Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito a birkice daga gym yake ya motsa jiki sosai kamar zai fadi Sabo da yunwa,gashi bai iya shan fresh milk ba Amai take sashi idan ya sha da Safe,
Gefen Meenat ya tsaya tare da cewa ya akayi ne ta Tsito? Harara Meenat ta aika masa,Maeesha bata ma san me suke ba tana can tana fama da tunanin Handsome Yarima da yake kasheta da kalamai masu dadi ita kadai take murmushinta.
Meenat tace Ameer da kasan kyau irin na Tsito da baka yi magana ba,Ameer ya tabe baki tare da cewa ai dai nasan kaf kauyen su Tsito basu da kamata yarinya bare ki min gori,Handsome kamata kema dan kin sanni ne kina ganina a banza kije kiga yanda yan mata suke rubibi na kulasu,da ace baki sanni ba da tuni kin mato a kaina,Allah ya kiyaye ai ni shekarunka sunmin kadan yaro dakai, Wukar da nake fere dankali ya karba ya fara taya mu yace ku matsa so kuke yunwa ta kashe mu a gidan nan, hmm Mufee ce taki fitowa ko lfy? Cewar Ma'eesha,Uwar Sa ido ina ruwanki dan bata fito ba mace da Mijinta ya kamata a aurar daku kuma ku daina sawa mutane ido,Maeesha tace mu ina ruwanmu dan tani su shekara a Bedroom in dai lfy shike nan, wurin 11am da kyar Aayan ya tasheni nayi wanka tare da Brush na sake gasa jikina na daura alwala tare da tayar da Sallah,Lokacin Aayan ya shirya cikin wani yard me Laushi Dark arsh color,Ina kallonsa yanda yayi kyau ya zarta kwatance, nayi adduoi na mike a hankali kamar yar kaciya na lallaba na shafa Lotion da turaruka tare da Sa Gown me kyau simple English wear doguwace har kasa sama ta dan dame kasa ta bude pink color nayi kyau sosai,powder kawai na shafa tare da lipgloss red sama sama na yafa dan siririn gyalena a kaina,uban gashina nayi acuci dashi.

Aayan sai bina yake da kallo so yake sai ya kara yi Amma na ki yarda ko fuska ban bashi ba,na dan dingisa har gabansa na zauna gefensa a saman Bed na kwantar da kaina a cinyarsa ina kallonsa nace ina kwana ya rufe min baki da Sauri tare da cewa ni ya dace na duba lfyr ki My Dear,ya jikin?Nace da sauki yunwa nake ji kasan bana jure yunwa ni,Ki kwanta bari na kawo miki abincin da kaina nasan su Meenat sunyi ma yanzu,Yatsunsa nake wasa dasu nace so kake su gane sai yanzu ka angwance gashi sai murna kakeyi kana fita zasu gane tunda ka kasa boyewa jiya ka kwashi dadi,Dariya Aayan yayi ashe dai matar tawa bata da kunya da yawa,fuska ta na boye a kirjinsa,tashi muje Amma tafiyarki ta canja ya za ayi kawai ka rikeni sosai irin soyayya ce,haka za ayi.
Hannunsa ya zagayo ta kuguna ya manneni a jikinsa tare da rikeni sosai muka fara Tafiya a hankali,nace wash Allah ina famuwa wajen da zafi kawai ka daukeni Bazan iya bin Steps ba.
Ba musu ya daukeni kamar Jaririya tare da cewa kin tabbata baza kiji kunyarsu ba? Nace waye bako na ciki,Ameer ne kuma shi baya shiga sabgar wani bazai ma kalle mu ba.
Suna Dinning suna Break suka hango mu muna sakkowa,Meenat ta Radawa Ma'eesha sabon Salo yau suka canja,Maeesha ma a kunne tace Mufeeda yanzu ko kunya bata da ita,Ameer yace nima dan rada min naji,Dariya sukayi Ma'eesha tace Bada ni ba,Meenat tace dole kai sai kaji nan a hankali ta karkata gefen Ameer tace Sabon salon su Aayan muke kallo a sama ko kunya babu kallesu,Ameer yana dariya ya dan Saci kallon yace uhmm wannan harka tayi nima Allah ya kawo ranata har sun tayar min da tsohon tsumina.
Suna ganin mun karaso suka daina kuskus duk na tsargu nasan halin Meenat.
Aayan suka fara gaisawa sai ni,sun saba kullum faran faran ina jansu da wasa Amma yau suka ga shuru sai dai na kwanta jikin Aayan lagwaf, Aayan yace ina abincin fa naga Table sai kadan? Meenat tace bamu dafa daku ba Sabo da Sis sai tace baka cin Kaza da Kaza shi yasa muka yi iya namu in ta fito sai mu tayata tayi muku naku.

Aayan ya janye na gaban Meenat ya mikawa Mufee,ya janye na gaban Ma'eesha da Ameer ya mikawa Mufee Amma na Ameer shi ya cinye da kansa matarsa baza taci ragowar wani ba,Meenat baki bude take kallonsu hankali kwance suke cin chips and Egg dinsu harda tea din,Aayan yace kuje ku dafa wani ku in kun gama kuci,Mufee ko magana banayi cin abincina nakeyi duk Aayan ya wani rude ya rasa inda zai Sa kansa ya rasa ina zai sani ko me zai min bakinsa a washe yau shi kadai yake ta hira a Dining Ameer mamaki ne ya kamashi dan shima bai san Aayan haka yake ba da surutu gashi ya kwace musu abinci sun cinye musu,Meenat ya kalla da suke ta kallo na yace kuje ku dafa ma kanku wani abun,Darling me zaki ci? Ko kin koshi yanda yake min maganar ma a hankali kamar Jaririya sai da naji kunya,ido na daya na kashe masa sannan nace farfesun Kifi nake so da dambun naman Kaza,Aayan yace to Kunji ayi mata yanzu da wuri kar a dade kai Ameer kuje ko wanke wanke ka tayasu,Dariya Ameer yayi tare da cewa Yaya harda ni ina namiji kasan ni ban iya shiga kitchen ba bayan haka ma Meenat ta gama rainani a gidan nan zagina takeyi,Meenat tace wlh sharri yake min ni ko hararar Sa ban taba yi ba fa, Ma'eesha tace dan Allah muje muyi Sauri zanyi bako ni anjima,Meenat ta kalli Aayan Ya kasan Bakon nata? Aayan yace pls kuje mana kun dameta da surutu kanta zai fara ciwo,ina jinsu sai dai nayi musu Alama da hannu kamar wata sarauniya wai ni ga me miji ana so na nace kuje pls da kyar na furta hakan cike da yanga.

Kitchen suka wuce har Ameer din shi abin ma dariya yake bashi na Aayan to yau me Mufee ta bashi ne haka,Maeesha sarkin kida bluetooth speaker ta dakko ta ajiye a kitchen tare da hadawa da wayarta ta fara Sa musu kida sun cika kitchen da kida, Ameer da Ma'eesha sai bin wakokin sukeyi dama sune sarakan waka,Maeesha ita a wajen rawa ba kunyar uban kowa takeyi ba rawarta take cashewa suna aikin,Ameer kuwa Babban yaro ne sai dai yayi Alama da hannu,Meenat kallo take kawai tana dariya suna girkin suna cinyewa duk dambun naman sun cinye rabi dama kadan sukayi,Farfesun kifin ma haka,Ameer yana ma Meenat magana a daina cinyewa bata ji sanda yayi maganar ba ya dauki spoon daga Cikin farfesun ya dau zafi sai da ya dan tsaya yanda bazai Konata ba Amma zata ji zafi ya daura mata a bayan hannu,a zabure Meenat ta juyo tana yarfe hannu nan take ta koma gefen sink Bowl dauke da ruwan da suka wanke kifi da nama hannayenta biyu ta tsoma ciki ba tare da Ameer ya sani ba sai jin tafin hannayen Meenat biyu a fuskarsa gefen sajensa tana shafa masa kamar me shafa mai, karni yaji da Sauri yaja baya yana dauke numfashinsa ga Ameer da tsantsami baya son karni ko kadan yanzu zai fara Amai,Meenat bata sani ba har sumarsa ta bi ta shafa masa ta karfi yana zillewa.
zuciyarsa har ta fara tashi da Sauri taga Hankalinsa ya tashi ya fito da Sauri tare da wuce mu a Dining ya fada Bedroom,tunaninmu da Meenat sukayi fada Aayan yace Meenat ce ta bata masa shi kuma ga fushi wlh aure zan daura musu,Dariya nayi nace hmm Ai Ameer ke tsokanar ta.
Ameer yana ciki sai wanka yake shekawa kamar zai cire fatarsa ya dade yana abu daya ya fito zuciyarsa na tashi still haka ya shafa Lotion yayi sabon shiri kayan da ya cire a leda ya zuba su tare da fitowa ya wuce mu ya jefa su a dustbin na Compound,Ya kara dawowa Bedroom da Sauri sai kakarin Amansa muka jiyo,Kaji kamar Ameer Amai yakeyi,Aayan yace wani abu ya gani na kyankyami ko karnin kifi yaji haka yake yi,Amma kasan haka kace ya taya su? Na manta ne sai yanzu na tuna Amma tambayi Meenat ko dama bashi da lfy ne.

A hankali na mike da kyar nake Tafiya har kitchen nace Meenat me ya samu Ameer,ba komai spoon me zafi ya Dora min a hannu shine na shafa masa ruwan kifi a fuska,Maeesha tace wlh har sumarsa ta shafa masa,fuska na bata baki da kunya dalla jibeki ta Tsito kawai sai kije kiyi jinyarsa gashi can yana ta sheka amai a toilet Aayan yace baya son Karnin kifi danye baki kyauta ba,Kirji Meenat ta dafe tare da cewa wlh ban sani ba Sis Allah Sarki to me zanyi in na je ma? Harara na watsa mata ki wanke toilet ki gyara ko ina.

Lokacin Aayan ya shiga wajen Ameer dake toilet yana ta faman Amai,Doctor ya Kira tare da sanar masa nan take Doctor yace ga magani nan ya bayar a kawo,15mnt wani Nurse yazo a mota har gidan dake Aayan duk ya sansu suka gaisa ya Bada magani a leda tare da yanda za a shasu ya tafi,ni kuwa uwar son abin duniya har Dustbin naje na zakulo kayan Ameer da ya jefar nace wannan ai fariya ce na bawa me wanki nace ya wanke su ya goge idan ma Ameer baya so sai na kaiwa Shehu me kanti na tsohuwar unguwarmu wanda muke buga masa waya ya kaiwa Ammah.

Meenat Zata shiga Bedroom din Aayan yace ai sai kinyi wanka sosai zaki shiga Sabo da kina zuwa kusa dashi yaji wani karnin amai zai kara yi,Cike da tausayi Meenat ta wuce Dakinsu a ranta tace shi yasa suna fara taba kifi yaja baya ya koma karshen Kitchen ya zauna a can,amma kuma yana cin kifi kadan kadan kawai danyen ne bai son karninsa kuma.
Ma'eesha ce ta karasa komai tare da shirya Dining ta gyara kitchen da komai ta wuce Bedroom lokacin Meenat har ta gama hadewa cikin Lace Sky blue riga da skert tasha kyau ga iya kwalliya,turare tayi ta shafawa iri iri Sabo da kar taje Yiwa Ameer Sannu yaji Karni a jikinta ya fara Amai,ta fito Aayan ya mika mata maganin ki tambayeshi me zaici ki bashi,ina kwance saman cinyar Aayan nace Meenat kar ki sake wlh ki masa rashin kunya Kinji na fada miki,Dariya Meenat tayi sannan tace to ni ina ruwana dashi?
Shiga dakin tayi da mamaki yanda Dakin yake komai Neat kamar na mace,saman Bed ta hangoshi ya dukunkune cikin bargo yana rawar Sanyi,Meenat ta karasa gefensa da Sauri tace Sannu Ameer kayi hakuri ban san Baka son Karni ba,duk da ciwon nasa sai da yace ta Tsito in ba shirmenki ba wa yake son Karni? Murmushi nayi me zaka iya ci yanzu? Ba komai,to tashi kasha magani inji Ya Aayan,haka yace ai sai dai ki hauro saman Bed ki bani Bazan iya tashi ba, farko dai Dan zuba min ruwan tea me zafi ki zuba zuma spoon Uku sai ki matsa lemon tsami kadan ki kawo idan na sha sai na iya shan maganin,dan da nan tayi yanda yace ta Hau tsakiyar Bed din sannan ta bude blanket da kyar ya fito tare da dan Zama kadan,ta daura masa cup a baki ya shanye zumarsa tas,sai ta mika masa ruwa da magani kala biyu ya shanye sannan yana rawar sanyi ya koma ya kwanta, Amma ba amai kawai ya saka harda zazzabi ba? Meenat ta tambaya, Ameer wanda yasan shi dama ciwonsa na Sha'awa na motsawa sama sama to harda shi yau,Yace baza ki gane ba Meenat ciwon biyu ne suka hadu,Da tausayi Meenat tace Sannu Allah baka lfy.

Ameer ya dan kalleta kadan yaga zata bar dakin nan take ya fara nishi yana ohhh wash cikina da Sauri Meenat ta dawo gabansa a gigice ta haura saman Bed din tana ciki kuma again?ko maganin ne ai Ameer fari ya kama yi da ido wai ya sume,Meenat ta rude harda kuka tana dan Allah ka tashi karka mutu kaji tana jijjiga Ameer ya kara lumshe ido Meenat taga fa kamar ma ya dauki hanyar mutuwa gashi ya wani kankame cikinsa dai dai mararsa ya dafe wajen kam kam,Meenat da kyar ta iya cire hannunsa saman Marar ba riga a jikinsa sai Wando 3qrt Shakewa taji yayi yana shidewa kawai sai taa maida hannunta saman Marar tasa tana latsata ko ina ba tare ma da tasan me take ba,Ameer dadi ya gama kasheshi sai nishin dadi yake da numfarfashin dadi, a ransa yace Hajja ma na girmi wayonta bare ke,zaki kasheni ban shirya tafiya ba, ita kuma tunaninta zafin ciwo ne sai ta kara dagewa tace kana jin sauki?Yace da kyar banji me kika ce ba fada min a kunne na,so yake kawai tayi masa magana ya kara Jin sweet, haka ta kara bakinta a kunnen Ameer tare da cewa kana jin sauki? Wani sanyin dadi yaji nan take kafin kace me Ameer ya wani rike Meenat gam gam yana shidewa Meenat ana kukan Tausayi wai yana jin jiki, sai ga Ameer har ya warke ras ya samu nutsuwa zazzabi ya sauka sai gumi ke keto masa Sabo da dama cutar tasa ta Sha'awa ce kuma garin latse latse ta sauke masa ita ya dawo hayyacinsa.

Muryarsa taji yace ba kyau Allah ya hana taba mutumin da ba muharraminki ba kin jawo min Allah zaiyi fushi dani ki tafi zan fito naji sauki na gode,da Sauri Meenat ta cire hannunta daga Cikin Ameer tana Harararsa ta sauka daga Saman Bed din da Sauri tayi waje abinta ta bar Ameer yana dariyar jin dadi yasan yau daba dan Allah ya kawo Meenat ba da maybe mutuwa zaiyi da ciwon Sha'awarsa tuni dan rage zafin ma da yakeyi da mata ya daina,yanzu ya tuba baya kula ko wacce ya mace Sabo da yaga duk bata lokaci ne.
Meenat na fitowa ta tarar na zauna daram a cinyar Aayan yana bani farfesu ina ci,sai shagwaba nake masa ina Hawaye yana lallashi, tunanin Meenat zanji kunya kawai sai taga nayi mursisi ko a jikina sai ma kara lafewa da nayi a jikinsa ina shakar kamshinsa,da Sauri Meenat ta fasa wucewa ta koma dakin Ameer Sabo da wai taji kunya, dariya nayi kawai,Meenata a ranta tana to wai Sis me aka yi mata yau ne komai kuka shi kuma yau ya Zama maye a kanta gaba daya lfy kuwa?

Ameer lokacin ya shiga wanka Meenat ta dan jira wai ko zata ga mun tashi Amma sai ta dan leko ta kofa taga muna nan muna Holewa haka ta hakura ta fito da Sauri ta shige Bedroom,Maeesha kuwa tana palon baki tare da Yarima suna hira.
Aayan ne ya daukeni tare da cewa an koshi haka muje ki kwanta zanje wurin Daddy, ka gaishe min dashi sai na warke zanje,h ar Saman Bed ya kwantar dani tare da rufa min Blanket bai dade da fita ba bacci me nauyi ya kwashe ni.

Yau Daddy kansa yasan Aayan yana cikin farin ciki me tsanani,Daddy ya kalleshi tare da cewa fada min Son wanne abin farin ciki ne ya same mu?Aayan ya fara dariya wacce Daddy ya rasa gane ta mene,Aayan nasan baka boye min komai sanar min mene? Daddy kunya nake ji fa abin kunya ne,Sanar min naji muyi farin cikin tare,Daddy na Warke jiya ya fada tare da rumtse ido wai kunya,Murmushi Daddy yayi na jin dadi tare da cewa Alhmdllh Son Allah ya kara lfy me dorewa da nisan kwana, jeka tunda yau kunyata ka koma ji,da Sauri Aayan ya bar part din Daddy ya dawo namu,kayansa ya cire da Sauri daga shi sai boxers ya shigo blanket dina ya shige jikina sai bacci.

Sai wurin 3pm na farka na ganshi a jikina kara lafewa nayi a jikinsa ina shakar daddadan kamshinsa me sanya nutsuwa,hannunsa ya daura saman kirjina yana baccinsa cikin nutsuwa,tunawa nayi bamuyi Sallah ba ga La'asar ta kusa fuskarsa me matukar kyau tare da sajensa na shiga shafawa a hankali,shima a hankali ya bude idonsa ya saukesu a fuskata me cike da nishadi,bamuyi Sallah ba muna ta faman bacci na karasa ina sauka daga Saman Bed din sai toilet, nayi brush tare da wanka nayi alwala na fito sai lokacin ya shiga shi ma,ban jirashi ba na fara yin sallah sannan na shafa Lotion tare da turaruka nasa kayana lokacin ya fito La'asar tayi na yi Sallar sannan na zauna gaban Mirror na tsantsara kwalliya tare da Sa Atamfa green riga da skert nayi kyau na mamaki,ina gyara Bedroom din ya idar da sallolinsa tare da addua,na gyara room din har toilet komai Kal kal duk da ba wani lfy ce dani ba Amma Haka na daure na yi.

Hajja ce Tare da Abbi suka shigo gida sun dawo daga gidan ko zasu ga Daddy Amma gidan an kulle ba kowa haka suka dawo jiki ba kwari,takaici ya damu Hajja,Abbi yace yanzu ina zamu gansu? Hajja bakin cikinta bata dauki kudi ko sisi a gidan ba,yanzu bata da ko kobo,haka kowa na gidan babu me shi,Gold din matan su Abbi ma iya na kunnensu ne da abin hannu basu da komai,ga ba abinci,har Companies na Aayan sunje bai je aiki ba kuma an hanasu shiga,zama sukayi kowa yayi jugum jugum,Abbi sani yace Hajja bafa aci ba,me zamu ci a gidan dole ciki sai ana bashi hakkinsa,Abbin Ameer yace idan fa na gaji wlh zan tsinewa Ameer na huta yaro dan iska tambadadde ya barmu ko kallonmu baya yi yana can yana jin dadinsa, dama Hajja tana cikin fushi ai ko ta hayayyako da masifa rufe min baki dan Iska da bayanka me zubin na Kwadi, Ameer din nawa zaka la'ana ahir dinka duk jikokina nafi sonsa, Mujaheed yace ai ba shi ya kar zomon ba,duk ba kece kika jawowa kowa ba yaja tsaki,Hajja ta Harare shi da gogoronta irin na yorubawa tasha bakin kwalli a ido bajagau,Khaleel yace mu kawai a san yanda za ayi damu muci abinci,Umman Ameer tace ga dankunnen Gold dina a siyar a siyo abinci,Haka ma matar Abbi Mustapha,da Abbi Sani sai Matar Abbin Yara duk sun Bada nasu,Hajja tace Kai Sani kaje ka siyar dasu ka siyo kayan abinci,sannan ka kawo min dubu goma a ciki zan ajiye a aljihuna kasan zama ba kudi masifa ne,Abbi yace haba Hajja ko masu dankunnen ba a bawa ko 1k ba sai ke za a baki har 10k kin san fa abinci har kayan girki sai an siya,Haneefa ta bude Jakarta tace ni gashi na taho da 10k gashi a bawa Hajja mu huta,da Sauri Hajja ta fisge kudin ba ko godiya,Sajeeda tace dubu biyar gareni kwandala Bazan bawa wata katuwar tsohuwa ba gashi Mujaheed da Khaleel ku rike a hannunku,haka Meenal duk cikin yan matan tace ga Wata 3k Ni Abbi Mustapha zan bawa nawa Sabo da shi ke bani kudi idan na rasa ku kuwa dazu duk ni na siya muku Waina da miya kuka ci kuka koshi Bazan kara muku ba.
Hajja tace Allah sarki duniya Aayan da Daddy tunda suke mana komai basu taba yiwa kowa gori ba.

Wani dan yaro Sabeer yace Mommy ruwa zan sha babu,Hajja ta taso da Masifa zaka ci ubanka kai baka san babu ba ance ba ruwan roba a nan ko purewater babu dan Iskan yaro matsiyaci,Sajeeda tace kaje ka balle kan pampo yaro ka kwankwadi ruwa idan typoid ta kamaka ne hanji ya bule ka sheka lahira dan ni nasan wlh indai a haka zamuyi rayuwa ba shakka mutuwarmu ta gabato cututtuka kadai sun ishemu ruwan pampom ma wasu gurbatattun abu ke fitowa ta ciki.

Haneefa ta sosa cinyarta tace karzuwa ce zata kamani kwanan nan ,Meenal tace ya Ilahi muna karbar rayuwa,Mujaheed ya sheke da dariya tare da cewa ths is just the begining matukar Hajja na raye,kwana biyu kacal, dundu Hajja ta zuba masa a baya.
Kuka akaji Hajja ta saki tana komai ace nice Allah ya Isa abin ya kai har mutuwa ake jawo min da lfy ta da kwari na, Abbi yace kiyi hakuri baza su kara ba,Hajja ganin yayanta Maza na wajen ta fara shure shure tana mutuwa zo ki daukeni na huta ga jikoki birjik suna ji sai Khaleel ne yaja tsaki tare da cewa wuya kika ji shi yasa kike kiran mutuwa da sanda muna gidan daula da jin dadi me yasa baki nemo mutuwar ba,ki rufawa kanki asiri wlh karki mutu yanzu sai kin tuba idan ba haka ba Ki ci duka wajen walakiri da bulalar wuta, Hajja tana Hawaye tace ubanka da uwarka ka fadawa haka Mutuwar tazo ya fiye min wannan rayuwar ta talauci.

Su Abbi an dan siyo kayan abinci matan suka siyo kayan girki tare da na cin abinci duk na talauci haka gidan sai Abbi ne yaje ya karbi bashinsa hannun wani da yake bi Dubu Dari sune ya samu ya siyawa kowa katifa karama sannan aka sawa gidan kaya da sauran kaya haka na talaka,kitchen ma aka kara yan kayan cin abinci da kayan abinci ana dan cin garau garau, duk yanda suka so ganin Aayan ko Ameer ya gagara,har Yarima sun nema yaki saurarar su,ganin haka Hajja tace su hakura ai indai Daddy ne zai nemeta tunda uwarsa ce kuma yana yi mata biyayya su danyi hakuri na dan wani lokaci,gashi yan samari da yan mata sun hana a siyar da wayoyinsu manya tare da laptop dinsu sunce a mutu da yunwa akan a siyar gashi abincin da yan makaranta duk sun cinye kudin su Abbi,a bincin ma sabo da suna da yawa da wuri ake cinyeshi gashi babu me aikin yi ko fita basa yi a unguwar yaran ne kadai ke zuwa schl Abbi yace kudin makaranta na karewa sai dai a maida su ta Gomnati,Mujaheed da Khaleel kuwa su Abbi sunyi sunyi dasu su karkade takardunsu su fara fita neman aiki amma sunki Sam,sabo da ba a musu tarbiyar neman na kai ba,ba a nuna musu tun farko cewar ka nemi naka yafi akan ka dogara da kudin wani ko na ubanka,basu san wahalar duniya ba.
Su Haneefa yan mayuka masu kyau duk sun kare an fara duhu duk da cewa suna da haske amma sabo da ba irin rayuwar da suka saba ba kenan duk sai suka fita daga hayyacinsu sai masifa da rashin kunya da suke yiwa kowa a gidan musamman Hajja da suke ganin laifinta ne. Saurayin Meenal ne ya bata Dubu ashirin suka samu aka sa carpet a Palo da bedrooms,shima sai da ta dinga rokar shi ta zubar da ajinta sosai ya dan Sha minti da ita sannan ta samu kudin.
Matan su Abbi kuwa yanzu yar biyayyar da sukewa su Abbi Ashe duk ta kudi ce yanzu fada da masifa kawai ke tashi a gidan babu me Zama lfy,Hajja da tayi magana su zageta,Hajja ba kudin zuwa wajen bokaye sai cin goro da take tashen yi ba dare ba rana.
Tun daga wannan Rana Hajja Sabo da bata son talauci take kiran mutuwa ko a dakinta sai kaji tace mutuwa kizo ki daukeni da wannan rayuwa,tace to yaran wai ina suka buya haka ko ina an kasa ganinsu da ace sun bude mana gidan ma sai mu kwashi yan kadarorinmu da kudadenmu ko banza ma kafa kanmu cewar Hajja,Haneefa tace ah Hajja kiwa Daddy da Aayan baki mana wlh da nice ke tsinewa Daddy kawai zanyi.

Harara Hajja ta zabga mata tare da cewa to ai yafi ubanki dan uwarki ubanki

Please Login or Register in order to submit comment