Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai dai mu zuba miki idanu ko?, ina ita me ɗaure miki gindin?".

Ummi dake zaune ƙofar ɗakin ta tace; "ina jinka ai faɗi abinda kake so ka faɗa", Baba yayi ƙwafa yace; "yauwa ai ina so kiji da kunnen ki ne".

Ya kalli.Isa da Mama Jummai yace; "kuma ina so kuji abinda zan faɗa domin ina so ku zama sheda".

Ya dawo da kallon shi kan Nusram sannan yace; "kin sami mijin auren", Nusram ta girgiza kai tace; "dan Allah Baba kayi haƙuri".

Baba ya ɗaga mata hannu yace; "sati me zuwa ɗaurin auren ki da Isa", Ummi tace; "wannan ne ba zai taɓa yiwuwa ba wallahi matuƙar ina da rai".

Baba ya miƙe yace; "shikenan sai ki fara shirya kayan ki na tafiya Dabai", babu tsoro ko shakka Ummi tace; "to shikenan".

Nusram ta fashe da kuka ta riƙo ƙafar mahaifin nata tana faɗin; "dan Allah Baba kayi haƙuri", ya zare ƙafar shi yace; "wallahi matuƙar wanda zaki aura be zo gobe ba to sai Uwar ki ta bar gidan nan sannan kuma auren ki da Isa babu fashi", be jira me zata ce ba yayi ficewar shi.

Nusram ta cigaba da kukanta cikin baƙin ciki, yanzu shikenan tayi sanadiyar rabuwar iyayen nata kenan, Ummi tazo ta miƙar da ita tsaye tace; "kada ki damu muje ɗaki".

Mama Jummai tayi shewa tace; "ahayye! Zamu gani dai idan tusa zata hura wuta ai duk wanda yaja dani sai naga bayan shi".

Ummi ta juyo tace; "ta Allah ba taki ba, duk sharrinki akan ki zai ƙare", daga haka taja Nusram suka shige ɗaki.

Mama Jummai tace; "ni yanzu ba zan ce miki komai ba amma ki sani ƴar ki zata shigo hannun mu ne nan da lokaci kaɗan zaki gane ruwa shayi ne".

Nusram ta zuba tagumi tana kallon Ummi na haɗa musu kaya, Nusram tace; "Ummi dan Allah kiyi hakuri ki bari na auri Isan kawai, in dai hakan zai saka ku cigaba da zaman aure da Baba".

Ummi tace; "ki bar wannan maganar Nusram, ki haɗa naki kayan domin kuwa tare zamu tafi dan wallahi ba zan taɓa bari ki auri Isa ba".

Nusram ta saka kuka tace; "ni kuma Ummi ba zan iya bari auren ku ya rabu ta dalilina ba, Ummi me zan ce da Nusreen da kuma Kubra", Ummi tace; "ba wannan na tambaye ki ba, ki tashi ki.haɗa kayan ki kawai".

Dole.haka Nusram ta fara haɗa kayan ta, tana yi tana kuka, Ummi kuwa ta miƙe ta fice don ɗauro alwala tazo ta tada sallah.

Ganin.fitar Ummi yasa Nusram miƙewa, jakar ta ƙarama ta ɗauko, kuɗin da Aunty ta bata ranar da taje gidan ta ɗauko ragowar ta saka a ciki ta ɗauki wayar wannan da bata san ko waye ba ta saka a ciki sannan ta saka hijab ta fice.

Akan ta dai ake faɗa ko to gwara ta bar gidan, dan ita ganin ta hakan shine maslaha kawai ba zata iya zama taga wannan ranar ba wacce zata kasance itace ta zama silar rabuwar iyayen nata.

Sai yanzu take data sani ta amsa auren Yaya Sulaiman ɗin wata ƙila ta sami mafita akan wannan bala'in da yake tinkaro ta, ta juya ta kalli gidan Allah sarki! Ummi ko yaya zata ji idan ta gane cewa guduwa Nusram ɗin tayi?.

Wane hali Ƴar uwar haihuwar nata zata ji a yayin da labari ya iske mata akan abinda Nusram ɗin tayi, yanzu ƴan layi dasu Mama Jummai zasu sami damar gorantawa Ummin, anya kuwa abinda kike so ki aikata Nusram ba kuskure bane?"abinda zuciyar ta ke faɗa mata kenan.

Ta girgiza kai tace; "wannan itace kawai mafita akan abinda ke damuna, dama ace Ummi zata yarda ne na auri Isan da rabuwar auren su ai gwara auren Isan", ta ƙara sauri a ƙoƙarin ta na ganin ta bar inda aka santa.

Haka ta iso bakin titi, lokacin ma yawanci mutane sun shiga sallar Isha'i, ta ƙara damƙe jakar dake hannun ta, kuɗin ciki tana tabbacin zai ishe ta ta sauka wani garin idan yaso sai ta siyar da wayar nan ta sami wajen zama da kuma jarin da zata riƙe kanta.




#LIKE
#SHARE
#COMMENTS


*babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

📖📖47-48📖📖

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Addu'a A Kan Abokan Gaba

اَللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ اْلأَحْزَابَ، اَللَّهُمَّ اهْزِمْهُمْ وَزَلْزِلَهُمْ.

Allahumma! Munzila-l-kitabi, sar'a-l-hisabi! Ihzimi-l-ahzaba. Allahumma ihzimhum wa alzihlum.
Ya Allah! Mai saukar da littafi, Mai gaggawan sakamako! Ka karya kungiyoyin abokan gaba. Ya
Allah! Ka karya su, ka girgiza su.


*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖47-48📖📖


Abdus-samad yayi miƙa tare da yin hamma, agogon hannun shi ya duba ƙarfe shida harda rabi, gaskiya ya gaji daga fara aikin shi yau.

Cikin sauri ya fara tattara kayan shi domin tafiya, Tameer ya turo ƙofar ya shigo, ganin yadda yake haɗa kaya yasa yayi dariya yace; " duk ɗokin aikin kuma har ka gaji".

"amma dai ka san lokacin tashi ya wuce ko, a ƙa'ida 4 ya kamata ace na bar nan", Tameer ya buɗe baki cikeda mamaki yace; "a matsayinka na Co-ordinator".

Ya.lumshe ido yace; "as normal staff bari ka gani na gudu wajen First Love", be jira me zai kuma cewa ba ya fice.

A harabar Companyn ya haɗu da Surayya, "yauwa wuce mini da wannan gida, ki cewa First Love zan je Rigasa", ta amsa da to.

Ya shiga motar shi ya tafi, a hanya a ka fara kiraye-kirayen sallah wannan dalilin yasa ya sami masallaci yayi parking sai da ya idar da sallah sannan ya tafi.

Wani ƙaramin Mall yayi parking, ya ɗauko takardar ya juya ta a hannun shi, shi dai gaskiya babu abinda ya fahimta game da takardar.

Ya duba cikin Mall ɗin mutane ɗai-ɗaiku ne a ciki, wata matashiyar budurwa ya hango da sauri ya nufi inda take.

"amm dan Allah taimaka mini da wannan takardar", Yarinyar ta juyo, a tare suka zaro idanu.

Cikin mamaki Khausar tace; "Abdus-samad", yayi murmushi yace; "dama kecce", ta jinjina kai tana dariya.

"me kazo yi, mu ga takardar", ta faɗa tana miƙo hannu, ya saka mata takardar, ta ɗan jima tana dubawa sannan ta ɗago tace; "na san dai ba ƙanwarka ta aiko ka ba haka ba Mama bace, faɗa mini gaskiya budurwar ka ce ko?".

Ya shafa sumar kanshi yace; "in faɗa miki gaskiya, ƙanwata ce ta aiko ni", a tare suka yi dariya.

Ta janyo kwando ta miƙo mishi tace; "to sai ka riƙe muje ko?", be musa ba, tana gaba yana bayan ta haka suka dinga zagaya wajen sai da ta tabbatar da ta ɗauki duk abinda ke list ɗin sannan suka wuce wajen biyan kuɗi.

Atm ya miƙa musu suka zare kuɗin su duka, sannan suka zuba musu a leda, duka ya ɗauka suka fice.

Khausar ta tsaya jikin motar ta tace; "to daga barin asibiti kuma shikenan sai naji shiru".

"wallahi abin ne ya kwanta mini sosai, amma kiyi haƙuri na miki alƙwari zan zo insha Allahu", Khausar taja ajiyar zuciya kafin ta saka hannu cikin purse ɗin ta sannan ta zaro wayarta ta miƙa mishi tace; "idan na baka number na gaba cewa zaka yi ka manta amma yanzu ka saka mini taka sai ni na nemeka dan ni ba zan manta ba".

Abdus-samad yayi murmushi kafin ya amshi wayar ya rubuta mata sannan ya miƙa mata tare da ledar siyayyar ta, yace; "na gode sosai, bye", ta ɗaga mishi hannu.

Wajen motar shi ya nufa, ya buɗe ya shiga sannan ya tada ya tafi, Khausar tayi dariya cikin farin ciki tace; "mafarkina zai zama gaskiya🙄, cikeda murna ta shiga motarta ta bar harabar wajen.

Koda ya isa Hayin rigasa, cikin Estate ɗin a cike yake da mutane, sai da ya tsaya suka gaggaisa da mutane ya san dama hakan zata kasance idan yayi la'akari da yadda family meeting ɗin su ya matso duk wani na nesa cikin wannan satin suke saka rai da zuwan shi.

Da sallama ya shiga falon, yaron dake wasa ya nufo inda yake, Abdus-samad ya ɗaga shi sama ya cilla sannan yace; "my Boy yaushe kuka dawo", yaron yace; "jiya muka zo tare da Daddyna".

Ya ajiye shi ƙasa sannan ya riƙe hannun shi, Brr Hauwa ke zaune saman sofa gabanta Laptop ne tana dannawa sai Fatima ita kuma takardu take haɗawa.

Abdus-samad ya gaishe dasu, babu laifi duka sun amsa musamman ma Fatima dan ita basu da wata matsala a tsakanin su.

Hanyar ɗakin Malama yayi, Fatima tayi saurin kiran shi, ya juyo zuwa gare ta, "Hajja na ciki ka shiga ka gaishe da ita tukunna", abinda ta faɗa kenan.

Ya san me take nufi don haka babu wata gardama ya nufi nata ɗakin, a kashingiɗe take da jarida a hannun ta.

Yayi murmushi, "wato yau bokon ta tashi kenan da daddare", ya faɗa cikin ranshi ta ɗago tana amsa mishi sallamar da yayi.

A ƙasa kusa da ƙafarta ya zauna, ta dube shi ta ɗauke kai, "barka da dare Hajja, ina wuni", ta ɗebi sakwanni kafin ta amsa da "lafiya", daga haka be kuma cewa komai ba itama bata kuma cewa komai ba.


Tsayin lokaci babu wanda yayi magana, ya miƙe yace; "Hajja sai da safe", har ya fita be ji amsar abinda ta faɗa ba, ta bi bayan shi da sannan tace; "Allah ya tashe mu lafiya".

Tun kafin ya shiga ɗakin yake jiyo muryar su wanda hakan yake tabbatar mishi da cewa fira suke kenan.

Da sallama ya shiga ɗakin, ya zauna saman kujera yana dafe kanshi, Fadila ta ƙaraso inda yake ta janye hannun nashi tace; "duk gajuyar ce".

Ya balla mata harara sannan ya miƙe, kusa da Malama ya koma, "ina wuni?", sai da ta shafa fuskar shi sannan ta amsa da "lafiya lau, ina Maman ka?", yayi murmushi yace; "tana lafiya".

Ledar daya ajiye Fadila ta ɗauka tana murmushi tace; "ah lallai matar ka ta huta", bece mata komai ba sai ma miƙewa da yayi.

Fadil yace; "ba dai har zaka tafi ba", ya lumshe idanu yace; "Fadil na gaji da yawa, dole ce ma ta biyo dani nan ɗin amma da gida zan wuce wallahi", Fadil ya miƙe domin raka shi nan ya yiwa Malama sallama sannan ya fice.

Yadda ya bar su haka ya dawo ya same su, sai dai wannan karon Brr Hauwa, waya take amsawa, sai da safe yayi musu sannan ya fice.

"to bari na bar ka a nan sai da safe", faɗar Fadil kenan bayan sun ƙaraso inda ya ajiye motar shi, ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha sannan ya buɗe ya shiga.

Ya kunna motar kenan, Saleema ta ƙaraso da murmushi a fuskarta ta ƙwanƙwasa glass ɗin, sai da yayi jim sannan ya zuge glass ɗin.

"wannan wane kalar zagaye ne, ya zaka shigo ka tafi dan danan?", ya lumshe idanu yace; "Aunty Saleema na gaji ne sosai".

Ta langwaɓar da kai tace; "amma ai ka ƙaraso ko ganin ka nayi kafin ka wuce ko?", ya shafa gashin kanshi yace; "wallahi sauri nake yi".

"dan Allah mu ƙarasa mana, jin zuwan ka har na shiga kitchen na dafa maka abinci yanzu kuma kace sauri kake yi", ya ɗaga kafaɗa sannan ya buɗe mata ƙofa.

Tayi murmushi sannan tace; "yauwa ko kaifa", ta shiga sannan ya tada motar suka ɗauki hanyar Part ɗin su.

Tare suka jera har cikin gidan, duka suna zaune a falo, yana shiga suka yo kanshi, ya dafe goshi wannan dalilin yasa baya son zuwa gidan gabaki ɗaya.

Saleema ta jera mishi abincin a gaban shi, Haɗaɗɗen spouch chicken da kuma milk shake, be wani ci da yawa ba domin gajiyar dake tattare dashi a yanzu kawai kwanciya yake buƙata.

Sallama yayi musu sannan ya fito inda Saleema ta biyo shi don ta rakashi, "yausha Abba zai dawo", ta ɗan yi jimm sannan tace; "ba zai wuce sati me zuwa ba Abban Nihal kuwa yana hanya", ya ɗan ja numfashi sannan yace; "Allah ya kawo su lafiya", ta amsa da ameen, da haka suka yi sallama inda ya shiga motar shi itama kuma ta juya cikin gida.

Shi ya san ba lallai a ƙare lafiya ba, a duk shekara babu ranar da yake tsoron zuwan ta irin wannan ranar ba ta yin meeting ɗin su, ya shafa kan shi yana faɗin; "ya Allah!".

Kamar ance ya kalli gefe ya hangota tsaye a bakin titi, kallon ta yayi sosai ya lura kamar bata cikin hayyacin ta, har ya gifta sai kuma ya dawo a hankali ya yi parking.

Glass ɗin ya sauke sannan ya leƙo da kanshi, Nusram dake zare idanu, tana ƙare damƙe jakar dake hannun ta, ganin wanda ya leƙo yasa ta ɗan ja baya kaɗan.

Yayi murmushi yace; "ina zaki je?", Nusram ta haɗiye wani mugun yawu sannan ta fara tafiya cikin sauri, ai gwara ta koma gida ko kuma ta hau titin mota ta bige ta da wannan mugun mutumin.

Abdus-samad kuwa ganin hakan yasa yayi saurin buɗe motar ya fito, ganin tana ƙoƙarin kwasawa da gudu yasa ya cafkota.

Ta wage baki zata yi ihu yayi saurin saka hannu ya toshe bakin, "kin manta abinda na faɗa miki kenan ko?", da sauri ta girgiza kai.

Kasancewar kowa hada-hadar shi yake yi ya saka babu wanda ya lura da halin da suke ciki, hannun ta ya riƙe ya jata har zuwa mota ya buɗe ya saka ta sannan shima ya shiga ya ja suka bar wajen.

Nusram babu abinda take yi banda zare idanu, tunanin ta ɗaya shine ta gama rayuwa ita kam tata ta ƙare.

"ina zaki je?", kamar daga sama taji tambayar, bakin ta na rawa tace; "ina so na bar garin nan ne", ya ɗan juyo ya kalle ta kana ya sami waje ya tsaya.

Sosai yanzu yake kallon ta yayin da ita kuma take faman wasa da yatsun hannun ta, sai da ya nazarce ta sosai kana yace; "kada dai kice mini gida kika bari".

Ta ɗaga kai tana cigaba da abinda take yi, ya girgiza kai yace; "kada ki sake ki fara wannan kuskuren, kin san me zaki tarar a inda zaki je ko kuwa kina tunanin matsalar da kike ciki wacce zaki tarar ba zata kaita ba, kina da tabbacin wani abu ba zai same ki ba, kina da iyaye wane hali zasu kasance? Kina da ƴan uwa bakya tunanin su, kin san kalar rayuwar da zaki shiga, kin san meye matsayin mace me zaman kanta?".

Ta girgiza kai, ya ɗan ja numfashi yace; " *KARUWA*!, kin shirya amsa wannan sunan", Nusram idanun ta ya kawo ƙwalla.

Hannu ya saka ya zaro tissue ya miƙa mata, ta amsa ta goge hawayen dake fuskarta tace; "to ai na rasa wanda zai aure ni ne", ya ɗan yi jim sannan yace; "kamar ya kenan?".

"Baba ne yace na fito da mijin aure kafin sati biyu, gashi sati biyun ya cika ni kuma bana da tsayayyen saurayi wanda zai aure ni".

Ya jima sosai kafin yace; "yanzu bari na maida ke gida gobe zan zo na sami mahaifin naki", ta ɗago da sauri ta kalle shi tace; "zaka aure ni ne?".

Shiru yayi be tanka ba, Nusram ta kuma cewa; "idan har ka san ba aure na zaka yi ba kawai ka barni na tafi", kamar an fizgo maganar yace; "naji na amince zan aure ki".

Daga haka babu wanda ya kuma magana, ya tada motar ya juya zuwa maida ita gida har suka isa ƙofar gidan babu wanda ya kuma magana.

Bayan yayi parking be ce komai ba, ganin hakan yasa Nusram buɗe ƙofar, har ta saka ƙafarta waje sai kuma ta dawo.

"ka tabbata zaka zo goben", babu wani dogon tunani ya ɗaga mata kai, tayi murmushi tace; "ni ban damu da sai munyi zaman aure ba, koda dai sati ɗaya ne, sai ka ƙyale ni na tafi", ya gyaɗa kai, tayi murmushi ta juya ta fice.

Abdus-samad ya bi bayanta da kallo yana tunani haka gaban shi yana faɗuwa, "wane matsala kake ƙoƙarin jefa kanka a ciki ne?", ya faɗa yana dafe saitin zuciyar shi dake bugawa da ƙarfi.


#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖49-50📖📖


cikin natsuwa yaja motar shi ya bar ƙofar gidan, duk yadda yaso yayi tunani abin yaci tura dole ya watsar da komai ya maida hankalin shi kan tuƙin da yake yi.

Ƙarar shigowar saƙo wayar shi yasa ya kalli wayar, be duba ba dan be kawo wani me mahimmanci bane.

Ta ƙofar baya ya shiga gidan nasu domin baya so ya haɗu da kowa babu abinda yafi buƙata a lokacin irin ya kwanta ya huta.

Yana shiga ɗakin shi bayi kawai ya wuce kanshi ya sakarwa shaya, ruwan na sauka a jikin shi ya lumshe idanu, gaba ɗaya abubuwan daya faru ya fara dawo mishi.

Cikin sauri ya buɗe idanun shi yana dafe kanshi yace; "me ka janyowa kanka Abdus-samad?", tambayar da babu amsa kenan.

"koda yake ai idan ka yiwa mahaifinta bayani zai fahimce ka domin kuwa babu wanda zai so ƴar shi ta faɗa wannan halim", abinda zuciyar shi ta faɗa mishi kenan.

Koda ya fito ya tsane jikinshi sannan ya ciro kayan barci ya saka, jikinshi ya feshe da turare kana ya janyo wayar shi.

*love is hard and will always be, but remember somebody loves u and that one is me*

Abdus-samad ya taɓe baki, number ne babu suna dan haka be damu da sanin waye ba domin kuwa irin wa'innan saƙonnin har gajiya yake da buɗe su.

Be jima sosai ba barci ya kwashe shi, Brr Farida kuwa jin shirun yayi yawa yasa ta nufo part ɗin shi, kamar yadda ta zata ya dawo ɗin, zuwan ta na uku kenan sannan ta tarar dashi.

Ɗakin da duhu sai dai ƴar fitilar gefen gado dake kunne, tayi murmushi sannan ta taka zuwa kusa da gadon.

Ta jima tana yin addu'a kafin ta tofa a hannun ta kana ta shafa mishi a jiki, yayi juyi cike da gajiya, Brr Farida tayi murmushi kawai.

Ta san dama hakan zai faru shiyasa koda ya dage akan zai fara aiki ta hana, ranar farko kenan duk yabi ya gaji.

Cikin natsuwa ta fara mishi tausa, aikuwa malam Inusa🤣 harda ajiyar zuciya, ta jima sosai kafin taja mishi blanket ɗin, peck tayi mishi a goshi kafin ta fice daga ɗakin.

Nusram kuwa koda ta shiga gida bata sami kowa a tsakar gidan ba, cikin sauri ta tura ƙofar ɗakin nasu wanda tana da tabbacin Ummi ta turo ƙofar ta shige.

Ummi dake saman abin sallah ta juyo tana kallon Nusram ɗin, Nusram ta saukar da kai ƙasa tana wasa da hannun ta.

Ummi tace; "daga ina?", Nusram tace; "Ummi dan Allah kiyi haƙuri", Ummi ta girgizai kai kawai, cikin sauri Nusram ta shige cikin ɗaki.

hijab ɗin jikin ta, ta cire sannan ta faɗa saman katifar su, lallai rayuwa kenan, wayar dake cikin jakar ta ciro kamar koda yaushe hoton shi dai shine take kallo.

"ashe dai a cikin masu shan jini akwai nagari? To kodai kema siyar dake zai yi ko kuma ya bawa gunki jinin ki?", abinda zuciyar ta take raya mata kenan.

Zumbur ta miƙe zaune, "koda yake ma ai gwara ya bawa aljanin jini na ko na huta da wannan rayuwar", wata zuciyar ta sake faɗa mata haka.

Addu'a tayi kafin ta kwanta, bata jima ba barci ya kwashe ta, tana me fatan gobe ta sami mafita.

Washe gari da safe bayan sun idar da sallar asuba, Baba yazo ƙofar ɗakin nasu ya ƙwalawa Ummi kira.

"Maimuna fito", Ummi ta miƙe ta fice, ya kalle ta ya kauda kai yace; "fatan dai kin haɗa kayan ki na tafiya ko?", Ummi cikin dakiya tace; "eh ko korata kake ne na tafi yanzu", ya ɗaga kafaɗa yace; "kusan hakan ai".

Ummi ta girgiza kai sannan ta juya zuwa ɗaki, Nusram dake tsaye tana jiran Ummin domin taji duk abinda ya gudana, Ummi ta kalle ta tace; "ɗauko jakunkunan mu tafi".

Nusram hawaye ya kawo mata, ta girgiza kai, da sauri Ummi ta girgiza mata kai tace; "kada ki soma Nusram ya kamata ace zuwa yanzu kin sami.ƙarfin zuciya, ɗauko kinji", Ummi

Please Login or Register in order to submit comment