Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne a jiki,sai yanzu ya tuna Abbi ke neman Sa yaje tarbo Bakin Daddy,amma abin mamaki baki daga Abuja su rasa lokacin zuwa sai dare kawai dai yace gani nan yanzu su jirani,Abbi yana ta masifa ka wulakanta mutane Sabo da kai ga me kudi ko to kayi gaggawar fitowa,burinsu ya fito ya taka maganinsu,Ni kawai ban yarda da fitarsa ba kishi nake ko wayo zai min macece da yace daga U.S take,nan take na fashe da kuka ganin ya mike da gaske fita zaiyi, a hankali yace mene ne? Ni..Allah ba inda zaka fita,Indai ka fita Bazan kara tayaka kwana ba kawai baka so na,mirmushinsa me tsada yayi tare da cewa kina jin yanda Abbi ke fada bakin Daddy suna jira na kiyi hakuri naje naga ko su waye mana,Yanzu wasu bakin kirki ne da Dare haka ni Dai Allah baza kaje ba na sani ko wajen budurwarka zaka je.

Hakura yayi kawai da fita Sabo da yaga da gaske tunanina yana da budurwa gudun Zargi sai yace Ok na fasa to,murna na fara yi tare da kashe wayoyinsa gaba daya na ajiye gefe,shi kuma yana zaune gefen Bed na zagayo ta bayansa tare da Zura hannayena ta cikinsa na rungumeshi gaba daya a jikina,bai san sanda ya lumshe ido ba jin yanda Albarkatun kirjina suka sauka a bayansa,Kasa jurewa yayi ya juyo tare da matsane a kirjinsa gaba daya kamar zai fasa min Kashi, gaba daya ya tafi dani ban san sanda na biye masa ba alhalin nace na daina yarda yana taba min jiki yanzu sai na bashi wahala Amma sai gashi na kasa jurewa,har mamakin kaina nakeyi yanda nake da Feeling me karfi kan Aayan bana jurewa.
Da Zafi zafi muke Sarrafa juna kowa na nuna kwarewarsa Har Aayan ya dauki Hanyar Cinma burinsa Amma sai kawai sha'awarsa ta tsaya cak ya gagara komai,ni kuwa dama gyaran jikin da nayi nace shike nan na hakura ya samu abinda yake so Sabo da son kudi na bana so nayi asarar kudin gyaran jikina gwara ko mutuwa zanyi kawai ya Mori kudinsa tunda dama danshi nayi gyaran idan ba ayi ba ai na rafka asara tare da bata lokacina.

Kallonsa nayi da tausayi sosai Sabo da yana da sha'awar abin Amma kuma bazai iya ba wannan Masifa ce,sai dai yayi ta shan wahala,shuru kawai naga yayi ya fada dogon tunani,Nace Man ya akayi ne? Har yau baka warke ba ko? Kai kawai ya daga min,da kyar yace min am so sorry na kasa baki hakkinki shi yasa bana son auren nan,amma kiyi hakuri idan kinga da matsala ko zaki shiga wani Hali tunda ban san ranar warkewa ta ba ki fada min duk da ina sonki nasan da kyar idan zan rayu babu ke zan iya hakura, Hawayen tausayinsa ne ya ziraro min nan take nayi Sauri na rufe masa baki nace karka kara ambata in Bazan iya ba zamu iya rabuwa ka daina ba kai ka daurawa kanka ba Allah ne kuma watarana zaka warke,kayi hakuri itace Kaddararmu ba shi nake so a tare da kai ba wlh ko shekara nawa zakayi a duniya zan iya hakura mu zauna tare,Allah idan har kaji ni Mufeeda nace ka sawwake min ko mu rabu ko zan bar gidan nan abu na farko da zaka min kawai ka kaini gidan malamai masu Rukiyya kawai ba kalau nake Ba ko Aljanu sun shafe ni ko an min asiri kaji na rantse.
Ka daina damuwa ko kasawa kanka tunani, na gode Baby Na gode yake ta maimaitawa I love u so much My wife,yanzu in naji kince mu rabu ko zaki barni na...da Sauri na karasa ka kaini Ruqiyya wajen Malamai kawai asiri aka yi mana,Dariya yayi kadan tare da kara kankameni a jikinsa.

Can kuwa su Abbi suna ta faman kiran Aayan a kashe ma wayar,Abbi yace iyyeeeeeee ehhh lallai yaron nan fa ya fara tsallake iyaka dan muna daga kafa ne kawai idan mukayi sake muna jiran Hajja to lokaci zai kure mana,da gani yar iskar matarsa ce ta hanashi fitowa wlh bazai wuce ita bace,Abbi Sani yace dama naga Alama yanzu sai abinda tace Gwara mu fara maganin shegiya,akwai Maganinta Hanifa ko Sajeeda zan bawa aikin su zuba mata a abinci inda da kanta zata bar gidan a nemeta a rasa taje can tayi ta garari a duniya.
Abbi yayi dariya sannan yace ai har kannenta kar a bari su dawo tunda sun tafi dangin ubansu to su zauna can ko su Bita ita Mufeedan su karata can,da banyi niyyar kulata ba Amma yau ta shiga gonarmu,Washe gari da Safe Saturday Ameer yana Bedroom muma haka na hada mana break na shirya a Dining na koma ina taya Aayan shiryawa Sajeeda ta samu yanda zatayi ta bude kofar ta shigo a hankali tare da kallon gefe da gefe ta tabbatar ba kowa a wajen sannan da Sauri ta karasa saman Dining ta bude duk kalolin abincin dana shirya ko wanne ta barbada garin maganin sannan ta rufe a hankali ta juya zata tafi duf Numfashinta ya dauke na wasu dakiku sakamakon ganin Ameer da tayi tsaye a bayanta ya harde hannaye a kirjinsa,yana mata wani wulakantaccen kallo.

Nan take jikinta ya fara mazari, ba zato taji mahaukacin Mari ta ko ina,zafi ya hada ta kamar an dosana mata wuta a fuska,Fisgo wata waya yayi ya fara tafkarta yana Ball da ita,tun tana neman agaji har ta garara,ni kuwa munji kamar hayaniya amma hankalinmu bai kawo ba,Ameer ne ya samu Kwalaba ya fasa tayi cako cako ya jawo Sajeeda kiiii har palo ya zauna saman Kujera,Fuskarta ya rike da karfi tare da dagata,tana kuka tana bashi hakuri tasan Ameer bashi da Imani zai iya yankar jikinta da Kwalaba,kamar me aski ya fara karta mata Kwalaba tun daga goshi jini na tsatsafowa,Sai yanzu muka fito nan muka hango irin muguntar da Ameer ke aikatawa,Aayan ne yayi magana da karfi Ameer me ya faru wannan wanne irin rashin Imani ne?

Gashin Sajeeda ya fisga da karfi tare da cewa confess dan uwarki,nan take Sajeeda tana kuka ta fara tonawa kanta asiri da Abinda Abbi ya sata aikatawa,Ni Mufeeda Salati na fara nace Ameer hada da kirjinta duk ka karce shege a Zane mata ko ina,Aayan yace no..Ameer kyaleta taje mun godewa Allah ma haka tunda ya nuna mana,baki na turo nace ni dai baza a barta ba sai an cire mata farcen kafa na Babban yatsa ta karfi zan tsige shi,Aayan yace ba a nan gidan ba ke tashi ki tafi,tana mikewa na damkota tare da yarda ta kasa Aiko Sajeeda ta fini karfi kawai sai ta rufeni da Duka sosai na koma neman a taimakeni,Aayan yace au Sajeeda naji tausayinki an barki shine zaki dukar min Mata to na fasa,Sajeeda da fuska duk zanen Kwalaba da jini tace ae din tare da gallawa Aayan Harara kafin ta maida idonta ya kafeta da Mari hagu da dama tare da bude kofa yayi short da ita waje ya maida kofar ya rufe,Ameer yace na fada ma basu da kunya.

Nace ai wlh sai naci ubanta idan na kamata sai na karya mata hakori sai na tsoma mata yatsa a ruwan zafi, dariya Aayan yayi yace ai tafi karfinki gashi zata ji miki rauni a banza nan nace ai kyaleta nayi kawai Amma mu fada a wajenmu harda na siyarwa dan Babanta. Kwashe abincin nayi gaba daya na juye a leda na kai Dustbin Ameer ya fita dasu waje,haka na dan dafa mana saukakakken abinci abincin mu me dadi muka karya,s ai mita nakeyi na hana kowa sakewa.

Tunda Hajja da Abbi suka ga abinda aka Yiwa Sajeeda suka shirya Tafiya can kasar Kudu cikin wani kauye wajen Babban sabon bokan da aka basu lbr anyi,
Har wanda ya basu labarin bokan gaba daya da shi aka shirya yayi musu Rakiya banda Hajja ta dai ce Abbi yayi komai.
A jirgi suka sauka a Enugu daga nan suka dauki Taxi wai ya kaisu wani daji ko a garin Enugu tsoron bin hanyar Dajin akeyi Sabo da matsafa sunyi yawa a dajin, Driver yayi ta Maza yana Tafiya dasu yana tsoro ko yan yankan kaine,yana Tafiya yana jan tsaki yana Chaiiiiii Alaji,suna jinsa har dai ya kaisu dai dai inda zasu dan shiga dajin da kafa mota ko machine basa shiga sai da kafa,Suka sauka tare da bashi kudi yace Alaji always making juju Money,go and Meet ur Malam is Better than to visit ths land wooo, u have to be very careful with ths place,ahhh see me see troble because of Money so people can do anything in ths world they can even kill them self,Abbi yace Abeg carry ur Wahala and Go stupid Taxi Man,shi dai me Taxi ya figi motarsa bayan ya gama surutunsa.
Dan cikin dajin suka shiga kadan sannan Me Rakiya yace anzo wajen,Abbi yace ya sunansa kace? Mutumin yace sunansa SHAKYLGANCY sai kace dan India cewar Abbi,ai a india ya koyi har kar nan Alhaji cewar me Rakiya.

Suna zuwa wajen anyi Ado da komai Red Abbi yace Shakylgancy.....Shakylgancy.....Sai ga Shakylgancy bugul ya bayyana kamar Aljani wani me mummunar suffa,Cikin harshen turanci Abbi ya koro baya nansa,Shakylgancy ya kece da daria sannan yace shima cikin turancinsa yace 1million Amma baza a biyashi sisi ba sai in magani yayi suka ce Shakylgancy baza mu iya dawowa nan ba karbi kudi kawai ko yayi ko baiyi ba karbi kawai zamu dinga contacting dinka a waya idan ta kama dole nayi kokari mu dawo,Shakylgancy ya washe hakoransa tare da wani hancinsa kato kamar tattasai ya karbi kudi yace suje zasu ga aiki.

Bayan su Abbi sun fito gefen titi tare da Dan Rakiya suna neman Taxi wata mota ta yan Mafiya matsafa ta shararo da gudun tsiya dan Rakiyar su Abbi shine a gefen titi motar na zuwa tayi gaba dashi ta markadeshi a titin fit kansa ya dinga gare gare kamar Ball a saman titi,su Abbi sunyi mutukar firgita shi da Abbi Sani nan suka ga fa an kashe banza motar ko slow down bata yi ba,aiko su Abbi suka take da gudu suma suka mike titi sambal suna ta yi kamar yan tseren gudu basu san sanda suka watsar da takalma tare da babbar rigarsu ba,dama Abbin Sajeeda cewa yayi suje sun wakilceshi shi tsoron zuwa kudu yake yi tunda watarana a Crossriver akasace wani a gaban sa shike nan ya firgita.

Sai da su Abbi suka yi Nisa sannan suka samu Taxi da kyar ta kaisu Har airport a Hanya suka siyi Sababbin takalma Amma Sabo da rashin Imani ko Jimamin Mutuwar abokin Rakiyar tasu basu yi ba sai Abbi da yayi karfin halin daukan hoton gawar a waya Sabo da ya nunawa iyalansu gashi wancen talaka ne shi da iyalansa Amma an mutu a shirka,nan ba aci ba can ba a ci ba,a kiyaye talaka ka lallaba kanka ka samu a Aljanna.

Yau ni kuwa shirye shirye mukeyi Su Meenat zasu dawo daga Maiduguri Ameer yafi mu Zumudi wurin Magrib sai gasu kuwa da kaya Niki Niki sun shigo sai murna lokacin Yarima yazo sun finta tare da Aayan,sai hira mukeyi muka ci muka sha,Ameer yace Duk kunfi kyau a Kauyen Rimin Gado har kumatu kuka yi,Meenat tace ai baka kyauta ba tunda ka wani gudo,yana dariya yace tab ina wani zan iya zama a wannan garin toilet ce tashin hankali ana kallonka a waje,ga wata katifa kamar ta jariri,dariya mukayi gaba daya muna haka sai ga Aayan tare da Yarima,Yarima yana ganin Ma'eesha wani sanyi ya fara ratsa shi ita kuwa Ma'eesha kunyarsa takeji kwarjini yake mata wata uwar signa ya mata da ido ai ko Nan take gaban Ma'eesha ya fadi rass Sabo da lokacin Ma'eesha ta cire Ameer dama shakuwace Sabo da yawan mu'amula da sukeyi ganin kuma kamar shi wata mace bata gabansa yasa tace ke Ma'eesha shafawa kanki ruwa,
Ma'eesha tana Satar kallon Yarima ta gaisheshi ya amsa cike da fara'a, duk ta kasa sukuni ni kuwa ina gefen Aayan nayi shuru na lula tunanin asara da zata hau kaina kwanan nan na gama kashe kudin gyaran jiki mijin bai mora ba,danni a kan ayi asarar kudin nan gwara na kusa mutuwa na farfado kawai.
a hankali Aayan yace ya akayi? Ya rada min a kunne,ajiyar zuciya na sauke nace kai dai bari kawai asarar kudade nake ta yi kwanan nan,ina ta zuba adashin da ba a dauka,Aayan bai gane me nake nufi ba yace ke na rasa inda kika gado son kudi haka wacce asara kikayi na biya ki? Nace baza ka gane ba a bar zancen Amma ko ka biyani Bazan iya daina tunaninsu ba,tunda har yau me kayan ma bai yabe su ba ko da baki yace kayan nan sunyi sun kuma hadu etc ba a ce min kala ba bare naji dadi da kwarin gwiwar karbar asarar danayi tunda bai samu damar siyan kayan ba.

Aayan iya tunaninsa ya kasa ganewa me nake nufi wani kuma waye wani?to Business sukeyi? Nan fa kishi ya cika shi tab yasan zata iya indai Mufeeda ce zata iya, Yarima Ya rasa inda zai saka kansa dama yake jira kawai su dan kebe da Ma'eesha ya karbi Number ta kullum cikin tunaninta yakeyi,Sai ko Ya mike yace zan tafi Aayan sai mun hadu,Aayan yace bari na rakaka,a'a zauna ban son Rakiyar Katon Gardi ni Ma'eesha kawata ce zata rakani,Dariya mukayi gaba daya Ameer yace da Alama Ya Yarima girma ya fadi ka fada akan yar wannan yarinyar,Meenat tace Ss1 kawai fa,Ma'eesha ta harari Meenat tace Gwara dai ni ko a hanya duk mutanen kirki ke tareni suce suna so ke kuwa fa Kwaja,Fela etc ku bari na dawo wlh na fasa rufa miki asiri dama kince kar na fada na yarda to na fasa Bari na dawo na baku latest a Maiduguri da Rimin Gado,Ameer dama kadan yake jira yace muna jira Sauri yau wlh komai dare bazan kwanta ba sai naji.

Aayan yana Dariya yace gaskiya a rufa mata asiri,Meenat tayi mukus tasan yau Tata ta kare,Yarima ya dan jima yana jan Ma'eesha da hira sama sama duk shima akwai ji da kai bai fiya magana ba Number dinta ya karba ya bata tasa sannan ya bata kudi taki karba,babu yanda baiyi ba Amma taki karba nan ta kara birgeshi sosai.
To yan mata pls a rage nuna zalama wajen Saurayi ko idan kika ga mutum ya fiye yi miki kyauta dan Allah watarana ki dinga jayayya kice baza ki karba ba ko da kina so ki dan dinga kai zuciya nesa sai ki kara birgeshi,sai masu jarabar Rokon Samari abu kawai yan mata Direct kice yi min Kaza ko bani Kaza ko yaushe kuma ba kunya ba komai wlh ba tarbiya ce ba,kina zubarwa kanki mutunci da na iyayenki a dinga daga kafa ana hakuri da yanayi na Babu ba har ayi ta roke roke ba, ko ina wasu zakiji suna wancen ina ba yar manya bace Bazan iya ba na tsani me roko etc.

Ma'eesha na dawowa Ameer yace matso nan Hajiyata ki bamu mu musha,Meenat tace Sis Mufee kin gansu ko,Mufeeda tace nima baza kunne nayi yarinya, Babbar banza cewar Aayan,dukan wasa na danyi masa kadan tare da kwanciya a cinyarsa , Ma'eesha tace kai Allah ya bawa Meenat farin jini samari iri iri tun daga Rimin gado yan fulani suka dinga cika kofar gida.

Farko mun fita siyo pure water muka hadu da wani zai je kiwo da shanunsa ya tare mu yana washe baki idan kun ganshi abin dariya yana busa hayakin wiwi Yace hooai Yan Birni aradu wagga Bingel tana Burgeni, wannan ke nake so ya nuna Meenat tare da cewa Sunana TSITO, nan muka fara dariya jin sunansa Ma'eesha tace in kun ganshi wlh yaci sunansa Tsito wani siriri ne kamar a busheshi gwara Kwaja ma yana da Katon ciki Amma Tsito shi ba dan cikin ma,Meenat tace to Dan Uwarki ai Tsito yafi Kwaja lfy da ganin cikin Kwaja ai na cuta ne,kuma Tsito kyakyawa ne,Ameer yace mu dai ba ruwanmu Tsito muka sani,Ina dariya nace karki kara zagar mana Uwa akan kice dan Uwarki gwara kice dan Ubanki Better,Make min baki Aayan yayi shi Abban shine ba a so ba kyau,baki na turo cike da shagwaba nace da zafi fa...Zan rama ne.

Ma'eesha tace Daga Tsito kuma sai NA AGWAGWAJI shi kuwa a yan fulanin ma dan Daba ne duk wanda yaga Meenat tayi masa magana sai ya farfasa masa jiki,Ameer yace kice dan karamin yaki ta hada,Meenat tace Allah ya bani ya zakuyi dani ehe,Dariya muka dinga yi Jin har Dan karamin Saniya Na Agwaji ya bawa Meenat tana can gidan Inna an daureta za a sata cikin Shanu ana kiwata mata ita,Nace Business Sabo Sarkin Kasuwanci cewar Aayan jin yanda nake ta murna Meenat ta samo Saniya zata girma ta Haifo yayanta.
Ma'eesha tace Arzikin Meenat bai tsaya a nan ba kullum samarinta suna hanyar kawo mana kaji da zabbi muna yankawa mu sha farfesu iri iri,Na ciji yatsa nace me yasa kika cinye a ciki banzaye maimakon ku siyar ku tara kudin ku kawo min ko dankunnen Gold na siya muku dan karami,Aayan ya kalleni baki bude yace da kudin kajin? Nace of Course.

Ameer yace inye to wannan buhun kayan naku fa? Ma'eesha tace duk Samarin kauye ne suka tara mana su danyar Gyada,gero,wake etc,A Maiduguri kuwa samarin Meenat harda Conductors na mota,yan Napep etc me dubu daya me dubu biyu haka muka cinye musu kudi,Nace to ke kuma fa in haka ne kece me bakin jini,Meenat tace tsakani da Allah duk wani me kudi indai kinga rantsatsiyar mota ta tsaya to ba shakka wajen Ma'eesha aka zo zance,ni dai Meenat ina ga asiri akayi min daga me kaji sai me Saniya,gyada da gero tare dasu waken Suya hhhh muka dinga dariya,Aayan yace sorry Sis zaki samu wanda yafi kowa kudi kuma na gari kema,ni kuwa nace Meenat haka Allah yake lamarinsa ni kam Ruwa ta sha aradu,Rankwashi Aayan ya zuba min,Ameer yace ni wlh ji nayi gwara haka ita ba iyayi ba dama Allah yasan manufar jaki shi yasa ya hanashi kaho.

Meenat ta gaji da abinda Ameer yake mata ta mike cike da shagwaba tayi kansa wai zata kwala masa spoon ya mike suka fara zagaya mu a palon muna zaune, sai da na gaji nace Meenat kun damemu can u stop ths Nonsense pls? Meenat tace ai kuna jinsa abinda yake ce min kun kasa yi masa fada,Maeesha ce abar duka ai ba Ameer ba tunda ita ta fada mana,Haushi Meenat taji ta jefar da spoon din tayi Bedroom abinta .










AsmaBaffa
[1/28, 10:00 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA







101-102








Official









By
AsmaBaffa








Mun dan jima muna hira bayan tafiyar Meenat sannan na mike nabi bayan Meenat Bedroom dinsu,Maeesha ma ta shigo,Ameer ma ya tafi shirin bacci,Aayan yana samansa jirana yakeyi nazo mu kwanta,Ni kuwa yau dakin su Meenat nake son kwana Sabo da musha hira ta ganin juna,Meenat tace ban gane ba?Ya zaki zo nan ki Kwanta mana mijinki fa?Nace hira zamuyi,Maeesha tace shike nan mun shiga Uku Meenat baza muyi bacci ba yau,Meenat dariya tayi hmm ai mijinta zan kira mata idan mun gaji,ina kallo sukayi shirin bacci nima na mike na feso wanka na shafa turarukan kamshi iri iri sannan na kwanta gefe,Maeesha tace wai Mufee har yau baki ciki ba? Gaskiya ya kamata ace kina da cikin Aayan,baki na tabe tare da cewa mu ba yan iska bane a kujera yake kwana ina Bed,dariya sukayi Ma'eesha ta kalle ni lallai Sis maida Karuwa yar Iska ni mamakina Banga kinyi rashin ko yar lfy ta first night ba,nima kullum zura ido nake Amma ai nasan tuni Su Mufee an san kan harkar Cewar Meenat, zanci ubanki wlh ni sa'arku ce wai dan kunga kunyi saurin girma,so kuke ko me na kwashe na fada muku? Meenat tace mu ina muka Isa daukan wannan maganganu na manya ki rike abinki dama shawara zamu baki munga ko kamar Aayan yana da matsala ne shine muka samo mafita a Maiduguri.

Masifa na fara wacce mafita uban wa yace muku mijina nada matsala idan banda ta Family nifa bana son Sa ido Meenat ku kiyayeni,Allah baki hakuri ai gani mukayi mu da ke duk daya ne ba wanda ke boye maganar dake damunsa yaushe Mama Mufee ta dawo mana haka bamu sani ba bayan Ammah ta bar mana wasiya rike zumuncinmu,yau miji yafi mu daraja shike nan.
Jikina yayi sanyi nan nace ai kune wlh bakwa ji sam Amma akwai matsala Meenat,lokacin Aayan yana can yana ta faman jira nazo muyi baccin mu Amma shuru shuru sai tsaki yake faman ja yana juyi.

hannun Meenat na rike muna kwance nace Meenat kuji ni ina cikin neman taimako na addua Asara ta hauni,na tafka babbar asara,jikina da kyauna duk nema yake ya kare a banza,jibi uban Hips dina,kalli tun ina karama Allah ya hore min na shanu masu kyau da birgewa,kalli skin dinmu,amma a haka aka ce idan kana da kyau ka kara da wanka kalli yanda nake zabga uwar kwalliyar da shiga iri iri a gidan nan,yanda nake kashewa jikina kudi bai tsaya a nan ba sai da na dangana ga zuwa gidan gyaran jiki na biya makudan kudi an tsunami nasha an gyara skin,lungu da Sako anyi masa filla filla Amma ku kanku da kallona kun san na kara kyau da canjawa,kalli yanda nake sheki da walwali,kalli yanda nake kamshi ko abu na rike sai ya tafi da kamshi na,kalli ku kanku yanda kuka rude da kyauna gashi komai ya kara cika duk da cewa kun sanni Amma sai da kuka Koka yanda nake sheki da uban kyau,

Meenat tace mun gane,to asarar tayi muni da kashe kudina yayi yawa Amma kun san Aayan asiri na jikinsa har yau bai warke ba,bazai iya komai ba sai tabe tabe,kinga ko ba komai Sabo da lafiyarmu ma ya dace ace an daina taso da sha'awa kuma taki kwanciya,kamata yayi ace mijina yana alfahari dani kamar ko wacce mace,amma ni kaina nake zargi ko nice ban iya yanda zansa yayi amfani dani ba,bayan wannan asarar kudin gyaran jiki so nake nima ace kwalliya ta biya kudin sabulu ace mijina yana yabo na yana susucewa a kaina,amma ace ina sheka Ado bana ganin ya zauce ina kanta.
Dariya Ma'eesha tayi tare da cewa wlh ya susuce kece bakya ganewa kinga yanda yake binki da uban kallo duk inda kika Gilma,kuma kin gama zautar da shi,bakya ganin yanda yake kishinki me kike so kuma? Meenat tace akwai matsala ace mijinka bazai biya bukatarsa da kai ba,kuma ribar soyayya da aure a hayayyafa,to ki kwantar da hankalinki kinga Wani Saurayina a Maiduguri dan gidan gawurtaccen malamin Sunna ne Malamine na Sunna basa tsafi ko shirka addua zasu baka kayi suma su tayaka kuma ba kwandalarku ana dacewa,Maeesha kin tuna Masa'udu Shekare wanda akace yayi shekara da shekaru a Cikin Uwarsa kwantacce kafin a haifeshi? Wanda ke zuwa kusan kullum yana damun mu da Fassarar Hadisai? Ma'eesha tayi dari tare da cewa au wai Shekarau kike nufi? Dalla Shekare yake ba Shekarau ba,ae gaskiya ne kam malamai ne,ni kuwa nayi tsalle na dire cewar Bazan tonawa mijina asiri ba gaskiya,Meenat tace to kin gwammace ya zauna da cutar wani abun sai ana fada ake samun mafita,ai ba wanda yafi karfin cuta a duniya ba a kunya a cuta gwara a

Please Login or Register in order to submit comment