa ma wlh da wasu ne ko hanyar da yabi basu isa sun bi ta ba,amma ke har yana kyaleki ki shiga gidansa har ya saki aiki,a raina nace ni ina ruwana da zai taimakawa Ammah ai da na yarda ko kullum yankar naman jikina zaiyi ba matsala,haka na fita na bar gidan na koma gida, my
Ammah sai fada take min ta gaji da yawon da nake ranar ta sa min doka tace bazan kara fita ba sai bayan sati biyu ko me za a siyo Meenat ta karba taje ta siyo.

Tun daga Ranar ban kara fita ba ko kofar gida Ammah ta hana,ina zaune da wayata ina game Ma'eesha na kallo Meenat ta tafi cefane kawai sai ga kiran Yarima,jiki na rawa na daga muka gaisa yace gobe na kai Ammah Hospital din an gama biyan komai da komai,sabo da murna ban san sanda Hawaye suka kwararo min ba,na dinga godiya ina masa addua yace ba komai ko mene ake ciki na kirashi a waya,nan take na sanarwa dasu Ammah kowa murna haka ma Meenat da ta dawo harda Rawa,ranar har Nafeela mukayi na godiya ga Allah.
Washe gari da wuri muka shirya tare da daukan Ammah a napep muka tafi asibitin Murtala.
Ba bata lokaci akace Doctor mu yake jira an biya komai da komai yau za ayi wa Ammah gashin kashi tare da sauran aikin da za ayi mata,muna ta addua aka shiga da ita.
Abin da ya bamu mamaki shine abinci lafiyayye na resturant take away tare da ruwan roba carton biyu,tare da lemuka iriri sai fruits da kayan hada tea duk aka dinga shigowa dasu wai inji Boss dinMufeeda,ni kuma tunanina ya bani dama Yarima ne,kuma ina tunanin so na yake.
Haka harda su flask na tea dana abinci da cups tare da spoons sai plates wai duk inji Yarima,abin ya bamu mamaki muka dinga murna,na koma gida domin kwaso kayan jinya,mota wata sabuwa naga tasha gaba na,Aayan na gani kawai sai na karasa jikin motar tare da cewa ina kwana?ko saurarata baiyi ba yace shiga mota,ban so ba amma ya zanyi haka na shiga gaba na zauna ina jira ya kaini inda zai kaini,sai naji muryarsa me sanyi da dadi kamar na suma haka naji,yace karbi waya Yarima zaiyi magana dake,waya na karba a tsorace muka gaisa yace Mufeeda kike ko?

nace ae yace to gaskiya zan fada miki duk kudin aikin nan da komai bani na biya ba Aayan ne ya biya abokina,yanzu haka an fede Ummanki amma baza a dinke ta ba sai anyi deal dake akwai sharadi idan kin yarda sai a karasa mata aikinta ta tashi idan baki yarda ba kuma a barta haka ta mutu,a firgice tare da fara kuka nace mene sharadin?yace Aure za a daura muku da Aayan na kasuwanci domin shima a gida ance dole ya kawo mata ko a bashi wata akwai abinda yake so ya nunawa yan gidansu kin gane zai miki bayani idan kin yarda,nan take nace abu me sauki muje a daura indai Ammah ta zata tashi,yace Amma dole sai da danginki nace ba komai muje suna Borno da wasu a kauye nan kano,y ace za kuje a jirgi ai sharp sharp.

Waya nayi da Meenat basu San halin da ake ciki ba nace su kula da komai sai gobe da safe zan dawo,Guess house din Aayan muka je dashi ba tare da ya ko kalleni ba nima haka ina mamakin duniya babu na Allah,muna zuwa ya mika min wasu kaya a kwali yace je kiyi wanka sosai ki sa,da sauri na fada bedroom dake palon nayi wanka da Sallah na shafa lotion da komai kwalliya ce kawai na kasa yi sabo da halin da nake ciki na sa kayan na shafa turaruka yanda nayi kyau abin ba a cewa komai kamar yasan size dina doguwar rigar Arab ce fitted me shegen kyau da ado kamar wata Amaryar Larabawa haka ba dawo da mayafinta,black da adon sky blue nasa takalmin da na gani sky, harda wata jaka itama sky,na fito sai dai kirjinsa babu Nonon kirki yan kana na ne dasu kowa yaganni yaga yarinya danya danma ina da tsayi kuma ba kiba ba ramammiya bace,normal nake yar cakwas dani. wayyo shi kanshi yasan na hadu amma sai ya dauke kai yana yatsina fuska,ya shirya cikin sky blue yard me shara shara kamar Amarya da Ango lallai zamu kwashi yan kallo,amma gaba daya zuciyoyinmu ba dadi,ni haushinsa ma nake ji,shima haka,

muje naji yace tare da cewa bani da lokacin yi miki bayanin dalilin aurenki da nace zanyi,amma ina da dalili,ki nutsu Rayuwar gidanmu da zaki shiga daban take,da kanki zaki gane me yasa na aureki idan kin shiga gidan,bazan cuceki ba karki sa rai ina sonki, ko zan faranta miki,ko zaki ji dadi no Kasuwanci ne deal ne,zan biya ki kudin da zaki kula da yan uwanki kuji dadin duniya tare da Ummanki zan biya mata kudin hospital da komai,ko mene kike so a duniya zan baki,ni kuma zaki aureni ki zauna cikin kunci dan baza ki so Zama dani ba baza kiji dadi ko da minti daya ba,sannan ga matsalar family na sai kinbi a sannu zaki gane matsalarsu ko kiyi Nasara a Kansu ko suyi a taki wannan ya rage naki,ko da ace ina Sonki na aureki to fa ni bana haihuwa, kuma an auna lafiya nake amma nayi aure har sau Uku ban taba yiwa wata ciki ba,ba asibitin da banje ba,sannan zaki ji ance ina da Hawan jini ina da Diabetes wannan karya ne lafiya kalau Alhmdllh kawai fada nayi dan na samu sauki wajen family ta wani ban garen,bance ki dagawa kowa kafa ba a dangina sabo da ni kike aure ba su ba,amma banda rashin kunya karki soma raina min yan Uwa thts all,idan kin kiyaye zaki samu kudi da jin dadi,sauran yaki ya rage naki,ni dai ina da manufata da burina na aurenki wanda a yau zaki fara ganin daya.lets go,bana bukatar kiyi wani abu dan ki faranta min rai sabo da na tsani mata kaf banda uwata yayi gaba abinsa.

Ni ko a raina ban dauka serious ba tunda bani da wayo yarinya ce ni ga karancin ilmi,ai sai nace tunda zan samu kudin kula dasu Meenat da lafiyar Ammah kawai a daura banyi tunanin komai ba,duk na rude har na matsu a daura domin a mayar da Ammah a dinketa ta samu Lfy burina kenan,abinda ban sani ba tuni ma har anyi aikin an gama komai Ashe wayo suka yi mini dan ba yarda da wuri.
Gidan make up ya kaini da kansa yace na shiga ina shiga naga ana ta karramani Ashe sun San da zuwana,nan fa aka gyara min gashi da kwalliya yar sama sama,na fito shi kanshi saida ya kalleni ya kara kallona,amma sai ya tabe baki na shiga yaja muka tafi sai gidansu dake GRA,a cikin motar yace karki tunanin auren zan sakeki da wuri tunda kema dan kudi kikayi ni aurena ba saki sai da dalili,ni kuwa kudi nake nema dama kawai nace karka damu ni ma dan kudi nayi ai kasuwanci ne kawai nima idan kudin sun isheni zan nemi saki sabo da na auri wanda nake so ni insha'allah kamar yanda nake yar sunna sai nayi auren so da kauna na sunna.

Baki ya tabe ba tare da yace komai ba har muka shiga cikin gidan kafin na fito yace kiyi kamar muna son juna a gaban iya Family na,kudi da Ammah kawai nake hangowa nace to an gama, fitowa yayi nima na fito muka jera kamar masoyann gaske abin birgewa muna tafiya can wani part sai ga yan matan nan da samari birjiki muna hangosu kowa da abinda yakeyi na nishadi,a hankali yace action nan take na tuno kudi da Ammah ta kawai na kakalo murmushi lafiyayye na saki ina masa wani kallo da kowa zai ce Masoyina ne mun shaku da juna.
A hankali yace Good job Ashe lallai Yarima bincikensa yayi gaskiya kina son kudi,murmushi nayi nace na gaske ma kuwa ai na shaku da kudi a duniya bani da burin da ya wuce kudi,Muna tafiya muna magana tunanin mutane ai duk soyayya ce da kallo kawai ake binmu, muryarsa naji yace karki gaisar da kowa nasan ke village girl ce,nace an gama in dai da kudi baza ka samu matsala dani ba,wani kallo ya min yana yatsina fuska muna tafiya,yan matan nan suna ta mamaki yar iska nan Ya Aayan zai aura tab ai kuwa zata ci duka,nan take kishi ya turnike su zai auri wata ba su ba ga mata kyawawa a gidansu yan Uwa,nan take suka ci Alwashin ganin bayana,dan haka daya a ciki ta taso cike da kishi tace ya Aayan badai kazamar nan zaka aura ba,dama itace kace zaka kawota bayan gamu a gidan ka Zaba mana,kallo ma bata ishe mu ba harda ni ,aiko ta fusata tare da jawo gyalena ke yar matsiyata,na rigada na gama rainasu nan take na fisge mayafina tare da cewa kinci sa'a ina da muhimmin Uzuri banda lokacinku amma da kin San yau kin rike gyale me daraja nayi gaba abina,dan ta kara Jin haushi ma kawai nayi ta maza na rike hannun Aayan a karo na farko,yayi matukar mamaki nan take ya canja fuska,nace Business ne ka bari a gama lfy na fika Sanin dokokinsa muje kawai nima ina da dalilina na yin hakan a sannu zaka gane. mamaki
Ya cika shi a fili yace lallai Yarima yayi bincike me kyau,nace ba karya indai akan kudine shirka da kisa ne kawai bazanyi ba.
Muna wuce wajen yan matan na saki hannunsa ya juyo tare da gasa min harara karki kuma taba min jiki,nace an gama sai da dalili duk cikin kudinka,har muka shiga part din tsohuwar nan wato Hajja,tana takama da isa na durkusa har kasa na gaisa ta tsabar tsufa bata gane nice nazo polio ba,cike da wulakanci ta amshe ni,sai ga wasu dattijawa yan gayu su Hudu mata sun shigo nan ma kaina kasa cike da ladabi har kasa na gaisar dasu suma dai a wulakancen suka amsa,sai ga maza manya su Uku sun shigo ciki har da Abbi duk suna kama da Alama brothers ne,suma haka na gaisa su Abbi ya gane ni murmushin mugunta ya saki ya kalli Aayan tare da cewa karuwar taka zaka aura kenan,lallai bariki tayi dadi,dayan cikin su yace ke bafa ya haihuwa ba lafiyayye bane amma kin bamu mamaki da zaki aureshi to mudai baza mu rufe miki cutarsa ba idan kudi kike nema ma ki shafawa kanki ruwa idan kuma tuna ninki aure na gaskiya to kece a wahale,mamaki ya kamani amma na tuno Ammah kawai nace ina sonsa haka sabo da Allah zan aureshi,Abbi yace a ina danginki suke? dangina na uba suna Maiduguri,na kalli Aayan cike da fara'a nace ai munje da kai rannan kasan ko ina ka basu address suje,ido na kifta masa,mamaki ya kamasu karfa da gaske soyayya muke da Aayan gashi ma yasan dangina.

Yace muje na saukeki a gida ko,Abbi yace no Ku tsaya dole da ita za a tafi gaban iyayenta muka sani ko karya take,nace ba damuwa,muna zaune aka shirya tafiya maiduguri a jirgi abinka da Naira,Manyan mata su biyu su Abbi su Uku sai Aayan da ni kuma,ina kusa dashi babu wanda ke kula kowa,wai abinka da masu kudi sai gani a jirgi ina tsoro dai haka na maze,mintina kadan sai gamu a Maiduguri Allah yasa muna zuwa watarana,nasan ko ina,motoci aka kawo musu yan gaske nayi jagora har gidan su Abbanmu,nanfa yan uwansa Allah sarki suka dinga murna cewar Ammah dani mun girmamasu mun basu hakkinsu za ayi min aure amma su aka barwa komai a matsayin su na dangin uba,haba shi Kanshi Aayan yayi mamakin irin mutunci da karramawa da aka musu duk da cewa ba masu kudi bane amma an mutunta su matuka,matan ne kadai suke ta yatsina fuska suna tabe baki kun san dama mata sunfi maza kasa danne abu.

Nan take abin mamaki sukace a daura Aure domin su Abbi su gama shirya mugunta a kaina.
Dangin Abbana sai da suka tabbatar ina so da yarda ta sannan kawai suka tara mutane a masallaci shi kanshi Aayan baiyi tunanin Abbi zai ce yanzu za a daura ba,shi Sam bai ma kawo nan kusa za a daura auren ba,nan take dana sani da nadama suka lullubeshi.

Nima haka har kuka a boye yar yarinya dani yanzu na shiga 17yrs ace za ayi min aure,tunowa nayi Ammah na can rai a hannun Allah,ina zaune naji ana guda kamar wasa wai an daura Sadaki Dubu Dari Uku,ina jin yanda nayi tsada a sadaki na sai gashi ina murna naji kudi domin ni in dai kudi ne an gama kawai,har wani yanga na fara yi daga jin sadakina Dubu Dari uku,Aayan kamar ance an masa mutuwa ya kasa boye fushinsa,nan na karbi Numbers na dangin mu na basu tawa muka musu Sallama zamu dawo Kano,har kudi na dan basu kadan cikin na sadakina da kyar ma suka karba domin Aayan ya basu kudi masu yawa.

Bamu zarce ko ina ba sai kano a jirgi,muna sauka sai kauyen Rimin Gado dangin Ammah mun samu kadan daga ciki na nuna musu kaf dangina an karbemu a mutunce sai dai nace Ammah tace a gaishesu bata da lafiya ne,kamar yanda na fadawa Dangin Abba, sunji ba dadi har wasu sunce zasu zo dubata.
Sharp sharp muka gama komai suma sunsha kudi wajen Aayan amma kowa yasan wannan Ango bashi da fara'a kamar ba auren so ba haka muke dashi sosai yake fushi a fili.

Su Abbi sai kus kus sukeyi ana shirya mugunta.
A ranar muka dawo cikin garin Kano bani da burin da ya wuce naje naga Ammah ta samu sauki,daga ni sai Aayan a mota,yana Driving, cike da zumudi nace kayi waya naji an gama aikin tunda na yarda an daura auren,kallo na yayi a matukar hasale yace an dade da Gama mata aiki tuni anyi komai je ki gani,a hospital din ya saukeni ya figi motarsa ya barni tsaye baki bude da jakata a rataye,nace oho dai ni tunda zan samu kudi shike nan,ya kaga Ammah ta samu Lfy?gashi nayi auren da take buri nayi,na cikawa Ammah burinta gashi nayi auren da takeso,da sauri na shiga dakin da su Ma'eesha ke ciki special room aka bamu sabo da Naira.

Ina shiga gabana yaba da dum ganin su Meenat suna Rusa uban kuka,ga mutum nan a lullube da alama gawa ce,lokacin dare yayi jakata na jefar a kasa a tsorace na karasa tare da bude gawar Innalillahi na maimaita domin Ammah ce tabbas ta rasu.
Zubewa nayi kasa sumammiyya,nan likita suka shigo aka mai Dani gadon tare da rufuwa a kaina da kyar na farfado ina uban gunjin kuka,sai hakuri ake bamu su Meenat suna rungume a jikina,kwana mukayi kuka ni tunanina laifin Aayan ne mugu su suka kashe min Ammah ta gashi ya zalunceni na yarda an daura min Aure dashi amma sunyi ganganci da Rayuwar Ammah ta rasu wayyo Allah,yau ina Algus da nakeyi sabo da maganin Ammah duk sabo da kar ta mutu tasha wahala nake tsoro,kullum yawon neman Kudi na tsallake risk da dama don kawai na samo kudin magani.

Ba tare da Sanin uwata ba naje nayi auren kasuwanci don sabo da kar ta mutu ayi mata magani ta warke,nayi duk abinda zanyi amma kash baiyi amfani ba,sai ma gani nake ina zargin kaina cewar da hannuna na kashe Ammah domin nice na damu sai an mata aiki duk da cewa an fada mana cewar aiki biyu za ayi mata da na kafafu sai kuma wani a cikin Mahaifarta shine me matsalar ba lallai ta tashi ba,amma na dage sai anyi gani nake zata warke,dana sani da nadama nake ta faman yi,Ammah na zaune lfy na damu gashi ashe ta hanyar aikin da kudin da komai amma sai lokacin ta rasu,burina bai cika ba domin bani da burin da ya wuce nayi kudi Ammah taji dadin duniya tare da kannena sannan nayi aure Ammah taga mijina da jikokinta amma kash babu ko daya da ta gani domin wannan auren ma na Kasuwanci ne.
Iya karfina na kwalla kara da ihu,kowa sai ya tausaya mana,kuka muke ba ji ba gani tare da tumami harda birgima tare da shure shure abin sai wanda ya gani,sai da muka kwana cir muna abu daya,gari ya waye ma muka daura. lokacin akace Muzo mu nemo yan uwanmu maza a dauki gawa.
Nan take nayi waya dangin Ammah kaf da Dangin Abbah da sauran makwafta da abokan arziki tuni zancen ya watsu Ammah ta rasu,Allah ya taimakeni dangin uba na ne suka daura min Aure,haka dangin uwata da saninsu.h ar mamakin auren nakeyi sabo da kudi wai nan a rana daya anyi an gama komai gaskiya kudi sunyi a rayuwa.









AsmaBaffa
[1/3, 11:17 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA






21-25






Official






By
AsmaBaffa







CHOICE ths page is for u...😍❤

ASYCOOL ina kika boye ne?



Fans masu sharhi ta ko ina ina matukar Godiya da kulawa ina jin dadi yanda kuke kokarin yin Sharhi abin ba a cewa komai sai godiya Masoya ta ko ina,Allah ya bar zumunci ya biya muku bukatunku na alkhairi,tsakanina daku sai godiya,insha'Allah kowacce da page dinta masu sharhi,shine farin cikina da zan baku na yanda kuke sharhi.loves u all.😍😘😍😘❤❤









Gaskiya duk Wanda ya San Ammah mutuniyar kirki ya girgiza da mutuwar nan,nan take asibitin ya samu halartar dangin Ammah maza da mata da yake mutuwa ce har sunzo mana.da taimakonsu aka bamu gawar muka tafi da ita dan gidanmu na talauci,nan fa dangin Abba ma na Maiduguri sun samu Damar zuwa da yawa,ga yan unguwa harda kawata Nawwara,su Shehu me waya sune kan gaba,Adamu Kansila ma yazo haka aka hada gawa tare da sallatarta aka kaita gidanta na gaskiya,Kuka mukeyi sosai musamman ni da Meenat,Maeesha ba hankali sosai Sam bata ma damu ba sosai har ta daina kukan,mu kuwa sai nasiha ake mana da Wa'azi ana bamu hakuri, washe gari kuwa da safe ana ta kawo mana abinci daga makwafta,ga wani dangin Ammah sun dafa,

Ma'eesha tasha baccinta ta tashi ba hankali ta fara bude abincin iri iri sai ta rufe ta dawo gefe na tare da nuna min da yatsanta tana Sis ni wancan nake so cike da shagwaba tace ni me tiririn can nake so,saida ta bawa mutane dariya,da rana kuwa tana cin tuwon shinkafa tace Sis wai kamar ana biki? Muci tuwon mu musha Kokonmu Ammah ta tafi Rimin Gado kafin ta dawo. haka muke ta amsar gaisuwa,har akayi sadakar uku dangin nesa duk wasu sun tafi sai iya na Ammah mata da wasu mazan su uku wanda suke uba daya da Ammah,makwafta suna kawo mana abinci iri iri kullum,da kudin sadakina nake yin komai na kashe kudi sosai domin mutuwa yanzu kamar biki haka take,Meenat sunji ana ta ce min Amarya Allah sarki jiya aka daura mata aure sabo da har yan unguwar mu sun San anyi auren domin munzo da Aayan tare dasu Abbi sunga gidanmu na asali da muke rayuwa,haka kuma na hada su da wasu manyan dake makwaftan mu tunda mu bamu da yan Uwa a cikin kano sai abokan arziki,gashi Ammah na

Please Login or Register in order to submit comment