Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga haka babu wanda ya kuma magana a tsakanin su, fin minti biyar sannan aka buɗe ƙofar falon aka shigo da sallama.

Taɓ 🤔! Kallo ya koma sama shaho ya ɗauko giwa 😂😂.

Wata ƴar ƙwalisar tsohuwa ce baƙa ta shigo falon tana taku ɗai-ɗai, ko kayan jikin ta ka kalla kasan cewa ba ƙamar mace bace dan ita mayafi ta yafo saman atamfar da ta saka Holland, ɗinkin doguwar riga wanda ya zauna a jikin ta sosai babu abinda take sai tashin ƙamshi me shegen daɗi.

Kallo ɗaya ta yiwa Brr Farida ta ɗauke kanta, itama kuma Brr Farida bata kalle ta ba, sama da minti biyar shiru sannan Brr Farida tace; "ina wuni".

Taja tsayin lokaci me nisa kafin ta iya cewa; "lafiya lau, ƴar mulki", Brr Farida ta saki wani murmushi na ƙasaita.

Wacce ke saman dinning ɗin ta gama cin abincin ta sannan ta sauko itama kujerar tazo ta zauna ta ɗauki remote ta kunna plasma ɗin dake maƙale a jikin bango.

Ɗan juyowa tayi ba tare da ta kalli ɓangaren Brr Farida ba tace; "ina wuni Brr?", Brr farida ta amsa da ; "lafiya lau Fatima".

Babu wanda ya kuma magana hakan ya bawa Abdul damar gaishe da kakanin nashi guda biyu duka sun amsa babu yabo ba fallasa sai dai wannan ƙasaitar tana nan.

; "Ina wuni Aunty?", Fatimar ta kalle shi tace; "lafiya lau, fatan ka dawo lafiya", ya amsa da lafiya, wacce dai ke rubutu ce har yau bata ɗago ba balle ma naga ya fuskar ta take.

Abdul yace; "Ina wuni Brr", cak ta tsaya da zana biron da take saman takardar sai da taja lokaci kaɗan sannan ta ɗago.

Kyakkyawa ce ajin farko dan sai nace ta kusa kamo Brr Farida a kyau, fara ce sosai wanda farin ta har ɗaukar idanu yake yi kana ganin ta ka san ƴar hutu ce gaba da baya.

Cikin hausa irin ta ƴan boko da kuma zamanin yanzu wacce take cike da ƙaƙale tace; "brr!? Ashe haka kake kiran uwar ka kenan?".

Brr Farida ta saki wata irin dariya me cike da nishaɗi da annashuwa kafin ta janyo ɗaurin ɗankwalin ta ya dawo gaba tace; "wallahi idan kina ƙoƙarin haɗa kanki dani Brr Hauwa dariya kike bani sosai, kema fa cewa ki kayi Uwar shi ai kin san tsakanin mu da bambamci".

Brr Hauwa cikin fushi tace; "ai a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe ne Brr Farida", aikuwa babu sanya tace; "nifa na riga da na zama ƙadangaren bakin tulu zama dani ya zama dole".

Brr Hauwa tace; "kada ki manta kayan aro har abada na aro ne, kuma wata rana gaskiya zata yi halin ta".

"ko a yanzu kasuwa ta faɗi ɗan koli yaci riba sannan ki sani ni ɗin ruwan jakara ce idan baki sha ni a kauye ba zaki sha ni a birni".

Cikin sauri kafin Brr Hauwa tayi magana Fatima ta dakatar dasu ta hanyar cewa; "wai meye hakane kuke abu kamar yara ƙanana ku baku haɗuwa waje ɗaya ne sai kun nuna halin ku".

Brr Hauwa tace; "wane kalar hali ai wallahi ko yanzu na san sama tayiwa yaro nisa sai dai ya ɗaga kai ya kalla, domin kuwa idan na raina kasuwa ko sautu bana bayarwa".

Brr Farida ta miƙe tsaye ta taka har gaban Brr Hauwa tace; "nafi ƙarfin ki kira ni da ƙarama domin kuwa ke kanki kin sani hangen dala ba shiga birni bane kuma ba girigirin ba tayi mai, irin ku masu cika baki suna bani mamaki sosai ki sani ni ɗin ce Brr Farida Alƙali har yanzu sunan a haka yake be canza ke in banda ruwa ya daki babban zakara da idan aka ce ki kalle ni ki faɗa mini wata maganar da ba zaki yi ba wallahi koda kuwa kuɗi aka baki kada ki manta nifa itace kabari ce na danne uban kowa dakalin majina a hauni a zame na hau mutum na zauna dai-dai, murucin kan dutse ban fito ba sai da na shirya, kainuwa dashen Allah ba dashe na mutum ba.

"da bamu san asalin ungulu ba sai muce daga misra take, dama dangin ku ai dangin taƙama ne da taka haye", amsar brr Hauwa kenan wacce ke tsaye gaban Brr Farida.

"kada ki manta tunkan a haifi uwar me sabulu balbela take da hasken ta kuma dama ɗawisu ai kowa da zanen ta ya ganta, ke ƙaramar yarinya ce Hauwa ki bini a sannu idan ba haka ba zan koyar dake darasin da ba'a taɓa yi miki ba", daga haka Brr Farida ta ɗauki jakar ta sannan ta juya wajen tsofaffin biyu dake kallon su tace;

"zan tafi Malama, Hajja sai anjiman ku", tana gama faɗin hakan ko Abdul ɗin bata yi zaman jira ba tayi waje kawai.

*tofa abu ya fara fin ƙarfin jin Deeje ƴar gidan Ahmadu jikan inusa, ni kaina a dunƙule suka bani shiyasa nima na baku a haka amma zan ajiye biro na haka har sai naje na tambayo fassarar wa'innan maganganun dan kada inje ko bindige ni suke nufi ayi*.


*kuyi haƙuri da abinda kuke samu daga gare ni kunji na san ina yin delay ɗin posting ɗin amma ku ƙara haƙuri saboda ina da uzururruka a gaba na sosai*.


#LIKE
#SHARE
#COMMENT
#VOTE

*Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.






♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*godiya gare ku*.

*Aishatu Babayo*.
*Salamatu( kaka ta)*.
*Hafsat A garkuwa*
*Aunty Ummee*
*Kamal no love*
*Rukayyat Imam (Mama na)*
*Ibanatu*

Na gode sosai da sosai ku ɗin aminan ƙwarai ne kuma mutanen kirki ina ji daku sosai da sosai.

*ina cigayar Khairat aminullah, da Hajjaju dan Allah wanda ya gane mini su ya taimaka yace One Love na neman su*.



📖📖13-14📖📖



Hajja tace; "lallai wuyan ki ya isa yanka Farida har gida kizo ki zage mu tas", ita dai Brr Farida bata san suna yi ba dan tayi nisa da tafiya.

Brr Hauwa tace; "yaushe dama take da wata tarbiya irin tarbiyar gidan su kenan, kuma irin ta take bawa yaran dakta tunda shi yaji ya gani".

Fatima tace; "dan Allah ya isa haka, ku bar naganar mana", Hajja tace; "ba zamu bari ba Uwar mu sai munji duka".

Abdul kuwa a hankali ya sulale ya bar musu ɗakin domin ya san idan sun gama kan shi zasu dawo nan aka barsu da cece kuce ɗin su wanda baya ƙarewa.

Ɗakin ya tura ya shiga a hankali yana nan yadda yake, komai a tsaftace, ya saki murmushi sannan yace: "Fadil kenan akwai tsafta", gefe ya ajiye jakar shi sannan ya faɗa saman gadon.

Ya jima yana tunani wanda shi kanshi be san na meye ba, sannan ya miƙe ya nufi bayi yayi wanka, cikin riga shirt mara nauyi fara da kuma wando jeans fari ya shirya.

Koda ya fito falon dai ya nufo babu kowa a ciki sai yara guda biyu da suke wasa, suna ganin shi suka nufo shi, ɗai-ɗai ya dinga ɗaga su sama yana ajiyewa.

Namijin yace; "Uncle A baka zo da Adnan ba?", ya ɗaga mishi kai yace; "ai yana gida saboda makaranta", Yaron yace; "da kazo dashi da ba sai mu dinga tafiya daga nan ba".

"au hakane kuma fa! To yanzu dai kayi haƙuri sai idan na sake dawowa", yaron yayi murmushi, maccen kuwa ita daga gani bakin ta ma be buɗe ba dan haka ya riƙo hannun su zuwa falon ya zaunar dasu.

Ɗakin dai wannan tsohuwar ya nufa, tana zaune tana linke kaya, tunda ya shigo take kallon shi tana murmushi har yaja ya zauna kusa da ita.

Shi dai be san me yasa yake son matar ba kuma yake ganin tsananin ƙaunar shi daga idanun ta a iya sanin shi kishiyar mahaifiyar baban shi ce.

Wayar shi ya zaro ya nemo number ɗin Mum ɗin shi, sai da tayi ringing sosai sannan ta ɗaga.

"Baby sai yanzu ka tuna dani kenan?", ta faɗa tana dariya wacce dariyar tana zuwar mishi har cikin kunnen shi.

Ya shafa sumar kanshi kamar yana gaban ta yace; "First Love barci ne ya kwashe ni", sai da tayi jim sannan tace; "fatan dai kayi addu'a", ya ɗaga kai yace; "eh sosai ma".

Haka suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa, har take fada mishi ashe Daddyn su yayi musu oder na motoci?" yace; "eh amma ni nafi so ya dawo ne".

Ta ɗan yi dariya sannan tace; "ai zai dawo ne yace ƙarshen watan nan in Allah ya yarda yana hanya, yauwa na san mota ɗaya tayi maka kaɗan shi yasa nake jin zan ƙara maka koda biyu ne su zama uku kenan".

Yayi shiru na wani lokaci kafin yace; "Mum ki bar ɗayar kawai ta ishe ni rayuwa", tace; "ba zai yiwu ba dole ka ƙara tunda kaga baka da wata motar a yanzu, gobe idan kazo office ɗina za'a turo mini da hotuna sai ka zaɓa kawai, maganar fara aikin ka fa?".

Ya shafa gefen fuskar shi yace; "Mum ni ina so na fara idan Daddy ya dawo saboda komai yana buƙatar tsari sannan kinga ban san ina su Yaya Tameer suka tsaya ba".

"hakane shikenan mu bari idan ya dawo ɗin, I love you", yace; "love you too", sannan ya katse wayar.

Malama taja dogon ajiyar zuciya tana ɗauke idanun ta daka barin kallon shi domin kuwa duk tsayin wayar da suka yi tana kallon shi ne har ya gama, haka kuma wani abu yana taso mata daga ƙasan zuciyar ta.

Abdul yace; "Malama wai ina Fadila ne da Fadil?", tace; Fadil na wajen aiki Fadeela ma haka", shiru ya biyo baya kafin kuma ya dube ta yace; "nifa yunwa nake ji".

Bata kalle shi ba tace; "kaje wajen Hajja mana nasan ba zaka rasa abinda zaka ci ba ko kuma ka tafi part ɗin Abban ku".

Girgiza kai yayi yace; "bari dai naje Part ɗin Abban amma wajen Hajja ɗin nan da sauƙi dan na san su Husna basa nan suna makaranta ba lallai a samu abinci ba", daga haka ya fice.

Shiru ƴar tsohuwar tayi tana me bin inda ya fice da kallo, sosai ta kasa daurewa ta saki kuka me cin rai wanda ni dai ban san dalilin kukan nata ba.

Tunda ya fita yake haɗuwa da matasa da ƴan matan gidan wa'inda wasu sun dawo aiki wasu kuma sun dawo makaranta, haka suke gaisawa cikin mutunci duk da dai halin nan nasu na shariya da taƙama da wasu suka ɗebo.

Shifa tsarin gidan su yana bashi mamaki, sai mace ta kai shekara ashirin da biyar bata yi aure ba wata talatin duk wai da sunan boko don dole ne sai kin gama university kuma sai kin fara aiki shi yasa dan kuɗi fa akwai su haka ilimi.

Wani gidan dake ɓangaren daman shi jeri na huɗu gida na biyu nan ya ƙwanƙwasa me gadi ya buɗe mishi suka gaisa cike da girmama juna sannan ya shiga ciki.

A garden ya jiyo hayaniyar su wanda hakan ya nuna mishi suna can kenan, a can kuwa ya tarar dasu.

Ƴan mata guda uku da samari guda huɗu sai mahaifiyar su dake zaune a gefe da laptop a gaban ta alamu ya nuna aiki ma take yi.

"Lallai muna da manyan baƙi ga baƙon India a gidan mu", ɗaya daga samarin ya faɗa, Abdul ya harare shi yace; "bana son yawan surutu fa Kabeer har ka dawo kenan?".

Ya miƙa mishi hannu suka gaisa sannan yace; "ban daɗe da dawowa ba dan ma na biya na ɗauko Aunty Khaleesat ne a office daba dan haka ba da tun Uku zan dawo".

Sauran ya miƙawa hannu suka gaisa duk suna tsokanar shi, shi dai kawai murmushi yake yi, ɗaya daga cikin matan data kafe shi da idanuwa.

Ya kalle ta ya zaro idanun nashi yace; "ya akayi ne Saleema", Murmushi tayi tana kauda kai, biyun suka kalli juna suka kwashe da dariya.

"Wallahi Abdul ina ji gaba ma cewa zaka yi ka girmi har su Abba jifa wai Salima babu ko ɗan Sister ma a jiki".

"to ai ba wai ta girme ni bane da yawa", Maman nasu ta riƙe haɓa tace; "kai Abdul lallai na shaida son girman ka to ba Saleema ba ko Hafeeza ta girme ka, kaifa sa'an su Fadil ne da Fadeela kaga kuwa tsirar ka da Muhibba wata biyu ne Muhibba kuma su Fadeel wata ɗaya suka bata, ai daga Kabeer sai Kamal sune ƙannan ka amma duka sauran sun girme ka".

Ya juyar da kai yana murmushi, Hafeeza tayi dariya sannan tace; "Mummy ta tona maka asiri dai", ya ɗan juyo ya harare ta kaɗan sannan yace; "nifa yunwa nake ji".

Cikin sauri Saleema ta miƙe tana faɗin bari nayi maka setting ɗin table sai kazo kaci", babu wanda yayi magana sai fira da suka cigaba a tsakanin su.

Gidan Ambassador Ibraheem Yunusa Nagimi kenan, Jakadan Nigeria a ƙasar Italy, shi mahaifin Abdus-samad yake bi, yana can ƙasar Italy ɗin sai dai lokaci zuwa lokaci yake kawo ziyara ƙasar ta nigeria.

Yana da mata guda biyu amaryar ita ke can inda sukan yi wata shida-shida ne sai ɗaya ta canji ɗaya, doka ce ta familyn basa fita waje suyi gida hakan yasa dole ya ajiye yaran nashi a nan.

Ƴaƴan shi takwas biyu ne kacal suka yi aure yanzu haka shida suna nan basu yi aure ba, cikin wa'inda suka yi auren akwai Muhsina da Maryam, Muhsina ita ke aiki a bank Maryam kuma lecture ce a nan KASU dake kaduna.

Sai Adam wanda yake aiki da companyn NNPC yana da shekara talatin har da biyu sai Saleema dake cikakkiyar likita me shekaru talatin, sai Hafeeza me ashirin da takwas ita kuma tana aiki a ɗaya daga company na gidan ne sai Muhibba me shekaru ashirin da shida sai Kabeer me ashirin da biyar sai Kamal me ashirin da uku daga kan Muhibba zuwa ƙasa su karatu suke yi.

Saleema ta ƙaraso inda yake tace; "na gama zaka iya tasowa", babu musu ya miƙe ita kuma ta biyo bayan shi.

Ta wata ƙofa ƙarama suka biyo sai gasu a ƙaton falon gidan, inda yake cike da kayan mire rayuwa dinning area suka nufa wanda nan ɗin ma wani sabon kallo ne a wajen.

Da kanta tayi serving ɗin shi sannan ta koma gefe ta zauna tana kallon yadda yake cin abincin, cikin natsuwa sosai babu wata hayaniya ko tashin hankali.

Sai da ya gama sannan ya juyo ya kalle ta yace; wannan kallon fa ya kusa yayi yawa", tayi murmushi tana kauda kai gefe shima murmushin yayi yana miƙewa tsaye.

Da sauri ta miƙe tsaye ta matso kusa dashi cikin sauri ta riƙo hannun shi tace; "Abdul kayi kyau", ya sakar mata murmushi yace; "na gode sosai", daga haka ya zame hannun nashi ya fice.

Tana tsaye tana kallon shi har ya fice daga falon, ajiyar numfashi tayi tana me dafe kumatun nata da hannuwa biyu.

Ita tun ba yanzu ba Allah ya jarabce ta da tsananin son ƙanin nata wanda ta kan rasa ina zata saka kanta.

Shi kuwa Abdul yana fita suka haɗu da Muhibba tayi ihu tana yo kanshi, cikin sauri ya kauce ya balla mata harara yace; kefa matsala ta dake rashin hankali".

"au dan ma na nuna farin ciki da ganin ka", Kabeer dake kwasar dariya yace; "Allah na rasa ina ƙasaitar ta take tafiya idan ta ganka", Muhibba ta cilla mishi harara.

Juyowa tayi tana kallon Abdul ɗin wanda shi kuma yake ƙoƙarin ficewa daga gidan, "ina zaka je ne?".

Be juyo ba ya bata amsa da zan tafi part ɗin su Hajja ne", da sauri ta biyo shi tana faɗin; "muje na raka ka", ya dafe kai shi dan dai yana jin yunwa ne yazo gidan nan amma hayaniyar su ta dame shi sosai.

Suna tafe tana mishi surutu shi dai kawai kallon ta yake yi sai murmushi lokaci zuwa lokaci, haka har part ɗin Hajja.

Suna shiga Fadila dake zaune a saman kujera ta tashi da sauri tana ihun murna, ya girgiza kai yana me yin murmushi ƙarfin hali.

Kujera ya samu ya zauna yana faɗin; "bismillah", Muhibba ta zauna a gefe Fadila a ɗayan gefen, haka suka saka shi a tsakiya kafin su hau fira.

Firar da suke ma ba wata me hayaniya bace sai dariyar su kaɗa-kaɗan da zaka dinga ji lokaci zuwa lokaci.

A haka har Fadil ya fito, ɗan saurayi dashi wanda suke kusan sa'anni da Abdul ɗin, sai dai abinda zai baka mamaki yadda duk Abdul ɗin ya ɗarasu kyau kasancewar yanayin shi daban.

Fadil yace; "kaga Sarki ka taso mu wuce ka rabu da wa'innan", babu musu ya miƙe, yayin da Muhibba ta turo baki tana faɗin; "kai Yaya Fadil sai kazo ka wani janye shi, kai baka zauna anyi firar zumunci da kai ba shima sai ka wani hana ayi dashi".

Kafin ya basu amsa Abdul ɗin ya fito sanye da kayan ƙwallo kalar na jikin Fadil ɗin, yana zuwa suka fice.

Bayan sun fita Abdul yace; "nifa bana son na wannan Estate ɗin mu ɗan je na gamji mana", Fadil yace; "to shikenan ai Abban Nihal baya nan zamu iya tafiya", haka suka fice daga cikin gidan.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*HAYIN RIGASA, KADUNA*.


Nusram ta harari Nusreen tace; "wallahi kiyi sauri mu tafi dan na gaji gashi kuma ina buƙatar hutawa", Nusreen ta yamutsa fuska tace; "to a haƙura da zuwa Tudun Nufawan mana".

"sai kunje shi na san duk kece kike so ki janyo salalan tsiya to wallahi baki isa ba kin san gobe akwai bikin Wasila ƴar gidan Malam Hassan kuma ta riga tazo ta tambaya akan Nusram take so tayi mata kitso da kwalliya ko amma shine kike so ki janyo abinda zai hana ku zuwa gobe bata da lokaci idan kuma kika sake kuka fasa zuwa yau to gobe zaki je ke kaɗai kenan?".

Nusram ta girgiza kai tana faɗin; "Ummi zamu tafi yanzu Rim dan Allah kiyi ki ƙarasa", Ummi tace; "ku dai kuka sani", ta cigaba da ƙulla sigar ta.

Nusreen ta miƙe tsaye, tana sanye da atamfa kalar blue da ratsin ja da kuma ruwan toka sosai atamfar ta haska kalar fatar ta, fuskar nan ta ɗauki kwalliya sosai.

Hijab ta ɗauko kalar ash ta saka takalmi da jaka ƴar ƙarama swagger kalar ja ta saka sosai tayi kyau wanda itama Nusram ɗin shigar da tayi kenan sai dai ita fuskar ta babu wata kwalliya sosai.

Ummi ta irgo kuɗi ta miƙa musu tace; "gashi nan ku kai mata kuce zamu yi waya anjima, sannan ta ƙaro muku Curry da thyme harda citta duka domin ta waje na ta ƙare saura ku daɗe".

"insha Allah da wuri zamu dawo", faɗar Nusram kenan tana ƙoƙarin saka kuɗin cikin jakar ta.

Kamar koda yaushe Mama Jummai ta tsakar gida tana faman ɗora manyan tukwane domin girkin siyarwa, Ameera da Sahura suna taya ta.

Haka suka fice ba tare da sunyi mata magana ba wanda ina ganin dalilin Nusreen da bata so su kuma ɓatawa da ƴar uwar tane.

Koda suka isa bakin titi basu jima ba suka sami abin hawa inda suka hau zuwa Tudun Nufawa.

Har ƙofar gidan me Keke Napep ɗin ya kaisu, Nusram ta ciro kuɗin shi ta miƙa mishi, gidan babu laifi ya haɗu domin kuwa harda get a jiki.

A hankali suka tura suna masu jero sallama, daga can cikin gidan aka amsa sannan suka shiga, ɗakin dake gefen hannun hagu suka ga takalma wanda ya nuna musu Auntyn tasu tana cikin ɗakin.

Ɗaki ne wanda take sana'ar ta a ciki komai na kayan ta to a ciki yake haka ma idan masu siye sun zo nan take kaisu.

Suna shiga suka tarar da Ƴan mata uku da kuma wata ƴar matashiyar mace wacce ba za'a kira ta da tsohuwa ba, Matar tana ganin su ta sakin murmushi tace; "yauwa Allah ya kawo mini ku, kamar kun san aiki yayi mini yawa".

Nusreen ta yamutsa fuska tana cuno baki, Nusram kuwa zama tayi sannan tace; "meya faru Aunty?",

Wacce ta kira da Auntyn tace; "dama wa'innan da kike gani muke gyara dasu yau kwanan mu goma sha takwas kenan, to yau kinga aiki yayi mini yawa ga kaya zan je amsowa domin ɗazu an aka kira ni akan kaya sun iso ina so naje na zaɓo kada a riga ni ga kuma jakunkuna da zan haɗa guda hamsin da biyar wa'inda ƙanwata Kaltume zata wuce dasu Borno to aikin duk ya caɓe mini tunda kunzo sai ku taya ni".

Nusram tace; "babu komai Aunty, ga wannan ma inji Ummi tace a kawo miki wai zaku yi waya ga kuma wannan kuɗin kayan mu ne dubu talatin da biyar ga na Yaya Sulaiman shima dubu arba'in sai ki ajiye mishi, naso muje can ɗin da kanmu amma tunda kina da aiki zamu hakura kawai sai ki ce mishi ya sake haɗo mana wasu kayan zuwa gobe na rigunan kuma da turarruruka idan kin dawo sai ki bamu ko?".

Auntyn tace; "yauwa ƴa ta yanzu wanne zaki yi", Nusram tace; "bari na fara yiwa amaren dilka idan yaso Rim kuma sai ki bata sample ɗin jakar sai ta fara yi miki kafin na gama".

Auntyn ta gallawa Nusreen harara sannan tace; "ai banga alamar zata yi mini ba ganin yadda take yatsina fuska", Nusreen tayi dariya tana fadin; "haba dai Aunty zan yi miki mana sai dai kin cika saka aiki ne idan mutum yazo".

Aunty ta riƙe baki tana faɗin; "Nusreen ni ɗin lallai wuyan ki ya isa yanka", Nusreen ɗin tace; "wasa nake miki ina Adam fa?".

"yana gidan Halima sai gobe zai dawo", Nusram tace; "Aunty kije ki manta da wannan kawai", aikuwa", Auntyn ta faɗa kawai tana miƙewa

Please Login or Register in order to submit comment