Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waige-waige.

Ya buɗe gaban motar, ta tsaya tana tunanin ta shiga ko karta shiga, shi dai kallon ta kawai yake yi yana murmushi dan yanzu abin nata nishaɗin yake saka shi.

Ita kuwa tsakani da Allah take tsoron shi, dan bata mishi kallon mutumin arziƙi sai canza kama yake yi mata, bata kai ga ƙarasa tunanin ta ba taga ya nufo inda take, cikin sauri ta juya zata gudu, taku ɗaya ya ƙara ya cafko ta.

Janta yayi, faɗi take; "dan Allah ka ƙyale ni na tafi wallahi ina da ƙanwa da mama, kada ka cutar dani nima ba'a son raina ranar nan na faɗa maka magan-ganun nan ba", be saurare ta ba sai da ya tura ta cikin motar sannan ya maida ƙofar ya rufe kafin ya zagaya ya shiga ya tada motar suka fara tafiya.

Nusram gabanta banda faɗuwa babu abinda yake yi, gani take kawai ɗaukar fansa yake so yayi akanta na rashin kunyar da tayi mishi washe garin ranar da ya kaita asibiti.

Shi kuwa Abdul a hankali yake tafiya, lokaci zuwa lokaci ya kan juyo ya kalle ta, babu wanda yayi magana a tsakanin su, ita dai tana ƙanƙame da wayar shi har suka ƙaraso wani botique.

Ya fito ba tare da yace mata komai ba, Nusram dai tana zaune tana zare idanu, ɓangaren ta yazo ya bude sannan ya saka hannu yaa janyo ta, hannun ta ya riƙe gam sannan ya fara tafiya, zuwa lokacin Nusram ta fara cire rai da ƙara numfashi dan kawai ta kawo cewa gidan yankan kai ne ganin irin yadda wajen ya ƙayatu.

Yana shiga ƴan wajen suka fara gaishe dashi, Nusram na rungume da wayar shi a ƙirjinta, idanun ta ya kawo ƙwalla, wato ma shine babba a wajen kenan, wayyo! Ummi🙆.

Wani mutumi ɗan saurayi ya ƙaraso inda yake bayan sun gaisa sannan ya shiga gaba suna binshi a baya har zuwa wata ƙofa, ya buɗe musu suka shiga.

Wani ɗan ƙaramin falo ne me cike da kayan alatu, ga sanyin ac, be zauna ba ya kalli ɗan saurayin yace; "Nura hijab zaka ɗauko mata".

Wanda aka kira da Nuran yace; "yallaɓai wane kala?", Abdus-samad ya kalli Nusram, doguwar riga ce a jikin ta, ta yadin saytin kalar blue da pink, ba tare da ɓata lokaci ba yace; "kawo blue", Nusram ita dai banda zare idanu babu abinda take yi.

Babu jimawa yaron ya dawo hannun shi ɗauke da leda, ya miƙowa Abdus-samad ɗin, shi kuma ya nuna mishi Nusram dake tsaye.

Da murmushi a fuskar shi yace; "Madam ga hijab ɗin ko?", kamar wacce zata zuba da gudu tace; "ni?", yace; "eh mana", ta kai hannu a tsorace sai kuma ta janye.

Tana tsoron kada ta taɓa taji ance masu shan jini idan suka baka abu ka taɓa shikenan sai ka zama doya ko wani abin ko kuma ka ɓace gaba ɗaya.

Nura ya kuma cewa; "haba Madam ki amsa mana dan Allah", Nusram ta share hawayen daya zubo mata tace; "Allah ba zan amsa ba kar naje na ɓace, su kuke ku shanye jini na", Nura dabe fahimci me take magana akai ba ya maida kallon shi kan Abdus-samad ɗin yace; "yallaɓai........".

Abdul dake danna waya amma jin abinda ta faɗa yasa ya tsaya, wato har yanzu bata dena mishi kallon mugu ba kenan? Lallai zai koya mata hankali, ya miƙe ya matso kusa da Nuran yace; "bani hijab ɗin jeka kawai".

Nura ya miƙa mishi sannan ya juya ya fice, inda take tsaye ya nufo, da sauri ta fara ja da baya, ganin ta kai bango yasa ta fara faɗin; "dan Allah ka tsaya, nifa ba ƴar iska bace".

Ya saka hannu ya dafa bangon yace; "to waye ɗan iskan kenan" ta runtse idanu tace; "dan Allah kayi haƙuri ka barni na tafi", hannun shi ya kai saman kanta sai kuma ya fasa, ya ɗan matsa baya sannan ya miƙo mata hijab ɗin yace; "saka mu tafi", taƙi amsar hijab ɗin kuma taƙi kallon shi.

Cikin jin haushi ya finciko ta, ta dawo gaban shi sannan ya warware hijab ɗin ya saka mata kafin ya kama hannun ta yaja suka fice.

Har sun kusa ƙofar fita sai kuma yaja ya tsaya, janta ya kuma yi suka koma ciki, basket yaja ya fara ɗebar kaya, kayan make up na mata turarruka da kuma atamfofi da lace.

Be jima ya kuma janta aka zuba musu kayan a leda sannan suka fice daga wajen, sai da ya buɗe mota ya saka ta sannan ya koma ya buɗe baya aka zuba kayan, ya shiga mota yaja suka tafi.

Babu wanda yayi magana har suka isa Hayin Rigasa, har ƙofar gida ya kaita, tana ƙoƙarin buɗe ƙofa yace; "heys!, duk ranar da kika kuma gani na kika tsorata to tabbas daga ranar sai na kai jinin ki wajen gunkin mu", yana faɗar haka ya buɗe mata ƙofar.

Nusram jin abinda ya faɗa yasa ta fara yarfe hannu tana bashi haƙuri, ta miƙo mishi wayar tace; "dan Allah in dai dan wannan ne kake bibiyar rayuwa ta kayi haƙuri ga wayar ka".

Ya jingina da kujrerar da yake kai, ya saka hannu ya janyo ledar ɗazu ya miƙa mata yace; "gashi kayan da wa'incan suka amsar miki, yanzu fita ki bar mini mota".

Ta share hawaye tace; "ka amshi wayar ka, kayan kuma bana so na gode ni dai dan Allah kayi haƙuri", ya ɗaure fuska yace; "zaki amsa ki fice ko sai na canza ra'ayi yanzu na wuce dake wajen gunkin mu", kan ya rufe baki ya wafce ledar baki na rawa tace; "Allah ya baka haƙuri, na gode", ta fice daga motar.

Abdus-samad ya bi ta da kallo har ta shige gida, yayi murmushi wato dai duk girman mace da wayonta a tafin hannun ɗa namiji take kenan?.

Cike da nishaɗi yaja motar shi ya tafi, babu abinda yake yi sai murmushi dama asibiti zai je sai ya fara biyawa wajen Ƙawar Brr Farida ya kai mata saƙo, shine fa suka haɗu dan haka kai tsaye ya wuce asibitin.

*********⬇️⬇️**********

Hajiya Salma ta kalli ƴar ta cikin ɓacin rai amma da yake Alhaji Mustafa yana wajen sai ta daure tayi murmushi tace; "haba Khausar tunda yace zai dawo ai zai dawo ne, ki daure kici abinci nan kinji".

Alhaji Mustafa da be daɗe da shigowa ƙasar ba ya sami wannan mummunan labarin ko gida be jeba daga Airport ya wuto asibitin hankalin shi a tashe.

Kusa da ita yazo ya zauna sannan ya riƙo hannun ta yace; "ki daure kici abincin kin ji zai zo yanzu", Khausar ta maƙe kafaɗa alamun bata yarda ba.

Hajiya salma ta buɗe baki zata yi magana ya turo ƙofar tare da yin sallama, Alhaji Mustapha jikin shi har rawa yake yi ganin wanda ya shigo.

Abdus-samad shima dai da kallo ya bishi, cikin ranshi yana mamakin dama wannan ƴar Mustapha Abubakar Tuge ce?.

Hajiya Salma kuwa kamar ta ɗora hannu akai tayi ihu haka take ji, ya gaishe dasu sannan ya ƙarasa inda take.

Khausar ta saki murmushi tace; "ina ka tsaya tun ɗazu nake zaman jiran ka?", ya ɗauki plate ɗin abincin ya ɗebo ya nufi bakin ta dashi.

Ta buɗe baki ta amsa, yayi murmushi har kumatunshi ya lotsa yace; "dama yunwa kike ji kenan?", ta kai hannun kan kumatun shi tana murmushi, haka ya bata abincin har ta cinye.

Da kanshi ya taimaka mata ya gyara mata kwanciya, ta riƙe hannun shi gam, be hanata ba sai ma fira da suke yi sama-sama.

"ban sani ba ko jinin da ka bayar ne yasa nake gani kamar mun jima da sanin juna", ya ɓata rai yace; "waye ya faɗa miki".

"baka san ina da ƙawa a nan asibitin ba?", ya ɗaga mata gira ɗaya tayi dariya tace; "ai nima likita ce amma ɓangaren mata", ya ɗaga mata yatsu alamun jinjina👍.

Haka suka cigaba da fira tsayin lokaci sannan yace; "to yanzu ki kwanta sai da safe ko?", tace; "to amma gobe zaka zo da safe?", ya girgiza mata kai "sai lokacin dana sami dama, bye", daga haka ya fice.

Alhaji Mustapha ya miƙe da sauri ya bishi, har ya kusa parking lot, "Abdus-samad", ya kira shi, ya ja ya tsaya.

"mun gode sosai da kulawar daka nuna mata", abinda Alhaji Mustapha ya faɗa, Abdus-samad ya ɗan yi murmushi yace; "babu komai, Allah ya bata lafiya dai kawai".

Ya shiga motar shi yaja ya bar Alhaji Mustafa a tsaye cike da mamaki farin ciki da kuma damuwa.

Gashi ga ɗan shi amma bashi da damar zuwa kusa dashi, hasalima ƙara matsar ɗan nashi da zai yi hakan barazana ce ga rayuwar yaron dan a haka ma koda yaushe cikin barazana yake da takurawa akan yadda zai kawo ɗan nashi wajen Appu domin sadaukar da jinin shi ga oregbu.

Haka ya juya ya koma cikin asibitin cike da damuwa, Hajiya Salma dake laɓe tayi ajiyar zuciya kafin itama tayi saurin barin wajen tana godiya ga Allah da asirin su be tono ba.

Washe gari da safe Abdus-samad be samu damar zuwa asibitin ba, domin Brr Farida da ta tsare shi suka tafi court tare.

Hajiya Salma ta kalli jug ɗin dake cike da haɗaɗɗen juice taja tsaki, ta maida kallon ta kan Khausar wacce ke kwasar barci hankali kwance ta gama zaman jiran shi be zo ba.

Ta zaro wayar ta ta kira Alhaji Sa'eed, "yau fa bezo ba gashi tun ɗazu na haɗa mishi nake zaman jiran shi", Alhaji Sa'eed yayi dariya yace; "kada ki damu ina ji a jikina mun kusa yin nasara".

Brr Hauwa ta amshi wayar tace; "kada ki damu zai zo ne abinda ya kamata ki maida hankali akai shine ki tabbatar ya sha kafin ya bar asibitin.

Tace; "tabbas kuwa zai sha kafin ya bar asibitin nan, ku dai ku jira kirana kawai dole wannan shegen yaron ya mutu".

Alhaji Sa'eed yace; "da kyau, haka nake son ji, muna zaman jiran ki", ta amsa da to sannan ta kashe wayar.

Babu jimawa Abdul yayi sallama ya shigo, Hajiya Salma ta washe baki bayan sun gaisa tace; "ai ta gama rigimar baka zo ba tayi barci", ya matsa kusa da Khausar ɗin yace; "to bari na tafi kawai na dawo da yamma".

Da sauri Hajiya Salma tace; "a'a ka zauna mana ko wani abu ne ka sha tukunna sai ka tafi ya juya yace; "kada ki damu Hajiya nagode", tace; "aikuwa ba zai yiwu ka tafi yanzu ba", dole tasa ya koma ya zauna ta miƙo mishi.

Kiran wayar shi ya hana ya kai kofin bakin shi, sun ɗan jima suna magana kafin ya katse wayar ya duba Hajiya Salma yace; "idan ta farka kice mata nazo na tafi amma wata kila anjima na dawo", kamar zata yi kuka tace; "shikenan amma da ka sha koda kaɗan ne", yayi murmushi yace; "am ok, thanks" daga haka ya fice.

Hajiya Salma kamar ta ɗora hannu a kai tayi ihu, cikin jin haushi ta kira Alhaji Sa'eed ta bashi labarin abinda ya faru.

Shima dai ranshi ya ɓace amma yace kada ta damu komai nada lokaci idan ya tsallake yau wata rana zai faɗa ne.


Sai da suka ƙara kwana biyu sannan aka sallame ta, zuwa lokacin ta sami sauƙi sosai, Alhaji Mustapha kuwa kullum sai ya zo asibitin ko dan haduwa da ɗan nashi suna haɗuwa amma ba yadda ko wanne uba Ke so ba.

zuwa lokacin kuma saura kwana sha biyu Family meeting ɗin su Abdul ɗin, dan shi tunda aka sallami Khausar daga asibiti be kuma zuwa ba hasalima be je gidan su ba ko sau ɗaya.

cikin kwanakin da Baba ya ɗibarwa Nusram har anci kwana bakwai, zuwa yanzu kam hankalin Nusram ya fara tashi sosai domin kuwa bata da hanyar da zata sami mijin da yake shirye ya aure ta cikin sati ɗaya.

Tunda kwanakin nan suka matso kullum sai Nusram tayi tsayuwar dare tana addu'ar Allah ya fitar da ita daga wannan halin da take ƙoƙarin faɗawa.

Ummi kuwa a haka zaka ganta cikin jarumta amma da zarar ta keɓe babu abinda take sai kaiwa ubangijinta kukan ta, Aunty ma duka abin ya dame ta sai dai bata da yadda zata yi.

Yau ta kira Nusram ta waya tace tazo tana nemanta, duk da yamma ta fara yi haka Nusram ta shirya, niƙaɓ ta ɗaura a fuskar ta domin kuwa sa idon na ƴan layin su ya fara yin yawa.

Koda ta isa gidan ta sami ƴan gyaran jiki da kuma masu siyayya, Nusram ta taya ta wajen gyaran amaren da kuma tattara kayan.

Bayan sun gama ta kalli Aunty tace; "Aunty bari na shiga wajen Aisha yanzu zan dawo", Aunty tace; "to kada ki daɗe kinji", ta amsa da to.

Gidan dake jikin gidan Auntyn nan ne inda Yaya Sulaiman yake da amaryar shi, lokacin bikin Nusram bata sami damar zuwa ba saboda Baba da ya hanata fita ko'ina.

Ta sami Amarya Aisha sun jima suna fira domin tana da kirki sosai, sai da ta tsare ta har taci abinci sannan ta ƙyale ta taho.

A zaune ta sami Aunty kusa da Abba gefen shi kuma Yaya Sulaiman ne, ta yi mishi murmushi sannan ta maida kallon ta kan Abba ta gaishe dashi cikin mutunci ya amsa da sakin fuska har yana tsokanarta.

Sai da ya ɗan yi shiru sannan ya kira sunan Nusram, ta amsa tana me ƙara yin ƙasa da kanta.

"kin san dai tun kina ƙarama kike gidan nan ko?, anan kika tashi har kika girma, mun san halin ki mun san abinda zaki iya aikatawa da wanda ba zaki iya aikatawa ba, Nusram ni da Auntyn ki kallon ƴa muke yi miki, haka Sulaiman da ƙannen shi kallon ƴar uwa suke yi miki, abinda ya shafe ki ya shafe mu haka abinda ya shafe mu na san ya shafe ki, in da yau zaki ganmu cikin matsala na tabbatar da cewa zaki yi duk yadda zaki yi kiga mun fita daga wannan matsalar to dan haka dole ne muma idan muka ganki a cikin matsala muyi ƙoƙarin fitar dake daga cikin ta, jiya Auntyn ki ta same ni na faɗa mini halin da kike ciki keda mahaifiyar ki, na san da cewa ba zaki taɓa so ace ta dalilin ki auren iyayen ku ya rabu ba, a gaskiya da ace tun farko mun san da cewa hakan zai faru to tabbas da Sulaiman ba zai auri kowa ba sai ke amma da yake Allah shine masanin komai, abin be faru ba sai bayan auren, kin san dai da cewa samin miji a zamanin nan wuya yake yi, wanda kuka shekara kuna soyayya ma sai yaci amanarki balle wanda kake nema cikin abinda yake ƙasa da sati ɗaya to kallon wannan yasa muka yanke shawara shine Sulaiman dai ɗan uwan ki ke dan haka mun bashi izini zai aure ki nan da sati ɗayan in Allah ya yarda, naso ma tun jiya naje gidan ku na sami mahaifin naki amma Sulaiman ɗin ya roƙeni akan mu bari mu ji ta bakin ki tukunna wannan shine dalilin da yasa muka ce to kizo, kin amince da zaɓin da muka yi miki?".

Nusram kuwa tun lokacin da suka haɗa ta da Yaya Sulaiman numfashin ta ya fara sama, hannu ta saka ta dafe ƙirjinta tana addu'o'i har ta samu numfashinta ya ɗan dai-daita.

Ta kalli Aunty haƙiƙa su ɗin masoyanta ne wa'inda ba zata taɓa mantawa dasu ba, ba zata iya kallon Aunty tace; "bata son ɗan da ya fito daga cikin ta ba, idan tayi la'akari da yadda ta ɗauke ta kamar ƴar data haifa, tun tana ƙarama take ɗawainiya da ita".

Abba mutumin da yake nuna mata kulawa wacce ta rasa daga mahaifin daya haife ta, shiya tsaya mata a lokacin da take buƙatar taimako, lallai ba zata taɓa kallon shi tace bata son abinda ya fito daga jikin shi ba.

Yaya Sulaiman wanda ya zame mata yaya guda ɗaya tamkar da dubu, taya zata kalle shi tace ma bata son shi, wanda yayi hidima da ita tun tana ƙarama, har ta girma ko ranar bikin su duk kayan data saka ko kuɗin da tayi amfani dashi shine ya basu ba zai taɓa yiwuwa taƙi shi ba.

Taja ajiyar zuciya goshin ta sharkaf da zufa ta buɗe bakin ta wanda yayi nauyi tace....................".


*ZUCIYATA WHERE ARE YOU, gafa Nusram ɗin ki cikin tasku, kizo ki taimako ta, godiya gaba ɗaya kacokam ga *RAYUWAR ABDUS-SAMAD FANS CLUB* da kuma *ZAMA NA AMANA 2* musamman ma *ZAKARIYYA KHADIJA, AISHATU BABAYO(ZUCIYA TA), ABDUL ƘIRU, IBNATU, MAMAN ABDUL* banda bakin yi muku godiya.


#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*



♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖45-46📖📖


Tace; "nagode Aunty, kin nuna mini ƙauna wacce koda ace ke kika haife ni iya wacce zaki bani kenan, Abba ka kula dani kulawar da ko Mahaifina be bani ita ba ban ɗauka a komai ba face kai ɗin matsayin Uba, me zan iya ce muku da kuka bani Yaya wanda yake kula dani a matsayin ƙanwar shi, abinda yasa kullum hankalina ke kwanciya saboda Allah ya bani madadin duk wani abu dana rasa, da farko ya bani Uwa biyu yazo ya bani Uba kamar ka Abba sannan ya haɗa mini da Yaya idan ban godewa Ubangiji ba ai nayi mishi butulci".

"wallahi umarnin ku ni mai yin biyayyace, sai dai kuma kada mu duba kanmu a kowanne lokaci mu dinga duba wasu ma wa'inda zamu iya cutar dasu suma, Aisha amarya ce da yin auren su befi sati biyu ba nan kuma da sati ɗaya sai ayi mata kishiya anya kuwa an mata adalci?".

"Aunty ki ɗora wannan abin a kanmu idan da ace Safeena za'a yiwa haka ko Halima fa? Na san ba zaki taɓa jin daɗi ba, to a bar magana tasu ma idan kuma ni aka yiwa fa?, ko Nusreen data ɗebi kwanaki a gidan ta ba zamu ji daɗi ba ace anyi mata wannan, to yadda ba zamu ji daɗi iɗan anyiwa namu ba to muma kada mu yiwa wani, na gode ƙwarai da wannan shawara sai dai nima ku duba nawa magan-ganun dan Allah".

ɗakin yayi shiru, kowa yana tunani daban dana ɗan uwan shi, Nusram ta kuma cewa; "dan Allah kada mu aikata aikin da za muyi dana sani amma idan har kuna ganin abinda kuka yanke shine dai-dai to ni meyi muku biyayya ce".

Abba yace; "tabbas abinda kika faɗa Nusram gaskiya ne, mutane zasu zage mu sannan bamu san wane irin kallon dangin ta za suyi mana ba, dan haka zamu cigaba da taya ki da addu'a kawai".

Nusram tayi ƙasa da kai tace; "na gode Abba, Allah ya ƙara girma", Yace; "Ameen, Allah yayi muku albarka, Sulaiman tashi ka maida ita gida".

Ya amsa da to sannan ya miƙe daga gaban iyayen shi, itama ta miƙe tana yiwa Aunty Sallama, Aunty tace; "Allah ya tashe mu lafiya Nusram Allah kuma ya dube ki, ki gaishe da Maman ki", tace; "to.

Har suka isa ƙofar gidan su Nusram babu wanda yayi magana, kowa kuma abinda yake tunani daban.

Nusram harta yunƙura zata buɗe ƙofa ta koma ta zauna, tace; "Yaya kayi haƙuri da abinda ya faru ba wai ba zan iya auren ka bane a'a zan so ace kaima ka fahimce ni kamar yadda suma suka fahimce ni".

Yaya Sulaiman ya numfasa yace; "kada kice komai, waye zai fahimce ki sama dani, mun rayu tun muna yara tare kallon abu kika yi na san me kike nufi balle har ta kai ga kin furta, kije gida kawai sai da safe nima zan taya ki da addu'a".

Tayi murmushi tace; "na gode sosai sai sa safe", yace; "Allah ya tashe mu lafiya", tana fita ta haɗa ido da Baba wanda ke tsaye yana jiran fitowar Isa da alamu lissafi zasu yi ko wani abin.

Yaya Sulaiman ya danna mata horn ta juya ta ɗaga mishi hannu, ya ɗago mata hannu sannan yayi reverse ya bar wajen.

Cikin natsuwa ta fara tafiya, "barka da dare", abinda ta faɗa kenan lokacin da tazo gifta Mahaifin nata, Baba yace; "waye ya ajiye ki a mota yanzu?".

"Yaya Sulaiman ne", cikin daka tsawa yace; "rufe mini baki gantalalliya ni zaki rainawa wayo, wato Sulaiman ne ya kawo ki ko, kai ni kam banyi sa'ar haihuwa ba, to bari kiji wallahi daga kwanakin dana ɗibar miki babu ƙari, nan da sati ɗaya idan baki fito da miji ba ni da ke ne", Nusram tace; "to Baba", ta wuce gida.

Tana shiga zaure Isa na fitowa daga ɗakin shi, ya kalle ta ya kwashe da dariya yace; "baki da miji da ya wuce ni ɗin nan".

Bata kalle shi ba ta shige cikin gida, Mama Jummai dake gaban murhu tace; "an gama yawon ta zubar ɗin kenan?", itama dai Nusram bata kulata ba.

Ɗaki kawai ta shiga, ta yiwa Ummi sannu da gida, Ummi tace; "ya kika baro su", tace; "suna lafiya sun ce ma a gaishe dake", Ummi tace; "masha Allah".

Har zuwa lokacin da suka kwanta Ummi bata tambaye ta ya suka yi da Aunty ba itama kuma bata faɗa mata ba.

Ta zurfafa kanta cikin tunani ganin cewa gobe fa saura kwana shida kenan, dole tayi wani abu a kai idan ba haka ba tana ji tana kallo matsalolin gidan su zasu fi ƙarfin ta.

Shawarar da taji ta kwanta mata a rai ita ta fara ƙoƙarin bi, dan haka cike da ƙwarin gwiwa tayi barcin ta.

Washe gari da safe duk wasu ayyukan da ta san zata yi duka

Please Login or Register in order to submit comment