Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kana tace; "in tafi in barku ne ko kuwa zata zo mu wuce?".

Babu wanda yayi magana a cikin su, sai lokacin taji shesheƙar kukan Nusram ɗin, da sauri ta juyo ta kalle su.

Abdul kuwa kamar ma ba wani abun yake mata ba, ta kalli Dr Saleemar cikin tsananin azaba tace; "Aunty Saleema hannu na".

Jin hakan yasa da sauri Dr Saleemar ta nufo inda suke, ganin yadda ya murɗe mata hannu yasa tayi saurin ƙarasawa inda suke.

Hannun shi ta riƙo tace; "Abdul meye haka, dan Allah ka sake ta", kamar ba zai sake ta ba can kuma ya hankaɗe ta kana ya juya ya fice.

Nusram ta faɗa saman carpet ɗin wajen kanta ya bugi kujera, taja numfashi sannan ta saki kuka.



#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*



♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖57-58📖📖

Cikin sauri Dr Saleema ta ƙarasa kusa da ita, ta janyo zuwa jikin ta sannan ta saka hannu tana jijjiga ta alamar rarrashi.

Sun jima a haka kafin Nusram ta tsagaita da kukan nata sannan Dr Saleema ta taimaka mata ta miƙe, da kanta ta kwaso mata jakarta da kuma wayar ta sannan suka fice daga office ɗin hannun su sarƙe dana juna.

Ko da suka fara tafiya babu wanda yayi magana a tsakanin su har suka isa gida, suna yin parking motar Fadil ma na shigowa.

Dr Saleema ta kalle shi tayi murmushi, shima da murmushi a fuskar shi ya gaishe ta, ta amsa cikin mutunci.

Ya maida kallon shi kan Nusram, Nusram kuwa kanta na ƙasa tana shafa hannunta wanda yasha murɗa.

"ina wuni?", ya faɗa, ba tare da ta ɗago ba tace; "lafiya lau", Fadila kam data kasa haƙuri ganin ƴar kyakkyawar baƙuwa a Estate ɗin su yasa tace; "Aunty Saleema ina kika samo wannan kyakkyawar".

Dr Saleema tayi murmushi tace; "ƙawata ce dake karatu a nan KASU", Fadila ta matso kusa da Nusram ta riƙo hannun ta.

"zaki zama ƙawata?", tambayar da Fadila tayi kenan, Nusram ta ɗago idanun ta kana ta zuba shi akan Fadila lumshe idanun tayi sannan tayi murmushi tana jinjina kai.

Cikin jin daɗi Fadila tayi dariya tace; "Allah na gode maka na samu ƙawa kyakkyawa, ni sunana Fadila, mu ƴan biyu ne kinga ɗayan nan", ta faɗa tana nunan Fadil wanda ke tsaye yana kallon su.

Shi sai yanzu yake ƙare mata kallo, lallai kyakkyawace yarinyar kuma ɗan uwan nashi ya sami mata me kyau, sai dai yadda auren nasu yazo ne abin babu daɗi.

"yauwa kefa ya sunan ki?", Fadila ta kuma tambayar Nusram, Nusram tace; "sunana Nusram", cikin matuƙar murna Fadila ta maimaita sunan.

"Wow! Nice name", zata kuma magana Dr Saleema taja hannun Nusram kana tace; "Fadila bari mu shiga ciki kinga yanzu muka dawo kuma duk mun gaji kuma kuje ku huta muma zamu huta anjima sai ku haɗu ko gobe".

Daga haka suka yi sallama sannan suka tafi, Fadila dai sai santin kyawun sabuwar ƙawar da tayi take.

Suna shiga suka sami Muhibba zaune da ita da Kamal, cikin sauri suka miƙe dukan su, Muhibba ta ƙaraso wajen Nusram da sauri.

Ta riƙo hannun ta kana tace; "Nusram ɗita kun dawo, tun ɗazu nake zaman jiran ki", Nusram tayi murmushi, abin mamaki Kamal shima daya zuba mata idanu murmushin yayi.

"Muhibba pls bakiga duk ta gaji bane ki bari ta huta mana", faɗar Dr Saleema kenan, Muhibba ta cuno baki tace; "Aunty to ki bari muje da ita nawa ɗakin sai ta huta ko?".

Dr Saleema ta galla mata harara sannan taja hannun Nusram ɗin suka shige ciki, bayan sun zauna ta dube ta tace; "ki shiga kiyi wanka", bata musa ba ta miƙe ta fara kwaɓe kayan jikin ta.

Dr Saleema ta miƙe ta fice wayarta a hannun ta, tana ƙoƙarin kiran Abdus-samad ɗin, be ɗaga ba har ta gama ringing ɗinta, dole ta haƙura.

Nusram kuwa tuna irin yadda gidan suke sonta sai taji farin ciki, kowa ƙoƙarin janta yake yi, "Allah sarki Nusreen kin faɗi gaskiya, ina jin matsalolina sun ƙare kenan, da alamu lokacin farin ciki na nima yazo".

Nace; "anya kuwa Nusram abinda kike tunani hakane?".

Tana fitowa ta hau shiryawa, jar doguwar riga ƴar kanti ta saka mara nauyi, ba tare da ta ɗaura ɗankwalin ba ta yafa shi saman gashin kanta.

Dr Saleema tayi sallama ta shigo itama jikin ta sanye da riga doguwa zubin buba amma ita dark blue, da alama wanka tayi ta shirya a wani ɗakin.

"yauwa yanzu ki fito muje mu ɗan tattaka ko?", Nusram tace; "to Aunty", sannan ta biyo ta, haka suka jera har waje.

Wannan karon babu kowa a falon sai Mummy, suka yi mata sannu da gida ta amsa kana suka fice, a ƙafa suke tafiya.

Tafiya sosai suka yi, sun wuce gidaje, Nusram sai kalle-kalle take yi, akwai jama'a sosai a Estate ɗin kuma wasu idan sun zo wucewa sukan gaishe su ko kuma su su gaishe dasu.

Abinda ta fahimta shine akwai girmama juna a tsakanin su, sannan kasancewar su ƴan boko yasa suke yin komai a waye babu gidadanci.

Sun je wajaje da dama kamar filin ƙwallo, Cinema, Clinic, Hall etc, sosai Nusram ta yaba da tsarin Estate ɗin.

Ana kiran sallar magrib suna shigowa gidan, sun samu falon babu kowa hakan ke nuni da sun tafi sallah kenan, don haka suma suka wuce suka yi alwala suka yi sallah.

Basu tashi a wajen ba har sai da aka kira isha suka yi kana suka miƙe suka fito, duk suna kan dinning dan haka suma suka yi joining nasu domin cin abinci.

Kamar dda safe Kamal da Kabeer idanun su na kan Nusram yayin da ita kuma duk ta jita a takure domin irin kallon da suke binta dashi.

Haka dai har suka gama sannan suka koma saman kujeru suka zauna, Dr Saleema tace; "wai ina daddyn ne?".

hafeeza tace; "wai ashe a Abuja ya sauka sai zuwa gobe zai sake biyo flight ya zo Kaduna", Dr Saleema ta jinjina kai alamar gamsuwa.

Ɓangaren Nusram kuwa Muhibba ta maƙale mata sai surutu take yi mata yayin da Kamal da Kabeer suka maida ita abin kallo.

Wani ta bata amsa wani kuma tayi murmushi kawai, Dr Saleema ta miƙe kana tace; "Nusram tashi muje ko?".

Muhibba tace; "haba Aunty dan Allah yanzu ba zaki bari muyi fira ba, idan ma kunje ɗakin fa aiki zaki yi yayin da ita kuma sai dai ta zauna tayi shiru ko kuma tayi barci dan Allah ki barmu muyi fira ko Nusram ɗita?".

Nusram ta ɗaga kai alamar eh, Dr Saleema zata kuma magana Mummy ta dakatar da ita; "ya isa haka ki tafi ki bar su mana", ba dan taso ba ta tafi ta barsu a falon.

Har ƙarfe sha ɗaya da rabi suna tare suna fira kuma alhamdulillahi firar tasu ta ɗauke mata damuwar da take ciki, a yadda ta lura Muhibban babu ruwan ta akwai fira sannan idan ta kalle ta ta kan tuna mata da tata ƴar uwar wato Nusreen.

Su Kabeer ma jefi jefi suka saka musu baki a firar tasu kan wani lokaci sai ga Nusram na kwasar dariya sosai.

Mummy ta kalle su tace; "firar ta isa haka, Muhibba raka Nusram taje ta kwanta, kuma duk ku tashi haka sai da safe kuma".

Muhibba ta riƙo hannun Nusram ɗin suka miƙe suka tafi, koda suka shiga sun samu Dr Saleema har tayi barci dan haka Muhibba tace; "kinga tayi barci kizo muje ki kwana a nawa ɗakin".

Nusram tayi saurin girgiza kai tace; "a'a ki bari mu haɗu gobe", Muhibba taja numfashi tace; "shikenan, amma kinyi alƙawari gobe zaki zauna tare dani?".

Nusram ta girgiza kai tace; "sai dai idan mun dawo tare da Aunty tukunnan", Muhibba tace; "shikenan Allah ya kaimu, gobe zaki shiga makaranta ne?", Nusram ta girgiza kai tace; "sai sati me zuwa asibiti dai zamu je tare da Aunty".

"shikenan, amma sati me zuwan ki tabbatar kin neme ni kinji", Nusram tayi murmushi tace; "to shikenan", maimakon su rabu sai da suka ƙara ɓata awa ɗaya kana suka yi sallama da juna Muhibban ta tafi.

Ranar Nusram da farin ciki ta kwana, tuni ta manta da abinda Abdus-samad yayi mata, lallai mutane rahama ne.


********* ***********

*UNGUWAR SARKI, KAƊUNA*

Abdus-samad na barin asibitin kai tsaye gida ya wuce, be samu Brr Farida a gida ba, dama kuma yayi tunanin hakan domin kuwa suma sun fara shirye-shiryen tafiya meeting.

Sumayya ta taso da gudu ta tarbo shi, "Yaya sannu da dawowa", ya kama kumatun ta yaja yace; "yauwa ƴar ƙanwata".

"Mummy ta tafi Court tace daga can zata wuce gidan Alƙali (Family House ɗin su)", jin abinda ta faɗa yasa yayi ajiyar zuciya sannan yace; "shikenan Allah ya dawo da ita lafiya, bari naje na huta", Sumayya ta amsa da to.

Yana shiga bedroom ɗin shi wayar shi nayin ƙara, Khausar ce dan haka ya ɗan yi jim kafin ya ɗaga.

"Hi, barka da yamma", abinda ta faɗa kenan bayan ya ɗaga, kamar wanda aka tilastawa yace; "ya kike?".

"Lafiya lau nake, sai dai har yanzu da ka ƙi yarda mu kuma haɗuwa shine abinda ke damuna".

Beyi magana ba saima kwaɓe kaya da ya fara yi, jin yayi shiru yasa ta kuma cewa; "dan Allah ka bani address ɗin ka idan yaso ni sai nazo".

"zan shiga wanka, na gode da gaisuwa ko?", ya kaudar da waccen maganar, ta ɗan yi jim alamun ba haka taso ba cikin sanyin murya tace; "shikenan sai anjima", be bata amsa ba ya katse wayar.

Yana ajiyewa kiran Dr Saleema ya shigo, kamar tana gaban shi ya haɗe rai, tunowa da abinda yarinyar tayi mishi a rayuwar shi ya tsani mace me tsiwa.

Da ganin tana da rauni yasa yake tausayin ta amma abinda tayi mishi yau sai ya saka yaji ya tsane ta sosai, wayar ya ajiye kana ya shige bayi.

koda ya fito shiryawa yayi kawai cikin kaya marasa nauyi sannan ya fice daga ɗakin, babban falo ya nufa inda ya sami Brr Farida zaune ga kaya a gabanta.

Ya ƙarasa inda take ya kwanta saman ƙafar ta, Brr Farida da suke lissafi da Tameer da Sameer ta ɗago ta kalle shi, murmushi tayi kafin suka cigaba da abinda suke yi.

Yana kwance yana jin su har suka gama sai da aka fara kiran sallah sannan ya miƙe, itama Brr Faridar ta miƙe hannun su sarƙe dana juna suka nufi sama.

A bayin ta yayi alwala sannan ya fice masallaci, inda ita kuma tayi tata alwalar ta kabbarta sallah.

Be dawo ba sai da akayi isha'i, yana shigowa Daddyn su shima ya shigo dan haka tare suka jero.

Suna yin sallama, Adnan ya taso da gudu yana; "Oyoyo Daddy", Dr Abubakar ya ɗaga ɗan nashi sama yana cillawa yana dariya.

Brr Farida ta ƙaraso inda suke, ɗan rungume juna suka yi kana tace; "barka da dawowa Likitana".

"sannu da ƙoƙari Lauyata", suka saki dariya a tare, Abdus-samad ya kauda kai yana murmushi, hannun shi Brr Farida ta riƙe.

Ya ɗago ya kalleta yana ƙwaɓe fuska, kafin yace wani abu taja hannun shi sun shige ciki, kan dinning duk suka ƙarasa.

"ku bamu minti goma sha biyar muna zuwa", ta faɗa sannan taja hannun Dr Abubakar suka hau sama.

Sun jima kan su sauko, a maimaikon coat dake jikin Dr Abubakar ɗin yanzu jallabiya ce dark blue alamu na nuna wanka yayi kenan.

Sun ci abinci sannan suka koma saman kujeru inda suka dasa fira, shi dai Abdus-samad da idanu kawai yake bin su.

Yana da tarin tambayoyi wanda ya san Brr Farida ba zata amsa mishi su ba, tabbas yana ji a jikin shi a rayuwar shi akwai wani al'amari me girma.

To menene wannan? Amsar da baya da ita kenan, kuma wacce keda ita ba zata taɓa yarda ta faɗa mishi ba, to akan wane dalili kenan?.

har suka tashi daga firar ya saƙa wancan ya warware wancan haka ya tafi ɓangaren shi cike da tarin tambayoyi a ranshi wanda be samu amsar su ba ko kaɗan.

Koda ya kwanta barci bezo mishi ba dan haka duniyar tunani ya faɗa wanda ba zai amfane shi da komai ba.

Brr Farida dake tsaye saman kanshi taja numfashi, tun ɗazu ta shigo amma be sani ba kuma idanun shi biyu.

"anya kuwa nayiwa yaron nan adalci kuwa?, to me zan fada mishi?

Taɓa shin da tayi shine ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya faɗa, "First Love har kin shigo?".

Ta riƙe hannun shi tace; "Baby bana so kana damun kanka, ka kwantar da hankalin ka ka dena tunanin akwai abinda nake ɓoye maka, abinda nake son ka dashi shine ka cigaba da addu'a kawai".

Abdus-samad ya ɗaga kai, ta shafa fuskar shi tace; "yauwa My Boy", addu'a tayi mishi sosai kafin ta fice daga ɗakin.

Abdus-samad yabi bayan ta da kallo yana mamakin yadda take nuna mishi babu komai bayan alamu sun nuna akwai abinda take ɓoye mishin.

Haka ya cigaba da tunani har barci ya kwashe shi be sani ba.

yau saura kwana biyu su tafi Rigasa meeting, duk wani abu da suka san zasu samar dashi ta ɓangaren su to sunyi kamar kayan da zasu saka, abinda za'a tafi dashi da sauran su.

Brr Farida da kanta ta shiga gyara yaran nata, sai da ta tabbatar da komai ya tafi dai-dai sannan hankalin ta ya kwanta, washe gari kawai hanya zasu ɗauka domin ana gobe kowa ke zuwa kuma ba'a dawowa sai washe gari kwana biyu kenan da ɗan gari da wanda ba ɗan gari ba duk sai sun hallara.

Taro ne wanda yake da girma sosai sau ɗaya suke yi a shekara dan haka kowa yakan bar duk abinda yake yi domin ya halarta.

Yau dai Abdus-samad yake ƙoƙarin amsa gayyatar Khausar a karo na farko, dan haka koda ya taso wajen aiki part ɗin shi ya wuce wanka yayi kafin ya shirya domin tafiya.

Farin yadi ya saka me shara-shara wanda babu hayaniya tare dashi domin kuwa aikin da akayi mishi kaɗan ne, kanshi sanye da hula zanna bukar sai maiƙo take yi.

Ya feshe jikin shi da turare sannan ya kwashi wayar shi da makulli ya fice.

Tunda ya doso falon ƙamshi ke tashi, duka suka bishi da kallo, Sumayya tace; "wow! Yaya ka ganka kuwa gaskiya kayi kyau".

Tameer yace; "wannan wanka haka sai ina?", Sameer yace; "kai daga ganin wannan wankan ai sai wajen ƙanwar mu ko?", shi dai be ce komai ba sai murmushi da yake yi.

Jin abinda Sameer yace yasa ya kalli Brr Farida, itama shi take kallo tana so ta gano gaskiyar abinda Sameer yace hakanne, hasaso me take ƙoƙarin yi yasa shi saurin kauda nashi idon kafin yace; "First Love bari naje wajen wani abokina na dawo".

Kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa, cikin sanyin murya tace; "a dawo lafiya", ya amsa da ameen sannan ya juya ya fice.

Brr Farida ta bishi da kallo kana tayi ajiyar zuciya, idan kuma abinda Sameer ya faɗa gaskiya ne fa?, tuna hakan yasa gaban ta faɗuwa.

Zata yarda da komai amma ba zata lamunci wai Babyn ta yaje taɗi wajen wata ba, ita da kanta zata nemo mishi mata me kyau da asali da dukiya ba wai ƴar matsiyata ba.

Cikin sauri ta janyo wayar ta, wata number ta nemo wacce aka yi saving da Jameel, wajen message ta shiga.

*Ga Abdus-samad nan zai fito yanzu ku tabbatar kun bishi kunga inda yaje, ku kira ni ku faɗa mini*.

Wannan shine abinda saƙon nata ya ƙunsa, tana turawa ta ajiye wayar cikin damuwa, yaran ta kuwa sanin inda damuwar ta take yasa suka tashi suka bata waje.

Duk suna mamakin yadda ƙarara bata so a jinginawa Abdus-samad ɗin budurwa, ko meye dalilin ta oho!.

Abdus-samad kuwa kai tsaye ya yiwa Unguwar su Khausar kutse, ya sami securities a tsaye a bakin wajen, be wani sha wahala ba domin kuwa Khausar ɗin ta sanar dasu zuwan nashi.

Ɗaya daga cikin masu tsaron gidan shine yayi mishi jagora har cikin falon baƙin, Abdus-samad yabi falon da kallo sosai tsarin falon ya birge shi.

Gida ne wanda ya amsa sunan shi ya ƙayatu sannan kana gani ka san cewa mamallakin gidan me kuɗin gaske ne bana wasa ba.

Wata ƴar matashiyar budurwa ta tura ƙofar ta shiga, tana zaune saman kujerar kwalliya tana fuskantar madubi, budurwar ta ɗan taɓe baki.

Tun da aka gama kwalliyar take zaman kallon kwalliyar wacce aka kashe maƙudan kuɗi domin yin ta, gaba ɗaya jiya zuwa yau ta hanasu sukuni da zuwan baƙon nata.

"Aunty baƙon ki ya iso yana falon ƙasa Hassan yace a sanar dake", jin abinda aka faɗa yasa tayi wuf ta miƙe, turare ta ɗauka ta kuma fesawa a jikin ta a karo na babu adadi ta kuma kai kallon ta jikin madubin.

Ta kalli matashiyar nan tace; "dan Allah nayi kyau kuwa Siddiƙa kina ganin zan iya birge shi".

Siddiƙa tace; "wallahi kin yi kyau sosai kuma koshi dutse ne sai yaji kin birge shi", jin abinda Siddiƙar ta faɗa yasa tayi ihu ta runguma Siddiƙar.

Sai kuma ta sake ta kafin ta ƙara gyara kanta sannan ta fice, cikin yauƙi da yanga ta nufi falon baƙin.

Hajiya Salma dake hangota ta taɓe baki tana jan dogon tsaki, yaushe zata yarda shirin ta ya ruguje, tuno abinda suka shirya yasa ta saki dariya.

Cikin sauri ta nufi kitchen ɗin kulolin dake saman cabinet ɗin ta buɗe lafiyayyen girki ne wanda Khausar ɗin ta saka akayi domin tarba Abdus-samad.

Sai da ta leƙa ta tabbatar babu wanda ya taho sannan ta ciro wani ƙullin magani ta buɗe ta zuba a ciki, cikin sauri ta rufe ta fice daga kitchen ɗin.

Khausar ta shiga da sallama a bakin ta, Abdus-samad ya amsa mata, ta ƙaraso da sauri kamar zata shige jikin shi.

ya ɗan janye daga jikin ta, "finally yau gashi kazo gidan mu", yayi murmushi kawai.

Jameel ya kira Brr Fairda ya faɗa mata cewa Abdus-samad gidan Alhaji Mustapha Tuge ya shiga, sosai hankalin ta ya tashi jin abinda aka faɗa.

Meye alaƙar shi da Alhaji Mustapha ne da har yaje gidan, lallai dole ta ɗauki mataki idan ba haka ba asirinta yana daf da tonowa.

"oh! mustapha na tsane ka a rayuwata", abinda ta faɗa kenan.

Khausar ta ƙwalawa Siddiƙa kira, cikin sauri tazo, "muje mu kawowa baƙona abin motsa baki", hakan ta faɗa sannan suka fice daga ɗakin.

Babu jimawa suka dawo ɗauke da wa'innan kololin, Hajiya Salma dake laɓe ta saki murmushi a ranta tace; "taka ta ƙare Abdus-samad".

ta kalle shi tana me tura mishi plate ɗin tace; "dan Allah kaci mana, tun safe nake wahala akan wannan girkin dan Allah kaci".

Abdus-samad yayi murmushi sannan yaja plate ɗin gaban shi, cokali ya saka ya ɗebo haɗaɗɗiyar fried rice ya kai bakin shi......


*ban san haka littafin nan haka yake da masoya ba sai jiya, gaskiya naji daɗi sosai Allah ya saka da alkhairi nagode sosai*.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouƙ*.



*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

Please Login or Register in order to submit comment