Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)

*Heart you so much*







*labari ne ƙirƙirarre,banyi dan cin zarafin wani ko wata ba,idan yayi dai-dai da rayuwar ki to an samu daidaito ne amma ba wai niyar tozarci ko wani abin ba*.

*Masoyana wa'inda na sani da wa'inda ban sani ba ina miƙo godiya ta a gare ku,sannan ina fatan zaku bani haɗin kai a wannan kamar yadda kuka bani a ƙareenateey,sai dai ina me baku haƙuri domin kuwa wannan zai fi ƙareenateey tsayi sosai duk da wancan ɗin ma yankewa nayi amma wannan babu wannan maganar dan haka ina fatan zaku bani haɗin kai sannan kuma zakuyi jimirin bibiyar shi har izuwa ƙarshe nagode sosai*.

Bismillahir-rahmanir-rahim.

📖📖01-02📖📖

Jejin dake hanyar Abuja idan ka baro kaduna,tafiyar mita ashirin daga ƙauyen banguwa,wani madaidaicin gida wanda yake kusan ginin ba'a ƙarasa shi ba.

Manya-manyan Bishiyoyi sune suka yiwa gidan ƙawanya inda baka hangen komai daya shafi gidan,ƙaton get ne irin na da wanda keda nauyi da kuma daɗewa.

Daga cikin gidan kuwa,wata irin farfajiya ce me girman gaske wanda ciyayi da kuma rairayi suka rufe wajen ba zaka iya gane yanayin ƙasar wajen ba.

Ƙofar da zata sadaka da ciki kuwa ƙofa ce ta ƙarfe me matuƙar nauyi,daka shiga wani falo ne ƙarami me duhun gaske wanda idan baka yi da gaske ba zaka iya bugewa,babu wani tarkace a falon banda kujeru da kuma tum-tum wanda suke ajiye a ƙasan carpet ɗin ɗakin.

Ta ƙaramin corridor kuwa doguwar hanyace wacce ke ɗauke da ƙofofin ɗakuna jere masu yawan gaske,daga ƙarshen corridor ɗin kuwa wani falon ne wanda yake babu kyan gani,saboda komai na ciki kalar ja ne,sannan ga wani irin tururin hayaƙi da yake fita me matuƙar ban tsoro da tashin hankali.

A ƙalla mutanen dake jere tsaye sanye da zani babba kalar ja jikin su babu riga,fuskar kowanne na nuna damuwa da ɓacin rai,sama dasu ishirin,kowanne kanshi babu koda ɗigon gashi.

Wani mutum duka suke kallo wanda yake zaune saman wata ƙatuwar kujera wacce gefen ta kuwa gunkin zakuna ne hannun dama dana hagu,gaban shi kuma ƙwarya ce babba wacce ke saman wuta tana ci sosai da sosai.

Tsayin minti biyar babu wanda yayi magana kafin can wani dake gefe yace cikin fusata da damuwa.

"haba Tuge wai wayo kake son ka gwada mana ko kuwa ɗan naka so yake yafi ƙarfin ka,yau shekara ashirin da biyar kenan da yiwa *oregbu* alƙawarin bashi jinin matar ka da ɗanka amma babu ɗaya daya samu".

Wannan dake zaune saman kujerar ya ɗago idanun shi da suka kaɗa suka yi ja ya zubawa wani mutumi wanda yake durƙushe gaban wannan ƙwaryar,cikin fusata yace; "bakaji tambayar da akeyi maka bane ko kuwa baka da amsar da zaka bayar ne?".

Cikin matsananciyar damuwa yace; "nayi iya yina *Appu* amma abu ya gagara matar nan ko gidan ta bata bari na kusanta kuma kun san hakan sannan dai-dai da rana ɗaya bata taɓa barin jikin su babu kariya ba shi kan shi yaron nawa ba sani na yayi ba,kuma fa kun riga da kun san hakan kuma tunda na yiwa Oregbu alƙwarin jinin sa aikuwa babu makawa jinin nashi ne".

Wannan daya kira da Appu ne ya miƙe tsaye sannan ya ɗauko wata sanda doguwa daga saman ta kuma tsini gare shi kamar kibiya ya ɗaga ta sama sannan yace; "har yanzu Tuge da sauranka,baka cika aƙawarin daka ɗauka ba dan haka sandar zama magaji tana nan a ajiye sai lokacin daka cika sannan Oregbu ya fara gajiya idan har baka kawo jinin ɗaya daga cikin su ba nan da lokaci kaɗan ba zaka fuskanci fushin shi".

Tuge ya buɗe baki zai yi magana Appu cikin tsananin tsawa yace; "maganar Oregbu itace magana baya buƙatar martani ko kuwa gardama,a fara gabatar da wankan tsari",dole yaja bakin shi yayi shiru.

Wani me ƙaton ciki ya taho cikin sauri ya ciri wannan ƙatuwar ƙwaryar dake saman wuta ya ɗaga ya miƙawa Appu shi ya fara sha sannan ya kwarara jinin a jikin shi wanda bana da tabbacin jinin na meye sannan aka miƙawa Tuge shima yayi yadda Appu yayi sannan sauran mutanen dake wajen.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
*HAYIN RIGASA,KADUNA*.

ƴan mata guda biyu ne suka sauka daga Keke Napep a bakin titi,dukan su suna sanye da pink din hijab wanda ya saukar musu dan har ya wuce gwiwa,ɗayar fuskar ta tasha make-up ɗaya kuwa babu wani kwaliyya a fuskar ta sai dai duk da haka kyawun ta ya bayyana,dukkan su kama ɗaya gare su wanda hakan ya tabbatar mini da cewa ƴan biyu ne kenan.

Wacce tayi make-up ɗin ta ya mutsa fuska tace; "Ramluv,wallahi na gaji sosai",wacce aka kira da Ramluv ɗin tayi murmushi kawai tana buɗe purse ɗin dake hannun ta,ta ciro ɗari biyu ta miƙawa me Keken tace; "malam bamu canjin mu".

Me Keke Napep ɗin ya leƙo da kan shi yace; "haba Hajiyoyi ai bakuda canji,tun daga Tudun nufawa sannan ku nemi canji haba mana".

Wacce tayi make-up ɗin da yawa ta kalle shi ta wurga mishi harara tace"wallahi baka isaba sai ka bamu canjin mu ai dama ɗari da hamsin muka yi da kai sannan koda ka kawo mu baka shigar damu cikin unguwa ba mun kuma ƙyale ka shine zaka ce ba zaka bamu canji ba wallahi sai ka bayar".

Shima ɗan Keke Napep ɗin ya fito ya tsaya cikin faɗa da fitsarar ƴan zamani yace; "idan kuma na hana me zaki yi mini?",ta kalle shi taja tsaki tace; "au tambaya kake ma to wallahi zaka sha mamaki kaɗan daga aiki na wallahi na saka ayi maka dukan tsiya ƙaryar rashin mutunci kake".

Ɗayar ta kalli wajen sannan ta kalle su yadda kowanne keji da ɗanyan kai ga kuma waje ya fara cika cikin murya me rauni tace; "Rimluv dan Allah kiyi haƙuri kizo mu tafi",ta juyo ta balla mata harara sannan ta cigaba da masifar ta.

Yadda suke kamar zasu yi dabbe ga jama'a a wajen,gashi taƙi ta dena ya saka ƴar uwar ta fara hawaye wanda ita bama ta lura da ita ba,ita kuwa daman ƙoƙarin ta taja ƴar uwar tata su bar wajen.

"banza ɗan iska mara mutunci",Rimluv ɗin ta faɗa cikin fusata,hannu ya ɗaga domin sauke mata mari ya sauke akan ƴar uwar ta wacce ke ƙoƙarin raba su,Rimluv ta kalli ƴar uwar tata tace; "ka mare ta wallahi ba zaka ci bulus ba",itama ta ɗaga hannu ta kwashe shi da mari,wanda hakan yayi dai-dai da zuwan wani dattijo.

Cikin sauri yace; Nusreen kece da dambe da maza a titi harda mare-mare?",ganin wanda yayi maganar yasa ta saukar da kanta ƙasa tana cuno baki.

Cikin daka tsawa yace; "kin wuce gida ko sai na ɗauke ki da mari shegiya me baƙin hali",ta ɗago da zummar yin magana ƴar uwar tata tayi saurin matse hannun ta,shiru tayi tana ƙwafa sannan ta kalli me Keke Napep ɗin ta harare shi,hamsin ɗin da yake miƙo mata ta fuzge sannan ta juya tayi gaba tana faɗin"matsiyaci kawai".

Kowa a wajen da abinda yake faɗa,ita kuwa gaba tayi tana tafe tana masifa,dattijon nan yace; "ki rufe mini baki ko kuma nayi miki duka a wajen nan me mugun hali irin na uwar ta",shiru tayi tana jin wani tuƙuƙi a cikin ranta wanda hakan ba ƙaramin takurata yayi ba na rashin bata damar maida mishi da martani da ta hanata yi.

Can ƙarshen layin wani gida na rufin asiri za'a ce dan kana gani ka san talakawa ne,duk da dai ya sha sumunti sannan da ƙofa irin ta zamani a jiki,gaban gidan kuwa siminti ne a shinfiɗe wanda ya ƙara fito da gidan.

Tana shiga ta banko ƙofar wanda saura kaɗan wannan Dattijon ya buge,aikuwa ya fara ɗebe mata albarka yana banbamin faɗa,ita dai hannun ƴar uwar ta taja suka shige ciki.

Tsakar gidan kuwa yana nan yadda suka zata,duk tarkace alamun tun safe ba'a yi shara ba kenan,gefen famfo wata matace ƙatuwa tana zaune tana faman tace ƙullun wara wanda hakan ke nuni da kayan sana'ar tane.

Nusreen taja tsaki bayan sunyi sallama bata amsa ba,tace; "mutum dai wuta zai shiga idan yayi wasa domin kuwa rayuwar yanzu bata da tabbas kayi aiki nagari ma yaka cika balle kowa ya san da cewa Sallah da salati bata dami mutum ba ai ba abin mamaki bane idan mutum yaƙi amsa sallama".

Wannan matar ta taso cikin masifa tace; "ke mara kunya fitsararriya wallahi idan baki dena shiga harkata ba a gidan zan jibge ki naga wanda ya tsaya miki".

Nusreen ta wulla mata harara tace; "gwara ni Allah ne ya tsaya mini ba boka ba",wannan maganar caraf a kunnen Dattijon nan wanda ya shigo yana nashi masifar.

Kanta yayi da gudu,ita kuma ta zuba da gudu tayi wani ɗaki wanda yake daga can lungu tana faɗawa ɗakin ta rufo ƙofar.

Cikin haki yace; "wallahi zaki zo ki same ni ne shegiya me zubin mayu,matar tawa kike faɗawa haka shegiya da haihuwar ki gwara ɓarin ki,zan kuma zo kan uwar taki ne wacce ke ƙara zuga ki",yana faɗin haka ya juya.

Dai-dai ƴar uwar tata ya tsaya wacce ke faman zare idanu domin tasan akan ta abin zai ƙare aikuwa kamar yadda ta zata yana zuwa ya zuba mata rankwashi sannan ya kama kunnen ta ya murɗa yace; "ƴar iska munafika kina zare idanu kamar ƙwan nufawa",ta girgiza kai hawayen azaba yana zubowa daga idanun ta.

Sai da ya gaji dan kan shi sannan ya saki kunnen,ya fice yana bambami,wannan matar me ƙiba ta kalle ta cikin huci,da sauri ta nufi ɗakin da ƴar uwar ta ta shige amma kan ta kai taji saukar kwano a kanta wanda yasa ta ƙwalla ƙara saboda azabar zafi.

Nusreen na daga ɗaki tana jin ihun ƴar uwar ta ta yunƙura zata tashi mahaifiyar su dake zaune ta wurga mata harara,bata son ɓacin ran mahaifiyar tasu hakan yasa ta koma ta zauna tana wuci.

Ita kuwa Nusram ganin babu sarki sai Allah yasa ta miƙe ta ƙaraso bakin ƙofar ta ƙwanƙwasa,Nusreen tayi sauri taje ta buɗe mata sannan ta riƙo ta suka shigo tare cikin ɗakin.


🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*UNGUWAR SARKI,KADUNA*.

wani katafaren gida wanda kana ganin shi ka san ƴan gidan sunci kuma sun tada kai,wanda zaka iya cewa basu ma san talauci ba,ko'ina ka duba a bakin gida securities ne ke kaikawo domin tsare lafiyar ahalin gidan.

Daga cikin gidan kuwa a ƙaton falon wanda yaji kayan more rayuwa,samari guda biyu na hango zaune saman kujera,sai mace ɗaya dake zaune a ƙasa rungume da filo tana danna waya,daga gefe kuma wata yar budurwar ce gefen ta yaro wanda ba zai wuce shekara goma sha biyu ba hannun shi riƙe da littafi da alamu karatu take koya mishi.

Jin taku da kuma wani fitinannen ƙamshi yasa dukan su ɗaga kai suka kalli Upstairs ɗin suna jiran ɓullowar me wannan ƙamshin,wata matashiyar macece wacce a ƙalla zata kai shekaru arba'in zuwa arba'in da biyar,fara me ɗan ƙiba,tana da tsayi wanda shiya ƙara ɓoye ƙibar tata,jikin ta sanye da wani danƙareren lace wanda a ƙalla zai kai dubu tamanin zuwa tamanin da biyar,ɗinkin borno wanda yake plain zani ne da kuma rigar iya gwiwa wacce taji aikin wuta,kafaɗar ta kuwa ta yafa wani gyale milk shima me tsadan gaske ƙafar ta sanye da takalmi high hill hannun ta na hagu saɓe da riga baƙa irin ta lawyers,wanda take sanye da wani siririn agogon azurfa wuyan ta sanye da siririyar sarƙar zinare,hannun ta na dama riƙe da jakar ta ƴar ƙarama kalar ruwan madara da kuma key tana kuma rike da wayar ta wacce kuma kunnen ta ke sanye da eye piece da alamu ma ya nuna waya take amsawa,sai dai yadda take murmushi zai tabbatar maka da cewa wanda take wayar dashi mutum ne me matuƙar mahimmaci a rayuwar ta.

"Baby,maganar ƙarshe da zanyi shine dole ka dawo gida a cikin satin nan idan ba haka ba zaka sha mamaki na",ta ɗan yi shiru alamun na can ɓangaren magana yake yi.

Cikin damuwa tace; "Baby ba zan canza magana na fara gajiya da halin ka,kodan kaga na damu da kai zan kira Daddyn ku Allah na faɗa mishi wannan halin naka,and maganar ƙarshe shine ka biyo jirgi gobe ka dawo gida ko kuma ka ganni a England ɗin na dai faɗa maka",bata jira cewar shi ba ta kashe wayar sannan ta kalli yaran nata da suka zubo mata idanu tace;

"zan tafi wajen aiki fatan baku da wata matsala",ɗaya daga cikin wa'innan samarin yace; "Mum,maganar canza mini motar fa,kinga......".

"Tameer,ya isa haka! Ina mun gama wannan maganar ka jira Daddyn ku nan da sati biyu",ta faɗa,cikin sauri ya buɗe baki zai yi magana tace; ya isa haka! Sai na dawo",daga haka ta fice.

Wanda ta kira da Tameer yayi ƙwafa yace; "wallahi na gaji da halin Mummy me yasa bata damu da halin da muke ciki ba amma ta damu da wancan wawan?".

Ɗayan saurayin wanda suke kama sosai daka gansu ka san ƴan biyu ne yace; "Tameer ka dinga ƙoƙarin ɓoye fushin ka mana,Abdul fa ɗan uwan mu ne".

Cikin fushi Tameer yace; "Abdul! Na tsani wannan yaron kamar yadda na tsani mutuwa ta",wannan budurwar dake zaune tana danna waya tayi tsaki tace; "nifa Yaya Tameer wallahi ina bayan ka kuma ko ni na tsane shi dan dai bani da yadda zan yi dashi ne".

Ɗayar dake koyawa yaron nan karatu tace; "Kai Aunty Surayya ki dena faɗin haka Yaya Abdul fa ɗan uwan ku ne ya kama ta ku dinga sassauta tsanar da kuka yi mishi",cikin fushi Surayya tace"dallah rufe mana baki,keda Yaya Sameer ai naga bakwa kishin kanku kuma wallahi ko ku canza ko kuma kuna gani zaku mutu babu yadda zaku yi mu dai zamu san yadda zamu yi".

Sameer yayi murmushi yace; "Surayya Sumayya fa ta fiki gaskiya,koma meye dai ɗan uwan mu ne",Tameer ya juyo yace; "eh ɗan uwan mu ne amma kuma Mummy bata ɗaukar hakan kana gani abinda ya faru da ace Abdul ne ya nemi ta canza mishi mota data canza amma da yake ni ne sai dai na jira Daddy".

Sumayya tayi murmushi tace; "Yaya Tameer kaifa kana da kuɗin da zaka canza motar ka me zai sa ka jira Mummy?",suka yi shiru duka,ita kuma ta kalli yaron tace; "Fahad tashi muje kayi wanka",tana faɗin haka ta ja hannun shi suka shige ɗaki ta bar su nan tsaye.

Surayya na ganin haka tayi ƙwafa ta wuce itama ta barsu,Tameer shima yayi tsaki yace; "Sameer duk kuɗi na ya kama ta ace tunda na tambaya Mummy ta siya mini,kada ka ɗauka iya kaina hakan zai tsaya wata rana zai tsallako kanka",daga haka shima ya wuce ya bar Sameer a tsaye.

Sameer yayi ƙwafa yace; "mahaukata waye yace musu ana fito da ƙiyayya oho! Abdul ka ƙwace mana komai taya kuwa zan so ka???".


#LIKE
#SHARE
#COMMENT

* Babyn Abdul,Maman Meenal,Elham da kuma Farouk*


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖3-4📖📖


Nusram ke zaune bakin famfo tana wanke-wanke, tana ta sauri domin tayi ta gama gudun kada tayi lattin zuwa makaranta, Mama Jummai ta fito da tarkacen kayan kwanukan ta ta zube gaban Nusram tace, "gashi nan tunda ba za'a fito da miji ayi aure ba sai a zauna ayi mana bauta", Nusram ta saukar da kanta ƙasa kawai tana me jin zafin magan-ganun na Mama Jummai.

Nan ta zube su ta juya tana mita; "to dama meye amfanin ku a gidan yara tun nonowa suna kirji har sun faɗi amma kun ƙi ku fitar da mazaje,ai wallahi dani daku ne a gidan ga uwar can tsohuwar munafika kullum tana ɗaki a kile kamar kayan wanki Musa a baki Fir'auna a zuci", Nusram ta ƙara kallon hanyar bayin inda ta tabbatar da cewa Nusreen na jiyowa fatan ta dai ace bata jiyo duka ba,sai dai ta makaro domin kuwa duka magan-ganun Mama Jumman a kunnen ta suke kuma Allah-Allah take ta gama ta fito domin bata amsa.

Tana fitowa Nusram tayi sauri ta miƙe, idanun ta cike da hawaye tace; "Pls Rim kada kice mata komai dan Allah", Nusreen ta galla ma ƙofar ɗakin Mama Jumman harara sannan tayi ƙwafa ta wuce, Nusram kuwa ganin hakan yasa tayi ajiyar zuciya sannan ta cigaba da wanke-wanken ta, Kan wani lokaci ta gama sannan ta kwashe nasu ta kai ɗaki ta ɗauki na Mama Jumman ta kai mata itama ƙofar ɗaki sannan ta juye nata ruwan ta shiga wanka.

Bata jima ba ta fito inda ta shiga ɗaki ta tarar da Ummi na zaune tanawa Kubra tsifa yayin da Nusreen ke faman sheƙa kwalliyya, Nusram ta kalle ta tayi murmushi kawai sannan itama ta hau shiryawa.

Atamfa ta saka me kalar pink da ash sai ratsin fari da baƙi kalar ta jikin Nusreen ɗin sai dai banbancin shine ɗinkin domin kuwa Nusreen tata fitted gown ne ita kuma Nusram tata me buɗewa ce daga ƙasa, bata tsaya kwalliyya ba kamar ƴar uwar ta mai da hoda kawai ta shafa sai kwalli data zizara ta ɗauki hijab ta saka kalar ash wanda ya kasance kalar uniform ɗin makarantar kenan ta tada sallah, haka itama Nusreen ɗin sai da ta gama tata ƙyale-ƙyalen sannan tayi sallah suka fice cikin sauri suna yiwa Ummi sallama akan sun tafi islamiyyar.

Ummi tayi musu addu'a da fatan nasara sannan ta ɗaga Kubra domin ta gama yi mata tsifar saura wanke kan.

Suna fitowa suka iske yaran Mama Jumman Atika da Ameera sun dawo daga tallan shinkafa da waken data ɗora musu, Nusreen ta kalle su tayi tsaki tace; "mutum bashi da aiki sai yawon tallace-tallace wata rana garin jarabar son kuɗi a kwasowa mutum abinda zai jefa shi a masifa", Mama Jumman ta fara balbalin masifa ita dai Nusram taja hannun ta kawai suka fice.

Kan hanya ma sai faman masifa take ita dai Nusram bata kula ta ba har suka iso bakin makarantar, ana ta taron latti amma da yake Nusreen ɗin akwai rigima haka ta wuce cike da taƙama tana taku ɗai-ɗai.

Nusram kuwa da sauran ɗaliban suka tsaya suna kallon ta, Malam Abbas shima ya bita da idanu da sauran malaman dake bakin wajen, ganin da gaske take yasa shi daka mata tsawa yace; "Nusreen Abdullahi Dabai ki dawo nan", ta juyo cike da ƙasaita tace; "sunan haka yake malamin addini babu kuskure", duka wa'inda ke wajen sai da suka kwashe da dariya wanda hakan ya kuma tunzura Malam Abbas ɗin yayo kanta da bulala.

Tsayawa tayi ƙyam tana kallon shi harya kawo kusa da ita kafin yaja dan kan shi ya tsaya, tana ganin ya tsaya ta saki murmushin ƙasaita tace; "ya ka fasa ai da ka zuba mini a jiki kawai", ta ƙarasa tana mishi wani kallo.

Duk abinda yake faruwa akan idanun shi kuma yana kallon meke faruwa ganin idan beje ba za'a yi abinda be kamata ba yasa ya taho wajen da sauri.

"meke faruwa ne?", ya tambaya, Malam Abbas yace; "latti tayi amma tazo ta wuce kamar zata shiga ɗakin su", Malam Saleem yayi murmushi sannan yace; "Malam Abbas ai

Please Login or Register in order to submit comment