Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan suna primary five islamiyya ma sukan je kuma yana biya dai-dai gwargwado.

Ana auro Jummai komai ya fara taɓarɓarewa, amma duk da haka Maimuna ta cigaba da zaman haƙuri da Abdullahi.

Haka ta ɗauko ɗan shegen ta tazo dashi kuma Mal Abdullahi ya nuna yafi son shi sama da ƴaƴan daya haifa, tun yana ƙarami dan ya girmi su Nusram da shekara huɗu suka taso da ƙiyayyar juna, haka Jummai zata saka yayi musu dukan tsiya amma duk da hakan sai Nusreen ta san yadda tayi itama ta rama.

Sai da Jummai ta shekara guda sannan ta sami ciki, murna wajen Mal Abdullahi ba'a magana inda yake ganin zai sami ɗa namiji ta ɓangaren ta wannan ya bata lasisin shuka rashin mutuncin ta yadda take so.

Bayan wata tara sai gashi ta santalo ƴar ta mace aka saka mata Habiba, wannan shine abinda yaso ya kawo matsala tsakanin su sai dai da yake da asiri hakan be wani tasiri ba.

Kafin Habiba ta cika shekara ɗaya Jummai ta sake samun wani cikin nan fa sabuwar murna ta tashi, a lokacin kuma Nusram suka gama primary suka shiga aji ɗaya a secondry yayin da Isa ke aji uku a secondry.

Nan ma ta sake haifo mace inda murnar Malam Abdullahi ta koma ciki, ranar suna aka saka mata suna Sahura, sai da Sahura ta shekara Uku sannan ta sami wani cikin ta haifi mace aka saka mata Sakeena, to daga nan fa sai haihuwar ta ɗan tsaya mata.

Bata kuma samun ciki ba sai da su Nusram suka shiga aji huɗu a secondry shi kuma Isa yana aji shida a secondry sannan ta kuma samun ciki ta haifi ƴar ta mace aka saka mata suna Atika bata kuma cika shekara ba ta sami wata ƴar inda taci sunan mahaifiyar shi Kareema ake ce mata Ameera daga nan bata kuma samin wani cikin ba.

Nusram kuwa suna aji na shida a Secondry sannan maman su ta sami ciki, babu kunya ba tsoron Allah Malam Abdullahi ya fara murna akan zai sami ɗa namiji, nan kuma bakin Jummai ya mutu.

Su dai suka zubawa ikon Allah idanu, babu inda Jummai bata je ba don asiri amma kuma ciki yaƙi zubewa hakan ne ya ƙara tada hankalin ta.

Ciki na shiga watan haihuwa ta haifi ƴar ta mace, ranar Jummai har party sai da ta haɗa a gidan, su Habiba suna gama jss 3 ta cire su daga makaranta ta fara ɗora musu talla.

Haka Malam Abdullahi na kallo amma bashi da yadda zai yi da ita dole ya ƙyale ta, Kubra nada shekara ɗaya aka fara gane cewa aljanu sun taɓa ta wannan dalilin yasa Malam Abdullahi ya dena kwana a ɗakin Maimunar wai tsoron ta yake ji.

Ummi kuwa magani ta shiga nemawa ƴar ta, ta manta dashi, Nusreen kuwa ta buga tsalle tace Mama Jummai ce tayi mata asiri, sai da Ummi ta tsawatar mata sannan ta bari.

Tun daga lokacin da faɗa ya taɓa haɗa su da Nusreen ta kama ta zata dake ta Nusram taji haushi ta shiga.

Dama ance faɗan me haƙuri be iya ba, haka ta jibgi Mama Jummai da itace a kai dalilin kuwa Habiba ta fara tsayawa da saurayi sai takewa Nusreen ɗin habaici shine ita kuma ta gaza haƙuri har ta tsinkawa Habibar mari a lokacin Mama Jumman bata ce komai ba.

Sai da ta bari Nusreen ta saka guga a rijiya taje ta rufe ta da duka, Ummi tana zaune tana kallo bata ce komai ba, Nusram kuma na riƙe da Kubra tana shafa mata maganin da Auntyn Tudu (Hajiya Kaltume) ta amso ta kawo mata.

Wani haushi da zuciya ya taso mata, dama Maman ta ɗora abincin siyarwa tana dafawa ta saki ta tafi duka, wajen murhun ta nufa tana zuwa ta ɗauki itace ɗaya tayi kan Maman.

Tasa hannu ta janyo ta ta haɗa da bango, ta sa itacen ta dinga rafka mata a kai tun tana faɗin ta sake ta har ta gaji ta fara ihu, da kan ta Nusram ɗin ta sake ta Ummi bata ce komai ba.

Tunda ta sake ta, Maman tayi ɗaki bata fito ba a ranar girkin ma Habiba da Sahura suka ƙarasa suma a tsorace suke da Nusram ɗin domin sun san ba halin ta bane.

Baban na dawo ta faɗa mishi aikuwa har ɗaki ya bisu yayi musu shegen duka, wanda har ya jiwa Nusram ɗin ciwo a goshi wannan tabon shike bambace Nusram ɗin da Nusreen ɗin dan be ɓace ba sai dai ya disashe yadda sai ka ƙura idanu zaka ganshi.

Haka da Isa ya dawo ta sake faɗa mishi, shima ya kuma yi musu duka amma tun daga wannan lokacin ta tsorata bata kuma kai hannu ta daki Nusreen ɗin ba duk iya abinda zata yi mata in dai ta san Nusram ɗin tana nan sai dai suyi ta fatar baki, sai dai cewa da tayi tunda haka ne su da aure sai dai suga anayi.

Wannan be dame su ba domin sun san ta Allah ba tata ba, sun gama karatun su na secondry amma babu wanda ya taɓa zuwa sallama dasu.

Nan fa Baban ya kuma takura su da masifa ga Maman tana nata habaicin, Ana haka Habiba da Atika suka sami nasu tsayayyun nan fa gori da masifa ya sake tashi.

Babu me tanka musu sai Nusreen, haka abu yayi ta tafiya har aka zo aka yi biki ƴan dabai sun zo nan suka dinga shan surutu dan ma Nusreen ɗin tana mai da musu.

Bayan biki ne Auntyn Tudu ta bawa Ummi shawara maimakon zaman da zasu yi haka me zai hana su cigaba da karatu wannan dalilin yasa suka fara fafutukar shiga jami'a.

Lokacin da labari ya isa kunnen Baba cewa yayi ba saka hannun shi haka Ummin kan yi wankau da sana'ar ƙulle-ƙulle domin samun na rufin asiri.

Daga haka ma wata rana yace; "shifa ya gaji da ciyar da ƙatti dan haka zai dena bata kuɗin cefane", bata ce komai ba haka taje Dabai tasa aka siyar da shanun da take kiwo guda biyu.

Wanda wannan ne ya saka ta sami kuɗin dasu Nusram suka yi registration sauran kuma ta siyo shinkafa da taliya,macaronic,siga,gishiri,magi wake da sauransu ta fara siyarwa a gida.

Ita kuma dama Nusram ta iya kitso da lalle dashi suke samun rufin asiri, da taimakon Abba( mijin Kaltume) suka sami addmission a nan KASU inda Nusram ke karantar Business administration Nusreen kuma ke karantar Mass com.

Isa kuwa dama diploma yayi akan inter sci ya sami koyarwa a wata makaranta dake kusa dasu nan yake gangara rayuwar shi.

Duk da makaranta hakan besa su Nusram ɗin zama haka ba sukan je wajen Auntyn Tudu su amshi kayan ƙamshi, wato turaren tsinke dana wuta,humra,kwalakca, detol da air freshner su shiga dashi makaranta su siyar.

Abban ya buɗewa Sulaiman plaza inda yake siyar da takalma kayan sawa da sauran su wannan yasa har Takalma da sarƙoƙi sukan amsa su shiga dashi makaranta su siyar.

Suna aji ɗaya a jami'a Sakeena ta sami miji itama aka yi mata aure, wannan karon har duka sai da Baban yayi musu dan haushi.

Rufin asiri dai-dai gwargwado suna samu, Nusram kuwa idan ta sami lokaci har amarya ta kan shirya kwaliyya da komai-komai tana yi sai dai ita ɗin ba ma'abociyar yin kwalliyar bace a fuska sai dai takan yiwa wasu.

Nusreen dai ita tafi son karatun sama da sana'ar hannu wannan dalilin yasa bata cika maida hankali akan komai ba sai dai ta kan taya Nusram ɗin wajen kwalliya.

Wannan shine taƙaitaccen labarin su inda yanzu suke da shekara Ashirin da huɗu a duniya kuma har lokacin basu da tsayayyen saurayi gwara ma Nusreen ta kan samu sai dai tace bata so sai lokacin da ƴar uwar ta ta samu nata mijin.

*CIGABAN LABARI*.

Sai da Nusram tayi jinya na kwana uku sannan ta warke inda Allah ya taimake ta ƙarshen mako ne babu makaranta, Nusreen kuwa haushi ta dinga ji kamar me gashi Ummi ta hanata magana washe gari.

Yau litinin zasu shiga makaranta da wuri hakan yasa suka tashi suka fara aikace-aikace, sai da suka yi wanka suka shirya Nusram tayi wanke-wanke ta share gidan tsaf, Nusreen kuwa ta ɗora musu abin kari, kunu da dankali soyayye.

Nusreen ta fara shiga tayi wanka sannan itama Nusram ta shiga, kamar kullum sai da Nusreen ta fante fuskar ta ita kuwa Nusram bata wani tsananta ba, wani material ligaht blue da ɗigon fari da pink a jiki suka saka, hijab kalar light blue suka saka haka takalmin su.

Shaf-shaf suka karya sannan suka kwashi littattafan su domin tafiya makaranta, Ummi ta miƙo musu ɗari biyar tace; "gashi Allah ya kiyaye hanya", suka amsa da ameen sannan suka fito.

Mama Jummai na gaban murhu tana kwashe koko cikin ƙatuwar roba gefen ta Atika ce ke ɗauraye robobin zuba kokon, Ameera kuma na ƙoƙarin fifita wutar da samanta aka ɗora kaskon suya da mai a ciki wanda hakan ke nuni da cewa na suya ne.

Nusreen ta taɓe baki sannan tace; "ayi dai mu gani aikin banza", Nusram ta balla mata harara sannan tace; "ina kwana Mama?", haɗiye amsar da tayi niyar bawa Nusreen tayi sannan ta amsa gaisuwar Nusram ɗin shima a ɗan ɗage.

Nusram taja hannun Nusreen ɗin suka fice yayin da Mama take cewa; "an tafi yawon ta zubar ɗin ne", suna daf da shiga zauren gidan Nusreen ta juyo tace; "gwara mu fita muke muna yi wasu kuwa har zauren gidan uban su ake biyo su ana dannewa", basu jira me zata bada amsa ba domin kuwa Nusram jan hannun ta tayi suka fice kawai.

A ƙofar gida kan dakali suka sami Baba zaune gefen shi Isa ne, da alamu lissafi suke yi domin ga kuɗi ne ajiye a saman dakalin, Baba na ganin su ya haɗe rai, Nusram tace; "Baba ina kwana?", sai da ya ɗan ja tsaki sannan ya amsa da lafiya, ta juya wajen Isa tace; "ina kwana Yaya isa?", shi kuwa juyar da kai kawai yayi yana wullawa Nusreen harara.

Nusreen ta taɓe baki sannan tace; "Allah ya ƙara wai ke uwar biyayya ni Uwar mutum ma bata ishe ni kallo ba balle shi", daga Baba har Isan suka miƙe suka yo kanta, cikin sauri tayi gaba abinta.

Cikin tsananin jin haushin abinda ta faɗa Isah ya juyo ya kife Nusram da mari, Nusram ta saukar da kai ƙasa sannan tace; "kayi haƙuri Yaya Isa", tana faɗin haka ta juya tabi bayan ƴar uwar ta.

Har ta kusa bakin titi sannan ta tarar da ita, Nusram tayi yaƙe tace; "kai Rim gaki da tsokana ga tsoro, da haka kawai ne da sai na ta haɗaki da Allah akan ki ɗago ƙafa amma da yake kin san kinyi tsokana ai gashi har kin kusa titi", Nusreen tayi dariya tana faɗin; "ai wallahi ba zan tsaya aci zalina ba", haka suka ƙarasa bakin titi suka tari mota suka wuce makaranta.

Koda suka sauka kowa faculty ɗin shi ya nufa, sai wajen ɗaya sannan Nusram ta gama nata don haka tana fitowa ta fara bin wa'inda ta san ta basu kaya suka haɗa mata kuɗaɗen ta sannan ta nufi faculty ɗin su Nusreen.

Taje ta same su suna daf da shiga wata lecture ɗin hakan yasa ta sami garden gefen masallaci ta zauna ta ɗauki litattafan ta tana karantawa.

Basu suka gama ba sai uku, tunda suka fito take jiyo hayaniyar ta, cike da mamakin halin ƴar uwar tata, ta ɗago tana kallon saman steps ɗin da suke tunda hall ɗin a sama yake.

Bata bar surutun ba har suka sauko ƙasa, ita da wata budurwa ne suka bi bayan wata mata wacce daga gani ita sukewa hayaniyar, Nusram ta tashi ta ƙarasa kusa dasu sannan ta kalli ɗayar tace; "wallahi kema Yasmeen kina bani mamaki in banda haka meye na biyewa wannan".

Wacce ta kira da Yasmeen ɗin ta juya idanu tace; "kai Ram ashe haka zaki ce kin san me tayi ne takalmi da sarƙa ta amsa amma har yau bata biya ba kuma sati biyu kenan".

Nusreen ta wullawa matar harara, Nusram ta juya ta kalli matar tace; "kiyi haƙuri Maman Waleed wa'innan sai shiriyar Ubangiji kawai, kada ki damu duk lokacin da kika samu sai ki bada", Nusreen tace; "Ram kin san......", cikin sauri Nusram ta tari numfashin ta tace; "dakata ya isa haka ki dinga yiwa mutane uzuri mana haba".

Maman waleed ɗin ta kalle su ta watsar tace; "ai wallahi kun bani mamaki ashe ƙoƙarin tona mini asiri kuke yi to Allah ya fiku, kuma idan banda ƴar uwar ki wallahi da na bar ɗaukan kayan ki har abada, banza mara mutunci".

Nusreen abin nema ya samu dan haka tace; "tab ashe yau zan naɗawa mata duka nice mara mutuncin", Nusram ta kai mata duka tace; "wai ke me yasa kina girma ne kina hauka matar auren zaki daka??", Yasmeen tace; "koma wacece", Nusram tace; "Dalla ku rufe mana baki ku wuce muje", sai da Nusreen ta doka mata harara sannan ta bi bayan ƴar uwar ta yayin da Yasmeen itama ta bita.

Har suka fita bakin titi Nusram bata kula su ba, haka suka sami mota suka shiga, a Anguwar Mu'azu suka sauke Yasmeen sannan suka wuce.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸


Surayya ta fito cikin shiri, jikin ta sanye da doguwar riga ƴar kanti wacce taji stones ƙanana masu kyau, rigar kalar light blue, ta ɗauki kwalliya sosai sannan duka komai to match ta saka.

Cikin sauri ta sauko ƙasa, Mommy ta kalle ta sannan ta wulla mata harara tace; "kin raina ni ko? tun ɗazu muke zaman jiran ki".

Surayya ta sunkuyar da kai ƙasa tace; "Mum kiyi haƙuri", Brr Farida ta ɗaga mata hannu tace; "ya isa haka, ku wuce muje".

Sai da ta juya ta fara tafiya sannan na lura da kayan dake jikin ta, wata ƴar ubansun shadda ce me tsadar gaske, kalar blue dark, kanta kuwa head ne wanda aka mata ɗaurin steps gashi ya buɗe sosai wuyan ta kuwa murjani ta saka me tsada sosai, ƙaramin space ne sanye a fuskar ɗan ƙarami, jikin shaddar kuwa aikin hannu ne wanda ya fita sosai, mayafi ta yafa a kafaɗa kalar ruwan madara me haske haka takalmin dake ƙafar ta, agogon azurfa ne ke sanye a hannun ta fuskar ta kuwa tasha kwalliya ga wani annuri dake fita duk da irin girma da mulkin ta hakan be hana bayyanar farin cikin ta ba, wayar dake hannun ta take cillawa a hankali kuma kaɗan-kaɗan, cike take da nishaɗi da farin ciki.

Gefen ta kuwa, Fahad ne dake sanye da riga ja da wando blue jeans sai takalmi cover shoe baƙi me kyau, fuskar shi sanye da ƙaton glass.

Daga gefen daman ta kuwa Tameer ne shima sanye yake da ƙananan kaya irin na jikin Fahad ɗin wanda hakan ke nuna kenan anko suka yi, daga shi har Surayya fuskar nan tasu babu wani fara'a.

Tafiya suka yi me tsayi kan su ƙaraso harabar gidan inda take cike da securities maza da mata kowannen su sanye da suit, suna zuwa aka buɗe musu manya-manyan motocin dake jere suka shiga kafin sauran securities ɗin suka shiga sauran motocin, a haka motocin suka fara ficewa daga gidan.

*CANCANGI AIRLINE, KADUNA*, inda suka nufa kenan, koda suka isa wajen basu wani sha wuya ba domin kuwa ana ganin su ake kauche musu daga hanya dan kowa ya san familyn *NAGIMI* cikin Kaduna da kewaye balle kuma wannan da sun san ko wacece wato *Brr Farida Mus'ab Alƙali* ɗaya daga cikin member na *ALƘALI'S FAMILY*.

Ƙasa-ƙasa Tameer yaja tsaki yana me kallon agogon dake ɗaure a hannun shi, kusan da ragowar minti goma sha biyar kafin jirgin nasu yayi landing, cike da jin haushi ya ɗago ya ƙara kallon wajen, kusan kowa idan yazo sai ya kalle su kasancewar burin jama'a kenan ganin wannan ishashshen familyn domin kuwa family ne guda biyu masu ji da kuɗi da izza da taƙama da mulki kowanne ba baya ba wajen iya mulki da kuma ƙasaita sai ya kasance sunyi autayya sun haihu aikuwa abin kallo naga wannan wa'inda jini biyu ya gauraye a jikin su.

Ƙara jan tsaki yayi sannan ya kuma kallon jama'ar dake wajen wanda suka zubo musu idanu, maida kallon shi yayi kan Mummy wacce ke faman murna da farin ciki, cike da jin haushi yace; "ji yadda take murna sai kace Dad ne zai dawo", Surayya ta ɗago ta kalle shi fuska a ɗaure sannan ta nuna mishi hannun ta alamun lokaci.

Ya ɗan tura kan shi inda Mum ɗin take yana mata nuni da tayi mata magana, zaro idanu tayi sannan ta girgiza kai, Mum ta juyo ta kalle ta hakan yasa dole suka ɗan yi yaƙe gudun kada ta zargi komai.

Fuskar tace ta cika da farin ciki jin an fara sanarwa da isowar jirgin, ji take kamar ta ruga da gudu taje ta taro shi, Surayya da Tameer kuwa banda taɓe baki babu abinda suke yi.

Haka mutanen suka fara fitowa ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, yayinda Brr Farida ta ƙara zuba idanu tana jiran ganin ta ina ɗan lelen nata zai ɓullo.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da farouk*.




*ƳAR MUTAN ZAZZAU*



♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*


*ban san wane irin haƙuri zan baku ba, Kuyi haƙuri insha Allahu zamu shiga cikin novel ɗin sosai domin ina fatan komai ya dai-daita zaku dinga ganin shi kullum insha Allahu atleast sau huɗu a sati ko biyar, nagode*

📖📖7-8📖📖


Saukar mari kake ji tasss, kasancewar inda suke kamar hall haka wajen yake, inda aka ƙawata shi da jan labulaye, gashi kuma dare yayi sosai hakan yasa marin ya amsa a ko'ina.

Cikin tsananin fushi da ɓacin rai yake kallon shi, shi kuwa ya saukar da kanshi ƙasa, Appu ya nuna shi cikin karaɗi da gargaɗi yace; "ka kiyayi fushin Oregbu idan ka bari ya fusata zai tsine maka ya kuma cire duk wata alfarma da yayi maka".

kanshi a ƙasa yace; "ina neman afuwar Oregbu sannan kuma fatan hucewar zuciyar ka data Oregbu, nayi iya ƙoƙari na akan ganin na kawo shi nan amma wannan shegiyar matar ta hana gaba ɗaya taƙi bamu dama, amma yanzu tunda zai dawo ina ganin wannan wata damace a gare mu".

Cikin tsananin fushi Appu yace; "baka iya yi mishi komai ba yana can shine zaka wani ce ya kusa dawowa idan ma ya dawo ba zaka iya ba", Tuge ya buɗe baki zai yi magana Appu ya dakatar dashi sannan yace; "a fara gabatar da kwankwale".

Dole Tuge ya dakatar da maganar da yake so yayi ya koma baya, nan suka fara ɗaga hannaye suna wasu irin magan-ganu marasa kan gado, can wani jibgege ya shigo hakan yasa duka suka saukar da kan su ƙasa.

Nan ya fara zuba sassan jikin mutane cikin madaidaicin plate ɗin yana miƙa musu, haka suka hau ci gwanin ban ƙyama da tashin zuciya, su kuwa babu ruwan su daka gani sun riga da sun saba.


🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Cikin ƙasaita yake takowa, saurayi ɗan shekara ashirin da biyar kenan me jini a jika wanda yake da kyau da kwarjini ga kuma cikar zati da haiba.

Dogo ne yana da haske dai-dai gwargwado yana da zubin ƙarfafa, jikin shi sanye da riga kalar Ash da wando jeans blue-black ƙafar shi yana sanye da takalmi cover shoe me ruwan ash, fuskar shi me ɗan faɗi wacce take cike da haiba da kwarjini, me ɗauke da ɗan mitsitsin bakin shi wanda ƙananan haƙoran sa farare tas ke ciki, ɗan sajen shi irin na samarin yanzu wanda yasha gyara shiya ƙara ƙawata fuskar shi, Hannun shi na dama ya ɗago wanda yake da hsske saman fatar cike da gargasa baƙa wacce ta kwanta sai agogon Rolex dake maƙale a hannun ya shafa sumar kanshi wacce take kwance luf baƙa wuluk daga gani tana samun kula ta musamman ya shaƙi iska yana lumshe idanun shi wa'inda suke dama can kamar a rufen domin dogayen lashes da Allah yayi mishi, murmushi ya saki wanda har sai da gefen kumatunshi dama da hagu suka lotsa, haka ƙananan haƙoran shi farare suka bayyana.

Idanun shi ya buɗe a hankali sannan ya fara bin mutanen wajen da kallo a ƙoƙarin shi na gano ina abar ƙaunar shi take, wani ƙayataccen murmushin ya kuma saki sannan ya nufi inda take cikin sauri.

Brr Farida kuwa daman kamar ta kwasa da gudu ta tari ɗan lelen nata haka take ji, cikin tsananin kewa da ƙaunar juna suka rungume juna suna masu tsananin murna.

Tameer da Surayya suka taɓe baki suna juyar da kai cike da baƙin ciki, wanda su kuwa basu san ma suna yi ba.

Brr Farida ta ɗago ta shafa fuskar shi tace; "Welcome back, son", murmushi ya saki sannan yayi peck ɗin ta a goshi.

Hannun su sarƙe da juna suka juyo kowa ya kalle su sai sun birge shi ganin yadda kowanne ke ji da ƙasaita, Brr Farida ta kalli Tameer tace; "ka saka securities su ɗauko kayan", daga haka ta juya suka tafi.

Tameer kuwa kamar ya ɗora hannu a kai ya ƙwala ihu haka yake ji, wannan wane irin masifa ce, idan banda yana shakkar mahaifiyar tashi da ba zai taɓa aikata abinda aka saka shi ba, cike da jin haushi ya fizgi akwatin da kuma ɗaya jakar kamar su suka bashi haushi.

Kan ya ƙaraso har sun shiga mota hakan yasa ya ajiyewa securities kayan sannan ya buɗe motar ya shiga, su kan su securities ɗin sun fahimci akwai abinda yake damun shi dan haka suka kauce suka bashi hanya.

Cikin sauri suka saka kayan duka sannan suka buɗe motocin su suka shiga don zuwa gida, a cikin motar da aka ɗauko shi kuwa, kan shi na saman kafaɗar mahaifiyar tashi, yayin da ita kuma take ta sakin murmushi cike da farin ciki.

Surayya ta kalle su ta taɓe baki sannan tace; "barka da dawowa", kamar ba zai amsa ba tsayin daƙiƙa takwas sannan ya ɗaga mata kai ya maida idanun shi ya lumshe.

Surayya kuwa wani baƙin ciki yazo mata wuya ya tokare idan da ace babu Mommy a wajen babu abinda zai saka ta kalle shi balle har magana ta haɗa su.



Please Login or Register in order to submit comment