Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Akan dinning suka same su, duka uku babu wanda ya iya cin abinci, fatan Sameer da Tameer shine Mummyn tasu ta amince da zaɓin nasu yayin da Abdus-samad kuma tunanin halin da ya baro Mahaifiyar tashi shine yasa.

Yana ganin su yayi saurin miƙewa ya ƙara inda take ya rungume ta, Brr Farida tayi dariya tace; "My Baby kenan?", shi ya ja mata kujera ta zauna.

Ganin yadda yaran nata suke cikin damuwa yasa ta fara jan su da fira har suka sake da ita, nan suka ci abincin su cikin annashuwa.

Bayan sun gama suka koma saman kujeru suka zauna, Abdul ya ɗora kanshi saman ƙafar ta yace; "First love na tambaye ki?".

Tace; "eh Baby na", ya yi murmushi sannan yace; "Waye Mustapha Abubakar Tuge", Brr Farida taji saukar sunan kamar saukar aradu.

Cikin sauri ta ture kan nashi daga jikin ta sannan tace; "a ina kaji wannan sunan kuma waye yace ka tambaye ni?".

"shi da kanshi ne ya faɗa mini, kuma muna kama sosai dashi, kin san na sanshi tun a london domin kuwa yana yawan zuwa ɗaya daga cikin attajiran dake Africa".

Brr Farida tace; "to wannan shine amsar tambayar ka, shi ɗin me kuɗi ne wanda ake ji dashi a Africa, sai kuma me kake son sani?".

Abdus-samad ya girgiza kai domin yadda Brr Faridar tayi magana ya nuna a hasale take.

"yauwa First love ya kira ni da Murad", ya faɗa yana me kallon mahaifiyar tashi, Brr Farida ta miƙe tsaye cikin hasala tace; "na faɗa maka Murad baya nufin komai a wajen ka, kada kuma ka sake tara ta da wannan maganar idan ba haka ba ranka zai ɓace", tana gama faɗar haka ta bar falon.

Abdus-samad ya kalli Dr Abubakar, cikin sauri kafin Abdus-samad ɗin yace wani abu, ya kalli Sameer yace; "ka shirya gobe zamu je Hayin rigasa daga nan zamu wuce Abuja", yana gama faɗar haka ya wuce ya bar falon.

Abdus-samad ya kalli Sameer, Sameer ya ɗaga mishi kafaɗa alamun i don't care, shima Abdul ɗin ya taɓe baki kafin ya miƙe ya fice.

Kida ya shiga part ɗin shi bayi kawai ya wuce yayi wanka, a gaban mirror ya tsaya yana ƙara kallon kanshi, so yake ya gano meye suke da bambamci da wannan mutumin na ɗazu wato Alhaji Mustapha.

Komai nasu kala ɗaya ne gaba ɗaya kamar tasu har ta ɓace, bambamcin su kaɗan ne wato bakin shi ƙarami ne ba kamar na wancan ba, banda wannan kuwa babu abinda suke da bambamci da juna sai tsufa kawai.

Ya lumshe idanu, ganin fuskar ta yasa yayi saurin buɗe idanu, babu abinda yake tunawa sai lokacin da gashin ta ya bayyana.

Cikin sauri ya ɗauko kayan daya cire ɗazu ya hau binciken ribbom ɗin nata, babu jimawa ya ganshi a aljihun shi, ya riƙe a hannun shi yana kallo.

Tuno yadda fuskar ta ke nuna tsantsar tsoro a duk lokacin da suka haɗu yasa yayi murmushi a hankali ya furta; "Nusraaaaaam!".

Yasin yana Abdul yana ruwa 🙄🙄🙄.

******** ***********
*MAƘARFI ROAD, KADUNA (GIDAN AMARYA)*.

Nusram ta miƙe cikin yanayi na rashin lafiya ta nufi bakin ƙofa ta fice daga ɗakin, bata taɓa tunanin Alhajin zai kai zuwa yanzu be shigo ba.

Ta tsaya tana kallon falon nata, bata san lokacin data ja tsaki ba inama ace wannan kuɗin da maman nata da Auntyn ta suka kashe gidan wanda take so ne.

Kanta da yake sara mata ta dafe sannan ta nufi wata ƙofa data gani, ganin ta a inda take zato wato Kitchen yasa taji daɗi sosai.

Buɗe-buɗe ta fara tana neman abinda zata ci, babu komai wanda zata iya ci dan haka dole ta fito, hango fridge yasa ta nufi can.

Allah ya bata sa'a domin ta sami ruwa pure water a ciki me sanyi dan haka ta ɗauko ɗaya daga ciki ta wuce ɗakin nata.

Bincike ta fara yi har Allah yasa taga kayan dubulan ɗin ta nan kuwa ta ɗiba ta hau ci hannu baka hannu ƙwarya, sai da ta ƙoshi sannan ta kora da ruwa.

Ta kai kallon ta kan agogon ɗakin ƙarfe sha biyu da rabi duk inda ango yake ya kamata ace zuwa yanzu yana cikin gidan shi.

Mema zai saka ta damu bayan ba wani son shi take yi ba, ita kanta tayi mamakin rashin tsoron data nuna, Allah sarki Nusreen ko yaya take yanzu oho, ko ta dena kuka zuwa yanzu bata sani ba.

Nan taji hawaye yana zubo mata, Allah yasa ma Shureim yana tare da ita ta san cewa yanzu zai rarrashe ta, ita fa bata da kowa, ta share hawayen daya zubo mata sannan ta nufi bayi.

Alwala ta ɗoro domin tazo tayi nafila, ta ɗauki hijab ta saka, Sallama taji a falo kafin tayi wani yunƙuri taji an nufo ɗakin ta wanda yayi dai-dai da fitowar mutum daga cikin wardrobe ɗin ta.

Kallon shi take bakin ta ɗauke da addu'a don a tunanin ta Aljani ne, ya matso kusa da ita yace; "yauwa masoyiyata kiyi sauri mu tafi kafin wancan ƙaton ragon ya shigo".

Alhaji Baballe da yayi niyar shigowa jin abinda ke gudana a cikin ɗakin yasa ya turo ƙofar cikin fushi, ya bisu da kallo yadda fuskar Nusram ya nuna tsoro da kuma hijab ɗin dake sanye a jikin ta ya gasgata abinda yaji.

Ya nuna ta da hannu "wato sai da kike nuna ban isa ba haka Uban daya haife ki ma be isa ba wallahi, dan haka sai na sauya miki kamanni ta yadda gobe wani namiji ba zai ga wannan kyawun naki ba har ya janyo hankalin shi gare ki", yana gama faɗar haka ya kulle ƙofar inda ya tafi neman abin duka.

Ganin haka yasa Bangis ɗaga window ya dira yayinda ya bar Nusram kamar statue, bata dawo hayyacin ta ba sai da taji ana buɗe ƙofar.

Alhaji Baballe ta gani hannun shi riƙe da zabgegiyar bulala irin ta wayar wuta, nan jikin Nusram ya fara rawa; "ka dakata kaji wallahi ba abinda kake tunani ban.......", bata samu damar ƙarasawa ba sabida saukar bulalar da taji.

Sosai ta daku a hannun Alhaji Baballe wanda dama kamar ƴa take a wajen shi, dan dai kawai aure ya ratsa tsakanin su ne, dama fatar Nusram fashewa take idan taji duka dan haka dan danan ya fasa mata jiki.

Tana bashi haƙuri tana zagaye ɗakin haka yake binta yana duka, har ta faɗi a ƙasa amma haka yasa ƙafa ya dinga takata yana huci.

Sai da ya gaji dan kanshi ya ƙyale ta, a lokacin gaba ɗaya kukan ma ya dena fita sai dai hawaye kawai da take yi na tsabar azabar da ta sha.

Ta dafe cikin ta wanda ke mata wani irin tsananin ciwo, tana ji tana kallo ya kira police akan suzo gidan shi, amma bata da damar yin magana.

Ya tashi ya shiga bayi ya taro ruwa ya fita be jima ba ya dawo hannun shi riƙe da bokitin ya nufi inda take ya shara mata ruwan.

Nusram ta runtse idanu tana jujjuya kai cikin wahala da tsananin raɗaɗin da take ji a inda ya zuba mata ruwan.

Ya kamo wuyan ta ya shaƙe yana faɗin; "ina ɗan iskan saurayin naki yake?", Nusram babu baki wuya kam ta sha ta, idanun ta yayi ja babu abinda take jira banda mutuwa tazo ta tafi da ita.

Ƙarar isowar motar ƴan sandan ya ƙwace ta daga hannun Alhaji Baballe, hijab ɗin ta ya kama ya jata har zuwa waje inda ƴan sandan suke tsaye sannan ya cilla musu ita yace; "ku tafi da ita ku rufe mini ƴar iska kada ku sake ku bada belin ɗinta".

Ya juya cikin gida yana huci, Nusram ta daɗe kwance a wajen kafin ta iya miƙewa tsaye jiri na iyabar ta, ta kalli ƴan sandan dake tsaye a wajen su kansu sun tausaya mata duk da basu san laifin da tayi mishi ba.

Ɗaya daga ciki ya ɗago ankwa din hannun shi, Nusram cikin baƙin ciki ta miƙa hannun ta kamar wata ɓarauniya ko wacce tayi wani babban laifi.

Haka suka tasa ƙeyar ta cikin motar, Nusram ta ɗaga hannu ta kalli ankwar hannunta ta fashe da kuka tana me tausayin rayuwar ta.

Ta saka hannu ta janyo hijab ɗin ya rufe gefen fuskar ta a haka har suka isa ofishin ƴan sandan, haka suka shiga ciki, sai sa suka tambayi sunan ta ta faɗa musu suka ɗan yi rubuce-rubuce sannan suka ce ta cire ƴan kunnayen ta da zobunan ta haka ta cire duka dama babu komai a hannun ta dan haka suka iza ƙeyar ta zuwa cikin cell bayan sun saka ta cire hijab ɗin ta.

Koda suka maida suka rufe a wajen Nusram ta durkushe tana kuka me cin rai, wai yau itace a rufe a cell abinda bata taɓa tunani ba kenan, Aunty tace wata rana zata yi farik ciki ko sai yaushe wannan ranar zata zo??.



#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*



♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖37-38📖📖

Ranar duk iya satar barci sai da ya ƙyale Nusram, ga sauro ya sanyi ga raɗaɗin ciwon ta ga kuma zazzaɓin dake jikin ta ga damuwa da fargaba.

Kuka kam ta sha shi har ta bawa uku lada, tana yi tana istighfari; "Astaghfullah Allah idan laifi nayi maka kake jarabtata da wannan masifun domin na tuba ya Ubangiji ina me ƙanƙan da kai zuwa gare ka Allah ka amshi tuba na", abinda ta kwana ambata kenan.

Koda safiya tayi haka ta tasa fararau-fararau ɗin koko da ƙosai ƙwara uku a gaba tana kallo tana hawaye, duk yadda suke a gidan su basu taɓa irin wannan karin ba abinda ke ƙara bata mamaki shine yadda yau aka kawo ta Cell gashi ma har ta kwana.

Da safen ragowar wa'inda suka kwana a gidan biki ƴan Dabai ne kawai dan jiya tunda aka kai amare kowa ya wuce gidan shi.

Su ke ƙoƙarin haɗa abin kari babu wanda ya kula Mama Jummai wacce ke faman shewa da murna to babu wanda ya san ma me take yiwa murnar.

Tun da asuba Bangis ya kira Habiba ya shaida mata aiki yayi kyau, wannan shine silar murnar tata sai dai ba'a sami dama kan gidan Nusreen ba saboda lokaci ya ƙure.

Mama Jummai tace; "babu komai ai tunda ka ƙwato mana me maiƙon waccen zan ji da ita daga baya kada hakan ya ɗaga maka hankali".

To wannan shine ya saka su a cikin murna kuma suna jiran sakamako me kyau.

Wajen goma suna zaune sai ga Baba ya fita da sauri, Mama Jummai ta kuma aashe baki tana murna tana fatan ace aikin su ne yaci.

Baba kuwa ganin Alhaji Baballe harda ɗan duƙawa wajen gaishe dashi, Alhaji Baballe ya amsa a fuzge sannan ya miƙowa Baba takarda yace; "ka takardar matsiyacoyar ƴar ka nan na sake ta saki uku, sannan na baka nan da kwana uku ka dawo mini da duk wani kuɗi daka san na baka shi".

Baba ya ƙwalalo idanu waje, cikin rawar murya yace; "haba Alhaji me yayi zafi haka, meta aikata maka wanda ta cancanci wannan sakamakon?".

Alhaji Baballe yace; "oho sai kaje ka tambaye ta ni dai na gama magana ka dawo mini da kuɗi na kawai", Baba yace; "dan Allah Alhaji kayi haƙuri, kada muyi haka da kai na san cewa Nusram yarinya ce me biyayya ga haƙuri kuma".

Alhaji Baballe yace; "ne haƙuri fa kace, yarinyar dana kama da saurayin ta zasu gudu ranar da aka kawo ta gida na, har cikin gida na ƙato ya shigo zai tafi da ita".

Baba ya hau salati yana tafa hannu, cikin jimami yace; "Alhaji ka dai sake bincikawa amma ba halin ta bane, na san Nusram ciki da bai".

"oho wannan kuma kai ta shafa bani ba kaji na faɗa maka ka dawo mini da kuɗaɗe na kawai ni ba zan iya zama da ƴar iska ba".

Baba yace; "bafa za'a yi haka ba akwai ƙanwarta idan kana so yanzu ma sai a ɗaura muku aure", Alhaji Baballe ya girgiza kai.

Baba ya hau roƙon shi da Allah dan ya amince, sun jima a haka sannan Alhaji Baballe yace; "na yarda shikenan zanje na dawo zuwa ɗaya sai a ɗaura, kaima ka shiga ka faɗawa naka ƴan uwan", Baba yayi ajiyar zuciya ganin Alhaji Baballe ya amince yace; "insha Allahu yadda kake so haka za'a yi, yanzu ina ita Nusram ɗin take?".

Ba tare da damuwa ba yace; "tana ofishin ƴan sanda", yana faɗar haka ya shige motar shi ya tafi, Baba kuma ya shiga gida.

Ɗakin Mama Jummai ya shiga ya zuba tagumi, cikin Kissa tazo tace; "meya faru ne Baban Atika".

Ya ɗago ya kalle ta sannan ya bata labarin komai da yadda suka yi da Alhaji, cikin damuwa yace; "ni yanzu ban san ko zasu amince ba gashi nayi mishi alƙawarin wata".

Mama Jummai cikin ranta kamar tayi me dan murna amma a fili sai tace; "Ashsha gaskiya Nusram bata kyauta ba sai dai dama shekaranjiya Atika tace mini wani ɗan iska ya aike ta wajen Nusram ɗin amma na kwaɓe ta dan kasan surutun yara".

Baba yace; "kira mini Atikar", Mama Jummai kuwa rai fes ta ƙwalawa Atika kiea, dama tana laɓe tana ji dan haka babu ɓata lokaci ta amsa tana shigowa ciki.

"Atika ki taimaka ki rufawa Mahaifinki asiri ki yarda ki auri Alhaji Baballe dan Allah ki mini wannan alfarmar".

Atika ta ɗago tace; "Baba magana kake fa akan mijin ƴar uwata Nusram ai hakan ba zai yiwu ba na aureshi bayan yana matsayin mijiɓ ƴar uwata kuma suna tare".

Baba ya ƙara saukar da kai ƙasa yace; "Atika ki tsaya ki saurare ni, yanzu haka takardar Nusram tana hannu na ya sake ta saki uku, kuma yace sai na dawo masa da kuɗin shi, Atika kema kin san hakan bame yiwuwa bane dan ko gidan nan na ɗaga na siyar ba zai kai kuɗin daya bani ba Dan Allah ki rufa mini asiri kinji".

Atika ta ɗan yi shiru sannan tace; "shikenan Baba insha Allahu zan share maka hawayenka, zan kuma yi maka biyayya Allah yasa hakan shiya fi".

Baba har ƴar ƙwalla sai da yayi jin abinda ƴar tashi ta faɗa, faɗi yake; "Atika Allah yayi miki albarka", sannan ya miƙe ya fice.

Yana fita Atika tayi tsalle ta faɗa kan mahaifiyar ta, suka hau murna suna jin daɗi, Sahura ma na zuwa suka bata labarin abinda ya faru nan itama ta hau taya su murna sannan fa suka fara shirye-shiryen yadda bikin zai kasance.

Baba dake tsaye ƙofar ɗakin Ummi yace; "Maimuna! Maimuna!! Fito yau da ƴa ɗaya na haifa da sai dai na haɗiyi zuciya na mutu to Allah yasa ina da wata".

Ummi ta ɗan yi jimm sannan tace; "Baban Nusreen meya faru ne?", cikin ɗaga murya yace; "meye ma be faru ba Maimuna", ya zaro takardar ya miƙa mata.

Ummi ta juya takardar sannan tace; "ai baka ce komai ba ka san ba iya karantawa zan yi ba".

Mama Jummai dake bakin ƙofa ta tuntsire da dariya tace; "matsalar ka kasance jahili kenan", babu wanda yace mata komai.

"ƴar ki na Police Station mijin ta ya kamata *A DAREN FARKO* zata bi saurayi su gudu shine ya kai ta caji ofis yanzu haka acan ta kwana, wannan kuma takardar sakinta ne ya sake ta saki uku, na nemi alfarmar ɗaura mishi aure da ƴar uwar ta kuma ya amince dan haka yau ƙarfe ɗaya za'a ɗaura auren, yanzu zan je kasuwa na ƙara siyo abubuwan da babu sai a cigaba da biki kawai kayan ɗaki da komai da komai kuma za'a barwa ƴar uwar ta ne".

Yana gama faɗin haka ya juya yana faɗin; "bari Hansai( ƴar uwar shi daga Dabai) tazo muke kasuwa tare sai ta taho da abubuwan da babu", Ummi kuwa tana tsaye ne kawai ta rasa meke mata daɗi.

Baba Sailuba ta fashe da kuka aka shiga bata haƙuri tace; "ku dena bani haƙuri yau naga meke faruwa gidan Abdullahi, lallai ba hakanan ba Maimuna ki tattara kayanki kawai mu tafi gida, dan ni yanzu zan bar garin nan".

Ummi ta girgiza kai sannan tace; " Baba meye amfanin tafiyata a yanzu bayan nasan cewa babu me amso mini ƴata wajen hukuma idan har na tafi to haƙuri na na shekaru ashirin da ɗoriya ya tashi a banza kenan dan haka Baaba kiyi haƙuri zan zauna kawai a nan".

Baaba Sailuba tace; "shikenan na fahimci wane irin zama ake a gidan Abdullahi, dan haka ku haɗo kayanmu, mu tafi gida kawai", ta ƙarasa tana goge hawayen daya zubo mata.

Haka yawancin ƴan Dabai suka tafi sai ɗai-ɗai ku wa'inda ke goyon bayan Abdullahin, Ummi kam banda zubar da hawaye babu abinda take yi.

tun daga waje suka fara jiyo faɗan Aunty, tana shigowa taja wata doguwar ajiyar zuciya sannan ta kalli Ummi ta balla mata harara tace; "Wallahi idan kika zauna sai baƙin cikin ɗa namiji ya kashe ki", muryarta na rawa tace; "yau wai Nusram ce tayi kwanan Cell!?", ta fashe da kuka.

Ummi ta taso zata riƙe ta, Aunty ta dakatar da ita ta ɗora da faɗin; "kada ki taɓa ni Maimuna, haƙurin ki a da ke yake cutarwa amma yanzu ya fara taɓa ƴaƴan ki, abin ban haushi kamar mara gata mace da kwanan Cell, dan yana da kuɗi shikenan sai kuma ya dinga taka duk wanda yaso haka ake rayuwa wannan ba adalci bane, wallahi ko ki tashi ki ƙwatarwa kanki da ƴaƴan ki ƴanci ko kuma daga yau kada ki kuma nema na".

Ummi ta koma baya ta zauna sannan tace; "shikenan Kaltume kije kawai inaji gawata kuke so a ɗauka a gidan nan, na ɗauka ke kin fahimce ni ashe ba haka bane, Kaltume banda yanda zanyi".

Aunty tace; "ke kuwa kike da yadda zaki yi amma idan har kika zauna kika zuba idanu to wallahi zaki kamu da ciwon zuciya kuma ba matsalar su bane".

Tana gama faɗar haka tayi waje a zuciye, sauran ƴan ɗakin suka riƙo ta, ta kalli ɗaya daga ciki tace; "sakeni Hadiza dole ne mu kwaso kayan mu domin kuwa babu ƙwandalar ubanta a ciki".

Ummi tayi saurin miƙewa tace; "kiyi haƙuri Kaltume ki bar wannan maganar", ta juyo cikin fushi tace; "ba zan bari ba", ganin abin kamar zai zama faɗa yasa Hadiza da Karima suka riƙe Aunty suka yi waje da ita, tana kuka Ummi na kuka haka suka rabu kowa rai babu daɗi.

Ummi ta share hawayen fuskarta tace; "Allah kana ji kuma kana gani idan har dan inyi biyyaya ga umarnin daka bayar na cewa mata ta yiwa miji biyyaya, Allah ka duba halin da nake ciki ka ceto mini yarinyata sannan ka shirya wa'inda suka mata wannan sharrin Allah ka bani ikon ganin ƙarshen su", Hadiza dake tsaye tace; "ameen dai".

Aunty kuwa sai da ta tsaya a zaure ta goge hawayenta sannan ta ɗauko waya ta kira Sulaiman ta faɗa mishi halin da ake ciki.

Cikin tashin hankali yace; "yanzu Mama zan je duk wani police station na nan kusa domin sanin wanne aka kaita", Aunty tace; "yauwa maza kaje dan Allah yanzu zan kira Baban ku shima domin ganin ta yadda zai taimaka mana".

Yaya Sulaiman na ajiye wayar yayi saurin fita daga shagon cikin sauri, mota ya shiga hankali tashe yana kuma mamakin irin wannan abu dake faruwa ga wannan baiwar Allah".

Babu inda be zaga ba amma abin haushi duk inda yaje cewa ake yi ba'a kawota nan ba abinda be sani ba shine Alhaji Baballe ya bada umarni akan kada su sake su nuna an kawo ta nan.

Har zuwa yamma Yaya Sulaiman be sami inda aka kai Nusram ba, duk wani Police Station da ya sani na kusa dana nesa yaje amma be samu ba, har ya fara fita yankin nasu wato Kaduna North, har zuwa dare babu labari.

Aunty kuwa sai yamma ta koma gidan, hankalin ta ba wani a kwance yake ba, koda ta isa magana ta yiwa su Hansai akan su fito a tafi buɗar kai amma abin mamaki suna fitowa Baba ya maida su.

"waye zai kai Atika ɗakin mijin ta idan har kuka kwashi jiki kuka tafi kuma", Hadiza tace; "Haba Yaya amma a al'ada yau ake buɗar kai", Baba ya karkata kai yace; "to ni nace a fasa ba shikenan ba, Atika ta fito ku wuce kawai".

Aunty cikin zafin zuciya ganin duk sun tsaya tayi hanyar waje, wayar Halima ta kira da ta Safeena sai Sa'adatu da bata yi aure ba, babu jimawa suka iso nan tace; "su shiga gidan su kwaso mata kaya zasu wuce buɗar kai".

Sun so tambayar ta abinda ya faru amma ganin yadda take ranta a ɓace yasa suka ja bakin su, suka yi shiru koda suka fito da kayan nan suka haɗu da maƙwabta guda biyu da kuma Hadiza wacce ta kasance ƙanwar Ummi da kuma Karima suka wuce buɗar kan Nusreen.

Sun shiga mota sannan Sulaiman ya kira Aunty, "Mama babu inda banje ba amma wallahi ban sami inda suka kaita ba", Aunty ta ɗanyi jim sannan tace; "na kira baban ku yace zai kira dpon yankin amma shiru har yanzu ka kira shi kaji ya suka yi", Sulaiman yace; "to".

Koda suka isa Unguwar Rimi gidan Amarya Nusreen, dole Aunty ta saki fuskarta gudun zargi, sun tarar da gidan akwai sauran baƙi, nan suka yi duk abinda ya kamata.

Sun zo tafiya Nusreen ta riƙo Aunty hakan yasa su Halima suka fice, Aunty ta dubi Nusreen tace; "ya akayi ne Amarya", Nusreen ta saukae da kai ƙasa tana wasa da yatsunta.

Aunty tace;

Please Login or Register in order to submit comment