Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce kina so,tunda kin yarda ko mutuwa ma jikan naki yayi baki da damuwa, Nan Hajja tace da dai yafi a dage sosai ta zube masa makudan kudi ta bar wajen,tayi waya da malamai da dama duk akan aikin sannan taje wajen wasu ma sunfi biyar Sabo da a hada karfi da karfe kuma sun bata tabbacin ba matsala.

Makara mukayi don har rana ta fito bamu sani ba muna manne da juna muna bacci,lokacin Meenat har ta hada Breakfast da komai,Maeesha kuwa gyaran gidan ta fara kasancewar yau Ba schl,ni na fara bude ido na da kyar na iya zare jikina cikin nasa sabo da gaba daya ya makalkaleni ta ko ina ko juyi bazan iya ba,wannan ne ya tashe shi daga bacci,muna hada Ido na runtse ido, kawai sabo da kunya,Murmushi ya saki har ina jin sautinsa da sauri na sauka daga Bed din na shige hadaddiyar toilet dinsa nayi Brush da wanka kana na dauro Alwala na fito dan guntun Towel dinsa na daura na fito ina goge gashina,yana Saman Bed ya tsaya sai kallo na yake sannan ya mike shima ya shiga wanka,kafin ya fito na idar da Sallah na shafa Lotion dinsa tare da turarukansa har gashina na gyara shi sosai ina haka naji muryarsa yace kawo min Towel dina ko ki bude Wardrop ki miko min new, wai dan kar a bata kaya da yawa nayi Sauri na dauko Jallabiyarsa fara nasa dan tight short dinsa na Sa Jallabiya ba karamin kyau nayi ba duk da tayi min yawa kowa ya kalleni yasan nayi kyau.

Toilet din na nufa na manta kawai na murda Handle na shige gaba daya da Sauri ya juya min baya yana ta masifa ban kalleshi ko daya ba na fito da gudu nace kayi hakuri mantawa nayi wlh na kara dan tura kofar na dan tura hannu na tare da mika masa ya karba ya zuba su a washing machine sannan yace miko min wasu ki bude part din karshe,da Sauri na bude na dauko tare da kara miko masa ya amsa ya daura sannan ya fito ina dariya nace na gani dai abin tsoro ma, murmushi yayi yace ke kika sani kuma,Wajensa na karasa kawo na tayaka Allah na iya ni nake shirya su Meenat ma fa, na zuba Lotion a hannuna nace to juyo mana ni ko dama wayo zan masa dan na taba masa jiki ne Sabo da yana birgeni,shafa to kiyi kuma Sauri sallah zanyi na fara murza masa Lotion ina ta murmushi dan fatarsa sai laushi kawai,nazo waist dinsa na tsokaneshi Sabo da naga baya so a kalle masa tsaraici nace kwance towel din nayi Sauri mana dariya yayi yace a'a ki kwance da kanki kai.

Ina gamawa yace saura kaya to ya dauko wani Yadi shara shara fari me shegen kyau karamin dinki fitted na Maza yan gayu,da Singlet sai short ya miko min karasa aikinki, na karba kuwa ya dauka zan wani kasa sai ya karbe yasa Boxers dinsa,nasa masa singlet yasa wandon kayan na Sa masa rigar, da Sauri ya gyara sumarsa tare da fesa turaruka ya tayar da Sallah,ni kuma na fita tare da sauka kasa na duba na ga me su Meenat suka dafa idan basuyi ba nayi,tea suka sha da Doya da kwai kawai,sai farfesun kaji,na dinga masifa kun san dai bazan fito da wuri ba dan Iskanci sai kuyi wani Doya kawai da tea mijina yana ci ne? Ba sosai yake ci ba,Meenat tace au bamu birgeki ba a hakan? Ke da kika ce hira zaki je kuyi kawai ki dawo sai yanzu zaki fito duk hirar ce tun jiya? Shike nan bacci bazai kwasheni ba nama kwana din ina ruwanki ke zaki tsara min abinda ya dace nayi kece gaba dani ko nice gaba dake? Daga yau ma acan zan dinga kwana sai me kuma? Dariya Meenat tayi kawai tace ah mun gane, to gyaran gidan fa? Ya kika gani ya miki ko shima mijinki bazai masa kyau ba? Dubawa nayi nace wannan ai nasan kun iya dama kuma na gani kunyi kokari,bari to zo ki tayani muyi masa Kunun Gyada,da su muka shiga kitchen din suka taimaka min Dan danan muka shirya lafiyayyen kunun gyada,na fara soya dankali suka ce sun gaji su nace to kuje ku huta,suna fita sai ga Aayan ya shugo kitchen din a bayana ya tsaya kamar zai shige jikina ina jin kamshinsa a saitin kunne na yayi magana a hankali yunwa nake ji fa ki danyi Sauri,yana fadan haka ya fita ya barni nan ina jin jikina wani iri.

Tunowa nayi da zan fara yanga ta na daina cin abinci a gabansa da yawa Sabo da kar ya rainani gashi kuma bana koshi da wuri sai na shirya dabarata yanzu duk girki sai na samu na zuba a kitchen din in ci abina na koshi sai na rage space kadan idan anzo ci a dining sai aga ina ta yanga naki cin abincin da yawa sai dai na dan ci kadan,
Cikin rashin Sa'a yau nace zan fara tunda tare zamu ci a dining,na zauna na ebi chips din na zuba kunun gyada ta,farfesun kajin dasu Meenat sukayi nan ma na zuba Naja gefe ina cin abina a nutse,Kawai Aayan yazo zai shigo kitchen yaganni kicif ina cin abina,nan take ya gane me zanyi don Allah ya zuba masa basirar gane abu,dariyace ta kamashi me karfi ya danneta,ya juya palo dan kar na ganshi naji kunya.
Saida na koshi sannan na sha ruwa na gyara lips dina na fito na shirya Dining na gyara kitchen din na fito,Aayan yana Dining yana jirana nazo na zuba masa ni kuma na zuba komai dan kadan kamar dan yaro ne zaici irin yar gayun nan, yaga ina ta wani juya cokali a ciki ina tsakura,shiko yana ta cin abinsa har farfesun,ya kalleni yace kici mana wannan dan abincin nufinki zaki ci? So kike ace bana baki abinci ko so kike ki rame? Baki na tabe ina yatsina fuska na ce ya isheni haka,ya kalleni tare da danne dariyarsa yace me yasa kika daina cin abinci ko baki da lfy? Na shagwabe fuska nace ni...yanzu bana son wani ciye ciye da yawa,yace to kiyi hakuri kici kinji yanda ya zage yana ta lallabani sai naci abinci ni kuma ina botsewa haba sai naji wani dadi nace lallai Aayan ya fara sona sosai ji yanda yake ta kula dani yana damuwa sai naci abinci,ni kuwa sai yanga nake wai ni a dole na masa wayo ban san shike min wayon ba.

Kusa dani ya dawo yace Dole sai ya bani da kansa nafi ci na koshi yaga wasa nake da cikina so nake cuta ta kamani,nan take na Tsorata Sabo da na koshi taf cikina ya cika,ina ji ina gani ya zauna ya dinga dura min abinci da kansa,kamar zanyi amai Amma yaki saurara min,Dankali da Kunun gyada ya dinga danna min,ya dawo kan farfesu,tun ina dannewa nace dan Allah na koshi Amma dama Sabo da mugunta ya shirya min yace sai na cinye ya san ina da ci,Idona ya kawo Hawaye na fara kuka ina bashi hakuri Amma yaki yarda sai cusa min yake,sai da naci me uban yawa wanda kwakwaran motsi nayi sai nayi Amai,ya miko min yatsun Sa da ya bani farfesu dasu yace tsotse abinki,haka na tsotse yatsun tas shi kuma yanda nake tsotsar yatsun ne ya tayar masa da hankali nan take ya birkice,Sha'awarsa ta motsa da kyar ya dan danne yace ku shirya da yamma zamu fita zan dawo na daukeku,hararsa nayi nace to ina turo baki akan dura da yayi min.

Ameer dasu Mujaheed ne zaune a katafaren Palonsu suna game suna hira,Mujaheed yace ni fa guys wlh ina son beb din nan kanwar matar Aayan Meenat take ko wa? Khaleel yace ai yarinyar tayi ne ina fada ma gaba dayansu Allah ya zuba baiwa Barin ma matar Aayan gaskiya Ameer Banga laifinka ba,Ameer yayi dariya irin ta yan duniya sannan yace baza ma ku gane ba sai nan gaba,ni na hango abinda na hango,kullum da ita nake kwana nake tashi,Sajeeda dake gefensu taji haushi dan ita Ameer take so yanzu, rai bace tace haba Ya Ameer mene haka wannan cin fuska ne ina wajen fa wlh zan fadawa Abbi kasan dai yace Aure zai mana,Ameer ya kalleta shekeke ke dalla rufe min baki me zaki kaimin gidan nawa? Har daki kike bina muna aikata abubuwa zaki zo kice wani na aureki,Amma kasan dai ai kaine kace ba komai zaka aureni tunda kaine ka lalata ni,Mujaheed yace ko kunya bakwa ji ku rufe mana baki Hajja in ta dawo ku fada mata mana a fasa can da matsalarku,Cousins kenan dama haka akeyi ko mai ace cousin dina ne Kaza Kaza kullum kayi tunanin yan uwan ashe ana nan ana aikata masha'a tare,Mata har gidan kani ko wan babansu zaka ga sun tafi hutu an samu Cousin mace ko namiji ana ta shekewa,su kuma iyaye tunaninsu zumunci akeyi sai suyi ta jin dadi Allah kyauta.

Hajja ce sanye da glass dinta na ido ta zauna a Cikin jikokinta nan Fa Sajeeda tana kuka tace Hajja kinji wai Ameer bazai aureni ba, Hajja ta gyara zama fatarta duk tayi yaushi tace shi din banza,ya Isa ma,shi waye shi wlh wlh Allah daya sai anyi wannan aure kwanan nan ma kuwa ko sama da kasa zata hade,waye kai? Ka Isa nayi magana nasa doka da hukunci ka tsallake ko Ubanka Mustapha bai Isa ba bare kai karamin shege,nan Hajja tayi masa tatas yayi shuru yana ji Amma ya rantse indai Sajeeda ta shiga gidansa sai ya kusa hallakata da muguntarsa ita kuwa Sajeeda murna takeyi don tun da ta taso a duniya take son Ameer sosai Sabo da ya hadu shima ba laifi.

5:30 muka gama shirinmu tsaf mun hadu karshe yau kamar wata Sallah haka muka dau wanka,Aayan kuwa bamu san a inda ya shirya ba haka muka ganshi ya shigo cikin dakakkiyar shadda sea blue yanda yayi kyau ya zarta hankali ma,Maeesha ya kalla yana zuba kamshi yace kinfi kowa kyau yau,nan take naji haushi ni bai yabeni ba ai ni ya dace yace nayi kyau ba su ba,Meenat kuwa yace Yau kamar Queen haka kika koma nan take Meenat ta fara dariya tana tnx Yaya,Ma'eesha kuwa ta makale a jikinsa,ni da yau nafi kowa haduwa yanda nayi kyau har ya wuce misali Amma bai ce nayi kyau ba sai su Meenat,kasa danne fushina nayi sai kumbura nakeyi haka na karasa Sa sarka ta na dauki mayafi na da jaka nace muje Meenat da Ma'eesha suka yi waje ni kuma zan fito yana Bedroom din namu ya jawo hannuna na fisge abina,ya kara jawoni na fado jikinsa gaba daya,na sadda kaina kasa a saitin kirjinsa,hannaye biyu yasa ya dago da fuskata yana kallon lips dina tare da cewa wa kika sawa jambaki kuma? Nace masu sona na cikin gari idan mun fita nake Sa ran zasu kalla suji dadi, bakin ciki ne ya ziyarce shi me tsanani Amma sai ya danne ya hade bakina da nashi ya dinga sha,sai da ya shanye jambakin tas sannan ya dauki wipes a saman mudubi na dinga tsalle ina son guduwa amma ya rikeni tam da kansa ya goge min fuska tas ba abinda ya bari na kwalliya ta,hakan ma yaga baiyi ba sai ya jani toilet fuska ba walwala ya danna kaina a saman sink yasa soap ya wanke min fuskar tas ya goge min da towel nayi wani mugun Fresh jajayan lips dina suka fito natural sai na kara wani kyau kowa yasan Natural kyau na gaske nayi,ga kayan sun hau jikina,dankwalin dana kafa kamar gogoro ya zame ya jefa shi saman Bed ya dauki Hijab ya sa min duk da haka nayi kyau sosai sai ya cire Hijab din ma tare da cewa baki da kyau sam sam Bazan iya fita dake ba bari muje da kyawawana su Meenat,dama haushinshi nakeji ya bata min kwalliya kuma baice ina da kyau ba yanzu kuma wai ya fasa zuwa dani,ban san sanda na fashe da kuka ba me karfi, ba shiri yace taso taso mene haka wannan uban kuka zaki fasa min kunne,gyalena na dauka ina share Hawaye yace Sa Hijab na kara sakin kuka yace to yafa gyalen haka muje wannan masifa haka,ina dariya na yafa haka nabi bayansa,sai da na kara tsayawa a bayansa na zaro Powder a jakata muna tafiya bai San ina ta shafawa ba,na gama nasa jambakina red,kafin mu karasa mota har na gyara ribbom din gashina nayi acuci sosai na gyara mayafin aiko na dau kyau kowa ya ganni yaga yar gayu,nasa glass dina dan Brown nayi kyau ba a magana,yana juyowa sai da ya firgita kamar aljana kafin aje mota har na sake kwalliya yace zanyi maganinki a ransa tunda bakya jin magana dai dai nake dake.

Gaba na shiga Meenat da Ma'eesha suna baya shike Driving yau,katafaren store muka tsaya Meenat sai jin dadi muke muma mun Zama yan gayu,sabo da neman suna sai da na karasa tare da rike Hannunsa muka jera sabo da naga Yan mata sai shige da fice suke a wajen ko wacce ta Sha wanka, hannuna ya rike yana murzasu muna tafiya duk inda muka keta sai an kallemu,Kayan sawa iri iri yace mu zaba,dana tashi sabo da tausayin kudi abinka da ba a saba ba kawai sai na zabo atamfofi dasu laces materials dasu Ready made duk ba na sama da Dubu biyar daka biyar sai kasa,gani nake na gama kure karyar kudi, yana duba kudin yace a maida su wannan ai wanke kudinka ne Hajiya,da kansa ya dinga jidar mana kaya masu matukar tsadar gaske komai latest,haka takalma ma,bags ma ba a magana,har su cosmetics yana zabo me tsada muma muna daukan wanda muke so,har jewelries, muka je bangaren Inner wears yace su Meenat su zabi nasu aiko suka jida masu kyau iri iri,ya jani wani bangaren can daban na inner wears yace zabi size naki naga ko Bra kuwa kina sawa? kullum daga an dage miki riga direct ake tafiya can,Kunya naji na rufe ido nace Ina sawa mana amma a boye nake sawa na wanke a boye bana so ace kamata ina sa Bra,to mene a ciki dan kinsa yaja tsaki tare da cewa anya kuwa jinin birni ce ke? Nace a'a daga garinku nazo murmushi ya saki sannan yace mu bamu da dangi a Rimin Gado mu gaba da baya dan birni ne ni,muna ta Zaba iri iri masu kyau ya dauko min wata yar karama yace ga wata me kyau,Hararar wasa na masa nace kaima kasan sunfi haka wuce nan sai kace yarinya,muna dariya sai ga wata yar gayu tana kwas kwas da takalmi ga kamshi tana zubawa muryarta muka ji tace Aayan kaine a nan we finally meet here ohh,Dagowa yayi tare da zuba mata idonsa me matukar kyau ya danyi murmushi kadan sannan yace Sameera kece How u?longest time,tace am great ina ta so mu hadu wlh amma ba dama tun aurenka na farko fa gaskiya mun dade.

Wani kishi da bacin rai ya taso min na bata rai nayi kicin kicin na tashi hankalina gaba daya ina Harare harare,itace second wife din naka? Ina Yarima yana dariya yace yana lfy yar duniya kin buya amma dai kin sake aure yanzu ko? a'a aure ai sai na huta ina aiki ina samun kudina matsalar maza ta isheni baku da kirki Sam ni sai na huta zan yi Insha'allah,Jin bata da aure yasa na kara fusata na daure fuska na dawo gaban Aayan na juya bayana tare da kwantar da jikina a jikinsa muna facing juna da Sameera sai kallon Banza nake mata,Hannunsa na jawo guda biyun na sakalosu ta kafaduna ina wasa da yatsunsa,Murmushi Sameera tayi tare da cewa am sorry to say Aayan kasan bana boye abinda ke raina amma wannan tayi maka yarinya da yawa Aayan kamarka da auren kamar wannan da gani ma baza ta wuce 15yrs ba,ga mata a gari zunduma zunduma da ka fada mana ai da mun zabo maka manyan yara amma irin wannan ai kuruciya zaka sha baza kaji dadinsu ba.

Dariya sukayi gaba daya tare da wani tafawa abinda ya bani haushi kenan ya kara kuleni mene nasa na tafawa da mace,nan take naga fa ta fada min baka zata barni da takaici ban san sanda nace uhm Allah sarki kuma a hakan bashi da kamata dan ina masa abinda Babba bata isa tayi masa ba,tunda tsab nake daukeshi wanda nasan ko uwarki yafi karfin.....kafin na karasa yasa tafin hannunsa ya rufe min baki da karfi dan yasan sai na karasa ko za a mutu sai na rama,ina so na kwace baki na amma yaki Sakina ya toshe min da tafin hannunsa yana fada min a kunne kina magana wlh yau na lahira sai ya fiki jin dadi bakya jin magana ko ke ba a isa an miki abu kin hakura ba sai kice sai kin rama wannan wacce magana ce ta marasa kunya uwarta fa kika ce,Sameera ta kalleni sosai tace da Sameera kike zance yarinya zaki san kin zagi uwata,wlh sai kin San wa kika cewa haka,Allah ya taimakeki yanzu Kinci darajar Mijinki amma a sannu zan goge miki abinda ke kanki,Bakina na kwace nace Ba Sameera ba Allah yasa kece Sameeran Gaya🤣 wlh nafi karfinki kina magana kina cijewa ke ga yar daba karewar Daba munga Amana ta Alim ma😍 Sameera dama irin Masu takama da yan daba ne har yara ne da ita yan daba,bata da kunya duk abinda taga dama haka zata fadawa mutum shi yasa ko zaman aure bata iya yi,sabo da ko yaushe a shirin daba take kana mata zata sa yara yan daba suyi ma kaca kaca tana takama da kudi sabo da ubanta ita kadai ya haifa ya rasu ya bar mata dukiya me tarin yawa,Tun kafin ya mutu ya raba gado yaba yan uwansa ya barwa yarsa komai,shi yasa take abinda taga dama,kuma bata San mutunci ba duk inda take da kai zata iya ci ma mutunci ta ko wanne hanya,Aayan kuwa Business ne ya hadasu tsakanin Company nata da nasa tun da dadewa.

Ni kuwa nace komai dabancinki baza ki bude min ido ba kiyi duk abinda zakiyi nima baki San ko ni wace ba shi yasa har kike magana dani haka ina kyaleki,ki Bari watarana Business ya hadamu anan zaki gane true color dina,Tsaki taja ta bar wajen a fusace,Aayan yana ta kallon yanda nake tsiwa yar ficika dani gaban sangamemiya irin Sameera ko tsoro bana ji,na kalleshi nace girma ya fadi wlh ka ba dani ina ma kallon Ustaz har wani hannu kake hadawa da yan tasha,da gani wannan yar tasha ce gaka da fyallelliyar budurwa me zaka ji a hannun wannan me suffar mazan, kayi dacen mata amma baka godewa Allah kana wani rikewa wata hannu bayan ga hannun da zaka samu lada Allah kyauta ka daina irin wannan a gabana dan wlh ni bazan dauki a wulakantani ba dan baka darajani ba Sam,ka zubar min da mutunci ace Namiji yana da kamata yana rike hannun wata banza,wannan babban matsalace dole na tuntubi kaina Ashe ma ban kai mace ba.

Yana jina ina ta masifa kamar uwarsa yana dariya a ransa,yace to yi hakuri masifaffiya tunda bakya so na daina,wai nice budurwa shi baya daukana a budurwa Sam,yace wai ke nan budurwa ce? Bacin rai ya kamani sai na danne a fili nace a'a kwaila ce,a na dinga masa masifa ina zan rama zaka San ba budurwa bace ni daga yau na Canja salo again na fasa wannan Business din da mukace za muyi wani zanyi daban sai na sa kayi nadama har ni za a wulakanta dan anga ina biyayya ina cusa kaina ina kokari naga an zauna lfy shike nan za a gani,dariya yayi yace a'a dan Allah tsokanarki nakeyi fa muyi Business dinmu zan biya kudin,nace anki din sai na rama nima.

Mun gama siyayyar komai yasa aka kai boot din mota ya biya muka fito kenan sai ga Ameer da Khaleel tare da wasu yan mata masu suffar karuwai sai chewgum suke taunawa su a dole manyan yara,na kalli Aayan na bata rai nace kalli Meenat a gabanmu tsaya kaga abinda sukeyi kalli,ya kuwa kalla sosai ni kuwa wai dan kar ya kalli yan mata nayi masa wayo,Muna zuwa Ameer sai kallona yakeyi zasu shiga mu kuma zamu fito na bi ta tsakiyar yan matan nan a hankali yanda zasu ji nace yan iska sun dauko yan iska su a dole yan mata ana yaye baki a titi na wuce fit na koma kusa da Aayan,Khaleel ya fusata kwarai da maganata haka yan matan ma,Ameer kuwa so yasa baya ganin laifina sai dai ma birgeshi da nakeyi aransa ma cewa yayi wannan gaskiya kika fada Mufeedata tabbas yan iska ne suka dauko yan iska Allah ya baki basira tare da saurin ganewa🤣

Yan matan zasu zageni Ameer yace wlh duk wacce ta fadi ko bakar magana a kaina sai ya mata illa har fada suka so yi da Khaleel..
Muna shiga mota na tuna zanyi girki kuma kayan miyarmu ya kare nace Aayan kayan miya na manta,Yace to mu koma store din nace a'a danyi gaba wajen yar kasuwar can zamu samu.
Muna zuwa yayi parking nace sai ya fito munje tare,yace a'a nifa ban taba siyan abu a kasuwa ko gefen hanya ba a store nake siya,Na fara rokonsa dole haka ya fito muka karasa wajensu,sabo da tattalina da son kudi nace Malam kwano nawa nawa? Aayan yace nidai a zuba kawai mu tafi,nace a'a so kake ayi mana tsada bazai yuwu ba yo ni akan barkono kwano daya idan nazo sarowa Basai na yini a wajen ba ana ciniki ba kuma karshe kaga na siya arahar banza,Dariya Aayan yayi yace yini guda fa? Nace Cass ma kuwa, Agogon Dubu biyu ina siyoshi a Dari biyu da hamsim ni highest Dari biyar zan siyi shege,ka dinga zuwa dani siyayya kaga araha,Aayan kallona kawai yake yana dariya,Nace kai me kayan miya kwanon tattasan ne dari biyar a garin gaba gaba muke da zan siya haka,yace gaskiyar magana Dari hudu da hamsim baya tsada bana nawa kike so a siyar miki,Nace to ka rage,nafa San kan kasuwar nan,Aayan yace Haba Ke kuwa har kwano guda Dari hudu da hamsim kacal a kasa siya mene na tsada a nan? Harara na watsa masa tare da dan zungurinsa nayi masa magana a hankali bana son haka ba a yiwa yan kasuwa haka,zaka kashe min ciniki idan kasan haka zaka min ka koma mota yanzu duk ragi ai ragi ne,Aayan yace Malam zuba mana kwano biyar ga kudin ya zaro kudi ya mika,na fara rigima na cumimiye a jikinsa baza a biya ba kwano har Dari biyar gwara Ku tafi gida ni Ku barni a nan nayi cinikin ko Dari hudu na siya sai na samu Dari Dari ta Zama tawa,na dawo a taxi, ko kulani baiyi ba yace to tumatir fa,nace a tsaya ni zan Zaba da kaina,me kayan miya yana ta dariya yace kudi kudi ne ga gwalagwaje wanda ya gama lugwiguwicewa daf yake da rubewa kudinsa daban,ga masu kyau manya da kanana,nayi layin marar kyau gwalagwajen nace duk tumatir tumatir ne tunda dafashi za ayi mu sharbe miya Malam ga me sauki ba sai anyi asarar kudin ba a bamu wannan,Aayan dariya ta kamashi ta gaske ya dinga yi yace wlh baki isa ba gwara da Allah ya kawoni na gani dama abinda kike sawa muna ci kenan? Nace to sau nawa ka shanye miyar sa kana Santi ai ni in kaga lafiyayyan tumatir a fridge to na cin salat ne,ai ko harda kwalla Aayan yake dariya ni kuwa

Please Login or Register in order to submit comment