Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tsaki taja ƙasa-ƙasa gudun kada mahaifiyar tata taji tace; "mutum ba ɗan sarki ba ba kowa ba amma sai iya mulki da wulaƙanci", Tameer dake zaune kusa da ita yayi ƙwafa.

Brr Farida ta maida kallon nata kan Tameer tace; "kai baka ga ɗan uwan naka bane?", shafa kai yayi yace; "Mum tsakanin nida shi waye gab......", cikin daka tsawa tace; "shut up my friend, ina tambayar ka kana tambaya ta", ya saukar da kai ƙasa sannan yace; "kiyi haƙuri", ya ɗan kalli Abdul ɗin da idanun shi ke rufe yace; "Barka da dawowa".

Be buɗe idanu ba balle ya saka ran zai samu amsa sai dai ɗaga mishi hannu kawai yayi, Surayya duk da ɓacin ran da take ciki sai da abin yaso bata dariya, aikuwa ta hau tarin ƙarya dan ta san yadda Tameer ya kai matuƙa wajen ɓacin rai tana yin dariyar zai sauke akan ta.

Tameer kuwa ya maida kallon shi kan Brr Farida yace; "Mum ki ganni yadda yayi mini fa? Amma baki ce komai ba", Brr Farida dake danna waya ta ɗago tace; "ya gaji ne ka bari idan ya huta zai maka magana ne ai", daga haka motar tayi shiru kuma aka cigaba da tafiya.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*HAYIN RIGASA, KADUNA*

Koda suka isa gida Nusram ƙin kula Nusreen tayi, har zuwa lokacin da suka shirya domin tafiya makarantar islamiyya.

Ummi ma dai bata bi ta kan su ba, Nusram data fito daga wanka ta kalli Kubra tace; "Autar mu kina hutawar ki Ummi na ji dake", yarinyar ta ɓangale baki tana dariya.

A ɗan fizge ta kalli Nusreen wacce keta faman kwalliya, jikin ta sanye da shadda kalar orange doguwar riga, Nusram ta taɓe baki sannan ta hau nata shirin.

Kusan a tare suka gama sai dai kallon farko da Nusreen ta yiwa Nusram jikin ta yayi sanyi ganin ita sanye take da Atamfa me ruwan toka da ɗigon baƙi wanda ba haka sabon su yake ba, kasancewar Nusreen ɗin ke fara wanka dan tana daɗewa a shiri sannan duk kayan data saka yana nufin shi Nusram zata saka kenan, duk ranar data canza to tana fushi da ita kenan.

Nusram nada haƙuri sosai da kau da kai sai dai akwai kafiya sannan idan tayi fushi tana jimawa bata sauka ba, yayinda Nusreen take sha yanzu magani yanzu amma fa da angama ya wuce kenan.

Haka suka fito domin tafiya, Nusram ta buɗe jaka ta ɗauko sweet guda biyu ta miƙawa Kubra a hannu tana faɗin; "Ummi sai mun dawo", ta amsa tana bin yaran nata da kallo domin daga ganin banbancin kaya a jikin su ta san sun yi faɗa kenan.

Suna fita tsakar gida Ameera tana wanke-wanken kayan da suka siyar na rana, Mama Jummai kuma na kusa da ɗakin ta a zaune da ɗaurin ƙirji tana faman lissafa kuɗi.

Tana ganin sun fito tayi shewa tace; "kaga irin haihuwar da ake so ba irin wacce za'a dinga yawo kwararo-kwararo ba da sunan karatu dan an rasa mashinshini", yau dai tayi sa'a domin kuwa Nusreen ko kallon ta bata yi ba.

Kamar kurame haka suka tafi har izuwa makarantar, basu yi latti ba hakan yasa kawai suka shiga aji, har aka tashi babu wanda yayi wa juna magana.

Haka har suka iso gida, a ƙofar gida suka tarar da Baba a zaune a dakali yana jin labarai, suka mishi sannu da hutawa amma ko kallo basu ishe shi ba.

Suna shiga suka tarar da Mama Jummai gaban murhu tana ta faman iza huta, gefen ta kuma Ameera ce take shirya jarkunan kunun aya dana zoɓo.

"ba dole mutum kullum yayi ta baƙi ba, koda yaushe yana gaban murhu", faɗan Nusreen kenan, Mama Jummai ta wullo mata harara tace; "tunda jikin na Uban ki ne ba sai ki hana ni zama gaban murhun ba".

"ai dama nashin ne sanin dai ne da ba'a yi saboda ba'aje makaranta bane an san haƙƙin miji", ta bata amsa ba tare da shakka ba.

Mama Jummai ta ɗaga hannu ta nuna Ummi dake ƙofar ɗaki tana wanke shinkafa tace; "kin ga wacce bata yi makaranta ba kuma bata san haƙƙin miji ba", ta buɗe baki zata bata amsa Isa yayi sallama ya shigo.

Ta kalle shi ta kauda kai sannan tace; "ai naga saboda tsabar sanin haƙƙin mijin ne yasa aka taho da ɗan gaban fatiha", tana ƙarasa ta zuba da gudu tayi ɗaki.

Nusram data ɗauko tsintsiya domin share gidan ta girgiza kai kawai cike da takaici ta tsugunna ta cigaba da sharar ta, Isa kuwa cikin tsananin takaici yace; "shegiya ƴar isa ai da kin tsaya da yau sai na ɓalla ki a gida nan", cikin salon mugun ta ya sakarwa Nusram dundu a gadon baya wanda ta jishi har saman kanta.

Ƴar ƙaramar ƙara ta saki sannan ta durƙushe a wajen, yaja tsaki ya fice ya bar maman shi tana zuba masifar ta a tsakar gida.

Ummi bata ko ɗago kai ta kalle su ba, Nusram kuwa sai da tafi minti biyar sannan ta iya miƙewa ta cigaba da sharar ta tana yi tana share hawaye.

Koda ta gama sharar sannan ta ɗaura alwala tana kallon Nusreen tana leƙowa domin tabbatar da fitar Isa, sallah ta tayar ta ƙyale ta.

Bayan sun idar da sallah nan suka zauna har kiran isha sannan suka yi sallar, suna idarwa suka dawo falo suka zauna domin cin abinci.

Kasancewar garin da zafi yasa Nusram ɗaukar tabarma ta shinfiɗa musu ƙofar ɗaki sannan suka fita duka.

Suna cikin cin abinci Nusreen ta maida kallon ta zuwa ga Nusram tace; "wai Ram meye nayi miki ne da tun ɗazu kike share ni".

Jin hakan yasa Nusram tsame hannun ta daga abincin tace; "Rim magana kike fa akan dukan matar aure, wallahi Rim bana son wannan halayyar taki, kiga fa yadda kika dinga ɗaga murya kina faman faɗa akan abinda be taka kara ba balle ya karya haba Nusreen kina girma kina cin ƙasa, ki sani ba ko da yaushe ba ake faɗan abinda kaga dama ba, kwata-kwata Nusreen baki da haƙuri gaba ɗaya kin lalata rayuwar ki da tsiwa".

Nusreen tayi shiru tana sauraren ƴar uwar ta kamar da gaske, kafin tace; "tunda bakya so insha Allahu zan dena", Nusram ta saki murmushi tace; "yauwa ko kefa", haka suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa, Ummi kuwa murmushi kawai take yi domin taji abinda ƴar tata ta faɗawa ƴar uwar ta kuma hakan ya birge ta.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*UNGUWAR RIMI, KADUNA*.

Shureim ne kwance saman sofa wacce take ɗakin shi, idanun shi a lumshe babu abinda yake dawo mishi banda magan-ganun yarinyar yadda take juya idanu da yadda take tsiwar tata.

Ya saki murmushi a karo na babu adadi, ya ƙara gyara kwanciyar shi cike yake da muradin ƙara ganin ta, sai dai yana shakkar yadda zata tarbe shi dan da gani yarinyar babu raini a tattare da ita.

Abokin shi Naufal ya ƙaraso ya zauna kusa dashi sannan ya bubbugi gefen sofa ɗin, cikin sauri Shureim ya buɗe idanun shi sannan ya kalli abokin shi yace; "ya akayi ne kake tashin mutane suna barci?".

Naufal yayi murmushi yace; "ka dena magana irin haka mana, bafa barci kake ba idanun ka biyu don yadda kake murmushi wallahi yadda ka san sabon bazawari", tare suka hau dariya.

Sai da suka tsagaita sannan Shureim yace; "tsiwa ta", Naufal yayi tagumi yace; "yau kuma me tsiwar taka tayi?, kun kuma haɗuwa ne?", Shureim ya girgiza kai yace; "ina fa sai dai yau ina so ka shirya muje binciken gidan su na gaji wallahi".

Naufal ya ɗan haɗe fuska yace; "gaskiya ka bari ba yau ba dan nima ina da wajen zuwa", Shureim ya miƙe zaune yace; "lallai Naufal ni kake faɗawa haka ko saboda na gama yi maka amfani amma kada ka manta lokacin da kake neman auren Futuha na tsaya maka sosai".

Naufal ya girgiza kai yace; "gaskiya ka san Futuha tana da kishi sosai wallahi taji zan raka ka taɗi to abin ba zai ƙare mini da kyau ba".

Shureim yace; "banza matsoraci dan Allah wallahi ba zan bari mu daɗe ba", Naufal ya saukar da numfashi yace; "shikenan angon tsiwa", suka sake yin dariya.

Shureim yace; "yadda Mamie ta ƙosa nayi aure ne shiyasa bana so ta dawo ta samu magana ba tayi nisa a tsakanin mu ba, na kuma san zata ji daɗi".

Naufal yace; "ni ba wannan ba kada fa taje tayi ta mana tsiwa ne", Shureim yayi murmushi yace; "ai wallahi abinda nafi so tayi kenan", haka firar tasu ta cigaba cike da annashuwa.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

motar na yin parking Sumayya ta kwaso da gudu, shima cikin farin ciki ya buɗe mata hannu ta faɗa jikin shi tana faɗin; "Oyoyo Yaya na".

Ya riƙo hannun ta sannan yace; "fatan na same ku lafiya", cikin fara'a tace; "lafiya lau sai dai kewar ka da muka yi kawai".

Haka ya riƙe hannun ta suka shige cikin gidan, Fahad na zaune yana kallon cartoon ganin shigowar su yasa ya miƙe ya nufi inda suke.

Abdul ya tsugunna dai-dai tsayin shi yace; "little angel ya school", Fahad yace; "lafiya lau Yaya", Abdul yayi murmushi fahad ya ɗora hannun shi dai dai dimple ɗin shi yace; "Yaya na daina ganin wannan".

Ɗauke shi yayi cak ya ɗaga sama yace; "to ai yanzu na dawo zaka cigaba da gani", Brr Farida tace; "yanzu kaje ka huta anjima sai kazo kaci abinci".

Cikin shagwaɓa yace; "gaskiya ba zan iya haƙuri da cin abincin ki ba First love har sai anjima", Sumayya tace; "Yaya kamar ka san yayi daɗi kuwa".

Ya kama hannun Sumayya suka nufi dinning tana zuba mishi surutu shi kuma yana murmushi bayan shi kuma Brr Farida ce ita da Adnan.

Sai lokacin na juya na kalli falon babu kowa alamu ya nuna Surayya da Tameer sun bar falon kenan🤔.

Brr Farida da kanta tayi serving ɗin shi, haka ya dinga ci yana santi su kuma suna dariya, sai da ya gama sannan Brr Farida ta bari su Sumayya suka ci.

Shi dai yana gamawa ya miƙe ya nufi part ɗin shi domin hutawa, a hanya suka haɗu da Surayya, ta kalle shi ya kalle ta, cike da takaici ta nufi part ɗin su Sameer.

Ya taɓe baki yana me shigewa nashi part ɗin, lumshe idanu yayi jin irin ƙamshin dake tashi a ɗakin ya san aikin mahaifiyar shi ne shi yasa yake matuƙar ƙaunar ta.

Sai da yayi wanka sannan ya saka singlet da three quater ya kwanta, be wani jima ba barci ya ɗauke shi.



#LIKE
#SHARE
#COMMENT



*ƳAR MUTAN ZAZZAU*


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖9-10📖📖


Surayya cikin kuka ta shiga falon, Sameer dake kwance saman kujera ya tashi da sauri, wajen shi ta nufa tana zuwa ta faɗa jikin shi tana sakin kuka.

"wai meya faru ne?", ya tambaya, cikin sheshsheƙar kuka tace; "Yaya wallahi na kusa haɗiyar zuciya na mutu saboda baƙin cikin Yah Abdul da Mummy".

Cikin sauri Sameer ya miƙe yace; "wai me yasa kuke haka ne komai Abdul! Abdul!! Haba ya kamata ace kun canza wata maganar ok mutuwa zaki yi to kuwa sai ki shirya mutuwar domin kuwa Mummy ba zata taɓa dena son Abdul ba dan wannan kam daga Allah ne", yana gama faɗin haka ya kwashi wayoyin shi yayi waje.

Part ɗin Brr Farida ya nufa yana tafe yana tunani; "tabbas abinda ƴan uwan shi suke complain shima yana damun shi sai dai kuma shi ba zai yi wauta irin tasu ba".

Yana daf da shiga itama tana fitowa, jikin ta sanye da doguwar riga baƙa ƙirar Saudia, tayi rolling da gyale kalar peach, hannun ta riƙe da wani ƙaton littafi kamar diary.

Da sauri ya ƙarasa wajen ta yace; "sorry Mummy banzo yiwa ɗan lelen ki sannu da zuwa ba barci ne ya kwashe ni".

Ba tare da komai ba tace; "kada ka damu amma gaskiya banji daɗi ba", ya kwantar da kanshi saman kafaɗar ta yace; "sorry Mum", ta shafa kanshi tana faɗin; "ya wuce ai bari nayi sauri na tafi zan kaiwa Brr Isma'il wannan documents ɗin ne yanzu", ya kamo hannun ta yace; "muje na raka ki bakin get", babu musu yaja hannun ta suka tafi.

Suna tafe suna fira har suka iso bakin get ɗin, Securities cikin sauri suka buɗe mata ƙofa domin ta shiga, Brr Farida kuwa lokacin da ta saka ƙafa domin shiga cikin motar gaban ta ya yanke ya faɗi, cikin sauri ta juya ta kalli hanyar part ɗin shi.

Sameer yace; "Mummy lafiya kuwa?", da sauri tace; "Sameer Abdul", cike da takaici amma ya danne yace; "Mummy me zai same shi kuwa? Kawai ki tafi kada ki ɓata lokacin ki".

Ta kalle shi sannan ta girgiza kai tace; "bari dai naje na dubo shi na dawo", da sauri Sameer ya riƙo hannun ta yace; "kije Mum zan je na binciko shi I promise you", bata saurare shi ba ta nufi hanyar part ɗin nashi.

Shi kuwa da yake barci wanda yake cike da mafarkai marasa daɗin gani, wai gashi a ƙulle jikin wata ƙatuwar tukunya ƙasa kuma wuta ke ci ga wasu mutane dake sanye da jajayen kaya babu abinda suke kira sai *Murad*.

So suke su riƙe shi amma wutar taƙi ta basu dama, a duk lokacin da suka kawo hannu domin riƙe shi sai wutar tayo sama kaman zata taɓa su, wanda shi kuma yo saman da wutar take ba ƙaramin ƙona shi take ba.

A dai-dai wannan lokacin kuwa Appu ne gaban ƙatuwar ƙwaryar tsafin su, wacce take cike da jini da kuma wasu irin ganyayyaki kalar ja da shuɗi.

Sunan *Murad* yake ƙwala kira cikin ƙaraji da kuwwa, tar fuskar Abdul ta fito cikin wannan ƙwaryar yana kwance yana barci.

Wata mahaukaciyar dariya yayi sannan ya kira Tuge akan yazo ya gani, cikin sauri ya matso gaban katuwar ƙwaryar, tabbas shine wanda suke nema ruwa a jallo amma ƙaƙababbiyar matar nan ta hana taƙi basu dama su nufe shi da sharri.

Wani magani Appu ya ɗauko me kalar baƙi ya fara wasu surutai yana watsawa cikin ruwan, ya jima yana watsawa sannan ya cigaba da ƙwala mishi kira, a cikin ruwan ya buɗe idanu sannan ya fara yunƙurin tasowa zuwa gare su.

Sosai duka wajen suke murna ganin aikin su na tsayin shekaru ashirin da biyar zai cika, ta ruwan Appu yake ƙoƙarin janyo shi.

Sai dai shigowar Brr Farida yasa wajen ya dauki wata irin ƙara Ƙwaryar kuma ta kama da wuta wanda yayi sanadiyar matsawar su baya cike da tashin hankali gudun kada fuskokin su su ƙone.

Brr Farida kuwa ganin yadda Abdul ke haɗa zufa ga wata irin jijjiga da yake yi yasa tayi saurin jijjiga shi tana kiran sunan shi cike da tashin hankali.

A matuƙar razane ya buɗe idanun shi wa'inda tsabar masifa da tashin hankali suka canza kala da grey colour suka koma ja da yellow-yellow a haɗe, cikin matukar tsoro da tashin hankali ya faɗa jikin ta ya rungume yana sakin ajiyar zuciya.

Ta fara shafa bayan shi tana karanto addu'o'i tana tofa mishi, tun jikin shi na rawa har ya dena a hankali kuma ya numfashin shi ya fara dai-dai ta.

Sai da nutsuwar shi ya dawo sannan ya zame daga jikin ta ya kwanta saman gadon, Brr Farida kuwa ganin hakan yasa tace; "ai dama na faɗa maka indai ba zaka dena kwanciya barci baka yi addu'a ba hakan ba zai dena faruwa da kai ba, yanzu da ban shigo ba fa? Abdul ka dinga addu'a amma abu ya gagara".

Ya juyo ya riƙe hannun ta sannan yace; "First love kiyi haƙuri barcin ne yazo mini ban shirya ba, amma ba zan kuma ba", tayi peck ɗin shi a goshi tace; "yauwa Baby na, kada ka kuma kaji".

Ya ɗaga kai kawai, sai da ta kuma yi mishi addu'ar tsari da kariya sannan tace; "ka cigaba da barcin ka yanzu zanje na kaiwa Brr Isma'il wannan takardun na dawo".

Cikin sauri ya miƙe yace; "First love bari na shirya mu tafi tare", yana gama faɗin haka ya shige bayi domin wanka, be jima sosai ba ya fito inda ya samu har Brr Farida ta fito mishi da kayan da zai saka.

Haka ya shirya cikin riga peach da kuma baƙin wando, takalmi ya zura ya fito yana ƙoƙarin ɗaura agogon hannun shi.

Brr Farida dake tsaye tana kallon shi, gaban ta sai da ya faɗi ganin irin kyawun da yayi gashi yana tsananin kama da mahaifin shi.

Ya hura mata iska a ido, ta lumshe idanun sannan tace; "kayi kyau ɗana", ya riƙo hannun ta yace; "duk kyau na ai ban kai ki ba", haka suka jera gwanin ban sha'awa har waje.

Sai da ya buɗe mata ƙofa ta shiga sannan ya zagaya securities suka buɗe mishi shima ya shiga ya zauna, cikin natsuwa driver ɗin yaja motar sauran motocin suka rufa musu baya.

*FEDERAL HIGH COURT, KADUNA* bakin wajen Brr Farida suka yi parking, ta kalli Abdul da idanun shi ke ƙasa tace; "Baby ka jira ni bari na shiga na fito yanzu", kamar wani ƙaramin yaro haka ya maƙe kafaɗa, Brr Farida ta saki murmushi sannan suka fito duka, hannun su sarƙe dana juna suka nufi ciki.

A wani office suka sami Brr Isma'il ɗin yana zaune yana rubuce-rubuce, ta miƙa mishi documents ɗin sannan suka fito.

Sun ɗauki hanyar komawa gida Abdul ya kalli mahaifiyar shi yace; "First love in tambaye ki, wai waye *Murad*?".

Cak ta dakatar da tapping ɗin laptop ɗin da take yi tana zuba mishi idanu na tsayin minti biyu, har gaban shi ya fara faɗuwa, "a ina kaji wannan sunan?".

Abdul ya sunkuyar da kai yace; "mafarkin da nayi ne ɗaz....", tayi saurin dakatar dashi tace; "ya isa haka Abdul mafarki ne kawai kuma mafarki shirme ne".

Daga haka ta ɗauki waya tana dialing number ɗin mijin ta wato *DR ABUBAKAR YUNUSA NAGIMI*, tace; "Daddyn ku yace baka kira shi kace ka sauka lafiya ba".

Ya shafa kai yana faɗin; "ganin ki ya mantar dani shi", ta saki murmushi sannan ta kara wayar a kunnen ta, tana faɗin; "Assalamu alaykum hasken ruhina farin cikin Farida angon brr", a tare suka yi dariya yayin da Abdul ya kauda kan shi yana sakin murmushi, soyayyar mahaifiyar shi da mahaifin shi tana matuƙar birge shi sosai sam basa gajiya da juna sannan babu ruwan su da yaran su kullum cikin bege da ƙaunar juna suke.

Miƙo mishi wayar da tayi shiya katse tunanin da ya tafi, sai da yayi ɗan jim sannan ya amsa, cikin ladabi ya gaishe dashi, shi kuma ya amsa cike da so da kulawa.

"na san Mummyn ka tana ƙoƙari da kai sosai, babu wata matsala ko?", kamar yana gaban shi sai da ya ɗaga kai sannan yace; "eh babu", Dr yace; "to masha Allahu na yi muku order ɗin motocin ku kai da ƴan uwan ku nan da next week zasu iso".

"Daddy yaushe zaka dawo?", tambayar daya jefa mishi kenan, sai da yayi shiru sannan yace; "nan da lokaci kaɗan Insha Allah, kaje Hayin Rigasa?", shima ya jefa mishi tambayar.

" a'a, amma insha Allah zan je zuwa gobe", ya bashi amsa,Dr yayi murmushi yace; "to Allah ya kaimu, ka ƙara kulawa kaji", yace; "to", haka suka yi sallama sannan ya miƙawa Mummyn shi wayar wacce ta zuba mishi idanu.

Kauda kai yayi yana sakin murmushi, can ya kuma ɗagowa idanun nata yana kanshi, ya kwaɓe fuska yace; "First love, me kuma nayi?".

"ina zakaje kake faɗawa Daddyn ku nan da gobe?", ta tambaye shi, ya riƙo hannun ta sannan yace; "Mum muna magana ne akan zuwa na Hayin Rigasa", kauda kai tayi kamar bata ji me yake cewa ba shima kuma yayi murmushi ya kwantar da kanshi saman kujera.

Be san meke tsakanin Mummyn shi da dangin mahaifin nashi ba sai dai ya lura basa wata mu'amala sosai, shine ma me ƙoƙarin zuwa amma sauran basa zuwa sosai kuma itama bata tilasta musu suje kuma shima Daddy haka be wani damu da suje ba sai dai abinda ke bashi mamaki yadda Daddyn ke tilasta mishi shi yaje duk da Mummy bata so, to shi kanshi yaje sai ran shi ya ɓace wani lokacin sai dai duk da haka yana ƙaunar gidan.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*HAYIN RIGASA, KADUNA.*

Shureim ya kalli Naufal yace; "yauwa kaga wa'incan masu hijab ɗin ruwan toka to ɗaya daga cikin su ce, sannan suna wucewa zamu bisu a baya", Naufal dake ƙunshe dariya ya ɗaga kai duk da suna daga nesa ba zai gane yanayin su ba.

Idanu ya zuba musu har suka matso, duka kyawawa ne, masu haske sannan marasa ƙiba sosai, suna da idanu manya wa'inda suke farare hanci su dogo ne sai bakin su daya kasance ɗan madai-daici duka suna sanye da hijab me ruwan toka wanda ya ƙara fito da ainihin kyawun su, sannan kuma daga gani shine Uniform ɗin islamiyar tasu.

Ɗayar ya kalla, yadda take buɗe ƙananan haƙoran ta farare tas take faman zuba magana yayin da ɗayar ke sakin murmushi inda gefen kumatun ta ke lotsawa duka biyu tana kuma lumshe idanu da har yadda zarazaran gashin idanun ta ke rufe idanun ruf.

Iya kallo na ƙurilla yayi musu amma ya kasa gane makusar su sannan kuma ya kasa banbance su, duka kamar su ɗaya baya jin ko mahaifiyar su zata iya banbance su, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya maida kallon shi kan abokin nashi wanda shima su ya zubawa idanu yana kallo.

" to anan waccece tsiwar taka?", ya jefa mishi tambaya, Shureim yayi murmushi yace; "kaima daga gani ai ya kama ta ka bambamce mana, kalle su da kyau ka gani ƙwaƙwalwar ka ta hasaso maka", ya ƙarasa yana kai duba gare su tare da sakin murmushi kamar wani ɗan can haka 🙄.

Naufal ya ƙara kallon su, izuwa yanzu kuwa sun matso sosai kusa dashi kuma yana iya ganin su tarr da suna daf da gifta su, shi dai har yanzu ba zai banbance su ba domin kuwa ko agogon dake maƙale a hannun su me ruwan toka kala ɗaya ne haka zobe dake

Please Login or Register in order to submit comment